Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadi da drinks Zulaihat ta kawo wa mu sy, kana ta zauna, aka gai gaisa jiki a sanyaye...

"Jikin Ummi ne ya fara rawa yayinda bakin ta ya cigaba da motsi, cikin mamaki Zulaihat ta ce " ya rabb! Yau Ummi ke kokarin tashi bayan tsahon lokaci?" Ita kanta bata san maganar ya fito fili ba...

"Daman ta jima Bata motsa komai nata?" Ammi ta tambaya hankali tashi.

"Hmm anty Rahilat, ai Ummi ta kai wasu shekaru a haka bata ko motsa jikinta fa" inji Zulaihat.

Cikin sauri Aaban ya tashi ganin matar na ta kokarin tashi, tabbas a matsayin na doctor ya fahimci cewa matar na da karfin hali da karsashi, domin tana cikin ciwon sosai kuma take kokarin tashi...

A hankali ya daga ta zaune, ya dora mata pillow data kwanta a kai kan gadon bayan ta domin ta ji dadin zaman, kuma ikon Allah ta zauna yayinda idanun ta ke kafa kan mutane biyu "Ammi da Abrar"...

Wasu tagwayen numfashi ta shiga saukewa wanda kai tsaye mutum zai fahimci cewa na azaban ciwo ne...

" R...ra..hi...la...t ki... ya...fe...fe...min Ha...ki...ka... Ban...ri...ke Ama...nar ...sa..jee..d... ba.." Ummi tace baki na rawa domin maganar ma da kyar ta fizgo shi...

Kukan mai sautin gaske Ammi ta sa, lallai bawa ba'a bakin komai yake ba, haka zalika duk wanda ya dauke tsananin son duniya ya dora a kanshi yana cikin matsala babba kuwa, ga misali nan kan Ummi .

"Ki...kin...ji...? I...ina ....ji...ka...ta? "

Cikin kuka Ammi ta riko hannun Abrar dake zubar da hawaye itama zuwa gaban Ummi, meya ribar ta idan taki yafewa Ummi? Ko iya haka, ai ta ga ishara tun a gidan duniya, duniyar ma nawa take da wasu mutanen ke daukan ta da zafi, har su sabawa Allah...

"Ni na yafe miki duniya da lahira" inji Ammi.

Sannan ta kalli Abrar tace "diyata ga kakar ki nan, shin zaki iya yafe mata?" Ammi ta tambayi Abrar cikin sigar tambaya.

Kuka Abrar ta saki, kukan tausayin Kansu.

"Ammi idan har zaki iya yafe mata, dole nima in yafe mata, saboda kin fi cutuwa" inji Abrar cikin kuka.

Rungume Abrar Ammi tayi cikin tsananin so hadi da alfahari da diyarta.

Murmushi Ummi tayi wanda idan ka gani zaka yi tunanin kuka take kokarin yi, saboda halin ciwon da take ciki, ikon Allah kuwa wani sauki ta fara ji a jikinta wanda rabon ta da shi tun data fara rashin lafiya nan...


Hannunta na rawa ta ware wa Abrar alamun ta so gareta, kallon Ammi Abrar ta yi, jinjina mata kai Ammi ta yi alamun ta je, karasa jikin ta yi yayinda Ummi ta riko ta izuwa jikin ta.

"Ki...ga...far...ceni... Ji...ka...ta..., na...
Cikin sauri Abrar ta katse ta hadi da cewa " na yafe miki kaka"

Hawaye ne suka fara zubowa Ummi, nadama mai tsananin tsake na ratsa jikinta, ji take dama hannu agoga ya dawo baya, ba shakka da ta gyara kuskurenta, da ta nuna wa Ammi tsananin so, sai dai hannu agoga yayi gaba...

Gaba daya yan dakin sai da suka zubar da hawaye, wanda na zallan tausayi ne, Zulaihat kuwa murmushi farinciki ta saki domin ta san ko ba komai Ummi zata ji sauki ciwon ta, tunda har magana ta fara yi, duk da ta tsani halaiyan mahaifiyar ta, amma tana tsananin son ta tunda ita ta yi silan zuwan ta duniya.

