Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne da wata akwalar ce da an samu matsala, sadeeq yasa hannu xai bude kofar Ruhaimat tayi saurin rike shi ta marairaice fuska tace "pls kismat kar ka fita xata ji ma ciwo" murmushi yayi ya jawota a jikinsa "don't worry koh my Dil..babu abunda xatamin kawai kishi ne xan mata magana ok" "nikam tsoro nake ji" " kwantar da hankalin ki ok ..I Lov u" peck ya mata a goshi sannan ya saketa daga nan ya bude motar ya fita, ga jama'a nan sun maida hankulansu suna kallon ikon Allah a yayinda wasu ke kokarin kwace sandar suna bata hakuri.."haba sadee meyasa kike Abu tamkar karamar yarinya ne" "munafuki..azzalumi..macuci..mayaudari..da aurenka xaka xo kana Neman wata a waje?? Kuma ka rasa wacce xaka nema sai aminyata kuma matar aure??..Allah ya Isa, ka fitar da ita daga ckn motar nan Yau sai na hallakata" nan jama'a suka fara bin sadeeq da kallon mamaki yace "me kike fada ne sadee?..matata ce fah, pls calm down muje gida mu tattauna" 😳😳"waat...??? Matar ka ?? Dama itace amaryar taka??..ka cuceni ka yaudareni baxan yafe maka bah" nan ta fashe da kuka "sadee pls...let's go home" "bana son ganin ka munafuki kawai..mugu.. Allah ya Isa da auren cin Amana da kamin, ka rasa wacce xaka aura sai kawata?? Allah ya Isa" ran sadeeq ya baci sosai don ganin yanda ta tara masa jama'a. Hakuri ake bashi wasu suna Allah wadai da hali irin na sadiya ya xaayi ta dauko maganr gida taxo tana yadawa akan titi..Allah ya shirya tirr...da mata masu irin wannan halin.sadeeq ya shige motarsa ckn bacin rai ya sa mata wuta daga nan ya fice ya bar makarantar, gudu yake sosai a bakin wani katafaren hotel yayi parking ya fito daki ya kama ya biya kudin sannan ya dawo yaja motarsa xuwa ckn harabar wajen.Ruhaimat na rakube a gefe ya dagata cak ya wuce daki da ita sai kallonsa ake, a bisa gado ya direta sannan ya xauna kusa da ita "meyasa kike kuka..bayan ni ya dace nayi kukan saboda cin mutunci na akayi a bainar jama'a" ta cigaba da kukan nata nan ya jawota ya hau rarrashi dakyar ta share hawayen nata.wayarta ya hau ruri yaya Yusuf ne ta daga suka gaisa nan ya sanar da ita cewa Hajja dada ke son magana da ita, ckin xumudi ta Fara murmushi sadeeq kam se kallonta yake.hira sosai suka yi Hajja tace "ina magidan naki kullum sai boyeshi kike ko muryar sa ban taba ji bah"kafin ta bada amsa sadeeq ya kwace wayar yNa cewa " masoyiyata kina lafiya..Allah ya barmin uwargidata" dariya Hajja Dada tayi tare da cewa "toh maigidan na..dama kana kusa ne" "ina nan ...kinsan kishine da ita Shiyasa bata barina naji muryar nan taki don tasan yafi nata dadin sauraro" haka dai sadeeq ya Dade yana hira da Hajja Dada daga karshe sukayi sallama.

