Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kibiya na rufe idona ina addu'a alokacin ba
fargabar kamani da akayi ba nake fargabar nake hade
take da mugun tunani yanzu idan badura taci karo da
babbar mota ya za'ayi kenan? Ba zamu ko motsa ba nace
cikin zuciyata.
**
Idanuna a rufe ina addu'a badura kuma tana kwarara
gudu damu kamar zamu bar duniya abin yayi matukar
girgizani lokacin dana bude idona hakika dazu dana rufe
idona acikin birnin kano muke amma yanzu ga
mamakina sai na ganmu muna kokarin fita wajen kano
munata sheka gudu dansandan dake gaban motar ya
dubi badura cikin fushi.
Ina kike nufin kaimune? Ya buga mata tsawa
ofishin yansandann jiha ko ba can kace ba yallabai? Ta
tambaya babu isashshen haske a motar amma hakan bai
hanamin ganin murmushin daya bayyana kyawawan
lebban badura ba.
Hantar cikina ta kada murmushin irin wanda tayi minne
lokacin da salman ya dakeni da gindin bindiga acikin
dajin kaduna inda na sume ita kuma ta bada umarnin a
daureni bambancin kawai aka samu shine wannan karon
bani take yiwa murmushin ba wanda ke dauke da
barazana dakuma gargadi da wanda akeyiwa murmushin
tabbas nasan wani abu badura ke shirin aikatawa bana
kuma tsammanin abin zaiyi mana dadi gaba daya a
matsayina na wanda yayi digiri akan halayen badura sai
murmushin ya zame min kamar jar danja ce wanda ke
nuni da cewa ga hadari nan tafe bangama tunanina ba sai
kakkausar muryar dansandan ta sake cewa.
Ki kuka da kanki yarinya tunda har kika sake kikayi wasa
da hankalina sannan yaci gaba da cewa saina nuna miki
iyakarki idan har badura ta dago ta kallenshi to dutse ma
zai iya kallon ka idan kayi masa magana ta take totur din
motar gaba daya ruwan saman da akeyi kuma ya wuce
yayyafi ahalin yanzu domin tuni gaban gilas din motar ya
jike da kyar badura take ganin gabanta irin gudun da
badura ke shekawa shi yasa fuskar dansandan ta canza
cikin lokaci kankani sai duk kamanninsa suka sauya
idanunsa suka firfito saboda tsoro da fargaba ya juyo ya
kalleni sannan ya juya ya kalli badura wacce tuni tayiwa
kano nisa ni kaina bansan ko hanyar ina take bi damu ba
ruwan saman da ake shekawa da kuma duhun daren su
suka hadu suka juyar min da kwakwalwa dadin dadawa
kuma ga ciwon dake hannuna shima ya tsananta.
.
Tsaya na sauka don Allah dansandan yace cikin tsoro da
fargaba
don Allah ki tsaya na sauka wallahi na tuba
duk da yake hannuna na radadin zafi hakan bai hanani
yin murmushi ba nayi kokarin yin dariya amma na kasa.
Dansandan yayi matukar bani dariya wanda ke buga
mana tsawa sai gashi yana Magiya.
Ina zaki damu? Dansandan ya sake tambaya cikin rawar
murya
INDA BAZAMU DAWO BA
badura tace dashi adaidai lokacin ne akayi wata tsawa
mai karfi wacce tasa motar mu ta girgiza saura kadan
matukin motar mu ta kwace daga hannunta akayi walkiya
hakan shi ya sani ganin fuskar dansandan wacce ta hade
sharkaf da gumi gashin bakinsa sai diga yake da gumi
fuskarsa kuma ta koma launin gasashshen nama.
.
Ka nuna min kai dansanda ne badura tace dashi menene
amfanin bindigar dake hannunka? Ta tambaye shi tana
murmushi ko ka dauka ina tsoron zungureriyar bindigar
kane?
