Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

🐾




3⃣3⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```




_Allah ne kadai ya san karatun kurma_









*Shafin Masoya*



Wannan shafin naku ne masoya a duk in da kuke a fadin duniyarnan ina godiya da irin addu'o'i da fatan alkhairi da nakesamu daga gareku. Haka ina godiya da shawarwari da kuke bani Allah ya bar mu tare.



***CI GABA***







*LABARIN SHU’AIBU*



“Sunana Shu’aibu, ni haifaffen garin Bunza ne da ke karkashin jihar Kebbi, a unguwar Fulani aka haife ni nan garin Bunza, a nan na tashi na yi wayau har na girma, lura da ban mayar da hankalina kan kiwo ba duk da cewa ni Fulani ne gaba da baya, ya sa mahaifina ya tura ni karatu a garin gashwa da ke karkashin jihar Borno. Nan na yi karatu har na sauke alqur’ani, ina karatun litattafai, kafin na mallaki karfi da hankalin kaina, na kasance ina yin bara gida-gida domin na sami abin da zan ci domin in rayu. Da na mallaki karfin kaina, sai na dinga yin sana’ar dako a kasuwa, a lokutan da ba ma yin karatu a makaranta, nakan je kasuwa domin na sami abin da zan tallafawa kaina. Bangaren iyayena kuwa, tun lokacin da suka kawo ni karatu, bansake ji daga garesu ba, hasali ma su da kan su ko sau daya basu sake komawa ta kaina ba, tun abin yana damuwata, har ya bi jikina, yanzu banajin komai kan hakan. A in da muke kwanciya kuwa, zamu haura mu dari, kuma ga wurin matsattse wan da dole wasu sai dai su gwamu da wasu kan rashin yalwar wurin kwanciya, bayan wari na daudar jikinmu, numfashi ma kadai a gauraye yake, wanda shi karan kansa wata mabuda ce ta shigowar cututuka daban-daban. Wata rana da ba zan taba mantawa da ita ba, muna aiki da maraice a kasuwa, kusan lokacin magariba, na daukowa wata mata kaya da ta siyo tana gaba ina biyar ta daga baya, muna karasowa bakin kofar kasuwa, sai muka fara jiwo kara ta bindiga, mutane sai guduwa suke yi suna kokarin tserata da rayukansu, hakan ta sa mutane sai gwauruwa suke da junansu a halin fita daga kasuwar, sai faduwa mutane suke yi, ana take wasu, wasu a nan wurin suka rasa rayukansu. Ganin haka, na yada kayan matar da ke dauke a wuyana, na bi jama’a aguje da ke kokarin ficewa daga kasuwar domin su ceci rayukansu. Sai gudu muke yi, irin gudunnan na idan ba ka yi ka bani wuri, bugu da kari ga duhu sai kara shigowa yake yi, mune bamu tsaya ba har sai da muka kai tsakiyar jeji, kuma ga masifar duhu, saboda mun dauki awa biyar muna gudu, ba tsaiko. Muka tsaya tsakiyar jeji mu hudu ne, wata mata na tareda mu, sai wasu tsofaffi maza gudu biyu. Matar kuma gata dauke da tsohon ciki. Amma a haka take gudu kamar ba ciki a tattare da ita. Nan muka yada zango cikin jejin da bamusan sunansa ba, bamusan a ina yake ba, bamusan ina zamu nufa ba. Muna tsakiyar hutawa aka fara ruwa masu masifar karfi, dama tun da maraice munga alamun hadari, ba alamun ruwan zasu sauka, saukarsu kawai muka ji,dalili kenan da yasa muka fara sassarfa muna neman in da zamu labe domin mu buya daga shan kashin ruwan sama. Da kyar muka sami wani kwazazzabo mai zurfi muka shiga, duk da bai bamu cikakkiyar kariya daga shan kashin ruwan ba, ya taimaka wurin rage karfin ruwan daga dukan jikinmu kai tsaye. A lokacin ni ba ta kaina nake yi ba, na fi tausayawa matar da ke tare da mu, musamman yadda naga tana cira tana rawar sanyi, a duk lokacin da na kalleta na kuma kalli tsohon cikinta, sai kawai naji hawaye na kwaranyowa daga idanuwana. A haka ina tsaye har ruwan suka kammala sauka gaba daya, kallon da nake wa matar ya sa gaba daya banajin dukan ruwan. Wani abin tausayi, shi ne, wadannan tsofaffin da muke tareda su, a kalla kowannensu zai haura shekara saba’in, wannan shi ne dalili da ya kara tsayar da mu cikin jeji tsawon makwanni muna shan azaba da ganin bone. Domin kamar hadin baki, su duka biyu, suka kamu da rashin lafiya mai tsanani, ban yi zaton zasu rayu ba. Haka ni da wannan matar muke shan wahala wurin kulawa da su, musamman da yake tsofaffi da suke da bukatar kulawa ko ba ciwo bare ga dalili. A rayuwata, ban taba haduwa da mace mai dakakkar zuciya mai karfin hali irin matar da muke tareda ita ba. Duk da cikinta tsoho ne, bazaka gane hakan ba, yadda take tafiyar da lamura gata da sanin ya kamata. Haka nake fita farauta na nemomana abin da zamu ci, in da ita kuma take kokari wurin ganin ta gyara duk abin da na kawo ta sarrafa shi ya zama abinci, tsawon makwanni a jeji. In da muka tashi tukuru domin ganin mun nemawa wadannan tsofaffin magani. Da muka lura cewa sun sami sauki sosai, sai muka tashi daga masaukinmu in da muka mayar da shan kashin ruwa tamkar yin wanka.”