Kallon su Ummi take duk da bakin ciwon da take ciki bai hanata fahimtar tsadaddun kayan jikin su ba, haka zalika kallon daya zaka musu ka fahimci cewa suna cikin daula, fatar su kadai ya isa ya baka labari
"ba shakka su Rahilat sun yi arziki Ummi ta aiyana a ranta"...
Take zuciyar ta ta kara karyewa tana jinjina ikon Allah mai kowa mai komai mai canza komai a duk lokacin da ya so...

" ku...ma... Ku...yafe...min" in ji Ummi tana kallon su Anty Raheenat da yaya Nadeem domin bata manta wulakanci da yi musu suma ba

"Mun yafe miki" suka hada baki wurin fadin haka"

"Wai Zulaihat ina sauran yan gidan ne?" Ammi ta tambaya

Tabe baki Zulaihat tayi kana cikin jin haushin su tace "rabu da munafukai, kin san har da zugin su Ummi ta Kore ku, amma kisan da ta fara rashin lafiya, duk suka gudu babu mai zuwa kusa da ita, yayinda suka fara facaka da dukiyar ku wanda Ummi ta karbe

Wata rana na zo gidan nan, na shiga tashin hankalin sakamakon halin dana ga Ummi ke cikin ciwo da kasanta amma babu ko mutum daya mai kula da ita, shine fa na kira mijina na yi masa bayanin komai ya bani damar zama domin Kula da ita, ni kuma nace musu daga yau kada na kara ganin ko kafarsu dakin nan, sannan kudin na karbe yana wajena, duk da sun ci daga ciki... Numfashi ta sauke kana ta cigaba yanzu haka nasan suna part din su"

"Ki kira su mana mu gaisa" inji Ammi

Kwafa Zulaihat tayi kana tace "wallahi sun ci darajan masu daraja amma da baza su shigo cikin dakin nan ba"


"Ai Zulaihat wanna kudin mun yafe wa Ummi su har abada, bana bukata wallahi, ba kuma fushi nayi ba". Ammi ta fada

" haba anty Rahilat fushi kika yi dai? "

Murmushi Ammi tayi ta ce "Zulaihat da ina fushi kina tunanin zan zo nijer ne?"girgiza kai zulaihat tayi

"Toh kin gani har zuciya ta komai ya wuce, domin har abada Ummi mahaifiyata ce" inji Ammi

Jinjina kai Zulaihat ta yi tana mamakin tsananin sanyin hali irin na Ammi.

"Kira su" Ammi ta sake cewa ganin cewa Zulaihat bata son tashi, domin ta fahimci halin ta sarai, bata son su so dakin.

Da kallon Ammi ta bita da ta zo fita, ba laifi shekaru sun ja hali zanan dutse zulaihat na nan da fushin ta matukar aka tabo ta, girgiza kai tayi tana tuno rayuwar da suka yi a gidan...

Su kai kimanin su 30 da suka shigo dakin, wasu sun tsufa, wasu sun mutu, wasu sai bayan Ammi bata nan aka haifesu, ba laifi Ammi ta shaida wasu, haka su ma sun gane ta, duk da mugun canzawar da ta yi... nan Ammi ta shiga gaisawa da su, a kunya ce suka amsawa suna neman lafiyarta, "tace ta yafe musu"

Yayin da suke cike da zallan mamaki ganin Ummi a zaune, Gaishe su Abrar tayi, take suka gani cewa diyar sajeed ce wanna saboda tsananin kaman su da Ammi, basu wani jima ba suka fita a dakin...

Nan matan gidan suka shiga gyaran wa su Ammi inda zasu kwana, wanda ammi taji dadin hakan kwarai, "ba shakka mutanen gidan sun sanja halayen su... Ammi ta ce a ranta

Kasancewar akwai dakuna da yawa a gidan yasa aka ware wa Aaban daki shi kadai, haka zalika Ammi wanda Hanan tace tare da Ammi zata kwana, haka su Anty Raheenat suma an ware musu komai a wadace...

