Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasi kafin ta sake magana sai mukaji
anaMaganar tayi tasiri akanta saboda ganin irin yadda tayi
kasake tana kallona kuma tana wasi wasi kafin ta sake
magana sai mukaji ana kwankwasa kofa ta kalleni na
kalleta sannan amina ta sake kallona cikin takaici gumi ya
rufeni saboda nasan Amina a shirye take ta damkani a
hannun sojojin hawaye ya fara kwaranyowa akan
kyakkyawar fuskar Amina alokacin dasu kuma yan dadi
bindigar dake waje sukaci gaba da buga kofar ahankali
duk da yake kuwa sojojine wannan ba abin mamaki bane
idan akayi la'akari da kasancewar Amina yar gidan Kanal
muktar dole ne itama abata girma iya nata Allah ya isa
soyayya wallahi kin gama dani kin kuma cuceni tunda
kika fi karfin zuciyata har kika sa zan ceci ran makiyin
mahaifiyata Amina taci gaba da kuka bayan wasu yan
lokuta sai ta turani cikin daya daga cikin dakunan dake
fuskantar dakin banjira wani karin bayani ba sai kawai na
fada dakin na rufe na jingina kunne a jikin kofar dakin ina
sauraron abinda ke faruwa a dakin.
Ranki ya dade wani kurtun soja wanda cikakkiyar hausa
bata isheshi ba yace da Amina
Sannunka dai ta amsa sama sama haryanzu ina iya
sauraren haushin karnukan dake maraba dani gasashshe
awaje kinga motsin wani abu ko kamar gudun mutu anan
wajen sojojin suka tambayeta a'a wallahi banji komai ba
Amina ta amsa nayi mamakin irin yadda muryarta ke
bada amsa batareda tayi rawa ba
to shikenan to daman mun dauka ko kinji wani abune sai
da safe sojojin sukace da ita.
Lafiya dai? Ta tambaya a'a babu komai suka ce da ita
sannan naji an turo kofar an rufe bayan yan dakiku saina
bude kofar na fito Amina na zaune akan daya daga cikin
kujerun dake dakin sai yanzu ne na lura cewa ashe ma
wai akwai kujeru a cikin falon nata batayimin magana
nima kuma banyi mata ba saboda raina nima yayi
matukar baci ganin irin yadda amina ta kasa fahimtata na
matsa kusa da tagar dake dakin Amina sai naga wani tsani
a tsaye ajikin katangar gidan dake fuskantar dakin ga
dukkan alamu sabon fenti akayiwa bangon su kuma
ma'aikatan suka bar tsanin ajingine na gane haka ne ta
hanyar ganin gwangwanin fenti a makale ajikin tsanin
na sami hanyar tsira nace cikin zuciyata batareda na sake
duban Amina sai kawai na bude dakin inajin lokacin da
amina tayi firgigit ta tashi tsaye amma bacin rai baisa na
juyo ba sai kawai na nufi tsanain da gudu inajin lokacin
da wani katon kare ya kawowa kafara sura amma nasan
nayi masa fintinkau dakiku biyu sai gani akan katangar
gidan daga barin gabas a sannan ne kuma naji wani
radadi ya bugi hannuna kamar an sokeni da kibiya
karar bindigar daya biyo baya shi ya tabbatar min da
cewa harbina akayi karfin harsashin bindigar shi yayi jifa
dani kasan katangar na fada acikin wani katon kwalabati
da kyar nake numfashi juwa na daukata ahaka na lallaba
naja ciki na shige cikin bututun kwatar dake fuskantar
katon lambatun kwatar
radadin da hannuna keyi bai hanani jin kukan Amina ba
alokacin da harbeni Fadil ta kira sunana cikin Karaji
**
Fadil naji wata siririyar murya tayi kirana duk da yake
radadin harbin da akayimin ahannu na damuna saida
muryar tasa gabana ya fadi muryar da bazan taba
mantawa da ita bace muryar yarinyar da haryanzu
zuciyata takasa tantancewa shin
MASOYIYATA CE KO KUWA ABAR KINA CE?
