Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

safa da marwa alhaji shettima yake abedroom dinsa, gaba daya yarasa nutsuwarsa, kyakyawar fuskarta kadai ke masa gizo tun bayan ganin daya mata airport, ga wutar sha'awarta dake sake ruruwa ajikinsa, abun har mamaki yake bashi tayaya akan wanna yar karamar yarinya mai karancin shekaru zata sashi awanna yanayin?...

"ammina wallahi naga kin kara kyau sosai, yanzu wazai ce ke kika haifeni" abrar dake kwance kan cinyar ammi tafada cikin shagwaba tana jujjuya manyan fararen idanunta. dariya mai sauti ammi tayi tana girgiza kai "abrar zan fasa miki baki fa kin raina niko" ammi tafada tana dungure mata kai cikin wasa "sorry ammina tafada tana sake rungumeta. shafa kanta ammi tayi tana cewa "bari na saita mana dinning table muci abinci sai ki bani labarin kasar dakike karatu yama sunan kasar"?
"cyprus ammi"
"ywwa cyprus" ammi ta maimaita bayan ammi tayi setting table tace" abrar bari na kira daddynki muci abinci" take ta bata rai ( tofah jama'a kuji mun abrar mutum da gidansa🙄😃)
cikin nutsuwa suke cin abincinsu yayinda alhaji shettima ya kurawa lips dinta idanu har ammi ta ankara ta dan bugi kafadarsa cikin rashin gaskiya yace " wato hajiyata sai yanzu nakara ganin kamanin ku da diyata abrar" murmushi kawai ammi tayi bata kawa komai aranta ba, yayinda mutuniyar taku ko dago kanta batayi ba, shikam alhaji shettima ya daina damuwa da rashin sakewa da abrar ke nuna masa ya dauka hakan yanayinta yake tunda bai taba ganin ta furta ko nuna alamun rashin son shi amatsayinsa na mijin amminta ba...

suna gama jin abinci sai ga kiran hanan ta wayar ammi, nan suka fara hirarsu daga karshe hanan ta bawa mummyn su waya suka gaisa da abrar...

kokawa sosai sukeyi da mutumin dako fuskarsa bata gani domin ya rufe da face mask, ganin tana bashi wahala yasa wanna mutumin kwada mata kyakyawan mari daya sa ta saki ihu... afirgice ta farka ta ihun abakin ta, gaba daya ta jike da gumi, kirjinta bugawa yake tamkar zae faso rigarta ya fito, kallon agogan bangon dakinta tayi karfe 1:30am ya nuna mata dogayen kafafunta tasauke kasa kofar bathroom ta murda ta shiga, alwala ta dauro kana ta shimfud'a sallaya salla raka'a hudu tayi bayan ta iddar tayi karatun alqur'ani hadi da addu'a, domin sosai wanna mafarkin da take yi kwanan ke tsoratata...

"abrar dole in dinga damuwa domin basan ko yaya raheenat tareda mijinta na raye ba, ina kokarin boye damuwata domin kada alhaji yaji ko na raina kokarinsa akanmu ba"
"in sha Allah suna cikin koshin lafiya ammi idan kuma baza raye, Allah yasa sun samu rahamar Allah"
"hakane diyata ameen" inji ammi tana alfahari da yartata...

"ooh wanna yarinyar tana son haukata, alhaji shettima yafada yana dungure kansa, karshe dai haka ya baro office dinsa domin aiki bazai yu ba, sallama yayi cikin hadadd'an falon, abrar ce kadai afalo tana yankawa ammi cucumber domin wani film datake matukar so ake haskawa bataso tayi missing koda waje daya ne dalilin zamanta afalo kenan domin itakam tafison zama bedroom dinta, saboda sam bata kaunar ganin alhaji ko kadan ita kanta batasan dalilin tsanar hakan nan taji tsanarsa aganin farko data masa... "sannu da zuwa" tafada bayan ta amsa sallamarsa.
"yawwa daddy's girl" yafada yana binta da kallo yayinda yake ta faman lashe labbansa tamkar tsohon maye. "ina amminki?" ya tambayeta
"tana kitchen" ta amsa masa batareda ta dago ba...

