Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inuwarka kuma tana fadawa wata na'ura wacce ita da
inuwa take aiki zata dau kara don haka nake shawartarka
amatsayina na mai kaunar karka sake ka kusanci gilas din
da sarkar take har saika kashe duk fitilun dakin dakin
kuma zaka same shi a karshen kofar gidan ta goma sha
biyu daga hannunka na hagun idan kuma zaka shiga
gidan karka sake ka shiga ta kofa koda yake basai na fada
maba nasan kanada kwakwalwar da zata iya fitar dakai
Allah ya taimake ka Masoyina.
Daga Masoyiyarka BADURA
Mai neman Gafara agareka.
.
Acan wani bangare na cikin gidan kararrawar agogo ta
fara kuka wannan shine yake nuna alamar karfe goma
sha biyu tayi na linke takardar na mayar aljihuna na nufi
gado na kwanta amma na kasa barci na sake zaro
takardar naci gaba da karantawa kafin gari na ya waye na
karanta takardar yakai sau SITTIN 60
.
TARA 9
Na duba agogona sainaga karfe goma sha biyu saura
minti daya nan da nan na tashi tsaye na sakala jakar da
yayana ya ce karna rabu da ita sannan na fito daga dakin
na rufe gidan na jefa dan makullin a aljihuna sannan na
kama hanya ina rarrabewa acikin duhu kamar barawo
Tafiya ta tafi kenan ko na dawo ko kuwa sojoji su harbeni
babu mamaki kuma na zama abincin karnuka abin ya
zame min gaba siyaki baya damisa idan na dawo banyi
nasara ba hajiya binta tayi alkawarin aikawa dani barzahu
idan ma nayi nasara abiyu nake kona bar kasar kokuma
yansanda su kamani karshe kuma a dora min laifin kisan
zainab a rataye ni idan kuma duk wannan ma bata faru
ba idan nayi kuskure wajen shiga gidan Kanal Muktar to
nan ma dai na lalace wannan shine zabin Shaidan ko ina
Halaka
bayan tafiyar minti goma sha biyar ina bin bango kamar
kadangare na karaso Sultan road kirjina yana dakan uku
uku titin sultan a haskake take kamar rana akwai
kwayeyen wutar lantarki sama da tamanin anan tun daga
nesa na toge ina tunanin ta inda zan lallaba na karasa
gidan kanal batareda ana ganina ba amma hakan yaci
turo saboda babu damar nayi taku biyar cikin titin sultan
sai sojojin sun hangoni na duba bangaren kudu na titin
ga mamakina sai na hango wani kangon gida wanda a
tsammanina babu kowa acikinsa kuma tsakaninsa da
gidan Kanal muktar gida dayane wanda shi naga alamar
akwai mutane na sake duban gidan tsakanin kangon nan
da gidan kanal sai naga biyu daga cikin tagogin dakin
dake fuskantar iya gajeriyar katana agidan abude suke
daga inda nake tsaye ina sauraron lallausan sautin
turawan dake tashi agidan hakanshi ya sani tunanin in
har zan iya shiga gidan ta baya to da wahala masu gadin
suji shigata saboda kidan dake tashi bai iya barinsu suji
komai bayan haka ma kuma ai daye yayi babu mamaki
ma mutum dayane kawai ya rage baiyi bacci ba agidan
kuma koma wanene ina tsammanin saurayine dan haka
batareda dana barzuciyata ta sake min tunani ba sai na
nufi katangar kangon nan na dare kamar barawo kafin na
dira ciki sai da na hanga kofar gidan kanal muktar wacce
ke cike da yan mazan jiya.
.
