Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

at you like this..." Ya fada idanunsa cikin nata.

Murmushi ta sakar masa yayin da kwallan suka cika idanunta, kwallan farincikin samun gwarzon namiji daya tamkar da dubu, mai son farincikin ta.

"I love you" tace a kunya ce.

"I so much love you too, with all my heart" kana yace "no more talk, cinye naman ki ok?"


Jinjina masa Kai tayi, murmushi kan fuskar ta cigaba da cin naman ta, bayan ta cinye duka domin ko daya bata bari ba, tambayar ta yayi a karo mata ta ce a'a ta koshi, bill dinsu ya biya suka bar wajen... A hankali yake driving lifan din, yayinda suke hirar su ta soyaayya har suka isa gida....



" BAYAN KWANA BIYUI"

Bayan duk sun gama breakfast, gaba daya duk sun dawo falo suna hira, Hanan sai tsokanar Abrar take, amma ta kasa mayar mata saboda kunyar su mummy. "Hanan ki kiyaye ni fa, daughter dawo nan kusa dani ki zauna" Mummy tace tana yiwa Hanan hararan wasa, a kunya ce Abrar ta dawo kusa da Mummy ta shige jikinta, tana yi wa Hanan kwalo a fakaice...
Kallon so da birgewa Aaban ke binta da shi, yana farincikin yadda Mummy ta dauke ta a matsayin y'a da suruka a yanzu.


Wayar Mummy ce ta fara ringing, murmushi dauke kan fuskar ta ta daga kiran sakamakon sunan Amal da ta gani a rubuce kan screen di'n wayarta, "lafiya Amal na ji muryar ki haka?" Daga bangaren Amal kuwa sanar da Mummy tayi cewa mahaifin Adam ya samu hatsari yau kwana biyu, salati Mummy tayi kana ta shiga fada kan rashin gaya musu da Amal bata yi ba tun ranar da abin ya faru ba, haku'ri ta bawa Mummy hadi da bata uzurin cewa bata da nustuwa shiyasa bata sanar musu da wuri ba....



"Toh shikenan, muna nan zuwa, wani asibiti kuke?"

"Ai muna gidansu Adam, domin baban yace ba ya son zaman asibiti likita ke zuwa safe, rana, dare duba shi" ta karasa cikin sanyi murya da alama basu shirya da Adam din ta har yanzu ba..

"Allah ya tsare gaba"

Da " ameen" Amal ta amsa tana katse wayar...

"Mummyn'su meke faruwa ne?"

ajiyar zuciya Mummy tayi kana ta sanar da shi, jajantawa yayi kana ya umarce su dasu shirya domin zuwa duba majinyanci.


Kasa da awa daya duk suka shirya tsaf kana suka dau hanyar zuwa gidan su Adam, tun a hanya zuwa gidan gaban Abrar ke faduwa Wanda bata san dalili ba...

Bangaren Amal kuwa, a sanyaye ta sauke wayar daga kunnen ta, tana kokarin komawa dakin da aka kwantar da baba, domin wayar da zata yi ya sanya ta fitowa
daman, Kicibis suka yi da Adam dake kokarin fitowa, dauke kai yayi tamkar bai ganta ba, Wanda hakan ya sanya ta fito da kwalla "sweet Adam" ta kira shi, "lafiya" yace ba tare da ya juyo ba, ta baya ta rungume shi tace "ka sausauta min wanna hukunci ya yi min tsauri, na tuba" ta karasa tana sakin kuka...

Kamar kukan bai dameshi ba, haka ya zareta daga jikinsa ya bar wajen... Sai dai sosai kukan ta ke damun shi, yayi haka ne saboda gaba, tasan cewa dan Adam ba abun wulakantawa ba ne, a duk halin da yake ciki tunda Allah da kanshi ya karrama dan Adam, wane mutum yace zai wukalanta shi saboda wani dalili nasa Maras tushe....

