Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka nake ta jiranka har kasa
na fara tunanin ko wani abune ya faru?
Kada ki damu nace da Amina adaidai lokacin data tuka
motar mukaci gaba da tafiya dogon zagaye nayi don haka
kikaga na dade banida tabbacin cewa amina zata yarda
da abinda nake fada mata hakan ya samo asali ne daga
irin kallon da naga amina nayimin kallon da takeyi min ba
kallo ne irin na so ba saidai zan iya kiransa da kallon an
daukeni makaryaci
.
Fadin amina ta kira sunana batareda na amsa ba saitaci
da cewa akwai wani abu dana fahimci kana boye min
kuma sanin kankane bai dace ace kana matsayin
masoyina ba amma kana boye min matsalarka sannan ta
dubeni duba irin na SO
indai har da gaske kake kana sona to ka sanar dani
gaskiyar labarinka tun daga lokacin daka bar kano har
zuwanka kaduna Amina tayi shiru na dan lokaci tana
sauraron abinda zai fito daga bakina.
Bai kamata ba ace Amina tasan gaskiyar labarin domin
yin hakan yana iya jefata cikin hadarin da nake ciki idan
kuma na sake na fada mata cewa sharrin da akayimin
yana da alaka ne da yan uwanta Badura da Amira to tana
iya yin abinda ni zan kwana aciki domin idan taji gaskiyar
al'amarin tana iya zuwa ta fadawa babarta hajiya Asma'u
ita kuma Hajiya Asma'u tana iya fadawa mijinta Kanal A.
Mukhtar ya kai maganar kotu duk yadda aka juya ni zan
kwana ciki saboda babu wanda zai yarda bani na kashe
zainab ba hakan shi yasani yanke shawarar cewa zan sake
shiryawa Amina karya bazan sake tasan gaskiyar labarin
ba domin data sani gara na shiga gidan Kanal A. Mukhtar
din na sato sarkar idan da kwanana agaba to dole ne na
wuce koda kuwa ana ruwan wuta ne tattausan
murmushin shirin yin karya ya bayyana a fuskara adaidai
lokacin da Amina ta dan juyo daga tukin motar da take ta
fuskance ni sannan nace da ita.
Amatsayinki na masoyiyata ina zaton ya kamata ki yarda
da abinda nake fada miki koda kuwa karyane saboda shi
so hana ganin laifi ne ya masoyiyata ruwan raina mai
taimakona.....
Dakata. Amina tace dani basaika kurarani ba fadi abinda
kake son fada zan yarda dashi koda kuwa ba gaskiya bane
sannan taci gaba da cewa nasan daman fadin son
danakeyi ma yafi wanda kakeyi min amma ni na gode
Allah akalla dai yanzu kana saurarona akan da, wanda ada
ko hira bakaso kayi dani sai gashi yanzu da bakinka kana
cewa dani Masoyiyarka hakika wannan kalma ta
masoyiyata da kake kirana da ita itace kalma mafi dadi da
kunnuwana suka jiye min tunda nazo duniya in har kana
ganin rufe sirrinka agareni shine mafi soyuwa agareni
farin cikin ka shine abin sona rayuwarka itace abar
begena sannan taci gaba da cewa
Ka sani Fadil duk abinda kake so to nima zuciyata dolene
ta karkata zuwa kaunarsa koda kuwa ada batayi amanna
da shi ba.
Idanuwan Amina suka cicciko da kwalla wanda hakan
yasa da kyar take tuka motar so sartse ne fadil amina taci
gaba dacewa da kasan irin son da nake ma da baka boye
min abindake damunka ba idan da ka daure ka sanar
dani gaskiyar labarinka toh a shirye nake na mika
rayuwata wurin ceton ranka.
