Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin fakon asibiti, duk da tayi kwanan ne bayan da suka kammala sallar asuba, har rana ta fara fitowa kafin suka samu suka fito daga asibitin, sai godiya suke yi wa wannan nurse din kamar su yi mata sujada kan jin dadi, da suka fito daga sibitin sai suka biya wurin wata mai sayar da kosai kan hanya suka siya daga ragowar kudin da malama AISHA ta ba su, suka nufo gida.




QASIMU kuwa, da ya dawo da safe ya tarar da abinda ya faru da dakinsa, ya kuma tarar da matarsa tareda ‘ya’yansa ba sa nan, ya ce “kutumar uba! Wato shegiyar matarnan abin da za ta min ke nan? Wato idan ba na nan wurin maza take zuwa ta kwana? Ai ko za ta dawo ta same ni.”



Shigowarsu gidan, a hannun BILKISU leda ce dauke da kosai mai zafi, SAJIDA kuwa tana dauke da AMISHA, zumbur ya mike ya ce da ita, “gidan uwar wa kika fito?”





DR. ZAIN
[2/3, 4:40 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




🅾3⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```



_And in the end, it's not the years in your life that count. It's the life in your years._





*Shafin Masoya*

_Ummyn Yusrah_
_Star Nucy 360_
_80k_
_King boy Isah_
_Mlife_





***CI GABA***




Jikinta na rawa, ta mayar masa da amsa; “wallahi AMISHA ce ba lafiya, duka ruwan jiya a kanmu suka kare, shi ne muka fita cikin dare muka kai ta asibiti, domin duba lafiyarta, ka ga magunguna da aka rubuto likita ta ce a siya mata,” ta fada a dai dai lokacin da take kokarin nuna masa takardar maganin, AMISHA kuwa sai sharar barci take rike a kirjin mahaifiyarta.



“yimun shiru munafuka, dama ai ina ankare da ke, wato duk idan ba na nan fita yawon banza kike yi? Abin ma bai isa ki fita ke kadai ba, har sai kin tafi da yarana, lallai yau za ki ci ubanki”



“haba baban Bilki ya za ka je fe ni da wadannan munanan kalamai, ko halin diyarka ba za ka duba ba? Kalla fa yadda take faman cira da makyarkyata. Kuma idan lalaci zan je, da yara masu wayau zan fita? Me yasa ko da yaushe ba ka tsayawa ka dinga yi wa kanka adalci? Na san fadan da kake yi, duk bai wuce kokarin tserewa biyan kudin magani ba ne, kar ka damu, ni ban dora maka biyan kudin ba”.


“lallai SAJIDA hantsarki ta ja ruwa, wato ni nake magana kina mayarmun?” ya shareta da mari sai da ta fadi, tare da AMISHA, nan ta farka saboda jikinta ya doki kasa sosai. Ya bita da shuri, yana bugu a kasa, AMISHA kuwa sai faman rusa kuka take yi cikin radadi, sai da BILKISU ta yi sauri tazo ta dauke ta ta koma gefe, itama tana rusa kuka, haka ya daketa iya son ransa, ya kama hanya ya fita, ba tare da ya ko kula da me za su ci da safe ba.



Ba mai kokarin rarrasan wani daga cikinsu, a haka suka sha kukansu na wani lokaci, kana suka ci gaba da sabgar rayuwarsu, cen suna tsakiyar cin kosai da suka sayo daga kan hanya, sai ga muryar malama AISHA tana masu sallama, bayan da suka karba tare da yi mata marhaba, ta sami wuri ta zauna cikin sakin fuska, duk da ta so ta Ankara da damuwa da ke shimfide a fuskokinsu, amma a haka suke karfin halin boyewa, har da yi mata murmushi ita ma. Suka taya mata kosan, ta nuna musu ta ci abinci kafin ta fito, suka yi- suka yi ta ci ko kadan; amma ta kekasa kasa ta ki. Da suka kammala, ta sanar da su cewa ta zo ne domin ta nuna musu inda gidan nata yake, sai su saka ranar da za ta fara zuwa aikin. Ai ko nan suka yi cirko-cirko suna kallon juna ita da ‘yarta, lura da yanzu ta gama shan duka daga lusarin kidahumin mijinta da sam bai san darajar ‘ya mace ba. A zuciyarta ta yanke shawara, sai dai ya yanka ta, amma ba za ta fasa tura ‘yarta aikatau ba, domin ba za ta bari yunwa ta illata su ba, kuma ba za ta je yawon bara ba, haka ba ta da wani jari da za ta dinga juyawa, ba ta san lokacin da hawaye suka subuce mata ba. Malama Aisha ce ta ce; “subhanallah! Me ke faruwa malama SAJIDA naga kin fashe da kuka?” “ba komai, wani haki ne ya fadamin a idanu” “amma da mamaki, domin duka idanun naki biyu naga suna fitar da ruwa” “yawwa ku tashi muje sai ki nunamuna gidan naki” “to” kawai ta fada tare da mikewa.