*Reefat ce*😘😘😘
[3:16PM, 15/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*62*
BY *Reefat yahya*


La'asar tayi don haka Ruhaimat ta saka hijabinta ta tashi tsaye tana kallon kyakkyawar fuskarsa a hnkli yake sauke numfashi bacci yake ckn kwanciyar hankali, nan ta juya a hnkli ta fice daga dakin tana fitowa ta tare napep tace a sauketa a adsu... Ta shigo dakinsu tare da sallama gaba daya suka juya suna kallonta "lfy kuke min irin wannan kallo haka" rabia ta tashi ta rungumeta tace "Allah sarki Bunky hop kina lfy babu abunda ya tabaki koh..hankalin mu a tashe yake sai jin rumors kawai mukeyi a kanki" murmushi tayi tare da cewa "lfyata kalau babu abunda ya sameni" Ameena ta karasa kusa da ita tace "muna xaune kawai aka zo mana da labari wai sadee tace xata hallakaki..ah ah kina cin amanarta ..waya mutu waya tashi ..ga maganganu dai kala2* ""hmm..kanta ake ji" muneera ta gyara xama tace "don Allah bonky dama mijin Ku daya da sadee Amma baki taba fada mana bah" tabe baki tayi tare da cewa "toh da me hakan xai amfaneku..nifa sadee bata gabana da kun bar maganar ma ya fiye mana amfani" "hmm..Allah shi kyauta Allah ya Baku xaman lfy" "ameen" ta amsa daga nan ta shiga sabgoginta dama Ruhaimat bata son gulma Shiyasa ta kashe maganar.
Kiraye2* sallan magariba ne ya farkar dashi a hnkli ya bude idonsa yana bin dakin da kallo firgigit ya tashi xaune ya duba wayam babu Ruhaimat nan ya tashi ya leka bayi bata ciki , wayarsa ya cire dama meenah ta bashi num ta nan ya buga ckn kankanin lokaci ta daga tare da sallama yace "haba maini..ya xakimin haka, duk kinbi kin dagamin hankali wllhi" a can bangaren ta tace "am sorry kismat gani nayi yamma tayi har magariba ta gabato Shiyasa na tashi na tafi , kuma bana son katse maka bacci daz y ban tasheka bah" "um..um ni dai nayi fushi dake " ya fada ckn shagwaba "eyya fah kismat... Sorry plss" "um..um" "haba mai sona" nan ya kyalkyale da dariya yana jin dadin sunan, a duk lokacin da ta ambaci *mai sona* wani farin ciki ne ke xiyartar xuciyarsa yana matukar son ta kirasa da sunan "ok..my Dil na hakuri but anjima xan zo na daukeki tare xamu kwana a wannan hotel din"😳😳 ta xare ido tace "kwana kuma..?? A'a nikam bana so ka koma gun sadee ka kwana pls, ba girman ka bane kwana a hotel kana magidanci" "nasan da xaman sadee ai nace tare da ke xan kwana koh, Amma shikenan tunda baki so bari naje masallaci ..bye" daga nan ya kashe wayar da alama ransa ya baci da kalaman nata "ya Allah..badai fushi yayi bah" Ameena dake xaune bisa sallaya ta kura mata ido dama su 2 ne kawai a ckn dakin tace "bonky naji abunda kika fada Amma kinsan hakan bai dace ba koh..mijin ki ne fah, me a ciki don ya kama muku hotel haramun ne??, tun bayan aurenku kin taba kasancewa tare da shi?? Wllhi kiwa kanki fada ki cire wannan kunyar taki ki farantawa mijinki idan bahaka bah kina ji kina gani sadee xata rabaki dashi bar ganin cewa yana sonki wllhi sai kinyi da gaske don sadee bata da kunya xata iya yin komai don ta faranta masa, kuma kinsan halinta sarai ki xauna kina wani nokewa kada kiyi using opportunity ki saye xuciyar mijinki ki tsaya jin kunya a kwace miki shi" Ruhaimat tayi shiru tana saurararon meenah daga bisani tace "Allah ni kunya nake ji bansan ya xanyi bah" kwafa Ameena tayi tace "kunya koh?? Ki cigaba Allah ya baki sa'a kiyi ta kwashe xunubai daga karshe a kwace mijin ki huta" daga nan Ameena ta tada kabbara tana salla , Ruhaimat ta tashi tayi alwala ckn mutuwar jiki tayi sallah tana idarwa ta fada wanka bayan ta fito ta saka wata doguwar Riga Mara nauyi sannan ta dauko man shafawa brush toothpaste da duk wani abunda xata bukata ta saka ckn wani handbag , wayarsa ta kira baya dagawa tasan fushi yake don haka ta kalli muneera tace "bonky munee..don Allah kiyi hakuri ki saukeni somwia pls" hararinta tayi tace "ina ne somwiA wajen bashi da suna ne..kawai kice min jarabarki ta tashi xaki fita Neman mijinki" duka ta kai mata ta kauce suna dariya daga nan Muneerah ta dauko makullin motarta suka fice bayan Ruhaimat ta xumbula hijabinta har kasa.