Domin rayuwata batada amfani idan har ka kasance cikin
kunci amma tunda kana ganin rufe sirrin naka shine yafi
alheri to shikenan bana bukatar ka sanar dani saboda
sanar dani din wani abune da zai bakanta ma rai ni kuma
duk abinda zai bakanta ran abin begena to ina gaba dashi
daga nan Amina ta karawo motar wutar muka nufi birnin
kanon dabo bata ko jira kwakwalwata ta gama nazarin
abinda tagama fadamin ba duk da haka saida
kwakwalwata ta sake gargadina.
Kada ka sake ka fada mata idan kuwa ka fada mata to
kaine ruwa tsundum
kasan kuwa laifin wani baya shafar wani.
Misalin karfe goma sha dayan dare muka iso kano.
**
Kamshin furannin fulawowi ya bugi hancina a sakamakon
bude tagar dakin danayi na leka kaina ina nazarin
farfajiyar gidan wacce ke haske da wutar lantarkin dake
gidan bayan hanci na ya gamsu da irin kamshin furannin
dake farfajiyar gidan sai na juyo da kaina na sake nazarin
falon a tsanake cike kuma da mamakin irin son da Amina
takeyimin duk da yake ran Amina ya baci a sakamakon
yan maganganun da suka tsakaninmu a hanya amma
hakan bai hanata yi min abinda tayi niyya ba lokacin da
mukazo gidan talabijin na kano CTB sai Aminta ta juyo ta
kalleni murmushin karfin hali a fuskaa sannan tace dani
zankai ka gidanmu dake tarauni ka zauna acan kafin yan
sanda su sassauta nemanka nasan da wahala yan sanda
suyi tunanin nemanka agidan domin gidan sabone ba a
ko taba zama acikinsa kaine na farkon zama acikinsa
kwanaki hudu da gama gininsa mahaifina ya rasu na
kumayi gadonsa daga wajen mahaifina sannan Amina ta
danyi shiru ta dubeni tayi murmushi sannan tace idan
kana bukatar abinci zaka tarar da komai acikin firji zan
dawo gobe da rana domin mu sake tattaunawa sannan ta
juya ta nufi kofa ta barni ina bude baki cike da mamaki
kafin hankalina ya dawo jikina Amina ta fice daga dakin
abu na karshe da kunnena ya sanar dashi shine karar
tayar da motar Amina wacce ta fice da gudu ta nufi kofar
gidan alamace dake nuna cewa haryanzu bata Huce ba.
**
Karar kararrawar Agogon dake nane ajikin bangon dakin
ita ta tasheni daga nannauyan baccin da ya daukeni tun
karfe tara daidai na safe agogon ya nuna na tashi zaune
ina mutsutstsuka idanona hasken rana ya fara bayyana a
sarari yau garin babu alamar hadari sai dai idan iska ta
kada hancina yakan shaki kamshin Damina.
Saura kadan na fado daga kan gadon saboda tsoro wata
ajiyar zuciya akayi a bayana wacce ta tsoratani a iya
sanina ni kadaine a dakin tsoro ya hanani juyawa naga
wanda ke ajiyar zuciyar abayana
ina zaune kamar an zare min laka kuma kowanne lokaci
ina tsammanin naji bindiga ta zunguri kuguna can kuma
sai naji wata zazzakar murya ta kyalkyale da dariya nan
da nan na dago kaina sannan na ganta a zaune akan
kujerar dake gaban gadona fuskarta cike da annuri da
walwala tana sanye da doguwar riga fara wacce akayi
mata ado da bakaken duwatsu masu kama da zinare ta
lullube kanta da bakin kyalle farin ciki ya kamani har na
manta da halin da nake ciki.
Wallahi Amina kin ban tsoro nace da ita.
Amina ta dubeni tana murmushi daman nasan zaka
tsorata tace dani tun karfe takwas da yan mintuna nazo
ganin kana barci ne yasa na kyaleka saika tashi.
Kuma shine kika tsoratani?
