Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina jin dadin yadda kuke nuns kulawarku gare ni, kuma inaso ku San da cewa lafiya lau nake wiki ne ya rike ni kwana biyu, kuma dama on weekends ba na posting. Allah ya bar mu tare_






***CI GABA***




Sallamar malama AISHA ce ta katse raha da SAJIDA ke yi cikin ‘ya’yanta a daidai lokacin da suke cin abinci, bayan sun idar da sallar magarib, da kusan minti ashirin da wni abu. Cikin murna Bilkisu ta tashi ta tarye ta har da hadaawa da rungumarta. “sannu da zuwa, ke ce a gidan namu, ba ko sanarwa” SAJIDA ta fada, a daidai lokcin da take kokarin mikewa tareda neman ruwa daga Randa da ke kusa da ita, domin wanke hannunta. Bayan ta wanke hannunta, suka shiga gaisawa da malama AISHA, lura da akwai magana da ta kawo ta, sai suka shiga cikin daki, suka bar yara nan a waje domin su karasa cin abinci. AMISHA kam sai kokarin zabga loma take yi, ga shi an dade ba a hadu da miyar sure ba ga manshanu, da kamshinsa zai doki hancinka tun daga nesa, bugu da kari, SAJIDA gwana ce a tuka tuwon masara.



“naga kamar kina tafe da magana, shi yasa na ce mu shigo daga ciki”



“haka ne, akwai magana mai muhinmanci da ke tafe da ni. Ba sai na tsaya dogon sharhi ba, kinsan wa cece ‘yarki; wato BILKISU, kinsan irin halayya da kaifin basira da ubangiji ya bata, haka kina sane da irin burinta a rayuwa, na kokarin ganin ta yi karatu har ta kai wani matsayi da za ta zama abin dubawa a idanun mutane. Ba wannan ba ma, saninki ne a wannan zamani, idan har mace za ta koma gefe ta jefar da karatun zamani musamman a baya, tau ba ita kadai ba, hatta rayuwar ‘ya’yanta abin tausayi ce, domin yanzu zamani ya kawo, da mazaje sam ba su san me ake kira aure ba, ba su san ko kadan ba me ya dace da yaransu ko matansu, kawai abin da suka sani shi ne kawunansu. Karkashin wannan nake gani, ya dace ki saka hannu wurin ceto rayukan zuri’arki daga shiga gararin rayuwa. Inaso karkashin umarninki, na saka BILKISU makaranta. Dama naji ta kammala JLC nata, kinga yanzu ba wani nisa aka yi ba daga shiga SS1 sai na tuntubi malaman makarantarsu FATIMA, sai na sakata a makarantar, kinga ko ba komai rage wata wahala ce”




Ta yi doguwar ajiyar zuciya, kana ta ce; “ban ki ta taki ba, amma inada tabbas kan duk makaarantar da ‘yarki take, ba karamar makaranta ba ce, mu da ko na koko da kyar mukan samu, ina mu ina sakata irin wannan makarantar, na biyu, mahaifinta, lusarin mutum ne, ba zai bari na saka ta makaranta ba, domin hatta wannan aikin da take yi a gidanki, ban bari ya sani ba…”




Ta katse ta ta hanyar dafa kafadarta. “kalle ni SAJIDA, matsawar za ki biyewa wannan mijin naki, ba shakka rayuwar yaranki za ta taso a halaka, kiyi tunani, Allah ya sawwaka, yanzu ace ubangiji ya dauki rayuwarki, ya kike tunanin rayuwar yaranki ta taso? Wa zai kula maki da su? Nasan kina sane da ko kusa QASIMU ba zai kula da tarbiyyarsu ba, sai dai ya lalata tarbiyyar, idan za ki farka, yanzu y kamata ya yi ki farka ki aikata abinda ya dace”