Zan kuwa nuna miki ni dansandan ne
dansandan ya daga bindigarsa yayi saitin badura na rufe
idona cikina na rawa cikin yan dakikun da abin ya faru na
dauka harbawa zaiyi don haka sai nayi kalmar shahada na
kuma runtse idanuna ina jiran naji karar bindiga abu
daya na tabbatarwa kaina nasan in har ya harbi badura
acikin wannan gudun da take da motar to muma
rayuwarmu tazo karshe kenan hakan shi yasa wani irin
sassanyar gumi barkowa daga goshina zuwa kan fuskata
naci gaba da kalmar shahada domin na tabbata mu tamu
tazo karshe tuni har zuciyata ta fara ayyanawa wai gani
nan na mutu an daukoni amakara an nufi makabarta
dani.
.
Minti guda ya shude banji karar bindiga ba bankuma ji
motar ta hantsila damu ba don haka saina bude idanuna
domin naga abinda ke faruwa ga mamakina sai naga
dansandan ya maida bindigar hannayensa na rawa
KA HARBA MANA TSORON ME KAKEJI YALLABAI?
Badura kenan take cewa cikin zazzakar muryarta da ba
zan taba mantawa da ita ba
Ka tuna fa kai namijine acikin mazan ma kuma wai
dansanda tunda nake bantaba ganin mace mara tsoro
kamar badura ba na duba irin ruwan da ake tafkawa
gami da iska amma duk wannan batasa ta rage gudun da
takeyi da motar ba maimakon hakan saita kara take totur
din motar gaba daya dansandan dake zaune agaban
motar ya zama kamar mutum mutumi baya ko motsi
saboda tsoron abindake shirin faruwa idonsa akan..
Dansandan gake zaune agaban motar ya zama kamar
mutum mutimi baya ko motsi saboda tsoron abindake
shirin faruwa idonsa akan sitiyarin motar ya bude baki
kamar zaiyi magana sai yayi shiru babu mamaki gani yayi
maganar tasa ma bazatayi tasiri ba dansandan ya lumshe
idanunsa hakan shi ya bani damar tunanin cewa babu
mamaki addu'a yakeyi can sai ya nisa yace da Badura.
Ya kamata kisan abinda kikeyi bakisan wannan gudun da
kike halaka zai kaimu gaba daya ba.
Ina tsammanin halakar ita tafi dacewa damu badura tace
dashi idonta akan titin da muke bi dazun nan fa kake
shirin kai masoyina ga halaka kasan kuwa in har ina
numfashi abayan kasa babu wanda ya isa ya hana min
saurayi.....
Wa yace zai halaka shi? Dansandan yace muryarsa na
rawa lokaci lokaci kuma yakan kalli malejin motar wanda
tuni an kureshi har karshe.
Laifine ake zarginsa dashi don haka dolene na kama shi
tunda na ganshi ba laifina bane wallahi yanmata don
Allah ki tsaya na sauka ya fara magiya.
.
Kada kayi min magiya badura tace dashi ai kasan cewa
idan ka kaishi hannun mutananku hukuncin kisa za'a
yanke masa amma baka damu ba da rayuwarsa sai yanzu
ne kuma kake tsammanin zan damu da rayuwarka?
Sannan taci gaba da cewa rayuwata batada amfani
agareni in har na bari aka hallaka min rabin rayuwata
akan laifin da bashi ya aikata ba wallahi na gwammace ni
na salwantar da tawa rayuwar akansa sannan ta dubi
dansandan da kyau tace dashi Mahaifiyata da kuma
taimakona suka jefa laifin kisan kan da bashi yayi ba
akansa inason ka zama shaida kaima tace da dansandan
duk da yake kuma lokaci lokaci motar takan dan kufce
daga hannunta amma hakan bai hanata ci gaba da
maganar ba nikuma ban dainayin addu'a ba domin ni a
tsammanina kowanne lokaci dansandan na iya fushi yayi
kokarin hana badura tukin sannan kuma sauran abinda
zai biyo baya ba sai an bayyana ba.