Kitchen Zulaihat ta shiga domin hadawa su Ammi abincin, binta Ammi tayi kitchen suna girkin su tare, sosai hakan ya sa Zulaihat farinciki, "ashe har yanzu kyakyyawan halayen anty Rahilat na nan?"murmushi mai sauti Ammi ta yi kadai, sai a lokacin Zulaihat ta fahimci ashe zancen zucin ta ya fito fili...

Fita Aaban ya yi daga gidan tare da wani matashin saurayi daya kasancewa dan gidan, wanda a shekaru zai kai 15years, inda ake canza kudi zuwa daga na nigeria zuwa na nijer wato sefa suka nufa(idan ban yi kuskure ba sefa shine sunan da yan nijer ke amfani dashi).

Ba musu yaron ya bishi, domin sosai ya ji Aaban ya burge shi saboda iya wanka sa da haduwar sa, gaba daya kudin daya zo dasu hadi da ATM din shi yasa aka ciri kudi masu yawan gaske kana suka biya babban pharmacydrips, allurai, hadi da wasu magunguna ya siya wa Ummi dan kara karfafa jikinta...

Bayan sun dawo ya bawa yaron kudi wanda zai iya kai dubu40 a kudin Nigeria, sosai yaron ya yi murna domin daman keken shi ya lalace yana son sanja sabuwa...

Direct dakin Ummi ya je, ya jona mata Karin ruwan, kana yayi mata allurai, kallon shi Ummi ke yi, domin sosai Aaban ya burge ta, tana kuma farinciki daya kasancewa mijin jikar ta, hawaye suka gangaro mata, a haka har bacci ya dauke ta, shi Aaban kuwa sam bai lura da ita ba domin hankalin sa naga yanda ruwan drip din ke shiga jikin sa, ya juya kenan domin barin dakin, suka yi kicibis da Ammi, Zulaihat, Abrar da suka shigo dakin hannun su dake da tray, murmushi dauke kan fuskar su duka yayinda suke kallon Ummi...

"Mun gode fa, surikina" in ji Zulaihat Cikin jin dadi.

Murmushi kawai yayi kansa na kasa ya karasa fita a dakin, domin bai so sun gan shi ba, domin ba ya son ana masa godiya

Murmushi Ammi ta saki karo na biyu yayin da take alfahari da samun suriki na gari a ranta.

"Maza Abrar kai masa abincin sa" inji Zulaihat tana kallon Abrar dake sakin murmushi ba adadi, zallan soyaayyar pure heart dinta na ratsa ta...

Dai dai ta nutsuwar ta yi hadi da cewa "toh" kana ta fita

Kitchen ta nufa, ta hada masa komai a tray kana ta nufi dakin da yake

Yana kwance rigingine kan madaidaicin gado dake dakin, jin muryarta ya sa shi mikewa tsaye hadi da karban tray din hannunta ya ajiye, kana ya yi mata masauki kan faffadar kafadar sa, yana sakar mata Sumba a wuya, hadi da furta "I love you"

Kwalla so da tausayin sa suka Ciko idanunta, "I love you too, my pure heart"

Nan suka ci abincin su, suna hirar soyaayya, bayan sun gama ta fitar da kwanuka, da dadare kuwa ai fadan wurin kwanciya Abrar da Hanan suka yi, ita Abrar ta ce dakin inda aka sauke Ammi zata kwana yayinda Hanan tace sai dai ta tafi dakin mijinta ta bar ta da Ammi.

Sosai Ammi ke musu dariya, domin tamkar yan biyu haka suke wani zubin, daga karshe dai Ammi suka saka a tsakiya, suna gefe da gefen ta a haka suka yi bacci...

Kwanan su Ammi biyar suka yi sallama da nijer, sosai jikin Ummi ya yi sauki, domin har magana tana yi sosai, kullum bakinta baya gajiyawa da neman lafiyar su Ammi, Zulaihat ma tayi musu alkawarin kawo musu ziyara nigeria, kuma sosai Abrar ta zaga dangin abbin ta kafin su taho, yayinda dukkaninsu sai da Aaban yayi musu kyautar kudi mai tsoka kafin su taho, domin saboda su dama ya canza kudin zuwa sefa....


