Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga hannunsa mai dauke da Amal din sama, tsalle ta shiga yi tana kokarin kamo hannunsa amma ya ki bata damar hakan, itama ta ki hakur'a, ganin ze gajiyar da ita ya sashi sauke hannun ya shigar da ita kirjinsa kana ya nufi bakinta da apple di'n, ahankali ta bude small cute lips din'ta ta ciji Apple di'n, Kansa ya daura a saman kanta yace
"am sorry decent one, so sorry for what Amal did to you".

Shiru kake ji daga bangaren Abrar sai karan taunan Apple din'ta dake tashi, sai data cinye Apple din kana ya riko hannunta suka nufi cikin gida....

Suna shiga suka ga daddy zaune yana kallon sunnahTV, " barka da hutawa dad" yace yana kokarin wucewa
"yawwa barkanmu, Abokina dan zo mana"
Ba musu suka dawo ya zaunar da Abrar kan kujera yayinda shima zauna

"son ya batun lafiyarku India?"

"Tana nan dad, anjima zan je inyi booking flight" Aaban ya amsa wa daddy with full respect.

"A'a abokina, kubar tafiyar nan ba yanzu ba, da kallon mamaki Aaban ya bishi yayinda fuskarsa ke kokarin bayyana damuwa....

Noor Eemaan😉✍

Zuwa dare zan sake baku page 43_44.


SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S 📚✍

page 43-44

Murmushi daddy yayi domin ya fahimci tunanin daya darzu a ran Aaban, cikin zolaya yace "angon Abrar ba abinda kake tunani bane, ina nufin tunda bikin kanwarka Amal saura sati daya ya kamata ka tsaya a daura auren da kai, Allah basshi washegarin daurin auren sai ku tafi, tunda ba'a san tsahon lokacin da zaku dauka a can ba"...

Ajiyar zuciya ya sauke, kana yace " Ok Dad zanyi hakan " ya kara sa maganar yana Sosa kansa...da kallon kawai daddy ya bishi yana murmushi

"Assalama alaykum"
Sallamarsa ta karade dakin, amsa wa ammi ta yi tana murmushi tace "Adam har ka dawo daga zancen?" Ammi tace cikin tsokano domin zamanta a gidan, yasa shakuwa mai yawa shiga tsakaninsu domin sai kayi tunanin tayi shekaru masu yawa a gidan, kuma sosai yake debe mata kewa rashin yarta, duk da in ta kadai'ce takan yi kuka, kukan nadama, kukan rashin baiwa maganar yarta muhimmanci, babban abinda yafi damunta dare da rana shine a wani hannu yarta take? a hannun nagari ko akasin hakan? Duk yaya Alkasim mahaifi ga Adam da yaya Nadeem na matukar kokarin wurin bincike inda take...

"Eh antyna na dawo, ina anty raheenat take suka bar ki kedai?"

"Suna part di'n mama wato (mahaifiyar Adam)" har ya budi baki ze tambayeta sai kuma yayi shiru gudun kada ya tayar mata da mikin da ke ranta.

"Antyna bara na je part din mama zan dawo"

"Toh Adam sai ka dawo" ammi ta amsa.

Yana shiga part din Mama ya gansu zaune ita da yaya raheenat suna hira, bayan gaishe'n su dayayi sai yace
"anty raheenat wai yar anty rahilat data bata suna kamasosai ne?"

Kallon juna mama da yaya raheenat sukayi kana anty raheenat tace "eh toh suna matukar kama a lokacin da take da kananun shekaru, amma yanzu ban saniba ko yanayin fuskarta ya sanja, amma meyasa ka tambaya Adam?"...