Na maimaita na sake maimaitawa da ace Fadil ya halaka
garani na halaka a hanyar kare tasa rayuwar badura tace
don haka nayi niyyar tserar dashi daga sharrin da akayi
masa ban kuma ga wanda ya isa hanani tserar dashi din
ba sai ko ubangiji mahalicci amma ba dai mutum ko
aljan ko kuma mutanenku yansandan. Tace da
dansandan cikin sassanyar murya haryanzu dansandan
baice komai ba a tunanina banajin yana saurarer abinda
take cewa ma babu mamaki shi tunanin hanyar da zai
tsira da rayuwarsa yake domin gudun da badura take ya
wuce kima mima kuma abin ya fara bani tsoro.
Ya kamata ki dan saurara haka badura nace da ita akaro
na farko tun lokacin da muka bari cikin garin kano.
Haba Masoyina tace dani baka ganin idan muka tsaya
anan ritsamu zai sakeyi da bindigarsa ya kama ka? Ni ban
damu da kaina ba Fadil inda dan tanice to da saina barshi
ya tafi dani amma kai a'a bazai taba yiwuwa ba indai kaga
har na tsaya ya sauka to sai ya yarda da sharuddaina
guda biyu ta dubi dansandan.
Wadanne sharudaine? Fadi naji wallahi zan cikasu inhar
zaki saukeni
Sharadin farko shine ka jefar da bindigarka ta tagar
motar nan na biyu kuma shine ka koma bayan motar ka
kuncewa Fadil ankwar dake hannunsa
Na yarda dansandan yace nan da nan ya sauke gilas din
motar ya jefa bindigar kasa ta bada wata irin kara lokacin
data hadu da kwalta sannan sassanyar iska hade da ruwa
suka feso cikin motar saboda tagar motar da dansandan
ya bude nan da nan yayi sauri ya rufe sannan ya juyo
tsakanin kujerun gaban motar yace Miko Hannunka.
Ban sami damar mika masa hannun ba saboda abinda na
hango a gigice a tsakiyar titin muke bi wani gungumemen
reshen bishiyane wanda kuma cikin dakikar dana ganshi
kwakwalwata tasanar dani cewa yan fashine suka gindiya
shi nayi mamakin ganin Badura bata ko rage gudu ba.
Kalli Gabanki nace da ita cikin karaji dansandan ya rufe
idonsa jikinsa na rawa badura ta take birki motar tayi kuli
kulin kubura damu abu na karshe danaji shine karar
dansandan nan cikin gigita lokacinne akayi jifa dani waje
ta gilas din Motar.
.
14
Na farka agigice sakamakon sassanyar ruwan sanyin da
aka kwaramin a fuska bansan abinda ya faru garemu ba
tun bayan lokacin da mukayi hadarin nayi kokarin bude
idanuna amma abin ya gagara matsanancin ciwon kan
dake addabata shiyake barazanar raba kaina gida biyu
aduk lokacin danayi kokarin bude idona
Na fara kokarin tunanin abinda ya faru a kanmu koda
yake ban cimma nasara ba kwakwalwata ta daina tunanin
komai sai juyawa kawai takeyi kamar yadda hannun
agogona manunin dakika ke juyawa duk wannan bai tashi
hankalina sosai ba sai bayan danayi kokarin dago
hannayena domin na rike kaina wanda ke barazanar
rabewa saboda tsananin ciwo gabana ya fadi danaji
hannayena a daure sauke tamau abayana
Alokacin wato kwakwalwata ta fara tunani sosai na gane
cewa hadari mukayi amma daga nan ban iya tuna komai
ba hakan shi ya tabbatar min da cewa suma nayi to idan
suma nayi ina Badura? Kuma ina muke ? Na tambayi
kaina kamar amsar tambayata sai aka zungure min
kuguna da wani abu mai tsini tuni zuciyata ta ayyanamin
cewa mashine sai bayan dana bude idanuna ne sannan
na gane nayi Kuskure
Yana tsaye akaina..