Da kallo Amal ta bishi tana share hawayen fuskar ta tana fatan ya sauko su cigaba da rayuwar su yanda suka saba, domin ta gasu hakan nan, ta kuma dau darasi, dakin ta kamo, ta yi wa su Ammi sannu kana ta zauna kan ta a kasa, "ya haka Amal ki saki jikin ki mana, ko bakya jin dadi ne?" Ammi ta tambaye Amal tana kallonta.

Kunyar ammi mai yawa ce ta dirar mata, domin tasan cewa anty rahilat na sonta sosai, ta yaya ita kuma ta ki jinin ta a baya? Tabbas babu wata uwa da zata so hakan, ajiyar zuciya ta sauke tace"Anty babu komai" ta ce tana murmushin yake.

"Toh ai shikenan" Ammi ta ce tana mikewa hadi da cewa "bari na dauko miki mutumin ki nasan ma yayi sanyi yanzu( tana nufin kunun aya, kasancewar Amal na son shi)ammi ta karasa tana barin wajen, jinjina kai Amal tayi tana jin zuciyar ta na karyewa.

Barin Ammi dakin, yayi dai dai da shigowar su Daddy Wanda Adam yayi musu jagora har zuwa dakin inda majinyacin ke kwance...


kuyi manage kafin gobe, wallahi bacci nake ji sosai, daurewa nayi domin farincikin ku, much love my people.😘

Share✔
Vote✔
Comment✔
Edit❌


NoorEemaan
07082281566


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

Written by NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍


Wanna page din sadaukarwa ne ga mahaifiyata (mahmah) dama sauran dukkanin uwa a duniya, Allah ya saka muku da gidan aljanna. being a mother is not easy at all.👌💞


59-60

#mother's love



.....sallamar su ce ta sanya su mama lura da shigowarsu, "lale marhabun" anty raheenat tace, amsawa suka yi yayinda kan Abrar ke kasa domin wani faduwar gaba take ji sosai....


zama duk suka yi, kasancewar dakin da na girman gaske ya sa ya ishe su a wadace, banyan gaishe -gaishe da ya wakana a tsakaninsu hadi da tambayar ya mai ciki? cikin mutuntawa suka amsa har da mara lafiyan, yayinda Adam ke ta Addu'a akan Allah ya fito da Anty rahilat, baya so ya ce komai, yayi imanin cewa matukar ta fito zata shaida yarta... kasa hakuri ya yi ya kalli yaya Nadeem yace
"uncle nadeem ina anty rahilat?"
"tana zuwa taje daukowa Amal kunun aya" ya amsa, wani bugawa kirjin Abrar ya sake yi sakamakon jin sunan amminta....


a hankali Aaban ya ce " wiffy, ke kwanatar min da hankalin ki please, menene yake damunki? ga zuciyarki na bugawa" ya fada yana kallon saitin kirjinta, wanda idan mutum ya lura sai ga yanda yake bugawar da sauri sauri...


"Assalama alaykum " Ammi ta ce tana shigowa hannunta dauke da tray mai dauke da kunun aya mai sanyi hadi da glass cup.

Cikin kaduwa, zallan mamaki, farinciki ta dago kanta a dalilin jin muryar Ammin ta, tabass ko a magagin bacci, ko mafarki taji muryar Amminta zata gane, balle a zahiri...

Cikin sauri ta mike wanna sai a lokacin su Anty Raheenat suka lura da ita, tsananin mamaki ne ya kama su ganin mai kama da Rahilat...

"Ammina!" Ta ce cikin sauti kuka hadi da mamaki...

A firgice Ammi ta dago kanta sakamakon jin muryar diyarta, farincikin ta, zaro ido ta yi kana tray din hannunta ya zube kasa take komai ya tarwatse kasancewar mug din na glass ne, da mugun gudu Ammi ta nufeta ta na kiran "Abrarrrr!" Haka zalika itama Abrar ta nufi Ammi da gudun gaske...

cikin zafin nama Abrar ta dale jikin Ammi, kan centre carpet suka zube, sai dai sam hakan bai dame su ba, ba su kuma ji ciwon faduwar ba, kuma har yanzu suna rungume da juna suna kuka mai taba zuciyar mai sauraro, mikewa Abrar ta yi ta mikar da Ammi tsaye, riko fuskar ta Ammi ta yi tace "Abrar diyata, kice a gabana? Ko gizon da idanuna suka saba yi min ne?" Ta fada tana kara rungume...