Ba su zame ko ina ba si unguwar Danori, ta nuna musu gidanta inda take zama, daga ita sai ‘yarta FATIMA, mai kimanin shekaru sha biyar, wacce ke SS1 yanzu. Fatima fara ce kum gata da tsayi sosai, ba ta da jiki, wanda har ya sa ko shape ba za ka iya hango wa a jikinta ba, amma kirjinta cike yake da mama, duk da kananan shekarunta, tana gane karatu sosai a aji, haka tana mayar da hankali sosai a bangaren karatun addini, hakan ya sa ta zama mai ladabi da biyayya sosai a wurin mahaifiyarta, har ta kai ko kara mahaifiyarta ta ajiye, ba za ta tsallaka ba.



Shigarsu gidan, ita ta tarye su cikin murna na girmmawa, su BILKISU kam an sha kallon farfajiyar gida, domin ita ta dauka ko a turai ne take.



Tun daga kofar gidan, gida ne da ke dauke da ginin zamani, bayan electronic gate da yake da shi, aka sanya wata wire da ta zagaye wasu flowers na roba, wadanda ke fitar da launuka daban-daban na haske, a tsakiyar flowers din kuwa da suka zama kamar carpet a wurin, manyan itace ne na giginya, suma duka na roba ne, da kuma kalar nasu haske daban, shi yasa yara ke misalta gidan da Gidan Haske. Daga shigowarka gidan kuwa, ko mai gadi babu, kasancewar gate din da remote yake aiki, haka za kaayi tafiyar sama da minti talatin idan da kafa ne kafin ka iso harabar inda mutane suke, a gefe, parking space ne, sai dayan gefen da ke dauke da natural grass carpet, wanda masu bashi ruwa daban, nan FATIMA ke wasa da abokaninta, idan ka wuce wannan play ground, za ka zo ne inda aka zagaye kamar lambu, shuke-shuke kala-kala, su guava, lemu, mango da dai sauransu, shi yasa wurin a ko da yaushe dauke yake da sanyi, sai kuma kujeru da aka jera a tsakiyar itacen, inda ake shakatawa, daga nana kwai wani floor da aka yi wanda ta shi za ka iya shiga ainihin gidan, ta babban parlour da sauran dakuna.


Sai ta ce da su “kunga gidana, kuma nan nake so diyarki ta dinga yin aiki, saboda na yaba da hankalinta, kuma na yarda da tarbiyyarta”


“Ba abin da za mu ce maki sai dai godiya, ubangiji Allah ya biyaki, ke kuma BILKISU, kar naji ko nagani kin yi rshin kunya gareta, yi nayi bari na bari, duk yadda kikasan kina bani girma, ita ma haka nake so ki girmama ta”


“insha Allahu inna, zan kiyaye”



“game da tahowarta, kullum, driver zai dinga daukota kuma shi zai dinga mayar da ita”


“Muna godiya”


A nan suka ci abincin rana, bayan sun sha kallo a TV suka dawo gida.


Sai dai aka yi rashin sa’a, domin kuwa QASIMU, ya fi awa daya da dawowa daga yawonsa na banza, da sunan yunwa yake ji, ya dawo gida ne domin ya ci abinci.