daddare da misalin karfe shadaya daidai alhaji shettima ke tsaye abakin kofar dakin abrar yana leken ta tajikin window, sanye take da pyjamas farare sai bakin hijab half sunnah akanta, cikin nutsuwa take baccinta, take alhaji shettima yakara jin wani kwadayin kasancewa da ita, domin ayau yafara ganinta a irin wanna shigar duk da kayan basu kamata ba haka kuma basu nuna tsaraicinta ba, amma mafi yawan lokuta yafi ganinta da dogayen riguna da kuma hijabs dogaye ganin ta gyara kwanciyarta yasashi saurin barin wurin...

dakyar alhaji shettima yayi bacci awanna daren adalilin son zuciya da kwadayi daya daura wa kansa, amma ya kudurta aransa cewa agobe zae kawar da kishirwan daya dame sa, tunanin ta yanda zae bullowa al'amarin batareda an samu matsala ba.

*WASHEGARI DA YAMMA*
awani babban pharmacy alhaji shettima ya shiga can sai gashi ya fito da leda magani ahannunsa yana sakin murmushi ganin yana daf da cimma burinsa.....




SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌


A taya ni share please🙏

noor Eemaan ce✍

manage pls ba yawa wallahi bana dan jin dadin jikina.

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

page9-10

kwance abrar take hannunta rungume da teddy, sosai take jin wani matsananci zazzabi na sake rufeta ga zuciyarta da bugunsa yafi na koyaushe, duk da ammi ta kira doctor ya duba ta amma bata ji wani sauki ba sai ma karuwa da ciwon ke mata cikin zafin ciwo tace " ya Allah help me out" ta karasa wasu hawaye masu zafin gaske na biyo kyakyawar fuskarta...


"assalama alaykum" murya alhaji shettima ya karade gaba dayan falon, ammi dake kokarin shiga dakin abrar da hot tea ahannunta ta dakata cikin sauri alhaji shettima ya karaso wajenta "hajiyata lafiya na ganki haka" yafada fuskarsa na nuna damuwa. "abrar ce bata da lafiya" ammi ta fada hawaye na ciko idanunta. take ledan hannunsa ta fadi, cikin sauri ya dauka gudun kada ammi tagani, sai dai ya makaro domin ta gani " maganin waye wanna alhaji?"


" uhmm...eh...wato... maganin rage gajiya dana ciwon jiki na siyo miki domin kina yawan aikatuwa hajiyata kuma kin ki bari yan aiki suyi, yanzu ina abrar din ya jikin nata"? duk da halin da ammi take ciki na damuwa be hanata murmushi ba, domin alhaji yana kulawa dasu iya iyawarsa shiyasa yake kara samun matsugunni azujiyarta. " muje in duba ta" ya katse mata tunaninta babu musu tayi gaba yana binta abaya...


idanunta arufe tamkar mai bacci amma azahirin idanunta biyu kuma jin muryan alhaji shettima yasa ta rufe idon, "abrar ga tea ki tashi ki sha kinji" shiru babu amsa.

"bacci take fa ki barta kawai"

"ai bata ci komai ba alhaji"

ammi tafada cikin damuwa, cikin son kwantar mata da hankali yace " kada ki damu, kila data tashi taji sauki, sai taci abincin muje" duvet tasake rufa mata kana ta bi bayan alhaji asanyaye, abrar najin fitar su ta bude idanunta dasuka yi ja hadi da kumburi...


alhaji shettima na shiga dakinsa ya boye maganin daya siya, kana afili yayi wani dariya dashi kadai ya bawa kansa sanin ma'anarsa " a yau sai na kawar da kishirwan danake fama dashi akanki, koda zaki mutu kuwa domin tunda nake ban taba neman ko son abu narasa shi ba"...

bayan isha abrar tadan ji kwarin jikinta har dinner ta fito duk da bata ci wani abun kirki ba amma kwarai ammi taji dadin.