Cikin kuka har da shesheka Abrar tace "ni ce Ammina, ni ce diyarki Abrar"... Sun kai tsahon lokaci suna kuka ba tare da kowa yace musu komai, domin duk sun fahimci komai, ba shakka sun cancanci yin kuka ko zuciyoyin su zai samu saukin daga radadin da suka yi ta fama da shi tsahon wanna lokutan....


Ganin cewa sun ki daina kukan yasa mahaifin Adam dake kwance yin murmushi kana cikin muryar marasa lafiya yace " haba Rahilat, ya zaki biye mata kuna kuka? Bayan murna ya kamata ku yi, domin ranar da kike dade kina fatan zuwan sa kuma gashi ya zo"... Sausauta kukan suka yi, mahaifin Adam ya sake cewa "ku zauna" ba musu Ammi ta riko hannun Abrar ta zauna kana ta dora Abrar kan cinyarta, hadi da share mata hawaye da majina, sosai ta rike Abrar a jikin ta domin gani take zata sake rasa diyarta a karo na biyu...

Kwallan farincikin ne suka cika idanun Adam yayinda tausayin su ya cika zuciyarsa, murmushi yasaki hadi da ajiyar zuciya ganin Anty'nsa ta hadu da gudan jinin ta...

Aaban idanunsa a lumshe, yana jin radaddin kukan ta har kahon zuciyarta, wani bangaren kuma ya fi kowa murnan ganin wanna ranar, decent one dinshi ta daina kukan rashin ammi"...

Gyaran murya yaya nadeem yayi yace "Alhamdulillah dukkannin yabo ya tabbata ga Allah wanda ya nufe mu da ganin wanna ranar. " Rahilat ko zaki gaya mana ta ya ya kika kubuta daga hannu alhaji Shettima? " yaya Nadeen ya fada, duk da cewa ta basu labari a baya ya yi tambayar ne saboda su Abrar su ji, nan ta sake fada musu, sosai Abrar ta yi kuka, kukan tausayin Ammin ta, ashe rashin imanin alhaji Shettima ya kai haka? Ta aiyana a ranta.

Nan zance ya sake dawowa sabo, sosai aka sake yi wa Ammi fada mai hade da nasiha, ba ma Ammi kadai ba dukkanin su jikinsu yayi sanyi sakamakon jin nasihar da yaya Nadeen yayi mai ratsa zuciya..

"Abrar daga barin ki gidan alhaji Shettima cikin Daren nan, ina kike je? hannu wa kika fada?" Yaya Nadeem ya sake tambaya

Cikin kuka Abrar ta gaya musu komai, sai dai bata fada musu tana aure ba ta boye hakan saboda kunya, sannan bata san ya Ammi zata dau auren ba shin zata yi farinciki ko akasin haka?


Godiya mara iyaka su Ammi suka dinga yi wa su Mummy abisa rikon amana da su ka yi wa Abrar, Mummy kam har wani kunya ta ji, saboda irin godiyar da suke yi,"ba shakka dan Adam ba abin wulakantawa bane a duk halin da yake ciki, ni kam na dau darasi" Mummy ta aiyana cikin ranta...


Hawaye na bisa fuskar Amal ta karasa wajen Abrar ta nemi lafiyarta, ko aya Abrar bata bari ta kai ba ta tace ta yafe mata, haka zalika Mummy tun kafin tayi magana Abrar ta yi saurin rungume ta, kana a hankali tace "mummy ni diyar ki ce bai kamata ki nemi yafiyata ba" Abrar ta fada cikin girmamawa sukarta, sosai hakan ya yi wa Adam dasu Daddy dadi ganin komai na daf da zuwa karshe...

"diyata Abrar zaki iya yafewa Ammi ki, nasan ni mai tarin laifi ce a gareki, amma nayi nadama diyata" Ammi tace tana zubar da hawaye, cikin Abrar tace " ni baki min komai ba Ammi, bana fushi dake, kece komai nawa ina sonki sosai Ammina"... Ta ce tana kara rungume Ammi.

