Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa Bilkisu na zaune kusa tana faman zabga kuka, ta soke kanta a tsakanin kafafuwanta. Ganin haka sai mahaifiyarta ta je kusa da ita ta dafa ta, cikin firgita ta waigo. Ganin mahaifiyarta ce, sai ta rungumeta cikin sabon kuka.


Ta ce da ita; “ajiye kukan, abinda ke gabanmu yanzu shi ne, muyi kokari mu nemi ta inda zamu fita daga wannan wurin, domin na kashe shugabansu” cike da tsoro ta kalli mahaifiyarta da ke magana jikinta na rawa. “ina Amisha” zancen da ya fara fitowa daga bakinta kenan. Bataan lokacin da ta sake fashewa da wani sabon kuka ba, tana so ta gayamata me ya faru da kanwarta amma kuka ya hana, ganin haka, Bilkiu ta mike zunbur ta shiga tantin, ai ko sai ta fadi kasancewar ta kasa rike kafafuwanta, nan ta fara kuka tamkar an baiwa yaro alawa an kwace, har da ajiyar zuciya. Saai jijjigata take, a tunaninta zata farka, amma ina.


Cen Sajida ta shigo cikin tantin ta fara rarrasarta tana fadar “ki taso mu tafi kafin azzalumannnan su Ankara da ta’asar da nayi, kar gudunmu da kwnakin da mukayi muna shan wuya a jeji su tashi a banza, kinsan matsawar wadannan mutanen suka fahimci me ya faru, sai dai gawarmu”


Budar bakinta, ta ce, “gaskiya umma bazan iya barin gawar Amisha a nan ba”


“ka jimin karanbanin banza, kinaso ki gayami cewa kin fi ni son ta ne? akwai abubuwa da ke faruwa wadanda mutum ba yadda ya iya dole ya rungume su yadda suka zo, wannan kaddara ce ba mu muka tsara ko muka zabi rayuwarmu ta zo a haka ba, tsarin ubangiji ne kuma shi ya fi mu sanin dalili da ya sa ya aikata hakan akanmu, inada tabbaci ubangiji ya mana tanadi da zamu yi farin ciki da shi. Ki zo mu tafi, karshen rayuwarta kenan, babu wani abu da zamu iya yi a kai, abinda take bukata daga garemu shi ne addu’ah”


Ta yi ajiyar zuciya ta mike, daf da zowa bakin kofa, saai ta tsaya, ta juyo ta kalli mahaifiyarta da ke kallon inda gawar Amisha take kwance tana zabgar kuka, ta ce; “inna! Kinada hanya da zamu fita ne daga wannan gari, ki duba fa dazu da muna zagayawa, ko ina cike yake da tsaro mai tsanani da rana ma ke nan, bare da dare, ni fa ina jin tsoro”


Ta yi murmushi ta karaso kusa da ita, ta dafa kafadarta, ta ce “Mamanne kenan, a duk lokacin dabawa ya yi yunkurin aiwatar da abu, kada ya sake ya kalli hadaruruka da ke cikin abinda zai yi, ya kalli ina yake so ya tafi kawai, a lokacin ba abin da zai hana shi isa inda ya dosa, ba shakka bansan hanya ba, amma ke a tunaninki za a rasa wadanda suka san hanya? Kar ki manta akwai tsofaffi a gidannan wadanda sun yi shekaru da dama, dole a cikinsu akwai wanda ya san hanya. Zo muje” ta fada dai dai lokacin da take jan hannunta ya zuwa kofar fita.


Fitowarsu daga kofar da kyaurenta wani labule ne shudi, amma yanada kauri sosai, suka yi kicibis da wani mai aikin tsaro yana zagayawa a cikin garin, sun fito ne a daidai lokacin da yake wucewa ta kan layinsu, rike yake da bindiga AK47 wacce ke make da alburusai si aljihun rigarsa da na wandonsa da suma suke dauke da alburusai da ‘yan bamabamai.