Kodai ka tsorata kanka amina tace dani tana kallona
haryanzu murmushin bai bar fuskarta ba sannan ne na
lura da kurtun zuba shayi akan wani tebur dake gabana
agefensa kuma wani kwano ne na azurfa (Silver Plate)
wanda bansan ko menene aciki ba amina ta matsa kusa
da teburin sannan ta bude kwanon ganin abinda ke cikin
kwanon yasa cikina ya fara salati sai yanzu ne na gane
cewa inajin yunwa kwanon yana dauke da toyayyiyar
wainar kwai da biredi da kuma hanta,
zan tafi makaranta saina dawo ma sake tattaunawa
Amina tace dani yaushe zaki dawo? Na tambayeta duk da
yake kuwa bana son rabuwa da ita Amma tafiyarta ita
zata bani damar tunanin yadda zan fuskanci gidan Kanal
Mukhtar wajen sato sarkar zinaren da Badura ta sani.
Amina ta dago kai tana murmushi sannan tace dani ai ba
dadewwa zanyi ba yanzu ma wani aiki ne da aka bamu
tun kafin na tafi nemanka kaduna nake son nakai musu
ina kaiwa zan dawo kada ka damu kaji My Darling. Ahaka
muka rabu da amina ba don naso ba sai bayan da ta tafi
ne nagane cewa Amina ta karance takardar da badura
tabani domin ni a aljihun wandona nasata amma
dubawar da zanyi sai naganta a wandon aljihun rigata tun
da bata nuna min alamar komai ba nace cikin zuciyata to
ya kamata nayi shiru na manta da ita.
.
Amina bata dawo ba sai misalin takwas da rabi na dare
hankalina yayi matukar tashi badan neman yansanda
keyimin ba to dana bita makarantar ina ta faman safa da
marwa a farfajiyar gidan tun hudun yammacin wannan
ranar har takwas da rabi ina shirin yanke shawarata
karshe kenan sai naji karar mota ta nufo kofar gidan
Aminace bayan munyi yan mintuna muna hira takuma
fada min abinda ya tsayar da ita sai mukayi sallama
saboda tace ita bata dadewa awaje kasan yadda gidansu
yake mukayi sallama da ita akan yarjejeniyar cewa gobe
zata zo ta tayani zama domin ba zata makaranta ba bayan
na rakata har gindin motarta ta tafi sai na juyo da niyyar
na shiga daki anan ne to NA FARA GANINTA.
.
Tun kafin na shiga dakin naji wani kamshin kakkarfan
turare ya daki hancina ina tsammanin zai iya bugar da
mutum hakan ne ya tabbatar min akwai mutum a dakin
na dai lallaba na shi tana zaune akan kujerar dake
fuskantar gadona katuwar mata ce kakkaura zatayi
shekaru hamsin aduniya ta lullube kanta da bakin hijabi
hakika bansan ko wacece ba.
Fadil tace dani kana mamakin ganin bakuwar mace a
dakinka ko? To karka damu yanzu zaka san ko ni wacece
idan har kana bukatar sanin koni wacece din to nice
mahaifiyar BADURA.
.
TAKWAS 8
Kece wa? Na sake tambayarta cikin kaduwa da mamaki
Nice Hajiya binta babar badura tace dani haryanzu ina
tsaye a kofar dakin banshiga ba.
Abinda badura tayimin yasa duk wani wanda yake sona
da yan uwantaka dashi na tsane shi don haka kallo daya
nayiwa mahaifiyar badura naji na tsaneta bakuma nason
zama a dakin muddin tana ciki akwai wani abu a tattare
da hajiya binta dake bani tsoro irin kallon da takemin
dakuma irin yadda take murmushi tana kuma bata rai
alokaci guda shi ya sani na fara tunanin ba kanta daya ba
sabanin 'yarta Badura ita hajiya binta bakace mai jajayen
idanu can cikin loko kamar kwankwalati duk lokacin data
dubeni sai ta zazzaro minsu alama ce ta mahaukata don
haka sai na toge daga kofa ina shirin shekawa da gudu
aduk lokacin da bukatar hakan tataso idan akwai abinda
zanyi harta bar dakin to zanyi shi domin zamanta
agidannan hadari ne yana iya kawo karshena shin wai me
yakawota ma gurina? Kuma tayaya akayi tasan ina nan?