.
Fadil nice BADURA kada kaji tsoro nazone na ceci ranka
saboda kaunar da nakeyi ma badura tace dani adaidai
lokacin data sunkuyo ta kama hannuna tana niyyar fitar
dani daga cikin katon lambatun kwatar da nake ciki
Badura nakira sunanta idan kina tsammanin zan sake
yarda dake to kin zolayi kanki
idan kana tsammanin ni ba masoyiyarka bace Fadil to to
hakika kayi kuskure sonka ma yanzu nafara badura ta
amsa min
na sami kaina a kafadar badura tana jana ina tangadi
saboda jinin daya zuba ajikina yanada matukar yawa
idona a rufe badura ke jana.
Zan saka acikin but din motata badura tace dani saboda
duk yansandan garin nan an basu kamanninka ashirye
kuma suke su kama ka acikin harda kwararrun yandan
ciki daga durba hotel kaduna ban samu damar ce mata
komai ba saboda duk jikina ciwo yake ahaka na lallaba da
taimakon badura na fada cikin but din motarta ta mayar
ta rufe dani banida wani zabi sai abinda badura tayi dani
ahalin yanzu duk da yake kuwa har yanzu zuciyata bata
amince da duk abinda tace ba ahaka na kwanta cikin but
din motar kamar matacce amsa kuwwar muryar Amina
shi yaketa kai komo cikin kwakwalwata
FADIL FADIL FADIL
Bansan iya lokacin danayi akwance ba kafara ta kage
saboda rashin isashshen sukuni acikin but din motar bani
kumada tabbacin shin bacci nayi ko suma nayi nidai
kawai na farka naji badura tana ta tafka musu da
wadansu wadanda daga karshe na gane yansada ne.
.
Muna son muga bayan motarki daya daga cikin
yansandan yace da ita nace ma babu komai amma kaki
ka yarda badura tace inason naga babu komai din domin
an bamu damar bincikar duk wanda ya biyo tanan don
haka dole ki bude bayan motar ciwon dake damuna shi
ya hanani fargaba ko kadan bandamu ba ko su bude
koma su bari saboda idan ma sun barni babu mamaki
mutuwa zanyi saboda jinin daya zuba ajikina.
.
Bazaku bude ba to badura tace dasu cikin tsiwa kai
kirawo yallabai wannan yarinyar batada gaskiya daya
dansandan yace bayan wani dan lokaci naji takun sawun
wani dansandan agidan but din motar
ke yarinya munason ki bude mana but din motar nan
idan kuma bahaka ba zamu balla da karfi
Baka isa ba badura tace
tas naji karar mari ya daki dodon kunnena badura ta
kwalla kara mai tsanani ku kamata kusata a mota dan
sandan yace to yallabai saura suka amsa
kai kuma dauko guduma dansan ya sake bada umarni
na lumshe idanuna ina sauraron a bude bayan but din da
nake dan lokaci sainaji an fara dukan but din motar
dukan but din motar da ake daidai yake da bugun
zuciyata.
.
.
KASHI NA UKU
12
Aka cigaba da dukan but din motar kamar za'a
ragargazata ba dukan motar ne ya dameni ba abinda yafi
damuna shine jijjiga jikin motar da sukeyi duk lokacin da
jikin motar yayi rawa sai naji hannuna kamar ba'a jikina
yake ba haryanzu jini na zuba agurin da aka harbeni na
gane hakanne ta hanyar jin danshi danshi ko ina a
hannun rigata
Ku buga da kyau mana babban yansandan yabada
umarni nan da nan suka bude wuta suna dukan but din
motar duk karfinsu. Sannan ne kuma naji shiru an daina
dukan bayan motar irin shirun da zakajine a duk lokacin
da aka dauke ruwan sama kamar da bakin kwarya sannan
kuma aka dauke lokaci guda babu mamaki shirun danaji
tafi haka kakaraf naji karar bugun takalma a kasa ga
dukkan alamu wani yansandan suke sarawa sannan ne to
naji abinda ya sake sani fitar da rai daga rayuwa duk da
yake hankalina bajikina yake ba hakan bai hanani gane
muryar sojan nan daya yiwa Amina tambayoyi ba.
