Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitar hayyaci take cewa "mena maka? laifin me na aikata agareka daka nemi ka ruguza rayuwata? shin ni ba diyar matarka bace, ni ba tamkar yar jikinka bace? dan ba kai ka haifeni ba shiyasa ka cutar dani? da yar cikinkace zaka iya mata haka?" kuka take mai matukar ciwo tana maganganun nan ita kadai. hawayenta ta share amma ina wani na koran wani ta dora da cewa" na tsaneka tsana mafi muni na tsaneka fiyeda yanda na tsaneka a baya sau dubu, ya Allah kasaka min, ya Allah ki mun hakkin na, akan wanna mara imanin bawan naka" ta karasa wasu hawaye masu zafi suka cigaba da zubo mata sai faman buga kanta take a bango amma sam bata jin zafin hakan kamar zafin da zuciyarta hadi kasanta ke mata, ta kai awannnin uku masu kyau tana kuka hadi da maganganu masu matukar tausayi hadi da taba zuciyar, daga kanta tayi ta kalli sama take idanunta suka sauka kan agogan dakin mai hade da calender, tabass bata manta date din da abun ya faru, sai taga ashe kwananta uku akwance sai ta kuma rushewa da kuka "yanzu kwana uku ban yi sallah innalillahi, ammina ina kike?" tasake rushewa da wani sabon kuka...



toilet ta nufa yayinda take taka kwalaben turaren daya fashe, duk inda ta taka sai ka ga jini amma sam bata damu ba ta cigaba da tafiya, domin tafi jin zafin abunda ya faru da ita fiyeda yakan kwalaben dake shigarta ayanzu, wankan sarki tayi hadi dana sabulu tana yi tana kuka sannan ta dauro alwala ta fito, azaune ta fara rama sallolin dake kanta domin tsayuwar ya gagareta....

bayan ta iddar ta daga hannunta sama "ya Allah ka yafeni, ya Allah ka yafeni, ya Allah na tuba, ya Allah kasaka min abunda mijin ammina yamin ya ubangiji....." sai ta sauke hannayenta ta fashe da wani kuka mai matukar taba zuciya tama rasa addu'ar daza tayi... takai kusan awa daya tana kuka har idanunta wani yaji yaji take jinsa, tana kuma mamakin rashin ganin ammi da bata yi ba, cikin dauriya ta mike domin gaba daya bata da karfi ko daya ajikinta murda kofa tayi domin zuwa sanar da ammi, bata jin zata boye mata bata da kowa daya huce ammi aduniyar nan tana da kuma tabaccin ammi zata kwatar mata hakkinta gun alhaji shettima, shiyasa tun ganin data masa akaron farko taji tsanar ashe shine zai zama silan lalacewar rayuwarta gaba daya ta tsani gidan da duk wani abu daya dangaci alhaji shettima da wanna tunanin ta fita...

sallah ammi ta gama idarwa akurarren lokaci kamar yanda akwanakin nan take yawan yi, sosai hakan ke bata mamaki, burinta yanzu tasa tilon yarta a ido domin rabonta da ita kwana uku kenan, tana kuma mamaki rashin ganin abrar ko dai jikin ne ta aiyana aranta? ninke sallayan tayi kana ta bude kofar...

"Aabaan swerry meke damun ka this days gaba daya baka da kuzari hadi da walwala kuma ba haka na saba ganin jarumin dana ba" mummynsa ta fada tana shafa kwantacciyar sumarsa.

a hankali ya ware labbansa yace "nothing first love"

"don't tell me that son" mummyn ta fada cikin fushi.
sai kuma ta sausauta murya domin kaunar datake masa domin kaf cikin yayanta tafi ji dashi "yanzu akwai damuwar dazaka iya boye min?" ta fada cikin damuwa.

hannunta ya kamo kana yace" trust me first love babu komai kawai gajiyan aiki ne"

"ok fine i believe you my son" ta fada tana sakar masa murmushi.

