Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kauyuka shida ke kawo yaransu karatu, amma malami daya ke karantar da su, gayamin injimi ne da zai iya ba su ilimi yadda ya kamata? Ko kiga malami yana zaune yana jiran wai sai yara sun dawo daga jeji kafin su zo makaranta, haka har lokaci ya kure. Ko kiga malami shi karn kansa yana bukatar a ilmantar da shi, amma shi ne wai headmaster. Gayamin yadda zasu iya samun ilimi? Bangaren addini kuwa sai dai mu dora hannu a ka muce ‘innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ domin yadda kauyuka ke tura yaransu almajiranci kana dubawa kasan da lauje cikin nadi.”




“lauje cikin nadi fa?” Mustapha ya fada yana mai kallonta cike da daukin jin me za ta fada.




“Eh! Lauje cikin nadi kuwa” ta fada tana mai kara gyara zama. “ ka duba ka ga, galibi lokutan da ake tura yara almajiranci, lokaci ne da aka girbe albarkar abinci bayan damina, sai su tura yaran da sunan karatu saboda kar yaran su ci abincin da suka noma, idan lokacin noma kuma ya yi, sai kaga yaran sun koma gida wasu domin taya iyayen aikin jeji. Ka kalli yara da ake turowa, wasu shekaru uku wasu hudu, haba gayamin yadda yaro da ba ya da kwanciyar hankali abinci ma ba ya da tun tashinsa da safe hankalinsa na wurin me zai ci yau, ina zai sami abinda zai sakawa cikinsa. Yaro kankani da wurin barci ma ba ya da sukuni saboda zasu haura su dari suna kwance a wuri daya, ga rashin wanka, cututuka su biyo baya, ga haduwa da marasa tarbiyya tun suna kanani. Gayamin yadda malami kwaya daya zai iya ba wa yara sama da dari biyu tarbiyya. Duk ba nan gizo ke sakan ba, wasu ta nan ne ake lalata su, wasu su koyi shaye-shaye wasu su koyi fashi da sauran ta’addanci. Ki kalli yanayi na karatu da kuke yi ku da kuke a gaban iyayenku, sai ku kwashi ilimi har ku sauke alkur’ani, su kuwa su dauki shekaru ko baki basa iya tadawa.”




Bilkisu ta nisa ta kalli mahaifiyarta, ta ce, “tabbas inna haka ne, amma fa gwannati nada laifi”




“mamanne ke nan, gwannati bazata rasa laifi ba, amma kina sane da kashi 99 laifin iyayenne, ai ba hakkin gwannati ba ne kula da tarbiyyar yara, nata hakki ta bayar da hanyoyin inganta rayuwa da tsaro da walwalar al’umma. Laifinta anan shi ne; ta kasa tsayawa ta inganta makarantun tsangaya na almajirai, ta dauki malamai ta dinga biyansu, su kuma su dinga karantar da yaran a kuma hana su yawon bara, domin wannan yana kada kimar musulunci a idanun kafirai”





“Alla dai ya yi muna jagora” Mustapha ya fada.




Suka ci gaba da fira da kuma tattaunawa kan matsalolin ilimi, cen suna tsakiyar fira,sai ga wai mutum yazo kusa da su. Kafin ya karaso sai Mustapha ya ce da su. “ga limamin gari nan tafe…”




“y aka yi kasan shi ne liman?”




“kun manta a masallacin na yi salla?”




Yana karasowa sai ya yi musu sallama, suka amsa. Sai ya soma. “hal yastadi’u ahadukum attakallumu fil arbiyyah” (ko da wanda ke iya magana da larabci a cikinku?) cike da jin dadi kamar wacce za ta tashi sama, Sajida ta girgiza kai ta ce “na’am! Kai fa anta, wa kaifal umur” (eh! Muna jin larabci, ya kake ya lamura) “ bi khairin. Ra’aitu hazassabiyu yatakallamu ba’ada an tahaina minasswala, ka’annahu yuridu an ya kula lana shai’un muhinmun, fahimtu zalika hina baka lamma ra’ana la nafhamu luggatallazi yatakallamu bih” (da alkhairi, naga yaronnan yana zance cikin masallaci bayan da muka kammala sallah, kamar yana so ya sanar da mu wani abu mai muhinmanci, na fahimci hakan en, lokacin da ya fashe da kuka da ya fahimci ba ma jin yarensa)




