Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kana a hank'ali ta juyo hadi da sak'alo hannuwanta a wuyansa, "am sorry pure heart, 'bana so ka tashi da yunwa shiyasa" Abrar ta karasa maganar tana sak'ar masa murmushin ta mai 'burgewa, kasa jurewa yayi har sai da ya 'bata hot kisses kana ya hank'alin sa ya k'wanta... Kunna gas di'n tayi ta ciga'ba da girk'inta yayind'a y'ake lafe a jik'inta suna shan soyaayyar su....


Mun kusan hutawa duka, domin littafi ya na kan karewa, kuyi haku'ri wallahi bana da lafiya ne shiyasa ban yi posting jiya ba, naga texts dinku da yawa, in sha Allah gobe zaku jini much love❤

Banyi editing ba idan kun ga mistakes/ typing error ku yi haku'ri.

Noor Eemaan ce🖊

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌



✨MIJIN AMMINA NE SILA✨
( A heart touching story)

Written by
Noor Eemaan

Wattpad username
@NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊


#Ending

Page71-72


(Not edited)


_____________________📖sun d'auk'i tsahon lok'aci suna girk'in wand'a 'bashi da wani yawa, bayan sun gama had'a breakfast, ya taya ta d'auk'ar warmers suk'a jera a dinning table, kana suk'a shiga wank'a a tare k'amar yand'a ya sabar mata, bayan sun fito ta shirya ta cik'in wasu k'ananun k'aya, bomshort na jeans hadi da farar riga top, y'ay'ind'a ya yi mata parking gashinta a tsak'iya da farin ribbon, barima mai farin stone ya sanya mata, kana ya fito mata da white low shoe, murmushi d'auk'e kan fusk 'ar ta, ta mike ta fara shirya shi cik'in tsananin so had'i da alfahari da mijin nata, haka suk'e k'ullum sai dai idan Aaban dana fitar sauri ne k'owa ke shirya kansa....


Sosai shi ma ya yi k'yau cik'in shigar k'ananun kaya, hannunta ya kamo suk'a sauko k'asa, kan dining table suk'a yiwa K'ansu mazaunin, hak'an bai masa ba ya d'ora ta kan cinyar sa, a haka suk'a yi breakfast d'in... Bayan sun gama suk'a d'awo falo, tana kwance a k'irjinsa, d'omin Aaban ya gama shagwa'bata da zama a k'irjinsa...


Ringing d'in wayar sa ce ta k'atse musu hirar soy'aayy'ar su, ganin number hospital di'n sa ya sashi dan k'wabe fusk'a k'amar k'aramin yaro, d'omin ya riga yace ba inda zashi, yau ranar k'asancewa da decent one d'inshi ce...


K'amar yand'a yayi tunani ne, yana d'aga wayar aka ce ana buk'atar sa da gaggawa d'omin an k'awo wani patient... Yana sauk'e wayar d'aga k'unnen ya k'alle ta, saura k'iris ya yi dariya ganin yand'a ta k'umbura fusk'a dama bak'inta, da alama taji wayar da suka yi da yan hospital din...


"Allah ni 'babu inda zaka je, yau k'awai baza su bar min kai ba" ta k'arasa tana fashewa da k'uk'an na zallan sakalci...

Kallon ta k'awai yake yana mamak'in yawan rigimar ta kwanan nan, gashi bata da wuyan k'uk'a yanzu. Cikin son rarrashin ta yace " haba wifffy, nasan ki da tausayi fa, baki son mijin ki ya samu lada uhmm?"


Jikinta ne yayi sanyi, cikin shagwa'ba tace "toh kaje, amma zaka kaini gidan bestie Hanan please?" K'asancewar Hanan tayi aure watanin uku kenan tare da saurayin ta Khabeer wanda shi ya matsa aka yi auren a dalilin sa na cewa ya matsu ya mallake ta domin baya son wani ya yi masa kwancen ta...


"Sure! zan kai, mu je mu sauya kaya" ya fad'a yana daukar ta cak cikin sauri sauri yak'e take matatak'alar benen... Babu jimawa suk'a fito cikin shiga mai kyau da tsari...

'Babu jimawa suka isa hada'dden gidan Hanan kasancewar basu da nisa sosai, "k'arfe biyar zan zo in d'auke kinjii" ya fad'a yana murza soft palm din ta.