Kuka Ammi ta sa, kaunar yarta mai yawa na ratsa zuciyar ta, yayinda tsanar Alhaji Shettima ke kara yawa a zuciyarta...

"Ooh Abrar ko ta mu bakya yi ko?" Anty raheenat tace cikin zolaya.

Cikin jin kunya tace "kuyi haku'ri" kana ta shigar da kanta jikin Ammi, wanda sosai hakan ya basu dariya... Murmushi farinciki Ammi ta yi kana ta ce

"Abrar nasan kin manta dasu anty da yaya Nadeem ko?" Jinjina kai Abrar tayi domin bata ganesu ba saboda shekarun da yawa, nan Ammi ta shiga yi mata bayanin su daya bayan daya, cikin jin dadi ganin dangin Amminta ta sake gaishesu, yayin da suka rungume ta cikin farincikin...


Gyaran murya Daddy yayi kana cikin iya sarrafa harshe ya ce "mun aikata muku laifi, wanda Muke fatan zaku yi wa magana ta da zan yi yanzu duba na tsanaki, shiru yayi na yan mintuna kana ya cigaba, maganar gaskiya Abrar matar aure ce yanzu, kuma ba kowa bane mijin ta face dana Aaban, nan ya shiga basu labarin yadda auren ya kasance....




so sorry habibti's nasan kun gaji da jira, ku yi min afuwan, abubuwa ne sun hade min bana da lokaci, in sha Allah gobe zaku jini son so nake muku.😘



Vote✔
Share✔
Comment✔
Editing is not allowed❌




Noor Eemaan✍
07082281566


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

Written by Noor Eemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

Page 61_62

(not edited)
Cikin zallan mamaki su yaya Nadeen ke bin Daddy da kallo tamkar wani sabon hallita, Ammi ta fi kowa shiga mamaki mai yawan gaske... Kuka ta fashe da dashi a lokacin da Daddy ya kai aya a maganar sa, kuka sosai na zallan farinciki hadi da tausayin tilon yarta



Gaban Abrar da na Aaban kusan lokaci daya ya bada sautin "dam daram!" a tunanin su Ammi bata farinciki da auran.

"Haba Rahilat ya kuma kike kuka?" Anty Raheenat ta tambayeta, itama fuskar ta dauke da murmushi.


"Dole in yi kuka Anty, ace diyata tayi aure ban sani ba, wanda babu abinda ya janyo hakan face kin yi wa maganarta duba na nutsuwa, amma ina farinciki sosai da hakan Allah ya basu zaman lafiya"... Ammi ta ce tana kuka, yayinda idanun yan dakin ya ciko da kwallan tausayin su...



Ajiyar zuciya Abrar ta saki da ya taho da hawaye masu sanyi, haka ma Aaban ajiyar zuciya ya saki mai karfi da ya sanya Daddy kallonsa kana ya girgiza kai yana murmushi domin ya fahimci Aaban sarai.

"Mijin Abrar dita ka zo gareni" Ammi ta ce tana sakar masa murmushi, shima murmushi ya saki mai taushi take son matar ya darsu aransa, dai-dai gabanta ya durkusa, sumar sa mai yalwa ta shafa, hadi da sa masa albarka, cikin jindadi ya amsa hadi da jifan Abrar dake zaune har yanzu kan cinyar Ammi da kallo na
soyaaya...




Murmushi jindadi su Mummy suke yi yayinda farinciki ya cika zuciyoyin su, Hanan ce ta mike zuwa wajen Ammi, Abrar ta fara turewa tana cewa "malama tashi daga kan cinyar Ammi na, katuwa dake salon ki karya ta"


'Wallahi bazan tashi ba" Abrar tace tana murgudawa Hanan baki hadi da sakalo hannunta a wuyar Ammi...

"Toh wallahi sai dai mu raba dan ba zai yu ba, ai nima Ammina ce"....

Dariya yan dakin suka shiga musu, yayinda Aaban ya mato kan kallon Abrar musamman da ta murguda baki wa Hanan sai ya ga ta kara masa kyau ainun...