shima ya kakaro murmushin ya sumbaci hannunta yace" i love you first love"

cikin farinciki mummy tace " love you too"

cikin tafiyar sa ta burgewa ya nufi site dinsa dake gidan domin baya jin zai iya zuwa hospital yau gaba baya jin dadin komai tun daga ranar daya rasata....

mummy na kokarin fita daga dakinta abrar na shigowa, tsayawa ammi tayi tana kallonta yayinda take sakar mata murmushi hadi da ware mata hannyenta alamun ta karaso gareta domin ba karamin kewar yarta ta yi ba, cikin sauri ta rungume ammi hadi da fashewa kuka sosai har da shesheka.


"subha'nala abrar lafiya ko har yanzu jikin ne?" ammi ta tambayeta hadi da dago fuskarta sai alokacin ta lura da yanda fuskar tayi ja hadi da mugun kumburi ga kuma ramar datayi, zaro ido ammi tayi tasake cewa"innalillahi wa innah ilaihi raju'un abrar meke damunki gayawa amminki kinji" kara cukwuikuye rigar ammi tayi hadi da sake rungumarta tace

"A...m...mi mijinki ya keta mun haddi, ya mun fyade yau kwanana uku bazan inda kaina yake ba sai yau..... nan ta shiga bawa ammi labari komai data sani kafin dogon sumanta...


ammi jin maganar tayi tamkar saukar ruwan dalma akunnenta dan bubbuga kunnenta tayi domin tabattar da abunda taji tabass muryan abrar keta amsa kuwa akunnenta "mijinki ne ya min fyade ammi"...

kafadun abrar ammi ta rike da karfi "mekika ce abrar?"
Cikin kuka abrar ta maimaita mata komai kamar yadda tace sai ta dora dacewa "ammi mu gudu mu bar gidan nan, ammi mutafi domin zan iya mutuwa idan wani abu yasake samu na".

wani mugun tura ammi ta mata dahar ta fadi kasan tiles, cikin fushi ammi tace "ban taba tunanin cewa baki da hankali ba sai yau, anya abrar ba asibiti zan kaiki aduba min kwakwalwarki ba, yanzu kiyeyyar da kika wa alhaji har ta kai ki masa sharri, mutumin daya dauke ki tambar yarsa, mutumin daya kula da mu alokacin da muka zo garin dabamu san kowa ba, shi zaki yiwa kazafi" ammi ta karasa cikin daga murya hadi da matsanancin fushi.


Mikewa abrar tayi ta karaso gaban ammi hannunta ta rike hadi da cewa "ammi wallahi da gaske nake, wallahi ammi na rantse da girman ubangiji daddy mijinki shine ya keta mun haddi ke duba ni ammi dan ki tabattar ko ki tambayeshi, da idona na ganshi a dakina ammi ki yarda da yarki ban da kowa aduniya sama dake ammi kitaimaka mubar gidan zuciyata zata yi bindiga" ta fada tana dora hannun ammi a kirjinta dake beating so fast.

kwace hannunta ammi tayi da karfi hadi kifa mata maruka kyakyawa har sau uku ji kake tas! tas!! tatas!!! "wallahi na kara jin kince alhaji ne yamiki fyade sai na cire bakin, yaushe kika fara karya? wato ta nan kika bullo domin mu bar gidan ko? to karyanki ya sha karya, bazaki kasheni da raina ba, kuma kafin in kirga biyar ki bar dakin nan"

wani sabon kukan abrar tasake rushewa dashi har dashewa muryanta yayi ga makogaron ta dake mata zafi ga cikinta sai kugin yunwa yake amma duk hakan be dame ta ba, burinta ayanzu ammi da tayarda da ita
"ammi ki yarda dani, ba karya na masa ba banda kowa sama dake ammi ke kadai ce zaki iya kwatar min hakkina idan baki yarda dani ba ammi waye zae yard..."ko karasa maganar bata yiba amma ta janyota waje hadi danna key akofar. Dukan kofar abrar keyi da iya karfinta tana cewa"ammi ki yarda dani, wallahi shine" haka ta cigaba da fada tana kuka, takai mintuna arba'in azaune abakin kofar kana ta mike tana hada hanya ta koma dakinta...

bayan barinta wajen ammi ta fashe da kuka data rasa ko na menene amma ko alama bata yarda da abunda abrar tace ba, duk da tasan abrar bata karya, amma ta amince a wanna lokaci abrar tayi karya domin bata taba jin ko ganin hakan ba.