Sajida ta kalli Bilkisu da Mustapha, hawaye suka cika idanuwanta, ta kalli liman, ta sunkuyar da kanta kasa, sai ta ce “na’am ya imamu, ladaina khabarun, walakinnahu dawilun jiddan, walaisa ladainal waktul aan, la khabarnahu laka, walakinnal aan nu ridu musa’adataka an turshidana ila dariki ayyi baladin allazi arafta iza ataina bihi sa najidu assayyarah ila baldati Kebbi. Asaabatna musibati Boko Haram, madaina ayyaman narkudu wa nabta’idu anhum, hatta ataina ila baldikum haza. Sa’idna” (Eh! Imamu munada labari, amma yanada tsawo sosai, ga shi bamuda lokaci, da mun labartamaka shi, amma yanzu muna bukatar taimakonka, ka dora mu kan hanyar duk garin da ka san cewa idan muka tafi cen zamu sami mota da za ta dauke mu zuwa jahar Kebbi. Musibar Boko Haram ta far muna, munduki kwanaki muna gudu muna kokarin nisanta daga garesu, har muka karaso wannan gari naku. Ka taimakemu)




Ya kalle su cike da tausayi sai ya ce, “antumul aan duyufulliy, wala yumkuni li an utrikakum fi hazihillaila, indalikuu ma’iya ila baiti” ya fada a dai-dai lokacin da yake kokarin juyawa. (ku bakina ne a yanzu, bazai yiwu gareni ba na bar ku ku tafi cikin wannan daren ba, ku biyoni muje gidana)




Suka biyo ta bayanshi, suna tafiya yana yi musu tambayoyi suna bashi amsa. Duka da larabci, har suka karaso bakin wani gida wanda ba ya da kyaure, amma a zagaye yake da gini na laka, wanda aka yiwa babbar kofa, sai ta ciki da dauke da kofa uku, na matan aure sai bangaren rahegu da kuma inda ake bayawa a yi wanka. A dayan bangare kuwa wurin turke dabbobi ne, ya cika da awaki da tumaki, sai shanun noma guda biyu da jaki kwaya daya. Ya yi saallama, aka amsa sai suka shiga daga ciki, ya kira matansa guda uku, ya gabatar da su Sajida gare su, ai ko nan suka tausaya musu, sai kallonssu suke yi cike da mamaki. Tabbas kallo kadai idan ka yi zuwa ga su Sajida dole kaji tausayi ya ratsa ka. Aka shimfida musu tabarma, cen bakin dakin amarya, aka kawo musu tuwon gero (tuwon hatsi) da kunu, miyar batso aka kawo musu wacce ta ji man shanu, har yana dukan hancin mutum. Suka ci suka sha, suka bige da fira, bayan imamu ya ja Mustapha ya nuna masa inda zai kwana. Tun da subahin suka fita sallah, da aka iyar da sallah, suka dawo gida, imamu ya shirya kayansa na zuwa jeji, sai ya dawo gun Mustapha ya ce su je su yi wanka, zasu tafi ne wurin mai gari, suka yi wanka, aka kawo musu kari, da yake lokacin rana har ta fito. Suka ci, sauka dugunzuma ya zuwa wurin mai gari.





Da suka zo sai liman ya gabatar da su ya kuma sanar wa maigari da labarin da suka bashi kan kansu. Cike da mamaki, mai gari ke kallonsu. Ya tausaya musu, daga bisani, ya hada su da wasu dogarawa nashi, saman jaki domin su rakaye su gari na gaba. Haka suka ci gaba da tafiya tareda wadannan dogarawan, har suka karaso gari na gaba, aka yi sa’a a garin akwai masu Babura, kai tsaye gidan maigarin garin suka isa da su, suka mika masa takarda daga maigarin garin da suka fito, bayan an karanta, ya hada su da masu Babura domin su kai su babban birni.