Yana tsaye akaina dan kerera ne wanda ganinsa ya
tunamin da barbushe wanda na taba karanta labarinsa
acikin
(Kano Ta Dabo Ci Gari)
yanada jajayen idanuwa kansa shan kwalan kafane kansa
kuma aske yake tas yana kyalli kamar madubi ga
mamakina sainaga idonsa fari tas kamar madara sabanin
guntun ire iransu wadanda su idonsu jajur yake kamar
garwashin wuta boye kammaninsa masu firgitarwa
abinda kawai zan iya cewa sun kara masa shine sunfito da
kammaninsa irin na kumurcin maciji kada kaji ance
idanunsa fararene ka dauka kuma wai manya ne masu
kyaun gani sabanin haka shi nasa kanana ne kamar da
reza aka yankasu yana sanye da wando da riga bakake
tafkeken sawunsa kuma sanye cikin takalmin karfe irin
wanda kafiran da can sukayi yaki dashi.
Hakan shiya tabbatar min kuskurena a fili na tunanin wai
da mashi aka sokeni.
Na dube shi babu alamar murmushi a fuskarsa murtuk
yake kamar wanda aka sanar dashi adadin kwanakinsa
aduniya na duba izuwa bangarena na hagun annne to na
hango badura akan kujera suka zaunar da ita suka kuma
hadata da kujerar suka daure mukayi ido hudu da ita
idonta ya cicciko da kwalla abin mamaki kuma shine
dagani har ita babu wanda yayi koda kwarzane daga
hadarin daya faru akanmu.
Sannan ne to na tuna da dansandan nan babu mamaki
dansandan ya mutu sakamakon hadarin daya faru akaro
na biyu saina sake gane kuskurena ban karashe tunani
naba sai kofar dakin ta bude su uku ne suka fito dakin
dauketa dansandan suma dankara dankarane koda yake
banajin idan an hadasu duka ukun zasu kai girman
shugabansu.
Suka shigo dakin ahankali saidai kuma kowannensu yana
muzurai suna zuwa sai sukayi jifa da dansandan ya
gangaro ta matattakalar da fuska akan tsandaurin kataki
hade da karar data razani zakayi mamakin jin cewa inata
magana akan katako amma nasan baka gane abinda nake
nufi ba to bari na baka hoton yadda dakin da muke ciki
yake a bayyane da farko dai zan iya cewa bangon dakin
da kuma kasan dakin duk da katako aka ginashi
tangamemen dakine wanda keda taga daya da kofa daya
saidai shi kofarsa da tagar ba daya take da ta sauran
dakunan ba daka sani shi wannan daki tagarsa da kofat a
sama suke don haka ko su yan fashin saita hanyar amfani
da matattaka irin ta bene suke shiga dakin. Hakan shi ya
sani tunanin to idan ana ruwan sama yaya zasuyi kenan?
Nasan dolene ruwa ya cika dakin koda yake kuma banga
alamar zubar ruwan sama a dakin ba. In ka dauke wasu
yan tarkacen kayayyaki dake kusa da badura duk sararin
dakin babu komai sai wasu kujerun katako guda uku biyu
daga cikinsu a kakkarye suke mai dan kyan daga cikinsu
itace mai kafa daya
Faffadan bakinsa mai kama da saran adda ya fadada
izuwa abinda shi yake tunanin wai murmushine sannan
ne na gane cewa ashe bashi da hakoran gaba guda uku
wawilon dake bakinsa shi ya tuna min da bakin
kadangare.
.
Kayi mamakin ganinka anan ko? Ya tambayeni yana
kallona tsigar jikina tayi yarr ko kadan bana son
murmushinsa
Nine DAWAYE yace dani sana'ata kuma shine fashi da
makami abinda nafi kauna aduniya kuma shine na kwace
kayan da ba halak dina ba sannan ya kyalkyale da dariyar
mugunta kukan jaki yafi dariyarsa dadin ji na dubi
badura jikinta na rawa kamar mazari dansandan kuma
da suka jefo na kwance jini na fita da baki da hanci
hakika yana cikin matsananciyar azaba kuma na tausaya
masa.