A kofar hotel din Muneerah tayi parking tana tsokanar Ruhaimat wai taxo kwanan gida a haka suka rabu ta wuce ckn hotel din. Yana kwance bisa gado ransa a jagule ya rasa me ke masa dadi yaji yana buga kofa, ya tashi ya bude nan suka hada ido cike da mamaki yake kallonta "maini"! Murmushi tayi tabi gefensa ta wuce ya rufe kofar ya harde hannu a kirji yana kallonta.ta ajiye jaka tare da cire hijabi nan gashin kanta ya xube a gadon baya gown din ya amshi jikinta sosai kamshin turarenta ya gauraye dakin gaba daya. Sadeeq yayi galala yana kallonta yace "wow..u r too hot my pretty" ya karasa bakin gadon ya xauna suna fuskantar juna tare da sakar wa juna murmushi mai kayatarwa "I Lov u maini..I Lov u so much" 😘 ya sumbaci hannunta tace "I Lov u more mai sona" ya jawota ya rungumeta yana shakar dadaddan kamshin turarenta mai birkita kwakwalwA.daga nan ya fara Neman bakinta babu bata lokaci ya fara aika mata da sakonnin kiss masu xafi, tun tana nokewa har ta fara maida masa da martani sun Dade suna ckn wannan halin dakyar ta kwace kanta tana maida numfashi. Murmushi yayi yace "u are so sweet Dil..I Lov u more n more" ckn jin kunya ta rufe fuskaπŸ™„πŸ™„πŸ˜ŸπŸ˜Ÿ..daga baya kenan..ya ja mata hanci yace "wannan kunyar taki sai na cireta ai" dariya tayi ta boye fuskarta bisa faffadar kirjinsa.nan yasa hannu ya rungumeta yana shafa gashin kanta yace "kin ci abinci?" Kai ta girgiza masa alamar a'a, ya jawo wata bakar Leda bisa dirowa gasashiyar kaza ce tare da soyeyyen doya da kwai sai kuma maltina guda 2 da coca cola.. Ya gyara xama nan ya fara bata a baki tNa taunawa ckn Jan hankali yana faman lallabata sai xuba masa shagwaba take yi, nan ta tashi tace lallai dole sai ta basa a baki babu gardama ya amince daga nan ta fara bashi suna ci suna xuba soyayyarsu. Bayan sun kammala shi da kansa ya gyara gado yace taxo ta kwanta tace ba ynxu bah, game yakeyi da iPad nasa ta kwantar da kanta bisa kirjinsa yana shan maltina tana kallon yanda yake buga game din.kiran sallan isha akayi nan suka tashi tare sukayi jam'i, daga nan sadeeq ya fada wanka bayan ya fito sun Dan taba hira kadan Ruhaimat ta fara Hamma tace barci xatayi nan ya mata matashi da kirjinsa ya jawo bargo ya rufa mata.a hankali yake bubbuga bayanta dayan hannunsa na bisa kanta yana shafa suman kanta tare da hura mata iska a fuska, ckn kankanin lokaci bacci yayi gaba da ita yana kallon kyakkyawar fuskar tata😍😍😍...gauraye go n marry..lolxπŸ˜œπŸ˜œπŸ€—

*yaune da gobe da Jibi kawai gata war haka na my day*πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―πŸ‘―
*Reefat ce*😘😘😘
[3:17PM, 15/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*63*
BY *Reefat yahya*

