Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




1⃣7⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```






_Don't waste your time with people who seek attention they are just bored with there life._






*Shafin Masoya*



Her Excellency Hajiya Aisha Atiku Bagudu the wife of the governor of Kebbi State




***CI GABA***






Sai gudu suke yi gaba daya kaya da ciyawu da ke shimfide cikin jejin suka dinga fasa kafafuwansu, amma ko da wasa hakan bai raunana su ba, hasalima basusan ma cewa kafafuwansu sun fashe ba, sai kaimi suke karawa hadi da gudu na ganin cewa sun tserata da rayukansu daga wadannan azzalumai da suka dafo masu. Kara da sauti na wadanda ake kamawa daga bayansu, ita ta hadddasa Karin kaiminsu wurin gudun ceton rai, Amisha duk da jiki ba lafiya kuka kawai take sakarwa, lamari da ya kara saka Sajida a halin na shiga uku, ina zan saka kaina kenan, har ta sa sai hawaye ke kokarin kwarara da idanuwanta, ta rasa me ke mata dadi. Bilkisu kuwa ba babinda take yi sai kokarin taimakawa mahaifiyarta wurin ganin cewa ta dage sosai wurin wannan gudu na ceton rai, sai waigowa take yi tana sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki, idan sun yi kusa da su, ta sanar da ita, idan maan kama wata ko wani ta sanar da ita. A haka har aka kama da yawa daga cikinsu. Su kuwa sai gudu suke. Inda ubangiji ya cece su shi ne, da suka sami wani babban dutse suka haye. Ganin sun haye wannan babban dutsen sai ‘yan book haram din suka dakata da biyarsu din, suka fara zagayar dutsen domin su ga ko ba sojoji kan sa kafin su yi shawarar me kuma za su yi.



Sun jima suna zagayar dutsen, kafin babba daga cikinsu ya bayar da umarnin cewa su koma ainahin masaukinsu domin su ajiye wadannan da suka kama, su kuwa wadannan da ke kan dutse a zauna a tattauna a san yadda za a fatattke su har a kama su su shiga hannu. Nan take suka wakilta wasu daga cikinsu, suka kwashi wdanda aka kama din ya zuwa masauki. Saura suka tsaya suna shawara da karatun ta yadda za su bullowa wannan dutsen har su sami nasarar kama wadanda suka dare samansa.



Wadanda suka sami damar dare dutsen sun hada da Sajida da yaranta, sai mutuminnann mai bayar da labarin Nusaiba, da wasu mata guda biyu.



Dutsen akwai fadi a samansa sosai, yanada tayi kuma akwai wuyar hawa, sai dai idan ka sami hayewa gabadaya, za ka ga filinsa tamkar a kasa kake. Yana dauke da itace wadanda suka hada da Geza, Sabara, Anza da da sauran otace da galibi kan fito kan dutse. Iya kallonka ba abinda za ka iya hangowa face fili fallau har sai abin ya firgitar da kai.



Ba wani kyakkyawan shiri, duk da zazzabin Amisha ya tsananta, a haka ta shimfideta karkashin wani babban icen Kalgo, ta barta nan tareda Bilkisu da matannan guda biyu, ta kalli wannan mutumin, ta ce, “bawan Allah ya kamata ni da kai mu shiga wannan jeji mu gani ko za mu iya samun wuri mai saukin sauka kafin wadannan azzaluman su hawo, domin idan suka hawo tabbas kashinmu ya bushe, kan dutsenannan bana tunanin za mu iya tsira daga sharrinsu.” Gyada kai kawai ya yi, alamar gamsuwa, duk da cewa a ransa ba haka ya so ba. Dole ya bi ta suka fara zagayawa suna neman ta inda za su sauka kafin wadannan azzaluman su hawo ta kan dutsen. Aka bar su Bilkisu da fako, zuciyoyinsu kuwa kan bugawa kamar wadanda za su fito daga kirjinsu.