"NIGERIA"

Kwanan su biyu da dawowa aka shigar da kara kotu, da yammaci aka kawo wa alhaji Shettima takarda sammaci... Gaba daya ya sake lalacewa sai uban tumin sa hadi kansa mai dauke da tsanko dake ta shining (kyalli) zufa ke ta keto masa kamar yana gidan buredi, duk sanyin AC dakin ji yake kamar wuta ke ratsa jikinsa...

"Bazai yu ba, mutuncin na zube ba, dole in dauki wani mataki domin tsira da mutuncin da nake da shi a idon jama'a, kwara na koma kauyen mu in da ba za su yi tunanin can na jan ba har komai ya lafa" (what!? Readers daman alhaji shettima na da kauye? Kenan karya ya shararawa ammi? ku dai cigaba da bin alkalamin Noor😉✍)

Wasu files dinsa da takardun sa masu muhimmanci ya hada Cikin wani dan jaka, kana ya bar gidan ko mota bai dauka ba, domin so yake ya gudu ya bar garin yayi nesa da abuja ya koma wani gari ya kafa sabuwar rayuwar sa domin bai shirya kar ban tozarci ko kunya a idon duniya ba...

Cikin sauri sauri yake tafiya yayinda yake ta waiwayan bayan sa tamkar wani zautacce ko mara hankali, ana Cikin haka wani mai Babur ya taho da gudu ya buge sa , take ya fadi kasa yayinda jini ke fita a kafar sa sosai da alama a kafan ya ji ciwo, waro idanu mai mashin din yayi domin sarai ya gane shi....


Comment✔
Share✔
Vote✔
Edit❌



Kun ga na yi muku mai yawa ko? Toh kuma ku kyautata min ta hanyar yin min sharhi👌😊



fri jul 30 2:21am


✨MIJIN AMMI NA NE SILA✨
(A heart touching story)

written by Noor Eemaan
wattpad username @NoorEemaan


Juma'at Mubarak to you all my lovely fans, Alkhairin Allah ya kai muku a duk inda kuke.😘


ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Page 65-66

_________________📖 "tabbas wanna shine mutumin dana kai wa takardan sammaci ba jimawa gidan sa, toh meya fito yi dashi, ga yanayin sa ya nuna bashi da gaskiya" matashin ya fada a ransa yana kallon alhaji Shettima da ke cikin halin azaba, sam baya fahimtar kowa da komai.



Babur din sa ya bawa wani mai shago ajiya kan cewa zuwa dare zai zo ya dauka, kana ya tari mai adaidaita sahu, suka kama Alhaji Shettima aka sa shi ciki dan sahun kana suka nufi asibiti....



Direct emergency aka kai shi, suka yi treating ciwon nasa, kana suka kai shi dakin hutu, matashin nan mai suna Mansur kuwa direct gidan alkalin da case din ke hannun shi ya nufa domin sanar da shi halin da ya tsinci alhaji Shettima, kana ya bashi jakar takardun da tsinta a tare da shi....



Jinjina kai alkhali yayi domin a matsayin sa na alkhali ya fahimci wasu abubuwan...take ya bada umarni aka zuba yan sanda ciki da wajen asibitin domin gadin alhaji Shettima, haka alhaji Shettima ya kai kwana ki goma sha biyar cikin asibiti wanda zuwa lokacin ya fara taka kafar tasa.
police station aka kai shi sai da ya shafe kwanaki 5 Cikin cell wanda ba karamin azaba ya sha ba....



"RANAR SHARI'A"

Kotun cike yake da su, Abrar, Aaban, Hanan, Amal, Adam, Ammi, anty Raheenat, yaya Nadeem, mama, baba, (wanda yanzu ya ji sauki jikinsa) Mummy, Daddy.

Ta wata kofar a shigo da alhaji Shettima gaba daya ya sake fita hayyacinsa babu kyawun gani, tumbin sa yayi kasa alamun babu sauran jin dadi da Hutu, kansa na kasa kunya mai yawan gaske na saukar masa...

