Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayan sadee a wannan ranar ne Ruhaimat taji labarin sakin tayi fada sosai haka ta sashi a gaba tana masa fada tamkar ita ta haifesa yayi jugum yana kallonta sai da ta gama fadan nata sannan ya dauki makulli ya fice ya bar mata gidan, kwana 3 sukayi suna fushi da juna gaisuwace kadai ke hadasu dukkan su suna ckn damuwa suna kewar juna ba kadan bah haka suke daurewa.xaune take a falo ta kwantar da Mimi bisa cinyarta tana wasa da suman kanta da ya fara fitowa sadeeq yana xaune a can gefe yana kallon news Amma jefi2* yana satar kallonta.wayarsa ce tayi ruri ya daga "hello mamina" shiru yayi yasha jinin jikinsa don fada take masa tamkar xata bi ta ckn wayar ta samesa..sun share 30mins tana fada sadeeq dai sai hakuri yake bata don fada take masa akan sakin sadee da yayi jiya ta samu labari gun masu aikin gidan daga karshe tayi hanging call din, shiru yayi ya juya carab! Suka hada ido da Ruhaimat ya bata tausayi don shima Dan uwan dayar ne akwai shagwaba kuma baya son fada..ya marairaice tamkar xeyi kuka "my Dil kina ganin mami tayi fushi dani koh" murmushi tayi ta kwantar da Mimi daga nan ta koma kusa dashi ta xauna "com hre" ta bude hannayenta nan ya fada jikinta ta rungumesa ya kankameta sosai tana shafa gashin kansa tace "kismat baka jin magana n wat u did is wrong dole mami ta nuna maka fushinta..sorry koh is ok" ajiyar xuciya yayi tare da cewa "bayan kema kina fushi dani kin daina kulani" "ohh..c'mon is ok" peck ta masa a goshi sun Dade a ckn wannan yanayin daga karshe suka fada wata duniya daban.
**** _ina labarin ango imran ne??_ zaman nasu babu canji imran baya shiga sabgar yasmeen ita ko tabi ta damu baya kulata ko kadan haushinta yake ji don babu abinda ta iya komai masu aiki ke mata abu yaki ci yaki cinyewa dole yasmeen ta tattara ta koma gidan momin imran ta kai kararsa tace lallai baxata koma gidansa bah sai ranar da ya canza hali, imran kam bai damu bah haka ya cigaba da harkokinsa Ibrahim ma suna xaune lfy da meenah ynxu haka tana fama da tsohon ciki haka nan Ameena Mrs Aliyu jada.haka Rayuwa ta kasance akwana a tashi Ruhaimat ta gama bautar kasar da take ranar da xasu gama mami da baba sunzo tayata murna haka nan mutanen gidansu babu Wanda bai zo bah..umma Abba ya Yusuf anty Xee anty maryam da sauransu babu Wanda Ruhaimat tayi murnar gani kamar Hajja Dada , ranar ta rasa inda xata sa kanta don murna gaba daya sun nuna farin cknsu mami da baba sun jajanta mata dangane da labarin abunda sadee ta mata haka nan suka bata hakuri da karfin guiwa.bayan an watse daga taron gida suka wuce gaba dayansu meenah da Ameena duk sunzo, sun yini tare a gidan Ruhaimat abinci kala2* suka ci har xuwa dare sauran suka koma gidajensu aka bar umma Abba Hajja Dada da kuma Ameena su a nan zasu kwana.dakyar su umma suka amince don tsabar kunya nan Ruhaimat ta gyara musu dakuna daga nan sukayi sallama sun wuce don yin bacci, dakinta ta gyara ma Ameena daga nan ta koma dakin sadeeq fitowarsa daga wanka kenan nan itama ta wuce ta fada wankan bayan ta fito ta shirya suka kwanta don Mimi tana gun mami.
Da safe ta shirya musu breakfast tare suka karya da sadeeq da Ameena, da wuri su Abba suka shirya don komawa ya Yusuf ne yaxo daukarsu don ba nan ya kwana bah a can gidan hajiya maryam ya kwana.duk yanda Ruhaimat taso Hajja Dada ta xauna da ita fafur sunki amincewa dole ta hakura sukayi sallama suka tafi tare da Ameena. Da yamma mami ta shirya tare da Ruhaimat driver ya kaisu gidan su sadee mami na bin gidan da ido lallai suna ckn talauci, ckn mutunci inna ta karbesu ynxu tayi hankali ta koyi darasin rayuwa tayi sanyi kamar ba ita bah...sadee na ganinsu ta fashe da kuka Ruhaimat ma kukan take mami ce ke basu hakuri sadee tana kallon Mimi ta kara fashewa da kuka, sun Dade a gidan daga bisani mami ta ajiye musu kudade masu yawa tana bada hakuri akan sakin da sadeeq ya mata sannan suka fice daga gidan. Maimakon su koma gida gani tayi sun dau wata hanya daban gidan Alhaji sultan sukayi parking Ruhaimat ta fito tabi bayan mami.