Gaba daya wadanda ke cikin motar hankulansu suka dawo kansa, wasu sai sharan hawaye suke yi, in da wasu ke ajiyar zuciya. Wasu kuwa suka bige da mamakin, wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwa a duniya. Shi kuwa mai tukin motar sai ya kunna musu wakar ZAINUDDEEN ZAIN mai taken ALAMJIRI wacce suka yi da wani mawaki dan Katsina da kuma Ranking Boy dai-dai in da yake cewa;




_ya baro uwa ya baro uba duk a kauye_
_Fadi-nan-tashi-cen burinsa safiya ta waye_


_Ina za ya dora kansa, ba sukuni a barci_
_Ba sutura mai kyawu, walla ba abinci_


_lafiya ta kaurace daga garesa_
_Babu kwanciyar hankali babu walwalarsa_


_sama da su dari suke kwanciya a daki_
_Malami guda daya ba ya dora su tafarki_


_iyaye da gwannati ya kamata duk mu lura_
_su ne fa suke girma su zamemna lalura_


_tun suna kanani tarbiyya sun kasa samu_
_mu duba abinda ke faruwa a makotanmu_


_kula da yaranmu wajibi ne ai a kanmu_
_Idan muka kula kuma lada ai zamu samu_


…………………………………………..


Haka dai wakar ta ci gaba da tafiya, sautin na tashi a hankali, ta yadda ba ya hana kowa ya ji zancen wani. Shu’aibu ya ci gaba da labarinsa.



“muka ci gaba da tafiya, tsawon kwana daya muna tafiya cikin jeji tun da muka baro in da masaukinmu yake har Allah ya kawo mu wani kauye, munsami kulawa sosai daga mutanen kauyen, kwana daya muka yi a garin sai ga mayakan boko haram sun yi wa garin kawanya. Suka zagaye mu, sai suka yi magana da wata amsa amo, cewar, idan mu mazajen mun aminta mu shiga yakin da suke yi su kuwa matan su bi su su tafi da su, da suka ga alamun ba za a amsa musu ba, suka shigo garin, haka suka dinga kama mutane suna yankawa ba imani, ba kokkotawa. Su kuwa matan suka dinga kama su, da sunan wai ganimar yaki. Ganin haka, na kaikaici idanuwansu na ranta a na kare, in da wasu mutum biyu suka biyo ni, da suka tabbatar da cewa ko shekara aka yi bazasu iya kama bahillace a jeji ba da gudu dole suka sallama suka koma wurin jama’arasu. Kun ji rabuwa ta da tawagar da muke tareda su. Nasan ba shakka ba jinina ba ne, amma naji rabuwa da su tamkar rasa wani bangare na rayuwata. Wanda har yanzu mikin yana tare da ni, musamman na matarnan mai ciki. Yanzu Allah kadai yasan halin da take ciki. Ni kuwa da na tabbatar na tsere musu a gudu na nemi wuri na zauna domin in sami karfin tafiya da ci gaba da neman hanya domin in koma asalin garina wato Bunza a jihar Kebbi.”



Gaba daya motar kowa ya yi shiru ya sha jinin jikinsa. Shi kuwa shu’aibu ya ci gaba da labarin ibtila’in da ya same shi sanadiyyar Boko Haram.