" Wato dana je gidansu Amal naga wata mai kama da anty Sak, babamcinsu kawaivyawan shekaru da anty ta fita"

"Adam kenan sau nawa ana samun masu kamanin da yawa kuma babu wata dangantaka dake tsakaninsu? kuma banda abinka meye zae kai yar Rahilat gidansu Amal? Kuma ina fatan baka fadi wanna maganar Rahilat taji ba ko? Domin kada hankalinta ya sake tashi"... Mama yafada tana kallon Adam

" eh ban gaya mata ba"

"Yawwa kada ka bari ko da wasa taji, kila wata yar'uwar su Amal din ce, kada kazo baka da tabbacin Abu ka tayar mata da hankali, muna kokarin kwantar da hankali ta"

"Toh mama" yace domin yasan baza su fahimce shi ba, shi ya ganta da idanunsa tsananin kamarsu ya wuce ace kawai kamanin ne ba wata karfaffan alaka a tsakaninsu, yana kuma fatan idan sun je kai lefe su ganta suma, hakan zai sa su gasgata maganarsa....


Yau ya kasance ranar dasu ammi zasu kai lefen gidansu Amal, motar har biyu ce ta debi kayan yayinda su yaya raheenat, ammi tare da wasu yan'uwan mama ke wata motar daban, motocin sun tashi uku kenan.

Horn driver's din gidansu Adam suka danna, babu bata lokaci aka wangala musu yalwataccen gate din kasancewar an san da zuwan su, bayan sun faka motocin, kana driver's suka shiga fito da akwatunan suna shigar da shi cikin gidan sai da suka shigar da akwatunan duka kana su ammi suka shiga ciki, yaya raheenat ce agaba yayinda ammi ke baya da ita, sai sauran matan da suka biyo baya...

Sosai su mummy da mutanenta suka tarbe su cikin mutunci, mummy tadan yi mamakin ganin tsananin kaman da ammi da Abrar ke dashi amma bata kawo komai a ranta ba, akwatunan ba karya sun hadu, guda ashirin da hudu ne, hadi da kudi har million uku, bayan duk sunyi abinda ya dace suka mike domin tafiya, mummy ta basu tukwuici million biyu, haka suka rabu cikin mutunta juna, bayan sun fito duk sun shige motar saura ammi dake kokarin shiga, kamar ance to waiwayo ta hango Abrar zaune ta bata baya, yayinda wani kyakyyawan matashin saurayi ke yi mata yankan farce, haka kawai ta ji tanason ganin wanna budurwa har ta fara takawa taji yaya raheenat tace
"Rahilat ina zaki? Ki shiga mu tafi mana".
Bata ce komai ba ta shiga motar, sai lokacin tunani yazo mata, ita yanzu data nufi wajen su mezata ce musu? Tunda bata san su ba, suma ba saninta suka yi ba...


Bayan kwana biyu aka fara bikin Amal wanda suka fara da bridal shower, kamu, dinner, sai mother's eve, duk wani anko da akayi, sai da Hanan ta tabattar Abrar tayi domin har dinki iri daya ta musu, sedai Aaban yace bazata je ko wani event ba, dalilinsa kuwa shine bayaso ko da wasa awulakantata, ko wata ta gaya mata ba dadi, yasani cewa bata cikin hankalin ta amma matukar aka haiba tata har zuciyarsa yake jin ba dadi, Hanan tayi rokon duniyan nan ya ki, har alkawari cewa tare zaku zauna waje daya amma yaki amincewa. Saboda yasani ciwonta ze iya tashi a ko wani lokaci, hakan ze iya sawa wasu mutane su fadi wata kalma mara dadi akanta wanda shi bazai ji dadi ba, ba kuma zae jure ba, ya kuma san cewa da maza a wurin, shi bazae bari wani namiji ya kalle masa mata ba domin yana tsananin kishin'ta fiyeda zaton mutum, da wadanan hujojin ya ki bari Hanan ta kaita...

Washegari aka daura auren Amal da Adam wanda dubban jama'a suka shaida, da yamma aka kai Amal gidanta da babu wani nisa tsakanin sa da gidan su Adam, Amal tasha kukan rabuwa da su Mummy, Hanan ma tayi kukan rabuwa da yayarta sosai ....