Da safe ta shirya bayan sun gama brkfast sadeeq ya sauketa a makaranta ta wuce gun lectures daga nan ya koma gidan sadee, a falo ya sameta kwance idanunta a kumbure suke da alama tasha kuka har ta gaji.yayi sallama bata amsa bah a hnkli ya karasa kusa da ita yasa hannu xai tabata tayi saurin fusge hannunta tana hararinsa , murmushi yayi tare da cewa "am sorry pls ki saurareni" kuka ne ya kubce mata tace "babu abunda xaka gayamin sadeeq dama ka shirya aurenta ne don kaci amanata ..shikenan ai burinka ya cika" "am sorry wllhi bahaka bane, baba ne ya hada auren namu" haka dai ya cigaba da lallabata daga karshe ta bada kai bori ya hau.ckn salon soyayyarsa yasa ta mance duk wani bakin ciki da take ciki, yinin ranar tare sukayi a manne da juna hankalin sadee ya kwanta ta kara tabbata cewa Ruhaimat bata gabansa don haka ta sake ranta ta cigaba da nuna masa kulawa. Ruhaimat ko ta yini tana jiran kiransa Amma bata samu bah ta cika tayi fam tace lallai namiji kenan dubi yanda ya nuna mata kulawa a daren jiya Amma sai gashi Yau ya manta da ita yana can tare da uwargidarsa, haka ta yini cike da jin haushinsa har xuwa dare sannan ya kirata taki dagawa har ya katse ya sake kira nan ma bata daga bah a takaice dai 10miss calls taki dagawa. _30 minutes leta_ Tana kwance bisa bonk nata wata yarinya ta shigo tace "ana Neman Ruhaimat a waje" "bata nan" kai tsaye Ruhaimat ta bada amsa, murmushi Ameena tayi tare da cewa "tana nan fitowa " yarinyar ta tafi Ameena ta juya tana kallon Ruhaimat tace "haba kawata har yaushe xaki biyewa son xuciya ki ringa fushi da mijin ki? Idan kina yawan fushi wllhi baxaki ci ribar xama da kishiya bah..tashi kije yana jiranki" jikinta yayi sanyi haka ta tashi ta xura hijabinta ta fice daga dakin. Yana tsaye ya harde hannu bisa kirji yana jingine a jikin motarsa yayi kyau sosai wutar lantarki ta haskaka wajen ga jama'a kowa na sabgarsa, a hnkli take tafiya har ta karasa kusa dashi tare da sallama ya amsa yana kallonta har ckn ido.motar ta bude ta shiga a gidan baya ta xauna ya biyota ya xauna tare da rufe kofar , kamshin turarensa ya mamaye motar ta lumshe ido tare da jingina jikinta bisa kujera .hannu yasa ya jawota ta fada jikinsa yace "fushin me kike yi pretty..am sorry" kukan shagwaba ta fara masa nan hankalinsa ya tashi ya fara rarrashinta a hakan ya samu ya shawo kanta ta daina kukan, harshensa ya xira ckn bakinta ya fara kissing nata nan ya birkita mata kwakwalwa sun sundama ckn kogin masoya.bayan wani tsawon lokaci suka dawo hayyacinsu daga nan suka fara hira irin tasu ta masoya a nan yake shaida mata cewa gobe xai koma yola, kudi masu dumbin yawa ya mika mata ta karba tare da yin godiya dakyar suka rabu tamkar xasu hadiye juna daga nan ya mata sallama ya tafi.washegarin sadeeq ya koma yola bayan ya lallaba sadee ya gargadeta da ta kame kanta kada ta shiga hurumin Ruhaimat, ckn sadee ya shiga wata 8 gashi exams nasu ya gabato cikin kato ne sosai dakyar take iya tafiya kowa na tausaya mata. Kowane weekend sadeeq yana xuwa duban matayen nasa kuma har Yau babu abunda ya shiga tsakaninsa da Ruhaimat, soyayya kam ba'a cewa komai sadee da Ruhaimat kuwa babu mai kula wani.