Nan hira ta barke tsakaninsu, har da baba da ke kwance na sanya musu baki cikin hirar tasu jefi-jefi, sosai shima ke cikin farincikin wanna ranar...

"Ina da magana" Ammi ta ce kanta na kasa.

"muna jin ki Rahilat" in ji Mama

"Ina son a raba aure na da Shettima" Ammi tace tana runtse idanunta domin sunan shi ma bata son shi...

"Yo ko baki fada ba, wallahi kin gama zama a gidan shi, kuma dole mu maka shi kotu abi muku hakkin ku" anty Raheenat tace cikin kakkausar murya dake nuna tana jin tsana da haushin alhaji Shettima.


Hawayen farinciki ne suka zubo wa Abrar jin wai Ammi da bakin ta ta nemi rabuwa da alhaji Shettima...

Gyaran murya Daddy ya yi kana yace" ya kamata idan zamu yanke hukunci mu yanke ba a lokacin fushi ba, shakka babu Shettima ya cancani karban ko wani irin hukunci ne, sai dai bazan so sunan surukata ya baci ba, wanda hakan kan iya shafan jikokina in Allah ya yarda, saboda haka nakeso ayi shari'ar nan ba tare da duk duniya ta sani ba, saboda kare mutuncin surukata kuma diyata ".


Jinjina kai suka yi cikin gamsuwa, domin ba karya cikin abubuwan da ya fada, tabbas sunan Abrar zai iya baci a duniya wanda zai iya shafan yayan ta, domin yanzu abu zai faru, amma wasu mutane su lauya maganar ya dawo na batanci...

" sanna ya kamata ace mun ziyarci nijar domin Abrar ta gana da kakarta ta wurin uba da ma sauran yan uwansa na can" Cewar yaya Nadeen yana kallon Ammi.

Wani tsohon mikin ne ya taso wa Ammi, take ta ji ranta ya baci tuno wasu abubuwa da suka shude "ba zamu je ba yaya Nadeen ka gafar ce ni" ta ce kanta na kasa alamun girmamawa...

"Girgiza kai yaya Nadeen yace " nasan cewa abubuwa da yawa sun faru da ku, kun ga rayuwa wanda kaddarar ku ce haka, babu bawan da ya isa ya sanja kaddarar sa"... Nan sauran mutanen dakin suka dan sa baki har ta amince kan cewa zasu je...

Wanda suka saka ranar zuwa wato nan da sati biyu, wanda da sun dawo ne za'a fara shari'a da alhaji Shettima...

Sai bayan la'asar su Mummy suka yi shirin tafiya gida, ai Abrar makalewa Ammi tayi akan ita nan zata zauna, abun ma dariya ya bawa Ammi, "ina kika taba jin an yi haka Abrar? Shi fa aure da kike gani ba abun wasa bane, maza tashi mu je in raka ki" Ammi ta ce a hankali tana kallon Abrar...



Turo baki ta yi ta na share kwalla ta mike, Anty Raheenat na mata dariya, Aaban kuwa duk yana lura da abinda take yi,
Cikin mutunta juna suka sake yin sallama, Abrar bakin motar ta tsaya taki shiga har motar su Mummy ta fita daga gidan.

Daga cikin motar ya kura mata ido baya ko kiftawa,,,, iskar mai zafi ya furzar daga bakinsa, kana ya bude murfin motar ya fito, turo baki ta yi kanta a kasa, dai dai saitin ta ya tsaya ya ce "wifffy are mad at me?" (Matata Fushi kike da ni?)


Girgiza kai tayi, "then meya hani ki shiga mota?" Ya sake tambayar ta.

"I want to stay with Ammi" ta ce hawaye na ziraro mata.

"Idan na baki daman hakan, will you be happy?" Ya tambayeta

Cikin zallan zumudi ta daga kanta hadi da furta "eh" murmushi dauke kan beautiful innocent face dinta.

Murmushi ya sakar mata, duk da can cikin zuciyar sa baya son rabuwa da ita ko da na minti daya ne, amma ba yadda ya iya yafison farincikin ta fiye da komai, ya kuma san ta yi kewar Ammin ta ne...

"Na baki umarnin zama da Ammi, daga yau har zuwa ranar da zamu dawo daga nijer"

Ihun murna ta saki kana ta rungume shi ta ce "nagode sosai pure heart, am happy har nijer zaka bimu"

"Shhhhh! never mind, your happiness is mine" ya fada yana manna mata light kiss a saman forehead (goshi) din ta.

Nan suka yi sallama ya tafi cike da matsanancin kewar ta...

Bayan ta shiga ciki, Ammi ta zaro ido hadi da cewa "ya na ga kin dawo"?

"Shine ya ce in zauna tare dake, har sai bayan mun dawo daga nijer" tace tana washe teeth's dinta...

"Anya ba takura masa kika yi?" In ji Ammi tana tsare ta da idanuwa.

"Allah Ammi ban matsa masa ba, za ma ki iya tambayan sa" ta fada tana shige wa jikin Ammi, nutsuwa hadi da sanyin dadi na ratsa jikinta...


Nan hira ta sake barkewa tsananin su, kana kallon su zaka san cewa akwai kauna da shakuwa mai yawan gaske tsakaninsu kafin kaddara ta raba wanna kaunar hadi da shakuwan, sai dai yanzu Alhamdulillah zasu ce domin komai na daf da zuwa karshe...

Amal dake zaune ma ba'a barta a baya ba, domin wani son Abrar din take ji sosai a zuciyar ta, "Anty bari na sake dauko wani kunun ayan in ji Amal"

"Toh shikenan Amal, na ma manta ban dauko miki wani ba, wanna yar rigiman kanwar ta ki ta mantar dani" Ammi tace mata"

murmushi kawai Amal ta saki tana mikewa hadi da cewa "ai ta yi kewar ki ne sosai Anty"

tana fita Adam ya yi maza ya bita, tana daf da shiga kitchen din ta ji an rungumeta ta baya, ajiyar zuciya ta sauke domin ta fahimci ko wanene

" sweet Adam am so sorry bazan...."

"Ya isa komai ya wuce, a rayuwa ana so idan ka yi abu mara kyau toh ka yi saurin yin nadama" Adam yace yana sakar mata Sumba..." Nan suka dai dai ta tsakanin su (mata da miji sai Allah😍)



Har dare Abrar na manne da Ammi yayin hirar tasu taki karewa, har Ammi ta bata labarin zuwan su gidan kowa lefen Amal amma ikon Allah basu hadu ba, sosai Abrar tayi mamaki, hadi da jinjina ikon Allah. Sun kai biyun dare suna hira, sun kuma sha kuka tuno rayuwar su kana bacci ya yi awon gaba da su ba tare da sun shirya wa hakan na.


************************************
"NIJER"


Tsaye Ammi take ta kurawa gidan ido bata ko kiftawa, ba shakka wanna shine gidan da tayi rayuwa da Sajeed din ta, masoyinta na asali uban diyarta Abrar "Allah ya kyautata makwancin ka" ta fada a hankali hawaye na zubo mata. Gidan na nan yadda yake sai dan gyare gyare da ba a rasa ba...

Abrar, Aaban, anty Raheenat, yaya Nadeem, Hanan, su suka yi wa Ammi rakiya zuwa nijer, a hankali Abrar ta karasa wajen Ammi hadi da dafa ta idanunta cike da kwalla, domin duk da a kananun shekaru suka bar gidan amma, bata manta daren da Ummi (kakarta kenan ta wajen uba) ta kore su cikin duhun dare suka bar gidan....

"Ammi na!" Ta ce, a hankali Ammi ta juyo hadi da dora hannun ta kan na Abrar.