Washegari kuwa babu bata lokaci Aaban yaje booking flight sae de be samu direct zuwa India ba, a Syria jirgin ze tsaya haka yayi booking domin bayaso ko dan ya sake daukan lokaci basu tafi neman lafiyarta ba...

Yana shiga part dinsa, ya ganta kwance tana bacci, jikinta rabi a kasa rabi a gado, gyara mata kwanciyar yayi ya bata kyakyyawan Sumba a kumatun ta, kana ya bude wardrobe dinsa, take idanunsa suka sauka kan sadakinta wanda naira na gugan naira har million daya, "zan cigaba da ajiye miki su har ki samu lafiya domin hakkin ki ne" ya fada yana waiwayonta hadi da sakin murmushi... Sai kuma ya Dan daki kansa yana cewa
"mekake yi haka ne Aaban? kai kadai kana magana". Sai kuma ya girgiza kansa yayinda fuskarsa ke dauke da murmushin still, kayan dayasan zasu bukata ya hada awani madaidaicin jaka domin a tsarensa bayasan tafiya da kaya masu yawa musamman in tafiyar ta kasance mai nisa ce....

Washegari karfe goma dai dai ya gama shirya ta, cikin abaya maroon color dayayi matukar karbanta, yayinda shi kuma ke sanye da kananun kaya masu kyau da tsari, saukowa kasa suka yi, su Mummy na zaune suka jiran fitowarsu, tun daga nesa Mummy ke kallonsu, yayinda ta kasa gane yanayin da take ciki, duk inda ake neman ma'aurata da suka dace da junansa to indai an samu su Aaban an gama domin haduwarsu da dacewarsu na daban ne, bayan ya gaishe da mum and dad, Hanan ma ta gaishe shi, babu bata lokaci gaba daya suka mike domin yi masa rakiya...

Mummy tayi masa fatan sauka lafiya hadi da add'ua domin haka kawai ta ji jikinta yayi sanyi, daddy ma yayiwa Aaban fatan Alkhairi, da ameen duk ya amsa kana ya rungumi iyayansa cikin kaunarsu...

Hanan da idanunta suka ciko da kwalla ta rungume Abrar tace
"Allah yasa adace bestie Abrar, ki dawo mu cigaba da rayuwar mu yanda muka saba, nayi missing duk lokutan da muka kasance ciki a Cyprus" Hanan ta karasa maganar wasu hawaye na zubo mata.



Abrar kuwa shiru tayi kamar tana fahimtar abinda Hanan ke cewa, sai kuma tasa dariya mai tafe da kuka, tana kallon Hanan , bubbuga bayan Hanan Aaban yayi alamun rarrashi kana ya riko hannun Abrar suka shige motar driver ya ja suka bar gidan...


Bayan sun isa airport babu bata lokaci jirginsu ya daga zuwa sararin samaniya, kowa cikin jirgin harkan gabansa yake yayinda Hannun Abrar ke cikin na Aaban duk da tana kusa dashi amma hakan be wadace su ba sai da ya rike hannun, sun dan yi tafiya mai nisa sai kawai yaji ta fara dariya, sai kuma kuka ya biyo baya, hankalin jama'a ne ya fara yo Kansu, a karon farko ya hade bakinsu......

In Allah ya amince, gobe ma zan muku posting sae dai zaku ji ni ba da wuri ba.

Share✔
Vote✔
Comment✔
Edit❌
https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by Noor Eemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

masoyan mijin ammina ne sila ina matukar godiya da soyaayar da kuke nunawa books dina, na ga texts dinku bila adadin a group dina da ma sauran groups a bisa rashin jina da baku yi ba jiya, tnx all, here is your favorite book, so happy reading😊


Page 45-46

Ya dauki tsawon mintuna biyar a haka ba tare da ya ko sumbace ta ba, yayinda kyya wawan idanunsu ke cikin na juna basa ko kiftawa.... A hankali ya zare bakinsa ganin mood dinsa ya fara canzawa, kanta ya kwantar kan cinyar sa hadi da bubbuga bayanta, luf Abrar tayi bata ko motsin kirki, bata dauki lokaci mai tsayi ba bacci ya dauketa, jin ta daina motsi ya sa shi leka fuskarta... Ajiyar zuciya ya sauke domin fatan sa kenan tasamu bacci, lumshe idonunsa yayi tunanin yadda aikin zai kasance fall zujiyarsa.