Bakuga wata yarinya ba ta wuce tanan gurin? Sojan ya
tambaya gata can yallabai acikin motarmu daman ita
muke bincike mun dauka batada gaskiya don hakane ma
kaga muna balle bayan motar
bayan motar wa? Sojan ya bugawa dan sandan tsawa
sannan yaci gaba da cewa shin kasan ko motar wacece
kuke lalatawa?
Ranka ya dade wallahi bansani ba na tuna dansan yace
jikinsa na rawa
ai kana da sauran tuba sojan yace saimakaji ko yar gidan
wacece
na tuba yallabai dansan ya sake tuba
mu tafi gurin Kanal Muktar ka tuna agabansa sojan yace
dashi sannan ya buga masa tsawa ku fito da ita to yallabai
dansan yace nayi shiru ina sauraro numfashina sama
sama saboda jini mai yawan gaske ya zuba daga jikina da
kyar nake bude idanuna na kuma godewa Allah lokacin
da aka harbeni ta fito nemana
Gata yallabai dansandan yace aka danyi shiru sannan
sojan yace a fusace ai ba wannan muke nema ba banda
ita bakuga wata ba?
Yallabai wallahi ba muga kowa ba sai wannan Alamar jin
dadin da yafita daga bala'i a bayyane take acikin kalamin
dayayi.
Banga amfanin zamanku anan ba tunda har kuka bari yar
gidan oga ta bace kuma tanan ta biyo
yallabai wallahi batanan ta....
Ku saki wannan yarinyar sojan ya buga musu tsawa
inason ku shiga motarku ku zagayawa zaku gano mana ita
mu kuma zamubi ta bayan titinan ko zamu ganta kun
gane ko?
Yes sir yansandan suka amsa baki daya ga yadda na
fahimta sojan yanada dan mukami saboda irin yadda naji
yansandan na bin umarninsa sau da kafa basu gardama
karar cin tayar motocin yansandan dana sojojine ya
tabbatar min da sun tafi ba'a dade ba sainaji badura na
kokarin bude but din motar da kyar ta samu ta bude
saboda yansandan sun mommogada bayan motar na
kumayi mamakin yansandan saboda ganin basu karbi
dan makullin but din ba daga hannun badura da sun
karbi dan makullin motar da tuni ina hannunsu nayi
mamaki matuka da dabarar hakan bata fado musu ba
idanunsu ya rufe wannan wani abune daga ubangiji nace
cikin zuciyata.
.
Fadil badura tayi kirana
Na'am na amsa da kyar tayi ajiyar zuciya sannan ta kamo
hannuna marar ciwon da niyyar fitar dani daga cikin
motar matsanancin ciwo ya saokeni nayi yar kara badura
ta rike numfashinta sannu Fadil tace dani na yunkura da
kyar jikina babu laka ko kadan da kyar badura ta fito dani
daga bayan motar tana fitod ani na yanke jiki na fadi
numfashina sama sama da kyar nake shakar iska badura
ta sake dagoni sama ta hanyar sake kama daya hannun
da haka tajani ranga ranga har jikin motar muna zuwa
saita bude ta turani ciki ahankali sannan ta rufe ta zagayo
gaban motar ta shiga ta tashi motar sannan ta tuka ta tafi
dani inda bansan ko inane ba koda yake dai alokacin
banida zabi amma kuma haryanzu bansaki jiki da Badura
ba badon harbin da akayimin ba to da yanzu mun rabu
ciwon ya sake sukata naji kaina yayi dum ba'a jima ba
bakaken taurari suka bayyana a idona daga bayane na
fahimci ashe suma nayi.