Nayi farin ciki da kamaku danfashin yace dani yana
murmushin mugunta duk da yake kuwa bamu sami
komai a gurinku ba amma akalla mun kama makiyammu
ya nuna dansandan da takalmin karfensa mai tsini
Makiyanmu ne dan fashin yace dani kune kawai da kuke
neman halal kuke tunanin masoyan kune amma a zahiri
makiyanku ne tunda yanzu ma babu mamaki yana shirin
kulla muku sharri ne.
Maganar dake fitowa daga bakinsa babu kai ba gindi su
suka sa na fara tunanin ko mahaukaci ne domin agurina
dansanda ba makiyi bane duk da yake kuwa suna nan
babu adadi suna farauta ta nasan cika aikinsu sukeyi
rashin sani ne kawai yasa suka kasa gane gaskiya.
.
Kamar yadda suke kama mu suna harbewa haka muma
idan mun kamasu bazamuyi musu ta dadi ba zamu kashe
duk wanda yazo hannunmu acikinsu har da abokin
tafiyarku ya nuna dansandan dake kwance maganar tayi
matukar girgizani nakuma zargi badura cikin zuciyata
saboda ita tayi sanadiyyar kawo shi ga halaka duk da yake
kuwa ni take kokarin tsewarwa.
Acan ma daya bangaren badura nata zubar da kwalla jin
cewa za'a kashe dansandan nan shi yasa jikinta ya sake
daukar rawa.
Kada ka damu danfashin yace dani yana dubana bazamu
kashe ka ba amma zamu mai dakai yaronmu ita kuma
yar uwarka mai dafa mana abinci sannan ya sake
kyalkyalewa da dariyar mugunta babu mamaki gome
zamu kashe makiyinm ya nuna dansandan bakuma kisan
bindiga zamuyi masa ba kisan da zamuyi masa bana farat
daya ne ba
sannan danfashin ya sunkuyo inda nake kwance yana
zazzare idanu daga inda nake ina iya jin hucinsa kamar
giwa.
Da'ayi maka irin kisan da zamuyi masa dan samari gara a
harbe ka da KIBIYAR AJALI ka mutu lokaci guda.
Sannan ya sake..
.Gara a harbeka da kibiyar ajali ka mutu lokaci guda
sannan ya sake dosaro gashin bakinsa kusa da fuskata
kasan irin kisan da zamuyi masa? Ya tambayeni ban amsa
ba ni ko motsi bana iyayi don razana
da farko zamu yanke kunnuwansa daya bayan daya
sannan mu yanke hancinsa zakuma mu datsa hannunsa
na dama da kuma na hagun sannan kafafunsa da haka
zamu kashe shi.
Badura ta kwalla kukan razana da maganar dayayi daya
daga cikin yaran da suke tsaye a bayansa ya matsa gaba
ya falleta da mari har sai da kanta yayi baya dakin yayi
shiru na dan lokaci bakajin komai sai hucin katon
shugaban yan fashin nan sannan ya dubeni yace dani kayi
mata nasiha dan samari idan ta sake yi mana kuka anan
itama haka zamu kasheta
Bansan lokacin dana sami kaina ina amsawa ba.
**
Idan ka dauke sheshshekar kukan badura da kuma
numfashin dan sandan nan dake kwance babu motsin
komai adakin minti biyar kenan da ficewar yan fashin
basu kuma fice daga dakin ba sai da nima wani daga
cikinsu ya falla min mari.
.
Dolene nasan yadda za'ayi na tserar da rayuwar
dansandan nan koda kuwa idan na tserar dashi din zai
sake kokarin buga min sai yanzu ne na tuno da ankwar da
dansandan nan ya buga min a hannu nayi mamakin
yadda akayi har yan fashin nan suka cire ta daga hannuna
batareda na farka ba.
.