"toh Allah ya bada sa'a"

"Ameen decent one, I love you"

"I love you too pure heart" tace tana sakar masa murmushin ta, har ta fita daga motar ya ce "baki ji ba" waiwayo wa tayi, da hannu yayi mata alamar tazo, dawowa cikin motar, fuskar ta ya kamo hadi da kamo lallausan labb'anta ya shiga kissing d'inta, martani ta shiga mayar masa itama cikin salon daya kara rikita shi....

Tuna cewa ak'wai patient dake cik'in mayuwancin hali yasa Aaban zare labb'ansa. "Take care ok, zan kira ki da zarar na samu any space, and extend my greeting to Hanan" yace yana sake bata light kiss a lips d'insa"

Jinjina masa kai ta fita hadi da daga masa hannu, sai da ya ga shigarta cikin gidan kana ya bawa motar sa wuta ya harba kan titi da gudu...

'Da sallama d'auke a bakinta ta shiga falon Hanan, sauri juya baya Abrar tayi ganin Hanan kwance jikin Khabeer, dariya Hanan ta saki domin sosai Abrar ta bata dariya. "Barka da zuwa bestien mu" yace yana zare Hanan daga jikin sa. Sai a lokacin ta juyo suk'a gaisa a mutunci da khabeer din, kana ya bar falon domin dama yana da shirin fita ne...

Sai da Hanan ta dawo daga rakoshi, ko zama bata yi ba tace "Allah ya shirye ki, wai ke kunya"

"Allah Hanan baki da kunya, kina gani na kika cigaba da kwanciya a jikinsa"

"Toh ya son ranki" ta fad'a tana yin fari da idanun ta.

"Tabe baki Abrar tayi tace "A'a babu"

Dariya Hanan ta sake yi mata domin idan ta tuno irin juyin da Abrar tayi sai ta kasa rike dariyar ta.

Murguda mata baki Abrar tayi tace "wallahi in kika isheni da dariyar nan sai na koma gidana, dama kika samu zan wunin miki"

Dif Hanan ta dauke dariyar muguntar ta hadi da cewa "yeeeeeh da gaske zaki zauna har yamma?" jinjina kai Abrar tayi murmushi dauke kan fuskar ta...

Rungume ta Hanan cikin farinciki kana tace "zauna in baki story" Abrar sarkin son labari ta ce "bestie am pregnant fa, yau wata biyu kenan"

Wani tsalle murna Abrar tayi ta rungume Hanan, sai ga suka gama murnan su Abrar tace "wayyo dadi! Kice mun kusa zama Mummy's, toh Allah ya raba ki lafiya bestie na"

Cikin jindadi Hanan tace "Ameen ya Allah, ke ma Allah ya baki".

Da "Ameen" Abrar ta amsa cikin farincik'i domin bata taba damuwa ba, haka shima Aaban, saboda sun sa a ransu cewa haihuwa ta Allah ce, kuma lok'aci ne, ba kuma sun wani jima bane balle su sa K'ansu a cik'in damuwa...

Haka suka cigaba da hirar su gwanin sha'awa, sai bayan sallar azahar Aaban ya samu sararin k'iran Abrar, tana kwance a dak'in Hanan d'omin wani bacci bacci mai d'ad'i ke fizgar ta, har mamaki tak'e d'omin ita ba ma'abociyar baccin rana bace, har Hanan na tsok'anar ta wai ta samu ne, dariya k'awai tayi mata d'omin ita kam bata ji wani alama na masu cik'i a gareta ba...

Har ta fara baccin ringing d'in wayar ta ya tashe ta, idanun ta a lumshe ta yi sallama cikin zazzak'ar muryar tace
"Assalama alaykum, pure heart"
Wa'alaikumu salam, wifffffyyyy"

Yanayin yand'a ya kira sunan ya sa ta kara lumshe idanunta, "kina lafiya, yana ji muryar ki so slow hak'a?"

"Bacci" tace a tak'aice.

Ya dan yi mamak'i jin wai zata yi bacci da rana, abun da bata yi, amma a fili sai yace "have you eating?" ( kin ci abinci?)
"Yeah pure heart"
"Good girl, bari na barki ki kwanta, amma kafin nan ki fad'a min wani abu mai dadi"

"Murmushi tayi tace " toh in yi maka wak'a?"