Duk yadda kuma akayi akwai wani da yasan ina nan
bayan..
Duk yadda kuma akayi akwai wani da yasan ina nan
bayan ita.
.
Me yakawo ki nan? Na tambayeta
yakamata ka shigo ka zauna tace dani
ki tashi ki fice daga gidannan nace da ita domin banga
hujjar da zatasa ki shigo min gidaba batareda dansani ba
hajiya binta ta kyalkyale da wata irin dariya dariyar data
sa tsigar jikina ta tashi gashin jikina ya mimmike gurmi ya
karyo min hakika yanzu na tabbata mahaukaciya ce cikin
lokaci kankani kuma saita murtake fuska sannan tace
dani
kai yanzu baka jin kunya kace nan gidanka ne gidan
Amina kuma sai ya zama naka? Ta sake kyalkyalewa da
dariya ko ka taba ganin saurayi yaci gadon budurwarsa ?
Fadil ya kamata kasan halinda muke ciki domin ina son
sanar dakai wasu muhimman batutuwa danake tafe dasu
ko kanaso kuwa ko baka so.
Me yasaki tsammanin zaki iya sani na saurare ki dole? Na
tambayeta,
saboda nasan muddin ina tare dakai dolene ka saurareni
domin idan ka gudu ma baka da wurin zuwa ko
kanadashi Fadil? Ta tambayeni nayi shiru duk da yake
nasan ba kanta daya ba dole ne na yarda da abinda ta
fada yanzu tabbas banida wurin zuwa
to ki fada ina daga nan nace da ita kana tsorona ne? Ta
tambayeni to idan tsorona kakeji saika zaba tsakanina da
yansanda wa zaka saurara fadil na gaji da bata lokaci tace
dani idanuwanta masu kama da kwankwalati suka juya
sukayi jawu idan baka shigo ba tace dani tana murmushi
irin na wadanda kansu ya tabu to zanyi ma irin abinda
NAYIWA ZAINAB.....
na rike numashina cikin tsoro da kaduwa,
kina nufin kice kece kika kashe zainab? Tayi dariya sannan
tace.
Banda ma kashe zainab danayi akwai wasu abubwaunda
duk zan sanar da kai yanzu kuma dole ne ka saurara na
juya da niyya na fita da gudu domin na tabbata
mahaukaciya ce.
Gudunka bazai ka ga komai ba sai halaka tace dani
gargadin da yafito daga bakinta shi yasa na sake juyowa
na fuskanceta sannan ne naga wani abu kamar karfe ya
turo kanta ta cikin bakin lullubin da tayi idan ka gudu zan
harbe ka Fadil shigo ka zauna in kuma bahaka ba kaima
kabi zainab lahira kan bindihar ya bayyana a fili na kuma
tabbata ina motsawa zata harba dole kanwar naki ce
tasani na nufi cikin dakin kamar kazar da kwai ya fashewa
aciki na nufi kan gado kusa da inda jakar da yayana ya
bani take na zauna koda na zauna sai nace da ita
menene wannan kiketa faman nuna ni da ita tunda na
zauna,
Hajiya binta tayi dariya sannan tace KIBIYAR AJALI ce
maganin yara masu taurin kai irinku idan bakayi min
shiru ba da tambayoyin rainin wayo daka saba to ka
ayyana azuciyarka tsakaninka da mutuwa baifinida kai
din nan ba.
Ai daman duk mai rai matacce ne nace da ita don Allah
kuma bari nayi miki tambaya shin da wannan bindigar
kika kashe zainab......?
Kafin ta bani amsa sai kofar dakin ta bude sannan ya
shigo hannunsa sanye cikin koren wandonsa akwai
alamar datti ajikin farar rigarsa SALMAN ne.