Kwanci-tashi har na fado garin Mubi, in da a nan ma harin Boko Haram ya tarar da mu, dalili kenan da yasa dole na yi kaura, na yi amfani da ‘yan kudi da na tara ta hanyar dako na shigo mota ya zuwa garin Yola. A Yola na sauka a wata unguwa da ake kira Anguwan Tana, a nan ne na hadu da wasu samari masu kirki, duk da talakawa ne, sun bani kulawa sosai yaddda ya kamata. Nan na dinga zama, duk da safiya nakan fita neman kudi, idan na sami aikin lebaranci ko dako nakan yi, a hankali ina tara kudi, har na sami guzuri da na tabbatar zai kai ni garina na Bunza a jihar Kebbi. Shi ne na shiga mota domin na koma gida.”



Yana kawowa nan ya yi shiru, suma dai wadanda suke cikin motar shiru suka yi kamar wadanda aka umurta. Cen wani tsoho da ke zaune daga tsakiya ya kada baki ya ce; “wasu lokuta mutane na bani mamaki musamman wadanda suke tura yaransu yawon almajiranci, sai ka ga an tura yaro almajiranci tun bai ma mallaki hankalin kansa ba, wani ko wando bai iya dorawa ba, baisan hagu bare damarsa ba amma a haka za a tura shi almajiranci, abin takaici sai a kaiwa malami shi, ba abincin da zai ci, ba kudin kula da lafiyarsa ba ko sutura a tatter da shi, mafi mamaki sai kaga lokcin da ake tura su almajiranci sai bayan an kammala girbe abinci ne. idan muka kalli garuruwa da suke dauke da ‘yan ta’adda galibi zaka ga sun fi yawan masu yawon bara ne da sunan almajiranci, yaro tun yana kankani zuciyarsa ta mutu da bara, ta ya zai girma ya nemi na kansa ko ya tsaya da kafafuwansa? Allah dai ya kyauta”




Ya fada bayan ya ja dogon tsaki. Nan dai suka ci gaba da tattaunawa, driver kuwa sai sharar gudunsa yake yi, idan ya canja wannan wakar ya saka wannan.




DR. ZAIN
[2/4, 7:52 PM] Dr. Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾





3⃣4⃣







Na





*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_






® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```



_People will stare..._

_Make it worth their while._









*Shafin Masoya*



_Sis Naja'at_
_Aisha_
_Fatima_
_Zainab_

Kawayena na kaina




***CI GABA***






Haka suka ci gaba da tafiya cikin motar idan wannan ya bayar da nasa labarin, wancen ya bayar. Kwanci tashi har suka karaso garin Gusau, dole suka lallaba gudun kar su hadu da masu garkuwa da mutane. Suka karaso Sokoto, suka ci abinci suka karaso Kebbi.



Duk da cewa ta dauki lokaci mai tsawo batazo garin ba, fasali na garin bai rikitata ba. Aka saukar da su a tashar sir Yahayya Memorial Hospital Birnin Kebbi, kasancewar suna tareda wani tsoho da ta yi wa alkawarin cewa zata taimake shi, basu nemi motar zuwa garin kalgo ba, sai ta tsayar da wasu jama’a ta tambaye su in da sansanin *‘YAN GUDUN HIJIRA* yake. Aka sanar da ita cewa sansanin guda biyu ne, akwai daya da yake a bayan Oando bye-pass kenan, sai daya da ke unguwar malala quarters hannun riga da sabuwar makabarta. Ganin na malala quarters ya fi zama kusa da su sai suka nufaci cen. Ita da Bilkisu da dan tsoho, suka gangara gangaren malala cikin keke napep, duk in da suka ga taron jama’a sai su tsaya su tambaya, a haka har suka kawo daf da kofar gidan.



Gida ne da ba shafar siminti a bulon ginin haka ba fenti ba kyaure kai kofa ma babu, akwai fadi da gidan ta ciki amma duka kofofin dakunan ba wacce ke da gambu duka labulayya ne aka rufe kofofin da su. Gida ne da cikinsa akwai mutane sama da dari biyu, kama tun daga kananan yara ya zuwa manya maza da mata.



Da maraice suka isa gidan wurin karfe biyar da minti arba’in da wani abu, suka yi sallama da masu gidan, sai wata mata da ake kira Hauwa’u ta fito. Sajida ta yi mata bayanin daga in da suka fito. Bayan matar ta nisa, sai ta ce da su, gaskiya ita ba ta da damar karbar shi tsohon a gidan, amma tana zuwa, fitowa da zata yi bayan ta shiga cikin gidan, sai ta fito da wani saurayi dogo baki da shi mai suna Sani. Ta bar shi da su nan tsaye ta koma cikin gida.