Abin mamaki kofar hidan kanal muktar kamar rana sojoji
sun rarrabu har kashi uku kashin farko mutum ne suna
tsaye suna muzurai kowannensu rikeda zungureriyar
bindiga a hannu suna jiran koda kudane su harbe kashi
na biyu kuma mutum ukune suna hira biyu daga cikinsu
suna rike da karan taba abakinsu dayan kuma yana wasa
da hancin bindigarsa kashi na uku kuma mutum hudune
suna wasa da karta daga can gefen su kuma wani katon
sojane mai nadadden gashin baki yana zukar sigari katon
takalminsa na kafar dama yana barazanar fashewa ga
dukkan alamu dashi sojan yaje yakin duniya na daya
sojan ya kai kimanin shekaru saba'in ina kuma
tsammanin shine mai fada aji agurin na tabbatar da
hakan adaidai lokacin da wani dogon soja ya fado wajen
kamar daga sama sojan na sanye da hular malafa mai
kamar gare gare sojan ya kame agaban katon sojan nan
Morning Sir (barka da asuba) yace dashi cikin harshen
turanci katon sojan ya daga kansa sannan yaci gaba da
zukar zigarinsa shi kuma daya sojan sai ya zauna wajen
masu wasa da katin adaidai lokacin na dirga cikin kangon
gidan nan.
.
Akan wani abu lallausa na dira takalmina ya bada wani
kara cus na tsayye gefe guda cikin razana sannan naji
wani irin wari ya daki hancina nayi sauri na zaro yar
karamar fitila cucila na haska akan abinda na taka cikin
kaduwa saiga mushen wani katon kare mai dauke da
farin kyalle awuyansa abinda zuciyata ta raya min shine
wannan daga cikin karnukan Kanal muktar ne ya mutu
aka jefo shi nan na godewa Allah da yasa ba akan mai rai
na dira ba nayi wa karen kallo daya sannan nayi gaba da
sauri ina haska cucilar kangon an fara ginashi amma
ginin baiyi nisa ba hakan ne ma yasa ciyawa ta fara yiwa
farfajiyar tsohon kangon kawanya
gidan yayi shiru kamar makabarta bakajin komai sai
sautin bugun zuciyata naci gaba da tafiya ina sanda na.
Gidan yayi shiru kamar makabarta bakajin komai sai
sautin bugun zuciyata naci gaba da tafiya ina sanda na
nufi katangar gidan nan da yake makwabtaka da kangon
ina tafiya ahankali tare kuma da zagaye duk inda wata
duhuwar ciyawa take aduk lokacin dana dan taka sahuna
da karfi akan ciyawar sai baraye da jabaye su fita da gudu
su nufi ramukansu wasun su kuma cikin karkashin wani
tarin katako suke shigewa katakon tari gudane kuma a
zaube yake agindin katangar gidan wacce ita nake kokarin
kaiwa domin na samu damar shiga daya gidan na kusa
dashi.
.
Koda na matsa kusa da katakon da niyyar na takashi na
kama katangar sai naji motsin wani abu a saman
katangar tsohon ginin nan motsin yaso ya razana ni
amma dana tuna da cewa gidan fa a cike yake da beraye
saina dake da farko har naja da baya na makale ajikin
katangar amma da tunanin beraye ya fado min sai
zuciyata tace dani babu komai kaidai kayi hankali kar
shegen tsoronka yasa har ka dirga daya gidan da karfi su
jika don haka sai kawai na nufi katakon da sauri takun
farko nayi shine da kafata ta dama kafin kuma na dago
kafata ta hagun sai naji wani abu ya fado akan kafata ta
damar abin lallausane kuma ina tsammanin yana da
tsayin gaske na gane hakan ne ta hanyar nannade kafata
da abin yafarayi cikin dan lokaci kankani sai naji kaina
yayi min nauyi dim tsoro da fargaba suka hanani motsi
abu na farko daya darsu cikin zuciyata shine Maciji ne ya
nannade ni nayi karfin hali na zaro fitilar cocilata daga
aljihuna na haska kan kafata domin naga abinda ke
Faruwa
Abinda hasken fitilar ya dauko min yasa numfashina
daukewa yakumasa gumi ya fara zuba daga fuskata zuwa
wuyana kamar ruwa alokaci guda kuma ya sani tunanin
mutuwa
Innalillahi Wa'inna Ilaihi Rajiun Nace cikin zuciyata wani
dogon macijine wanda nake tsammanin yayini a tsaye
idan har baifini tsawo ba to ni kuwa bazan fishi ba bakine
kakkaura wani abu mai kama da dan kunne dake makale
a kunnensa na hagu shi ya kara fito da siffarsa ta masifa
da kuma razanarwa na lumshe idanuna ina jira ya sare ni
na huta daga inda nake tsaye inajin sautin kidan bandirin
dake tashi a daya gidan dake makwabtaka da ni da kuma
Maciji.