"1 WEEK LATER"

"alhaji shettima ne tsaye jikin kofar dakin abrar da misalin biyun dare bayan ya zubawa ammi maganin baccin nan cikin juice batare da ta sani ba, tura kofar ya dinga yi da iya karfinsa yaki buduwa alamun ta rufe kenan gashi ba shida extra key na dakin ta, haka ya juya yana mai jin ba dadi, domin yana son sake kasancewa da ita, baya jin zai hakura da ita ko ta wani hali kuwa...


abrar dake zaune kan sallaya ta rushe da kuka domin tana jin duk abunda yake tama rasa abunyi, domin ko kadan batason sake ganin sa domin shidin abun tsorone, ga ammi bata kulata ko ta gaisheta bata amsa mata, komai ya cakude mata har tunanin guduwa take dawanna shawaran ta kwanta tana lazumi...


kamar kullum tana rufe adakinta ta rame sosai domin bata cin abincin daga ruwa sai lemo shima sai taji cikinta na murdawa alamun yunwa sannan take sha, kallon dakin tayi gaba daya ya dawo tamkar na mahaukaci, domin har yanzu abubuwan data farfarsa da wanda ta zubar kasa suna nan yanda suke haka take takawa yayinda kwalaben ke shigar kafarta amma sam bata damuwa, gashi tayi kokarin guduwa security suka hanata duk da nuna musu tayi cewa abu zata siyo suka ki amincewa sannan suka bata tabbacin alhaji ya ce kada abarta ta fita ko da kofar wajen gate ne, tuno hakan data yi yasa wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo mata, " ya Allah gani ga gareka, ya Allah ka shiga tsakanin na gari da mugu"
mikewa tayi ta dauki tsintsiya ta shiga share dakin, bayan komai ya dawo saiti adakin ta nufi toilet ta wanke sai idanunta suka sauka kan doguwar riga mai kalan sea green tsurawa rigar ido tayi, duk iya tunaninta batasan inda rigar ta fito ba, kuma ita bata da koda mai yanayin rigar ne balle tace nata ne ba, wata zuciyar tace "kika sani ko alhaji shettima ne yasa miki?" Yayinda dayar zuciyar tace " hakan bazai taba yuwa ba, mutumin daya keta min haddi, har zai iya suturta jikinki, bayan shine mutum na farko daya fara ganin sirrin jikinki bayan ammi"

gyada kanta tayi alamun gamsuwa da abunda dayar zuciyar ta raya mata, ga rigar na wani irin kamshi mai sa nutsuwa, wankewa tayi kana tayi wanka ta fito bubu gown mara nauyi tasa, sai ta haye gado ta janyo teddy dinta ta rungume da hannu daya, lumshe idanunta tayi tana tunanin makomar rayuwarta tadau tsahon lokaci tana tunanin kana ta ware idanunta ahankali take ya sauka akan diamond ring din hannunta, zaro manyan idanunta tayi cikin mamaki....