Har yanzu labari bai fara ba



DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




🅾4⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_The world is moving so fast these days that the man who says it can't be done is generally interrupted by someone doing it_








*Shafin Masoya*


_Feenah Baby_
_Maryam Adamu_
_Maryam Mrs Isma'il_
_Khadija Muhammad Wani_
_Firdausi Feedo_






***Ci gaba***





“dama ai nasan taurinn kanki, ba zai bari ki yi mani biyayya ba, wato a duk lokacin da na fita, sai ki dauki, la’antattun kafafuwanki kema ki fita iskancinki ko? Don ubanki, zo yau sai kin gayamani, gidan uban da kika fito” ya fada a dai dai lokacin da yake kokarin zare belt daga dan zugaggen kunkurunsa. Ganin haka jikinta ya kwashi bari, domin ta san muddin belt dinnan ya fito daga gidansa, ba zai koma ba har sai jikinta ya yi jina-jina. BILIKISU kuwa tuni ta fara kuka, domin tasan yau ba mahaifiyar tata kadai ba, har ita sai tayi gashin bai da ruwan zafi.





“don tsabar iskanci ina maki magana, kina wani kallona kamar wata saliha, na ce gidan uban wa kika fito?” ya fada yana zare idanu.





Jiki na rawa, ta ba shi amsa. “dama jikin AMISHA ne ya yi, tsanani, shi ne muka koma domin a duba lafiyarta”




“da izinin wa kika fita?”




“naga ba ka kusa ne, kuma wannan abu ne da ya shafi, lafiyar diyarmu, shi ne naga ya dace na kaita”




“oh! Wato kina so ki nunamin cewa ni bansan daraja ko hakkin ‘ya’yana ba kenan, ke ce wacce tasan darajar ‘ya’ya? Dakata! Ba ma wannan ba, ina abin da kika dafa yau, ni yunwa nake ji”




“sai da tayi shirun kusan minti daya, sai sake-sake take yi ranta, yawu ma idan ta yi yunkurin hadiyewa, a haka suke subuce mata, ta kalle shi ta ce; “gidannan mun fi wata shida rabonka da ka kawo mana ko magi, kuma duk sana’a da na dauko, kai ke cinye jarin, duba ka gani, kalli ‘ya’yanka, ko yara da ba sa da uba, ba za su wulakantu kamar yadda ka bar ‘ya’yanka ba, na ji ni ba ka so na, ban damu ba, domin saninka ne nima tilstani aka yi, amma tunda har ka ji har ka iya haihuwa da ni, ai ya kamata ka kula da yaranka…” saukar belt kawai ta ji a tsakiyar kanta, kfin ta maido da hanklinta ya dora mata duka a bai, sai dukan ta yake da belt, kasancewar belt din da karfe a jikinsa, ya farfasa mata jiki, sai kuka take yi, shi kuma sai zaginta yake yana rusa ashar. Shi ne bai barta ba, har sai da ya ga ba ta motsi, ya dawo kan BILKISU ya zabgamata belt, ganin zai illatata tayi makota a guje, ko da ta fita ta tarar da mutane sun taru, amma sai shakka suke na shiga gidan, domin kuwa sun san matsawar suka shiga fadan zai dawo a kawunansu. Haka ta ratsa cikin taron jama’a da ke wurin a gigice tana rusa kuka tareda sosa wurare da ya zabgamata belt. Nan ta fara fadin “ya kashe mamarmu…” jin haka jama’ar da ke wurin suka runtuma cikin gidan, ai ko suka tarar da ita a kwance ba ta ko motsi, a dayan gefe kuwa, AMISHA ce sai faman zabgar kuka take yi, daga cikin wadanda suka shigo gida, akwai maza da mata, sai wata mace ta yi kanta domin ta tabbata ko mutuwa ta yi, shi kuwa QASIM sai fadar yake “wa ya kawo ku cikin gidana, wallahi ko mutum ya fita, ko na illata shi” jin haka, wani saurayi majiyi karfi, ya tinkaro shi ya fara shar mashi mari, yana cewa, “idan iskanci kake takama da shi, saninka ne mu munfika, idan kuwa hauka ce a kanka, to wallahi mune maganinka..” ya ci gaba da dukansa, sai da mutane suka rike shi. Sai fadar ke bar shi ya koyamasa hankali. Matar da ta je duba SAJIDA ta tabbatar da ba ta mutu ba, nan suka zuba mata ruwa, zuwa wani lokaci ta farfado, tare da jan wata doguwar sheda.




Wata mata ta ce da ita; “wai ke me kike ciki ne da ba za ki rabu da wannan mahaukacin ba, ke fa kyakkyawa ce, amma ji yadda kika lalace, kalli ‘ya’yanki ki gani, ba tarbiyya kadai ba, har ilimi rasawa za su yi, gaskiya ki sake tunani”




Inda wasu na tausaya mata, wasu kuma suna yi mata fada, a haka dai suka barta, shi kuwa gogannaka tuni ya fita kan kunyar duka da ya sha daga saurayin unguwwa.