*SYRIA*
Cikin tafiyarsa ta burgewa yake taka matattakalan benen jirgin, yayinda Abrar ke kwance har yanzu tana bacci kan faffadar kafadansa... Taxi ya tsayar ya gaya masa ya kai kaisu hotel mafi kusa da airport din, babu jimawa suka isa hada'dden hotel di'n,... Aaban ya biya mai taxi hakkin sa kana ya kara daukan Abrar a kafadansa, cikin sauri ma'aikatan hotel din suka dauki jakarsa, kudin yan Awannin da za su yi ya biya kana ya karbi mukullin dakin... Kwantar da ita yayi kan gado ya shiga toilet domin yin wanka domin ya warware gajiyan jikinsa, ya dauki tsahon mintuna 30 yana wankan kana ya fito daure da towel a jikinsa, yayinda ruwa ke diga a kan hair dinsa.
singlet da boxer ya saka, kallon Abrar yayi ya ga tana baccin har yanzu, kayanta ya shiga cire mata a hankali kana ya daga ta cak zuwa toilet...

Cikin jacuzzi ya sanyata a hankali, bata rai tayi cikin baccin a sakamakon ruwan daya ratsa jikinta, murmushin shaukin sonta ne ya subuce masa.... Domin yadda tayi ba karamin kyau ta kara masa ba, ruwa ya debo a tafin a hannun sa ya shafa mata... A hankali ta fara bude idanunta dake cike da bacci har yanzu, wani kyau ya ga idanunta sun kara masa, labban sa ya dora akan nata ya bata light kiss, fuskarta ya fara wankewa, mistakely shower gel di'n ya shige idonta, kara ta saki kana ta shiga goge fuskarta a singlet din sa, gaba daya ya rude ganin ta cikin wanna halin, fuskarta ya kamo ya shiga wanke mata cikin sauri- sauri sai da ya tabattar sabulun ya fita kana ya shiga wanke mata sauran jikinta, a towel ya nado ta kana suka fita, lotion mai kamshin gaske ya shafa mata kana ya sanya mata blue jeans da riga fara, full, long hair dinta ya taje mata, yayi mata parking da farin ribbon...

Kamo fuskar ta yayi yana kallon baiwar kyau da Allah yayi mata "so cute" yace mata hadi da kamo kumatun ta, itama kumatun sa ta kamo tace "so cute" murmushi yasaki kana ya kira hotel din akan su kawo abinci, babu bata lokaci suka fara knocking, bude kofar yayi ya karbi abincin... kan cinyarsa ya dora ta suka shiga cin abincin, duk da fiye da rabin abincin Abrar ce ta cinye...( acici lolz)

Bayan sun gama ya fita hadi da rufe Abrar a dakin, wani flight yaje yayi booking wanda ya samu jirgin da zai tashi nan da awa uku zuwa India. Bayan ya koma ya tarar da Abrar kwance shiru ta kura wa waje daya ido, jikinsa ya jingina da kofa, yana binta da kallon tausayi da matsanancin sonta, a hankali ya tako zuwa gareta hadi da Sanya fuskar ta cikin tafin hannunsa yace "decent one please ki daina tunani is not good for your health ok" kallonshi tayi kawai take, sai kuma tasa dariya mai tafe da kuka alamun ciwonta ya tashi, cikin rashin jin dadi ya rungumeta, idanunsa a lumshe yana bubbuga bayanta alamun rarrashi....