**
Sassanyar ruwan sanyin da aka yayyafa min a fuska shi ya
taimaka wajen farkowata daga suman danayi badura na
zaune a kusa dani kofin ruwan sanyi a hannunta na
hagun hawaye na kwarara akan kumatuna abin yaban
mamaki idan na tuna da cewa wai yau ga badura tana
kuka da hawayenta saboda wani mummunan hali dana
shiga na dubeta nayi murmushin karfin hali..
Wai yau ga badura tana kuka da hawayenta saboda wani
mummunan hali dana shiga.
Na dubeta nayi murmushin kafin hali.
.
Sai bayan data dawo min da murmushina ne na lura da
inda aka harbeni a daure yake da wani farin kyalle.
Menene kuma abin kuka Badura? Na tambayeta ba
abinda kukeso kenan ba ku ganni cikin bala'i bada
hakkina ba?
Ai abinda ya kamata kiyi shine farin ciki da dariya ba kuka
ba kina jin zan sake yarda dake ko kuwa....
Jiwa ta daukeni naji kamar zan sake suma numfashina
sama sama nayi luuu zan fadi baduta ta tareni tana kuka
bayan dan tsawon lokaci sai hankalina ya dan dawo jikina
na bude ido badura na kallona.
Daman nasan bazaka sake yarda dani ba Fadil badura
tace dani muryarta na rawa mahaifiyata ta riga ta lalata
rayuwata tunda tayi sanadiyyar daka tsaneni ka kuma
tsani yar uwata Amira na fada maka ba laifina bane Fadil
amma kaki yarda tace dani cikin karaji da sheshshekar
kuka.
Tausayinta ya kamani duk da yake kuwa ban yarda da ita
ba saura kadan na amince da ita kuma sauran kalamanta.
Karka yarda da ita wata zuciyar tace dani shashasha ka
manta abinda tace dakai a durba hotel kaduna? Daga
baya kuma ta butulce maka? Kaine mutum na farko dana
fara jin sonsa azuciyata lallai kam na tuna bazan amince
da ita tunda kalamin data fada abaya bai hana mata
cutata ba da kuma sanadiyyar jefani awani mawuyacin
hali
.
Kana jin zaka kashe zainab a banza ne? Bani na kashe
taba. Maganganun badura da suka faru a kwanakin
bayane suke dawowa zuciyata zaman kuma da nake
yanzu agaban badura wacce hawaye ke kwarara daga
fararen idanunta ina iya jin siririyar muryarta garai garai
kamar a faifain rediyo inda take cewa
DAURE SHI DA KYAU DON KA SAN KAKKAFAR NE...
.
Badura na kira sunanta bata amsa ba
banajin akwai wani sauran kalami daga bakinki da zai iya
sawa na amince dake tuni kin fada min ire iren kalamai
masu sanyaya zuciya masu kuma karyar da zuciya su
kuma yaudari duk wanda ya amince da mai muryar don
haka duk wani dadin baki da zakiyi yanzu kamar
maimaicine ga abinda kika fada min kwanakin baya kuma
kika yaudareni bari na tambayeki Badura nace da ita
kanta a sunkuye tana zubar da hawaye haryanzu kofin
ruwan sanyin na hannunta tayi far da fararen idanuwanta
wadanda ada sukan sa gabana faduwa saboda so da
kauna amma yanzu bazan iya fayyace tsakanin mu da ita
ina ganin sanin abinda ke tsakaninmu da badura sai ko
ubangijin daya halicci kaddara damu kuma baki daya.
Me kake son tambaya? Tace dani cikin sheshshekar kuka
na dubta sannan naci gaba da cewa ke a ganinki Badura
da kece amatsayina nikuma a matsayinki na badura kina
ganin zaki sake amincewa dani? Tayi shiru bata amsa ba
sannan naci gaba dacewa
To ashe kuwa in dai hakane bai kamata ma kifara ganin
laifina don naki amincewa dake ke bari ma ta wannan
shin halin da nake ciki ayanzu kina ganin zan samu damar
tsira kituna fa duk wani dansanda dake garin nan nemana
ruwa ajallo yake ina amfanin badi babu rai badura?