*Reefat ce*😘😘😘😘
[11:39PM, 19/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*71*
BY *Reefat yahya*

~an imaginary Lov story~


❀❀❀ _Reefat tana sonku_😘😘😘

Sun shigo falon tare da sallama, imran ya fito zai wuce masallaci kenan ya daga kansa suka hada ido da Ruhaimat yayi saurin dauke kai yace "mami barka da xuwa Ku karasa suna ciki" yayi wucewarsa Ruhaimat de tana mamakin sauyin da yayi bahaka ta sanshi bah..Momi tayi farin ckn ganinsu a nan sukayi magrib sannan suka koma falo suna hira yasmeen ta shigo tare da sallama tana cewa "wash..Momi na gaji wllhi nayi rawa Yau ba kadan bah" tsaki Momi ta ja tare da cewa " Allah ya shirya.. Ki jira mijin naki don ya shigo yana tambayar ki, dama karya kika min da kika ce shiya baki izinin xuwa gidan bikin" dariya tayi sai ynxu ta kula da su mami tace "lah..Momi baki mukayi" "Mara kunya..wannan mahaifiyar sadeeq ce tare da matarsa" murmushi tayi "ina yinin Ku" mami ta amsa ckn sakin fuska , Ruhaimat ta juya kenan suka hada ido yasmeen ta bude baki cke da mamaki tace "ahh..wannan ce matar sadeeq?, amma ai ba ita bace wacce na Sani" "amaryar sa kenan sunanta Ruhaimat" tabbas yasmeen tasha ganin hotunan Ruhaimat ckn wayar imran kuma ta San cewa imran yana matukar kaunar Ruhaimat.. Amma mamakinta shine yanda ta canza ta kara kyau ga kuma dressing nata mai daukar hnkli ..sabanin da ta Santa da hijabi tana mata kallon bagidajiya, da wannan tunanin ta wuce dakin Momi "hajiya mami kina ganinta ai..haka nake fama kullum gani nan sai raba fada, wllhi nagaji abun nasu baya karewa" mami tace "meya kawota nan gidan bayan ga gidan mijinta" "wllhi bata da hankali ko kadan iyayenta sun sangartata..ni tausayin imran nake ji hakuri kawai yake ya xuba mata ido" "gskiya kiyi kokari ki wayar mata da kai don na lura tNa ckn duhu batasan ya ake rayuwar aure bah..kina cutar da danki a banxa ga mata nan birjik meyasa kuka xaba masa wannan fisararriyar" "uhmm kedai bari kawai..xanyi bakin kokarina" "Allah yasa mu dace" wayar Ruhaimat ya sake vibrating a karo na 5 murmushi mami tayi tace " chewing gum naki koh..nasan yana can yana jira tashi mu tafi" Momi tayi jugum tana kallon Ruhaimat.. Allah sarki imran da Ibrahim sunyi rashin mace ta gari .."toh Momi imran mun tafi" "nagode kawata Allah ya bar xumunci..dota nagode koh" daki ta wuce ta fito dauke da wata bakar Leda ta mikawa Ruhaimat dakyar ta karba tare da yin godiya daga nan suka wuce gida.
Sati 1 su mami sukayi daga nan suka koma Abuja tare da Mimi Ruhaimat tayi kewar yarinyar sosai don ita take kipin nata busy...wata sabuwar rayuwar soyayya suka shimfida tamkar xasu hadiye juna tare suke yin komai idan yana office ma suna makale da juna a waya haka Rayuwa ta cigaba suna rokon Allah akan samun haihuwa don har ynxu shiru kake ji kamar an shuka dusa.xaune yake bisa carpet grass a yayinda Ruhaimat tayi matashi da cinyarsa a garden din gidan suke suna shan iska tana karanta masa littafin *kissoshin annabawa* yana jin dadin tarihin annabi Yusuf da take karanta masa sai faman lumshe ido yake, Momi ce tare da yasmeen suka shigo masu gadi suka shaida musu inda masu gidan suke kai tsaye wajen garden suka nufa yasmeen na raba ido tana mamakin girma da kyawun gidan saboda bata taba xuwa bah gidan da sadee ta xauna ne taje sau 1.sadeeq ne ya hangosu yace "maini munyi baki tashi ki xauna" ckn sauri ta tashi ta sanya hijabinta don kananan kayane a jikinta "lah..Momi Yau kece a gidan namu..barka da xuwa" ckn tsananin kunya Ruhaimat ta musu maraba , sadeeq yace "mu je ciki koh" daga nan suka koma ckn gida a falo suka xauna Ruhaimat ta jera musu kayan motsa baki bayan sun gaisa sadeeq ya tashi ya fita Ruhaimat tabi bayansa a bakin motarsa ya tsaya nan suka rungumi juna ya manna mata peck a kumatu yace"ki kula kanki idan sun tafi ki kirani ok.." "Ok..u too takkia" "Lov u" "Lov u more..banda kallon mata" murmushi yayi tare da cewa "ni me xan kalla a jikin wata mace..I have u I have everything" murmushin jin dadi take daga nan ta daga masa hannu yaja motarsa ya tafi.duk abunda sukayi akan idon yasmeen mamaki ne karara a fuskarta..dama haka Ruhaimat ta iya soyayya? Yaushe ta waye haka? Xama tayi bisa kujera tana bin falon da ido har taji ta raina kanta..ikon Allah kenan wai Ruhaimat ce ckn wannan katafaren gida haka?, koda Ruhaimat ta shigo yasmeen bata daina kallonta bah..minti 50 sukayi a gidan sannan suka mata sallama.. Cake doughnut da kunun Aya ta xuba musu ckn bakar Leda sai kayan makeup da turarukan humra masu kamshi ta rakasu har bakin mota ta ajiye ledojin a gidan baya godiya sukayi yasmeen ta ja motar sika koma gida. Momi ta kula da halin da take ciki tun bayan dawowarsu daga gidan Ruhaimat "yasmeen meke damunki na ga kin xama wani iri" "Momi magana zamuyi" "ok go ahead"......


*Reefat ce*😘😘😘😘
[9:26PM, 20/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*73*
BY *Reefat yahya*