PLS SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


ataya ni share dan Allah🙏

Noor Eemaan✍


https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan

page15-16

ganin diamond ring a hannunta domin ita kwata-kwata bata sa zobe, "toh ya akayi zoben nan ya zo hannuna" ta fada abayyane, sai kuma ta kwabe fuska ganin bata da mai bata amsa tambayan amma koma menene taji kawai ta kamu da son zoben.

zaune yake a office dinsa yana sipping hot coffe a zahirin gaskiya idan ka ganshi zaka yi zatan bashi da ko digon damuwa amma abadi'ni damuwa ce fall cikinsa kawai tsananin dauriya da jarumta ce irin tasa nutse ya dire cup din hannunsa ya bude lockern sa take rigar abrar daya cire mata hadi da ribbon dinta mai kalan red suka bayanna, daga rigar yayi ya tsura mata ido tamkar abrar zata bayyana ajikin rigar ne, rigar ya kai hancinsa ya shinshina yana lumshe ido yana matukar son kamshin rigar domin ba kamshin turare bane, kamshine na ainihin jikinta duk da ya wanke amma kamshin na nan ajikin, ya kai kusan minti goma rungume da rigar kana ya mayar cikin lockern domin kullum da shi yake zuwa aiki haka zalika idan ya tashi da rigar yake tafiya domin baya iya bacci sai da rigar shi kanshi mamaki kansa yake idan yana wandanan abubuwan amma ya alakanta hakan da matsananci tausayin yarinyar da ko sunanta bai sani ba. ajiyar zuciya yasauke hadi da cewa " where on earth are you decent one" sai kuma ya dafe kansa yace" Aaban you re going crazing"...


da misalin karfe biyar na yamma ya tashi daga hospital ya nufi gida, yana hanyar komawa gida aka tsayar dasu a junction sai yaga wata matashiyar budurwa kamar abrar tsaye tana kokarin tsallaka titi cikin sauri ya balle murfin motar ya tsallaka amma sai yaga ba ita bace...
dafe kansa yayi yasake tsallaka titin batare da yace komai, kuma alokacin an bada hannu wasu mutane sai faman masifa suke ya tare musu hanyar hucewa da sauran maganganu, yawan magana baya daga cikin dabi'ansa hakan yasa shi shiga motarsa kawai batare da ya tanka musu ba...
hakan nan ya ji ranshi ya baci ya rasa dalilin sa na yawan damuwar da halittan da bata san yana existing aduniya ba, yayi iya kokarinsa wajen ganin ya manta da ita arayuwa amma ya kasa...

cikin sanyi take tafiya yayinda take murza zoben hannunta, tun daga nesa take satan kallon ammi yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri sauri, zama tayi agaban ammi ta dora hannun ta akafar ammi tace "ammi barka da hutawa"
"lafiya" ammi ta fada fuskarnan a daure.
yawu ta hadiye domin yanzu har wani tsoron ammi take ji, domin tunda ta haife ta bata taba koda yimata tsawa ba balle ta kai ga mari, hawayene suka zubo mata tace "ammi ni zan tafi in yi nesa dake, bazan iya cigaba da zama agidanan ba ammi, na gwanmmace in koma niger wurin maman abbina ko da zata kasheni da zaman gidan nan ammi ki taimaka min" mikewa ammi tayi ta janye kafarta tace" matukar kika fita daga gidanan da nufin yin nesa dani ban yafe miki ba" tana fadin haka ta bar falon cikin sauri....


kuka mai tsuma zujiya abrar ta fashe dashi hadi da kifa kanta akan kujera ta cigaba da rerawa, ana haka sai ga alhaji shettima, taji shigowar mutum wanda take da tabaccin alhaji shettima ne amma sam bata dago kanta ba, ga jikinta sai rawa yake karasowa yayi hadi shafa bayanta yace" relax abrar daddy's girl, you are so sweet, i mean on bed gaba daya kin gujeni tun daga daren mu mai dadi" ya karasa maganar hadi da lashe labbansa

jitayi kamar an watsa mata tafashashen ruwan zafi adalilin shafa bayanta daya yi, kalamansa kuwa tamkar tsukar mashi haka taji akunnenta, take duk wani tsoronsa da take ji ya gudu dago kanta tayi ta tofa masa yawun bakinta tace" tir da budurwa zuciya irin naka SHETTIMA mugu bakin azzalumi Allah ya saka min abunda kamin ka siye ammina da kyakyawan halaiya, amma bata san kai bakin munafiki ne kai ba, mai fuskar biyu" tana fadin hakan ta bar gurin da mugun guda tana kuka...