"Yeah sure ina so" ya amsa mata yana gyara zaman sa kan k'ujeran office d'insa.

Cikin zazzak'ar muryar ta mai d'auke da amo na bacci ta fara yi masa wak'a kamar haka...



_Ehh a bayanin farko Kaine hasken da bai rabarka. A misalin farko kishina bai bari watta ta kusheka, tunda ka zama bango rabarka sai ni kadai matar ka tausayi da kulawa nice na dace na kwanta kirjinka. Ruwan gubar yanmmata ko sun shaka zasu amayoka muyi gama kar muyi baya fushi ko fada babu tsakanin mu..._


Wani lum lumshe ido Aaban ke yi, yayinda wani sanyin dadi ke ratsa kunnenwansa, saboda gardin muryar ta. Cik'in shauk'in soyaayya yace " sing more please wifffy"

Turo baki tayi tace " pure heart baccin yaci karfina fa"

"Its ok, yi baccin ki, love you bye"

"Love you too" tace tana gyara kwanciyar ta.


*KARFE BIYAR NA YAMMA*

Zaune Abrar take ta yafa mayafin ta da alama tafiya zata yi, sai faman k'iran wayar Aaban t'ake bata shiga, cikin damuwa tace "hanan bari na tafi gida nayi girki kila aiki ne yayi masa yawa"

"Toh ki tafi da Motana tunda baki zo da taki ba"

"A'a banason yin driving, zan dauki keke napep drop"

"Toh shikenan muje in raka ki"...

Sai da Abrar ta hau keke kana Hanan ta koma gida cike da kewar bestien ta...


* * * * * * * * * *

Har karfe goma Aaban bai dawo gida ba, gaba daya hankalin Abrar ya tashi idanun nan sunyi luhu luhu saboda k'uk'an data sha, haka ta takure jik'inta wace daya ko fitilan falon ma bata kunna ko ina duhu ne sai sheshek'ar k'uk'an dake tashi shine kawai zai sa mutum fahimtar cewa ak'wai mutum cikin falon...


'Duk da ta k'ira wayar sau ba adadi, amma hak'an bai hanata cigab'a da kiran ba....bangaren Aaban kuwa gudu yak'e shararawa a titi burin sa kawai yaji shi a gida gaban decent one dinshi, har yayi gama sai kuma yayi rivas ya tsaya d'aid'ai wurin masu siyar da nama na zallan rago, babu abunda ke tashi a wurin sai k'amshi, babu bata lok'aci ya siya mata mai yawan gaske domin yasan cewa zata iya cinyewa tunda ma'abociyar son nama ce....


'Daidai yazo kofar gate din gidan ya danna horn, babu bata lok'aci mai gadi ya b'ude gate hadi da gaishe shi, amsawa yayi kana ya faka motar d'aid'ai parking lot kana ya dauki kayan aikinsa hadi da ledan ya nufi cikin gida...


Yana shiga falon yaga duhu sai k'uk'an Abrar dake tashi a hank'ali cik'in sauri ya lalubu muk'unin wuta ya k'unna kasancewar wayar sa ta mutu, cikin matsanancin damuwa ya k'arasa wajen ta hadi da dago ta izuwa jik'insa gaba daya, ihu hadi da shure shure ta fara tana cewa "ka sauk'eni, ni ka sauk'eni ka k'oma, idan na mutu sai ka dawo ka dauki gawa ta" ta k'arasa tana rushewa da kuka, domin ba karamin tsorata tayi ba ganin har goman dare bai dawo ba, abinda bai taba yi ba...

Ganin da gask'e tana neman fin k'arfina sa ya sa ji saurin kamo lallausan labb'anta ya fara sumbatar ta hurrily tamkar zai cinye bakin, tun tana shure shure har jik'in ta ya saki tana karban sakonin, sai da ya tabbatar da jikinta ya gama saki kana a hank'ali ya zare labb'ansa yana sauk'e numfashin, luf Abrar tayi a k'irjinsa suna sauk'e numfashin itama, sun kai mintuna biyar a haka kana ta kwace jikinta tana turo baki hadi da kwabe fuska ita ala dole fushi take, murmushi yasaki, yana tunanin ko me yasa yanzu tak'e saurin yin rigima, yasan bazata fahimce shi yanzu ba...

