Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsini alburusan bindiga ne dan
sandan ya rike numfashi sannan ya taba kafadata ya nuna
min jikin bangon dakin bindigogi ne amakale suna reto
akalla sun kai talatin da biyar yawan bindigogin shiya
tuna min da labarin yakin duniya na biyu.
**
Ka taba harba bindiga? Dansandan ya tambayeni na
girgiza kai matsa nan kagani yace dani sannan ya fara
nuna min yadda ake amfani da ita idan ka taba nan saika
makala dan yatsanka ajikin kunamar bindigar saidai
kuma wannan bindigogin tsohon yayice bari na zabo ma
ta zamani dansandan ya sake nazarin bindigogin da suke
makale ajikin bangon dakin sannan ya zabo wata yar
gajeriya mai launin azurfa sannan ya bude gurin da ake
jera harsasai sai da ya tabbatar babu komai aciki sannan
yace dani idan ka rike kunamar ka taba nan saikaja
kunamar ahankali rike ka gani yace dani na karbi bindiga
jikina na rawa tunda nake bantaba rike bindiga ba
ballantana ma harna harbata Ja kunamar to ahankali
dansandan yace dani na rufe idona jikina na rawa sannan
naja kunamar bindigar tayi wata yar kara Dass wannan
shine ya zama karshen koyon bindigar abinda ya biyo
baya shiya sani jefar da bindigar dake hannuna duk da
yake da farko na dauka itace tayi karar to amma nasan
zolayar kaina kawai nake karar bindigar ya ratsa sararin
dajin daga dakin ina iya jin kukan namun dajin da suka
watse da gudu aka sake harba bindigar wannan karon sau
biyu aka harba ajere.
.
Sun dawo dansandan yace dani a rude tuni har bindigogi
biyu sun fado hannunsa cikin minti guda kuma ya jera
musu alburussai na juya a rude zan fice daga dakin
saboda ganin badura na waje bankula ba kafar
dansandan ta tade ni na fada da baya a tsakiyar dakin naji
kamar kwankwasona zai fashe na rasa abinda yake min
dadi domin nasan in har suka kama mu ba shiri to
kashinmu ya bushe to amma ba haka abin yakasance ba.
.
Fadil muryar badura ta daki dodon kunnena a sanyaye
rawar da muryarta keyi shiya tadani zaune zumbur
kwankwasona kamar zai fashe don radadi ganin fuskarta
kuma shi ya sani mikewa tsaye.
Sun biyo mu nan Fadil ta wani kamar zatayi kuka na shiga
uku Fadil bakaga irin bindigogin da sukazo dasu ba
sannan hawaye ya fara kwarara akan kyawawan
kumatunta.
Su wanene? Na tambayeta duk da yake kuwa nasan ko su
wanene din.
Yansanda ne tace dani dan sandan dake kusa dani
bindigogi biyu ahannunsa sai fuskarsa ta washe don jin
cewa yan uwansa sun iso.
Kaga munsami hanyar tsira kenan yace dani bai rufe
bakinsa ba sai mukaji dirin mota gidan kuma motar ta
nufo tana zuwa saita daki kofar gidan kofar tayi sama
sannan ta fado a ratattake abin yayi matukar girgizani
lokacin da motar tashigo a zatona zanga yansandan suna
firfitowa kowannensu da harbi ka ruga ahannunsa amma
maimakon haka sai naga yan fashin nan suna durowa
daga cikin motar babbansu shi yafara dirgowa dif.
Sannan sauran biyun suka fito da sauri kowannensu
bindigarsa ahannunsa na karshen daya fito shi yasani na
gane abinda ke faruwa yansandane suka biyo su yau rana
ta baci lokacin daya fito daga cikin motar hannun rigarsa
na dama rine yake da jan jini jajur yana tafiya yana
tangadi bayan rigarsa ma arine yake.
Duk abindake faruwa akan idonmu ke faruwa hakan
kuma baisa yan fashin sun lura damu ba badura tayi
sauri ta shigo cikin dakin. Rufe kofar dansandan yace
dani nayi sauri na rufe kofar amma muna iya ganin
abinda ke faruwa ta wasu kofofin dake jikin kofar kargen
ba'a dade ba yan sanda suka shigo gidan da gudu acikin
katuwar PATHFINDER irinta yan fashin tun kafin motar ta
tsaya yansandan suka fara dirgowa suna boye kansu
yansandan sun kai su ashirin hakan shiya tabbatar min da
cewa bayan motar tasu babu kujeru atunanina kuma a
tsaye sukazo saboda babu yadda za'ayi mota taci mutum
ashirin in har da kujeru acikinta. Tuni sauran yan fashin
sun shige cikin dakin nan mai kofar sama dayan da aka
harbe ne kawai ya rage bai shige ba yana saman kofar ya
zura kafarsa ta dama zai shige sai wani kurtun dansanda
ya hango shi sannan ya daga bindigarsa ahankali yaja
kunamar.