*11:00pm na dare*

"karbi ki sha maganin nan, domin ina tabattar miki cewa zaki ji dadin baccin ki ayau"

"nikam alhaji daka barshi bana jin shan maganin nan" domin hakan nan taji hankalinta be kwanta da maganin ba.

"a'a hajiyata idan kika min haka bazan ji dadi ba ina son kyakyawar matata tasamu bacci mai matukar dadi musamman ayau"

ba musu ta karba ta sanya abaki ya mika mata ruwa ta kora dashi, bayan awa daya ammi ta fara jin wani azababben bacci tamkar wacce ta shekara bata runtsa ba....

alhaji shettima dake kallonta tun dazu ya saki wani murmushi jin dadi, gyara mata kwanciyan yayi hadi da rufeta da bedsheet mikewa yayi ya shiga toilet be dau lokaci mai tsayi ba ya fito da alama wanka yayi...

*1:00am na dare*
a hankali ya bude dakin ya fita, duk da yana tabbacin cewa ammi bazata farka nan kusa ba, yana zuwa daidai bakin dakin abrar ya fito da facemask ya rufe fuskarsa sai ya zamana baka ganin komai nasa sai idanunsa...

cikin kwanciyar hankali take baccinta fuskarta tayi fayau har dan rama tayi na rashin lafiyan data yi, sadaf sadaf ya karasa bakin gadonta salitaf ya fito dashi daga aljihunsa a hankali ya manna mata abakinta haka ma hannunta ya kama yana kokarin daurewa ta bude idanunta, kasancewa bacci ta bai yi nisa sosai ba afirgice ta duro daga kan gadon tana zare idanunta, bakin kofa ta nufa tana kokarin budewa amma ina ta kasa domin ya rufe da key kuma key din baya jikin kofar, jitayi an daga ta cak an wullata kan gado baki ta bude tasaki ihu amma inaa ihun be fito ba sai a lokacin taji alamun anyi silling bakinta, hannun tasa zata cire salitaf din ya damko hannu, shafa jikin ta yafarayi jitayi wani karfi ya zo mata fisge dayan hannunta tayi nan suka hau kokawa har Allah ya bata ikon cire facemask din fuskarsa, tsoro, firgici, mamaki ne suka dirar mata lokaci daya kara murza idanunta tayi, amma still daddy mijin amminta take gani, sotake tayi magana amma ba hali, abangaren alhaji shettima kuwa ba haka yaso ba, domin so yayi yagama abunda zeyi ba tare da taga fuskarsa, amma duk da haka bayajin ze iya hakura da ita...

nan ya kara danne hannayenta da hannunsa guda daya, ya fara yi mata abubuwan da baki bazai iya furtawa ba, ganin tana neman bashi wahala kawai sai ya yaga rigarta baiwar Allah abrar kuwa sai kokawa take amma takasa kwatar kanta gashi daman ba lafiya gareta ba...

babu ko digon tausayi ya afka mata, kwata kwata beyi la'akarin cewa itadin karamar yarinya ce ba, beyi la'akarin cewa itadin yar matarsa ce ba, beyi la'akarin cewa ita din tamkar yar cikinsa ce ba, gaba daya kwadayi da son zuciya sun dakushe imaninsa, abrar kuwa azaban daya ratsa kwanyarta yasa tasaki wani razananan ihu wanda da'ace bakinta abude yake toh ba shakka har makota sai sun ji ihunta, daga nan bata kara sanin inda kanta yake ba...


