Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine bansan iya yawan yan sandan da suke
gadin bangaren gabas na lambun ba duk da yake dai
nasan har yanzu gungun yan sandan basuda masaniyar
abinda ke faruwa a bangaren gabas na lambun addu'a ta
daya itace Allah sa na samu damar yaudarar dan sandan
dake bayana tun kafin wani yazo ya tadda mu
Kada ka sake ka motsa yace dani bansan abinda yake nufi
ba amma zatona yana jiran ruwa ya tsagaitane mun jike
shakaf amma ni duk da haka zafi nakeji akayi wata
walkiya mai hasken gaske duk lambun ya haske sannan
wata tsawa mai karar gaske ta biyo baya amsa kuwwar
tsawar ta sake rikita lambun dan sandan dake bayana sai
yayi zaton shi zata fadawa yana rawar jiki sainaji saitin
bindigar ya kauce daga bayana banjira wani abu ba sai
kawai na fadi rib da ciki nasa kafata na doke shi a kirji
bindigar dake hannunsa ta fadi can gefe guda muka tashi
lokaci guda muka shiga tsere kowa na kokarin daukar
bindihar ruwa ya dada tsugewa da karfi santsin cabin
ruwa ya kwashi dan sandan sai gashi a kasa kamar wanda
aka jefo daga sama baiyi wata wata ba sai ya rike idon
sawuna nima na fadi kansa muka shiga kokowa cikin
cabin abinka da wanda ya manyanta kafin minti daya
saiga dansandan yana numfashi sama sama nayi masa
diban karan mahaukaciya na jefa shi bayana idona ya
gama rufewa ahalin yanzu fada kawai nake kamar
mahaukacin doki domin nasan idan sauran yan sandan
sukazo to fa kashina ya bushe kenan.
Dan sandan dana jefar gefe guda yayi kokarin tashi
amma sai juwa ta dauke shi ya fadi sannan sai ya tashi
naga ya dora hannu aka zaiyi ihu na duba inda bindigarsa
ta fadi na raruma kafin ihun nasa yagama fitowa saina
kwada masa gindin bindihar a tsakiyar ka yayi taga taga
ya fada cikin cabin da fuska biyu kenan nace a zuciyata
**
Ko kadan bana son fada da dan sanda ba don komai ba
kuwa sai don dokace mai tsanani amma kuma irin halin
danake ciki ya zama dole na kwaci kaina.
Rigata ta jike sharkaf da ruwa bayan na dawo da
numfashina daidai saina gyarawa jakar dake bayana
dauri sannan na kama kafar dansandan dana dole na
boye shi shima a karkashin bishiya
lambun yayi shiru bakajin komai sai dirar zubar ruwa
akan kwanukan gidajen jama'a dake bayan lambun sai
kuma jefi jefin cabal cabal din ruwa danake ji na
takalmin yan sanda acan bangaren arewa ina tsammanin
sun fara tunkarar gidan saidai kuma ruwan da akeyi shi
ya bata musu lamari domin duk takun da suke inaji har
yanzu fa suna tsammanin inada bindiga.
Nasa gabana gabas ina dansa ahalin yanzu na fara hango
katangar gidan ta cikin wata bishiyar lemon zaki marar
ganye da yawa saidai kuma kaiwa ga katangar shine yake
da matukar hadari domin babu mamaki wani dansandan
na nan a na gadin wajen kamar da bakin mala'iku sainaji
nayi sama kamar karmamai sai bayan dana fada cikin
cabalin ruwan da fuska sannan na gane cewa ashe fa wai
kafafuna aka kwarfe na mirgina sau uku cikin cabin
ruwan sannan nayi karfin hali na tashi zaune ina kokarin
gane me ya faru katon dan sandan wanda zaka iya ganin
jajayen idanunsa daga cikin duhun daren na tsaye a kaina
jibgegen kakkauran mai fadin kafada kamar kofar gareji
zaiyi wuya ka banbance tsakanin wuyansa da kansa da
farko sai ka dauka mutum mutumi ne hannunsa daya
yiwo kaina kamar harsashi shi ya tabbatar min da cewa
ba mutum mutumi bane.