~an imaginary Lov story~

Baba ya kira ya sanar dasu akan cewa visa dinsu ya fito daga nan Ruhaimat ta xaga danginta na ckn yola da jimeta sannan suka wuce jada a nan tayi kwana 3 tayo sallama da iyaye da en uwanta suka dawo yola washe gari jirginsu ya daga xuwa Abuja, mami tayi murna kwarai da gaske meenah tana can ta koma sai bayan ta haihu xata dawo gidan minjinta.mimi ta girma tayi wayo ga jiki bulbul gwanin sha'awa tana ganin Ruhaimat ta fara dariya Ruhaimat ta dauketa tana mata wasa, bayan kwana 2 da xuwansu suka cigaba da shirin tafiya don saura kwana 3 tafiyar tasu.Ruhaimat dauke da Mimi tana mata wasa sai dariya take kyalkyalewa a falon mami suke mamin na xaune a gefe tana kallonsu a can kasar xuciyarta kuwa tausayin Ruhaimat ne ya kamata ..tana mata adua Allah ya bata haihuwa Allah ya axurtata da ya'ya masu albarka, sadeeq ya shigo da sallama ckn shigar kananan kaya yayi kyau sosai Ruhaimat na satar kallonsa.kusa da ita ya xauna yasa hannu xai dauki Mimi yarinyar taki amincewa ta kara makalewa Ruhaimat, dariya mami da Ruhaimat sukayi sadeeq ya marairaice yace "mami kina ganin yarinyar nan..tun shekaran jiya fah taki amincewa na daga ta" "toh ba sai ka hakura bah malam" ya bata fuska kamar xeyi kuka Ruhaimat ta fakaici idon mami ta masa gwalo nan ya kara harzuka "mami kina gani tana min gwalo" "wa kenan?" Haushi yasa ya bar musu falon suna masa dariya. Ruhaimat tace " Allah mami kin shagwaba ya sadeeq dayawa" murmushi mami tayi tace "wato kin koma team din su meenah koh" dariya tayi tace "aa mami's team nake" meenah ta shigo rike da pancakes a plate murmushi Ruhaimat tayi tare da cewa "acici's" tsaki meenah taja tace "sanin kanki wllhi larura ce don da bahaka nake bah" dariya mami take musu "haba mami dariya kke xaki min " " meenah me xan miki" ta bata fuska tace "dama ai anty Ruhaimat bata laifi" mami ta tashi tsaye tace "kinga tafiyata don nasan wasu abubuwan kuna yine don ganin idona" daga nan ta fice tana dariya, Ruhaimat ta matso kusa da ita tace "haba mutuniyar kinsan nida ke mutu ka raba..wasa nake miki my meenah" murmushi meenah tayi tare da cewa "lokacine yarinya.. Ai naki na nan tafe" hira suke sosai meenah na jajanta batun sadee , sadeeq ya shigo yace " lallai maini..kina ganin mijinki yayi fushi ya tafi Amma kin kasa xuwa ki bashi hakuri kin xauna kina biyewa wannan mai surutun tsiya koh" "hmm..su miji manya" meenah ta fada tana dariya nan Ruhaimat ta sauke Mimi bisa cinyar meenah tace "xauna a nan my bby kinsan baban naki Dan rigima ne" murmushi yayi ya jawota suka jera suna shirin barin falon meenah tace "oh..antyna babu ko kunya" "babu harkar kunya yarinya..ke waya San me kike yi a gidan naki" dariya sukayi gaba dayansu nan suka wuce bangaren su. Da yamma suka shirya sadeeq ya daukesu a mota suka fita yawo tare da Mimi da kuma meenah basu dawo gida bah sai xuwa dare, haka suka kasance ckn kwanciyar hnkli har xuwa ranar da xasu tafi gaba daya familyn suka dugunxuma xuwa airport dakyar aka raba Mimi da Ruhaimat ta makalkale a jikinta da aka rabasu kuwa ta fara kuka nan hawaye suka cika idanun Ruhaimat a haka suka shiga jirgi tana xubda hawaye, sadeeq ne ya daura mata belt ya kwantar da kanta a kafadarsa yana faman rarrashinta dakyar ya samu ta daina kukan daga nan jirginsu ya daga✈✈✈✈don xuwa Saudi arabia d most wonderful country.
******* sun sauka lfy hotel ya kama musu kafin ya nema musu inda xasu xauna permanent, bayan sunyi sallah sun huta ne ya kira iyayensu ya sanar dasu sun iso lfy daga nan suka fada wanka.tare suka shirya nan suka hau gado kanta na bisa kirjinsa haka sukayi bacci mai dadi.
Haka Rayuwa ta kasance Ruhaimat ta fara xuwan makaranta fannin addini take karantawa haka nan sadeeq ya fara xuwa PhD classes nasa a garin jeddah, rayuwar so da kula tare da mutunta juna sukayi duk Wanda ya kallesu dole yaji sun burgeshi kowannensu ya maida hankali sosai gun karatun da suke..a kwana a tashi ba wuya gun Allah Yau sun share shekara 2 a kasar saudiya nan suka fara shirin xuwa ganin gida.Ruhaimat tayi kyau tamkar a saceta a gudu har Yau babu labarin ciki kuma daga shi sadeeq har iyayensa babu Wanda yasa damuwa a ransa basu fidda tsammani bah a ganinsu komai lokaci ne Mimi ta girma sai shegen surutu,yaran meenah 2 duk mata haka nan yasmeen ta haifi danta namiji Ameena Aliyu na da yara 2mace da namiji.sati 2 Ruhaimat tayi a jada tayi mamakin ganin sabon ginin da aka musu Hajja Dada tsohuwa mai ran karfe ita ta fada mata cewa baba ne ya bada kwangilar gidan tsakaninta da surukan nata sai godiya taje xiyara a can yola yasmeen ta karbeta da hannu biyu, haka nan taje gidansu sadee Allah sarki Rayuwa tana kwance sai abunda aka mata ta xama abar tausayi..duniya kenan ( mohulai Allah semti😟😟).

*3 years leta* xaune take bisa gadonta mai alfarma a can madinatul munawwara katon ciki ne da ita sai marairaice cewa take sadeeq yana xaune yana faman ririta ta "haba maini ina xaa samo saki a nan garin" kamar xatayi kuka tace "ni nasan bara'a rasa bah kawai ni faten saki xanci😫😫 " ta karashe maganar tana kuka gaba daya ya rikice haka yake fama da ita tunda ta samo ckn bata son yayi nisa da ita ga kuma kwadayin tsiya..ynxu ckn Nada wata 6 .ya gama PhD dinsa ita kuma tana final year nata tana hada masters don tayi degree ta gama ynxu tana kan masters, tayi xurfi ckn karatu sosai addini ya shigeta ba kadan bah don tana da kwazo sosai ynxu haka ana inviting nata conference ko seminar a garuruwa daban2* ckn fadin kasar.haka sadeeq yake fama da shagwaba sai lallabata yake kamar kwai har Allah yasa ta sauka lfy ta haifi danta kamar Dan larabawa, baba mami umma Abba Hajja Dada meenah Ibrahim imran yasmeen da kuma momin imran su suka zo suna yaro yaci sunan Abba wato Abubakar😍😍.. Abubakar Dan Abubakar jikan AbubakarπŸ‘πŸΌπŸ‘πŸΌ bayan suna sukayi aikin hajji gaba dayansu sannan suka dawo 9ja..

*Reefat ce*😘😘😘
[9:27PM, 20/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*72*
By *Reefat yahya*