*BAYAN AWA DAYA*
sauke numfashi alhaji shettima yake yi yayinda katon cikinsa ke sama da kasa, salitaf din bakinta ya zare ganin ko motsi bata yi ba ya bashi mamaki, jijjiga ta yayi amma shiru bata motsa ba, ruwa ya debo ya kwara mata nanma shiru, bude dan karamin firgji dake dakin yayi, ya fito da babban goran ruwa mai matukar sanyi ya kwara mata shi duka ajiki amma still shiru bata motsa ba, take wani gumi ya karyo masa, gaba daya kansa ya kulle, hannu ya kara ahancinta yaci tana numfashi ajiyar zuciya ya sauke

dakinsa ya koma, ya canza kaya yazo fita sai ya tsaya yakalli ammi dake bacci sai kuma ya bar dakin cikin sauri, gaba daya ya ciccibi abrar har zanin gadon daya baci da jini, kai tsaye parking space ya nufa a kujeran baya ya shimfudeta kana ya zagaya ya tada motar hadi da danna horn take mai gadi ya mike afirgice domin har bacci ya fara daukarsa, ganin alhaji da kansa ne yasa shi saurin bude gate din yana cewa "lafiya kuwa alhaji" amma ina alhaji be ji sa ba...

nesa da asibiti alhaji shettima ya faka motarsa, lullube ta yayi da zanin gadon kana ya dauke ta cak yanufi asibitin da ita yana tafiya yana waige waige dayake kuma dare ne domin uku saura minti goma babu mutane ahanyar, daidai bakin gate din asibitin ya kwantar da ita cikin sauri-sauri gudu-gudu ya koma motarsa hadi da bata wuta ya bar wurin...

daga dakin operation ya fito agajiye likis yake, office dinsa ya shiga yana godiya ga Allah daya bashi ikon kamalla operation din sucessful, burinsa yanzu ya tafi gida yasamu bacci, ruwa mai sanyi ya dauko a firgji, tunda ya kafa bakinsa bai dire ba sai da ya shanye ruwan tas, jakarsa ya rataya hadi da daukan mukullin motarsa da wayoyinsa ya fito, daidai inda yayi parking motarsa ya nufa ya tayar da ita mai gadi ya bude masa get ya fita, yana fita idanunsa suka hasko masa abu cikin farin zanin gado domin akwai wadataccen haske aciki da wajen asibitin dauke kansa yayi tamkar be gani ba ya cigaba da tafiya...

har yayi nisa yaji hankalinsa yaki kwanciya ga abunda ya gani, sai gizo yake masa juya akalan motarsa yayi ya shiga dawowa hanyar asibitin yana zuwa bakin gate din asibitin ya fito, kai tsaye wurin ya nufa tsugunnawa yayi ya kurawa farin zanin ido yayinda yake bin duk inda jini ya bata ajikin zanin da kallo, babu ko digon tsoro ya yaye zanin da ya rufe afuskarta take beautiful face dinta ya bayyana gabansa ne yafadi domin tsaf ya fahimci abunda ya faru ...

"innalilahi wa innah ilaihi raju'un" ya furta can kasan makoshi, jiyayi akwai alamun numfashi atare da ita cikin zafin nama ya daga ta cak gabadaya har da zanin gadon ya nufi cikin asibitin da ita...

PLS SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan ce✍

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

Written by noor Eemaan
wattpad@noorEemaan

Page11-12

cikin sauri sauri yake tafiya da ita yayinda abrar ke kwance a faffadan kirjinsa tamkar mataciyya, nurses dake duty suka yi saurin turo gadon nan na marasa lafiya, ko kallonsu be yi ba ya shiga office dinsa da ita, sororo nurses din nan suka yi suna kallonsa " ko dai kanwarsa?" daya cikinsu ta tambaya.

Wata daga cikinsu na shirin bada amsar suka ji ya bude kofar, fuskarsa a dinke tsaf yace akawo masa box din treatment yana fadin haka ya koma office dinsa, cikin sauri aka kawo masa, har nurse din ta nemi taimaka masa ya dakatar da ita, ba musu ta fice domin kaf ma'aikatan asibitin suna matukar girmama shi domin sosai yake musu kwarjini...