" ki karfafa zuciyar Rahilat mu shigo ciki ko? In ji anty Raheenat jinina kai Ammi ta yi kana ta riko hannun Abrar suka fara takawa yayinda su Anty Raheenat suka take musu baya, banda Aaban dake tsaya ba tare da ya shiga ba, wanda ba su lura ba har sai da Abrar ta juyo ta gan shi tsaye, da ido ta yi masa alamun ya taho, makale kafada ya yi kamar karamin yaro, murmushi ya subuce mata domin sosai ya burgeta, magana ta radawa Ammi take ta juyo ta ce "taho Dana" ba musu ya fara takowa... yayinda Abrar ta sakar masa gwalo, murmushi kawai yayi yana mamakin iya tsokanar ta, wanda bai san ta iya ba..

Da kallo Ammi ke bin part din su na gidan, take komai ya shiga dawo mata, haka Abrar tunanin Abbin ta ya dawo mata sabo fil wanda yasa ta ziraro da hawaye.

Suna shiga haraban gidan suka yi kicibis da Zulaihat (wato kanwar Sajeed, idan baku manta ba a shafi kan farko) cikin mamaki Ammi ta ce "Zulaihat!" Dago kai Zulaihat ta yi jin kamar ta san mai muryar.

Waro ido tayi tace "anty Rahilat kice min da gaske ke nake gani ba gizo idananuna ke min ba Ina yata Abrar" ta fada cikin yaren buzaye kana tayi mix da hausar ta dabe gama kwari ba.

Rungume ta Ammi ta yi tace "nice Zulaihat, nice tsaye a gaban ki, na yi kewar ki sosai kanwata" in ji Ammi.

Kuka Zulaihat ta saki, kukan farinciki, bata yi tunanin zata sake ganin su Ammi ba har ta koma ga Allah, kullum bata da aiki sai na kuka hadi da jin haushin halaiyan ummin ta.

"Abrar ki zo ga Zulaihat, baki manta ta bako?" in ji Ammi

Jinjina kai Abrar tayi duk da ta manta kamaninta amma sunan ta na zaune daram a kwakwalwarta, durkusa ta yi domin gaisheta, Cikin sauri Zulaihat ta rungumota tana jin soyaayyar diyar yayanta...

Riko Abrar Zulaihat ta yi a jikin ta tace "Mu shiga daga ciki" ba musu suka bita a baya yayinda ta yi musu jagora har zuwa bangaren Ummi...




Kuyi min haku'ri sister's na barku kuna jira na, wallahi jiya bacci ne ya dauke ni, ina cikin typing zuwa dare zaku ji in sha Allah idan ina free...


Share✔
Vote✔
Comment✔
editing is not allowed❌❌

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

Written by NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

page 63-64

(not edited)

______________________📖 zaro ido Ammi ta yi cikin kaduwa hadi da mamakin ganin Ummi acikin wani matsanancin yanayin.

"Zulaihat me ya sa mu Ummi haka?" Ammi ta tambaya tana bin Ummi dake kwance da kallo cikin halin matsanancin ciwo....


"Hakkin ku" Zulaihat ta ce idanunta cike da kwalla

Cikin sauri Ammi ta durkusa gabanta tana cewa "Ummi!" Kura wa Ammi ido Ummi ta yi yayin da bakinta ya fara motsi alamun zata yi magana, amma ta gagara furta komai...

Cikin tausayawa halin da Ummi take ciki Ammi ta share kwalla, wai yau Ummi yar gayu, mai ji da dukiya ce kwance cikin wanna matsanancin halin?...

"Zulaihat Baku kai ta asibiti ba ne?"

"Anty Rahilat na gaya miki cewa hakkin ku ke bibiyar Ummi domin babu irin asibiti da bamu je ba, babu kalan maganin da bata sha ba, amma babu wani sauki, ta kai kusan shekaru bakwai cikin wanna halin tun tana iya cewa a nemo mata ku ta nemi yafiyar ku har ta ma daina magana sai dai kawai ta bi mutum da kallo....

" innalillahi wa Inna ilaihi raju'un " Ammi ta ce tana kuka, domin duk mai imani dole ya tausayawa halin da Ummi ke cik, domin wani mugun rama tayi baka ganin komai sai kashishuwa.

"Ku zauna bayin Allah" ki jin Zulaihat.

A sanyaye duk suka zauna, domin suma sun tausayawa halin da take ciki.

Ruwa

Please Login or Register in order to submit comment