Nan mai gabatar wa ya karanto laifi Alhaji Shettima, domin su Aaban basu dauki lauya ba haka alhaji Shettima... Gyara zaman gilashin sa mai shari'a yayi kana ya ce "alhaji Shettima ana tuhumar ka da yi wa Abrar diyar matar ka fyade, shin kana da ja ko ka aikata?"...


Shiru kotun ya dauka baka jin motsin komai sai sautin kukan Abrar dake tashi sosai, saboda tuno komai da ya faru, Aaban dake gefen ta ya kasa cewa komai saboda yanayi da yake ciki...

Sun dauki mintuna biyar kyakyyawan ba tare da alhaji Shettima ya ce komai ba, haka kawai yaji bakinsa ya kasa motsi, cire gilashin sa mai girma mai shari'a yayi, domin baro baro alamun rashin gaskiya ya bayyana a tattare da alhaji Shettima, kallon shi yayi na yan mintuna kana Cikin hikima ga shiga gaya masa illar zinah hadi da azaba mai tsanani da rabbul samawwati ya tanadar wa duk wanda ya aikata zina kasancewar mai shari'a na da ilimin addini mai zurfin gaske....

Abun mamaki jikin alhaji Shettima yayi wani sanyi kalau, sai yanzu nadama hadi da matsanancin kunyar gamuwan shi da Allah ya saukar masa...

Dago kansa yayi yayin da muryan sa na rawa gwanin tausayi yace " ya mai girma mai shari'a duk abinda kace, nina aikata su, da kaina nayi wa Abrar fyade, yarinyar da zan iya haifa a cikina, hakika na cutar da Abrar da ma Rahilat... Ya karasa yana zubewa kasa yayinda wasu zafaffan hawaye suka zubo masa gwanin tausayi, shi kanshi bazai iya tuna when last da yayi kuka a duniya ba....

"Alhamdulillah! A bisa rashin wahalar da kotu da baka yi ba, kotu ya yanke maka hukunci kisa ta hanyar jifa, har Allah ya karbi ranka, haka Allah ya yanke hukunci wa duk wanda ya aikata zina, alhalin yana da aure, don haka hukunci ka kenan, Allah zai yafe maka wanda laifi daka aikata na zina matukar aka jefa ka ta hanyar jifa, ko da a ranar tashin alkiyama, ubangiji bazai tuhumeka kan wanna laifin na zinah ba Allah ya tsare imanin mu"


Kallon Abrar yayi yace " Abrar Sajeed Aaban, babu hukunci daya hau kanki kamar yadda yake a shari'a kasancewar ba da son ranki komai ya faru ba.

"Sannan zaka saki Rahilat kamar yadda ta bukuta, domin tana da hujojji masu karfi" mai shari'a ya fada

Kuka mai suna kuka dukkansu keyi banda Aaban da idanunsa suka yi jajur tamkar gauta, kukan Abrar din shi ya fi komai dakula masa lissafa gashi ya kasa hana ta kukan, domin ko magana ma bayason yi.

Haka mai shari'a ya buga guduma kana ya tashi, alhaji Shettima abin tausayi wani kuka mai sautin gaske yake har da majina, nadama mai tsananin yake ji, yanzu ina jin dadin ya kai shi? Ga abin da son zuciya ya janyo masa...


**************************************


Tsaye suka a inda za'a binne shi, gabaki dayan su idanunsu yayi luhu luhu saboda kukan da suka sha, yayinda gefe mutane ne tsaye masu yawan gaske da basa su lissafu ba, wanda sune zasu jifi alhaji Shettiman, gaban Ammi ya durkusa ya ce "Hajiyata!" Sai kuma ya fashe da kuka haka ma Ammi, goge majina yayi kana ya cigaba "ki yafemin ko na samu salama a kabarina ya fada yana nuni da ramin da aka yi domin shi... Hakika son zuciya bacin ta, ga abinda son zuciya na ya jawo min, kiyafemin dan Allah na tuba! na tuba!! na tuba!!! Hajiyata kice kin yafe min".