Katon hannunsa mai kamar farantin waina ya cakumi
kwalata ya dagoni safayau kamar biredin mahaukaciya
kafata da kyar take taba kasa ya kwada min mari sau uku
idona ya ganemin taurarin wahala kamar tarin yashi naji
kamar saman kaina zai cire yafado.
Sai ka san ka daki dan sanda yace dani daga yau ka sake
kashe wani muryarsa mai kama da kwankwatsa kafafuna
sai reto suke falau falau kamar bulala mai baki biyu cikin
gigiya da takaici na kutufi hancin dan sandan alamun da
ya nuna alamu ne na irin wanda aka doka da gudumar
totuwa agadon baya
kaje ka sake kwarewa a dambe dan sandan yace dani
adaidai lokacin ne ya saki kwalata tareda dukan kirjina
dukane irin wanda zai iya kayar da katangar bulon siminti
na fadi rica.... Kamar wanda iskar gas ta doka hankalina
ya fara fita daga jikina kuguna kamar zai fashe nayi
kokarin tashi abin ya gagara dana yunkura sai naji kamar
gini ya fado min.
Dan sandan baya ko kokarin fito da bindigarsa domin
yasan zaiyi wuya na tsira daga hannunsa ya yarda da
kansa nafara tunanin daya naushe ni gara ya harbeni da
bindiga akafata naushinsa yafi bindiga hadari don kuwa
dukansa zai iya kashe mutum fatar daya kada kayi zaton
abinda nake fade gaskiyane kai kanka kasan wahalace
tasani tunanin haka.
Cabal cabal naji karar dansandan nacewa ayayinda ya
keto cabin ruwan dake tsakaninmu dashi nayi ta maza sai
gani a zaune dolene yanzu nasan yanda zanyi na rage
masa haukan karfin dake kansa in kuwa na sake yayi min
irin dukan dazun toh nasan yau banida wajen kwana sai
gidan DAN KANDEIn kuwa na sake yayi min irin dukan dazu to nasan yau
banida wajen kwana sai gidan YARI
.
Ya matso kusa dani tsakaninmu dashi bai wuce takun
sawu uku ba dabara ta fado min saina yanke jiki kafin
kiftawa da bisimillah sai gani facal cikin cabin duk da yake
babu cikakken hasken da zan iya ganin fuskar dan sandan
sosai duk da haka zan iya cewa naga hakoransa suna
murmushin mugunta a zatonsa sarewa nayi na fadi in har
yana tsammanin zan kamu haka kamar wani jikakken
zakara to yana bukatar sake tunani sau dubu acikin
kowace dakika daya.
Na harbo kafara kamar KIBIYAR AJALI
jibgegen dan sandan yayi kokarin kauce tunbinsa amma
ina ya makara gindin takalmina ya daki tumbinsa sainaji
kamar na daki salkar ruwa dansandan yayi kara irin karar
da zakaji daga bakin kwado da farko na dauka bazaiji
dukan ba saboda ganin naushin danayi masa ya shanye
shi kamar wanda na daki bango
duk wannan rikicin ya farune cikin dakika biyar na sake
yunkurawa gaba na sake dukan cikinsa sau biyu
dansandan yayi baya taga taga kamar zai fadi sannan sai
naga ya tsaya cak kamar mashi yana fuskantata katon
cikinsa a hannu naji kamar motsin ganye abayansa wani
dan siririn dansa ne yake matsowa ahankali cikin sanda
walkiyar da akayi ita ta bani damar ganinsa kirjina ya fara
dukan uku uku dole ne yanzu nayi wani abu na tabbata
dansan bai ganni ba.
Dan uwa me kakeyi hakane?