Tsawon lokaci tana sharar kuka, tare da jinyar rauni da miki da mahaukacin mijinta ya mata. Tana cikin kuka ta jiyo sallamar wasu maza a bakin kofar gida, wanda ya sa ta share hawayen da ke riganganiyar kwarara daga idanuwanta, cikin sifar tausayi ta kalli, BILKISU da ke gefenta itama tana sharar kukan. Ta dauko tilon hijabin da suke bani-bani ita da diyrta. Ta suri takalmi da sun fi shekaru shida har sun sude kan dadewa, kuma kafar daban-daban, ta fita domin ganin su waye a kofa. Isar ta sai ta ga wasu ne daga unguwar tasu, wasunsu ma ta san su sosai, bayan sun gaisa da ita, suka shaida mata cewa, sun zo ne domin su gyara mata rufin dakinta da iska ya dauke. Saninta ne wannan ba karamin tashin hankali ba ne idan QASIMU ya dawo, domin ba shakka ba zai rasa bin da zai fada ba, ga wannan gyaran. Amma a haka ta ba su dama su shigo suyi aikin musamman da suka sanar da ita cewa, taimako ne daga kungiyar unguwar, dam sukan taimakawa duk wanda irin haka ta faru da shi. A ranta tan cewa, sai dai duk abin da zai faru ya faru, amma ba zan bari diyana su wulakanta cikin zafin rana, ko ruwan sama ba, musanmamn da yake yanzu lokacin damina ne, ga masifar zafi ga shi ko da yaushe ruwan sama zai iya sauka.




Suka fara shigowa da kayan aiki, suka kawo langa-lang (kwano) suka jibge katakai da kusoshi, wasunsu rike da hammer wasu rike da bar ta cirewa ko gyaran kusa, da dai sauran kayan aiki, su da yawa ne shi ya sa suka kammala aikin cikin lokaci kankane, ai ko nan ta dinga yi musu godiya kamar za ta rusuna.




Bayan sun wuce, cike da murna suka gyara dakin nasu ita da BILKISU, inda AMISHA take shimfide kan tabarma tana sharar barci, duk da jikinnnata har yanzu da alama zazzabi. Da suka kammala, ta aiki BILKISU domin ta yo masu cefane, kasancewar sun samo kudi daga gidan Malama Aisha. Da ta dawo suka dora abinci, tuwon dawa da miyar kuka.
(ayi hakuri, wanan layin missing up ne, amma a hakan ma zai karantu)



Ai ko cikin gudu da murna ta je ta siyo abubuwan da aka aiketa ta siyo.



Sai murna suke yi ita da ‘ya’yanta ganin yadda aka gyara musu dakinsu har rufin nashi ya dawo sabo. Suna cikin murna sai ga sallamar driver ya zo daukar BILKISU, nan suka yi sallma da mahaifiyaarta ta tafi.




Wucewarta da kamar mintuna hamsin sai ga QASIMU ya dawo, kallo daya za ka masa kasan cewa yana cikin magagi na maye, tafiyarsa kadai ma ta isa ta fassara haka. Daga shigowarsa, ya ce; “ina yarannan suke ne, ki fiddomin da su, akwai wani dan siyasa da ya yi sanarwa cewa, duk wanda yake da ‘ya’ya marayu, ya kawo su a gani, za a dinga daukarsu zuwa kasashe domin su dinga yin aiki, sai a dinga biyan mahaifinsu ko mahifiyarsu wasu kudade, kinga dama ce muka samu ta mallakar kudi, ko ba komai wannan talaucin nasan ya ishe ki….” “tabbas ban taba sanin baka da hankali ba sai yanzu, shekaru nawa muke cikin talauci da ukuba da kangi, sau nawa a rayuwarka ka taba tunanin kawo muna dauki ta hanyar da ya dace sai yanzu da ka ji wai kudi za ka samu? Wato duk abinda kai ba za ka amfana ba, ba za ka yi shi ba? Tau ka karkade kunnuwanka da kyau ka ji; kyaleka da nake yi, ba wai tsoronka nake ji ba, ina kyaleka ne saboda kai shugaba ne a kaina, tunda ka kasa fahimtar haka, inaso kasan cewa ni ba lusara ba ce, da zan mika wa ‘yan siyasa ‘ya’yana ba, wadanda ko kadan ba sa tausayin talaka, wannan da kake gani, suna amfani da ku ne domin su cinma burinsu, kodai ta hanyar yin tsafi da ‘ya’yanku, ko su sayar da su hannun kafurai arna a kashashen waje a dinga zina da su ko ayi tsafi da su. Talauci ai ba hauka ba ne, wallahi idan har ka ga ka dauki daya daga cikin ‘ya’yana, sai idan kashe ni ka yi”