* MUMBAI INDIA*
Bayan sun sauka india a birnin mumbai, hotel ya sake kama musu, washegari da safe suka nufi babban hospital din mai suna "CITY HOSPITAL" babu bata lokaci suka gana da babban doctor kwakwalwan mai suna "IRFAN WAJEED KAPOOR" wanda tare suka yi karatu da Aaban din a nan India, kuma tun a nigeria suka gama magana da Aaban akan ciwon ta...

Bayan duk sun sake yi mata gwaje-gwajen daya dace, kana suka sa ranar yin aikin jibi, wanda aikin nada hadarin gaske, kila ta dawo da memory'n ta ko kuma a samu a kasin haka domin ciwonta ya zama chronic sosai, a hakan ma dan tana samun kulawa ne....

Jiki Aaban ya yi sanyi haka suka bar asibitin, yana fatan a dace, wuraren shakatawa ya kai ta irin daban-daban, sosai ta dinga yin shirmanta yana biye mata, wanda hakan ya dan debe masa damuwar da yake ciki...

Daga karshe ya kaita inda ake siyar dasu snacks a bakin hanya kuma sosai taci... yana cikin biyan mai snack's din kawai ya ga tasa gudu tana raba'wa ta tsakanin motoci, gabansa ne ya bada dam! Bai san nawa ya biya mai snacks din ba, haka ya shiga binta da zafin nama, gaba daya ya neme ta ya kara sa... Hankali tashi ya shiga kotsawa ta tsakanin motocin hadi da kwala kiran sunanta... can ya hangonta tsallaken titi tana cigaba da kuka, shima tsallakawan yayi, ya kara gudun domin ya cin mata...

hannunta yayi nasaran damkewa kana ya riko ta gaba daya zuwa jikinsa yana sauke wata katuwar ajiyar zuciya hadi da lumshe idonsa...
"bazan juri rasa ki a karo na biyu ba, please karki sake haka decent one". Ya fada yana sake kamkameta a jikinsa, Abrar kuwa dariyar ta kawai take hadi da ajiyar zuciyan gudun data tika, taxi ya tsayar suna koma hotel dinsu....

*BAYAN KWANA DAYA*
Yau ya kasance ranar daza'a yiwa Abrar aiki, sosai Aaban ke cikin wani hali na matsanancin damuwa, sai dai kasancewar sa namijin gaske yasa kai tsaye bazaka fahimci hakan ba...

bayan sun shiryata cikin uniform mai kalan blue, suka nufi dakin Operation din da ita, cikin sauri ya kara sa gareta hadi da riko hannunta daya, yayinda ya dora dayan a kan fuskar shi yace "wifffy... Allah ya bada sa'a, I know zaki dawo da memory'n ki domin ke jaruma ce, I love you" yarasa hadi da bata hot kiss a goshi...

turata ma'aikatan hospital din suka shiga yi zuwa dakin operation, yayinda ya ke jiyo dariyar ta dake tashi sosai hadi da kuka... da baya da koma ya zauna a kujera, sai a lokacin wani tunani ya zo brain dinsa, shin idan ta dawo dai dai zata gane shi? Shin zata karbi shi a matsayin mijinta? Shin ya zata ji idan taji labarin auren dake kanta? Gaba daya kansa ya kulle, kwantaccen sumar sa ya hargitsa yana fadin "ya Allah"....


ban yi editing ba, saboda ban da time kuyi hkr, much love my fans😘.

SHARE✔
VOTE✔
COMMENT✔
EDIT❌


✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by Noor Eemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚✍

EID MUBARAK TO YOU MY FANS, ALLAH YA MAIMAITA MANA💫✨🌝 💞

page 47-48

haka ya cigaba da zama a wajen idanun sa kuri kan kofar operation din, babu abunda ke tashin sa sai Allah...

yana cikin wanna halin yaji wayar sa na ringing, a hankali ya zaro ta cikin aljihun sa ba tare da ya duba wanda ya ke kiran ba ya kara wayar a kunne, "Son how are you?" jin saukar muryan Mummy a kunnuwan sa ya sa shi lumshe ido kana ya ware su a hankali... "Am fine" ya amsa a kasalance

"No you are not son, gayamin menene"...
Ajiyar zuciya ya sauke yace "Mum an shigar da decent one dakin operation".