Na dubi dansandan dake kwance magashiyan akasa jini
na fita ta baki ta hanci haryanzu kayan ruwan na jikinsa
na yunkura zan tashi sainaji ko ina ajikina na ciwo
hannuna inda aka harbe ni ya dada kumbura abin ya bani
tsoro saboda idan ba magani na samu ba zan iya hasarar
hannun sa'a daya nayi yan fashin nan basu daure
kafafuna ba sabanin dansandan dake daure tamau kamar
damin goro na sake yunkurawa zan tashi zaune sainaji
juwa ta daukeni na koma na kwanta numfashina sama
sama yake zuwa ba'a dade ba bakake da fararen taurari
suka bayyana a idona.
.
Aka kwara min ruwan sanyi a karo na biyu wannan karon
daya daga cikin yaran dan fashin nan ne yazo yana tsaye
a kaina kofin ruwan sanyi a hannunsa ba'a dade ba sai
kofar saman ta bude jibgegen shugaban yan fashin ne ya
nufo inda muke ya tako ahankali takan matattakalar
benen idona akan matattakar benen tuni na fara
tsammanin kafar benen zata ruguje saboda nauyinsa
amma ga mamakina saigashi ya sauko lafiya matattakala
uku ta rage ya sauko sai yayi tsalle ya diro tsakar dakin
baiko damu ya karasa sauran matattakalar benen ba
danfashin baiyi magana ba ya dai tsaya ne kawai akaina
yana muzurai.
Kwance shi yace da daya dan fashin cikin muryarsa mai
kama da kwarankwatsa kamar daga sama sai wuka ta
fado hannun dan fashin wannan shi ya tabbatar min da
kwarewarsa wajen iya fada ya nufi badura da wukar
tsirara ahannunsa gabana ya fadi domin a zatona soketa
zaiyi amma sabanin haka saiya fara yanke igiyar bayan
dan lokaci saiga duk igiyoyin da aka daure badura akasa
badura tayi mika sannan ta mike tsaye tayi taga taga saita
koma kujerar ta zauna banyi mamakin hakan ba ko
wanene ya kwana daya a daure baci ba sha dolene ya
kasa tafiya danfashin ya yiwo kaina da wukar yana zuwa
sai ya yanke igiyoyin da suke daure da hannayena sannan
ya kama hannuna mai ciwon na runtse ido sannan na
budesu adaidai lokacin ne mukaji motsi a kofar saman
dakin daya daga cikin yan fashin ne yake tattakowa zuwa
cikin dakin farantin kayan abinci a kansa ahannunsa
kuma na dama kuttun zuba shayi ne FLASK yawuna ya
tsinke cikina yafara salati sai yanzune na gane inajin
yunwa.
Zamu baku abinci kuci danfashin yace amma ba zamu
baiwa abokinku ba domin shi yau da yamma nan zai
bakunci lahira na dubi dansandan cikin tausayi da kyar
yake numfashi na dubi badura itama ta dubeni sannan
dan fashin yace dani idan kun gama cin abincinku ku bar
kwanukan anan kuna kuma iya fita ta saman dakin domin
kuga yadda gidan namu yake saidai bamason tabe tabe
akwai gurin wanka kuma awaje kana fita zaka ga kofofi
guda takwas a jere mai launin fanti kore itace kofar
bandakin sannan ya zazzaro idanu yace dani cikin gargadi
da barazana da kuma tsoratarwa.
Karka sake ka zolayi kanka babu mamaki tunanin gudu
zaizo kanka to idan zaka gudu Bisimilla amma duk abinda
ya faru akanku karka zargi kowa ya kyalkyale da dariyar
mugunta kayi shirin gudu idan zaka iya amma karka
laifina idan ka samu kanka a kabari sannan yayi shiru na
dan lokaci yana kallona.
Idan kayi niyyar gudun ma dan samari to ka tabbata
babu inda zaka kana cikin dajin falgore ne atsakiyarsa
kuma kake tunanin tsunduma babu gida gaba balle baya
babu kuma abokam hira sai namun daji idan ka sake ka
fita daga dogayen katangun gidan nan banajin zaka sake
taku biyar batareda damisa ko zaki sun afka maka ba
macizai ma sun isheka kawai sauran muggan namun
dawa kuwa kamar su giwa kura mugun dawa karkanda
da dai sauransu duk wadannan wasu abubuwane da zaku
ke gaisawa dasu duk safiya saidai kuma ina tsoron na
gargadeka da cewa idan har kana son rayuwa aduniya to
kayi zamanka anan idan kuwa ka gaji da zama aduniya to
ga fili nan ga mai doki daman mun dade bamu baiwa
zakunan wajen nan abinci ba.
Babu mamaki.
Babu mamaki garabasa zata saukar musu ku biyu kenan
ya nuna dansandan dake kwance da kakkauran
danyatsan hannunsa mai kama da Ayaba.
.
Idan mun gama dashi namun daji zamu jefawa su
lumashe shi ya danyi shiru sannan yace
nasan yace nasan zakayi mamakin ganin mun dauko ku
daga wani dan gari kusa da kano mun kawo ku har nan to
abinda nake son ka gane shine bamu fiye fashi akusa da
gidan ba ka kiyaye dan samari mu zamu fita sai mun
dawo suka fice ta saman dakin basu dade da fitarsu ba
sainaji karar harbin bindiga babu mamaki ta haka ne
suke korar namun dake gurin kafin su shiga cikin
motarsu.
.
15
Ya kamata mu bashi abinci badura tace dani kina nufin
mu kwance shi kenan? Ta gyada kai idan suka dawo fa me
kike zaton zai faru ? Na tambayeta ta kalleni tayi dan
murmushin karfin hali abincin da mukaci da kuma
ruwan da muka samu mukayi wanka shiya taimaka wajen
dawo da kuzarinmu dukkan wata gajiya yanzu ta fita daga
jikinmu abinda kawai ke damuna yanzu shine hannuna
dake damuna da ciwo a kumbure yake sumtum.
Idan sun dawo sai mu yaudare su mu doddoke su tace
dani batareda ta dubeni ba.
Kamar yaya mu daddake su ? Na tambayeta banjira ta
bani amsa ba saina ci gaba da cewa kina tsammanin mu
uku zamu iya doke karfafan yan fashi guda hudu?
Ki duba ki ga yadda hannuna ya kumbura fa kuma koda
lafiya lau hannuna yake sanin kanki ne ki mu uku muka
hadu bazamu iya doke shugabansu ba kuma bayan haka
ma har yanzu bamu da tabbacin ko su hudu ne kawai ko
kuma sauransu na makale awani wurin badura tayi shiru
na dan lokaci sannan tace
Banajin sun wuce guda hudu domin da sun wuce haka
babu abinda zai hanasu shigowa dasu nan in ma basa nan
nasan zai iya sanar damu cewa akwai wasu a makale ko
dan ya tsoratar damu amma abinda zamuyi shine mu
fara kwance dansandan da farko sannan sai muyi
shawara har da shi nasan dai baai dace ba ace munaji
muna gani anyi masa kisan gilla ko kuwa me ka gani
DARLIN?
Mamaki yakamani saboda jin cewa duk iya surutun da
suka faru tsakanina da badura abaya bata taba kirana da
Darling ba sai yanzu da muke cikin hali na kaka ni ka yi
ban bari ta gane cewa kalmar data fada ta girgizani ba
sainaci gaba da cewa.
.
Na yarda da maganarki DARLI....
nayi shiru ina kallonta bansan yadda akayi bakina ya
subuce ba badura na kallona tana murmushi fuskarta
cike da farin cikin jin kalamin daya so ya fito daga bakina.