Har ya so ya tada fada, ganin yadda ta cije, dole ya hakura, har zai fita, sai ya kyalla idanuwansa ya hango rufi da aka yi musu. Sai ya kada baki ya ce;



Har yanzu lbarin bai fara ba



08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾



🅾5⃣




Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_Remembering that you are going to die is the best way I know to avoid the trap of thinking you have something to lose._




*Shafin Masoya*


_Banida baki da zan yi wa masoyana da kuma mabiya wannan littafin godiya, ina alfahari da ku duk inda kuke haka ina yabawa hadi da godiya kan addu'o'i da fatan alkhairi data gareku. Allah ya bar mu tare._




***CI GABA***




“ina kika samo kudin gyaran wannan rufin?”



“ba ni na gyara ba, dama a unguwa akwai kungiya ta taimakon kai-da-kai, su ne suka tausaya wa halin da yarana suke ciki, suka zo suka yi mana wannan gyaran”




“sun baku wasu kudade ne?”



Cikin ranta ta yi wani bahagon murmushi mai dauke da takaici, a ranta tana ewa, ba shakka, duk wanda Allah ya jarabta da auren miji jahili wanda bai san me ake kira hakkin aure ba, yana cikin damuwa, wato shi ba ya da tunani idan ba a bashi kudi ya salwantar ba? Sai tace “a a! ba su bamu ko sisi ba.”




Ya rafka tsaki ya wuce, har da gunaguninsa.




BILKISU kuwa, bayan an gabartar da ita ga sauran ma’aikatan gidan, tun daga masu baiwa flowers ruwa, har masu aikin girki da sauransu, sai kuma aka nunamata gidan da kuma inda za ta yi aiki, wato goge-goge na bangaren FATIMA, hakan yasa aka kawota wurin FATIMA domin su ga juna.




BILKISU wankan tarwada ce, irin yarannan ne masu tsayi sosai, amma ita tana dan da kaurin jiki, gata da tsawon gashi, sosai ta biyo mahaifiyartaa a fuska, amma ta dara mahaifiyarta kyawu nesa, tanada dogon hanci ga dan tsukakken baki, sai dai muryarta ba siririya bace, tana dan da kauri, idanuwanta ba farare ne gaba daya ba, sunada ratsin ja, ko saboda yawan kuka da take yi ne oho! Tana dan da sauri wurin magana, sai dai akwai kaifin tunani da saurin fahimtar abu ko karatu.




Da sukaa ga juna, ta tsunduma aiki, ita kuwa FATIMA ba abin da take yi illa assignment da aka basu aji, tana assignment din tana satar kallon BILKISU ita ma din dai satar kallonta take yi.




Da ta kammala aikin sai ta kirata suka zauna suka fara fira, a cikin firar ne take tambayar ta wacce makaranta take, inda ta sanar da ita, cewa tun kammala JSS3 nata karatunta ya tsaya, kasancewar dama mahaifiyarta ce ke daukan nauyin katun nata, ga shi kuma mahaifiyar yanzu ba jari ko kudin da za ta kula da karatunta.



“yanzu idan za a saka ki makaranta za ki koma”



Bayan ta saki murmushi, na jin dadi ta amsa “sosai kuwa, banida buri irin in yi karatu mai zurfi har na zama lawyer, idan har na sami damar komawa makarannta ba karamin farin ciki zan yi ba”




Itama sai da ta saki nata murushin sai ta ce da ita, “kya iya tafiya, naga ba sauran aiki”



Ta je dakin Malama AISHA ta tarar da ita sai karatun Jarida take yi, ta shaida mata cewa ta kammala har FATIMA ta sallameta, za ta koma gida ne, “haba BILKISU komawa gida tun yanzu? Sai ka ce wacce ake kora, ba za ki tsaya kiyi wasa ba?” shirun da tayi kanta a sunkuye shi ya nunawa malama AISHA cewa hankalinta yana gida, sai ta jawo hannunta, ta zaunar da ita parlour ta shiga ta dauko mata abinci dafaffe da kuma kayan abinci wadanda ba a dafa ba, tace, kuci wannan, wannan kuma ku dinga dafawa, a kai-a-kai. Ta kira driver ya dauki kayan ya kai su a mota, suka tafi.