Siririn sandan ya tambaya cikin harshen turan nan da
nan nayi saurin na kwanta ahankali cikin cabalin na
mimmike kamar fatalwa
.
Wayyo cikina ya kasheni kawo min taimako dan uwana
nayi maganar ne cikin harshen turanci
idan baka harbi katon nan ba kasheni zaiyi nasake cewa
cikin harshen turanci karar harbin bindiga da hasken
wutar data fitar daga bakinta da kuma aradun da akayi a
daidai lokacin hade da walkiya sai suka hadu suka
kurumta kunnen jibgegen dansandan yayi kuka
Ka kashe dan uwanka kaiw awa yayi taku biyu gaba ya
fadi da baya agabana cikin hasken walkiya sainaga jini na
bulbulowa daga gwiwarsa ta kafar hagun nayi ajiyar
zuciya akalla dai bai mutu ba nace cikin zuciyata.
Karar bindigar da kuma aradun da akayi alokacin su suka
hadu suka ruda matsoracin siririn dansandan nan da yayi
harbin yana harbin sai ga bindigar ta kwace daga
hannunsa ta fadi kasa a tsammanina bai taba harbi da ita
ba sai yau cikin rudanin nan na tashi nayi kan dan sandan
da gudu kamar kibiya yaga tahowata don haka sai yayi
kokarin kai usir (abun busa) bakinsa idan na sake ya busa
usir din to ni ina bukatar addu'a kenan domin nasan
wajen na iya cika da yan sanda cikin minti daya nayi
kokarin kai kutufo bakinsa adaidai lokacin da iskar
bakinsa ta fara busa usir din naushin ya hada da iskar
bakinsa suka bada irin karar da zakaji idan tayar da keke
ta fashe dan sandan ya fadi wanwar hancinsa da bakinsa
na tsiyaya ban koma ta kansa ba domin nasan an gama
masa aiki saina harba da gudu na nufi takantar lambun.
.
Ruwan saman da ake tafkawa kamar da bakin kwarya ya
fara tsagaitawa shirun dake kambun ahalin yanzu ta fara
rayuwa da hayaniyar gudun yan sanda acikin ruwa daga
can bangaren lambun usir mai karan gaske na tashi
kamar algaita lallai ina ganin bala'i amma duk wannan
kadan ne idan na tuna da sato sarkar gidan kanal
mukhtar soja fa ba dansanda bane banbancinsu a
bayyane yake.
Nayi tsalle na kama katangar lambun sainaji an rike
kafata wani dan gajeren dan sanda ne tsatstsama
tsawonsa bai wuce takun kafa biyar ba ya fizgoni da wani
irin zafin nama na mamaki santsin ruwa ya kwashe shi sai
ya saki kafara ni kuma hannuna ya rabu da katangar na
fado kan tsakiyar cikin dansandan sainaji kamar na fado
akan kwallon kafa nayi tsalle gefe guda daidai lokacin ne
dansandan ya tashi yayi yo kaina abinda da gajeren
mutum tuni sai gashi acikina yayi sama dani ya hadani da
bangon ya matse ni kamkam da kyar nake numfashi
kamar daga sama sai naga wani abu kamar katako ya
taho daga saman katangar dansan bai kula ba yanata
kokarin fasa min ciki da matsa katakon ya daki tsakiyar
kan dan gajeren dansan nan yayi yar dani ya fadi ko
motsawa baiyi ba na dube shi na hada masa naushi a
fuska kafafunsa suka mimmike sannan yai shiru kamar
matacce
.
Kama nan Fadil wata siririyar murya tace dani daga
saman katangar muryar sananniyace agareni saidai bazan
iya tunawa ko ta wacece ahalin yanzu.