K'itchen ya nufa domin k'ishirwa yake ji sosai... Take hancin Abrar ya juyo mata k'amshin naman, a hankali ta mike ta dauk'o ledar naman zama ta yi ta bud'e naman tana lek'ensa, domin bata so ya ganta tana ji domin kad'a ya dauk'o ta sauk'o daga fushin, tana ci tana k'ukan rigima, fitowar sa daga kitchen yayi d'aid'ai da nama kwaya uku data cusa a bakinta, wata dairya ce ta taso masa, wanda ya kasa riketa, karon farko a rayuwar su da Abrar ta ga yana dariya, kura masa ido tayi domin ba karamin kyau dariyar tayi masa ba... Sai ta fashe da k'uk'an sak'alci ta nufi wajensa hadi da rungumesa, sosai shima ya k'amk'ame ta yana ciga'ba da dariyar sa.

Sai d'aya ga k'uk'an bana karewa bane ya shiga lallashin ta da k'alamai masu sa nutsuwa, domin sam bayason ta dinga kuka musamman saboda rashin lafiya na baya, Amma yanzu abu Kazan sai k'uk'a shagwa'ba da sakalci.

Ganin tayi shiru sai sauk'e ajiyar zuciya take ya sa shi riko hannunta suka zauna, kan cinyar sa ya dora ta ya cigaba da bata naman sai d'ata ci ya ishe ta kana ya kyaleta. Daukar ta yayi suka nufi upstairs wank'a suka yi a tare, ya daura towel fari yayind'a ya d'aura mata bathrobe ash color suka fito, bayan ya shafa musu mai saukin zafi, kana ya cire towel d'insa da bathrobe din jik'inta a haka suka kwanta ya rufe musu duvet, ajiyar zuciya suka saki kusan lokaci daya "bazaka ci abincin ba?" Ta tambayeshi cikin muryar rigima, "bayan baki damu da cik'ina ba, ina zuwa kika fara min rigima" ya fada tamkar wani yaron dan shekara5 .

Sai taji ba d'ad'i ita k'anta bata san meke sata yawan rigimar nan ba, a fili tace "toh ba kai bane ka tafi ka barni na d'auka wani abu ya sameka hank'alina ya tashi sosai pure heart, bazan juri ganinka cikin wani mayuwancin hali ba"

"Bubbuga bayanta ya shiga yi domin yaji muryar ta ya fara rawa alamun k'uk'an shagwa'ban zata yi ba. " am so sorry wifffy, wallahi ban huta ba tun bayan wayar da muka gama dake, a yau mutanen da aka kawo cikin mayuwancin hali da yawa suke, ga wayata ta dauke domin ban ma samu lok'acin saka charge ba, amma duk inda nake a ko wani hali nake kisani cewa kina nan daram anan" ya fada yana dora hannunta kan k'irjinsa...


Murmushi tasaki hadi da cewa "Allah ya baka ladan taimako, ka tashi mu je ka ci abincin, domin nasan tun abincin safe baka ci komai ba"

"Kibar abincin nan wifffy,l zuwa safiya, kafin mu fara wayar nan na sha fresh milk babban gora"

"Are you sure?" Ta tambayeshi Adams

Murmushi yayi yana jindadin kulawar sa gareta yace "sure wifffy"

A haka suka kasancewa kowa na sauraran bugun zuciyar dan'uwansa har abinci ya daukesu... Misalin biyun dare ya fark'a sak'amak'on jik'in Abrar dayayi zafi rau, yayinda take baccinta hankali k'wance kamar ba itace jik'inta ke zafi ba, ba tare da ya tashe ta ba ya dauk'o ruwa mai sanyi da towel ya shiga goga mata ajiki sai daya tabattar da jikin ya daina dumi kana ya kwanta rungume da ita, da tunanin go'be zai checking d'inta....


Washegari k'uwa da safe yace tayi fitsari domin ak'wai tunanin da yake yi, soyake ya tabb'atar, aik'uwa hasashen sa gaske ne domin a gwajen farko ya nuna tana dauk'e da ciki na tsahon sati uku...

