Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kallo ya girgiza kansa domin yasan halin matarsa kwarai, shiyasa be dakatar da ita ba. "Abokina ka kara hakuri, mummynku zata sauko with time, indai ta nine ina baka goyon bayan aurenta, Allah ya kuma bata lafiya"

sai alokacin ya bude idanunsa yace "nagode dad" hadi da sakar masa murmushi, shima dad mayar masa yayi da martani kana ya mike ya nufi part dinsa...

kura wa Abrar madaidaitan sexy eyes dinsa yayi, take kuwa idanunsa ya gano masa rigar daya sanya mata asibiti, sai ya sake kallon hannunta yaga diamond ring din daya sanya mata a hannu, dafe kai yayi cikin takaicin kansa na kasa ganeta da yayi tsayin wanna lokacin sai yau...

Hanan data kura musu ido tana kallonsu ta share hawaye, tabass ba yanda Allah baya ikonsa, ace tasan Abrar amma ashe yayanta na faman nemanta, mikewa tayi ta nufi wajensu tace
"ya Aaban kayi hakuri in sha Allah everthing will be alright, sannan wallahi ban taba sanin cewa ita kakeso ba da tuni nasada ku da ita, domin itace wanna kawar tawa a cyprus, ina maka murna samun kamilan mace kamar Abrar, ina kuma goyon bayan ka aureta, domin ta cancanci farinciki arayuwa, she deserve it ya Aaban"... tana gama fadin haka ta ruga dakinta da gudu tana kukan tausayin Abrar...

da kallon Abrar tabi hanan yayinda ta kyakyalle da dariya, sai kuma ta mike zumbur ta dauko teddy data gani kan kujera ta rungume, sai kuma ta dauko remote dake kan centre table ta rosa shi da tiles, sai tasa kuka hadi da dago teddynta ta kura masa ido tace
"sai na kasheka, saina kashe ka shettima! tafada tana dukan teddy tamkar shettima ne agabanta, gaban Aaban ta dawo tace zaka bani wuka in kashe shi ko?"...

kwalla ne suka ciko masa idanu amma bayajin ze iya bari su zubo, gaban babban plasma taje ta shiga dukkan shi da dukkanin karfinta, tasowa yayi yakamo hannunta, tirjewa take tana nuna masa dinning table, fahimtar abunda take nufi yasa shi nufar wajen zaunar da ita yayi kana ya dauki plate hadi da serving spoon ya zuba mata jollof rice daya sha kayan lambu ya kuma wadatu da naman kaza spoon yasa mata, amma ko kallon cokalin ba ta yi ba, tasa hannunta biyu ta fara ci, ci take sosai tamkar bata taba cin abunci ba, kallon so da burgewan yanda take cin abunci yake mata domin ko kadan beji haushi hakan ba, tana gama ci yasiyaya mata juice a glass cup tana kai bakinta ta firzo shi gaba daya sai kan farar rigarshi gaba daya ta bata rigar, sai ta kwabe fuska tana nuna masa ruwan faro shima zuba mata yayi awani glass cup ta kuwa shanye shi tas tana lashe baki hadi da sakin gyatsa, murmushi da be shirya ba ya tsubuce masa kana yasa tattausan hannunsa ya dauke shinkafan daya makale gefen cute lips dinta.


"Amal matukar ina raye babu wanda mad girl din babu yayanku, domin ina zan kai wanna abun kunyar?"

"mummy relax ki kwantar da hankali, nima ina bayanki wallahi, tayaya ya Aabaan the hole classic guy ya kare da low class irinta, low class dinma mahaukaciya, na tsaneta ma ni mummy, na kuma san ya Aaban na matukar son ganin farincikin ki beze taba iya auranta ba tunda kin nuna bakya so"...