murmushi alhaji shettima yayi duk da yayi mamakin yanda ta kira sunanshi gatsau ba dan sakayawa, abunda ko mahaifiyarta bata taba yi ba, cikin rashin damuwa ya shafo yawun data tofah masa ya sumbata yace"my sweet abrar, dole in mallakeki ko ina so ko bakya so"....

ammi kuwa tana shiga dakinta ta fada gado hadi da fashewa da kuka tausayin yarta ne fall aranta, musamman ramar data yi wanda ya daga hankalinta amma batason nuna damuwarta afili, sam bataso ta bawa abrar fuskar ta cigaba da cewa alhaji ne yamata fyade domin bazata taba amincewa ba....

sallama alhaji shettima yayi ya shigo dakin da ammi take saurin ta share hawayenta, murmushi dashi kadai ya bar wa kansa sani yasaki kana ya aro damuwa ya yafa afukarsa kamar gaske yace" hajiyata lafiya? gaba daya yanzu baki da walwala ki gaya min damuwarki please"
murmushi karfin hali tayi kana tace " ba komai alhajina, kawai rashin walwalar abrar ne ke damuna"
ta fadi hakan domin bata so koda wasa yaji wanna maganar na sharrin da abrar ta masa.

"kiyi hakuri da ita, kinsan yarinya ce ita wata rana zata daina" ya fada kamar mutumin kwarai, jinjina kai ammi tayi cikin gamsuwa.

washegari ammi na zaune a dinning tana breakfast ita kadai domin alhaji ya fita da wuri yau ta kuma kira abrar tace wai ta koshi gaba daya tsakuran abinci take ta kasa ci ana haka sai ga wayar ta na ringing, dagawa tayi hadi da sallama amsawa ammi tayi hadi da cewa wacece dariya hanan tayi hadi da cewa
"lah ammi baki gane ni ba, hanan ce aminiyar abrar"
"oho hanan ce, kina lafiya ya mutan gidan, iyayen kalau?"
"lafiya lau ammi suke, ga mummyna ku gaisa"
'toh bata"
"assalama alaykum" mummy hanan ta fada
"wa'alaikumu salam, ina wuni hajiya" ammi ta fada.
"ina wuni ammin abrar, ya gida ya ayyuka"
"wallahi alhamdulillah "
"toh masha Allah ina abrar diyata, kullum hanan bata da hira sai na abrar abrar" dariya ammi tayi cikin farinciki domin tana matukar kaunar duk mai son gudan jininta "aikuwa abrar bata nan"
"toh har hanan na cewa a hada ta da driver ta kawota, to ai shikenan ki gaisheta idan ta dawo"
"zata ji in sha Allah nagode kwarai"
amsar wayar hanan tayi tana cewa"ammi ki gayawa abrar ta fara shiri saura sati daya mu koma school"
"toh zan gaya mata hanan" ajiyar zuciya ammi tasaki bayan ta kashe wayar, kwata kwata bataso wani ya fahimci halin da suke ciki shiyasa tace abrar bata nan...


bayan kwana uku da misalin karfe 12 na rana alhaji ya bawa ammin makudan kudade hadi da drivern da zai kaita akan ta yi wa abrar shopping tunda saura kwana hudu ta koma cyprus, yana ganin tashin motarsu ya koma cikin gida direct ya nufi dakin abrar....