Sosai farincik'in mara mitsaltuwa ya wad'atu a fuskarsa, sujjadah yayi yana godewa wa Allah, bayan ya dago ya daga ta cak ya shiga juyi da ita a sakin suna dariya... "Na kusan zama Daddy" yake maimaitawa yayind'a ya ciga'ba da juyi da ita, sai da ya gaji dan K'anshi kana ya dire ta hadi da rungumeta gam gam cikin murya da amon sa ke fitar da farincik'in yace
"alhamdulillah ya Allah, thanks wiffy I will soon be a Daddy"

Jin maganar tayi k'amar wasa tace "are you kidding me pure heart? Da gaske kake zan zama Mummy?"

"In sha Allah wiffy, domin you are three weeks pregnant" ya fada yana shafa shafaffen cikinta...

"Alhamdulillah" tace tana rungume shi farinciki mara mitsaltuwa na ratsa ta.



* * * * * * * * * *

'Bangaren su kwaro kuwa wani sun ki fadin wanda ya aikesu, domin suna ji a jikinsa alhaji Shettima zai sa ayi billing su, sai da suka ci bakar wuya kana suka ambaci wanda ya aikesu, take aka je gidan alhaji Shettima suka ga ya dawo foundation d'in taimakawa marasa k'arfin halin da marayu, nan suk'e jin labarin cewa alhaji Shettima ya rasu...

Bayan sun dawo suka sanar dasu kwaro komai, kana suka yanke musu hukunci d'aid'ai da laifinsu...haka suka k'asance cikin gidan yari suna girban abinda suka shuka nadama hadi da tsoron Allah na ratsa su, k'ullum cikin neman yafiya suke a wurin Allah.


*** *** *** ***

Sanye take da kayansu na lawyer yayinda cikinta ya dan tasa domin kai tsaye zaka iya hango tudunsa daga cikin kayan nata, Hanan ce a gefen ta itama da cik'in yayi girma domin yana watanin sa na shida ne yanzu, kan case din da suka yi yau suk'e tattauna akai kasancewar suna aiki a kotu daya ne, sosai ake ji dasu a kotu domin sun k'asance masu aiki da gaskiya... Bayan sun gama tattaunawan nasu suka rabu da juna cike da kewar juna kamar yadda suka saba domin amintar su babu abinda ya ragu sai ma karuwa dayayi...

Direct hada'dden gidan Ammi d'ata siya mata suka nufa, tana shiga falon taga Ummi da Zulaihat hadi da Ammi zaune da suna hira, zaro ido tayi ta kira sunan Ummi da Zulaihat cikin mamakin domin bata san zasu zo ba, saboda yau kwana biyu suka yi waya, tun kafin ta karaso Zulaihat ke cewa "yarnan kibi min jikalle a hankali" kunya ce ta kamata, gaishe su tayi cikin farincik'in ganin su.

Cik'in tsananin son yarta tace "ai na kira wayar ki domin in Sanar dake zuwan su amma baki daga ba"

Sai a lokacin ta dubi wayarta ta ga missed calls da yawa ciki har da na pure heart dinta, kallon mahaifiyarta tayi mafi soyuwa a ranta tace "Ammi ashe wayar na silent ban sani ba"

"Ni ko in ce, toh ya aiki" Ammi ta tambaya cikin kulawa.

Cikin shagwa'ba ta amsa wa Ammi da cewa "Lafiya Alhamdulillah, da addu'arki ina ganin nasara da haske kullum"

Murmushi Ammi ta saki, murmushi alfahari da yarta tace " Allah ya albarkace rayuwar ki, ya raba ki lafiya"

"Ameen ya rabb Ammina" tace tana rungume Ammin ta cik'in farincik'in...

"Daga min anty na, shagwa'babbiya kawai" Zulaihat ta fada cikin wasa, dariya suka yi duka, sai bayan la'asar ta bar gidan ta nufi gidan ta...



Tana shiga gidan ta faka motar kana ta shiga cikin gidan, motsi taji a kitchen hakan yasa ta nufi kitchen din tana tunanin waya, Aaban ta hango tana k'ok'arin dora tukunya, dariya ta sanya ganin yadda ya hada gumi, kallonta ya tsaya yi fuskar sa a kwabe yace
"ke fa nakewa girki kike min Dariya"
Cikin dariya tace "na daina toh"
"Amma yau ka dawo da wuri"
Rungume yayi ta baya yana dan juyi da ita yace
"eh, ya Ammi?"