Haka rayuwa ta kasance har suka fara final year exams nasu karatu suka sa a gaba babu kama hannun yaro, a wannan lokacin ne aka sa ranar auren Ameena da Aliyu bayan ta kammala makaranta ne xaayi bikin nasu. Sun gama exam lafiya daga nan kowane department suka hada party sunyi hotuna kala2* daga karshe suka rabu suna mai kewan juna, ranar da xasu watse sadeeq ne yaxo daukarsu atafau Ruhaimat ta ki amincewa su tafi tare dole ya hakura ya kyaleta ya dauko sadee suka wuce yola Ruhaimat kuwa tare suka tafi da Ameena ckn motar muneerah.gidan anty xee ta kwana don xasu tafi Jada ganin gida, washe gari suka shirya suka tafi ckn xumudi Ruhaimat ta karasa ckn gidan tana kwalawa Hajja Dada kira "Hajja nah..kina ina" Hajja ta fito suka rungumi juna cike da farin cki .sati 2 ta share a gidan iyayenta daga nan ta fara shirye shiryen bikin Ameena, a yola aka daura aure daga nan suka kawota Jada a nan akayi fansa aka watse.Ruhaimat ta fara shirin komawa gyaran jiki aka sake mata ta kara kyau sosai gobe ne xata je yola daga can xata bi jirgi xuwa Abuja, tayi kwalliya da yamma tana xaune a falon Hajja Dada tana chat ..kamar a mafarki taji muryar sadeeq ckn sauri ta daga kanta carab! Idanunsa suka fada ckn nata, yusuf na gaba yana biye dashi a baya dakyar ta saita kanta ta amsa sallamar.ckn falon suka karasa nan ta tashi ta kira Hajja Dada tare suka fito Hajja na faman washe baki "Yau maigidan nawa ne a falona..lale maraba da xuwa" ya amsa yana murmushi Yusuf yace "ki kawo masa ruwa man Ruhaimat" ckn jin kunya ta tashi bangaren umma ta wuce ta debo lemuka da ruwa mai sanyi sannan ta koma bangaren Hajja.Yusuf ya tashi ya fice hira sosai sadeeq yake da Hajja tamkar sun Dade da sanin juna, Ruhaimat dai ta xauna tana kallonsu a takaice dai sadeeq ya kwana a gidan a yayinda Ruhaimat ta karasa shirinta don da safe xasu tafi.

*Reefat ce*😘😘😘
[3:18PM, 15/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*64*
BY *Reefat yahya*

Misalin 7am suka bar kofar gidan su Ruhaimat sadeeq ke tuki tana xaune a gefensa babu Wanda yayi magana har sunyi nisa ya juya yana kallonta "wato baki yi missing dina ba koh" kayataccen murmushi tayi tare da cewa "kalli hanya pls" nan ya sake siteri ya yana kallonta "pls mai sona ka daina wasa da mota don Allah concentrate pls" beyi magana bah hasali ma kwanciyarsa yayi a jikin kujera Ruhaimat kam tsoro ya kamata ta marairaice "don Allah ka daina irin wannan wasan pls.." "Oho ba sai mu mutu tare bah tunda baki sona" "haba yaushe yace bana son ka" "gashi kuwa bakiyi missing dina bah..wen last kika.." Bai karasa ba tayi ihu don ganin wani trailer ya doso hanya nan ta kulle ido, murmushi yake sannan ya Dora hannunsa bisa siterin ya cigaba da tuki yana dariya yace "matsoraciya kawai..sai shagwaba da rigima kika iya ga kuma kishin tsiya Amma tsoro kamar farar kura" a hnkli ta bude ido ganin yana tuki yasa ta murguda masa baki tace "ehh..din ina ruwan mutum dani" nan ko ya sake siterin tayi saurin kwantar da kanta bisa kafadarsa idanunta a kulle tace "kayi hakuri don Allah.. Wllhi na daina baxan kara bah" murmushi yayi sannan yasa hannu ya cigaba da tuki ya kara wuta sai gudu yake.har a wannan lokacin kanta na bisa