Sai tafiya suke, har suka dauki lokaci mai tsawo, ba inda suka ga dutsen ya kare ko alamar wurin da za a sauka, lamarin da ya kara tayar musu da hankali kenan, ganin sai kara nutsawa suke cikin jeji kuma kan dutse, sai mutumin ya bada shawarar cewa ya fi dacewa su koma, su dauko mutanensu ayi wannan tafiyar ta neman wurin sauka tare, musamman ganin duhu ya fara shigowa. Da farko ta so ta ki aminta da shawarar, sai daga baya ta aminta, suka juyo. Inda suka bar su, a nan suka tarar da su kuwa, hankulansu a tashe, Amisha kuwa kamar wacce ake karawa wutar zazzabi, jikinnnata ya kara zafi, ko motsi na dole kadai take iya yi, Bilkisu kuwa aikin kuka kadai take. Sai da suka yi mamaki ganin nama a kusa da sun a zomaye da bushiyoyi. Dalilin da ya sa Sajida ta tambaye su kenan, “wa ya kawo wannan?” cikin sanyin jiki, Bilkisu ta karba, “mu muka je muka nemo, ni da wannan” ta nuna daya daga cikinsu. Nan take suka gyara naman, suka hasa wuta suka ci. Bataayi mamakin hakan ba, saboda ta san yarinyarta tanada karfin zuciya, kuma tasan komai za ata iya aikatawa domin ta taimaki wasu, bare da yake ga kanwarta na neman taimako.



Bayan sun kammala cin naman, cen dare ya fara shigowa, suna tsakiyar taimama domin su sauke sallolin da ke kawunansu, sai suka fara jiwo sauti cikin Amsa Amo (loudspeaker) kamar haka; “kun nuna bajinta da har kuka iya tserewa mayakanmu, amma munaso ku san da cewa, wannan gudu naku, ba zai tseratar da ku daga hannunmu ba, saboda mun fi ku sanin jejinnan sosai, zai fi muku idan kuka sallama kawunanku, ba zamu cutar da ku ba, dama mu manufarmu mu dora kowa kan turbar Islama, a ajiye karantarwar yahudawa da nasara a rungumi sunna da Qur’ani, kar ku tsorata mu ba azzalumai ba ne, ba ma kisa, jihadi ne muke yi. Ku mika wuya, ba zaku cutu ba.”



Cike da mamaki suke kallon juna, inda zantukan sun ratsa daya daga cikin matn da ke wurin, har da cewa da su, “ya kamata mu gaggauta mika wuya tun da sun tabbatar muna da xewa ba za su cutar da mu ba, ya fi mu ci gaba da wannan gudun da sam ba tsira ko alamu tsira a cikinsa, ku kalla fa ku gani, wuni daya kenan ba wanda ya saka ruwa a cikinsa a cikinmu, mu kalla fa muga, wanka ba a ma zancensa, abinci a jiye zancensa shima, inaga mika wuya ne kawai mafita a garemu, kunji da kunnuwanku cewa ba za su cutar da mu ba, kuma kan daular musulunci suke gudanar da lamuransu”



Ta jima tana yi wa wannan matar kallon takaici, da jin kamar ta shara mata mari ko ta jefo mata asshar, amma sai ta hadiye, wasu hawaye masu zafi suka fara fito mata, muryarta na rawa ta kalle ta ta soma. “ke yanzu har za ki dauki zancen wadannan azzaluman? Idan da gaske suke yi ke da kike talaka kila ma bakida ilimin book, me ye hadinsu da ke da har za su shigo su dagulamaki rayuwa ta hanyar raba ki danginki da yaranki da mijinki, hakan ne taimako, kuma a naki tunni haka musulunci ya tanadar ko ya koyar? Wannan amsa amo da suka yi amfani da ita, in ce itama yahudawa da nasara suka kawo ta, domin a tarihi bamu taba jin cewa kakanninmu sun yi amfani da irinta ba wurin isar da sako, bindigogi da ke hannunsu, gaba daya na yahudawa da nasara ne. tau su da ke fada da abinda yahudawa da Nasara suka zo da shi, me ye kuma na amfani da kayan Yahudawa da nasara? Tabbas akwai lauje cikin nadi. Ba sa kisa suka ce, kinga tun nan sun nuna maki makaryata ne, domin shakka banayi, ba za su rasa yin kisa a gaban idanuwanki ba, kuma kisa na wadanda basu ji ba su gani ba, ga talaka mai kokarin neman abinda zai sakawa cikinsa, ya nemi inda zai dora awazarsa. Kada kdimewa da neman mafita ya sa ki manta zaluncin wadannan azzaluman ‘yar’uwa, ubangiji da ya je fo mu a wannan halin ba shakka bai manta da mu ba kuma zai nema muna mafita, ko nan kusa komai dadewa ko a duniya ko mu ji dadin mafitar a gobe kiyama. Wannan ita ce jarabawarmu, mu kafe kafafuwanmu, mu dage damtse, ba shakka mafita na kusa, ai duk abinda ya zamo daya, to kamar ya kare ne”



Ta yi ajiyar zuciya har kunya ta kamata, tareda fitar da hawaye. Suka gabata, suka yi sallah har da Bilkisu, sai suka ci gaba d tafiya domin neman inda za su sauka, su kuma ga ko za su sami fita daga wannan jeji, da kubuta daga hannun wadannna makiya Allah da ke biyarsu.