Karar bindigar ta amsa kuwwa acikin dajin dan fashin
yayi taga taga ya fada da fuska cikin dakin duk da yake
banga sauran abinda yafaru gareshi ba nasan cewa YA
MUTU babu wanda za'ayiwa harbi uku daya a hannu wani
abaya sannan a kirji sannanya rayu zaiyi wuya.
**
Bakajin komai a sararin dadin sai amsa kuwwar karar
bindigogin yansanda da yan fashin suna musayar wuta
wani dan siririn dansanda fari wanda nake tunanin bai
dade da shiga aikin ba yafito daga maboyarsa ya budewa
dakin yan fashin wuta cikin lokaci kankani yayiwa wani
bangare na dakin katakon kaca kaca dankararen dan
fashin ya leko dansandan na kokarin lodawa bindigarsa
harsashi abinka da sabon shiga maimakon ya sunkuya a
maboyarsa sai ya tsaya kerere atsaye shi a zatonsa yan
fashin sun tsoratane don haka suka daina harbi dan
fashin ya saita kan dansandan sannan yaja kunamar
bindigarsa dansandan yayi sama ya fado sannan cikin
abinda bai wuce dakika biyar ba jini ya rufe fuskarsa
baiko shura ba inajin lokacin da dansandan dake kusa
dani ya rike numfashinsa cikin razana shima yaga abinda
yafaru Badura na gefe guda tana kuka.
Ya kamata na fita na taimaka musu dansandan yace dani.
Kana jin zaka iyayin abinda ya gagari mutum ashirin? Na
tambaye shi
bazan iyaba yace dani kuma bazan iya tsaiwa anan ba
inaji ina gani suna kashe mana yan uwa don me yasa ake
biyana?
Kafin nayi kokarin yin wani abu tuni dansandan ya
bankeni ya bude kofar ya fita lokacin daya banke ni
sainayi sauri nakai idona wajen yar kafar dake jikin kofar
domin leken abinda dansandan zaiyi baiyi cikakken taku
biyu ba saiga kan dan fashin nan ya leko sannan kan
bindigarsa ya leko.
Zai harbeka na gargade shi cikin karaji amma na makaro
karar bindigar dan fshin ta sake ratsa sararin dajin
dansandan yayi taku biyu gaba sannan yafadi da baya BAI
KO SHURA BA.
.
Jin na kwallawa dansandan kira shiyasa badura ta nufi
inda na leka itama ta leka akan idonta aka harbe shi.
Fadil ta kira sunana tana kuka don Allah kayi min wani
abu mana ina tunanin kuma abin shine zai zama karshe.
Menene? Na tambayeta cikin mamaki da tausayin halin
data shiga
Fadi mana badura banason naga kina kuka wallahi
kukanki shi yake dada karya min zuciya inason naji wata
kalma daya ta fito daga bakinka Fadil tace dani.
Wacce kalma ce? Na tambayeta.
Inason kace KANA KAUNATA DA BAKINKA
sannan kuma inason kace ka YAFE MIN DUK ABINDA
NAYI MAKA ABAYA DON ALLAH FADIL ka taimakeni ka
fada karka bari na mutu da ciwon sonka ban samu cikar
burina ba.
.
Haba badura kidaina fadin haka wayace zaki mutu ? Na
yafe miki badura.
Nace da ita na kuma gane cewa ba laifinki bane laifin
mahaifiyarki ce bakida laifi agurina Badura har abada ina
rokon ubangiji kuma ya tserar damu MASOYIYATA na
yarda da kaunar da kikeyimin Badura.
Tunda kika sadaukar da rayuwarki gurin ganin kin tserar
dani
INASON KI BADURA
INASON KI KECE ABAR BEGENA HAR ABADA RABIN
RAYUWATA.
.