Ta fashe da kuka wanda har sautinsa ya kasa boyuwa daga bakinta, ta kalli malama AISHA, ta sunkuyar da kai, a kwakwalwarta, ta fara hasaso yadda rayuwar yaranta za ta kasance da ace ba ta raye. “haka ne abin da kika fada na baki dama, ai yanzu ke matsayin mahaifiya ce ga BILKISU, kiyi duk abinda ya dace”




“yawwa! Na ji kina fadar ba kwa da kudin biya mata zuwa makaranta, hmm! Ai ina sane da shi ne dalilin da ya hana ta ci gaba da karatu, duka ta sanar da FATIMA, kuma ni banada niyyar ki biya ko da kwandala wurin karatunta, yanzu hakkin wannan ya dawo kaina, ni zan yi, kawai abnida nake bukata daga gareki, shi ne ki kula sosai da zuwanta makarantar ki dinga kuma bata kwarin guiwa. Sai ki kirata, ki sanar da ita yadda muka yi yanzu.”



“mamanne!”



“na’am inna” ta fada tareda tasowa cikin sauri, daga inda suke zabga fira ita da kanwarta, kasancewar sun jima da kammmala cin abinci. Daga shigowarta, ta nemi wuri kan tabarma ta zauna, dama dakin tabarmi biyu ne kadai a ciki, wacce suke kwana ita da kanwarta, sai wacce mahaifiyarta ke kwana a kai, domin QASIMU ba kullum yake kwana gida ba, duk da tabarmin sun tsufa, ba za ka ga datti a kansu ba.



Ta kwashe duk abinda ya sa ta kirata ta gaya mata, ai ko nan ta bige da murna, har da nunawa a fili. Ta dawo ta shaidawa kanwarta, suka ci gaba da firarsu, bayan Sallar isha malama AISHA ta koma gida.



Komawarta gida ta sanar da FATIMA yadda suka yi da mahaifiyar BILKISU. Nan FATIMA ta buge da murna, tana fada a ranta, cewa, tabbas za ta yi abokiyar zuwa makaranta. Nan ta koma dakinta ta ci gaba da karatu, inda mahaifiyarta ta buda startimes ta fara kallon Sunnaah TV. Washe gari, ta bi su FATIMA zuwa makarantarsu, domin ta zanta da principal. Da yake Rubby makaranta ce da dalibai ke fita a kalla 7:30am, inda duk dalibin da ya kai 7:45am ya makara. Kasamcewar tanaso ta gana da principal sai ta fita tun kafin 7:20am, bayan sun saukar da FATIMA ta nufi assembly ground da ke harabar makekiyar makarantar, kai tsaye ta nufi office na principal din, wanda daga shigarka, sanyin AC ke kokarin ya ratsa bargon jikinka, haka kamshin turaruka kala-kala za su dinga kawo zungura a kusurwowin hancinka. Zaune ta tarar da shi sai faman dube-dube yake a wani katon littafi da ya ajiye a gabansa, a idanuwansa kuwa wani medicated tabarau ne da ke taimaka masa wurin karanto kalmomi da ke jibge cikin littafin. Sallamarta ce ta mayar da hankalinsa ya zuwa bakin kofa. Office din nasa kai kace wani katon parlour ne, domin har da kujeru three seaters da two seaters aka kawata shi da su, a matsayin parlour da zai sadaka da ainahin office din da shi yake aikinsa, wannan parlour din da shi yake taryar baki ko guntun conference meeting. Bayan ya amsa sallamarta ya rufe littafin tareda dagowa da fuskarsa domin ya ga wa ke sallama, nan ya buge da murmushi ya ce; “manya, yau ku ne tafe? Ai da kin aikomin, sai nazo” ta buge da dariya, “kai dai principal ba ka gajiya da tsokana, ina ni ina tadowa da shehin malami” shima ya buge da dariya, bayan sun gaisa, ta gabatar masa da abinda ke tafe da ita. Da farko ya so ya nuna abin ba zai yiwu ba, amma da ta roki alfarma, ta kuma nuna maa yarinyar za ta iya cinma ‘yan ajinnasu, sai ya aminta, sai ya turata ya zuwa ga Vice Principal Administartion, dauke da rubutu, na nuna gansuwarsa kan a baiwa BILKISU damar zowa tayi karatu a mataki na biyu a makarantar gaba da primary, wato SS.