tura kofar abrar yayi luckily yaji kofar abude cikin murna hadi da zumudi ya shiga dakin domin daman da biyu ya tura ammi shopping din, abrar na zaune rungume da tedddy'nta ta yi shiru idanunta alumshe, jin an bude kofa yasa ta bude beautiful eyes dinta.gabanta ne yayi wani irin mahaukacin bugawa ganin alhaji shetttima ne, "a'uzubillahi minnar shaitanir rajeem" abrar ta fada cikin tashin hankali hadi mikewa ta nufi kofa domin guduwa tare kofar yayi yana dariya hadi da danna lock, toilet ta nufa da mugun gudu tana kuka saurin janyota yayi hadi da rungumeta, cizo mai zafi ta gartsa masa, saurin sakinta yayi yana shafa wajen, idanunsa sunyi ja, wani lafiyayyen mari ya kifa mata ya tura ta gado ya hau kanta kokarin romancing dinta ya fara yi, amma taki bari ganin tana bata masa lokaci yasashi afka mata hadi da rufe mata baki babu tsoron Allah.....

yana cikin aikata munmunan aikinsa yaji horn alamun su ammi sun dawo, da mugun gudu ya fita daga dakin kayansa ahannu abrar dake kwance tama kasa kuka sai na zujiya daya fi ciwo, gaba daya kwalwalwarta ta daina aiki takai kusan mintuna ashirin akwancen kana ta nufi toilet, sai alokacin wani kuka mai ciwo ya zo mata....

adaidai lokacin kuwa doctor Aaban ke zaune yana duba marasa lafiya jiyayi zuciyarsa tayi wani irin bugu da har ya dafe daidai saitin wajen...


SHARE PLS✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

hey sisters kuyi hakuri nasan wasun ku baku ji dadin abunda alhaji shettima yake wa abrar ba, amma ku sani ko wani dan adam da tasa kalar kaddaran, dan haka ku cigaba da bin alkalamina dan jin ya zata kaya abook din MIJIN AMMINA NE SILA...

kuyi manage pls banda a enough charge banyi editing ba.
love you all guys

noor Eemaan ce😉✍




https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

free book


page17-18

take jikinsa ya fara rawa dan shi kanshi bai san dalilin buguwan zuciyar sa ba ya dau kusan 20minutes a haka kana cikin dauriya ya cigaba da duba marasa lafiyan bayan ya gama ya kwantar da kansa a table, ya zuro hannunsa acikin locker ya ciro rigar abrar yayi matashi dashi tunaninta ne kawai ke kai kawo azuciyarsa yana fatan tana cikin kwanciyar hankali...


"WAYE DOCTOR AABAN"
Aaban abdur-rauf dane ga alhaji abdur-rauf mai fata da hajiya aisha, auren soyaaya iyayensa sukayi alhaji abdur-rauf dan asalin garin adamawa ne, yayinda hajiya aisha ta kasance shuwa arab aaban shine dan su na fari sai kanwarsa mai bin sa amal sai yar autansu hanan, alhaji abdur-rauf babban dan kasuwa ne domin yana hannun jari a companies yawa masu anan gida da kasar waje haka kuma yana da company's daya mallaka na kansa suna matukar son yayyansu, amma aaban shine mafi soyuwa agaresu, sun basu tarbiyya daidai gwargwado iyarsu. Aaban gaba daya karatun sa a india yayi ta idan ka cire primary school dayayi anan abuja bayan wasu shekaru yadawo da dinbin nasarori inda yadawo amatsayin babban doctor, domin har can a india sunso rikeshi domin ya musu aiki amma yaki acewarsa yafison yayi aiki akasar sa ta haihuwa wato nigeria bayan ya dawo alhaji abdur-rauf ya gina masa katafaran hospital, inda anan yake aiki yanzu ya kuma mallaka masa shi halak malak, amal kuwa tana serving ne yanzu a abia state ta kuma karanci banking and finances ne, sai hanan da take karantar law ayanzu, duk da kasancewar boko ta ratsa su amma sam basa wasa da addininsu, a kuma wanna turban suka dora yayansu a kai, aaban kyakyawa kuma lafiyayyen namiji ne mai ji da kuruciya, bashida yawan magana ahaka kuma bayason hayaniya baya kuma shiga abunda bai shafe shi ba, bai taba yin soyaaya ba haka kuma bata burgeshi, bai taba nuna damuwarsa akan wata mace ba bayaga mummynsa, amal, da hanan sai yanzu da tunanin abrar ya hanashi sakat wanda ya alakanta hakan da tsananin tausayinta ne... (LABARIN AABAN ATAKAICE KENAN)


yanzu gaba daya abrar ta dawo so silent kwata kwata bata magana kullum daki take wuni daga ta sha su yoghurt sai lemuka suma sai taji yunwar ta isheta ne kuma yanzu koda wasa bata barin kofarta abude koda da rana ne kuwa, bata da aiki daya wuce kuka domin kullum idanunta basa rabuwa da kumburi, ada har tana cewa bazata koma school ba amma yanzu ta gwanmace ta kuma cyprus ko ta huta da wanna gidan data yiwa lakabi da "bakin gida"....

a yau abrar zata koma cyprus tun karfe shida ta shirya domin flight dinsu karfe takwas zai tashi, burinta kawai taji ta bar gidan duk da tasan zata yi matukar kewar amminta tana kuma fatan watarana ammi ta fahimci gaskiya, da gari ya dan yi haske domin har bakwai da kwata tayi abrar ta fito sanye da turkish abaya red color sai ta yana kanta da mayafin abayan sai black wage shoe dake sanye akafarta duk da tayi rama amma hakan bai hana sihirtaccen kyawunta fitowa ba, yan kayan dazata tafi dasu kuwa tuni daya daga cikin ma'aikatan su kai mota, tana tsaye awaje domin driver yace alhaji yace su dan tsaya can sai ga alhaji da ammi sun fito, kallon ammi take tun daga nesa, cikin tafiyar nutsuwarta ta taka zuwa wajenta dan nesa da ita ta tsaya tace
"amminaaaa"
ammi kuwa jitayi wani abu ya taba zuciyarta, saurin dago kanta tayi taga abrar na sakar mata murmushi yayinda hawaye ke zuba a idanunta, itama ammi kwalla sun ciko idonta amma bata basu daman zubowa ba, ware hannunta tayi alamun abrar tazo cikin sauri ta karosa ta rungumi ammi hadi da fashewa da kuka sai tace "ammi zan tafi kisamun albarka" ta fada cikin sheshekan kuka, hawayen daya zubowa ammi tayi saurin sharewa kana tace"kina tare da albarkata akodayaushe Allah ya bada sa'a" tana fadin hakan ta koma cikin gida domin wani kuka ne ke kokarin kufce mata....

da kallon kauna ta bi amminta kana ta nufi mota, sai ga alhaji shettima ya tari gabanta hadi da cewa"my sweet abrar, zanyi kewarki sosai, anya zan iya hakuri ki dawo kuwa? kinga ya kamata ki kwantar da hankalinki ki bani dama da hadin kai dan in cigaba da dandana zumarki, ina mai tabattar miki ko nawa kikeso, ko mikike so aduniyar nan ni alhaji shettima zanyi miki shi, yakamata ki more rayuwarki domin har yanzun ke karamar yarinya ce kuma kada kiyi tunanin amminki zata taba yarda cewa ni na kusance ki koda kin gaya mata dom......" saurin dakatar dashi abrar tayi cikin tsanarsa haushinsa hadi da kyamarsa tace "an dai ji kunya tsahon najadu kawai, mugu, kana tunanin kazamin hannunka zai sake taba jikina? toh bazan kara barin hakan ta faru ba koda zan rasa raina kuwa kuma in sha Allah sai kaga yanda karshenka zai kasance" tafada cikin muryan kuka kana ta shige cikin mota driver yaja suka tafi....

Bayan isarsu airport driver yayi mata sallama yatafi tana tsaye tana jiran akira sunanta babu jimawa kuwa aka kirata can taji an kira

Please Login or Register in order to submit comment