Badura tayi ajiyar zuciya bayanta yana fuskantar kofar
dakin ni kuma bayana yana fuskantar cikin dakin
kowannenmu yana kallon abin kaunarsa soyayyar badura
ta motsa cikin zuciyata sannan na dubata sai ta sunkuyar
da kai tana zubar da kwalla bansan ko kukan farin ciki
bane ko kuma bakin ciki ba.
Fadil.... Ta kira sunana cikin sassanyar muryarta mai
daukan hankalin ma'abocin bege muryarta da bazan taba
mantawa da ita bace har abada arayuwata bata karasa
fadar kalamin dake bakinta ba sai yansandan dake waje
suka budewa Kofar dakin da muke ciki wuta.
Babu mamaki gargadin dansandan nan danayi shiyasa
suka san da wasu acikin dakin harbin kuma shi ya shuka
bakin ciki mara Misaltuwa acikin rayuwata aduk lokacin
dana tuna da mutuwar Badura sainayita zubar da hawaye
ruwan harsashin bindigogin yansandan duk abayan
Badura suka sami matsugunni ta kwalla kara sannan ta
fado kirjina.
Wayyo Fadil..
Wayyo Fadil..
Amira Amira sannan tayi shiru ahaka ta mutu ajikina
bazan taba mantawa da ranar ba har abada.
.
16
Bayan da suka harbe yarinyar data mutu tana begena sai
suka tsaya da harbin a zatonsu sun gama damu gaba
daya sannan sai naji sun budewa daya dakin yan fashin
wuta kasancewar kofar dakin damuke ta zama kamar
rariya saboda ruwan alburusai da akayi mata saina sami
damar ganin abinda ke faruwa badura rungume ajikina
ina kuka ban motsa daga gurin ba bana kuma tsoron
mutuwa bandamu ba na mutu kona rayu sai bayan da
badura ta mutu sannan nagane irin matsanancin son da
nakeyi mata sannan ne kuma na gane cewa duk da yake
itace asalin fadawata acikin bala'in dake faruwa akaina
amma hakan bai hana nafi sonta fiyeda da Amina ba
mutuwar badura kamar wata fitilace aka kashe ya
arayuwata.
.
Fadil.. Amsar kuwwar kalaminta dana ji akaro na karshe
shiyaketa kururuwa a kunnena akoda yaushe nakan tuna
irin yadda take kiran sunana aduk lokacin dataso sanar
dani wani abu don haka tun farkon labarin nake cewa
(Muryar da bazan taba mantawa ba)
.
Gawar badura a rungume ajikina ina leke ta kofofin da
harsashi yayiwa kofar hawayena na kwarara akan
kumatuna
lokacin da yan fashin sukaga ruwan harsashin..
Lokacin da yan fashin sujaga ruwan harsashin yayi musu
yawa sannan suka ga halaka karara sai suka rude suka
fara fitowa ba'a ko taba kasa ba aka dasu babbansu ne na
karshen hancin bindigarsa ne yafara fitowa sannan barin
wutar yabiyo baya nan da nan duk yansandan suka koma
maboyarsu suka buya hakan shiya bashi damar fitowa fili
haryanzu yana barin wuta wani dan gajeren dansanda
baki kakkaura ya leko da bindigarsa sannan ya harba
harsashin ya wuce takan danfashin lokaci guda kuma
danfashin yaja kunamar bindigarsa harsashin ya sami
dan sandan a goshi nan take ya shure baiko matsa ba
alburushin kuma daya kashe dansandan shine ya zama
harsashi na karshe acikin bindigar danfashin lokacin
dayaja kunamar bindigar sai bindigar taki tashi ba'a jima
ba da faruwar hakan yansandan dake boye suka gane
abinda ke faruwa nan da nan danfashin ya kwalla kara
cikin razana.
Kada ka harbeni yace cikin karaji saidai ya dan makaro
wani kurtun dansanda tuni ya auna kafarsa barinsa kuma
yaga asarane don haka sai yaja kunamar bindigarsa dan
fashin ya kwalla kara mai tsanani duwatsu da koramun
da suke zagaye dajin suka amsa kuwwa sannan danfashin
ya fadi da fuska wannan shine yakawo karshen musayar
wutar da akeyi tsakanin yan fashin da suka kama mu da
kuma yansanda mintuna biyu da harbe shi sai yansanda
suka fito daga maboyarsu suka daure danfashin sannan
suka masa ankwa ahannayensa.