key ya murza ajikin kofar cikin tafiyarsa dake nuna shi din cikakken namiji ne mai ji da kuruciya, ya nufi dan gadon dake office dinsa ya yaye labulen daya rufe gadon domin babu wanda zai taba tunanin da mutum kwance aciki, kura mata idanu yayi tausayinta fal zuciyarsa be taba ganin rashin imani irin wanna ba yarinya yar karama akawa wanna mumunan aiki, shin yaushe za'a daina yiwa yara mata fyade? yaushe za'a daina keta musu haddin su, yaushe za'a daina wulakantasu? duk ya jerowa kansa wadannan tambayoyin aransa...

sanin cewa tana bukatar taimakon gaggawa yasa shi fara yaye doguwar jikinta sama hadi da runtse idanunsa kana ahankali ya ware su awajen "damn it" ya fada yana buga gefen gadon da karfi, a akaro na farko bayan girmansa yaji hawaye masu dumi sun biyo kuncinsa, domin ba karamin ciwo taji ba jiyayi dazai ga wanda yayi wanna barnan da babu abunda ze hana shi farka shi gida biyu, cikin kwarewa yake aikinsa yayinda idanunsa sukayi wani ja tamkar garwashi, duk wanna dinki dayake yiwa abrar ko motsin bata yi domin zaka yi tunanin bata da rai a yanda take kwancen, bayan ya gama ya daura mata drip hadi da mata wasu allurori domin yaji jikinta da zafi alamun akwai zazzabi.....


hannu yasa akugu yana zagaye office dinsa hakan nan yaji wani radadi na domin sa azujiya, bacci da gajiyan dayake ji duk sun kaura a idanunsa, kan kujeran office dinsa ya dawo ya zauna yana mai daura kansa a table, bayan wasu mintuna dayake tabaccin cewa ruwan ya rage ya mike ya cire mata, kallon saman rigarta yayi yaga ayage tabaccin sunyi kokawa kenan? baya jin ze iya fita da ita dakin hutu da yaggegen rigar jikinta can tunanin wani riga daya siyo wa kanwarsa ya fado masa, wanda yake yawan mantawa baya kai mata gida locker ya bude ya dauko rigar hadi da warware ta rigar mai kalan sea green ne, sanya mata yayi hadi da janye na cikin daya yage kasa yalwataccen gashinta daya rufe mata fuska ya shiga tattare mata shi zuwa baya...


Har karfe biyar na asuba bata farka ba sai ya tafi masallaci yana hanyar dawowa ya lura da motarsa abakin gate, dafe kansa yayi domin shaf ya manta, kuma ikon Allah key din na jiki motar ayanda ya bari, rufe motar yayi ya nufi cikin asibitin yana fatan ta farka...


Tana nan a kwance still tamkar gawa, kallonta yayi na yan mintuna kana ya dauke ta cak ya nufi dakin hutu da ita, bayan ya gyara mata kwanciya, yaji knocking abakin kofa, runtse idanunsa yayi domin ahalin dayake ciki bayason takura ahankali ya motsa bakinsa "come in" yace still be bude idon ba, wata nurse ce ta shigo mai matsakaicin tsayi t "sir an kawo wani mara lafiya yana ta bleeding" ta fada cikin damuwa tashin hankali hadi da satan kallon abrar dake kwance ya kai kusan minti biyar bai bude ido ba bai kuma bata amsa ba, har ta cire rai da samun amsarsa taji yace " i will be there right away" cikin murna ta fita, duk da tasan cewa baya duty, amma ya amince, tabass kowa asibitin ya shaide sa yana da wanna halin kwaran matukar ya ga mara koda baya duty ya kan bashi taimakon gaggawa unlike sauran doctors din, kadai barshi baya shiga harkan kowa haka kuma baya fara'a, sannan tana mamakin wanna mara lafiya wacece da har ta samu matsayin da doctor da kansa ke jinyar ta da wanna tunanin ta fita...