Murmushi ta saki tace

"Ammi na lafiya, su Ummi da Mummy Zulaihat sun zo"

"Da gaske?"
"wallahi" ta amsa.

"zamu je gaisu in sha Allah"

"Toh" ta amsa tana murmushi...

"Ya unborn baby dina yake?" Ya fada yana shafa cikinta.

"Yana cik'in koshin lafiya"

"Toh mezaki ci yanzu?"

Cikin shagwa'ba tace "ni gurasa da nama zan ci" tace tana tande baki

Murmushi mai sauti yayi yana yaba kaunar ta da nama yace "toh yanzu ak'wai nama na siyo miki, gurasar ce babu"

" na iya gurasa pure heart"

"Toh shikenan, amma mu je na nuna miki wani abu kafin in taya ki kiyi gurasar"...

" toh" tace kana ta kashe gas di'n, da haka suka fita daga kitchen din...


Zaro idanu tayi ganin akwatuna d'aya d'aya har guda 30 masu kyau da tsari, zaunar da ita yayi kan gado ya cire takalmanta yana mata tausa, kallon shi take tama kasa magana "decent one, ga kayan lefen ki"

Cikin wani zallan Mamaki tace "kayan lefe kuma"

"Yes! Kayan lefen ki, domin kin cancanji fiye da haka, domin ke mai tsada ce, suna raina kullum, toh babu isheshen lokaci sai yanzu na samu time na hada miki da kaina, and I hope zaki so dukkanin kayan domin duk abinda kike so da kalar da kika fi so da zabar miki mafi ak'asarin su "...

Ya karasa yana sakar mata kiss a hannun ta, sanyayyar kwalla ne suka zubo mata, cikin sauri ta rungume shi tana cewa "nagode sosai pure heart, Allah ya maka da gidan aljanna, I Love you so much" ta karasa tana fashewa da kuka, domin sosai ta ji abin ya taba zuciyar ta, domin dukkanin sun sani cewa bata tare da budurcinta amma yayi mata lefen da ko wata budurwar bata samu ba, ita kuwa dame zata saka wa pure heart banda ta cigaba da yi masa biyayya hadi da bashi farincik'in mara mitsaltuwa...

Sauri hade bakinsu yayi yana kissing dinta a nutse, itama cikin nata salon ta shiga mayar masa da martani daga karshe suka Lula duniyar ma'aurata.... bayan sun yi wakan yana zaune kan cinyar sa, zata budi baki ta yi masa godiya yace "Shhhhhhh! Banason godiya, kin cancanci fiye da haka domin kina bani dukkanin farinciki, gashi kuma kina daf da Haifa min wani farincik'in" ya fada yana shafa cik'inta.

"I love you" tace tana kissing din shi a goshi, kana ta tashi daga kan cinyar sa ta fara bud'e akwatunan, kaya ne masu kyau, tsari, da tsad'a, da kyar ta gama kallon akwati daya na kayan saboda yawan su kana ta kalle shi a shagwa'be tace "na gaji pure heart"

Dariya yayi mata yace "raguwa, ki bari zaki dinga kalla a hankali, muje kiyi gurasar, hannu ta mika masa, cak! Ya daga ta suka fito yayind'a suke kissing juna cikin shauki har suka isa kitchen din.....


Alhamdulillah #Ending


Ina matukar godiya ga dukkanin masoyana, naji dadin kwarai da soyaayyar da kuka nuna books dina, ina rokon Allah yafe min dukkanin kuraren dana yi cikin book din, ya kuma bani ladan abun da na fada dai dai.

Please ku mun sharhi ta hanyar nuna min darasin da kuka dauka cikin labarin mijin Ammina ne sila.


Special thanks to:

Nimcy's library

One blood fans

The life challenge fans

Gidan mrs aliyu fans

Novels group

Iqbaal readers

Aliyu ibin umar fans

Ni da shi abu daya ne fans

Laylerh maleek group

ELegant online writer's

Ina matukar gode muku duka, da k'ok'arin da kuka yi min, Allah ya bar kauna.

Sai mun hadu a next book in sha Allah



Don't forget to share and comment✔
Editing is not allowed❌

Follow me on wattpad @NoorEemaan

07082281566
Tuesday 3/8/2021
7:30pm







An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java

Please Login or Register in order to submit comment