kafadarsa haka suka cigaba da tafiya bata San lokacin da bacci yayi awon gaba da ita bah, dai2* welcome to yola ta bude ido tare da daga kanta tana mamakin baccin da tayi har na 2hrs haka "wai...Ashe nayi bacci fah" ta fada tare da yin mika "ba dole bah..yarinya kinyi kewar mijin ki ba sai kin bude baki kin fada bah" murguda baki take tana hararinsa tace " ni nace nayi kewarka ne" "no nid to say dat madam..gashi daga jin soft skin kawai sai bacci, c'mon just say it out ban son pretending" "anki a fada din" dariya yake mata daga nan suka dau hanyar airport sai kuma ya juya yana kallonta yace "my dil ko xamu je kiga gidana sannan Ku gaisa da sadee ne" fuskarta ta kawar tana kallon window tace "sai wani lokaci" murmushi yayi tare da cewa "dil kishi koh" guntun tsaki ta ja tana magana ciki2* tace "har ta isa nayi kishi da ita ne" "wat..me kike cewa " " ni bance komai bah" daga babu Wanda ya sake magana a cknsu har suka kai airport din.bayan sun gama duk abunda ya dace suyi suna xaune suna jiran lokacin da xaa kirasu, wani mutum ne ya karasa inda suke ya risina ckn girmamawa ya gaidasu sadeeq yace "malam idi ka karaso" "ehh ranka ya Dade kayi hakuri bansamu xuwa akan lokaci bah" "ahh babu komai wllhi nagode da ka zo ynxun ma" daga nan ya cire makullin mota tare da kudade ya mika masa yace "gashi nan idan na sauka xan kira" "toh..yallabai Allah ya tsare" "ameen nagode" daga nan mutumin ya juya ya tafi.Ruhaimat ta juya tana kallonsa cike da mamaki gira ya daga mata "yan mata yadai" "dama tare xamu tafi?" "Oh..so kike na bar ki ke kadai mutane suyi ta kallon wannan kyakkyawar fuskar taki" ckn gatse tace "da ka fada min da wuri ai ina da nikabi sai na sanya koh" wani kallo ya mata daga nan ya jawo hannunta suka wuce don fasinjoji sun fara shiga, a ckn jirgin ma tana kwance a kafadarsa sai xuba shagwaba take yana faman ririta ta.sun sauka lfy driver ne yaje daukarsu daga nan suka wuce gida a makale da juna.
Bayan kwana 2 da xuwansu Ruhaimat tana xaune a falon mami tana kallon cartoon din *the 99* sadeeq ya shigo ya xauna kusa da ita yana kallon TV yace "me wannan?..dallah ki cire wannan abun " baki ta tura tace "ba kallo xakayi ba ni ka kyaleni na kalli abunda raina ke so" tsaki yaja yace "ynxu me amfanin kallon wannan abun don Allah" "ehh ..din shi nake son kallo" "pls ki canza mana xuwa aljaxeera sport pls" "um..umm ni wannan nake so" "bani remote din toh" "akan wane dalili" nan suka fara guje2* a ckn falon sadeeq yana son kwace remote ita ko taki ta bayar , baba ya shigo da sallama murmushi yayi yace "toh kajin mami an fara kenan" Ruhaimat ta turo baki tace "baba kace masa ya kyaleni nayi kallo nah" "cartoon take kallo fah baba " murmushi yayi yace "ni baxan iya raba fadan naku bah Ku bari idan justice zainab ta fito sai ta raba gardama" "wai hayaniyar me nake ji haka "mami ce take wannan maganar a yayinda ta karasa ckn falon, Ruhaimat na ganinta ta koma kusa da ita cike da shagwaba tace "yawwa mami na gara da Allah yasa kika fito ynxu..kin ganshi nan ya hanani kallon cartoon" "waya isa ya hanaki dota.. Falon mami ne fah" hannunta mami ta ja suka koma bisa kujera tana kallon sadeeq ta galla masa harara tace "idan kana son