Kuka mai sauti Ammi ta saki yayinda ta yi kasa itama tace " Alhaji na yafe maka, duniya da lahira"....

"Nagode hajiyata, har duniya ta dane, ina sonki, a yau zan bar duniyar nan mai cike da rudu, amma ko a cikin kabarina ne ina so ki san cewa kina nan a raina" alhaji Shettima ya fada yana buga kirjinshi da karfi...


Majina ya sake ja a karo biyar kana ya cigaba " na yi miki Karya cewa bana da iyaye, haka na taso ni kadai, toh ba gaskiya bane, ina da iyaye a kano rimin gado a kauyen atawa, na gudu na barsu ne sakamakon wani laifi tana aikata"

Cikin kuka Ammi ta zaro ido, domin bata taba tunanin haka ba, "wani laifi ka aikata?" Ta tambayeshi.

"Akwai wani saurayi mai suna Habu da muka yi fada, dan mai garin kauyen mu ne, wanda na caka masa wuka a gefen cikinsa sakamakon musu da muka yi kan abinda bai taka kara ya karya ba amma, shaida ya ribace mu har ta kai mu ga fada... na dai barshi cikin matsanancin hali na gudo domin nasan idan aka kama ni hukunci mai tsananin zan karba, amma ban sani ba ko ya mutu ko yana raye, haka zalika ban sani ba ko iyayena na raye har yanzu... Ya fada cikin kuka sosai,,, Sannan ina sana'ar shigo da basara/giya wanda maganar da nake miki su kwaro ma'ana yaran aikina suna hannun hukuma...ya karasa cikin rawar murya sannan ya cigaba da cewa

" Hajiyata, zaki iya zuwa kauyen mu ke nema min yafiya wurinsu iyayena, da iyayen Habu da ma kan shi Habu'n idan yana raye ko hakan zai sa na samu kwanciyar hankali a gidana na gaskiya (kabarin) sunan mahaifina malam Ahamadu, sunnan innah ta kuma juwariyya" ya karasa maganar cikin sigar tambaya

Duk da dumbin mamaki daya cika ta bai hanata yin magana ba"Zan je, na yi maka alkawari Alhaji" inji Ammi cikin kuka sosai yayinda haushin da tsanar sa na barin zuciya da gangar jikin ta...

"Nagode hajiyata, you re love forever, ina son ki sosai, na sake ki saki biyu, Allah ya hada fuskokinmu da Alkhairi a darul salam" yana fadin haka ya nufi wajen Abrar dake sake tsaye gefen Aaban tana kuka sosai...

"Daddy's girl?" Ya kira Abrar kunya, nadama, mara amfani na saukar masa, I no bana da darajan daya cancanci ki yafe min, amma ina rokon ki dan darajan Allah da annabi s.a w ki yafe min ko na samu kwanciyar hankali a kushewa ta, nasan na cutar dake cuta mafi muni wanda hardly ki manta a rayuwar ki, amma ki taimaka ki yafe min" ya fada yana kokarin yin kasa....

Cikin kuka tace "Daddy!" Sai kuma ta sake rushewa da kuka, cak! Alhaji Shettima yayi, ya kasa durkusawa a kasa ya kuma kasa mikewa saboda zallan mamaki da yake ciki, bai yi tunanin zata sake kiran sa da sunan da bai cancance shi ba, amma har kagon zuciyar sa ya ji dadin sunan kwarai,

Cikin nadama ya ce "da gaske daddy's girl, kin kira ni Daddy, am your Daddy? Are you sure what you just said came out from the innermost part of your heart" alhaji Shettima ya fada tana hawaye..

Jinjina kai tayi yayinda hawaye suka cigaba da zuba a fuskar ta, jin kanta take kamar zai fashe saboda wani mugun Sara mata da yake yi... Kana tace "na yafe maka duniya da lahira Allah yasa ka kwanta cikin sallama da kwanciyar hankali a kabarin ka...

"Allah ya miki albarka" yace hawaye masu zafin na zubo masa, yayinda yake jin wani nauyi na raguwa a zuciyar sa...