Aka zuro min kafa sanye da takalmin ruwa baki na kama
ta na yunkura sannan na kama saman katangar can kasan
katangar wani siririn layi ne wanda ya ziro min kafar shi
ya fara disa kasa ni kuma na bishi abaya ya kama
hannuna muka mike cikin wani loko da gudu wasu yara
suna karatun Islamiyya acikin wata rumfa suka zuba
mana ido suna kallon mu bayan wani dan lokaci saigamu
abakin titi motoci sunata zirga zirga saida naga mun nufi
wata bakar mota fasfanda sannan na gane mai ja na
yi sauri ka shiga AMINA tace dani rigar ruwan da tasa ita
ta maida ita kamar namiji fuskarta na kyalkyalin farin
cikin sake ganina
.
SHIDA 6
Aduniyar nan gaba dayanta banga wanda yafi masoyi ba
lallai duk wanda yace yana sonka koda da wasa ne to ka
rungume shi hannu biyu ada ban san haka ba sai da
Aminatu ta tseratar dani daga hannun yan sanda sannan
na fahimci cewa mai sonka shi yake bada rayuwarsa
wajen ceton taka rayuwar
Nayi tunani mai zurfi alokacin da Amina take zura gudu
damu acikin motarta aduk cikin abokaina banga wanda
zai iya min abinda Amina tayi min ba sai yanzu na gane
irin son da Amina takeyimin sone na hakika SON UWAR
YARA ba so irin na badura anuna ma so a lalata
rayuwarka akaro na farko tun farkon haduwatarmu da
Aminat sai naji kaunarta ta mamaye min zuciya cikin
minti goma sha biyar saigashi ina nadamar kin karbar
soyayyar amina da na yi hakika na wahalar da rayuwarta
nakuma zalunci kaina domin nasan abinda tayimin
tagama karya min zuciya ta sani na kamu da ciwon sonta
batareda na shirya ba in da ace Amina zatace bata sona
ahalin yanzu to da wahalar da zan sha sai tafi wacce tasha
linkin ba ninkin.
Tunanina ya katse adaidai lokacin da amina ta taka birki
sannan ta sauka daga kan hanya ta tsaya tsakaninmu da
kaduna yayi min biyar tun lokacin da muka shiga motar
babu wanda yace da wani kala. Amina ta juyo ta fuskance
ni tana murmushi sannan ta dafa kaina tace dani
Sannu Fadil wallahi kasha wahala kalli duk yadda ka canza
kamar ba kai ba yanzu da sun kashe ka ni yazanyi
aduniyar nan Fadil danima karshen farin cikina yazo
kenan.
Kiyiwa Allah godiya dayasa har yanzu inada sauran
numfashi nace da ita wata mota tazo da gudu ta wuce
mu kamar walkiya cikin hasken fitilar motar sai Amina ta
kula da hannuna inda gilas ya yanke ni tun ina kan
bishiyar gidan nan mai lambu nan da nan ta kunna yar
karamar fitilar dake cikin motar dana kula naga hannun
ya kumbura haryanzu jini na zuba kadan kadan.
Bari na daure ma Amina tace dani
dame zaki daure? Na tambayeta.
Bari ka gani mana tace dani sannan sai ta cire dan
kwalinta gashin kanta ya bayyana yana sheki kamshin
damina da kuma kamshin turaren dake jikin Amina suka
hadu suka cika cikin motar suka bada wani irin kamshi
mai faranta rai muka hada ido da ita sai kwarjininta yasa
na dauke idona kaunarta ta cika min zuciya begenta ya
mamaye kwakwalwata bansan lokacin data daure ciwon
da kallabin taba.
Kingazaki bata dan kwallinki da jini nace da ita
haba fadil lafiyarka ai tafi komai agareni tasa siraran yan
yatsunta masu taushi tana shafar saman fuskata
kalli duk yanda fuskarka ta kumbuta na matsa kusa da
tagar motar na dubi fuskata ajikin mudubi sai naga yan
yatsun jibgegen dansan dan guda biyar a fuskata fatar
bakina ma ta kara girma
babu komai Fadil amina tace idan munje gida sai mu
sami asibitin da zasu duba ka kada ki damu nace da ita
kedai kiyi kokari mu tsira tukunna
Fadil amina ta kira sunana hannunta acikin hannayena
tana matsawa dana lura sai naji yan yatsunta suna rawa
acikin tafin hannuna sannan taci gaba da cewa
nayi ma tambaya zaka bani amsa?