~an imaginary Lov story~

A hnkli yasmeen ta fara magana da cewa "Momi ina son komawa gidan ya imran Amma baya sona bansan ya zanyi bah..don Allah ki taimakeni wllhi ina matukar son ya imran , baya sona har ynxu yana bakin ckn rabuwa da Ruhaimat Shiyasa bana gabansa" "kiyi hakuri yasmeen.. Shi namiji tamkar jariri yake ke xaki koya masa komai tun da farko , amma rashin ilimin xamantakewar aure shiya jawo miki wannan matsalar...is not too late zaki iya gyarawa" ta gyara xama tace "Momi ya xanyi? Wllhi a shirye nake zan iya aikata komai don jawo hankalinsa" murmushi Momi tayi tace "Abu daya zaki yi" "menene wannan abun " "gidan Ruhaimat xaki koma ita xata koya miki duk abunda ya dace na tabbata xata wayar miki da kai" "Allah Momi kunyarta nake ji don naci xarafinta a da can baya " "kada ki samu damuwa..Ruhaimat yarinya ce mai hankali na tabbata xata taimaka miki" "shikenan Momi hakan xaayi " "kwantar da hankalinki gobe xan kirata a waya xan sanar da ita komai" "nagode Momi..wllhi baki ji yanda suka birgeni bah Yau da muka je gidan, gskiya Ruhaimat tayi dace a duniya " haka dai yasmeen ta cigaba da xancen Ruhaimat. Kamar yanda suka tsara hakan ta kasance da safe Momi ta kira Ruhaimat sun Dade suna magana daga karshe sukayi sallama nan ta kira driver ya sauke yasmeen gidan Ruhaimat don xata fita da motar saboda yasmeen bata taho da tata motar bah.
Sadeeq ya tafi office don haka Ruhaimat ta gyara gidan ko ina fes tayi wanka ta fito ckn ado na alfarma tamkar mai shirin xuwa gidan biki, yasmeen ta shigo tare da sallama cike da kunya Ruhaimat ta karbeta hannu bibbiyu bayan sun gaisa ta kawo mata kayan marmari bata ci bah nan Ruhaimat ta gane cewa yasmeen na jin kunyarta bisa abubuwan da suka faru tsakaninsu, murmushi tayi tace "haba yasmeen ki daina jin kunyata ki daukeni tamkar kanwarki uwa daya uba daya sannan kuma aminiyarki mai fatan ganin farin cknki, ina so ki mance da duk abubuwan da suka faru a da can baya" yasmeen ta sunkuyar da kai tace " kiyi hakuri nayi hakan ne bisa kuskure da zafin kishi saboda ina matukar kaunar imran Amma har Yau na kasa samun soyayyarsa, xuciyarsa na can wani waje yana dawainiya da son wacce bata San yana yi bah" "kina nufin ya imran wata yake so ba ke bah" cike da mamaki yasmeen ta daga kanta tana kallon Ruhaimat tace "tabbas..imran baya kaunata imran yana fama da ciwon sonki Wanda har abada baxai iya cirewa a ckn xuciyarsa" shiru sukayi suna kallon juna..rayuwar da sukayi tare da imran ya fara dawo mata a kwakwalwa..tabbas imran mai kaunarta ne Amma meyasa bai taba furta mata bah?? Take taji tausayinsa ya kama ta..Allah sarki dosti..Ashe haka yake fama da ciwon so kamar yanda ta fama lokacin da ta rasa sadeeq, lallai dole ta fidda shi ckn wannan halin ..hawayene suka cika idanunta tace "yasmeen ki min alkawari xaki dasa kaunar ki a ckn xuciyarsa xaki mantar dashi sunana a ckn rayuwarsa..xaki sa ya manta da duk wata alakar da ta taba faruwa tsakanina dashi, idan kinyi alkawari ni kuma a shirye nake da taimaka miki" "na miki alkawari insha Allah xan saye xuciyarsa ya fara sona Amma baxan miki alkawarin cewa imran