bayan yaje ya duba mara lafiya ya dawo ya tarar still bata farka ba, gashi bakwai har da minti arba'in yana da bukatar yayi wanka, zai je ya dawo domin yana saka rai kafin ya dawo ta farka, zoben hannunsa ya kalla baya mantawa sanna dayace germany wani course ya siyowa kanwarsa ita, saidai yayi mata kadan yatsan ta na kusa da karami ya kuma yi mata yawa a karami yatsanta, shima a iya saman yatsan ya tsaya masa, yana matukar son zoben sannan zallan na diamond ne har daukan ido yake, cirewa yayi daga yatsan shi da kyar kana ya kamo hannunta ya zira mata a yatsanta nakusa da karami yatsan ta kuma yayi cib a kyakyawan hannunta, shi kanshi bai san dalilin sa nayin hakan ba kawai ya tsinci kansa da aikata hakan ne, gashinta mai uban yawa ya shafa hadi furta "get well soon" cikin sauri ya fita be bar asibitin ba sai da ya yi kiran nurse dazata kula da ita kafin ya dawo...


"hello kwaro kaji abunda na gaya maka ko koda wasa kada ka bari asamu matsala ku kawo min ita ko ta wani hali"

"an gama alhaji" kwaro ya fada
"yawwa yi sauri ina gida daka daukota ka min waya sai mu hadu" kit ya kashe wayar yana kallon ammi dake shararan baccinta har yanzu ko motsi batayi ba, gumi ya share yana fatan kada a samu matsala, lashe labbansa yayi tuno da moment din daran jiya...

"kin zama tawa domin bana jin zan barki ki kufce min, dole in cigaba da lasar zuman ki abrar daddy's girl" ya fada abayyane yana dariyan samun nasara...


kwaro tare da manu suka shiga asibitin basu wani sha wahala ba suka gano dakin datake, nurse mai kula da abrar na zaune kusa da gadon taji kawai an bude kofar tana shirin magana kawai taji manu ya fito da wata sharbebiyyar wuka daga kasan booth din kafarsa sai kyalli take" kina magana zan falle kanki" manu ya fada yana muzurai, hannu tasa ta rufe bakinta tana hawaye, cikin sauri kwaro ya dauke ta ya fita da ita yayinda manu ya cigaba da tsareta da wuka kasancewar safiya ce babu wasu mutane hakan yasa babu wanda yasan halin da'ake ciki, bayan kamar minti 7da fitar kwaro manu ya shaka mata wani kyalle ahacinta take jikinta ya saki ta fadi kasa ko juyowa be ba ya fita cikin sauri ya tarar da kwaro cikin motar suka bar asibitin cikin sauri motarsa su kwaro na fita na doctorn nan nashigowa, domin ko breakfast yakasa yi babu yanda mummynsa bata yi da shi ba yaki, karshe dai sai a basket ta bashi tace lallai yatafi dashi...

bayan ya daidaita parking motarsa ya fito hadi da daukan basket din abincin ya nufi cikin asibitin ko office dinsa bai je ba ya nufi dakin da abrar ke kwance... wani abu mai kama da tsoro na neman dirar masa adalilin mugun ganin dayayi, sadai sam baya son wanna tsoron ya samu muhalli azyciyarsa domin jin tsoro baya daga ciki dabi'ar sa, gadon da abrar ke kwance wayam bata nan, ga nurse hannatu a kwance a kasan tiles cikin fitar hayyaci...

cikin sauri ya shiga bata taimakon gaggawa, domin ita kadai ce zata basa amsar dayake son sani, bayan awa daya ta farka tana ta sakin atishawa, dago kan daza tayi taga idanun doctor nan sunyi jajur yana yana mata wani kallo, gabanta ya fadi sai ta fashe da kuka domin batasan yaza ta ce masa ba, runtse idanunsa yayi kana ya waresu ahankali " a enough!!!" yace cikin tsawan da bai san ya iya ba.

take jikin hannatu ya fara rawa " ina take? i said where is she?" ya fada yana nuna gadon ga fuskarnan ba alamun wasa" wa...su...ne suka......... nan ta fara bashi labarin komai cikin rawar murya.