"daya fiye masa kuwa, domin matukar yayi kokarin auranta babu ni babu shi"... mummy tafada cikin matsananci bacin rai.


bangaren ammi kuwa har yanzu tana rufe adakinta, sai dai kullum alhaji shettima ya yi saurin tura mata abinci ya sake rufe dakin, tun tana gaya masa maganganu har ta dawo yi masa magiya akan ya bude mata taje neman yarta, amma ko kulata bayayi haka ze yi ficewarsa, ta rame sosai kullum bata da tunanin sai na yarta Abrar, bangaren alhaji shettima kuwa har yanzu ya baza mutanen sa nema masa Abrar domin acewar sa be koshi da ita ba, a gurbataciyyar tunaninsa yace matukar ya ganta, guest house din shi da ba kowa yasan dashi ba ze kaita, sannan ya cigaba da saduwa da ita har ta saba ta zama tashi domin kullum da matsananciyar sha'awarta yake kwana yake tashi.....


much love my beautiful people Alkhairin Allah ya kai muku duk inda kuke.❤



SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


NOOR EEMAAN CE✍

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚


this hole page this dedicated to my lovely niece nafeesat (feenah), much love my fee❤.

written by noorEemaan

page 31-32

kamar koda yaushe binta da idanu yake baya ko gajiyawa da kallonta, yayinda sunanta daya ji Hanan na kira ke masa yawa a kirjinsa, (Abrar) "you re so special my decent one including your name" ya fada cikin shauêkin sonta, tabass shi so babu ruwansa da kyau, kudi, wayewa, talauci, hankali ko rashinsa, mutum kan kamu da gashi ko da be shirya ba, hakika zafin soyaayar dayake mata baya jin akwai wanda ze yiwa masoiyarsa irinsa, domin a kallon farko a kuma haduwar farko zuciyarsa ta buga domin ita kadai, babban damuwarsa yanzu "mummy" domin so yake ya mallekata ta zamo halalinsa ko da ayau ne shi ashirye yake, kara binta da kallon yayi ganin yanda take hargitsa masa kayansa awardrobe a kalla ya gyara dakin yafi sau a kirga yau domin musamman yaki zuwa aiki saboda kula da ita, amma daya gama zata sake hargitsa dakin, sadai sam be damu ba matukar hakan ze bata farinciki, abunda yafi damunsa waye yake bibiyar rayuwarta? shine amsar dayake son sanin...

ganin yadda take sosa kai hadi jikinta yasa jin ba dadi, domin tabass tana da bukatar wanka dama wanke kanta, saboda tun ranar daya sake haduwa da ita rabonta da wanka gashi bata yarda da hanan bare yasa tayi mata duk da be manta gargadin mummy ba, cije lebbansa yayi kana yace
"mummy why!"
domin data amince da a ranar ze sanar da daddy cewa a aura masa ita domin ya samu daman kula da ita yanda ya kamata.

sai kuma yayi tunanin hada mata ruwan wanka ko zata iya wanka da kanta, mikewa yayi ta kuwa biyosa abaya, bayan ya hada mata ruwan wanka yace
"my decent one kiyi wanka kinji ina jiranki"
itama cewa tayi "my decent kiyi wanka kinji ina jiranki" tafada cikin kwaikwayonsa, murmushi yayi kawai ya fito hadi da rufe toilet din...

yana zaune yana jiran fitowar, ya kuwa ji karan bude kofa, kurawa hanyar ido yayi yana jiran karasowarta, "ya salam" yace bayan ta bayyana gabansa domin gaba ta jika kayanta da ruwa batareda ta cire kayan ba, ruwan har diga yake a kasan tiles, kusa dashi tazo ta zauna tana kankame jikinta alamun sanyi domin Ac na kunne, cikin tausayinta ya bude wardrobe dinsa ya dauka rigar sanyi mai kauri yasanya mata wanda yayi mata yawa, shi be san yadda ake kula da mutum ba, besan abunda ze mata taji saukin sanyin dake shigarta ba, Ac ya kashe kana ya riko hannunta ya kwantar da ita kan gadon hadi da lullubeta da bedsheet, kallonsa kawai take bata ko kiftawa yayinda hakoranta ke karo da juna "daf da kunnenta yace
"i love you"
cikin kunnensa yaji dariyarta na tashi da karfi, kallonta kawai yake cikin matsananci sonta, sai ta maimata maganarsa ta ce " i love you" yayinda ta cigaba da dariyar har bacci yayi nasaran dauketa...