Ina ganin zancen na amince dake baima taso ba domin
kuwa damar tsirata kadance nasan koba dade ko bajima
zasu kamani bazai kuma yiwu ace kullum inata guje guje
ba cikin tashin hankali.
Na kalleta sannan nayi murmushin karfi lokaci kuma na
cije lebena saboda ciwon dake hannuna ya takura min.
Mukayi shiru na dan lokaci babu wanda yasake magana
sai bayan mintuna uku sannan badura ta dago kai ta
dubeni.
Zan nuna ma cewa kayi kuskuren fahimtata tace dani
saikuma na nuna maka cewa nafi Amina kaunarka
tunanin raina zai baci shiyasa badura tayi sauri tace dani
Fadil karka dauka wai ina kushetane agabanka sam sam
bahaka bane abin dai kawai da nake so ka gane shine
nima masoyiyarka ce wacce kuma ke begenka fiyeda
Amina nayi shiru bance da ita kmai ba haryanzu kuma
bansan a ninda muke ba abin kawai dana sani shine
muna gefen titi motoci ne saboda lokaci lokaci motoci
sukan wuce ta kusa damu duk da yake talatanin darene
kuma daren damuna daga inda nake zaune ina iya ganin
walkiya ta cikin gilas din tagar motar badura wanda duk
suke a kulle kofar motar dayace a bude wacce badura ke
bangarenta a zaune agogon dake gaban motar shi ya
sanar dani cewa yanzu karfe uku da mituna ashirin na
dare hakan shi ya nuna sa'o'ina uku kenan da barin gidan
da Amina ta boyeni Badura ta dubeni taci gaba da cewa
kar fa kayi tsammanin duk taimakon da amina tayi maka
daga kaduna zuwa nan bansani ba ko kusa ba haka bane
idan kayi tunanin haka ma to ka zolayi kanka Salman ya
sanar dani duk yadda abu ya faru kuma ya sanar dani
duk yadda ya kwace ku ahannun dansandan daya ritsaka
acikin gero ta danyi shiru tana maida numfashi ko dan
jinin daya zuba ajikina inda ma nayi sa' shine alburushin
bindigar bai sami kashi ba naman hannun ya dan goga ya
wuce rashin samun kashin hannuna da harsashin yayi shi
ya bani damar kaiwa haryanzu a raye ya kuma bani
damar sauraron badura amma daya sameni to da yanzu
labari yasha bam ban.
.
Amina ta tserar da rayuwarka daga hannun
mafarautanku sassanyar muryar badura ce ta sake
kwarara zuwa dodon kunnena sai dai kuma ba gaba daya
ta tserar dakai ba Fadil tace dani cikin sassanyar murya
amma kai aganinka tayima wani babban taimako wanda
na tabbata hakan ne yasa kaso amina tayi shiru sannan ta
kura min ido nima na kalleta mukayi ido hudu bayan yan
dakiku na fara kawar da idanuna Fadil nayima tambaya
mana kamar yadda ka tambayeni dazun.
Tambayi mana nace da ita a sanyaye maganar data fara
yanzu ta fara tasiri akaina nasan har yanzu ban amince da
ita ba to amma kuma nasan abinda take fada gaskiyane
tabbas tserar dani da amina tayi shi ya sani kaunarta Fadil
badura ta kira sunana a sanyaye sunana ya zama kamar
wakace a bakin badura tana son idan zata yi min magana
ta kira sunana.
Zaka amsa min tambayar idan nayi maka?
Zan iya amsawa mana idan tanada amsa
Ada can to Fadil kana kaunar Amina kuwa kamar yadda
take sonka? Nayi shiru ban amsa ba saboda bansan abina
zance da ita,
Nifa fadil kwanakin baya kana sona kuwa?
Nayi shiru ban amsa ba yakamata ka amsa min tunda
kayi alkawarin zaka amsa min indai tambayar nada amsa.