Ta matso a hankali haryanzu murmushin na nan a
fuskata tana zuwa saita duba igiyar da aka daure
dansandan da ita na tashi nima ahankali kafata kamar ba
zata daukeni ba hannuna sai radadi yake bayan mun dan
dudduba igiyar sai mukaga ashe ba wani kwakkaran dauri
sukayi masa ba bamu dade ba muka kwance shi
dansandan ya dan matsa sannan yace ku bani ruwa
bangane abinda yake cewa ba saidana kara kunnena kusa
da bakinsa
badura ta miko min ruwa cikin katon kofi na bashi yasha
sannan na tashe shi zaune na wanke masa jinin dake
fuskarsa sannan na cire rigar ruwan dake jikinsa na
dauko sauran abincin da muka rage na bashi soyayyiyar
wainar kwai ce da hanta dakuma alkubus da miyar DAGE-
DAGE nayi mamakin ganin irin yadda yan fashin suka iya
dafa abinci amma dana tuna da irin rayuwarsu sai naga ai
dole ne ma su iya.
Awa daya kenan da gama cin abincinsa na raka shi
bandaki yayi wanka sannan muka dawo dakin muka fara
tattaunawa badura ce ta fara magana
Ina ganin abinda ya dace mufarayi shine mu zagaya cikin
gidan ina zaton zamu sami makamai kamar bindiga kaga
idan muka sami bindiga daidai muke mu ritsa su koda
sun kai ashirin kuma koda bindiga ce ahannunsu zamu
iya ritsa su tunda mu buya zamuyi kuma kaga bandakin
daf yake da kofar fita sai mu shiga ciki kaga suna shigewa
sai mu ritsa su ta baya idan sun ajjae makamansu kai
Fadil saika daddaure su kuma sai mu ritsa su idan ka
gama daure su saimuyi amfani da motarsu mu fice daga
cikin dajin nasan hanya bazata bace mana saimubi sawun
tayar motar nasan in Allah ya yarda zata kaimu kan hanya
kunga daga nan mun tsira kenan to yaya kuka gani ?
Ta tambayemu tana murmushi gaba dayanmu sai muka
amince da shawarar da badura ta bayar dmin babu wata
hanyar data wuce wannan amma da farko shine mu sami
bindigogi idan kuwa bamu samu ba to kashinmu ya
bushe.
.
Mukabi matattakalar benen da zatafitar damu kofar sama
gaba daya muka fita tsakar gidan kana fita zaka yi ido
hudu da kofofi guda takwas biyar daga cikin kofofin
sunada launin fari biyu kuma launin ja saikuma ta
karshen launin kore wato bandakin gidan
gidan zagaye yake da doguwar katanga wacce akanta da
wasu irin itatuwa masu karfin gaske a daure kuma
itatuwan suke da wata irin waya mai tsini tsini ina
tsammanin tsini tsinin shi yake hana damun daji
haurowa daga bangaren arewa na gidan wani katon
dakine mai wangamemiyar kofa a cikinsa motoci ne
LANDROVER guda biyu da kuma PATHFINDER guda daya
hakan shi ya tabbatar min da cewa dakin garejine
nakumayi mamakin ganin motocin nan har guda uku
kuma sababbi banda wacce ma suka tafi da ita.
.
Ina zamu fara shiga? Dansandan ya tambayeni mu balla
jar kofar ina tunanin.....
.
Ina zamu fara shiga? Dansandan ya tambayeni.
Mu fara balla jar kofar ina tunanin me yiyuwa anan ne
suke aje makamansu dansandan ya sungumi wani
mulmulallen karfe dake can kusa da katangar itatuwan
nan yana zuwa sai ya fara dukan kofar dakin ba'a dade ba
ta balle.
Ku shiga ku duba badura tace damu
Ni zan jiraku awaje inason leka waje ta kofar gidan tace
damu kiyi ahankali na gargadeta
babu komai darling tace dani sannan ne muka shiga
dakin mai tsananin duhun gaske ne saida muka fara
wangame kofar gaba daya sannan muka fara ganin kayan
cikin dakin banyi taku biyar ba cikin dakin idona ya
hango min wata katuwar akwatin katako ajikin bangon
dakin da dukkan alamu komai agidan na katako ne nace
cikin zuciyata na leka cikin akwatin shima sannan ne naji
tsigar jikina ta tashi wani sassanyar gumi ya fara barkowa
daga fuskata acikin akwatin reras suna kyalli kamar zinare
kowannensu bakinsa da

Please Login or Register in order to submit comment