Taurin kai zai nuna miki ne Hajiya?
Yanzu na dan tausasa shi yace da ita yana murmushi fice
daga nan shashasha wayace ka shigo kafin ta rufe bakinta
tuni salman ya bace daga dakin kamar aljani.
**
Ina son sarkar tazo hannuna gobe da misalin karfe biyu
na dare tace dani wacce sarka kike nufi? Na tambaya duk
da cewa kuwa nasan sarkar da take nufi
Sarkar da na dade ina burin mallaka tace dani na kuma
jefa rayuwata cikin hadarin gaske domin ganin na cimma
burina kada kaja min rai Fadil nasan kasan matsayinka
agurina yanzu idan baka sani ba to bari na fada maka
Sannan taci gaba da cewa kai yanzu kana matsayin karan
farauta tane yakuma zama dole kayi duk abinda na saka
domin idan kaki bin umarnina to bazan saurara ba wajen
ganin na bakanta rayuwarka kamar yadda baka daumin
sarkar nan ba zaka bakanta tawa rayuwar ina kuma yi
maka tuni da cewa duk abinda ya faru akanka ba laifin
kowa bane sai laifina don haka ina fatan bazaka zargi
'yata badura ba akan duk abinda ya faru itama ta taimaka
min wajen hadama tarkon ne don takura mata da nayi da
kuma tsorona da takeji inason ka sani Fadil taci gaba da
cewa cikin daga murya in da ta badura ne to da yanzu
baka cikin halin da kake ciki yanzu hakika badura ta dade
da Kamuwa da sonka idan baka manta ba lokacin da kake
Otel dinnan ta kaduna kunyi da badura cewa zatazo da
yamma ta sameka wannan alkawaru da tayi ma tayima
shine ran da kuka fara haduwa dakai a lambun otel din
wanda daga karshe baka samu damar ganinta ba sa a
daren wannan yammacin inda tayima karyar cewa wai
wani na barazana ga rayuwarta inason kasan cewa rashin
ganin badura da bakayi ba awannan rana ya samo asaline
da rashin son da takeyi ka fada cikin Bala'i ina kuma fada
maka duk wadannan abubuwa ne domin kasan cewa
badura batada laifi kuma masoyiyarkace ba dole bane ka
yarda amma zaka gane nan gaba
Ina fatan duk ka gane abinda nake fada? Hajiya binta tace
dani daga karshe kuma ina son snaar dakai cewa nice
Ummul Aba'isin duk abinda ya faru agareka nice kuma na
kashe zaina na sake maimaitawa
NI NA KASHE ZAINAB
Ni na kashe zainab na sake maimaitawa ni na kashe
zainab don ganin na cimma burina kuma kaima ma na
jefa cikin Bala'i badon komai ba sai don na bakantawa
Amina Rayuwa.
.
Sanin kanka ne amina na mutuwar son nasan kuwa
jefaka cikin bala'i kamar jefa Amina ne domin nasan zata
iya yin duk wani abu don ganin ta kubutar dakai sannan
hajiya binta ta kalleni ta kyalkyale da dariya.
Hakan shi ya kara tabbatar min da cewa ta gama zarewa
sai kayi hankali kuma tace dani na sami labarin akwai
yansandan ciki akalla guda uku suna nemanka an kuma
turo sune daga Durba hotel kaduna a iya sani na kuma
ba'a taba samun gwanayen yan sandan ciki kamarsu ba
na tabbata kuma muddin suna nan ba jimawa zasu
kamaka muddin kuma kana kasar nan don haka ma nake
baka shawarar ka sato min sarkar gobe mu kuma hadu a
daula otel karfe biyu na dare sannan taci gaba da cewa
banyi ma alkawari ba amma idan kayi sa'a zan iya baka
isassun kudin da zasu fitar da kai daga najeriya ko kuwa
me ka gani?