xai manta dake a ckn xuciyarsa bah..don nasan hakan baxai taba faruwa bah" numfashi ta ja sannan ta fara magana " yasmeen ina son ki Sani cewa xuciyar Dan Adam kamar miyace wadda akayi mata shiri na musamman don tayi dadi ko abarta haka taki yin dadi, kamar yadda tsiro yake nuna abunda aka shuka shi xaa girba..haka rayuwa take don haka ya xama dole mu kula da addininmu da lafiyarmu da kuma mazajen mu..idan har kina Neman soyayyar mijinki dole ne ki San wadannan abubuwan: da farko ki kasance mai tsafta... mai gaskiya..ladabi da biyayya..iya kwalliya..iya girki ..girmama iyayensa da karrama danginsa...iya magana..ki kasance mai hakuri..kibi umarninsa..iya tafiya, murmushi, shagwaba da sauransu" a takaice dai yasmeen ta yini a gidan Ruhaimat har yamma sannan driver yaxo ya dauketa suka koma gida.
Ta gama tsara kwalliya tana jiran dawowarsa bayan wasu yan dakika taji tsayuwar motarsa nan ta tashi xata fita sukayi arba a bakin kofa ya dagata sama tamkar baby yana juyata dakinsa ya wuce da ita bai direta ko ina bah sai saman gado sannan ya fada gefe "washh..nagaji my Dil " sumbatar goshinsa tayi tare da cewa "sorry mai sona..muje kayi wanka ka ci abinci ka huta sannan na maka tausa" ya tashi xaune yace "da gaske ??..oh my pretty kinsan I Lov ur massage ai" gira ya daga mata murmushi take ta gane meyake nufi daga nan ta bude fridge ta dauko masa exotic mai sanyi ya karba yayi sipping kadan ya mika mata ta ajiye yace "Allah ya miki albarka maini..I Lov u so much" "Lov u more my Dil" ya jawota ta fada jikinsa yace "akwai albishir da xan miki Amma sai kin min wanka xan gaya miki" dariya tayi tace "toh muje mana...wannan dai baxai hada fada bah" daga nan suka wuce toilet tare.
_40mins leta_...yana kwance rub da ciki tana masa tausa " pretty kinsa nayi overfeeding gashi ynxu kasala nake ji" murmushi tayi "shine mai kyau kenan.. Kullum haka xaka yi dama baka son cin abinci ynxu dura xan maka every day" dariya yake sosai "aw..wayo koh! Ban manta ba ai ..albishir da kace xaka min" "ohh..hakane har na manta wllhi, sorry dawo nan kusa dani" babu gardama ta kwanta dab dashi tare da kura masa ido "ihmm..ki shirya goron da zaki bani" "a shirye nake sir!" Dariya ta basa , hannu yakai yana shafa Dan karamin bakinta yace "na fadawa baba dream naki na xama international scholar , dazu ina office ya kirani yace ya sama miki admission a garin madina tare xamu tafi ni xanyi PhD Nah a king Abdullahi university of science n technology jeddah" wani irin ihun da Ruhaimat tayi ta kankame shi tamkar xata shiga ckn jikinsa.dariya kawai yake mata "nagode..nagode..nagode *mai sona* Allah yabar kauna Allah ya kara budi da bunkasar arxiki, tnx I Lov u so much" godiya take masa daga karshe ta fashe da kukan farin ciki nan ya fara share mata hawaye, wani killer kiss ta masa tace "wannan shine goron " dariya yake yace Sam bai amince bah haka ta kira baba da mami ta xuba godiya daga nan ta fara kiran yan uwa da abokan arxiki tana sanar dasu.har Abbanta saida ya kira baba ya nuna godiyarsa a wannan Daren ta farantawa sadeeq rai ba kadan bah, washe gari suka hau shirye shiryen tafiya.

*Reefat ce*😘😘😘
[9:28PM, 20/12/2016] β€ͺ+234 703 007 7024‬: πŸ’žπŸ’ž *MAI SONA*πŸ’žπŸ’ž
*74*
BY *Reefat yahya*

*an imaginary Lov story*

Bayan wata 4 Ruhaimat ta kammala karatunta suka dawo Nigeria tare da kyakkyawan little sadeeq mai kama da Ruhaimat sak babu inda ya barota sai hasken mahaifinshi da ya dauka yaron yana kyau mai firgitarwa ga uwa uba farin jini Abba suke kiransa gashi da girman jiki, tunda suka dawo mami ke rawar jiki da jikan nata ta daina kula Mimi ba kamar da bah wannan ne yasa Mimi ta fara jin haushin kanin nata. WatA 1 da dawowarsu Ruhaimat ta fara rashin lfy bata iya cin abinci tea kadai take sha sadeeq yayi ta rokonta suje asibiti taki amincewa mami dai dariya take musu don ta gane ciki da ita abunka da manya kenan. Dole ya hakura yana lallabata dakyar take iya cin abinci idan taci kuma amai ne zai biyo baya ta share sati 2 ckn wannan halin wata rana meenah taxo ganin gida bayan sun kadaita a daki tace "ke anty Nah kice mu fara shirin xuwa suna man" ta xare ido " bangane bah" murmushi meenah tayi tace "u min baki San kina dauke da juna biyu bah"😳😳 wat?..juna biyu?,

Please Login or Register in order to submit comment