“ina zaku cikin wannan daren?” ya fada yana mai jiran su bashi amsa


Cikin debe damua a fuskarta, ta amsa masa, “dama wannan yarinya ce ta kasa barci tazo ya samemu da mijina, kasan yau aka dauramuna aure, shi ne ya fusata yace in maidata dakinta ko ya yanka ni”


Ya fashe da dariya, ya ce “tabbas wannan karamin aikin shugaba ne, ke yarinya kina kukan rashin mahaifiyarki ne? je ki kai ta kafin ya jiwo zancenmu ya hada da ni ya yanka” ya wuce abinsa. Nan ta kara sauri, hart a karaso inda tsohuwar da ta kai ta inda ta yi wanka lokacin da suka zo. Da kyar ta samu ta tadata, saboda a hankali take tadantan gudun kar yara da ke kwance a dakin su farka. Tashin tsohuwar ta so ta yi magana sai Sajia ta rufe mata baki, da ta gane Sajida sai ta mike zaune, bayan ta sake bakinnata ne tsohuwa ke tambayarta, me ya kawota wurina cikin wannan tsalelen dare. Cikin rashi sanin inda za ata soma, ta kalli bilkisu da tun shigowarsu hankalinta yake tashe, kamar wace za atura a rami da ranta, sai ta cewa tsohuwa. “iia, nasan dai kinsan duk anda ya taimaki wani, shima ubangiji zai taimake sa, ba dogon suturtu nazo muyi ba, akwai babban al’amari da ya faru kuma ke kadai ce za ki iya taimakamani, ni da wannan marainiyar” “me ye ya faru ‘ya ta?” ta fada cike da son jin amsa daga Sajida. “iya….ta yi shiru, hawaye suka fara sauka daga kumatunta ta kasa furta komai. Ganin haka tsohuwa ta dafa kafadarta ta ce, “kar ki ji komai gayamin matsalarki, insha Allah zan sharemaki hawayenki” “ki taimakemu ki unamuna hanyar guduwa daga wannan garin, wallahi matsawar muka kwana a garinnan to da safe kisan gilla za a yi muna” “kisan gilla kuma? Ke da kike auren shugaban wannan garin gaba daya, wa ya isa ya tabaki, haba ‘ya ta” ta fada tana kokarin janyo ta a jikinta “bazaki fahimta ba ne” “ai sai ki fahimtar da ni” “na fa kashe shugaban, kashe ‘yata ya yi ni kuma bansan me ya faru ba, kawai naga gawarsa a hannuna” ta sake fashewa da wani sabon kuka, a wannan karon hard da sauti.


“lallai kin aikata babban aiki” ta yi shiru na wani lokaci mai tsawo, sai ta kalli Sajida ta kalli Bilkisu, cikin tausayi ta mike tsaye, ta ce “ku biyo ni.”


Suka biyota, ta shiga gaba suna biyarta bayan sun fito daga tantin, duk inda za su bi sai tsohuwar ta leka sai ta ce da su su dakata, ida tag a ba kowa sai ta fara wucewa daga baya sai ta yi musu alama da hannu cewa su zo, sais u biyo bayanta ahaka har sukayi nisa da tafiya cikin garin. Saura kiris wani ya gansu, sai suka shige wani tantani suka labe da ya wuce suka fito suka ci gaba da tafiya. Haka suka ci gaba da tafiya har suka karaso a wani tanti sai tace su shiga ciki, da suka shiga, tsohuwa ta tayar da wani saurayi mai kimanin shekaru sha tara, cikin firgita ya tashi, ganin tsohuwar ce, sai ya yi shiru, ya mata alama da hannu cewa lafiya. Ba tareda ta bashi amsa ba, ta jawo hannunsa suka fito, suka ci gaba da tafiya, har suka karaso wurin wata Katanga, daya bayan daya sukaa dare katangar, amma kafin su hau katangar sai da tsohuwa ta yi musu bayanin cewa, ita ba za tai ya biyarsu ba, domin za ta tsayar da su ne, haka idan ta bisu za a zargi wani abu, kawai su tafi, shi kuwa saurayin ashe dama jikanta ne, tamasa alkawarin wata rana za ta fitar da shi, shi ne take gayamasa cewar lokacin ne ya zo.


Ta yi bankwana da su ta kuma yi musu fatan alkahairi. Dadi a zuciyar Sajida kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha.


Ai ko suna kammala tsallakewa suka fara gudu na fitar hankali. Abinka da mutum mai zurfin tunani, ashe Sajida ta debo makudan kudi daga tantin shugabansu, bayan kudin sadakinta da aka damka mata a hannu, ta daure su a zane cikin leda, da su take gudu a jikinta. Bilkisu da saurayi ma sai aikin gudun suke yi.