Wannan wane birni ne zasu isa?






DR. ZAIN



[2/3, 5:05 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾




3⃣1⃣




Na




*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```





_komai kake gani da lokacinsa_








*Shafin Masoya*



Equity FM




***CI GABA***





Suka ci gaba da tafiya kan Babura har suka karaso garin Biu. Suka ajiye su a nan, suka koma kauyensu, su kuwa suka nemi mota domin ta kai su gari na gaba, da ya ke a garin da suka fito ambasu gudunmawa ta kudi da zasu yi guzuri da su, hakan batasa Sajida ta manta da kudi da ta debo ba daga garin da ta kashe shugaban boko haram da kuma kudin sadakinta da ke a leda a jikinta.


Shiga wannan garin fita wancen, har ubangiji ya kado su a garin Adamawa a unguwar Dandu. Ganin maraice ya karaso ta ja yaranta ta nufi guest inn da ke kusa da su ta kama musu kudin daki biyu, shi Mustapha ta kama masa daya, inda ta kamawa kanta da Bilkisu daya, suka yi wanka, kasancewar tufafin jikinsu su kadai ne suke da, dole su suka mayar a jikinsu, hakan ta sa dole da aka kammala sallar Isha suka fito neman tufafi da zasu saka a jikinsu. Suka nufi wani babban shagon sayar da kaya da ke unguwar AT unit. Suka siyo kaya kala biyu-biyu da zasu dan yi amfani da su. Suka dawo masaukinsu.



Sun jima a dakin da su Sajida suke, sai fira suke yi, da kokarin zantawa kan abubuwa da suka faru da su a jeji. Budar bakin Bilkisu sai cewa ta yi, “Inna me ya sa bamu gabatar da kawunanmu gun sarki ba ko wasu masu fada aji a gwannati? Na tabbata da bazamu kashe kudi haka ba, kuma hankalinmu zai fi kwanciya”



“bamusan tsarin garinnan ba, kuma da uwar maraice zamu sallamawa sarki ko gwamnati? Sai ma mu tafi a karyata mu ko a dinga yimuna kallon mabarata, tunda alhamdulillahi munada ‘yan kudi a jikinmu, kuma na tabbata ko ina ne a kasarnan zasu dauke mu su kaimu, ai gara mu tsara abu yadda mu mukaga ya yi mana dai-dai. Banida niyyar komawa Maiduguri, garinmu Kebbi zan je a garinmu na Kalgo wurin iyaye na. ko ba komai a cen za ki sami gata da bakisamu ba tun haihuwarki.”




Jin haka, Bilkisu ta waigo ta kalli Mustapha da tun lokacin da Sajida ta fara magana ya yi shiru, sai ta ce, “ya zamuyi da Mustapha? Na tabbata bazai so ya rabu da iyayensa ba.”




“haka ne, kuma ba wanda zai raba shi da iyayensa.”



Ta kalli Mustapha ta ce da shi, “kanada lambar mahaifinka ko mahaifiyarka?”



“eh! Inada lambobin duka daga cikinsu” ya fada.



“shi kenan, je dakinka ka kwanta” ta fada a dai dai lokacin da take kokarin mikewa daga kan gado da take zaune.



Ya tashi jiki ba karfi ya wuce dakinsa, inda su kuma suka rufe nasu dakin suka fara kuka na rashin Amisha da suka yi.




*MAIDUGURI*



Haka malama Aisha ta ci gaba da zuwa neman Sajida da yaranta a duk unguwa da ta ji cewar an ga wasu *‘yan gudun hijira* haka kullum kunnuwanta na kan redio idanuwanta kuna na kan talabijin kullum, ko Allah zai sa ta jiwo labarin inda Sajida da yaranta suke. Amma ba su ba labarinsu, ta kai sanarwa gidajen redio da talabijin amma kamar an shuka dusa. Hakan ta sa, sai dais u nemi wuri ita da ‘yarta Fatima su darji kuka son ransu.




Iyayen Mustapha kuwa, tun batan Mustapha da kakarsa, suka shiga tashin hankali, da har abin ya zamewa mahaifinsa kamar hauka, domin sai kaga shi kadai yana sambatu marasa ma’ana. Dole sai da aka tashi tsaye da neman magani kafin ya fara dawowa hayyacinsa. Kullum cikin mikin rashin dansu suke.




*ADAMAWA*



Haka suka kwana cikin bakin ciki da bacin rai duk da sanyin AC da ke dukan jikinsu, Mustapha a farke ya kwana har aka fara kiran sallah a kunnuwansa. Da suka kammala sallah, har ta fara lazimi, barci ya kwasheta, haka Bilkisu, kamar hadin baki shima Mustapha barcin yake yi, sune ba su farka ba sai zuwa sha dayan rana, suka shiga suka watsa ruwa, ganin Mustapha bai zo ba, ta tabbatar mata da lallai, barcin ne bai sake shi ba, ganin haka sai ta je ta tada shi, ta umarce shi da ya je ya yi wanka domin fita zasuyi. Suka dawo nasu dakin suka jira shi, da ya kammala wanka ya zo ya same su, a sababbin tufafi da suka siyo jiya su duka uku suka fita. Sune basu fita daga Taxi ba sai a unguwar wuro chakke, suka nemi inda ake sayar da waya, aka ce da su ba a sayarwa a nan, hakan ta sa dole suka nufi kasuwa, a kofar kasuwa ce suka sami masu sayar da waya, da suka saya, suka sake hawan mota ya zuwa ofishin MTN suka sayi layi, aka mata register da kyar suka mata, saboda rashin ID card. Suka fito bayan ta sayi kati ta saka. Suka dawo masaukinsu, bayan sun biya wani restaurant sun ci abinci.



Daga dawowarsu, sai ta ce da Mustapha ya saka lambar mahaifinsa a wayar, ya saka, sai ta kira, kiran farko kuwa aka daga.



“Assalamu Alaikum”



“wa alaikumussalam”


“barka da wuni”



“yawwa barka”



Don Allah ko kai ne Alhaji Kabiru?”



“eh! Ni ne Alhaji Kabiru, lafiya, da wa nake magana?”



“lafiya lau, sunana Sajida, a halin yanzu ina cikin garin Adamawa a cikin birnin Yola”



“tau malama Sajida me ya faru ne?”



Ta kwashe duk bayani da ya kamata ta yi masa ta yi, ta kuma sanar da shi cewa suna tareda yaronsa Mustapha. Cikin rawar murya da kadadi ya bukaci da ta bashi ya ji muryar yaronsa. Ai ko da ya tabbatar da cewa yaronsa ne, murna ba a ko iya bayyanawa.


Da ta karbi wayar, mahaifin ke cewa zasu zo shi da mahaifiyar Mustapha domin su dawo da yaronsu gida, bayan ya mata godiya kamar ya rusuna kasa. Inda ta nuna ba damuwa zasu jira su, amma su kokarta su taho yau.



Ya sanar da mahaifiyar Mustapha komai, da farko taso ta musa zancen ta zata wasa ake so a musu da hankali, amma da ya tabbatar mata da cewa ya ji muryar Mustapha sai ta aminta, ko wanka bai bari tayyi ba, ya kira driver ya ce ya zo ya kai su garin Yola.



Suka kama hanya, kasancewar hanyar ba kyau, dole sai da suka yi zagaye ta Gombe kafin su shigo garin Yola, wanda ya sa tun karfe daya basu iso ba sai sha daya da mintuna na dare.



Murna a wurin Mustapha da mahaifansa ba a cewa komai, dalili kenan da ya kara sa Sajida ta fashe da sabon kuka, ganin yadda suke nuna jin dadin haduwa da junansu.



Alhaji Kabiru ya jaddada godiyarsa ga Sajida kamar ya rusuna.




Sajida ta sanar da shi cewa, dama ta kirashi ne domin da safe suke shirin wucewa a garin Kebbi. Kebbi fa? Alhaji Kabiru ya fada cike da mamaki” ba fa gari ba ne da ke kusa, akwai nisa sosai, naji labarinku, ya kamata a ce kun huta sosai kafin ku wuce”



“Alhaji, ai babu daren da jemage bai gani ba, idan ka cire na daren mutuwarsa. Zaman hutu ba ya da amfani musamman idan da kaya a kan mutum. Kuna cikin farin ciki saboda kun hadu da yaronku, ni kuwa na rasa ‘yata a wannan tafiyar, kuma na dauki shekaru ban saka iyayena a idanuna ba, bare na ji muryarsu, ko na rungume su yadda kuka rungumi juna, ka ko ga babu hutu a wurina. inshaAllahu gobe zamu wuce tun da asubar fari.”




Da ya ga alamun batada niyyar fasa tafiyar dole ya hakura da rarrasarta, suka kwana nan ita da mahaifiyar Mustapha da Bilkisu, shi kuwa Alhaji ya kwana a dakin daa aka kamawa yaronsa Mustapha.




Ko karyawa basu yi ba, tun daga kammala sallah, Alhaji ya dauke su ya zuwa Adamawa sunshine da kansa. A hanya ya dauko makudan kudi ya bata, ta ce bazata karba ba, ita aikin Allah ta yi masa, ya nuna ai ba saboda mayar masa da yaronsa ya sa ya bata kudi ba, ya bata ne domin ta tallafawa marainiyar da ke tareda ita, gudun su shiga halin kakanikanyi domin batasan ya zata tara dda gida ba. Jin haka ta karba, kudi tsaba har dubu dari biyu da hamsin, ta yi godiya. Suka shiga mota, basu jma ba motar ta tashi. Dalili da yasa alhaji kabiru ya buga motarsa kenan ya zuwa Maiduguri da kansa, su kuwa su Sajida suka nufi Birnin Kebbi.



DR. ZAIN
[2/3, 5:06 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
----------------------------
_based on true life story_
🐾




3⃣2⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR.ZAIN_





_dedicated to: Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar Boko Haram_




*PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```



komai na rayuwa ubangijinmu ya Riga ya tsara
Tun daga kukanmu har muzo mu dara




*SHAFIN MASOYA*


Farida Gusau








***CI GABA***





Motar, mota ce kirar Sharon wacce ke dauke da mutum goma sha daya har driver, a gaba mutum biyu sai a tsakiya mutum hudu haka a kujerar baya mutum hudu ne a zaune. Sajida ce a gaba tareda Bilkisu, kasancewar sun rigayi kowa zowa, kuma hankalinta ya fi kwanciya idan ta zauna da yarinyarta.


Sai tafiya suke yi cikin motar, in da driver ya saka musu waka da suke cashewa da ita, waka mai taken *Rayuwa tana faruwa sai ta wuce kamar ba a yi ba* wacce Zainuddeen Zain ya yi tareda wasu mawakan Kebbi, a dai ai in da yake cewa.


_Dakata malam kaji na gayamaka halin rayuwa_
_Tamkar alawa ce, zakinta ba ya dorewa_

_Tun kana yaro kankani jikinka babu quality_
_Sai dai a ja hannunka garka a kaika titi_

_Abubuwa da dama ba ka iya yiwa kanka_
_Idan aka dauke ka baka so kuma ka yi kuka_

_Tufafi ma da kansu, mama ce zata sa ma_
_Yara manyan gobe, in ka manta na tunama_

_A hankali.., sai ga shi ka fara girma_
_Ka fara tara budare, su Asiya da Teema_

_A dinga duba bakin gatari, in an yi sara_
_Za aji dadin saran sosai in an yi gyara_

_A hankali malam, sai ga shi ka fara tsufa_
_Muryarka ta canja tafiya hadi da sifa_

_Kafin ka Ankara, rayuwarka sai ta kare_
_A kaika kushewa a barkka cen ka tare._




Haka wakar ta ci gaba da tafiyaa, har ta kawo in da Zainuddeen Zain ke cewa:



_Tsakanin samu da rashi ubangijinmu shi ya tsara_
_Dole sai wani ya rasa kafin ka zo ka dara_

_Mulki, kasaita ubangiji ya bada_
_Ya hore dawakai da kilisai ga masu fada_

_Ka manta komai, kai riko gagam ga duniya_
_Ba ka tari, ba rashi gaka da lafiya_

_A hankali a haka rayuwa take ta tafiya_
_Talakawa kana kallonsu cen kasa da fariya_

_Mulkin sai ubnagiji ya kwace ya bai wa waninka_
_Sai kayi magana ba wanda za ya ji ya bika_

_Haka ne halin rayuwa, juyi-juyi dan’uwa_
_Wani sai ka gan shi tsaye cak kama da kainuwa_

_Karamin mai wayau nesa ai ya fi mahaukaci_
_Komai zai zo maka da sauki, mahakurci_

_Kwatsam a haka rayuwarka sai ta kare_
_A kaika kushewa a barka cen ka tare._



Haka dai wakar na tashi a motar, su kuwa suna fira kala-kala, in da wasu ke firar sha’anin gabansu kamar kasuwanci da sauransu.


Cen bayan motar gaba daya, wata mata ce da gaba daya shekarunta bazasu haura ashirin da biyar ba, amma kan masifar ganin bone, gab daya fasalinta ya canja, zaka yi zaton ta haura shekaru hamsin a duniya. Zaune take tun shigarta motar ba wanda ta cewa ko kanzil, illa sai kokari kara rungume yaranta guda biyu da take yi a jiki, duk ba wnnan ne abin kallo ba, irin yadda cikin da ke jikinta har ya bayyana.


Ganin shirunta ya yi yawa, wata mata da ke kusa da ita ta kalleta tace da ita “baiwar Allah, tun shigowar mu a motarnan kike ta zullumi da kokarin rungume yaranki kamar wacce za a kwacewa, kallon yanayinki ba shakka ba za ki rasa labari da zaki bamu ba domin amfaninmu”.


Jin wannan magana da ta fito daga matar da ke kusa da wannan baiwar Allah, ya sa hankalin da yawa daga jama’ar da ke cikin motar ya dawo kan su domin jin me wannan matar za ata fada a matsayin labari rayuwarta.



*LABARIN NA’IMA*


“Sunana Na’ima” ta soma bayan ta share hawaye da suka gangaro a farar fuskarta. Tana magana da shesshekar kuka a tattarae da ita, kuma irin kuka da ke ratsa duk zuciyar mai imani. “muna zaune da mijina maisuna Jamilu a wani kauye da ake kira Minchika. Fulani ce ni gaba da baya haka maigidana Jamilu. Sana’ar maigidana ita ce, kasuwanci, ni kuwa ina sakar hula da tabarma. Wata rana da misalin karfe biyar na safiya muka fara jiwo kara da kuwwar mutane, hakan ta sa dole muka tashi ba shiri, domin mu tabbatar da abinda zukatanmu ke yi muna zargi na cewa mayakan boko haram ne suka yi wa garinmu tsinke. Hakan ta sa dole ni da mijina muka koma a guje domin mu dauko yaranmu guda biyu,dayan shekarunsa biyar”, ta fada a dai-dai lokacin da take dafa dayan yaro da ke kan cinyarta daya, “sunansa Sani, sai dayan yaronmu da shekarunsa biyu, sunansa Ahmad” ta fada a dai-dai lokacin da take kara rungumashi a jikinta, hawaye kuwa suka ci gaba da ganagarowa daga idanunta ya zuwa kumatunta. “Ba shiri muka fito, Ahmad na goye a bayana, in da Sani na rike shi a hannuna, shi kuwa Jamilu yana ta bayanmu sai gudu muke yi, a haka a gabanmu muke ganin yadda ake kama mutane ana yankawa dalili da yasa muka kara kaimi kenan wurin gudu domin mu tserata da rayukanmu. Wurin gudu kasancewar akwai dandazon masu so su tserata da rayukansu, muka rasa Jamilu, na so na koma na nemashi, amma na kasa, domin ina tsoron na koma, rayuwar yarana ta salwanta, dole muka ci gaba da gudu na neman tserata da rayukanmu, har muka fado cikin jeji. Fadi nan tashi cen tsawon kwanaki tara muna yawo cikin jeji, ba ruwa isassu, ba isasshen abinci ba tsaftar jiki bugu da kari gani dauke da ciki na wata har shida. Ga yara sai kuka suke yimin kan yunwa, wasu tsofaffi da muke tareda su, suka rasa rayukansu kan wahala, haka wasu yara da muke da su suka mutu. Wata rana muna cikin tafiya, Allah ya nufa muka karaso wani kauye, kamar hadin baki mu shida ne har yarana, ko sunan garin bamu fara tambaya ba, sai ga jirgin sama ya fara yimuna aman ruwan alburusai da bama bamai, ai kuwa nan hankalina ya tashi, na fara kallon yarana zasu mutu, ga shi bamusan wanne hali mahaifinsu yake ciki ba, nan muka runtuma cikin jeji gudu ya dawo sabo” ta fyace majina da ke kokarin fitowa daga hancinta, ta hanyar amfani da gefen zaninta, ta ci gaba. “wurin gudu, Ahmad ya bata, dole na ci gaba da gudu da goyon Sani ni kadai cikin uwa jeji ga tsohon ciki. Fadi tashi har na kawo wani kauye inda ake saka mutane a tsallake da su a jirgin ruwa, musamman wadanda irin ibtila’inmu ya far musu. Cikin ikon Allah a nan naga Ahmad, a hannun wani bawan Allah, na karbi abina bayan na yi masa godiya. Aka saka mu a jirgin ruwa aka tsallaka da mu, a haka har Allah ya kawo ni garin Yola. Zuciyata bata mutu ba, kan haka ban tsaya kada girmana ko mutunci na ba wurin yin bara, sai na nemi aikin wanke-wanke wurin wata mai sayar da abinci a unguwar Demsawo, na dauki kwanaki ina yi mata aiki, na tara ‘yan kudi, sai na dawo a unguwar Jambutu na ci gaba da kamawa wata mata dahuwar abinci a nan, kwana biyu da na tara kudi masu dan tsoka, sai na ce bari na nufi garin Kebbi, ko ba komai, munada ‘yan’uwa a cen kuma gari ne da ke da zaman lafiya sosai. Kunji labarin rayuwata a takaice.”



Tana kawowa nan, hatta driver sai da ya yi kwalla, Sajida kuwa ajiyar numfashi kawai take yi.


Wata a cikin motar, sai ta kada baki ta ce, “wai dama akwai mutane masu irin wannan rayuwar? Gaskiya kun ga ibtila’in rayuwa, Allah dai yasa kaffara ce a gareku, shi yasa bahaushe ke cewa, ‘ko a bakin kura, ya kamata mutum ya godewa ubangiji’, domin duk musiba da ka shiga, idan ka ji halin da wani yake ciki,sai ka tausaya masa dole.”


Juyowa kawai Sajida ta yi domin ta kalli, mai magana, ba taredaa ta furta ko kalma daya ba ta sake mayaar da fuskarta kan titi ta ci gaba da tuno abubuwa a suka faru da ita a lokacin da take karkashin kasimu.


Da suka kammala tattauna matsalar matar, sai wani da ke zaune a kujerar tsakiya, ya ce, “idan da wanda ke dauke da labari irin wannan ya bamu, ko ba komai zamu kara jin tsoron Allah mu kuma godemasa kan ni’ima da ya bamu komai kanakantanta kuwa.”


Gaba daya suka ce haka ne kuwa. Ganin haka, sai wani matashi da iyakarsa shekaru ashirin da uku ya gayara murya ya soma.



DR. ZAIN
[2/3, 5:06 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_


Please Login or Register in order to submit comment