Ganin an dauki lokaci mai tsawo har dare ya fara rabawa, ba tareda ko daya daga cikinsu ya zo ya mika wuya ba, sai suka fara hawo dutsen da niyyar kama su ko su aikasu lahira, musamman saboda sun gindaya musu sharuda da basu damar sallama kawunansu, amma suka ki. Suka biyo su a fusace. Sun jima tsaye suna kokarin neman hanyar da suka bi, kasancewar duhu ya mamaye dutsen sosai, sai sanyi da ke dukan jikin mutum dauke da wani iska mai dadi. Suna tafiya har suka karaso inda suka ci abinci suka kuma yi sallah. Kallon wutar wurin ya tabbatar musu da tabbas sun jima da barin wurin, dalili da ya sa suka kara kaimi kenan wurin ganin sun cinmusu sun tsayar da su.


Su kuwa sai tafiya suke yi, duk inda suka ga alamunsaukar dutse sais u nufaci cen, amma har yanzu ba alamun ta inda z sui ya sauka, dole suka ci gaba da tafiya, har safiya ta waye. Tun fara tafiyarsu take goye da Amisha, inda sauran suke a gaba ita kuma tana ta baya. Dayar matar da suke tareda ita ce, ta nuna musu gaskiya ita ta gaji, kuma ba za tai ya ci gaba da tafiya ba. Jin haka suka yi tsaye suka yi rarrasarta ta nuna gaskiya ita ta gaji sai dai a yada zango a nan. Mutumin da ke tare da su ne, ya ce, “idan muka tsaya a nan, duk gudu da muka yi cikin wannan jejin za tashi a banza ne, domin inada tabbacin cewa yanzu haka suna biye da mu, zamnmu a nan kuwa dole za su riske mu, ina amfanin badi ba rai ke nan? An yi ba a yi ba kenan. Ki daure ki tashi, ki duba har da karamar yarinya da daure, muyi hakuri, su dai da ke son su zlunce mu suka jure wuya, sai mu da ke kokrin kubuta daga rayukanmu….”



Suka yi juyin duniyarnan da ita, ta ki aminta da ta tashi, suka ajiye akan za su bar tan an, suka wuce. Tafiya ta yi tafiya, ga zafin raina sai kara dukansu yake, ga yunwa na cinsu ta ciki, ga gajiya a tattare da su, amma ba mai alamun tsayawa ko nuna karaya.


Azzaluman kuwa sai tafiya suke kamar wadanda ake karawa karfi, kowannensu da mummunar niyya a zuciyarsa, yana hango irin kisa da wulakanci da z su yi wa wadannan da ke kokarin sakaa su wahala, a cikin wannan sunkurun jejin. Suka ci gaba da tafiya, suna yi suna fira da yin ba’a a tsakaninsu, har suka tarar da wannan da ta kasa tafiya, kwance a karkashin wani ice da ta kare kanta daga zafin rana.



Ganin sun zagaye ta, cikinta ya fara rura, gaba daya yawun bakinta ya kafe ta kasa motsi numfashi ma ba ta san ta ya yake fita daga huhunta ya zuwa karan hancinta ba, cikin kidimewa ta ce, “wallahi sun ganni..”



Suka zagaye ta, sai dariya suke yi, ita kuwa sai kuka take rusawa, tana so ta gudu, amma sai take ji kamar kunkunceta aka yi cikin manyan kacoci.




Me za su yi mata?

Mu hadu a shafi na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:56 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




1⃣8⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```






Never trust someone who lied to you more than twice bcz he won' change at all and will pass for a stupid girl.