Da ta kai wa vice takarda, sai ya umarce ta da ta zo da yarinyar gobe, domin a mata interview, bayan ta rubuta entrance exams, ta nuna ba laifi.



Washe gari suka zo da BILKISU, ta rubuta entrance exams, bayan awa biyu aka kammala makin na jarabawar, ga mamaki sai ga shi tafi duk sauran da suka rubuta cin maki mai yawa, aka mata interview, malaman sai sake baki suke yi suna kallaonta yadda take zuba turanci, kamar wata da ta fito daga ingila, hakan ya sa vice ya gayamata cewa za abata science class, nan ta katse shi, ta nuna masa cewa ita lawyer take so ta zama, don Allah su taimaka mata. Sai suka barta a Art class, wanda dama shi ne ajinsu FATIMA.



Nan aka bata house (red house), aka kuma bata damar cewa ta fara zuwa makaranta daga gobe, cikin sauri Malama AISHA ta biya kudin makaranta da na uniform da na litattafai, da yake dama makarantar su suke dinkawa yara uniform, haka su suke siyar musu da textbook duk a cikin kudin makarantarsu. Ta karbi uniform, da textbook, da sport wears da sunan on wednessdaya za ta fara shiga aji.



Tun da misalin karfe bakwai na safe take tsaye a kofar gidansu, a jikinta farar riga ce da iyakanta kugunta dauke da dogon hannu, rigar ta sha ado da tambarin makrantaar da aka rubutawa ruby ta ko’ina, sai guntun skirt da zamu iya kira da ash colour duk da kala din da surki, wanda iyakarsa guiwarta, wanda ya sa dole take kame-kame cikin kunya, sai dan hijabi da iyakarsa wuyanta. (ohh! Mu nasara da yahudu sun hallakamu, ace har uniform iyaye ba zamu tsawatar ba, wannan shiga ta yahudawa haka.) takalminta kuwa bakake sai farin socks da ta yi kokarin rufe tsiraicinta da shi ta amfanin jawo shi har kusa da guiwa. A hannunta kuwa dan wane basket ne, da aka cika da abinci da za ta ci a lokacin break fast.



Cen sai ga mota ta tsaya daf da ita, FATIMA kuwa sai sakar mata da murmushi take yi, cikin murna bayan ta gaida su ta shiga motar suka nufi makaranta.



Har yanzu labrin baai fra ba



08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:46 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾



🅾7⃣



Na





*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_




® *PEN WRITERS ASSOCIATION*




```QUOTE OF THE DAY```





_The paradox of courage is that a man must be a little careless of his life even in order to keep it_






*Shafin Masoya*




Aisha Alto
Asiya Lame
Maman Ahmad
Ililee
Mr Smiles
Ummie Zuru



***CI GABA***







Cikin mota suke fira, inda FATIMA ke sanar da ita darussa da za a gabar musu da su idan suka shiga a aji, za su gabatar da civic education first period sai economics sai government, inda take gayamata halayyar kowanne daga cikin malaman. Da suka karaso makaranta suka nufi assembly ground kai tsaye, ba da dadewa ba, prefects suka fara tsara yadda za su shiga layin assembly tareda kula da su, inda ake bincikar masu zowa da datti ko wata kwalliya da ba ta dace ba, bayan sun fitar da kamar mutum biyar suka umarce su da su rusuna na kneel down a cen bayan layin assembly, kafin malamai suzo su yanke musu hukunci. Zuwa wani loakci sai ga malamai sun fara zowa, da principal ya karaso, bayan national anthem da ‘yan wasu abubuwa da aka gabatar. Sai principal ya yi dan jawabi cikin harshen turanci, aka sallami kowa ya wuce aji domin gabatar a karatu, su kuwa wadanda aka tsare aka sakasu aiki a matsayin horo.




SS1B shi ne ajinsu, bayan sun shiga sun zauna, sai surutu suke zabgawa, inda wadanda suka lura da akwai bakuwar fuska a ajin, sai dandazo suke yi domin sanin wacece ita, FATIMA kam har ta gaji da amsa tambayoyinsu, cen sai ga malamarsu Victoria ta shigo, da yake ita ce mai daukar su civic education, bayan sun gaidata, ta shiga kai tsaye cikin darasi. Da ta gama jawabinta sai ta fara yi musu tambayoyi, inda BILKISU tafi amsawa, dalilin da yasa Victoria ta kirata da friend kenan, shi kuma ne dalilin da yasa ‘yan ajin nasu, musamman masu kwazo a ajin suka fara daukan ta a matsayin kishiya. Haka malaman suka dinga yabawa kokari da kwazon BILKISU, sanadiyyar yin bakin jininta kenan a ajin.




Bayan kada kaaraurwar tara wato breakfast, cikin sauri suke fita daga ajin domin halartar wurin cin abinci, inda suka taru a bangarori daban-daban na makarantar, ko wa ya baje abinda ya zo da shi daga gidansu domin tarfawa cikinsa. BILKISU kasancewar batasan kowa a makaranta ba, ta je wurin FATIMA tareda abokaninta domin su ci abinci tare, cikin sakin fuska FATIMA ta tarye ta, su kuwa abokanin na FATIMA sai wani kallon mai bisa ruwa suke yi mata, suna ganin gaba daya wannan ba ajinsu ba ce. Ko magana ta yi musu sai su dinga fura iska a hanci suna tada kai, duk da haka BILKISU ba ta kula su ba, a haka ta koma gefe ganin ba su ba ta fuska ba, ta bude dan abincinta na talakawa dumamen tuwon masara da miyar kuka ta fara ci.