Sajida ta sake kwashe labarinsu da ya dace ya sani ta gayamasa, ta kuma nuna abin da ya zo da su nan shi ne domin su taimakawa wannan tsohon ya sami wurin da zai fake. Sai da ya dauki lokci mai tawo kafin ya fara magana. “gaskiya ba za mu iya barin shi ya zauna nan ba” “saboda me ke nan?” Sajida ta fada cikin mamaki da son jin me zai fito daga bakinsa. “saboda nan da kike gani, duka iyalinmu ne kadai, ba wani wanda ba ya da alaka da mu duk yawanmu da kika gani kuwa, eh! A halin yanzu gwamnati ke biya muna kudin hayar wurinnan, amma asali mu muka saka kudin jikinmu, na matsananciyar shan wuya muka biya hayar gidan, kinga wani wanda ba muharramin matanmu ba bai dace ya zauna a cikin gidanmu ba. Kinssan duniya kumaa ta wuce tunaninmu, yanzu bamuda tabbasa cewa ku ‘*YAN GUDUN HIJIRA* ne da gaske, domin ba rubuce yake a fuskokinku ba, haka bamusan halin shi wannan dattijon ba. ‘yar’uwa naji labarin da kika bayar, amma ki sani muma mun shiga musiba da irin wannan hali da kuma kuka shiga, saboda haka nasan ‘yan boko haram ba zasu yi kasa a guiwa ba har sai sun cinma burinsu, hakan kuma zasu iya yi ta kowacce hanya. Kuyi hakuri”



Ta yi ajiyar zuciya mai tsawo a ranta tana kokarin neman mafita, amma ina duk abinda ta yi yunkurin tunawa, sai ya tafi kamar kura da ke kan taga. Kawai sai hawaye suka fara fitowa daga idanuwanta, ta kalle shi, ta ce “malam Sani ka ce sunanka ko? Gaskiya ka bani kunya, ai shi taimako idan zaka yi baka tunanin sharrin shi wanda zaka taimaka, annabi cewa fa ya yi, muyi wa muminai zaton alkhairi, ko don tsufan wannan bawan Allah ai zaku taimaka masa, duka saura kwana nawa ya bar muku duniyarku, zancen matanku, wannan ai duk ya isa ya yi jikoki da ku. Ba shakka baka shiga ibtila’I da muka shiga ba, domin da ka shiga kuwa, da da gudu ka amshi wannan aikin ladan. Amma ai gari da yawa maye ba ya cin kansa. Ku zo mu tafi” ta fada dai-dai lokacin da take jan hannun Bilkisu a fussace.



Tsoho na daga bayansu suna tafiya cikin sauri, cen tsohon ya ce “yarnan dakata, kije zuwa in da zaki tafi, ni zan iya kula da kaina, duk abinda ya dace zan aikata ku tafi kawai kada na batamaku tafiya”



Ta kalleshi cikin bacin rai kamar zata shiga jikinsa ta dake shi.



“baba bari na tambaye ka, wa ka sani a garinnan?”


“yata ba wan da na sani”



“shi ne kake so muyi kisan kai ta hanyar barinka kai kadai, ai ko da ba mota ta hadamu ba, kai ka isa ka haife ni sosai, kana ganin ba hakki ne a kaina na taimake ba, annabi ya fada yana daga cikin kyawawa ayuka a girmama mai furfura, gashi baba kanka duka farin gashi ne, idan kuma lada ce baka so mu samu sai ka sanar da mu domin mu tafiya”



“ba haka nake nufi ba yata, kawai dai naga wahala ta maku yawa, kuma naji kina fadar har garin kalgo zaku tafi.”



“kar ka damu baba, mudai gama da matsalarka. Garin kalgo duka minti nawa ne daga nan Birnin Kebbi”



Suka ci gaba da tafiya har suka karaso bakin titi.