*Shafin Masoya*



MATAR YAEESH FANS




***CI GABA***




Sai zagayar ta suke yi, suna yin wata dariya wacce ke kara jefata cikin tsoro da tashin hankali, ganin ta kidime sai shugabansu ya yi alama da hannu, cewar a kashe ta kawai, ya bayar da umarnin ne ganin cewa, idan suka ce su tafi da ita, za ta rage saurin da suke yi na kokarin cinma sauran, haka ba za su iya barinta da rayuwarta ba.


Nan wani ya gabata, ya caka mata wuka da ya zaro daga kugunsa, ya sake daga wukar ya caka mata, har sau uku, duk lokacin da ya caka mata wuka, sai ya juya wukar a cikinta domin ya katse hanjinta, karshe ya tunkudeta ta fadi a mace. Suka ci gaba da tafiya domin su tarar da sauran.


Su Sajida kuwa sai tafiya suke yi cikin matsananciyar zafin rana, ga yunwa ga jikinsu na wari, ga shi ba mai takalmi a kafa, kafafuwansu sun fashe, amma kamar ba su fashe ba, domin ba sa jin zafi ko zafin rana. Suka ci gaba da nutsawa cikin jeji har suka hango inda za a iya takawa a sauka daga kan wannan babban dutse, da suka share awanni suna tafiya a kai. Sai dai matsala daya, wurin da masifar hadari, wanda da zarar ka kalli wurin saukar za ka fara ganin jiri, musamman da za ka zaci wata rijiya ce za ka shiga mai gaba dubu, duk ba wannan ne tashin hankalin wurin saukar ba, irin yadda acen kasan yake da ciyawu da itace manya masu dauke da kaya, kamar su gumbi da sauransu. Wannan ya tayar musu da hankali.



Gaba daya suka tsaya bakin wurin suna kallon ikon Allah. Komai jarumtar mutum dole zuciyarsa ta karaya, dole ya firgita, saboda hadari da ke ga wannan wurin saukar, musamman da ga alama ba wanda ya taba sauka ta wurin bare, su bi hanyar da ake sauka, su ne zasu buda hanyar.



Ganin sun yi tsaye ba wani motsi, Sajida ta ja hannun Bilkisu, ga Amisha goye a bayanta, ta fara sauka.



Cike da mamaki, mutumin da ke bayan su sai kallonta yake yi yana girgiza kansa, a ransa yana cewa. “tabbas duk duniya ba wanda yakai uwa mace son yaranta, ji wannan masifar, amma a ko da yaushe yaranta take fara kallo, ita ba ta damu ba matsawar dai yaranta za su rayu” ya girgiaza kansa yana mai jinjina mata.



Ganin abinda mahaifiyarsu ke so ta aikata, na jan hannunta domin su sauka tare, Bilkisu ta kwace hannunta, ta ce, “kar ki damu Inna, ki kula da kanki kawai da kuma Amisha insha Allah zan iya sauka, ina daga bayanki, saboda ke ba zan bari na fadi ba. Ba da son ranta ba, dole ta bar ta, ita kuwa ta kara gyara goyon da ta yi wa Amisha, ta ci gaba da sauka. Ganin ta fara nisa, sai Bilkisu ta biyo bayan ta, suna sauka, suna amfai da rike itace da ke jikin dutsen gudun kada su subuce. Mutumin ya umarci dayan matar da ta bi bayan Bilkisu, cikin tsoro ta fara bi ta bayanta, jikinta sai rawa yake yi, da ya ga ta fara nisa sai shima ya biyo ta bayansu, a haka suka dinga saukowa daga kan wannan dutsen. Cen suna cikin sauka, sai matarnan ta subuce, ta fado, haka ta dinga gangarowa ta doki nan ta doki cen har ta fado kasa, amma tun a lokacin gangarowar rayuwarta ta fita daga gareta, gawarta kadai ta isa kasa. Cikin sauri Sajida ta kalli sama, a zatonta Bilkisu ce ta fado, duk da bataji dadin mutuwar wannan matar ba, hankalinta ya dan kwanta ganin ba ‘yarta ba ce ba ta fado. Ta jima tana kallon yadda Bilkisu ke kokarin saukowa kafin ita ma ta ci gaba da saukar.



Haka suka ci gaba da sauka, har suka dauki wani lokaci mai tsawo, kasancewar dutsen yanada tsawo sosai.



Masu biyarsu kuwa, haka suka ci gaba da biyarsu ta amfani da sawu da kuma alamun wucewarsu, ba wanda za ka kalla ya nuna alamun gajiya ko yunwa a tattare da shi sai tafiya suke yi, kamar wadanda aka karawa karfi da kaimi.