Ajiyar zuciya ya sauke domin tana bukatar bacci, hakan zesa kwakwalwarta ya dinga samun hutu, dakin ya shiga gyarawa bayan komai yadawo tsaf tsaf, yaji ringing wayarsa na tashi saura picking call din yayi domin bayason ta tashi, number asibiti ya gani, dafe kansa yayi domin yasan kwanan zancen... yana dagawa yaji ance

"hello sir an kawo wani patient yanzu cikin mayuwanci hali your attention this needed please"

runtse ido yayi yayinda yasake waresu kan Abrar cikin rashin jin ba dadi yace " i will be there in a jiffy" ya katse wayarsa...

wanka yayi cikin sauri ya shirya, kana ya fice yana waiwayon Abrar yana fatan kada ta farka har ya dawo...


fitarsa da awa biyu kuwa ta farka da kukanta, yayinda ta shiga hargitsa dakin kamar ba dakin daya gyara ba, sai kuma ta mike ta sauko kasa, ai kuwa tayi arba da mummy, amal, hadi da hanan dake kwance, domin tun dazu takeso mummy ta tashi ta haura saman ya Aabaan domin duba jikin Abrar, amma mummy taki tashi kamar ma ta fahimci abunda takeson yi, Abrar kuwa ganin mummy yasa ta rabe jikin bango tana mata kallon tsoro, harara mummy ke jefa mata hadi jifan ta da mugayen kalamai, Abrar abin tausayi yayinda Hanan ke jin zafi abunda ke mummy keyi sai de bazata iya cewa komai ba...

"mtsssssweew mummy ni wallahi kada mahaukaciyar yarinyar nan ta zauna da bikina a gidanan dangin Adam su raina mu, kawayena ma ajina ya zube a idanunsu, (kasancewar bikin Amal saura wata daya, da saurayinta Adam wanda sun dade tare tun tana level 2 a jami'a).

mummy kuwa kasa bawa Amal amsa tayi saboda takaicin abinda ke cinta arai ace kamar ita danta ya rasa wacce yakeso sai mai tabin hankali, kuma wacce bata tare da budurcinta, itakam ina zata kai wanna abun kunya, idan har daginta ma suka ji wanna labarin ai ta banu, tabass taso Abrar tun kafin ma ta ganta, amma banda yanzu....

"mummy kiyiwa anty amal magana ta daina zagin bestie na, na shafa fada ita ba mahaukaciya ba ce"

wani mugun kallo mummy ta antaya mata, bata kara cewa komai ba tanufi wajen Abrar dake rakube har yanzu sai de tana zuwa wajenta ta cigaba da boye kanta cikin jikinta, Hanan na riko hannunta ta ruga sama bangaren Aaban aguje, dariiyar mugunta Amal ta sakarwa Hanan, kuka Hanan tasa ta nufi dakinta....

bangaren alhaji shettima kuwa zaune suke a guest house dinsa shi da yaransa su kwaro, "anya kwaro kuna aikin ku kuwa? ace har yanzu baku ganta ba duk tsayinç kwanakin nan?" alhaji shettima yafada cikin damuwa

"ai oga muna kokari fa, har dare muna nemanta, amma ko me kama da ita bamu gani ba, Amma oga mezai hana mu bincika asibitin daka sa muka dauko ta kwanaki, kila wani ya buge ta tana can" kwaro ya fada cikin muryansa ta yan jagaliyya bakinsa har wani karkacewa take, yayinda yake muzurai da kwala kwala idanunsa masa launin ja.