Idan kuma kana ganin zaka koma gidan yayanka to
bismillah kana komawa zan bugawa yansanda waya in
sanar dasu cewa yayanka ne ya boye ka kasan kuwa sai
sun wahalar dashi ko kuwa kana son yayanka ya wahala
akan ka ta tambayeni tana zazzare idanu har yanzu ban
saki jikina da ita ba domin a shirye nake na ruga da gudu
aduk lokacin data taso min saidai kuma abin da yafi
damuna shine bindigar dake hannunta hakika ko ban
fada ma ba kai kasan ba abinda yafi kome hadari irin ace
mahaukaci ya tsare ka da bindiga da dutse ma yaya
ballantana kuma da bindiga zan tafi Fadil kakkausar
muryar tace ta dawo dani daga tunanin dana fara tana
tsaye akaina tana muzurai har yanzu bindigar na
hannunta tana kuma saitin kirjina cikin murya mai dauke
da tsananin gargadi tace dani
ina fatan gobe warhaka kana can kana dauki ba dadi da
sojojin kana Mukhtar kuma gobe warhaka ina daula otel
ina jiranka ka kawo min sarkar sannan ta zazzare min
idanu tace dani idan har karfe biyu da rabi tayi ban ganka
ba to zanyiwa yan sandan waya na fada musu cewa nasan
inda wanda ya kashe zainab yake zan kuma sanar dasu
cewa nasan yarinyar data tserar dakai daga kaduna daidai
nake kuwa don ayi musu bayanin kamannin Amina nasan
bazaka so ba ace budurwarka ta wahala saboda kai ko
zaka so Fadil? Ta tambayeni akwai alamar gajiya da
surutu a muryarta,
abu na karshe kuma fadil tace dani adaidai lokacin da
hannunta ke kokarin kaiwa ga kunamar bindigar gumi
yafara tsatstsafowa daga goshina domin nasan tana iya
harbawa tunda ba cikakken hankaline da ita ba kafin ta
sake cewa wani abu tuni har nayi kalmar shahada cikin
carbi azuciyata domin cikin yan dakikun nan ni ina
tsammanin tawa ta kare na rufe idona ina jiran naji
harsashi yasami matsugunni akirjina.
Kada ka tsorata fadil tace dani duk da yake nasan ka fara
tunanin ko ba kaina daya ba amma hakan ba zaisa na
harbeka ba domin harbinka yanzu na nufin ni da
mallakar sarkar(kishiyata hajiya Asma'u) har abada kenan
na tabbata babu mai iya sato sarkar idan ba kai ba ko
banza dai kai Jarumine.
Haka kuma da kake tunanin koni mahauciya ce banga
laifinka ba domin kuwa lokuta da dama tun bayan
rasuwar mijinmu na fara tunanin cewa kaina ya tabu
inasonka kasani cewa babu abinda ya haukatar da
kwakwalwata sai tsabar tunani da bakin cikin son kan da
mijinmu ya nuna wajen rabon gado kuma kishi da son
ganin na mallaki sarkar nan shi ya kara lalatar da
al'amarun har kaima najefa cikin Bala'i
Amma duk da haka taci gaba da cewa da ace nabarwa
Hajiya Asma'u sarkar nan gara nayi sanadiyyar hallakar
mutane dubu acikinsu har da kai
Allah kayi mana tsari da tabin hankali nace cikin zuciyata
yanzu na kara tabbatarwa da cewa wannan matar dake
barazana ga rayuwata ta haukace saboda tsabar son
zuciya kishi da kuma rashin tawakkali ga ubangiji idan
karfe biyu da rabi tayi ban ganka ba zan baiwa salman
izini da ya harbeka domin banga amfanin zamamnmu
aduniya ba saboda in har bakayi nasara ba to banga
amfanin rayuwata ba ban iya rayuwa da bakin cikin
kishiya kuma....