A wurin cin abincin ne, kawayen FATIMA ke tambayar ina kuma ta rungumo wannan local girl haka? Ta yi musu bayani gaba daya. Ai ko nan suka far mata da fada, “wato saboda rashin hankali shi ne za ki jangwamowa kanki wannan? Irin su ne ke zowa kai tsaye su raba diya da mahaifiyarta, ki tsaya nan wai ku masu taimako, hala an gaya muku ubangiji da ya halicci kowa ba sai da ya leka zuciyoyinmu ba kafin ya raba muna arziki, wallahi wasu talakawa da za a yi su masu kudi, da anga tsiya”. Suka tafa hnnu suka sheke da dariya, ita kuwa FATIMA ko kallo ba su isheta ba, domin kacokam hankalinta na gefen BILKISU da sai satar kallon juna suke yi. Da suka kammala cin abinci suka fara zagayawa suna yawo, dalilin da ya sa FATIMA ta kira BILKISU ke nan domin ta nuna mata makaranta, su kuwa kawayen nata sai tafiya suke suna sukar BILIKISU cikin habaici da kalmomi masu zafi. Ita kuwa ko a jikinta, domin sai fada take yi a ranta, “tankawa, yabawa, biyar bashin matsiyaci” suna tafiya suna fira har lokacin komawa aji ya yi. Da suka tashi daga makaranta, ‘yan ajin nasu sai hararta suke yi, ita kuwa ko kallonsu ba ta yi ba, FATIMA kuwa bakin ciki kamar ta kuwwata, domin lokaci daya ta ji BILKISU ta kwanta mata a rai,musamman kyawawan halayyarta, ga shi kuma duka kawayenta ba wacce ke son ta. Ta yi nisa da tunani, cen ta jiyo horn na motar gidansu, cikin sanyin jiki su duka biyu suka shiga motar, kusan minti biyar ana tukin motar ba wanda ya furta ko harafi daya, cen BILKISU ta nisa ta ce, “na rasa wanne irin bakin jini muke da shi, ni da mahaifiyata, duk inda muka je sai kiga ana kyamar mu, hatta mahaifina ya tsane mu, ga shi first day dina a makaranta na fuskanci matsalar tsana, anya kuwa ba laifi muka yi wa ubangiji ba, zan tambayi mahaifiyata, ta yi wu a danginmu akwai wanda ya tafka zunubin da har mu an tarfa muna” ta fashe da kuka. Ganin haka FATIMA ta janyo ta ta dora kanta kan kafadarta ta fara rarrashinta, driver da tun shigarsu yake sauraren wakar Sani Sabulu, wakar Dikko na Gotomo, ya juyo cike da tausayi, ya ce, “ke BILKISU kar ki kara fadar haka, kinsan wasu yara ba sa da tarbiyya musamman idan suka ga ‘ya’yan masu arziki ne su, sai kiga suna wulakanta na kasa da su, ba su san da cewa, ubangijinnnan da ya basu arziki bai manta da sauran ba, sun manta mahaifansu ba wani abu suka yi wa uabngiji ba har ya ji bari ya biya su ta hanyar azurta su, ki ci gaba da hakuri, duk wanda ya sha wulakanci a inda yake neman abincinsa, ba shakka yana dauke da dimbin lada, ki kyalesu su kwashi zunubi” FATIMA ce ta karbe zancen, “haka ne, ai kamata ya yi ki tsaya kema ki nuna musu ke mutum ce, da me suka fiki? Kin fa fi mafi yawansu kyawu ga ki da ilimi da saurin fahimta, wanda shi ne dalilinsu na je fa maki karan tsana, sai ki bullashe kema tunda ba yadda za su iya da ke, kudin da iyayensu ke biya su kike biya, tau me ye bamabnci?” ta kara fashewa da sabon kuka, ita kuwa sai rarrashinta take yi, har suka karaso daf da kofar gidansu, duk da da kyar mota kan shiga unguwar, haka da reverse ake fita. Suka yi sallama ta shiga gida, da zinmar zuwa marice za ta zo.