dariyar jin dadi alhaji Shettima yayi yayinda yake shafa katon tumbinsa cikin jin dadi yace "wato kwaro kana da kaifin tunanin shiyasa nake yinka, kana da tukwuci na musamman haka za'a yi kuwa domin yanzu zamu tafi, tare da ni za'a je domin wanna karon zan je ne amatsayin ni ne mahaifinta bata tayi..."

gaba daya suka mike suka fito haraban gidan, kana suka shiga motar alhaji shettima kirar BMW kana suka bata wuta isar asibitin kuwa alhaji shettima yace kwaro da saura su zauna cikin motar, manu ya biyosa domin shi yayi shigar mutunci kaf cikinsu, babu musu suka zauna yayinda kwaro yace
"amma oga kana ganin matsala kawai ka bugo waya mu shigo, domin muna tare da kayan aiki"...

murmushi jin dadi alhaji shettima yayi yana jinjina kansa.

daidai lokacin Aaban ya fito yayinda waya ke makale akunnensa da alama waya yake kuma me muhimmanci, ga jakar aikinsa a hannu wanda ya nuna gida ze je domin gaba daya hankalinsa naga decent one dinshi, daidai ya fito daidai lokacin alhaji shettima suka taho... kafada da kafada haka Aaban da alhaji Shettima suka wuce juna... cak alhaji shettima ya tsaya hadi da waiwaya wa ya kalli Aabaan....

manage please yau aiki ya min yawa a gida.

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan😉✍

kucigaba da comment domin shi ze dinga karfafa min gwiwan typing, insha Allah inason kammala book dinan kafin ranar sallah idan kuma be yu ba toh, sai bayan sallah domin ina tafe da books masu zafi bayan sallah'n son so nake muku jama'ata💖


https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
(A heart touching story)

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚

written by noor Eemaan

page-33-34

kura masa ido yayi yayinda yake jin wani yanayi atare da kyakyawan saurayin da ko fuskarsa baya gani, haka kuma yaji hankalinsa gaba daya ya raja'a ga wanna saurayin wato Aabaan.
"oga ya kana yawa ne, kazo mu tafi muyi abunda ke gabanmu ko ya?" manu ya katse masa tunaninsa cikin muryansa wanda daga ji zaka tabattar da cewa shi din mashayine...

Ajiyar zuciya alhaji Shettima yasauke batare da ya kuma bawa manu amsa ba suka nufi cikin asibitin still hankalinsa naga Aaban,.... duk wani ward dake cikin asibitin suka duba amma babu ko me yanayin kalar fatar Abrar bare me kamaninta, guiwa asanyaye suka fito yayinda alhaji Shettima ya kurawa daidai inda motar Aaban ke fake dazu ido, sai de yanzu motar bata nan, huci mai zafi ya furzar ya kasa gane dalilin daya sa tunanin wanna saurayin kasa barin zuciyarsa.
"oga da dukkan alamu bakuyi nasara ba domin naga fuskarsa tayi ja jawur kamar jan kosai" kwaro ya fada ko dar be ji ba, alhaji Shettima ya saba da maganganun kwaro domin akwai yaba wa mutum magana mara dadi musamman idan ya shahu, maimakon ya bashi amsa se yace "kwaro baku ga wani saurayi tsaye a kusan da motata dazu ba?"
"Allah ya ja da ran oga ina mu ina lura dashi tunda ba abunda ya kawo mu ba kenan".
alhaji Shettima be kara cewa komai ba ya bawa motar wuta suka bar asibitin.....

bangaren Aaban kuwa yana isa gida ya tarar da mummy zaune kan kujera, gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, hakan ya kuma taba zuciyarsa domin ba haka ta saba tarban sa ba, part dinsa ya nufa yana fatan har yanzu Abrar bata tashi ba, mummy da kallon takaici ta bisa ganin wai saboda Abrar ya daina night duty ita shekara nawa tana fama dashi akan ya daina aikin daren nan amma yaki sai yanzu saboda mahaukaciya ta aiyana aranta....

yana shiga dakinsa ya dora hannu a kugu ganin yadda dakin ya dawo kamar ya shekara be ga gyara ba, kallonta yayi yaganta zaune da kayansa riga da wando ta dora saman doguwar rigar jikinta, murmushi dabe shiryaba ta tsubuce masa, domin kayan sunyi mata yawa matuka, cikin tafiyarsa ta lafiyayyen namiji ya shiga takawa zuwa gareta, kusa da ita ya tsaya yayinda ya kura mata idanunsa masu matukar kyau, sai a lokacin ta lura da shi, dariya ta shiga yi kana ta hau saman gadon sosai ta shiga tsalle tamkar yar shekara 5 kallonta ya dinga yayinda murmushi ya kasa barin kyakyawar fuskarsa, gasashiyar kaza mai romo daya siya mata ya bude mata ledan hadi da janyo yar table din glass ya dora akai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yayi mata nuni da naman, take kuwa ta fara ci da hannu biyu, hadi da debo romon da hanunnta ta dinga sha, kura mata ido yayi yana mata kallon birgewa... sai daya gama more kallonta kana ya shiga gyaran dakin domin duk gajiyan daya debo baya jin ze iya zama haka cikin dakin, bayan ya gyara ko ina ya dawo hayyacinsa kana ya bude sif dinsa domin daukan kaya sawa saboda so yake yayi wanka ana daf da kiran magriba, jiyayi ta rungummesa ta baya tana goge idanunta abayansa, kallon hannunta dake rungume akirjinsa yayi yaga gaba daya ta shafa masa ruwan romo da mai hannunta farar rigarsa, saurin juyo da ita yayi yaga tana ta runtsa idanunta, da alama tasa yaji ne idon, sai kuma ta sake daukan hannun yajin tana murza idon dashi, kamo hannun yayi ya nufi toilet da ita cikin sauri, sabulu yasa ya fara wanke hannu kana yasa tattausan hannunsa ya shiga wanke kyakyawar fuskarta sai daya tabattar dacewa yaji ya fita, bayan ta bude ido ta kalli kanta amadubin dake gaban sink, sai ta kuma juyawa ta kalle shi hadi da kyakyale dariya, kumatun ta yaja kana ya riko hannunta suka fito, direct kuwa ta nufi wurin sauran kazarta, cikin hanzari ya dauke ya shiga yagowa yana sanya mata a baki, haka ya dinga yi mata har ta cinye tas, hannunsa ta kamo ta sa harshenta ta shiga lashe hannun, kallonta kawai yake batare da ya hanata ba sai don kanta ta sakar masa hannun, a kwandon shara ya zubar da ledan kana ya shiga toilet, shower ya sakar wa kansa yayinda ya dafe bango da dukkanin hannayensa ruwan na dukan lafiyayyen farar fatarsa, yayinda tunanin yadda ze mallaki Abrar ke yawo azuciyarsa, yasani baya da matsalan komai se mummynsa yakuma rasa ta yadda ze bullowa al'amarin...
cikin toilet din ya sanja kaya kana ya busar da sumarsa da hand dryer ya fito, yana fitowa aka kwalla kiran sallah beyi wata wata ba ya bude kofar baya ya nufi masallaci dake cikin gidan, bayan ya dawo ya ganta kwance bacci ya dauketa, rigar nan ta tattare izuwa wajen cinyarta, take idanunsa suka gano masa kafarta da daya tafi daya kumburi, cikin sauri ya karasa gadon bayan ya gyara mata rigan, kafafun ya dora kan cinyarsa, ya kuwa ga daya yafi daya kumburi nesa ba kusa ba, dafe kai yayi cikin tausayinta yanzu dama kafarta tayi targade take tsalle tsalle hadi da gudu? shin bata jin zafi ya tambayi kansa, shi kam be taba lura ba domin rigar daman har kasan kafarta ta rufe gashi bata yi wata alama daze sa ya ankara ba, yama rasa yaushe taji wanna targaden? Gwada taba kafar yayi yaga bata motsa, sake tabawa da dan karfi yayi domin so yake ya gyara mata, takuwa farka ta sakar masa ihu hadi da kai masa bugu, be hanata ba har ta gaji ta daina, hadi da takurewa waje daya,
"am so sorry" ya fada yana kallonta, mutuniyar ko kallon gefensa bata yi ba.