**
Na Ajje gawar badura ahankali ina kuka lokacin
yansandan suka fara warwatsuwa ko ina cikin gidan
menene abinyi? Na tambayi kaina shin bari zanyi su
kamani ko kuwa me ma zanyine? Nace ahankali muryata
na rawa sannan ne na kalli cikin dakin sosai ga mamakina
sai naga dakin yana da tsayin gaske da zan yi sa'a dakin
yana bullewa ta cikin wani to da sainabi tanan in zurare
to idan na gudu ma ina zani awannan kungurmin dajin?
Na tambayi kaina sannan ne dabara ta fado min tunda
yansandan basa tsammanin akwai wani mai rai agidan
me zai hana na buya awani lungun idan sun gama
abunda zasuyi sun tafi saina fito nasan dai da wahala ace
sun tafi da motocin yanfashin gaba daya saidai.....
Tunanina ya katse adaidai lokacin ne idona ya hango min
wani teburi acan karshen bangon dakin ba tebur dinne ya
dauki hankalina ba abinda bantaba tsammanin zan gani
bane a dakin nagani akan teburin a ajiye abayan
mazauninsa kan talfon ne
hakika shine abu na karshe da nake tsammanin zangani
agidan nayi mamakin abinda yan fashin sukeyi da talfon.
Cikin doki da kaguwa saina matsa kusa da talfon ne harna
dauka saina tuna da cewa kofar dakin a bude na barta
kuma nasan kowane lokaci daga yanzu yansanda zasu iya
shigowa dakin don haka saina koma batareda na dubi
inda Badura take kwance ba bayan na rufe kofar saina
koma na dau kan talfon din sannan akaro na biyu tun
sa'ar dana fada cikin masifar saina bugawa yayana waya.
.
Wane ne ?
Aka tambaya acan daya bangaren gabana yafadi danaji
muryar yayana ce da kansa, nine fadil nace dashi
muryata na rawa.
Fadil yayana ya kira sunana muryarsa na rawa.
A ina kake? Ya tambayeni me kuma ke faruwa? Batareda
bata lokaci ba saina bayyana masa duk abinda yafaru a
gurguje tun daga farko har karshe sannan nace dashi ga
halin danake ciki kuma Badura ma gata nan agabana sun
harbeta yayana yayi shiru sannan yace dani saurara Fadil
da farko ina son nayi maka albishir dacewa ka kusan fita
daga sharrin da akayi maka.
Ban gaskata abinda naji ba.
Me kake nufi? Na tambaye shi
kwana biyu kenan da kama hajiya binta mahaifiyar su
badura sannan salman ma an kama shi dukkansu tare da
tsohon nan ma'aikacin Durba otel.
Amira fa? Na tambaye shi cikin doki.
Amira batada laifin komai itada yar uwarta badura.
Yaya akayi aka gane basuda laifi?
.
Ranar Talata din data wuce wasu jami'an bincike na
yansandan ciki dake aiki a daba otel kaduna suka zo da
shaidar da take nuna cewa hajiya binta itace tayi Ummul
Aba'isin faruwar komai sannan abin mamakin ma shine
ita wannan yarinyar ba'a cikin otel din aka kasheta ba
saceta akayi ta hanyar hada baki da dan tsohon nan mai
aiki a otal din
bayan da suka kasheta ne suka shigo da ita cikin dare tare
da taimakon dan tsohon nan suka kwantar da ita lokacin
dakaje dakin mai Lamba 3 daman kusan abin a shirye
yake....
.
Kana nufin kace ba'a cikin otal din aka kasheta ba? Na
tambaye shi.
Ko kusa ba'a ciki bane kasan fa irin matakan tsaron dake
otal din bazaka taba yin wani abu na rashin gaskiya ba
batareda an kama ka ba itama wannan bindigar dan
tsohon ne ya shiga da ita saboda hanyar da ma'aikatan
otel din sukebi babu na'ura mai kwakwalwa wadanda
kuma itace take nuna duk wani abu da mutum ya shiga
dashi otal din saboda haka dan tsohon nan shi ya
shigawar da hajiya binta da bindigar ciki ita kuma ta
shigo ta hanyar da kowa ke shiga ta kama daki a hawan
bene na uku shine ta bari saida asuba ta hayo hawan
benen ku ta harba bindigar domin ta saka kafito ka kuma
fada tarkonsu.
.
Nayi shiru cikin mamaki to tayaya akayi kukasan
wannan? Nasake tambaya.