Shigar ta gida ta tarar da mahifiyarta a daki, cikin sakin fuska da gaida ta, ta je ta canja kayan jikinta ta ajiye kan tabarma ta fiddo da wata ‘yar guntuwar toka da suke wanka da kuma wanki da ita, ta ajiye kan uniform nata. Sai ta fita ta suri buta domin ta yi alwala. Mahaifiyarta kuwa, sai kokarin gyara shinkafa take yi wacce za ta dora kan wuta, ajuma da maraice. Inda AMISHA sai wasa take a kusa da ita.




Bayan da ta kammla sallah, ta je ta wanke uniform nata, ta fita ta yo cefane da za a yi amfani da shi domin tuwon maraice, da ta dawo suka shiga fira da mahaifiyarta inda take tambayarta game da rayuwar makaranta, ita kuwa tana ba ta amsa, har aka fara kiran la’asar. Bayan ta kammala salla ta suri takalminta da dan tilon hijabinsu ta nufi ind take aiki. Mahaifiyarta kuma ta fada aikin abincin dare.




Bayan sun gaisa da malama AISHA, kai tsaye ta wuce lungun FATIMA, ta fara yi mata aiki, tana aiki suna fira har ta kammala, ta fito ta sami malama AISHA a parlour inda suka yi bankwana ta wuce daf da magariba. Aka kammala sallar magariba, lokacin hadari ya kankama har an fara iska mai dauke da sanyi da kuma kamshin ruwa, cen an fara kiran la’asar sai ga QASIMU ya shigo da abokaninsa guda biyu, ASHCO da LIVER, su duka uku sun sha giya sun bugu, sai surutu suke da su karan kansu basusan me suke fada ba. Cikin murna SAJIDA ta tarye su kasancewar ba bakon abu ba ne a wurinta mijinta ya shigo gida a buge, ta shimfida musu tabarma a waje duk da da alamun hadari, ta kawo musu abinci, ita kuwa suka wuce yin sallah ita da yaranta. Sai kyakkyewa QASIMU ke yi inda abokaninsa ke yaba wa girkin matarsa, har da sude hannu suna santi, sai labarai suke bai wa junansu kala-kala. Da suka kammala ta zo ta dauke kwannan ta kai wurin wanke-wanke ta ajiye, juyowar da za ta yi sai aka fara yayyafi, dalili da yasa ta canjawa kwannan wuri ke nan, ta rugo daki domin taga lafiyar yaranta, cike da mamaki, sai taga QASIMU na nunawa abokaninsa inda za su kwanta.




Ta yi tsaye tana kallonsa cike da mamaki irin ta ma rasa me za ta gaya masa, saboda gaskiya ta mata yawa, ta kalli su abokanin nasa ko a jikinsu su ala dole ga su za su kwanta da iyalin wani amma ko a jikinsu, ta kalli yaranta, AMISHA har ta fara rawar dari, BILKISU kuwa itama kallonsun kawai take yi. Budar bakinsa ya ce “ki zo bayan ASHCO ki kwanta, ke kuwa BILKISU da AMISHA ku kwanta tareda LIVER ni sai na kwanta ta cen ko a kasa na kwanta ai ba damuwa, yana fadi yana tangadi da kokarin watsi da hannuwa.




Bakin ciki ya lullubeta, take zuciyarta ta kawo a makogwaro, a ranta tace bari na nunawa mutuminnnan ba mashayi ne kadai mahaukaci ba. Cikin ruwan ta fito ta nufi inda suke daka, ta dauko tabarya ta nufato dakin……..




Har yanzu labarin bai fara ba




08034840276

DR. ZAIN
[2/3, 4:47 PM] Saudat A J: *'YAN GUDUN HIJIRA*
_Labarin Sajida_
-----------------------------------------
_based on true life story_
🐾








🅾8⃣



Na



*ZAINUDDEEN ZAIN*
_DR. ZAIN_





dedicated to: _Marayun da suka rasa mahaifansu a sanadiyyar boko haram_





® *PEN WRITERS ASSOCIATION*