Shimfuda sallaya yayi ya dauko qur'ani ya shiga karatu har aka kira ishaq kana ya mike, cikin nutsuwa yake gabatar da sallahn'sa bayan ya iddar yayi addu'oinsa masu tsaye, kana ya ninke sallayan, wayarsa ce ta fara ringing "my Dad" ya gani arubuce, amsa kiran yayi hadi sallama, daga bangaren daddy bayan ya amsa yace
"abokina ku sauko kuci dinner muna jiranku"
da kallo yabi wayar bayan daddy ya katse kiran, shi kam beso hakan ba, amma ba yanda ya iya, daukarta yayi cak suka fara saukowa, domin sam bayaso ta dinga take kafarta saboda dada kumburi ze kara yi tunda ba'a gyara ba, ya kuma san tana jin zafi kawai yanayin gushewar hankalin datake ciki yasa sam bata nuna alama..
suna daf da zuwa inda suke ya sauketa, kana ya rigo hannunta suka karasa wajen
"mum dad barka da dare" ya fada yana jawa Abrar kujera, daddy kadai yace "yawwa barka kadai abokina" yayinda mummy ta cika tayi fam tun lokacin da daddyn yace su sauko ta fahimci da Abrar yake nufi, ita yanzu komai ya jagule mata domin daddy ya dauke mata wuta sam yanzu baya shiga harkanta wanda tasan cewar fushi yake da ita domin sarai tasan halinshi, ga kuma danta mafi soyuwa aranta basa cikin yanayi me kyau, wanda hakan ke domunta domin ba haka suka saba rayuwa ba, gashi kuma bata san Abrar zuri'arta...

Bangaren Amal ma haushi ya cikata, ita wallahi ta tsani abrar, Hanan ce ta kai kallonta ga Abrar dake takure tace
"bestie Abrar yakike, how's your health"
Abrar kurawa Hanan ido tayi kamar meson tuno wani abu se kuma ta yi dariya hadi da maimaita abunda Hanan din tace, dariya daddy da hanan din suka mata, hanan tayi serving din su kana ta cikawa abrar plate hadi da nama da yawa domin tasan Abrar bata wasa da nama, tana direwa gabanta ta shiga ci hannu baka hannu kwarya, Amal da mummy se antaya mata wani mugun kallo suke yayinda Amal ke nata aboye domin tasan matukar ya Aaban ya ganta ta banu... sede Abrar batasan suna yi ba domin hankalinta naga abincinta...


Daddy ne zaune a bedroom dinsa yayinda laptop ke kan gado yana dannawa da alama abu me muhimmanci yake, fuskarsa sanye da medicated glass, ahankali ta bude kofar ta shigo, kan gadon ta zauna tace
"ina son magana da kai daddyn'su"
yakai muntuna goma be bata amsa ba, kana yace "ina jinki"
"haba daddyn'su laifi me na maka har haka"?
sai alokacin ya kashe laptop din hadi da zare medicated glass din idonsa yace" ni kike wa wanna tambayar? baki ji kunya ba? tsaya in tambayeki aysha mi kika dauki kanki eh? kina tunanin ita yarinyar nan Allah baya sonta ya jarrabe ta? ko kina tunanin Amal or Hanan bazasu iya shiga wanna halin datake ciki ba? shin idan sune awanna halin zaki ji dadi ace sun samu masu son su tsakani Allah amma uwar mijin taki amincewa? yi tunani ya zaki ji aranki, kamata yayi ki godewa Allah ya baki da nutsatse, kina tunanin cewa bazan iya aura masa ita ba ko ba da amincewarki ba? toh idan hakan ne tunanin ki, kinyi karya domin nine ubansa ina ko wani right akansa, dalili daya ne ya hana ni aikata hakan domin kawai yasamu albarkanki arayuwar auransa, kin ki tsaya ki ji abunda Hanan zata ce mana, ko Hanan bata ce komai ba ninasan kaddara ce ta fada wa Abrar domin aranar da'aka yi taron su a cyprus duban jama'a sun shaida nutsuwarta, cikinsu harda ni, amma saboda bakya ganin girmana muna magana a gaban yara kika zage yar mutane kika fice afalon bayan bamu gama magana ba, hakan da kika yi yadace? ya kamata ki nutsu kiyi tunanin, ace zabinki shine zabin danki batareda ku biyun ku san da hakan ba, bakya tunanin akwai wani alkhairi a tarayyansu? gaba daya kin aro wa kanki wata dabi'a mara tushe saboda kawai son zuciya da kuma bakin mutane, da bakin mutane na kisa da tuni bama a raye yanzu, idan bama taimakon juna tayaya zamu cigaba, mai kudi yace lallai sai me kudi, talaka sai talaka, mai hankali sai me hankali, mai lalura sai me lalura, gaya min idan bamu taimakon juna tayaya zamu samu cigaba akasarmu da ma duniya baki daya, arayuwarnan idan zaka yi abu yishi da zuciya daya hadi da kyakyawan niyya sai kiga Allah ya faranta miki ta hanyar da baki yi zato ba, ina shawartarki kiyi a hankali kada ki ji kunya nan gaba, ke musilma ce ki yarda da kaddara me kyau ko akasinta ta haka ne imaninki ze cika" .... daddy ya karasa maganar cikin fushi, sai kuma yace "ki rufemin kofana idan kin fita bacci zanyi" yana gama fadin haka ya yi kwanciyarsa hadi da juya mata baya, hajiya mummy kuwa hawaye ke zuba idanunta wanda na kasa gane ko na menene, takai mituna sha biyar masu kyau tana tunanin maganganun da daddy ya fada mata, kana ta mike asanyaye ta fice zuwa dakinta, nan ma kwanciya tayi kan makekken gadonta tana juyi yayinda kalaman daddy ke mata yawa akunne.

Wanna kenan

Washegari kuwa Aaban ya kai Abrar gidan wani gyara domin agyara mata kafarta, lokacin da mutumin ya fara gyaran ta runkunkumeshi, sosai take ihu mai dauke da kuka hadi da dariya, bawan Allah Aaban kuwa ya sha cizo, da yakushi, an dau tsahon lokaci ana gyaran domin kafar tayi tsami sosai, wani magani mai kamar mai ya bawa aaban yace a dinga shafa mata, kudi masu yawa Aaban ya bawa tsohon kana suka fito daga soro gidan mutumin tana rungume gefen sa...

yana kokarin sata a mota, daidai lokacin motar alhaji shettima daya bawa su kwaro domin neman abrar ta gifta, "wait wait mana, kwaro kamar ga yarinyar nan da oga ke nema fa" inji manu....


bangaren ammi kuwa gaba daya tasake lalacewa saboda damuwa, da abinci da bata iya ci, komai ya gama fice mata arai har da garin, tana add'ua Allah ya bata sa'an fita daga gidan idan ta nemo yarta zata koma kasarta ze fiye mata, tana awanna tunanin taji ana bude dakin alhaji ta kuma san da kyar alhaji shettima ya dawo awanna lokaci, cikin daga murya

tace "waye nan? abude ni dan Allah!!!"

cikin mamaki wanda ke kokarin bude kofar alhaji ya dakata hadi da nufar kofar dakin ammi yace
"matar yallabai ce?"

cikin rawan murya ammi tace
"eh nice, rufeni yayi adaki, batareda yasani ba"

mutumin be kawo komai aransa ba duk da yayi mamaki....ya kuwa zare sakatan hadi da bude kofar, take ammi taga

Please Login or Register in order to submit comment