Allagh sa nasani nace da ita
Fadil kana sona kuwa kamar yanda nake sonka?
Muryar ta na rawa kada kace nayi rashin kunya wallahi
sonka danakeyi yafi karfin na boye azuciyata kai kuma
naga kamar baka damu dani ba fadil don Allah ina rokon
arziki daya kafin muci gaba da tafiya ina son ka fada da
bakin ka cewa kana sona koda da wasa ne.
Sainaji dadin tukin da zan tserar damu daga sharrin
makiyanka ya masoyina bana son ace kana kusa dani
amma bansan matsayina azuciyarka ba.
Mukayi shiru na dan lokaci na kalleta nace da ita
AMINA kwanakin baya da suka wuce bana tunanin zan
taba kaunarki amma ayanzu sonki da begenki sun zama
ginshikin rayuwata wallahi Amina ina kaunarki bazan iya
bayyana miki yadda nakejin sonki acikin zuciyata ba na
baki amanar kaina sai yadda kikayi dani na zama naki
Amina bansani ba ko kema kin zama tawa?
Na tambayeta tayi min murmushin dana tabbatar na
farin cikin jin kalamaina ne.
Daman ni takace Fadil na gode da abinda naji daga
bakinka koda kuwa baikai zuciya ba.
Nima na saki murmushi kwatankwacin irin wanda tayi
min kada kiyi shakkar abinda na fada ya masoyiyata abar
kaunata kece tauraruwata ta shekara kauna so da bege
agareki bazan taba dainawa ba muka hada ido da ita
abinda ta gani a idona shi ya tabbatar mata da gaske nake
kunya ta kama mu gaba dayanmu sannan ta lullube
idonta da tafin hannayenta biyu wayyo rabin raina Amina
tace dani cikin murmushi.
Amina ta jijjiga kafadata na tashi firgigit tun lokacin da
muka ci gaba da tafiya na fara yin barci saboda gajiya da
kuma zazzabin dake damuna bayan Amina ta gane
zazzabi na damuna saita dauko gyalenta daga cikin wata
bakar jakarta ta rufeni dashi sannan mukaci gaba da
tafiya bana tsammanin Amina zata tasheni daga barcin
batareda wani dalili ba don haka batareda tambaya saina
tashi zaune kallo daya nayiwa fuskarta na tabbatarwa
kaina babu lafiya sannan na gansu acan gabanmu suna
tsatstsaye cakare cakare abakin hanya ko wannen su
sanye da bakar rigar ruwa da bindigoginsu a makale a
kafadarsu
Ko wannen su sanye da bakar rigar ruwa duk da yake
kuwa an dauke ruwan da bindigoginsu a makel a
kafadarsu.
.
Tun kafin mu karaso suka fara dallop mana fitila suna yi
mana alamar idan munzo mu tsaya acan gefen hagu
kuma na titin sun balbalawa tayar mota wuya tana ci a
kusa da wutar ne idona ya gane min wani dan karamin
katako ajikinsa an rubuta kamar haka cikin harshen
turanci
STOP POLICE CHECK
Amina ta taka birki muka tsaya.
Ka koma bayan motar ka kwanta banyi mata musu ba sai
kawai na fada bayan motar na kwanta aminta ta janyo
wani katon tamfal ta rufeni sannan ta juya ta nufi
yansandan bayan mun danyi tafiya sai naji motar ta tsaya
nayi mutuwar tsohuwa acikin tamfal din bana ko
cikakken numfashi saboda tsoron kar ajini zazzabin dake
jikina na riga na mance dashi ahalin yanzu inata kaina ne.
Sannunki hajiya wani gwarin dansanda yace da ita yawwa
sannunka da aiki Amina tace cikin dariya ya dukan ruwa?