Su Jami'an tsaron otal din sunada na'ura mai kwakwalwa
wacce take.
Su Jami'an tsaron otal din sunada wata na'ura mai
kwakwalwa wacce take daukar duk wani abun dayake
faruwa a otal din ko waya aka buga saita dauka bakuma a
binciken abinda ta dauka sai karshen wata to a irin
binciken ne aka gane duk irin makarcin da aka shirya
hatta ita badura da amira duk dakinsu daya anan otel din
da kake zaune shima salman anan hajiya binta takama
masa daki don haka duk lokacin da zasu tattauna sai
hajiya binta ta tarasu a dakinta saidai kuskuren da tayi
bata san da wannan na'ura mai kwakwalwa ba wacce duk
abinda suka tattauna yana cikinta kaga kenan banajin
akwai sauran wani abu da zakaji tsoro.
To yansandan da suka ritsani anan yaya zanyi dasu?
Zan bugo musu waya yanzu tunda suna da salula saimu
sanar dasu abinda ake ciki sannan wani abin kuma
yayana yaci gaba da cewa tare muke da kanal muktar
yanzun nan yazo domin bai dade da zuwa ba ka bugo
waya shima yazo akan maganarku da Amina dakuma
yadda za'a tserar dakai to inayi masa wannan bayanin
danayi makane ka bugo waya yanzu ma gashi nan akusa
dani sannan ya danyi shiru.
.
Fadil ina jakarka take? Ya tambayeni gabana ya fadi sai
yanzu na tuna da jakata da yayana yabani nayi shiru ina
tunanin inda na yarda ita.
Na manta inda.... Ya katse ni kafin in karasa.
Shikenan yayana yace dani ta cikin talfon din jiya muka
tsince ta acikin motar da kukayi hadari watakila zakaso
jin amfanin baka ita danayi to dalilinta shine a kasanta
akwai wata yar karamar rikoda mai dauke da maganganu
sanin yaudarar masu aikata muggan laifuka ne yasa
nabaka ita saboda tun lokacin dana hanaka tafiya ka nace
sai ka tafi saina ga ya dace na baka ita domin nayi tunanin
wani abu sakamakon haka zai iya faruwa akanka domin
su daman yawancin mutane irin hajiya binta sunfi
yaudarar yan yara samari kamar ka kuma jakar tana da
muhimmanci domin tana daya daga cikin abinda zai fitar
dakai a kotu kuma duk maganar da kukayi da badura
hajiya binta da amira dakuma salman duk suka ciki
wannan ma shaidace da zata iya fitar dakai daga karshe
banason barka cikin duhu ita wannan jaka ta yan sandan
ciki ce C.I.D yace dani.
Kana nufin kai CID ne yaya?
Banason irin wadannan maganganun ta talfon yace dani
abin yayi matukar girgiza ni duk da yake bai fada min da
bakinsa ba na tabbata yayana dansandan cikine CID Tab
abin da mamaki.
Gashi nan Kanal mukhtar yana buga musu waya waya
muryar yayana ta sake ratso talfon din mintuna biyar
dayin magana da yayana ta talfon sai abubuwa suka sake
juyewa awannan karon daga bakin ciki da kuntata zuwa
farin ciki abin kawai da ya rage farin cikin shine mutuwar
Masoyiyata Badura aka kwankwasa kofar dakin banyi
fargabar komai ba sai kawai na bude domin nasan su
yayana sun gama aiki dansandan yana tsaye sauran
yansandan kuma a bayansa.
Zo mu tafi yace dani na juya nayiwa badura kallon karshe
tana kwance lallauan gashin kanta mai kyalli ya rufe
idanunta haryanzu badura kyakkyawace duk da yake
kuwa ta MUTU wasu yansandan biyu suka shigo da gado
irin na asibiti suka dora badura akai sannan suka dauketa
suka tafi da ita na fara kuka saboda bakin cikin rabuwa da
masoyiyata badura.
Dansandan ya dafa kafadata ya jani har zuwa cikin mota
muna zuwa ya tayar da mota sauran yansandan suka
dane direban motar yaja mukayi gaba wata barewa da
wani dan zaki suka shige dajin da gudu lokacin da daya
sandandan ya harba bindigarsa sama na juyo na kalli
gidan yanfashin bazan manta dashi ba domin nanne aka
kashe MASOYIYATA BADURA.