Ga mamakina sai naga hannunta yayi sanyi bindigar ta
fara rawa ahannunta kamar zata fadi sannan sai hawaye
ya fara kwaranyowa ta kan manya manyan kumatunta
masu kama da kwallon kafa dakin yayi shiru na dan
lokaci ita a tsaye nikuma a zaune ina ajiyar zuciya bakajin
komai sai sheshshekar kuka daga hajiya binta acan wani
bangare na gidan ana ta danna hon din mota yayi wata
kara fom fom har sau uku kafin akara na hudu hajiya ta
fice daga dakin kanta a sunkuye bayan na bari takai
tsakiyar furannin dake farfajiyar gidan sai na mike na
biyo bayanta da gudu gudu ina zuwa kofar gidan, direban
hajiya binta yayi ribar wane to direban na tambayi kaina
salman ne ko kuwa ?
Nan da nan zuciyata taki Na'am da tunanin da ta farayi
ba salman bane saboda salman kato ne mai fadin kafada
kamar kofar garejin mota wannan kuwa dake tukin
motar dan tsatstsama ne duk kuma da yake duhun cikin
motar bai bani damar ganin fuskarsa ba nasan fuskar
matsoratace dashi to wanene kuwa? Kamar anso a bani
amsar tambayata sai direban ya.......
Kamar anso a bani amsar tambayata sai direban ya
kunna fitilar dake cikin motar cikin zafin naman da ya
bani mamaki sai hajiya binta tayi sauri ta sake kashe
fitilar duk motsin da sukayi ya dauki abinda bai gaza
dakika hudu bane jikina ya dauki rawa zuciyata ta fara
bugawa da sauri direban motar ne ya sani rawar bakuma
wani bane sai
DAN TSOHON NAN MAI FUSKA KAMAR MATSATSTSEN
LEMON TSAMI
mai aiki a durba otel idan baka manta ba lokaci na karshe
da muka hadu dashi shine a durba otel lokacin dana
shake shi a jikin bango ina gargadinsa da cewa kar ya
sake yacewa yan sanda ya ganni.
Yau kuma gashi tare da hajiya binta motar taci taya kuuu
sannan ta hau titi da gudu.
**
Zuciyata cike da tunani da kuma matsanancin mamakin
ganin dan tsohon nan ahaka na nufo daki jikina kamar
anyimin duka kwanaki biyu da suka wuce nasha yiwa
kaina tambayar cewa yaya akayi har wani mahaluki zai
saci jiki ya shigo kasaitacciyar otal kamar durba ya kuma
kashe mutum batareda jami'an tsaron otel din sun
ganshi ba wannan yana bani mamaki to amma yanzu na
daina mamaki domin na samu amsar tambayata yanzu
kam na tabbata wannan dan matsatstsen tsoho dashi
hajiya binta ta hada baki harta sami damar halaka zainab
saboda nasan kudi yana iya sa mutum yayi komai koda a
dane ballanata ayanzu to amma abinda yake bani
mamaki haryanzu shine menene hadin hajiya binta da
dan tsohonnan da har zai zama direbanta?
Kuma shin yabar aikin otel dinne kokuwa. gaskiya fa naga
dan tsohon nan ya dage tsakaninsa da Allah yana baiwa
yan sanda bayanin kamannina a jarida ashe saye shi akayi
aka kuma shirya tuggun jefani bala'i taredashi to Allah ya
toni asirinsa.
Na nufi gado nayi zaman yan bori akai alokacinne naji
wani abu ya danyi kabarbar a cikin aljihuna gaban rigata
nasa hannu na zaro takardar ahankali manta sam sam da
ita na bude takardar na fara karantawa kamar haka
takardar da Badura tabani tun ina Kaduna.
.
TSARIN GIDAN KANAL MUKTAR.