" ya ilahi fattaqun" ya fada yana hargitsa kwataccen suman kanshi, be kara ce mata komai ba ya fita daga dakin, office dinsa ya nufa ya rufe kansa ya aciki yama rasa yanayin da zai fusalta kanshi aciki...

"good job kwaro zaku ji alert dana je gida" alhaji shettima ya fada yana kallon abrar dake kwance abayan motarsa.
"Allah ya biya oga godiya muke" kwaro da manu suka hada baki wurin fadin haka....

ta kofar baya alhaji shettima ya shiga da abrar ya mayar da ita dakinta ya kwantar hadi da komawa dakinsa wanka yayi ya fito, ya ga ammi zaune kan gado hannunta dafe da kanta, kamar gaske yace " hajiyata sannu kin tashi?" da kallo take binshi ba tare da ta amsa ba jiyayi gabansa yabada ras! "ko dai tasan abunda ya faru ne?.... wata zujiyar tace ai bazata taba sani ba" domin an bashi tabaccin matukar mutum ya sha maganin nan toh sai ya dau awannin masu yawa yana bacci ba tare da yasan inda kansa yake ba.

"alhaji kalli tara saura banyi sallah ba, gaskiya bazan sake shan wanna maganin ba" ajiyar zuciya yasaki ganin ba abunda yake tunani bane...
"Toh shikenan hajiyata an gama duk yanda kikeso haka za'a yi" bara nayi sallah'n na dubo jikin abrar ta nufi toilet cikin sauri yana ganin shigar ta yasake zuba wanna maganin cikin shayin daya sa aka hada domin baya jin ze iya barinta taga abrar awanna halin da take ciki....



YANZU LABARIN YA SOMA👌AM SURE YOU GUYS WILL ABSOUTELY LOVE THE HEART TOUCHING STORY JUST KEEP ON FOLLOWING MY PEN.

NOOR LOVES YOU ALL💞


PLS SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌
https://chat.whatsapp.com/FEfWeTiufpk96my8yNBeaM

✨MIJIN AMMINA NE SILA✨

written by noor Eemaan
wattpad @noorEemaan

page 13-14

bayan ammi ta iddar ta sallan ko hijab bata cire ba ta nufi hanyar kofa " haba hajiyata ko dan tea din dana ajiye miki baza ki shi ba" ya fada yana marairaicewa kamar wani saurayi dan shekara 25 murmushi ammi tayi ta karbi shayin ta shanye tas take taji wani matsananci kasala hadi da jiri sun dirar mata lokaci daya baya baya tayi ta zauna akan gadon, can kuma sai ta kwanta babu jimawa bacci yasake daukar ta murmushi alhaji shettima yayi ganin yasamu abunda yake so domin yana sane ya zuba tablet din da yawa acikin tea din...


shiryawa alhaji shettima yayi ya fita wurin harkokinsa batare yasake duba halin da abrar take ciki ba, bakinsa awashe kamar mai tallan toothpaste domin wani nishadi na musamman yake ji...

"TWO DAYS LATER"
abrar na kwance kamar mara rai, domin bata motsi sam, amma abun mamaki hawaye ne suke zubowa ta gefe da gefen idanunta izuwa kunnenta, bayan kamar 30minutes ta fara kokarin ware idanunta ahankali, saurin sake rufewa tayi domin wani dishi dishi take gani, sake bude su tayi tana bin dakinta da kallo, can kwakwalwarta ta hasko mata abunda har ta koma ga Allah bazata taba mantawa, wani ihu mai karfi tasaki hadi da durawa daga kan gadon wani radaddi ya ziyarci kwakwalwarta daya sake hargitsa tunaninta, kayan dake jere kan dressing mirror ta fara hargitsa su tana cilli dasu duk wani abu mai fashewa da hannunta ya taba sai ta fasa, su gaba daya ta yanke hannunta da kwalba turare kuka take har da majina, kuka take mai taba zuciyan mai sauraro, kuka take da sautinsa ke fitar da asalin abunda ke zuciyarta, dole atausaya mata komai rashin imanin mutum kuwa. Cikin

Please Login or Register in order to submit comment