Shiru mummy tayi yayinda ta kasa tantance halin da take, a wani bangaren kuma ta na matuk'ar mamakin tsananin son da danta ke yi wa Abrar di'n... "ka kwantar da hankalinka son, everything will be fine, Allah ya bata sa'a" Mummy tace tana katse wayar...
bai iya amsawa a fili ba har ta katse wayar.

Bayan awannin takwas doctor Irfan ya fito tare da abokan aikin sa, cikin wani irin zafin nama ya kara sa wajen doctor, cikin turanci yace;
"doctor Irfan how is my wife? As she regain her memory?"...

murmushi doctor Irfan ya saki ganin yadda Aaban ya rude gaba da ya, ya kuma yi mamaki hakan domin bai yi tunanin Aaban zai so wata mace so soon har ta kai ga aure ba, domin a lokacin da suke school shi shaida ne akan cewa mata basa gabansa, duk da suna kawo kansu gareshi, kafadan sa ya dafa yace "please calm down doctor Aaban, ka karfafa jikin ka da ma zuciyarka, sai kace ba jarumin doctor'n dana sani ba".

"Irfan you won't understand, she's my life, inaso in ganta tana rayuwar farinciki kamar kowa"...

"In sha Allah komai zai zama normal" yanzu muje office dina in maka bayani ya fad'a yana kamo hannunsa, ba musu Aaban ya bishi....

bayan sun zauna, yace "Aaban you have to calm down sanan zaka fahimci bayanin da zan maka. jinjina kai yayi alamun "toh"

doctor Irfan ya hade hannuwansa cikin na juna kana ya fara cewa "the opperation went sucessful, duk da mun sha wuya matuka kafin komai ya daidaita, yanzu jiran farkawan ta zamu yi, zata kai awa biyar zuwa shida kafin ta tashi, muna fata ta dawo da memory'n ta"...

Ajiyar zuciya mai karfi ya saki kana yace "Thank you so much Irfan"

hannu Doctor Irfan ya mika masa suka yi masabaha yace " don't mentioned Doctor Aaban, you deserve it" domin baya taba manta taimakon Aaban gare shi ba, lokacin suna makaranta... haka dai suka cigaba da taba hira wanda yawanci Irfan din ne ke magana.

*SOME HOURS LATER*
cikin mutuwar jiki yake bude kofar dakin hutun da aka ma yar da ita wanda ya kasance na zallan glass ne, yayinda yake jin zuciyarsa na bugawa so fast, amma mutum ba zai fuskanci haka ba saboda jarumtar sa, tun daga nesa ya kura mata ido, fuskarta tayi fayau yayinda fatar ta ke fitar da sheki hadi da haske na musamman da ya kara mata kyau ainun...

bakin gadon ya zauna ya lalubo tattausan hannunta cikin na sa, kana ya bawa hannunta kyakyawan sumbata, ya kai awa daya a haka bata farka ba, sosai ya fada duniyar tunani, domin baya so ta nuna bata san shi ba idan ta farka domin baya tunanin zai jure hakan.

"AMMI NA!!!"..... Abrar ta kira sunan Ammi da mugun karfi, da ya shi dago kansa cikin sauri yayin da gaban sa ya bada ras!

"decent one kin tashi, ya jikin ki? ina yake miki ciwo yanzu? please ki mun magana" ya fada a rude fuskar sa cike da damuwa.

kallonta ta kai inda ta ji wani unique voice, kura masa ido tayi tana tunanin waye wanna hadadd'en saurayin? me yake yi tare da ita? me kuma take yi a hospital? amma ta kasa tuna komai, abu daya ta tuno, gudunta daga gidan mijin ammin ta, da haduwarta da wani mutumi da ko fuskar sa bata sani ba ta dai tasan ta nemi taimakonsa...