kallon news ka tafi dakinka mana..kazo kana takurawa er mutane" ya shagwabe fuska yace "Allah mami kin daina sona" tabe baki tayi sannan ta maida hankali gun TV , Ruhaimat ko tana kwance ta Dora kanta bisa cinyar mami tana kallo.baba dai sai dariya yake Sam..baya gajiya da kallon dramar tasu , sadeeq yace "uhmm..dama ina da magana" gaba daya sun juya suna kallonsa ya tashi ya koma kusa da baba yace "baba nagode maka Allah ya saka maka da gidan aljanna..Allah ya kara maka lafiya da tsahon rai..Allah ya tsareka da sharrin mutum da aljan" "amin..Amma irin wannan adua haka son" murmushi yayi yace "ina alfaharin kasancewa 'da a gareku ..mami baba nagode muku da duk irin so da kulawar da kuke nuna min..nagode Allah nagode maka baba da ka auramin macen da na Dade ina mafarkin samu, nagode da ka auramin Ruhaimat maini" cike da mamaki suke kallonsa mami tace "ban fahimceka bah" murmushi yake nan yace mata "mami kin tuna maini da nake yawan Baku labarinta..Ruhaimat ce " baba yace "wancan matar da aura kuma wacece? Bayan kai kace mana itace yarinyar da kake nema" nan sadeeq ya fede musu daga biri har wutsiya sun jinjina lamarin sosai mami tace"lallai hakika Allah shine mai yin yanda yaso kuma matar mutum kabarinsa" baba ya amsa da cewa "wannan haka yake..nidai fatana Ku xauna lfy Allah ya muku albarka" "amin baba" sadeeq ya Sosa kai yace "mami yaushe xaki bani ita mu koma yola tare" dariya sukayi mami tace "dama bana son ka wulakanta ta Shiyasa na hana amma ynxu tunda na gane itace muradin ranka, na amince Ku tafi tare Amma baxata xauna da kishiya gida daya bah" godiya ya dinga mata fuskarsa dauke da murmushi Ruhaimat ko kunya ce ta kamata ta tashi da gudu tabar falon suna mata dariya babu kunya sadeeq ya Mara mata baya, mami ta tabe baki tace "oh..wannan yaron bashi da kunya" baba yace " haba ai yayi kokari man..tun yaushe yake fama dake kika ki amincewa" dariya mami tayi tace "Allah ya basu xaman lfy" "amin" ya amsa mata.

*Reefat ce*😘😘😘
[7:02AM, 17/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*65*
BY *Reefat yahya*

πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚ _hapy buffday to me in advance.. Fans gobe akwai cin rice😜😜 ..shinkafa da dadi rengemπŸ‘― rengemgemπŸ‘―πŸ‘―_*Lov u all*

Kwance take bisa gado ta rufe fuska da tafin hannu sadeeq ya bude kofar a hnkli ya shigo kallonta yake yi nan ta kulle ido tana mai wani murmushi mai kayatarwa "kismat wai kunyata kike ji" batayi magana bah ya karasa xuwa gadon ya xauna kusa da ita tare da jawota jikinsa "I Lov u Ruhaimat.. I rily Lov u..son da nake miki ya wuce misali , pls ki bani hadin kai mu gudanar da rayuwarmu ckn so da kaunar juna..bana son wannan kunyan pls" a hnkli ta daga ido suna kallon juna nan ta fara masa wani irin kallo mai rikitarwa gaba daya ya rude ya rasa me xaiyi kawai ya rungumeta a jiki , kiran sallan magrib akayi don haka ya raba jikinsa da nata daga nan ya fada bayi yayi alwala ya fito ya wuce masallaci.da dare ta gagara fita cin abinci kunya take ji har daki mami ta kai mata abincin cike da kunya ta karba tare da yin godiya, a bakin kofa mami taci karo da sadeeq murmushi ya sakar mata

Please Login or Register in order to submit comment