Fadil inason kasan cewa wannan takarda na rubuta tane
don na sanar dakai wani abu dake cikin duhu wanda kai
baka sani ba na farko dai inason ka sani cewa duk abinda
yafaru akanka ba laifina bane ba kuma laifin yar uwata
Amira bane ko kusa babu laifin kowa acikinmu babarmu
hajiya binta ita ta takura min don na yaudareka kafada
tarkonta ni masoyiyarka ce Fadil kuma ina tayaka bakin
cikin abinda yake faruwa akanka ina kuma fatan Allah ya
taimakeka yakuma tsallakar dakai sharrin mahaifiyarmu,
ina kuma son na sanar dakai cewa mahaifiyarmu ba
kanta daya ba tun lokacin data dauki ranta ta kwallafa
akan sarkan nan ta gadonmu haka nan sai duk
Al'amuranta suka canza son zuciya da sharrin shaidan
suka rudeta ta fara tunanin mallakar sarkar ko ta halin
kaka.
Fadil da farko na dauka wasa take min daga baya sai naga
abin yafi karfin wasa ka yafeni Fadil badon ni ba wallahi
duk abinda nayi ma a da takura min akayi saboda
mahaifiyarmu tace idan ban yaudareka saita harbeni
nikuma danaji haka sai tsoro yakamani saboda ina gudun
ta harban matukar banyi abinda tace ba to tana iya
halakani domin kuwa ba kanta daya ba, tun farko dana
fahimci cewa kwakwalwarta ta tabu naso naga na sanar
da hukuma to amma saina tuna da cewa muddin na
sanar dasu cewa mahaifiyata tana barazanar kasheni to
gidan mahaukata zasu sata kasan kuma yadda gidan
mahaukata yake ba a basu kyakkyawan kulawar daya
kamata saboda an ga yawancinsu talakawane da marasa
gata kuma koda ana basu kyakkyawar kulawar ma
bazanso ace mahaifiyata tana cikin gidan mahaukata ba
bayan haka kuma Fadil zakaso kaji inda muka sami
Bindiga har muke wasa da ita akan rayuwarka bindigogin
dai su uku ne kuma na baban mu ne tun yanada rai
mahaifiyata ta sace su an neme su har an gaji bani na
sake ganinsu ba sai bayan da mahaifiyarmu ta fara shirin
tsunduma ka acikin bala'in nan sannan ta fito dasu ta
dauki daya ta baiwa Salman daya nikuma ta bani daya
amma ni bantaba amfani da tawa ba kada na cikaka da
surutu ni dai inason kasancewa ni masoyiyarka ce kuma
duk abinda kaga nayima har dukan da salman yayi ma
acikin dajin nan na kaduna nabar shi ya dake ka ne don
babu yadda zanyi dashine domin ina nuna alamar raina
ya sosu salman zai fadawa mahaifiyarmu domin shi ta
dauko shi haya ne domin yana kula da duk abinda nake
aiwatarwa akanka saboda ta lura da cewa tun lokacin
data nuna min kai amatsayin saurayin da zata tsunduma
cikin bala'in don ganin ta cimma burinta ta gane cewa na
kamu da
CIWON SONKA.
Kamar yadda nace abaya inason na sanar dakai wasu
abubuwa masu hadari guda uku dake tattare da gidan
kanal mukhtar na
1 farko dai inason kayi hankali idan ka shiga saboda
akwai karnuka masu cin naman mutane
2 na biyu kuma gidan yana dauke da kofofin shiga har
guda goma sha biyu kowacce kofa akwai kosassun
karnuka guda uku da kuma sojoji masu jajayen idanuwa
guda hudu idan kayi jimla zaka sami karnuka talatin da
shida kenan sojoji kuma arba'in da takwas ban da kuma
na kofar farko wacce ke dauke da sojoji goma shabiyu
kowannensu kuma bai dauki ran mutum abakin komai
ba.Sai kuma abu na 3 uku wanda shima yanada
muhimmancin gaske sarkar da mahaifiyarmu take son ka
dauko mata tana cikin wani gilas ne mai dauke da wata
irin fitilar lantarki mai tsananin haske babu kuma wanda
ya isa ya je kusa da gilas din sai inuwarsa ta fada kan gilas
din

Please Login or Register in order to submit comment