Dansan ya dan kyalkyale da dariya sannan yace
haba hajiya kinajin zamu zauna ne anan ruwa yayi ta
dukanmu ai kinsan zatayi wuya sannan yaci gaba da cewa
da za'a fara ruwan ma yanzu da duk gida zamu gudu
Don cika aiki ko? Amina ta tambaya cikin dariya abar
maganar dan sanda yace da ita ina zuwane hajiya zanje
kanon dabo amina ta amsa masa
ko zamu iya duba bayan motar ki a'a bazaku iya ba
Amina tace cikin dariya kai dan samari karka bata min
lokaci kaje can ka nemo wanda yayi muku kisan kai
amma banan ba ko kana tsammanin harkata harta kai ta
wadda zan dauko mai kisan jama'a abayan motata?
Kin cika surutu yan mata dan sandan yace
oho wato yanzu an tashi daga hajiya kenan na koma yan
mata to nima bari in kira ka yallabai idan baka yarda dani
ba to je ka duba amma kada ka nuna ka sanni idan muka
hadu dakai a kano watarana tunda sharri zakayimin
haba hajiya yan mata abin har yazo da haka kada ki
damu daman wasa nakeyi miki wanda muke nema ina
tsammanin tuni yabar kaduna mu ma munayine don
dole sannan dansan ya dan marairaice muryar yace da
ita
idan nazo kano a ina zamu hadu?
A daula otel amina tace dashi cikin rada wa zan tambaya
idan nazo dan sandan ya tambayeta kace kana neman
BABY
To shikenan sai nazo sandan yace zaki iya tafiya amina ta
taka motarta mukayi gaba koda mukayi gaba sainaji
karar wata katuwar mota abayanmu taja birki lallai sun
batawa dansandan shiri nace cikin zuciyata.
.
******** ******* ********* *******
.
Tsakaninmu da kano yanu bai wuce mil ashirin ba mun
wuce karfi da kadan tun da muka bar yansandan nan
babu mai cewa komai aminatu tana ta maka gudu damu
kamar zamu tashi tunda muka baro kaduna har zuwa
yanzu banga motar data wuce mu ba lokaci lokaci amina
takan dubeni tayimin murmushi murmushin shi yake
sani nake dan manta halin danake ciki soyayya da dadi
take agurin wanda ya samu mai sonsa.
Duk rikicin da mukayi da yansanda jakar da yayana
yabani tana bayana
KADA KA SAKE KABAR JAKAR NAN TA BATA KATAFI DA ITA
DUK INDA ZAKA...
maganar da yayana yayita jaddada min kenan daya bani
jakar alokacin da zan tafi kaduna na gyara daurin jakar
dake bayana hannuna ya dunguri aljihun gaban rigata sai
naji kabarkabar nazaro wata takardar daga ciki tasha
ruwa har ta fara bushewa amma haryanzu rubutun
jikinta bai goge ba na budata rubutun saman takardar shi
ya tuna min ko ta mecece tsarin gidan Kanal Mukhtar ce
shine abinda ke rubuce a jikinta takardar da badura
tabanice hade da jaridan nan tun ina gida mai lambu na
kaduna kada kayi zaton zan bar amina taga takardar don
haka saina saye ta a aljihuna.
.
Saura kadan hancina ya daki gilas din gaban motar a
sakamakon birkin da amina taja saida tayar motar tayi
kara kuu
can gaban mu motocine sama da guda biyar anfito da
mutanen ciki anata bincike mukayi shiru na dan lokaci
muna kallon abinda ke faruwa.