Da gudu ta karasa cikin gida tare da rungueme mahaifiyarta, da ke zaune kan wata tsohuwar tabarma da gaba daya ta side, tana yi wa AMISHA wasa. “kar ki ballamin kafa! Gara ke da sauran kuruciyarki” “wallahi inna dadi nake ji, kinga yadda suke son jama’a kuwa? Ni inda ma cen ne gidanmu, wallahi da na ji dadi…” “kowanne rai da kike gani BILKISU yanada kaddara da ubangiji ya dora a kansa, wayonsa ko dabararsa duk ba za su yi tasiri kan tsarin ubangiji ba, ko ai mu din ba mantawa da mu ya yi ba, kuma bamusan me ya tsara a kanmu nan gaba ba” “ba rashin godiya nake yi ba, kawai ina nuna farin cikina ne”



A dai dai lokacin ne driver ya fraa shigowa da kaya cikin gida, wanda ya sa BILKISU ta mike zumbur domin gaba daya ta manta cewa tare da driver suka zo. Bayan sun saka kayan gaba daya cikin gida, suka yi sallamaa da shi ya wuce.




FATIMA kuwa; daga fitar Bilkisu kai tsaye ta nufi dakin mahaifiyarta, inda ta tarar da ita zaune a parlour tana kallon tashar MANARA TV, cikin nutsuwa ta mayar da hankalinta ya zuwa ga ‘yarta, saboda jin irin sallamar da ta yi, tasan da magana a tafe da ita.



Cikin sakin fuska a kalleta ta ce, “kar dai kice har kin kammala assignment da naga kina rubutwa?” bayan ta saki murmushi, ta ce “na jima da kammalawa” “sannu agogo sarkin aiki, wasu lokuta sai ki dinga tunamin da mahaifinki, shima lokacin yana raye, ba ya wasa da aiki ko kadan, kinzo ki tayani kallo ne, duk da nasan ba son tashoshin da ake yin wa’azi kike yi ba” “a a! ba kallo na zo taya ki ba, nazo ne muyi wata magana” “inajinki, me ke tafe da ke?” “dama kan BILKISU ne, kinga tana da kuruciya har yanzu, kuma da lokaci, me zai hana ki sakata makaranta, ko ba komai taimako ne kuma ga alama z ata yi ambition mai kyau, saboda na dan tattuna da ita, har ta nunamin mastalolin da suka hana karatunta ya ci gaba, kinga mu da ubangiji ya yi wa budi, hakkinmu ne mu taimakamata tunda munada ikon yin hakan” tayi ajiyar zuciyaa na wasu lokuta kana ta kalli diyarta da ke zaune daga kasan kujera kusa da kafafuwanta, inda ita kuma take kan kujerar, sai ta shafo kanta cikin murmushi, hawaye suka zubo mata a lallaausan kumatunta, a ranta tana tunawa da kokarin kwatanta halayyar wannan yarinyar da ta mahaifinta, ga tausayi da son taimakon talaka. Sai ta ce da ita. “kar ki damu, dama ai saboda irin wadannan ne ubangiji ya wakilta mu akan wannnan dukiyar, kuma da ikon Allah zamu taimaka mata, zan je gidansu ajuma, in yaso da safe idan mahaifiyarta ta amince sai na je naga principal naku muyi magana, tunda kinga yanzu har kun dauki sati biyu da komawa, zan kokaarta nagani ko zasu yimaani wannan alfarmar” “nagode Mama” “ai ni ya kamata namaki godiya, ni da kika kawowa aikin lada har a daki”.






08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:43 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




🅾6⃣




Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_




dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```




_I learned that courage was not the absence of fear, but the triumph over it. The brave man is not he who does not feel afraid, but he who conquers that fear._





*Shafin Masoya*



_Tabbas ba zan iya mika dokacin godiyata ba gareku masoyana da mabiya wannan littafin,

Please Login or Register in order to submit comment