Sajida ta fara sauka, kafin Bilkisu ta karaso sai mutumin da ke tare da su. Har yanzu jikin Amisha da zafi, ga shi gaba daya yawun bakinta ya kafe, ba ta iya furta komai, ga yunwa ga ciwo, su kuwa ga yunwa ga gajiya a tattare da su.



Kallon tausayawa take yiwa ‘yarta ganin yadda jikinta ya fashe wurare da dama sai fitar da jini suke, sanadiyyar saukowa daga kan dutsen, amma ko a jikinta, ita ma ta nuna alamun cewa su ci gaba da tafiya, musamman da take ganin duhu ya fara shigowa.



Suka tada kawunansu sama suka kalli ta inda suka sauka, a ranta tana cewa. “lallai ubangiji yana yadda ya so, wannan wurin da mutum zai rantse cewa ya sauka ta nan, ba zan aminta ba, amma yau ni Sajida, ni ce na sauka a nan”



Suka ci gaba da tafiya ba tareda sanin ina za su nufa ba, su dai burinsu kawai su fita daga wannan jejin.



Su kuma suka ci gaba da biyo su har suka kawo ta inda suka sauka, cirko-cirko suka yi, suna kallon ikon Allah, suna kallo da tunanin ya aka yi har suka iya sauka ta wannan wurin. Duk da sun sha training kuma suna kokarin gwada training nasu a aikace, sai da suka karaya da tsorata wurin saukowa daga wannan dutsen. Sai kara tunzura suke yi da sakawa a ransu, matsawar suka kama su, to ba za su yi musu da sauki ba.



Suka fara saukowa daga kan wannan dutsen, wasunsu, dole suka fara saukowa duk da ba da son ransu ba ne. shugabansu shi ne a gaba, sauran na biye da shi, a haka suke amfani da itacen da ke kafe a jikin sutsen gudun kar su fado, suna sauka a hankali, duk da haka sai da mutum uku suka subuce suka fado a mace. Amma sauran ko a jikinsu. Suka ci gaba da saukowa.



Har suka sauko gaba daya, suka ci gaba da biyar sawunsu, wannan karon cikin gaggawa da sauri har da hadawa da gudu, tuni suka kunna fitillunsu masu masifar haske da nan take sukan makantar da wanda duk aka cinnawa haskensu a idanu. Sai sauri suke da zinmar cinma su Sajida.



Su kuwa sai tafiya suke, a gajiye, kawai dai suna yin tafiyar ne saboda ta zame musu dole, amma gaba daya sun yanke tsammani da za su tsira.



Tafiya ta yi tafiya, duk da sanyi na dare ya fara sauka amma gaba daya zufa ke ke fita daga jikinsu, a haka suka ci gaba da tafiya ba hutu, duk inda sua ga wani ice da suke tunani zai iya zama magani, sais u tsaya su diba, ta tattauna shi a harshenta, sai ta sakawa Amisha ruwan a baki, cikin ikon ubangiji kuwa sai ga shi ta fara samun sauki.



Ganin ta fara samun sauki, sai suka sami wuri suka yada zango, suka yi amfani da damar suka yi taimama suka yi sallah, suka dan huta na wasu mintuna kana suka ci gaba da tafiya wacce su karan kansu basusan ina za su dosa ba, kawai dai su fatansu su kubuta daga wadannan azzalumai su kuma fita daga wannan masifaffen jejin.




Su kuwa sai kara sauri suke yi, da nufin cinmusu, domin sunada yakinin cewa ba nesa suke da su ba, musamman da yake sunsan akwai mata da yara tare da su, dole su bukaci hutawa, domin a zatonsu sunada yawa sosai.



Cen dare ya raba tsakiya suka fara hango hasken fitilunsu, dalili da ya sa suka shiga sabon gudu kenan, duk gajiya da suke ji ta kau a lokaci daya, suka fara gudun ceton rayukansu, wurin yunkurawa Sajida ta fadi, dalili da yasa Amisha ta rafka kara kenan, ta fashe da kuka mai karfin sauti har sai da masu biyar su suka jiyo, ai ko suka hasko inda suke, suka tabbatar su ne. suka ce da wa aka hadamu idan ba da ku ba, suka nufato su a guje. Ba tareda jiran su tashi ba Mutumin da suke tare da shi ya ranta a na kare, Bilkisu kuwa ta tada mahaifiyarta suka dauki sabon gudu na ceton rai.