**
Wata daya kenan da rasuwar badura abar kaunata Yau
lahadi daya ga watan janairu ina zaune acikin dakina dake
gidan yayana amina na zaune acikin daya daga cikin
kujerun da suke dakin tana zaune acikin daya daga cikin
kujerun da suke dakin tana fuskantata fuskarta cike da
haske dakuma farin cikin jin cewa yau saura kwana goma
ayi bikinmu da ita shari'ar da akayi bata dauki tsawon
lokaci ba saboda shaidun da nake dasu kuma itama
hajiya binta ta fada da bakinta cewa ita ta kashe zainab
daga karshe an kaita gidan mahaukata saboda an
tabbatar ba kanta daya ba shikuma salman an yanke
masa hukuncin shekara biyar agidan maza saboda
taimaka mata dayayi shi kuma dan tsohon nan an yanke
masa hukuncin daurin shekaru goma sha biyar.
.
Aka kwankwasa kofar amina ta dubeni mukayi murmushi
inajin hajara ce tazo ta tsokaneni tace dani babu mamaki
nace ina murmushi.
Shigo ko wanene amita tace gabana yafadi zuciyata tai
kunci da farko na dauka Badura ce ta dawo amma nasan
nida badura har abada wannan AMIRA CE.
Ina kwananku? Tace damu lafiya kalau Amina tace.
Sannu da zuwa amira
nace da ita bata amsa ba saita miko min wani dan
karamin akwati na roba sannan tace sai anjima tafice
daga dakin Amina ta kalleni nima na kalleta sannan na
bude akwatin kamshin turare ya daki hancina wata
takarda ta fado daga cikin akwatin nan danan na dauka
na fara karantawa..
.
Daga Masoyiyarka BADURA.
Lokacin da kake karanta wasikar nan banajin akwai
abinda zaka iya min daya wuce addu'a ya Masoyina. Tun
daga ranar da naga babata ta tsundumaka cikin bala'i
saina yanke shawarar tserar dakai saidai kuma jikina
yabani cewa da wahala na tsira da rayuwata shine naga
ya dace na rubuta maka wasikar bankwana da msoyi
don haka kaji nace lokacin da kake karanta wasikar to ni
kam na riga ku gidan gaskiya masoyina abu daya nake so
ka rike a rayuwarka Fadil shine duk abinda zakayi kada ka
sake kabi son zuciyarka domin shi yake kawo dana sani.
Daga karshe inason ka sani cewe na mutu da masifar
sonka ina kuma baka shawarar ka auri yar uwata Amina
domin ita ta dace dakai ina kuma rokonka idan kun haifi
'ya mace kasa mata sunan BADURA.
domin ka rinka tunawa da wacce ta mutu domin tserar
dakai.
Daga karshe nake cewa Allah yasa ina cikin Matanka A
Aljannah Amin.
Daga Marigayiya Badura Abar kaunarka A Kullum.
.
Na aje wasikar a hankali hawaye na kwarara akan
kumatuna sai hakuri Fadil.... Amina tace dani muryarta
na rawa ita kanta tasan matsayin badura azuciyata
sannan Amina ta dauko dan akwatin ta mika mini.
Kaga abinda yake ciki Fadil tace dani abinda nagani acikin
akwatin zobe ne na zinare yana kyalkyali wata
kyakkyawar fulawa kuma acikin akwatin itace ke bada
kamshin dake tashi.
A rubuce ajikin ganyen fulawar sunana ne Badura ta
rubuta
DON'T FORGET WITH ME FADIL.
fadil kada ka manta dani na dauki zoben nasa a hannuna
sannan na fara juya fulawar a hannuna hawaye na zuba
akan fuskata.
.
Bazan taba mantawa da ke ba Badura. Nace ahankali
cikin zuciyata abinda nakasa baiwa kaina amsa shine
Anya kuwa zan sake son wata 'ya mace kamar Badura ?
Na Tambayi Kaina.
.
NAZIR ADAM SALIH (NAS).
.
KARSHE.
.
KIBIYAR AJALI
Na
Nazir Adam Salih
Ebook creator Shuraih Usman 99%
.
Zaku iya downloading wasu da dama daga cikin ebook namu ta hanyar ziyartar babban shafin mu na Hausaebook akan wannan adireshin www.shuraih.waphall.com
Wannan ebook din an sake shi ne A matsayin Happy Sallah ga daukacin Al'umman musulmai baki daya ,
Asha karatu lafiya


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment