Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abu daya ya rage masa jin dadi
shine bashida 'da ko daya a duniyar nan sai Agolansa
daya tal wacce yake mutuwar so kamar ransa wannan
Agola tasa ya dauke take ne kamar yar da ya haifa AMINA
itace Agolan Kanal Mukhtar.
.
Dakin yayi shiru bakajin komai sai motsin gayayyaki da
furannin fulawa dake ta gugar tagogin gidan hakika yanzu
ne na fahimci sabon salon danake shirin shiga duk da
cewa kuwa bansan abinda su badura ke nufi ba da
ambatar sunan Mukhtar.
Na dago kaina muka hada ido dasu sannan nace da ita
Menene to idan na san shi? Batareda ta dubeni ba sai taci
gaba da cewa
.
Shekaru biyar da suka wuce mahaifinmu Alhaji Ahmad ya
rasu a sakamakon hadarin jirgin saman daya rutsa dasu
in zaka iya tunawa yana daya daga cikin manyan masu
kudin dake kano yana kuma daga cikin manya manyan
marubuta littafi na kungiyar RAINA KAMA munyi bakin
ciki da mutuwarsa duk da yake yana nuna mana
bambanci tsakaninmu da yan uwarmu ya mutu yabar
mata biyu daga cikinsu akwai mahaifiyarmu Hajiya binta
dake zaune a unguwar tarauni cikin birnin kano sai kuma
kishiyar babarmu Hajiya Asma'u
sannan ta dubeni tace dani Hajiya Asma'u itace mowar
babanmu yafi sonta akan kowa daga ita sai yarta sai
abinda suka fada shi akeyi agidan idan baka manta ba
babanmu ya rubuta wasu littattafai guda biyu tun kafin
ya rasu littattafan da suka daga karshen bahaushe
aduniya sun sami karbu acikin najeriya gaba daya harma
wadanda basa jin yaren hausa sunyi kokarin koyonta
domin su sami damar karanta littafin Akwai kasashen
waje da dama da sukayi murna da fitowar littafin
musamman ma dayake yana taimakonsu wajen koyon
harshen hausa an gabatar da littafin shekaru biyar da
suka wuce tun kafin mutuwar mahaifinmu ya samu
kyaututtuka da dama daga manyan mutane dake cikin
birnin kano daya daga cikin kyaututtukan itace wata
SARKAR ZINARIYA wacce wani kwara ya baiwa babanmu
shi wannan kwara yana matukar son yaren hausa kuma
ya koyi yaren hausa ne saboda yin hulda da hausawa
wajen cinikayya mutumin daya koya masa hausa shine
BABANMU
Don haka lokacin da aka gabatar da littafin sai kwaran ya
tafi kasar waje a can yasa aka kero masa wannan sarka ta
zinare ajikinta an rubuta kalmar R.K da ruwan daiman
wato ma'anar kalmar R.K shine RAINA KAMA
Dalili kuwa shine littafin yafito ne ta karkashin Kungiyar
Raina kama kano.
.
Atakaice dai mahaifinmu ya raba gadonsa tun kafin
rasuwarsa da wata daya mun sami dukiya mai tarin yawa
saidai kuma abinda ya bakanta mana rai shine baiyi
rabon gado da sarkan nan ba da ya tashi sai yayi son kan
nasa ya baiwa yar lelen yarsa sarkar wato yar gidan hajiya
Asma'u kenan kada kayi tsammanin sarkat tanada wani
kudi ne mai yawa sam sam kudinta bai wuce naira
milliyan biyu ba da dubu dari biyar.
Fadil' badura takira sunana cikin wata murya wacce
taban tsoro.
Inason sarkar nan ta dawo wajena
Ta yaya zata dawo wajenki? Na tambayeta ta dubeni
sannan tace dani haryanzu baka gane abinda nufi ba in
baka gane ba to bari na karasa ma labarin
bayan mutuwar babanmu hajiya asma'u tayi aure bayan
shekara daya mutumin data aura kuma shine Kanal
Mukhtar yanada gida sultan road cikin jihar kano in baka
sani ba kuma na bari nafada ma duk cikin jihar kano in
ka dauke gidan Gwamna babu inda yakai gidansa tsaro.
Anan ne kuma nake so kaje ka samo min sarkar shiga
gidan wata sabuwar duniyace amma shiga gidan yafi
shiga hannun yan sanda awajenka ko har yanzu baka
gane abinda nake nufi ba?
Sannan ta kyalkyale da dariyar mugunta kada kayi
tsammanin shiga gidan kanal mukhtar kamar shiga
gidanku ne amma duk da haka gara masu gadin gidan su
harbeka da ace yan sanda sun harbeka acikin Jama'a
me nayi yan sanda zasu harbeni na tambayeta
'baka ma sani ba kanajin zaka
KASHE ZAINAB A BANZA NE ?
.
Kayi a hankali Fadil badura tace domin dole ne kayi
abinda nasaka domin itace hanya mafi sauki agareka
itace hanyarka daya Tal da zaka iya tsira idan ka kawo
sarkar kudin da zamu baka ya isheka kabar kasar nan
kaga ka tsira kenan.
.
Hakika yanzu daidai nake dana shaqe wuyan badura na
karyashi saboda rashin kauna sannan na dubeta nace da
ita
'idan nace bazanyi ba fa me zakiyi ?
Kada ka batawa kanka lokaci Fadil tace dani sannan ta
mike tsaye ta bude wata loka ta dauko wasu fararen
takardu masu dauke da rubutu ta jefo minsu hade da
wata jarida sannan tace dani
ni zan tafi sai kayi kokari ka san yadda zakayi ka isa birnin
kano sannan tayi min murmushi tace dani.
Bakada mafita dole ne kayi abinda nasaka babu damar
kaucewa kasan daman hausawa sunce
KIBIYAR AJALI
FALKE BAYA KAUCE MATA.
Sannan ta tura kofa ta juyo ta kalli su Salman da daya
yarinyar da nake tsammanin itace Amira Kuzo mu tafi
tace dasu suka bita kofar dakin adaidai lokacinne amira
ta juyo tace dani mu hadu a daula otel kano idan kayi
nasara idan kuma bakayi ba sai nace mu a hadu a filin
sukuwa wajen harbe
rufe kofar dakince ta tabbatar min cewa sun tafi na dubi
takardun nan da bansan abinda suke nufi ba ya zama
dole na duba su don haka sai na gyara zama na buda
jaridar an rubuta cikin manyan haruffa kamar haka
WANI DAN BINDIGA DADI YA HARBE MA'AIKACIYAR DABA
OTEL KADUNA
.
Guntu labarin kuma basai na fada maka ba yansanda
sunata nemansa ruwa a jallo an kuma rufe kowace hanya
da zata fita daga jihar kaduna....
Babu motar da zata fita batareda yan sanda sun yi mata
bincike ba. Abin dayafi bani tsoro shine dan tsohon nan
motsatstse ya bada shaidar cewa ya ganni na fito daga
dakin da zainab ta mutu akaryarsa cewa yayi wai har da
bindiga a hannuna wannan shaida ita zata kara tabbatar
da badura daga zargin ko bakinmu daya da ita
.
HUDU 4
Lallai Kibiyar Ajali hakika yanzu nasan kibiyar da badura
ta harben da ita ta sameni a makogoro samun da ta yi
min ina tsammanin shine zai zamo ajalina duk da yake
har yanzu inada damar da zan zare kibiyar daga jikina
batareda tayi sanadiyyar ajalina ba
saidai kuma damar kadan ce.
Mintuna biyar suka shude kamar wasa haryanzu
kwakwalwata bata fara aiki ba aduk lokacin dana fara
tunani sai tunanin abinda badura tace dani ya ruguza
tunanina kamar yadda ruwa ke ruguza tubalin yashi
'inason sarkar nan ta dawo wajena
idan kayi nasara ladan da zamu bakaya isheka kabar
kasar nan kaga ka tsira kenan.....
Wannan sune maganganun da suke rikita min
kwakwalwa.
Hakika badura taso kanta tayi amfani da rashin imaninta
wajen ruguza rayuwata acikin zabin data bani babu wani
mai sauki kamar yadda tace wai idan nayi nasara zan bar
kasar wannan kuma wani abu ne da ba zai yu ba idan na
bar kasar wajen wa za ni shin kuma ni da sake haduwa da
yan uwana sai a lahira kenan?
Duk wannan mai sauki ne a kan shiga satar sarkar gidan
kanal mukhtar abinda na tabbatar ma kaina shine
kwanana yazo KARSHE.
Badura ta bani zabin shaidan dolene na kira shi da zabin
shaidan domin kuwa babu mai sauki daga cikin biyun
idan nayi nasara nabar dangina yan uwa da abokaina
kenan har abada?
Idan kuma banyi nasara ba to wannan ba sai na fada ma
ba na mutu kenan dolene na samu zabin kaina na uku
idan har kuwa inason tsira ya kuma zama dole na rama
abinda badura tayi min sai kuma na samo wanda ya
kashe zainab in har ina raye
wannan shine alkawarin dana daukarwa kaina lokacin da
nake zaune acikin gidan nan wanda bansan ko awacce
unguwa yake ba.
.
Abinda yafi damuna yanzu shine hanyar da zanbi naje
kano na farko dai ko wace hanya acike take da masu
jajayen idanu suna nemana gashi kuma banida mota
bakuma kudi to idan ina da mota ma ta ina zanbi?
Kuma wajenwa zani idan na isa kanon domin na tabbata
yanzu yayana yasan halin danake ciki ahalin yanzu nayi
alkawarin bazan taba tunkarar gidanmu ba sai na abinda
ya turewa buzu nadi.
.
******** ***** ******* ********* *******
.
Sa'o'i biyu suka wuce batareda nasami wata kwakkwarar
shawara ba don haka sainaga zama bazaiyi min ba nan da
nan na tashi na nufi kofar dakin danake tsammanin zata
fitar dani har farfajiyar gidan na bude kofar ga mamakina
sainaga wani makaken lambu mai dauke da kayan
marmari iri iri ya zagaye ginin dakin danake ciki Lambun
yana zagaye ne da wata makakiyar katanga wacce bana
tsammanin zan iya tsallakata saidai idan nayi amfani da
tsani ya kamara na dan zagaya naga tsarinsa don haka
saina rufe kofar dakin na fito waje kafafuna babu ko
takalmi nabi wata yar siririyar hanya wacce nake
tsammanin zata kaini tsakiyar lambun.
.
Koda na juya na kalli dakin dana fito daga ciki sai naga ya
zama dan kankani acikin tafkeken lambun sannan naci
gaba da tafiya ahankali nabi wata yar siririyar hanya
wacce bishiyoyi sukayi mata inuwa tako wanne bangare
saida na wuce bishiyoyin nan sannan na hango wata
tafkekiyar kofa wacce nake tsammanin zata iya fitar dani
daga lambun batareda danayi tunani sau biyu ba sai
kawai na na nufi kofar da sauri tun kafin na isa kofar na
fara jin karar motoci suna ta wucewa ta kofar lambun
katuwar hanyace motoci sunata zirga zirga dada can
kuma tsallaken titin manya manyan kantuna ne wasu ana
saida kayan masarufi wadansu kuma ana ta ciniki iri iri
daban daban wata katuwar mota ta wuce kamar guguwa
adaidai lokacinne na hango wani shago wanda ganinsa
yasa gumi ka karyo min katon shagone a shafe da fentin
an zagaye kofar da wasu bakaken karafuna wani inyamuri
kato fari mai kaurin wuta yana zaune a kofar shagon
yanata girgiza kai kamar kadangare ga dukkan alamu dai
yana sauraron turawane a gefen hadun dinsa kuma wani
katon katako ne fari yana dauke da rubutu cikin harshen
turanci
EMAKA BUSINESS CENTRE
daga kasan katafon kuma anyi zanen wani mutum da
wayar talfo a hannunsa ko banfada maka ba zaka iya
tunanin cewa wannan shine mataki na farko da yakamata
na dauka domin fita ta daga kaduna batareda na bata
lokaci ba saina juyo aguje na nufo dakin ina zuwa na
bude shi na shiga da sauri batareda na rufe kofar ba
agogon bangon dakin ya nuna karfe goma sha biyu na
rana na bude cikin jakata na dauko wata rigar sanyi mai
hade da wuya nasa har na juya zan fita daga dakin sai
Har na juya zan fita daga dakin sainaga wani katon bakin
tabarau akan tebur nayi tsammanin na salman ne nan da
nan na dauka nasa na dubi fuskata a mudubi nayi
murmushi abinda nagani a mudubi shiya bani dariya
zaka iya kirana da Uche ko kuma chinedu na zama kamar
inyamuri duk wannan abin yafarune acikin abin da bai
gaza minti biyu ba.
.
Da gudu da sassarfa na isa kofar lambun ina fata dai
bazaka iya mamaki ba da irin shigar danayi wani abune
daka sani kusan kowa ahalin yanzu yasan halinda ake ciki
a kaduna yakuma san kamannina a hoto to amma yanzu
zaiyi wahala ka ganeni in dai har kayi la'akari da hoton
dake jikin jarida
banyi mamaki ba danaga na tadda kofar lambum a bude
kofat tayi kara kirr a daidai lokacin dana maida ita na rufe
bayan nayi jira kamar na dakika talatin na samu na
tsallaka titin.
Tun kafin na karaso shagon sainaga inyamurin ya shiga
shagon ni kuma nabishi abaya katon shagone wanda ke
dauke da manya manyan kujeru uku bangon dakin a
lullube yake da takarda ruwan gwal kana shiga dakin
zakuyi ido hudu da kayuwan talfo biyar uku daga cikinsu
jajaye ne biyun kuma farare duk wannan na kula dashi
ne cikin abinda bai wuce dakika hudu ba.
Menene lambarka? Inyamurin ya tambayeni cikin
harshen turanci
na zaro biro da da wata guntuwar takarda daga aljihuna
na rubuta masa lambar talfon din yayana dake kano
sannan na mika masa zauna acan ya nuna min daya daga
cikin kujerun da take fuskantar fararen kayukan din nan
guda biyu banyi cikakken minti daya da zama ba sai ya
miko min kan talfon,
tun kafin na karasa da kan talfon kunnena sai naji muryar
hajara tana cewa wanene?
Nine fadil nace da ita hajara matar yayana ce dake kano
kuma a wajenta na girma tun lokacin da iyayenmu suka
rasu a samakaon hadarin mota sai babban yayanmu ya
daukeni yakaini wajenta alokacin shekararsa uku dayin
aure tana matukar sona musamman ma dayake taga
banida kiwa da rashin jin magana
fadin kana ina? Tausayinta ya kamani saboda sheshshekar
kuka data farayi kada ki damu nace da ita kedai ki saurare
ni da kyau kiji abinda zan fada miki batareda najira
tasake tambaya ba sainaci gaba da cewa
don Allah hajara kiyi maza ki tafi gidan kanal mukhtar ki
sami amina idan kin sameta kice mata ni na aiko ki kice
mata ina tudun wada kaduna kuma ina bukatar taimako
da gaggawa domin ya zama dole nabar kaduna yau
dinnan kuma kice mata wannan itace damata ta karshe
ko na fice daga kaduna yau ko kuma yansanda su kamani
kinaji na hajara?
.
Na tambaya naji shiru na dan lokaci sannan sainaji
hajara tace dani fadil nace na'am ta sakeyin shiru jikina
ya fara rawa
hajara nayi kiranta yaya naji kinyi shiru in wani abu ne ya
faru ai saiki fada min ba sai kin boye min ba kinsan dai
wannan abu kaddarace kuma dole ne ta faru akaina
amma abinda nake so ki gane shine bani nayi kisanba
sharri akayi min ko kin yarda kasheta ? Wannan magana
danayi ita ta dawo da hajara cikin hankalinta
haba fadil tace dani daidai rana daya ban taba zaton zaka
iya kashe akuya da ranta ba balle mutum abinda
abinda yasa kaji nayi shiru shine aminar da kake fada
bata nan tun jiya da muka sami labarin abinda ya faru
tazo gidan nan da jarida wacce ke dauke da hotonka tana
kuka tace dani zata tafi kaduna wajenka ko nasan inda
zata sameka?
Nace mata wallahi bansan inda zata sameka saboda
kaima bakasan kowa ba shine tace ita dai saita tafi
nemanka don tace wai akwai gidan yan uwansu a kaduna
batace dake ga inda zataba?
Na tambayi hajara
Nima wallahi bata fadamin ba shikenan to nace da ita
saura kuma abu daya don Allah Hajara idan yaya yadawo
karki ce masa na bugo waya
saboda banason hankalinsa yatashi kema kuma kar
hankalinki ya tashi kinsan..... ta katseni da cewa
to fadil yaya zakayi ka tsira daga wannan sharrin? Kuma
tayaya zaka fice daga kaduna? Babu komai nace da ita ke
kedai kitayani da addu'ar nasara saina samo wanda ya
kashe zainab nakaiwa yan sanda shi a hannu.
Tayaya fadil? hajara ta tambaya haba hajara kin sanni fa
ban taba cewa zanyi abu na kasa ba
hajara ta fara kuka
fadil don Allah karka yadda su kamaka kaga in sun kama
ka.....na ajiye wayar talfon din bazan iya jure kukan da
hajara takeyi ba domin zai iya karya min zuciya basai an
fada ma ba kai kanka kasan bana bukatar karayar zuciya
ahalin yanzu.
**
Motsin wani abu da bansan ko menene ba shi ya tashe ni
daga nannauyan barcin danakeyi na tashi firgigit saura
kadan na fado daga kan benin danake kwance magariba
tayi duhu ya mamaye ko ina cikin lambun inka dauke
wani farin kyandir daya haskake kofar dakin dasu badura
suka kawoni. nayi mamakin yandda akayi bacci ya
daukeni a lambun tun lokacin dana dawo daga wajen
talfon nan saina koma daki na sako karamar riga na dawo
cikin lambun na fara tunanin abinda yakamata nayi
shawarar da na yanke itace idan dare yayi saina sulale
nabar gidan tunda a lokacin duhu bana tsammanin akwai
dan sandan da zai iya kamani hanya daya dana ga zata
fitar dani itace naje wajen wanzami ya aske min kaina
gaba daya nasa kaya masu datti
Idan duhu ya karayi sai naje tasha na shiga motar katako
irin wadanda suke safara daga kano zuwa kaduna nasan
in ba tsautsayi ba da wahala su kamani domin wadannan
motocin anfi bincikar kayan da suke dauke dashi sama da
mutanen cikinsu yanke shawarar keda wuya sainaga ina
bukatar hutu kuma gashi inuwar dake lambun tana da
sanyi sai kawai na kwanta.
.
Motsin danaji yabani tsoro na duba sai naga dakin a bude
da kuma tabbata a rufe na barshi lokacin dana fito dadin
da dadawa kuma sai naga dakin gauraye da haske hakane
ya tabbatar min da cewa akwai wani acikin dakin dan da
nan na mike tsaye na nufi dakin da sanda ta hanyar boye
jikina abayan bishiyoyin da furannin da sukayi layi a
lambun taku ashirin daidai yakaini kofar dakin sannan sai
na tsaya cak ina sauraron wani abu dayasa tsigar jikina ta
tashi in dai ba kunnena ne ya fada min karya ba toh naji
kamar jiniyar yan sanda kafin na karasa tunani tuni duk
zagayen unguwar da lambun yake ta gauraye da kukan
jiniya ko ina kudu da yamma harda arewa bakajin komai
sai kukan jiniyar yan sanda batareda sanin hakikanin
abinda zanyi ba saina dare wata bishiya dake kofar dakin
na hau can samanta na mike tsaye ina hangen bayan
lambun
Tafaru ta kare nace cikin zuciyata abinda na hango ya
kada min hantar cikina yansanda sun zagaye lambun
kamar kasa ahalin yanzu kukan jiniyar tayi sauki bakajin
komai sai kwat kwat din gudun yansanda a iya hangena
ina iya ganin kudu arewa da yamma amma bana iya
ganin gabas saboda manyan benayen da sukayi shinge a
bayan lambun ta bangaren gabas da suka zagaye lambun.
.
Karar Bindiga ya cika min kunne ina tsammanin yan dadi
bindiga ne suke gargadina da cewa sunzo harsashin ya
daki gilas din tagar dakin dake kasana wani radadin zagi
ya mamaye hannuna na dama dake rike da reshen
bishiyar dana ke kai na shafa sai naji danshi a hannuna
raina ya baci dana tuna da badura duk abinda akayimin
ita ta janyo min kada kayi tsammanin zan tsaya su
kamani kamar mace ni ma fa ba karamin shaidani bane
idan aka takura min duk da yake nasan ko wanene ni dole
ne in tsorata ni dai har kaga yawan yansandan da suke
jirana awaje.
.
Tunanin badura ya sake fado min in dai akwai yadda
zanyi dolene nayi kokarin tserewa yansandan nan ko ta
halin kaka inaso ace koda sun kamani to ya zama na
rama abinda badura tayi min na tashi tsaye na hangi cikin
lambun sainaga kamar yansandan sun fara shigowa ga
wanda baisan me ake kira yaki ba idan yaga yawan yan
sandan da suke jirana sai yayi zaton wannan shine farkon
yakin duniya na uku batareda na sake tunanina sau biyu
ba sai na saki reshen bishiyar nayi kasa na tabbata ko
wanene ke cikin dakin badan sanda bane yakuma zama
dole naga ko wanene kafin nayi shirin gudu
abu daya dayake bani kwarin gwiwa shine yansanda
bazasu motso kusa dani cikin gaggawa ba domin suna
tsammanin inada bindiga
Na daki kofar dakin da kafata ta bude na shiga ina dube
dube banga kowa ba kofar wani dake fuskantata a bude
take na nufi kofar da dan sanda tun kafin na karasa
sainaji kamar mutum ne ke numfashi sama sama a dakin
na tura kofar ahankali na shiga.
.
Tana kwance a gadon da suka daureni tasha dauri da
igiya kamar damin gero tana numfashi daidai jajayen
kayan data zo dasu dakina a otal din daba sune ke jikinta
saidai yanzu duk sun yayyage alamun tasha wuya
awajena
mukayi ido biyu da badura sai tayi min murmushi.
Ina fatan ka gane abinda nake nufi da
KIBIYAR AJALI ?
Tace dani abinda kawai ya rage yanzu shine suzo su
sameni a kwance shi kenan kai kuma kazo hannu
.
Kina nufin kice bazasu yarda da cewa ni na daureki? Nace
da ita.
Ba sai an fada musu ba shin menene amfanin jaridar
dana baka? A tsammaninsu kayi niyyar kashe ni ne kenan
bakada mafita idan suka sameni to na tsira kenan abu
daya da bazan sake na musu ba shine inda gidanku yake a
kano wannan wani abu ne da zasu nema da kansu na
kalleta cikin haushi sannan nace ita kina tsammanin ni
mahaukaci ne zan nufi gida ahalin yanzu
badura tayi murmushi
fadil tace dani karka batawa kanka lokaci kayi kokari ka
tserewa abinda ke jiranka waje damarka ta karshe kenan
sannan taci gaba da cewa idan kana ganin ba wani abu ne
yansanda su san gidanku ba to bari nafada ma ba abin
wahala bane na fadawa yan sanda cewa yayanka yasan
inda kake kaga zasuyi tsammanin shi ya boyeka ta danyi
shiru sannan ta sake murmushin mugunta bazaka so ace
an azabtar da yayanka ba saboda kai kada kuma kayi
tsammanin idan yan sanda sun saki yayanka zai sami
cigaba da aiki agidan redio ba abun kunya ne ace
ma'aikacin gidan rediyo ya boye mai kashe jama'a da
gangan kawai don saboda dan uwansa ne idan muka bi ta
fuskar siyasa wannan zai janyo abin kunya da maganganu
ga gidan rediyon.
Nayi shiru ina tunani lallai yarinyar nan ta gama sanin
sirrina ciki da waje haushi ya kamani nayi taku guda na
gaggawa na kifa mata mari don karin haushi maimakon
tayi kuka sai ta kyalkyale da dariya lokaci guda kuma sai
ta kwalla ihu kamar wacce ake zarewa ido cikin dakika
uku na gane abinda ke shirin faruwa na fadi rub da ciki
adaidai lokacinLokaci guda kuma saita kwala ihu kamar wacce ake
zarewa ido cikin dakika uku na gane abinda ke shirin
faruwa na fadi rub da ciki adaidai lokacin ne aka fara
ruwan harsashi ta cikin tagogin dakin in danayi sa'a sai
harsashi daya daga cikin dubun harsashen da ake zubowa
dakin ya daki katuwar fitilar dake like a bangon dakin
fashewarta keda wuya sai dakin ya zama kamar kabari
saboda duhu
na manta da zancen badura yanzu ta kaina nake duhun
dakin shi ya bani damar yin wani abu naja ciki ina laluben
jakata zakaga wawanci na idan kaji cewa ina neman
jakata cikin wannan lokaci maganar yayana ita nabi
lokacin da zan taho kaduna sai ya bani wata jaka baka
yace dani duk inda zaka katafi da jakar ka kada ka sake
kuma ka bata bansan abinda yake nufi ba amma nasan
akwai ma'anar yin hakan.
Bayan dan lokaci na sami jakar na rataya ta abayana nayi
amfani da wasu igiyoyin roba dake jikinta na daureta a
bayana lokacin gudu yayi nace cikin zuciyata na tashi
cikin sanda na leka tagar dakin dake gabas banga motsin
komai ba cikin lambun banyi tsammanin daman zanga
motsin wani abu ba amma bangaren kudu da arewa
nasan yanzu ya zama tarkon mutuwa nayi shiru tunanina
ya katse wata katuwar murya na magana cikin bututun
magana tana cewa
FADIL FADIL FADIL
Munsan kana ciki ka ajiye bindigarka kafito hannunka a
sama.
.
BIYAR 5
Mun san kana ciki fadil muryar ta sake cewa kafito a
hankali hannunka a sama muna so ka fito ta kofar dakin
zaka hadu da mutanen mu guda uku mun baka mintina
biyu ka fito in kuma bahaka ba to zamu sa yaranmu su
kamo ka da rai ko babu rai
gidan yayi shiru bakajin komai sai jefi jefin motsin yan
sanda abayan gidan na lalubi bangon gabas na tashi tsaye
naja tagar dakin kadan kadan har ta bude wata sassanyar
iska ta bugi fuskata sama tayi bakikitin da hadari anata
walkiya iska na kada rassan bishiyoyin dake lambun na
kurawa cikin duhun lambun ido ina kokarin ganin motsi
sassanyar iskar dake lambun tattare da duhunsa suka
kara razana daren da barazana mai ban tsoro kada kayi
tsammanin hakan zai hanani dirga cikin lambun ko kusa
yanzu babu alamar tsoro a tare dani raina yagama baci.
Bayan idona ya tabbatar min da babu kowa kusa saina
kama karfen tagar na dafe ajiki na dago kafafuna biyu na
zurasu waje kaina na ciki sannan na juya kaina na kalli
inda badura take nace ita sai gani na biyu amma kada kiyi
tsammanin kinyi nasara ba'a gane jarumi sai yaki ya kare
batareda najira wani abu ba saina dirga cikin lambun
ganyayyakin bishiyoyin lambun su suka hana yan sanda
suji sautin dirgata cikin lambun duk inda ka taka cikin
lambun ganyayyaki ne sun lullube kasar wajen kamar
siminti ga dukkan alamu yayi shekaru rabonsa da shara.
Badura ta kwalla kara kara ne irin wanda zakaji daga
bakin wanda ake azabtarwa adaidai lokacin ne naji
katuwar muryar nan taci gaba da magana ta cikin
bututun magana
Fadil haryanzu kanada sauran minti daya kada ka sake ka
taba yarinyar nan ta wajenka idan ka tabata harbinka
zamuyi na tsaya cak a inda nake wani motsi agabana shi
ya dauke min hankali bayan dakika uku sai naga wani
tsamirmirin dan sanda yana sanda yanufo gindin bishiyar
na rabe abayanta na godewa Allah dayasa bakar rigace
ajikina na tabbata bai ganni ba baya kuma zaton ina
wajen ayanda yake tafiya da gadara yana tsammanin ina
cikin dakin ne dan sandan ya matso kusa dani
tsakaninmu dashi bai wuce taku daya ba bantaba ganin
tashin hankali irin wannan arayuwata ba dan sandan ya
fara sanda a tsammanina bayaso naganshi ne domin
yana tunani a kwance nake a tsakar dakin indai haka yake
tunani to lallai yana bukatar sake sabon tunani
numfashina ahalin yanzu sama sama ne dan sandan ya
leka tagar dakin ahankali ta hanyar sunkuyar da kansa
kasa kasa ya dan karkatar da kunnensa yana sauraron ko
zaiji inda badura ke kara banjira wani bata lokaci ba saina
takura na daka tsalle cikin abinda bai wuce dakika daya
ba sai gani akansa muka fadi rikica akan matattun
ganyayyakin bishiyar abinda yaso ya bani dariya domin
lokacin dana fada kansa nayi zaton zai fadi da
gwiwowinsane amma abin mamaki sai naji kamar na
fada akan karmami muka mirgina sau biyu a kasa nayi
wuf na rufe bakinsa adaidai lokacin dayake shirin ihu na
dunkule hannuna na kirba masa naushi a muka miki yayi
wani irin kuka mai ban dariya nataka ruwan cikinsa sai ya
tashi zaune kamar sifirin dana dauke kafara kuma daga
ruwan cikinsa sai ya koma ya baje da farko na dauka na
kashe dan tsamirmirin sandansan nan amma dana taba
kirjinsa sai naji yana bugawa.
Ahalin yanzu an fara ciga da yayyafin ruwan na kama
kafar dan sandan na jashi kamar buhu har karkashin
wata bishiyar goba mai yawan ganyayyaki akalla zai kai
sa'a guda kafin a same shi
ya isa haka wata siririyar murya irinta matsorata tace
daga bayana ka ajje bindigarka ka daga hannayenka sama
kada ka manta muryar tace dani daidai nake dana
harbeka a gadon baya amma abinda mukafi so shine
mukama ka da ranka motsin yaudarar daya daga gareka
zai zama shine motsinka na karshe aduniya
.
Aka fara iska da ruwan sama hancin bindigarsa a tsakiyar
gadon bayana indai har na samu damar zillewa dan
sandan dake bayana to ina da cikakken kwarin gwiwar
cewa zan iya ficewa daga lambun amma abinda yafi
damuna

Please Login or Register in order to submit comment