Karshen rayuwarsu kenan?
Duk wahalar da suka yi nan ne karshen rayuwarsu?
Za su tsere musu kuwa?
Me zai faru da su?



Duka amsoshinku suna cikin shafi na gaba.




DR. ZAIN
[2/3, 4:57 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




1⃣9⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_Be the first rate version of yourself and not the second version of someone else_ 💃





*Shafin Masoya*



*PEN WRITERS ASSOCIATION*

MAMAN ALEESHA
MAMAN SADIQ
NUSAIBATH
MEENERT FARUK
AMINA GUNABI
KHAUSAR M NASEER
YAR FATHER
AUNTY MUMMY
KAMAL NO LOVE
NORDEEN AMRABAT
NABILA DIKKO
ZAINAB USMAN
DIYUART YUSUF
SHAFA SALFAZ


***CI GABA***



Cikin rashin shiri suke gudu gashi tsakiyar dare ba sa ma gcanin inda suke dora kafafuwansu. Sai kitar jeji suke yi ba shiri, har suka cinma mutumin da ke tare da su suka wuce shi a guje. A duk lokacin da suka yi nisa da gudu sais u waigo su ga har yanzu biyarsu suke yi, su kuwa sais u kara gudu. A haka har suka cinma mutumin da ke bayansu, suka kama shi. Gani haka hankalin Sajida ya tashi matuka. Suna cikin gudu, sai kafafuwan Bilkisu suka shige cikin wasu ciyawu suka sarke, ta fadi, dalili da ya sa dole mahaifiyarta ta tsaya kenan domin ta tada ta, kafin ta sami tada ta, har sun zagaye su, ganin haka ta rungume yaranta tana fadar, “kuyi wa yarana rai, ni ku tafi da ni, amma don Allah kada ku cutar da marayun Allah”



Sai dariyar mugunta suke yi mata suna zagayar su. Cen sai babbansu ya karaso, aka yi masa hanya ya karaso ta kusa da ita, ya ce, “wannan ce ta wahalar da mu haka, tabbas yau karyarki ta kare, nag a yadda gudunki zai kubutar da ke daga hannunmu, tun farko mun baku damar mika wuyanku, da hakan ba ta faru d ku ba”



Ya bayar da umarnin a zo masa da su. Nan take aka daure hannayensu aka iza su kamar bayi, tareda mutumin da suka fara gudu, ana tafiya ana dukansu da bulala ana kuma izar su sai kace wasu bayi. Cikin mamaki taga babban nasu ya fiddo da wata waya, ya dora a kunne ya koma gefe bayan ya danna lambar da yake so ya kira, ya yi waya tad an lokaci kadan, saai ya dawo suka ci gaba da tafiya. Zuwa wayewar gari suka yada zango a wani katafaren fili mai yalwa sosai. Cike da mamaki tag a sun fito da abinci kalar wanda za a dafa kadai ko a siyo a shago, ko shago irin manyan shaguna, suka fara ci, suka basu suma suka ci, cen sai suka fara jiwo karar mashuna da mota. Ashe wayar da ya yi ya kira ne ya yi kwatancen inda suke, shi ne mutanensu suka karaso domin su wuce da su masauki.



Aka tura su cikin hilux ta baya, sauran suka shiga ta gaba, sai wasu suka hau Babura, suka buga ya zuwa masaukinsu, sai wakoki suke yi da kuwwace-kuwwace.



Sansanin wuri ne mai yawan gaske, wanda aka killace da wata gina da aka yi da laka, wacce ita ce aka yi wani gini da ita da zai ba wad an garin kariya daga masu kawo hari, haka duk wanda zai shiga garin dole tan an zai iya shiga, bayan masu fakon kofa sun aminta da ya shiga. Idan ka shigo harabara kallo dole za ka dinga mayarwa, boda yadda aka kawata wurin da gine-gine dole ka kira shi da kauye mai zaman kansa, ga mutane nan saai sha’aninsu suke yi ana kai da kawo, a ce karshen garin ma bowhole ne da ke bayar da ruwa a duk lokacin da aka bukata, wanda ake amfani da generator wurin ta yar da shi. Akwai dabbobi cikin garin kama daga shanu har

Please Login or Register in order to submit comment