Suka tari keke napep suka hau, ta ce ya kai su government house. Ya ajiye su a in da ake parkin motoci ta waje, ta taka ya zuwa gate din gidan, in da ta yi kicibis da masu tsaron kofar, kama da ‘yan sanda sai sojoji da kuma civil defence. “me ke tafe da ku?” daya daga cikin masu tsaron kofar ya fada, in da sauran suka kora musu na mujiya, ai kallon su suke yi kasa da sama. Ta kwashe labarinsu ta gaya musu. Cikin yi musu kallon uku saura kwata, daya daga cikin masu tsaron kofar ya ce, “gwamna ba ya nan ku tafi” “tau don Allah ina zamu sami mai kula da walwalar al’umma?” “shima ba ya nan, ku tafi aka ce” “malam ya da haka kake wani korarmu kamar wadanda suka zo bara? Hakkinmu ne fa muka zo mu taimaka su saukar amma kake mana haka?” “bara wa ya sani ko barar kuka zo, ke wallahi ko kubar kofarnan ko rayuwarku ta baci”




Ta yunkura ta yi magana, tsoho ya ja hannunta ya ce “yata zo mu je”



Suka tafi, suna tafiya tana mita da fada, har suka kawo Diamond bank suna tafiya tsoho ke gayamata.



‘yata ai wannan kadan kika gani, halin masu gadi kenan, sai azo neman gwamna da magana mai muhinmanci amma wadannnan su hana, suna zaluntar gwamnati suna zaluntar talakawa suna zaluntar kawunansu.”


Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina zasu nufa ba. Daf da bakin first bank a round about ta central mosque suka hau keke napep. Bilkisu dai bata ce komai ba. Suka nufaci dayan sansanin “*YAN GUDUN HIJIRA* da ke bayan Oando. Nan ma aka gaya musu kamar yadda aka gaya musu a malala, dalili kenan da ya sa suka nemi wuri suka zauna domin ganin ya ya dace su bullowa lamarin. Gata ta iso jaharsu ta dauka komai zai saitu, amma wankin hula na so ya kai ta dare. Suna cikin zantawa suka jiwo kiran sallar magariba.




Suka tafi a massallaci da ke kusa, tsoho ya shiga masallaci ya yi sallah, in da suka tsaya daga waje suka yi sallah. Daga kammala sallah tsoho ya tarar da su a bakin masallacin, suka ci gaba da tafiya, har suka karaso kan titi da ke hannun riga da sabuwar tasha. Suka jira abin hawa, basu samu ba, sai suka ci gaba da tafiya har suka karaso kan babban gate na sabuwar kasuwa ta gaba, in da gobara ta yi barna. Duka suna tafiya ne, suna neman mafita ta hanyar tattauna shawarwari. Daga karshe suka yanke shawarar zasu tafi da shi a unguwar badariya su nema masa in da zai zauna, da suka karaso unguwar badariya a keke napep aka saukar da su dai-dai ‘yar kassuwar badariya, suka nemi gidan mai unguwa aka nuna masu, suka tafi suka yi magana da shi suka kwashe labarinsu suka sanar da shi, ya dauki alkawarin zai kula da tsoho da ikon Allah. Da akayi isha suka yi sallama da maigari ita da Bilkisu suka nufaci garin kalgo, bayna ta kawo kudi har dubu ashirin ta bai wa tsoho, ta ce ya tanka jalli da su ya sami sana’a ya dinga yi da zai dinga kula da kansa.



Badariya gari ne da ke da kafaffen tarihi, amma a halin yanzu unguwa ce a cikin Birnin Kebbi, kasancewar gine-gine sun tarar da su. Mutane ne da a zamanin baya sun fi shahara da farauta da noma, Hausawa ne, amma sune surke da Fulani da Zabarmawa. Wan da ya sa suka zama kamar tanti na kasuwanci da kuma harkar gini saboda hadewarsu da Birnin Kebbi.



Kai tsaye a tashar da ke Haliru Abdu keke napep ta ajiyesu, suka tari mota da zata kai su Kalgo. Cikin mintuna kadan motarsu ta tashi.




08034840276

DR. ZAIN
[2/24, 7:48 PM] Dr. Zain✍🏾: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾



_last page_



3⃣5⃣







Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```





_Mulki da kasaita ubangijinmu shi ya bada_







*Shafin Masoya*




Yan Gudun Hijira Fans
MATA TUBALIN AL'UMMA


***CI GABA***






Daga saukarsu daga keke napep a farkon titi daga round in da zai sadaka da babban filin wasan kwallo na Haliru Abdu, wanda ya fi shaahara da Haliru Abdu mini stadium Birnin Kebbi, in da ta fuskarsa ne ake samun motoci da zasu dauki mutum ya zuwa bunza, kalgo jega minna kamba da dai sauran gruruwa. Nan wata mota ta tsaya gabanssu tun kafin su karasa in da motoci ke taruwa. Suka yi sauri suka shiga motar, kamar yadda mai motar ya umarta, a cwarsa doka ce daukar mutum kan hanya, amma su aikaatawa suke ba ruwansu. Daga shigarta ta tambaya, nawa ne kudin motar, ya ce da su naira dari-dari zasu biya. Ya buga mota suka ci gaba da tafiya. Daga ita sai Bilkisu a motar, sai wani dan saurayi da ya ce shi a Federal University Birnin Kebbi za a ajiye shi FUBK. A kan hanya ya dauki wasu da zasu tafi kalgo, har dai motarsa ta cika, mutum biyu a gaba sai mutum hudu a baya.


Sai fira ake yi cikin motar, in da Sajida ba abinda ke ranta irin tunanin halin da zata trar da gida, anya kuwa ma zasu shidata? Batasan lokacin da hawaye suka fara kwaranya daga idnuwanta ba, sai ji kwai tayi Bilkisu na kokarin sharemata. Dalili ke nan da ya mayar da hankalin wata mata da ke kusa da su ‘yar kimanain shekar 29, amma zaka yi zaton ta haura shekaru arba’in kan galabaita da shan wahala. Budar bakin wnnan matar ta kalli sajida ta ce, “bauyar Allah, komai fa ya yi zafi, to maganinsa Allah sarki, kin ganni nan, ba musiba da ban fada ba, babu tashin hankali da ban gani ba a rayuwa, amma dole na jingine komai gefe, na kurawa sarautar ubangiji idanu na yi wa kaina fada domin na gina kaina da kaina. Ba abin da kuka zai haifar maki, face mutuwar zuciya” cikin sanyin jiki Sajida ta juyo ta kalli wannan matar da take fara sol duk da ba kyakkyawa ba ce, sai ta kada baki ta ce, “ke kuwa boyar Allah wacce musiba kika shiga haka? Ki sanar da mu wata kila mu amfana muma mu sami izina daga labarinki.”


*LABARIN SHAMSIYYA*


Bayan ta nisa, sai ta soma.


“Sunana Shamsiyya, ni asalin ‘Yar garin Wamakko ce, da ke cikin jahar sokoto, mahaifina da mahaifiyata duka haifaffun sokoto ne, amma yanayin aiki yasa a garin Tambuwal aka haife ni, nan nayi karatu na primary da secondary, haka jami’a a Usman Danfodio University Sokoto nayi karatun diploma. Bansami aiki ba, kasancear yanayi na kasa idan ba wanda ya tsayamaka, kai talaka sai dai ka yi hakuri, duk da kyawun takarduna kuwa, a haka na sha yawun neman aiki ba dare ba rana, har na gaji dole na saduda. Kan haka mahaifina ya sakani a gaba akan tilas sai na fiddo da mijin aure, ni kuwa ba mai tara samari ba ce, wanda nake so kuma na bincike shi bai shirya ba, kan haka na sha tsangwama da barazan daga mahaifana kan lallai zasu aurar da ni ga duk wanda suka ga dama, na sha kuka har idnuwana suka kumbura, har kuka ya zama tamkar wani bangare na rayuwata. Haka na ci gaba da kokartawa na gani ko zan iya taimkawa Jamilu saurayina domin mu samu mu yi aure, amma abin ya ci tura, kasancewar shima kamar ni baisami aiki ba, sai ya yi lebaranci kafin ya sami ya kula da mahaifansa da kannensa guda uku. Wannan ya sa na shiga damuwa matuka. Kwanaki da mahaifana suka dibamin akan lallai na fidda miji, suka cika, hakan ta sa suka sake zaunar da ni suka bincike ni kan zancen, na kasa basu magana da zata gamsar da su, hakan ta kara tunzurar da su, suka ce tabbas zasu hadani da wani wai Alhaji Rabi’u da ke nan Tambuwal, tsoho ne da zai haura shekaru saba’in, amma mai kudi ne sosai, ni kuwa a lokacin shekaruna 25. Na ci kuka sosai, tun da safe na sami Jamilu, na sanar da shi abinda ke faruwa. Ranar kamar ya yi hauka, ya rasa me ke yi masa dadi, a haka ya rarrasheni ya nuna na kwantar da hankalina, bamu isa mu canja kaddarar Allah ba, shi dai yanada tabbaacin cewa yana ji a jikinsa, shi zai aure ni. Zantuknsa sun

Please Login or Register in order to submit comment