Shin su rayuwarsu kullum a gudu suke?
Ina kuma za su dosa?
Duk amsoshinku na a shafi na gaba




DR. ZAIN
[2/3, 5 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾



2⃣3⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```






_On average, women say 7,000 words per day while men manage just over 2,000 words._








*Shafin Masoya*




*MUGIRAT MUSA*



***CI GABA***





Ba zancen tsayi ko wasa, saboda sun rigaya sun san cewa matsawar suka tsaya aka tarar da su a wannan karon ba zanncen kamu ba ne, kisan gilla za a yi musu, duk gudun da suka dauki kwanaki sunayi zai tashi a banza kenan.


Sai ketar jeji suke yi a kidime hankulansu a tashe, idan suka dauki kamar awa biyu suna gudu sai su tsaya su huta, a haka har safiya ta waye suna kan gudu. Ganin hasken rana ya bayyana, ya sa suka tsaya suka yi taimama suka yi sallah, ba tareda sun tsaya doguwar addu’ah ba suka cigaba da aikin gudu.


A gari da suka fito kuwa, dama shugaabannnasu shi ke bayar sallah, da lokaci subahin ya yi aka ga bai fito ba, aka dan kara minti goma, ind wasu ke tunanin auren da ya yi e ya hana shi fitowa sallah da wuri, aka gabatar da wai ya jagoranci sallar.


Da suka ga har ga shi safiya ta waye ama ba shugaba ba alamunsa, kasancewar duk safiya yakan hau mimbari ya yi musu irin huduba da ta kamace su. Ganin haka, sai wani ya je kofarsa ya dinga yi sallama, ganin ya dau lokaci mai tsawo yana sallama, amma sam ba alamun za a amsa, ya sa yazao ya sanar da saura mutane, sai wani na kusa sosai d shugaban, ya zo ya shiga dakin, ai ko nan ya yi tsaye ya sha jinin jikinsa, yana cikin dakin ya yi kira da babbar murya, cewa “ku zo ku ga abinda na gani” nan sama da mutum biyar sukaa rugu cikin dakin. Sai kallon gawar shugabansu suke yi wacce hart a fara kamewa sosai, a gefe kuwa gawar Amisha ce, da ke kwance cikin jini. Nan take wani daga cikinsu, mataimakin shugaban ya bada umarnin a kawar da gawar ta shugaban ayi mmata sutura, ita kuwa Amisha ayi wurgi da gawarta cen cikin jeji. Ya fito ya hau mimbari ya soma jawabi.


“saninku ne duk mai rai mamaci ne, kuma a iya zamanku na wannan garin kun shaidi adalci daga garemu ta hanyar baku kulawa yaddda adini ya ce a baku, amma kamar kullum ita musiba haka take bibiyar mumini har ya zuwa ranar da zai hadu da ubangijinsa, jiya annoba ta sauka a wannan garin namu da ta yi sanadiyyar salwantar rayuwar shugabanmu, tabbas kaddara gaskiya ce, haka daukar fansa ma gaskiya ce. Mu ke fita domin takara, ama yau mu aka zo har gidanmu neman magana, to walahi inason ku shaida, ba za mu kyale wannan cin fuska da akaa yi muna ba, za mu duki fansa, idan na ce fansa, ina nufin fansa da ake kira fansa. Ba wadannan kadai ba da ke da hannu a cikin abin d ya faru ba, hatta asu alaka da su a wannan garin sai mun nunamuku azabar da zasu sha kafin wadanncen su shigo hannu”


Ya yi alama da hannu cewar wasu su gabata a gabansa, sai ga wasu karti biyar majiya karfi wanda kowannensu idan ya yi kashi a jeji ya umarceka da ka korewa kashin kuda bazaka bari kuda su taba masa kashi ba kan masifar karfi, ga kowannensu kato a kirar jiki, kuma duka bakake wulik, fuskokinsu kamar sai da aka zabo, ba mai alamar imani a cikinsu ko tausayi. Ya ce da su. “kunsan halina, bana bukatar na yi maku dogon sharhi kan ni waye. Bana tausayawa wanda ya saba umarnina,kuskure kuwa ba ya cikin kamus dina, inaso ku kawomin wannan matar da ta aikata wannan aikin, bandamu da wadanda take taredasu ba, ita kadai nakeso ku kawomin, kuma a raye, bandamu ba yadda zaku jagalgalataa ba, nidai ta zo hannuna a raye kawai, ko da kuwa gunduwa-gunduwa kuka yi mata. Ku saurara, da zarar awa 48 ta shude baku kawota ba, kada wanda ya yi gigin dawowa wannan garin, ba sai na gayamuku hukuncin da zai hau kanku ba.


Cilin sauri suka dare Babura masu tsayi sosai na tayoyi, irin Babura da a kaashen waje kadai ake kera irinsu, da suka fito daga garin sai suka raba hanya, kowa ya dauki hanya daya domin yunkurinsu na cinma su Sajida. Kowannensu ya baiwa babur nasa wuta ya noshi jeji ba tsaiko.


A garin kuwa suka ci gaba da lamuransu na shagalin nada sabon shugaba, wanda ya soma nashi dokoki da tsare-tsare bayan sun kawar da gawar shugaba da ya mutu. Ana tsakiyar shagali, ya sake hawa mimbari, sai mai kira ya yi kira, dalili da ya sa kowa ya halarta ke nan, a wannan wuri da kusan nan ne magama da wurin taro a duk lokacinda wani abu ya faru, ko kuma ake da wani sako da za a gaya musu.


Cikin bacin rai yake magana, inda ya yi umarni d a gabatar masa da duk wani wanda ke da alaka da Sajida aa garin, cikin kankanin lokaci aka gabatar masa da mutumin da ke basu labarin Nusaiba. Jikinsa sai rawa yake yi. Shugaban ya yi umarni da a kaimasa shi a dkin tuhuma. Dakin tuhuma, daki ne da ake ajiye masu laifi omin a bincike su kan wai laifi da ake zarginsu, a tarihin garin ba wanda ya taba shiga dakin tuhuma ba tareda rayuwarsa ta salwanta ba. Haka suka ja shi yana kuka suka shiga da shi wannan dakin da ake zaluntar marasa karfi.


Cen sai ga shugaban ya shigo dakin, suka dora mutumin kan kujera inda suka daure hanneyensa ta baya, shi kuwa yana a zaune, suka kuma daure shi ta gabansa da kafafuwansa a wuri daya, yada ba zai iya motsawa ba, a gefen hagunsa da damarsa, karti ne rike da manyan karafuna masu tsini sosai.


Aka gabatarwa da shuban kujera a daf da wannan mutumin, ya kalle shi ido cikin ido, ya ce, “kar ka wahalar da ni ba bata lokacina nazo yi ba, ya aka yi suka gudu suka bar ka baya, ko kai sai a daren yau ka shirya naka gudun”?


Bakins na rawa, hawaye na rigangar fita daga idanuwansa yake magana, “wallahi bansan komai ba gameda wannan abu da ya faru, ya ma zan iya sanin wani abu, tun da aka kammala daurin auren, aka turamu ya zuwa wani daki, wanda munada yawa a cikinsa, kuma ko fitsari zaka fita, jami’ai naku har biyu ke rakayar mutum, kan haka ne da fitsari na kwana a marata gudun kar na aikata laifi, wallahi ko da wasa ba zan yi gigin aikata kisa ba, bare irin wannan kisa, ai idan na yi shhi, kaina ne na kashe. Yallabai wallahi bansan komai ba”


Zaumbur shugaban ya mike, sai da ya fara tafiya ya kai bakin kofa, saai ya daga hannunsa sama, ya saukar, ganin haka wadanda ke a gefen dama da hagun wannan mutumin sai suka girgiza kawunansu. Daga fitar shugaban, sai daya aga cikinsu ya yi amfani da wannan karfen da ke hannunsa ya caka masa a kirji, har sai da ya fito ta bayansa, yana nishin fitar rai, dayan ya dubi kansa ya faskara masa wannan katon karfen, har sai da kwanyarsa ta bayyana, ya mutu b atareda ya ko shura ba.


Suka duki gawarsa suka yadda a jeji.


Su Sajida kuwa sai faman gudu suke yi, saurayin da tsohuwa ta hada su da ne ya bukaci su tsaya domin su huta. Cike da jin haushi Bilkisu ta kalle shi, ta ce, “malam ba ka da hankali ne, kallemu ka gani, munyi kwanaki muna wannan gudun, idan muka biyemaka, duk gudun da muka yin a kwanaki ya tashi a banza kenan, domin tarar da mu zasuyi, abinda muka aikata kuma na tabbata ba za su taba yafemana ba, ina amfanin badi ba rai kenan, tafiyar da ba fashi fa zaman baya ba ya yi mata, kawai mu ci gaba da gudu har ya zuwa inda zasu tabbatar mun kubuta daga wadannan azzaluman sai muyii hutun dalili”


Ya kalleta sai haki yake, “anya kinada tausayi kuwa a zuciyarki, tun cikin dare fa muke gudu gashi har rana ta fara kaifi, kike kum zancen mu ci gaba da gudu, sai kace gudun famfalaki”


“hmm! Samari kenan, ai wannan ya fi gudun famfalaki domin gudun ceton rai ne” Sajida ta fada. “ka daure kar ka bada maza mana, kalli fa mace ce, kuma sa’ar kanwarka, idan har zata iya jure wahala kai matashi ai ya kamata ka tabuka fiye da ita”


Ya yi shiru na wani lokaci, sai ya kalli Bilkisu ta ke masa kallon haushi da ganin ya tsaida su.


“Inna idan ya gaji mu bar shi nan idan ya huta, sai ya tarar da mu gaba, kar ki manta fa, ba za su taba tsayawa ba har sai sun ga sun cinmuna, kuma burinsu a kanmu ba mai kyau ba ne”


Jin haka, saurayi ya mike zumbur, suka ci gaba da aikin gudu, cen suna cikin gudu, suka jiyo sautin babur ta bayansu, dalili da yasa suka shige kenan cikin sabarru domin su boyewa ko waye ma tafe. Suna cikin boyon suka hango daya daga cikin wadannan kartin ya zo wucewa ta kusa, da su, ashe ya jima yana biyar sawunsu ne, da yazo inda suka shiga boyo sai ya ajiye babur din ya fara duban ko zai gansu.


Ganin haka sai Sajia ta yi wata dabara, suka bar Bilkisu nan a boye, sai ita da saurayin suka zagayo ta bayan wannan katon, shi kuwa sai duba yake ko zai gan su.


Sajida ta je kan jikin babur nashi ta daauko wasu karafuna guda biyu manya, duk tana yi ne cikin sassarfa gudun ya jiwo motsinta.

Cen yana cikin dubawa, sai ya hango duhun mutum, ya kara matsawa wurin, ganin ya dosata gabadaya ta kidime ta mike tsaye, kafin ta gudu, ya yi caraf ya kameta, ya ce, “ku daina wahalar da kawunanku, ba a tsira a hannunmu sam” ya fashe da wata mahaukaciyar dariya, ya dauko ta kamar jinjira ya dora a wuyansa, Bilkisu sai kuka take tana kiran Inna zo ki kubutar da ni.


Ya fito daa ita daga cikin surukin sabaru daa kalage, ya ajiyeta, ya fara tambayarta ina mahaifiyarta, ta yi shiru taki amsa masa, ganin ba zata amsa ba ya shara mata mari, har sai da bakinta ya cika da jini, ta fashe da kuka ta dafe bakinta,


“za ki yi magana ko sai na ill………


09039951083

DR. ZAIN
[2/3, 5:00 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




2⃣4⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_A beautiful face will age and a perfect body will change ,but a beautiful soul will always be beautiful.._









*Shafin Masoya*



*Asiya Abubakar Imam*


***CI GABA***




….illata ki?” ya fada yana mai zaro idanunsa ya zuwa gareta, ganin haka ta tsorata har ta fara ja da baya, ta amfani da jikinta tana motsawa kasancewar ta fadi a sanadiyyar mari da ya kaftamata.


“da fa ke nake magana”


Ta kara tsorata sai kuka take tana ja daga baya, bai Ankara ba shi kuwa ji kawai ya yi an kawo masa bugu a ka da karfe, juyowa da zai yi aka kara buga masa, ya yi tangal-tangal kamar zai fadi, amma zai ya jure ya yo cikinsu, ganin haka suka zaude, ya kawo duka ya sami saurayi a baki, nan take bakinsa ya fashe, karfen da ke hannunsa ya fadi. Ganin haka, kafin ya mike Sajida ta yo cikinsa ta sake bugamasa karfen da ke hannunta a ka, sai ya fadi rica! Ganin haka saurayi ya mike cikin sauri ya kama mata, suka ci gaba da dukansa har sai da suka tabbatar ba ya motsi.


Bilkisu kuwa inbada kuka ba abinda take yi sai kokarin taba bakinta inda ya mata rauni.


Ganin sun kawar da wannan katon, Sajida ta zauna, ta mike kafafuwanta ta tada kanta, sama hawaye suka dinga fitowa daga idanunta kamar birgaggen famfo, ta dinga wasu addu’o’I a zuciyarta kawai dai zaka ga bakinta yana motsi. Bilkisu ta rarrafo ta kwanta a jikin mahaifiyarta, inda saurayi yake tsaye a kansu, duk da shima a jigace yake, ya tausaya musu matuka.


Budar bakinsa, ya ce, “yanzu me ye mafita?”

Sajida ta kalleshi, gaba daya hawaye sun jika fadaddar fuskarta, idanuwanta sun yi ja sun kumbura kan masifar kuka, gashin kanta gaba daya ya yi taushi kan azaba da zufa da ta jika shi, kafafuwanta kuwa burum-burum kan masifar kura. Ta ce, “kaga wannan? Kadan ke nan daga musibu da muka shiga cikin wannan *GUDUN HIJARA* da muka tsinci kawunanmu a ciki, yanzu zamu ci gaba da gudu ne, har ya zuwa inda ubangiji ya sada mu da mafita ko wata sabuwar jarabawar.”


Suka mike suka ci gaba da tafiya, har dare ya fara yi, ganin haka suka tsaya suka yi salloli da ake biyarsu, saidai suna tsakiyar rama sallolin sai ga ruwa un fara sauka, da suka kammala sallar sai suka nemi wuri domin su buya, kasancewar fallau jejin yake, dole suka hakura a karkashin sabara, ruwan a dukansu, sai cirar sanyi suke, amma a yada suka iya, suka sha kashin ruwan a sama da awa biyar kuma masu tsananin karfi. Da ruwan suka tsaya, duk da da barci a idanuwansu, haka suka cigaba da tafiya, da yake sun galabaita kuma sun jigata, ba sa iya gudu.


Ba tareda sanin ina za su nufa ba, sai tafiya suke ba abinda ke zukatansu irin yau su gan su sunn tarar da wani gari, amma kamar su debe tsammani, domin har safiyar Allah ta waye, ba gari ba alamrsa, dole suka ci gaba da tafiya a haka, suna tsoron su tsaya wadannan azzaluman su tarar da su, ga shi kuma yunwa sai dibarsu take, ita gajiya ba a ma maganarta domin yaddda suke jan kaffuwansu kadai a yayin tafiyarsu ya isa ya bayyana maka hakan. Ganin sun gaji sosai, kuma ga rana ta fara, zafi, ta kuma lura da yaran yunwa suke ji, sai suka ratse kan hanya, suka nemi wani katon dutse, suka zauna cikin kadarkonshi, suka nemi wuri suka gyara, yadda zasu sami kariya daga zafin rana ko saukar ruwan sama, ta hanyar amfani da itace da ciyawu. Sai ta umarce su da su zauna su huta, ita kuwa ta shiga jeji domin ta nemo musu abida za su ci.


Ba ta sami dawowa ba sai zuwa maraice, inda ta zo musu da bushiya kwara hudu, wadanda ta yi amfani da baki ta yanka, kasancewar ba abin yanka. Dama kafin ta dawo sun shiga jeji su debo itace, da idan Allah ya sa ta dawo da abin farauta sai a gasa.


Haka suka gyara inda za a gasa naman, suka tara itace masu girma guda hudu sai ciyawa mai dan yawa, suka kafa wasu itace masu dan tsayi guda biyu sai suka gilma wani ice kwaya daya, wanda a jikinsa suka dora duka bushiyar da suka gyara guda hudu. Aka samo duwatsu na kankara guda biyu, suka dinga bugasu har suka fitar da wuta, wacce ta kama ciyawar, suka ci gaba da hurawa har wutar ta kama sosai. Suka ci gaba da gyara wutar har naman ya gasu gaba daya, suna yi suna fira. Aka saukar da nama suka ci. Ganin dare ya fara, kuma ga shi suna jin kishi na ruwa, Sajida ta ci gaba da tafiya cikin kadarkon har ta tarar da inda ruwa suka taru sosai, ta sha, ta wanke jikinta, daga bisani, ta zo ta kai su suma suka sha, suka wanke jikinsu, ganin haka sai suka nemi wuri kusa da ruwan suka kafa ‘yar bukka.


Haka Sajida ta ci gaba da kulawa da su, tana kuma amfani da damar tana jan kunnuwansu musamman domin su fahimci juriya da yadda da kai su ne sinadarin kowacce rayuwa. Haka suka dauki sati daya a wurin, ganin ruwan sun fara raguwa, sai suka tattara nasu ya nasu suka ci gaba da wannan makauniyar tafiya, da basusan ina suka fuskanta ba.


A garin ‘yan boko Haram din kuwa, da awa 48 suka shude, shugaban ya ga wadanda ya tura basu dawo da Sajida ba, sai ya tura wasu, ya ce, ya basu umarnin su zo masa da su Sajida da kuma wadanda ya turan

Please Login or Register in order to submit comment