Ya kamata ki kashe fitilar motar na ce da ita kwakwalwata
ya fara tunanin mafita yansandan kano fa ba irin na
kaduna bane idan Amina ta yaudari wani ya yarda toh
wani bazai yarda ba sannan ne dabara ta fado min duhun
gero ya rufe ko ina abakin hanyar na kalli amina nace da
ita zan sauka nabita cikin gero ke kuma sai kiyi gaba idan
sun gama binciken ma hadu agaba karki tsaya sai kin
baiwa min daya baya sannan ki jirani nayi mata
murmushin tabbatar mata da abinda na fada kada ki
damu rabin raina nace da ita banjira wani abu ba sai
kawai na bude murfin motar na dira amina ta bari saida
na shige duhun geron sannan taja motar tayi gaba.
Ruwan saman da akayi a kano baikai na kaduna ba amma
hakan bai hana cikin duhun geron sanyi ba abin ka da
mai jin zazzabi nan da nan saina fara rawar dari na daure
naci gaba da tafiya cikin geron bayan yan mintuna saina
fara jiyo hayaniyar yan sandan sunayiwa masu mota
tambayoyi tsakanina dasu bai wuce taku shida ba amma
duhun geron bazai barsu su ganeni ba na karaso wata
duhuwar gero akusa da wajen akwai wata katuwar
bishiyar kuka don haka sai nabita bayan kukar da nufin ci
gaba da tafiya sannan ne nayi tuntube da wani abu na
wuntsila gaba nazo da fuska a kan tushiyar gero da farko
na dauka kututturen bishiyane ya tadeni amma karar
razanarKIBIYAR AJALI 19
.
Amma karar razanar danaji abayana shi ya tabbatar min
ba kututture bane.
.
Kana motsawa ina harbeka dansandan dogo ne siriri yana
rike da bindigarsa a hannun dama hannunsa na hagu
kuma rike da wandonya yana barazanar sullubewa duk
da yake ya tsorata saida abin yaso yabani dariya saboda
ganin dan sandan fitsari yake nayi tuntube dashi na tashi
tsaye ina rawar jiki hancin bindigarsa akan goshina
babu mamaki ma kaine mutumin da yayi kisan kai a
kaduna dansan yace cikin fushi me kakeyi anan ya daka
min tsawa aikin da muka sashi yakeyi wata murya ta
amsa masa tambayarsa daga baya idan baka aje
bindigarka ba to saidai ku mutu tare kana harbinsa ina
harbinka muryar tace daga baya dansandan ya saki
bindigarsa kasa yana rawar jiki kamar mazari cikin razana
sai ya saki wandonsa kasa yafado daga shi sai diras
mutumin ya zagayo ya dauke bindigar dansandan cikin
mamaki da razana saina gane ko wanene mutumin da
ban taba zato zan gani ahalin yanzu ba duk da yake akwai
duhun dare hakan bai hana ni ganin kayan jikinsa ba
KOREN WANDO DA FARAR RIGA abinda ya dada razanani
shine yadda akayi ya biyoni batareda na sani ba
Salman na kra sunansa muryata na rawa
.
KASHI NA BIYU 2
.
BAKWAI 7
Salman nakira sunansa muryata na rawa.
Hakika al'amura sunata faruwa agareni kamar a majigi
daga wannan sai wannan daya bayan daya kamar jan
carbi nikam yanzu nafara fitar da rai da rayuwa
musamman ma danayi la'akayi da irin bala'in dake
samuna bi da bi kamar yayan carbi sai yanzu ne na yarda
cewa duk wanda yakibin maganar na gaba dashi to lallai
yana tare da nadama domin danabi maganar yayana nayi
zamana a gida to da yanzu saidai nima na karanta irin
wadannan abubuwa da ke faruwa agareni kamar yadda
kuke karantawa ahalin yanzu duk wannan tunanin
nayishine lokacin da salman ya dago kai ya dubeni yana
murmushinsa irin maisa kananan yara mafarki
dansandan dake gefenmu yayi sororo kamar mutum
mutumi ga dukkan alamu yana tsammanin alburushin
bindigar salman zai iya ratsa jikinsa akowane lokaci daga
yanzu domin irin tsayuwar da dansandan yayi ba dan
yana numfashi ba da sai ka iya kiransa matacce amma
mutuwar tsaye
kayi mamakin ganina ko? Salman ya ce dani na dago
kaina dube shi da niyyar nayi magana amma tsoro da
mamaki suka hana harshena fadin komai.
Kada kayi tsammanin zamu barka kayita aiki batareda
saninmu ba Salman yaci gaba da cewa dole ne mu sa ido
aduk abubuwan da kake don ganin ka cimma nasara
wajen sato sarkar saboda haka ko kana niyyar wata kurda
kurda ko kuma wata yaudara don kin bin umarninmu to
ka tabbata bazaka kai labari ba domin duk abinda ke
faruwa tun daga kaduna ina nan kusa dakai sannan
salman yayi dariya yace wannan umarni ne daga uwar
gidata Badura kuma zanci gaba da binka abaya a baya har
sai ran da naga kaci narasa wajen sato sarkar ka kuma
baiwa badura sarkar kamar yadda muka tsara maka cewa
daula otel ce wurin da zamu hadu ka bada sarkar idan
kayi haka to sannan ne zan rabu dakai amma yanzu kam
da kai Allah ya hadamu zanyita binka kamar yadda ajali
ke bin rai zan kuma fada ma wani abu Fadil Salman yace
dani bance dashi komai ba don haka sai yaci gaba da
cewa masoyiyarka amina ni nayi mata talfon agidan data
sauka na kaduna na kuma sanar da ita inda kake domin
tazo ta kwaceka daga hannun yan sanda za kuma kayi
mamakin ganin mun kyaleka kafita garin kaduna kai
kadai amatsayin mai laifin kisan kai kuma ta cikin hadari
iri daban daban to munyi hakane domin mu gwadaka
muga jarumtarka to hakika yanzu muna sa ran cewa idan
akwai mutumin da zai iya sato mana sarkar to kaine gumi
sai kwarara yake daga goshina zuwa bayana tunda na
fada cikin bala'in nan sai yanzu ne naga Allah ya budo
min hanyar da zata fitar dani idan yansanda sun kamani
idan baka sani ba to bari fada ma salman nata sharara
labari bayako tunanin cewa gaban shaida mai kwari yake
bayaninsa dansan dake gabana ya isheni shaida fatana
daya shine Allah yasa Salman ya barshi da ransa wannan
tunani shi yasa na fara tunanin cewa Salman ya tabu
hakika mutum mai hankali bazai taba fadar laifin daya
aikata agaban dansan ba.
.
Tunanina ya katse adaidai lokacin danaga salman yafara
murmushin muguntarsa kirjina ya fara dakan uku uku
domin murmushin salman yana bayyana ne aduk lokacin
dayake shirin aikata tabargaza kafin na karasa tunanina
salman ya daga bindigarsa ya daki kan sandan duke ne
irin wanda zai iya jefar da ingarman doki dansan ya kifa
da fuska da wani irin kuka mai kama da na karamin yaro
bai ko shura ba a tunanina ya mutu idan kuwa ya mutu
da kuwa damata ta karshe ta subuce kenan Allah yasa bai
mutu ba nace cikin zuciyata yakamata ka kama gabanka
salman yace dani a fusace Amina nacan tana jiranka
kada ka sake kiran sunan Amina nace dashi bana son
kusa ta cikin wannan rikicin nidai dana riga na shiga to na
shiga amma ita ku barta waje guda.
Ta riga ta sa kanta salman yace dani idan ma kuma da
batayi saurin sa kanta ba to dolene anan gaba ta shiga
saboda me kace haka? Na tambayi salman ka tambayi
badura salman yace dani sannan yayi murmushi
Saboda me kace haka? Na tambayi salman
ka tambayi badura salman yace dani sannan yayi
murmushi kafin na sake tambayarsa wani abu tuni
salman ya sake bacewa acikin duhun daren da yafito
kamar Fatalwa
.
*********** ******** ********* **********
.
Rabin raina ina ka tsaya ne

Please Login or Register in order to submit comment