"Ka yafe min kai ma dan Allah, na shiga gonar da ba tawa ba" ya fada yana kallon Aaban cikin kunya.

Matse hannun Abrar dake cikin nasa yayi kana ya daga masa kai kawai...

"Nagode" alhaji Shettima ya fad'a.

Kana ya kalli alkali yace "ya mai girma mai shari'a ku shaida na mallakawa Abrar dukkanin dukiyata duniya da lahira... na..."

"Nagode, amma bana bukatar duniyar ka, zan dai amsa na gina, asibitoci, gidan marayu, da sauran su duk wani aikin lada domin Allah ya kai ladan gareka" Abrar ta fada cikin kuka

Hawaye ya share kana ya ce "ba komai, nagode miki sosai, hakika hajiyata ta yi miki tarbiya mai kyau, ki dinga yi min addu'a kinji"...

Jinjina kai tayi saboda kukan ta da ya karu.

A hankali ya fara tafiya yana tunkarar ramin sa, hawaye ke zuba kan fuskar sa, tsoro mai tsanani na lullube shi domin bai san a yadda zai fuskanci ubangijin sa da tarin munanan aiyukan sa ba...

Yana shiga ramin ya fashe da wani sabon kuka, kana ya shiga daga wa su Ammi hannu, hawaye hadi da murmushi da ya fi kuka ciwo na zubo masa
" zan yi kewar ku sosai" yace yana cigaba da daga musu hannu kana mutanin da aka tanada suka fara jifan alhaji Shettima da dutse....

Sunan Allah hadi da istigifari dauke a bakinsa, rungume Aaban Abrar tayi domin ta kasa kallon alhaji Shettima, yayinda tsoron Allah mai tsananin na ratsa ta da ma dukkanin mutanen da ke tsaye a wajen, shima rungume ta yayi sai yanzu wani kwalla ya zubo masa, domin duk rashin imanin mutum dole ya ji tausayin alhaji Shettima, duk da a baya yana matukar kishi da alhaji Shettima sannan ya tsane shi, amma yanzu ya yafe masa...

Tun yana tsaye kan kafafun sa, har ya zube kasa saboda galabaitan da yayi yi... Daga karshe ya yi Kalmar shahada kana ya daina motsi, alamun ya amsa kiran ubangijin sa...

Wasu mutane ne suka zo suka rufe shi da kasa gaba daya, a hankali gaba dayan su suka isa ga kabarin nasa suna kuka, addu'a duk suka yi masa kana Daddy ya bawa masu gyara kabari kudi kan cewa su gyara ma'ana su yi siminti domin kada ruwan sama ko wani abu ya burma kabarin, har da wasu Karin mutanen100 da kabarinsu ya lalace sosai, ya biyawa domin a gyara, take mutanen suka fara aikinsu...

(Ya jama'a mu kasance masu taimako musamman wa marasa hali/kudi, wallahi idan kaje makabartu dole ka zub da kwalla, mutanen da dama kabarin su ya lalace, wanda basu da halin gyarawa, amma wasu na da arzikin biya domin a gyarawa yan uwa muslimai amma basa yi, masu arziki da wadata ku taimakawa mara sa shi, ta haka zamu cigaba da gina kyakyyawar al'ummah, hakika taimako abu ne mai kyawun gaske da baka san ta wace hanya Allah zai biya ka ba, Allah ya bamu ikon taimakawa juna).


Haka suka bar wajen jikin kowannen su a sanyaye tsoron Allah na ratsa su, yayinda hawaye yaki barin fuskar su, kwara ma mazan cikin su. Duniya kenan duk wanda ma ya dauke ta da zafi har ya sabawa Allah toh ba shakka karshen sa da kallo, mummy ke wanna tunanin...


*************************************

Kwana bakwai da mutuwar alhaji Shettima, Ammi ta je har kano tare da rakiyar yaya Nadeem da Anty Raheenat, basu sha wani wahala ba suka gano gidan. Gidane mai zagaye da langa langa, kallo daya zaka yi wa gidan kasan cewa masu

Please Login or Register in order to submit comment