jin kanta zai fara ciwo, yasa ta lumshe idanunta yayinda wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata, tana kuma tunanin ko ina take yanzu? A hankali sautin kukan ta ya fara fitowa fili, yayinda idanunta ke a lumshe...

cikin damuwa yace "decent one, kiyi shiru, ciwon ki baya bukatar kuka please"...

saukar muryan sa ya sa ta ware idanun ta, hannun ta dake cikin nasa ta fincike tace "who are you? waye kai? ko shine ya turo ka ka karasa rayuwata? ai ga ni gabanka ka yi yadda kakeso dani"... ta karasa tana fashewa da wani mugun kuka mai matukar ratsa zuciya.

ko kadan bai ji dadin kalaman ta ba, amma sam bai ga laifin ta ba, domin ta ga rayuwa wanda kafin tabon ya bar zuciyar ta za a dau tsahon lokaci...

"Decent one i will explain everything, zan yi miki bayanin komai, amma ki kwanatar da hankalin ki, maganar na bukatar nutsuwa"...

cikin kuka ta katse shi tace "ni banason sanin komai, ka gayamin kai waye? ina nake? "....

runtse ido yayi da karfi kana ya waresu yace "kina india mumbai, wani zaro ido tayi cikin mamaki abinda yace, mamaki bai gama kama ta ba sai da ta ji yace
"kuma ni mijinki ne"...

gaban ta ya bada wani mahaukacin bugawa, duk da babu karfi a jikin ta hakan bai hana ta mikewa ba, tana masa wani duba daya kasa tantancewa, kuka tasa, kana tasa dariya hadi da tafa hannuwanta, kai tsaye zaka san cewa kukan da dariya ne na matsananci damuwa... "kana cikin tunaninka kuwa? kada ka yaudareni, domin babu mutumin da zai auri ragowan mijin am... ta kasa karasawa dalilin wani mugun kuka daya taho mata...

sumbar kansa ya hargitsa da hannunsa hadi da cije labbansa da karfi domin kukan ta yafi komai dagula masa lissafa, hannunta ya sake kokarin rike wa taki bashi daman hakan, bai takura mata yace "ya kamata ki nutsu haka, nasan cewa kin manta rayuwan da muka yi a baya, a sakamakon memory'n ki da ya dawo, shiyasa nakeson ki bani dama, nayi miki bayani"... ya fada cikin lallashi.

shiru tayi babu amsa sai kukanta daya cigaba da tashi wanda hakan bai kamata ba saboda lalurar ta...

ganin bata son bashi dama, ga kuma kuka n da take yi yasa shi mikewa ya bar dakin, office din doctor Irfan yaje yace masa ta farka kuma memoryn ta ya dawo, murna sosai doctor'n yayi ya kuma ba shi tabbacin cewa zuwa gobe ko jibi za'a basu sallama, jinjina masa kawai Aaban ya iya yi hadi da bashi hannu suka yi musabaha, wajen hospital din ya fita da motar Irfan, kasancewar ya san garin sosai duk da an kwana biyu rabon sa da mumbai din, wani hadadde'n restaurant ya je ya yi mata take away na lafiyayyen abinci, domin shi kam baya jin zai iya sa komai a cikin sa saboda halin damuwar da yake ciki....

kamar yadda ya tafi ya barta haka ya dawo ya same ta, gaban gadon ya karasa yace " decent one, tashi ki ci abinci"

idanunta da suka yi jajir ta kafa masa kana cikin kuka tace "bana ci, ni ka mayar da ni inda ka dauko ni, ban san waye kai ba"...

"huci mai zafin gaske ya furzar, yama rasa tunanin da ya dace yayi, domin ta hargitsa masa tunaninsa duka, kalma mafi ciwo da ta ce bata san shi ba...

Cikin son danne bacin ransa yace "Am sorry, zan miki bayanin komai matukar kika bani hadin kai, amma yanzu ki ci abincin"...

"Nace maka bana ci, ka rabu da ni, ka tafi!" ta fada cikin kuka mai karfi har

Please Login or Register in order to submit comment