Na sakeyin shiru na dan lokaci sannan nace da ita.
Bangane abinda kike son tambaya ba nace da ita na fadi
hakane domin na baiwa kaina damar tunani
haba fadil kasan amsar mana kaidai kawai kace tayi ma
nauyi sannan danyi murmushi tsigar jikina tayi yarr
murmushinta shi ya tuno min haduwarmu ta farko a
durba hotel kaduna lokacin ina cikin mayen begenta
amma yanzu fa? Na yiwa kaina tambayar fam miliyan
guda.
.
Idan amsar tayi maka nauyi fadil bari ni na amsa ma da
farko dai tunda can nasan baka son amina itace dai take
kaunarka ana cikin haka ne muka hadu na sani fadil tace
dani cikin daga murya kana mutuwar sona a kwanaki
kadan din da suka wuce amma sakamakon abinda
mahaifiyarmu ta kulla sai duk ka tsaneni ka kuma fara
begen amina saboda taimakon da tayima to nima zanyi
ma taimakon da yafi na amina domin ni zan tserar
dakaine gaba daya cikin tashin hankalin daka fada
Tayaya? Na tambeyata cikin mamaki murmushinta mai
sa gabana faduwa ya sake bayyana a kyakkyawar fuskarta
duk da yake babu cikakken haske acikin motar babu
kuma farin wata a sararin samaniya hakan bai hana min
ganin fararen hakoranta ba.
Yanzu kayi tambaya abin kaunata tace dani zan iya tserar
dakai ta hanyoyi da dama sanin kankane cewa duk
abinda mahaifiyata ta kulla maka da masaniyata kuma
dani aka kulla komai duk da yake kuwa bana so kamar
yadda na sanar dakai tun farko tayi shiru tana duban
bangaren da nake zaune ta cikin gilas din motar sannan
ta juyo taci gaba da cewa
Zan iya saida rayuwata don ganin na bada shaidar da zata
tserar da rayuwarka agaban alkali domin wannan itace
hanyar da kawai zan gamsar dakai cewa nafi Amina
kaunarka tayi ajiyar zuciya sannan muka yi ido hudu da
ita dan duhun dake cikin motar bai hanani ganin
hawayen daya fara sartu a idontaba.
Nasan Fadil ba zasu kyaleni hakaba tace dani tana
sheshshekar kuka indai Alkali yaji duk labarin dolene ya
dau mataki akaina dakuma yar uwata Amira akalla ko ba
komai za a iya yanke mana hukuncin shekaru biyar koma
fiyeda haka agidan yari kaga kuwa babu rayuwa mafi
kaskanci irin ace yarinya kamata agidan maza to amma
hakan shi yafi soyuwa agareni tunda kaidai rayuwarka
zata tsira kuma ko ba komai na nuna ma kauna fiyeda
Amina wacce ta kasa hanawa sojojin gidansu su harbeka.
Na kalleta cikin mamaki me kike nufi na tambayeta
abinda nake nufi shine ta kasa kare lafiyarka bayan kuma
tana ikirarin wai ita masoyiyarka ce idan soyayyar
gaskiyace me yasa bata boyeka ba? Na kasa amsa wannan
tambayar akaro na biyu kenan na dubi Badura itama ta
kalleni idanunta cike da kwalla ko kusa wannan batayi
kama da badurar dana sani ba a kwanakin baya badurar
dana sani a kaduna dakakkiyace wacce bata kuka bata
kuma tsoron komai amma sai gashi wannan badurar
tana kuka da hawayenta agabana tana kuma kokarin na
amince da ita wai har zata saidai rayuwarta akaina abinda
mamaki kodayake....
.
Bansamu damar karasa tunanina ba indai har ba idanuna
ne sukayi min karya ba to naga motsin wani abu ta cikin
gilas din motar mu tsigar jikina tayi yarr
alokaci guda kuma badura ta fahimci hakan muka dubi
dubi gurin gaba daya mutumin ya nufo gurin ahankali
hannayensa cikin bakar rigar ruwa bansan ko wanene ba
Badura takai hannunta zata hanye gilas din motar domin
mu sami damar ganinsa nayi sauri na gargadeta
kada ki bude nace da ita cikin rada mutumin yaci gaba da
nufi inda muke babu cikakken hasken da zan iya ganinsa
gaba daya sakamakon bakin hadarin da ya zagaye sararin
samaniyar mahaliccin komai
amma hakan bai hana farin fentin da akayi rubutun
saman hularsa tona asirinsa ba POLICE a rubuce a saman
hular kwanon dake kansa yana matsowa ina kara ganinsa
sosai numfashina kuma yana dada yin sama sama tuni
jikina yayi nauyi ba kamar da ba lokacin da sauran jini
ajikina na lumshe idona ina kokarin maida numfashi
sannan na sake budewa dansan ya matso sosai tsakaninsa
da motar.
Dansandan ya matso kusa sosai tsakaninsa da motar bai
wuce taku shida ba zungureriyar bindigar harbi ka rufa a
rataye a kafadarsa yanata muzurai kamar kowane lokaci
zai iya bude wuta duk da yake kuwa babu tabbacin
harsashin dake cikin bindigar yakai Uku.
.
Dansan ya kwankwasa gilas din motar bangaren da nake
daga baya kuma ya ya dallaro cocilarsa mai hasken gaske
ta cikin gilas din motar cikin sa'a dansandan bai kula da
bangaren badura ba wacce kofar ta ke bude ahankali sai
badura ta janyo kofar ta rufe lokaci guda kuma ta
sunkuyo tace dani lumshe idona na yarda ta ita wajen
yaudara don haka sai na lumshe idanuna sannan ne ta
janye gilas din motar hasken fitilar dansandan ya kara
haskake cikin motar idanuna ba a rufe suke gaba daya ba
don haka ina iya ganin gashin bakin dansan wanda ke
tsaye yana hasko mu karan sigari a bakinsa hannunsa
agogo mai lamba lamba ne a daure 3:35 abinda ya nuna
kenan.
.
Kuna shirin kwana nan ne? Katuwar muryar dansandan
ta daki dodon kunnena saidai kuma tsawar da yayi bataui
tasiri ba a sakamakon tsawar asali da kararta ya keta
sararin samaniya hade da walkiya mai hasken gaske
alokaci guda kuma aka fara yayyafar ruwa.
Ko bakuji ba ya sake daka mana tsawa ku bude kofar
motar yace damu badura tayi sauri ta bude kasancewar
hannun da aka harbeni bangarenta yake a boye
me kuke anan? Ya sake tambayarta.
Kaga yallabai daman wallahi neman wanda zai taimaka
min nakai shi gida nake motar taki tashi kuma gashi tatul
yake da ruwan BAGAJA.
Me kike nufi?
Ya tambaye tayi murmushi ina nufin ruwan yan birni ko
sai nayi ma gwari gwari GIYA to. Tace dashi adaidai
lokacin ne dansan ya dallara hasken fitilar a fuskata
sannan naji ya sunkuya ya dan daki kafadata sannan yace
tashi abokina yaudarar karya kake shin kana tsammanin
duk yandan garin nan basuda hotonka Haba Fadil tuni
har bindigarsa ta fado hannunsa.
.
13
Idan har ana sabo da bindiga to ya kamata ace na saba da
ita wannan bashine karo na farko ba bakuma na biyu ne
ko na uku ba da aka ritsani da bindiga tun sa'adda na
fada tarkonsu badura mai kofa daya sai wasa da bindiga
ya zama kamar wasan gargajiya agareni duk da yake
kuwa ba dadinsa nakeji ba ko kusa ban zolayi kaina ba
domin nasan ba' saboda da bindiga ko banza dai tafi
maciji kwarjini domin duk lokacin da aka ritsaka da ita to
kafarka daya alahira take daya kuma a duniya a wannan
karonma zungureriyar bindigar dansandan a kirjina
bakinta yake kasan kuwa ko banza zaiyi wuya na bayyana
ma irin faduwar gaban da nakeyi awannan lokaci saidai
zan iya baka misali da mutumin dake zaune akan sanda
kuma agaban rijiya gaba dubu.
.
Fito da hannayenka waje dansan yace muryarsa na dan
rawa kada kuma ka sake kayo kokarin yin wani abu ya
gargadeni haryanzu badura na zaune acikin motar bata
ko motsa ba yayyafin ruwan kuma da aka farayi bai
hanani gumiba nayi kokarin fito da hannayena gaba daya
amma hannun da aka harbeni yaki daguwa idan na daga
hannun sainaji kamar an sokeni da kibiyar Ajali
dansandan ya fahimci cewa banason fitowa da hannuna
na dama don haka sai ya matsa kusa dani hancin
bindigarsa manne akirjina dan yatsansa na hagun akan
kunamar bindigar ta hakane yayi amfani da hannunsa na
dama ya dago hannuna mai ciwon radadi ya sokeni na yi
yar kara amma bai fito fili ba
ka dago hannunka mana dansandan ya buga min tsawa
kayi masa ahankali harbinsa akayi a hannun yana kuma
da kyau ace ka maida bindigar kafadarka domin baka
bukatar amfani da ita idan kabar shi ma bazai iya guduwa
ba muryar badura ce ta ratsa shirun daran haryanzu ana
yayyafar ruwan saman kuma bakin hadarin na nan anata
walkiya saidai kuma hakan baisa an tsuge ruwan da karfi
ba.
Dansan ya dubi badura idonsa cike da shakka da kuma
zargin abindatace sannan ne ya hasko cocilarsa kan
hannuna alokacin to yaga jinin dake jikin kyallen shi ya
tabbatar masa kumari da hakan.
Ahankali cikin nutsuwa da kwanciyar hankali fuskarsa
cike da annaurin yin nasarar kani sai dansan ya dauke
bindigar daga kirjina sannan ya mayar da ita inda take
rataye kafadarsa kenan a daidai lokacin to ankwa ta fado
hannunsa kayi kuskure daka mayar da bindigar nace
cikin zuciyata badura ta karanci abinda nake shirin
aikatawa don haka sai tayi sauri ta gargadeni ta hanyar
girgiza kanta bansan abinda take nufi ba amma sanin
cewa ita kwararriyace gurin yaudara saina rabu da
sandan ya matso kusa dani sannan yakama hannayena
yabuga ankwa ga mimakina sainaga ko taka tsantsan
bayayi saboda shi azatonsa karfina ya kare gaba daya
sauran na naushi wuyansa amma dana tuna gargadin
badura saina rabudashi ya buga ankwar ahannuna
sannan ne abin yayimatukar girgiza ni ya faru kamar a
wasan kwaikwayo sai bindigar dansan ta sake fadowa
hannunsa a wannan karon hancin bindigar yana saitin
kan badura
shiga ki tuka motar dansan ya buga mata tsawa cikin
muryarsa ta yan doka dumi ya lullubeni na kalli badura
cikin takaicin hanani dukansa datayi ita kanta bata taba
zaton dansandan ita zai ritsa tatuka motar ba ta kalleni na
kalleta sannan ahankali saita
Ta kalleni na kyalleta sannan ahankali saita fice daga
kusanidani ta rufo kofar alokaci guda kuma shima
dansandan ya rufe kofar dake bangarena na dama
sannan ya daga bindigarsa yaci gaba da saitin badura
bayan dan lokaci baduta ta shiga motar shima dansandan
ya shiga kusa da ita ya zauna sannan badura ta tashi
motar yanzu kam na tabbata na kamu banga yaudarar da
badura zatayi ta tserar dani ba.
.
Ofishin yansandan cikin jiha zaki kaimu dansandan yace
cikin kakkausar muryarsar wacce ke cike da amon samun
nasara badura ta fizgi motar da gudu muka harba kan
titin kamar

Please Login or Register in order to submit comment