```QUOTE OF THE DAY```







_Always acknowledge a fault. This will throw those in authority off their guard and give you an opportunity to commit more._







*Shafin Masoya*


Zainab Jibril
Umaima Jibril

(My biological sisters)





***Ci gaba***



Daga shigowarta ta tarar da ASCHO shi har ya kwanta ya ragamata inda za ta kwanta ita, shi kuwa LIVER yana kokarin gyara inda zasu kwanta Shi da AMISHA da BILKISU, gogannaka kuwa yana tsaye yana kallo, a tsarinsa sai sun kwanta kafin shi ma ya kwanta. Daga shigowarta bata yi wata-wata ba ta fara musu da duka tim-tim-tim! Dalilin da ya sa suka fito daga dakin kenan a gurguje, suna “ke ya kina harkar yawa, wannan ba yi ba ne..” suna fada cikin maagagin maye. Ta ce “idan kai jahilin mahaukaci ne, bari na nunamaka ni mahaukaciya ce da ko lasisi banida, in ba jahilci ba, iyalinka wai za ka ce wani katon banza ya zo ya kwanta su hada jiki a shimfida daya, shaye-shaye hauka ne hala? Ku kuma imbanda jahilci da hauka da rainin hankali wai har ku biye wa wannan tsarin saboda tsabar lalacewa, ai ko a yahudawa ba za a sami masu irin wannan aikin ba…” su duka hudu sai dukansu ruwan sama ke yi, ita kuwa sai faman zuba take yi, tana fadan tana kara jin haushin abin, cen QASIMU ya kada baki yace, har yanzu dai cikin mayen yake, “ke nan gidana ne ni keda ikon in tsara duk yadda na so ba wata shegiya da ta isa ta hana ni, da zan gina gidan, Naira nawa kika bani?” Ya fara zarar belt daga kugunsa. Wasu hawaye suka fara kwaranyomata, ta rasa hawayen me ye, na zama mijinta jahili, mahaukaci, marar kishi, lusari, wawa, dakiki ko me? Ta kalle shi ido cikin ido ta ce “QASIMU wallahi bari in gaya maka, kalle ni da kyau, zan iya daukar irinka biyu ba tareda na gaji ba” ya kalleta ya tabbatar ko a jeji suka hadu ba abinda zai iya yi mata. “ko ka dawo cikin hayyacinka ko in illtaka da wannan tabaryar, ku kuma ku fita gidannan tun kuna kalluwa ko in muku raunin da har makiyanku sai sun tausaya maku” jin haka suka kwashi kunyarsu sumu-sumu suka nufi waje cikin ruwan sama da iska, sa’arsu daya iskan ba karfi. Ya juyo ya kalleta sai haki take kamar wacce ake yi wa kidan tauri a ka, gaba daya ya tsorata domin bai taba ganin ta shiga yanayi irin wannan ba, ta kalle shi ta ce. “idan ka ga dama ka iya shigowa, idan kuma abokaninka za ka bi ga hanya cen” ya dubi ruwannan kara karfi kawai suke yi, ya nufi daki, sai makyrakyatar sanyi yake yi, ta ajiye tabarayar ita ma ta nufi dakin a fusace.



Ta tarar da yaranta suna cikin damuwa, ta gyara musu inda za su kwanta, inda ta shimfida dayan tabarmar domin su kwanta ita da mijinta.



Su ASHCO kuwa, daga fitarsu sai sabbatu suke suna fadan, kai wannan matar akwai masifa, ita ko irin wayewarnan ta zamni ba tada, amma fa gaskiya ta iya girki kawai dai ’yar masifa ce. A haka har suka karaso inda za su kwana, gaba daya tufafin jikinsu sun jike su kuwa sun sha kashin ruwa sosai har da makyarkyatar sanyi su ke yi.



Har yanzu dai QASIMU kallonta kawai yake yi, ya kuma tabbata a buge ba abin da zai iya a jikinta, sai kawai ya ci gaba da mitarsa, ita kuwa ta ci gaba da rarrashin yaranta, musamman BILKISU da ta lura hankalinta ya tashi.



Washe gari bayan sun iyar da sallah suka dauko kur’ani suna karantawa kamar kullum, har zuwa wani dan lokaci suka dora Karin kumallo, ba da jimawa da kammala Karin nasu ba sai ga driver ya iso, sun fahimci hakan ne, sanadiyyar har cikin gidansu FATIMA ta shigo, bayan sun kammala gaisawa da mahaifiyarta, ta suri littfanta da dan kwandonta wanda ke dauke da abincin da za ta ci dama ta jima da shiryawa suka fice.



Kamar kullum; yau ma ita ce zakara a bayar da amsoshin da malamansu ke tambayarsu a cikin aji, wanda shi ne dalilin kara tunzurar da mahassadanta.



Da suka tafi cin abincin tara, haka suke nuna kyama gareta a fili, dalilin da ya yi sanadiyyar FATIMA ta shigar mata fada, har suka bata da abokaninta. Sai fada suke; yanzu kan ‘yar talakawa kike fada da mu? Hala kin manta inda muka fito, kin manta shakuwa da muka yi da ke? Ta amsa musu , “idan dai haka ne zaman tare, ba shakka ba inda wannan tafiya za ta kaimu sai ga halaka, shin mun manta cewa da mai kudi da talaka duka bayin Allah ne? ku dakata nai muku tambaya, shin mu da iyayenmu suka mallaki dukiya, wata gwaninta suka yi wa ubangiji ne ta sanadiyyarta ya basu dukiya? Shi talaka daga sama ya fado ne ko

Please Login or Register in order to submit comment