**
Bansan iya tsawon lokacin danayi a sume ba nidai na
farka naji wani abu yana gugar kafata na haska cocilaya
cikin tsoro da fargaba nida a tunanina rayuwata tazo min
karshe amma yanzu sainaji kamar macijin yabar kafata
na tabbatar da hakan alokacin da hasken fitilar ya dauko
min katon macijin nan a kwance gefe guda hakika idan
akwai abinda yafi mutuwa to shi wannan macijin yayi
domin kallo daya nayi masa na tabbata bashida rai an
kuma farayi masa rami aciki na juya hasken fitilar wajen
kafata don ganin abinda ke lasar kafata anan ne to na
gane abinda ya cinye macijin nan hasken fitilar ya dauko
min idon wata katuwar jaba mai dogon baki kamar
asuwaki tana lasar kafata ga tsammaninta nima ko
macijine nayi zunbur na mike tsaye sannan cikin zafin
nama na nufi katanga da gudu ina nayi tsalle na kama
katangar ta hanyar taka tarin katakon nan dake yashe
agindin katangar beraye da jabaye da kuma sauran ire
iren kwarin da suka saba zama cikin tsohon ginin wasun
su kuma suka nufi cikin ciyayin da sukayiwa gidan
kawanya koda na lura sainaga jaba tafi yawa fiyeda bera
agidan.
*
Nayi kimanin mintuna biya ina zagaya cikin gidan kamar
barawo ina tafiya da sanda kamar gajimare kamar yadda
nayi tsammanin sautin kidan dake tashi shi yabani damar
tsirga gidan batareda wani ya jini ba ginin gidan ginin
gidajen gwamnatine kamar dai yadda sauran gidajen
suke awannan titin angina shine a tsakiyar farfajiyar
gidan wannan shi ya bani damar zagayawa ko ina cikin
gidan.
Daya daga cikin abinda na lura shine katangar gidan data
raba gidan kanal mukhtar da gidan tanada tsayin gaske
akan katangar kuma kusoshi ne da miyagun kwalabe
masu barazana ga hannun duk wanda yayi kokarin
kamawa abu na biyu kuma dana lura na kuma gargadi
kaina shine gidan danake ciki akwai maigadi na gane
hakan ne saboda ganin wata yar rumfa akofar gidan
acikin rumfar na lura da wani kasko na kasa cike da
garwashin wuta jajawur wannan alama ce dake nuna
cewa maigadin tsohone don haka cikin gadara sainaci
gaba da zagayawa batareda fargabar komai ba.
Haryanzu sautin na tashi acikin dakin saidai kuma
wannan lokacin an canza kaset din daga bandiri zuwa na
turawa zanso ace nasa kowanene acikin dakin tuni
zuciyata ta fara zargin wanda ke dakin shin me ya hanashi
barci? Wannan tambayar ita tasani na nufi tagar dake
bangaren gaba da gidan wacce kuma itace take fuskantar
katangar gidan kana muktar nayi sa'a na sami tagar a
bude take banjira wani abu ba saina fara bude ta ahankali
har dai na sami yar kofar da zan leka to a sannan ne na
sake ganinta tana zaune akan kujera tayi tagumi a kusa da
ita kuma dan tsohon nan ne mai fuska kamar
matsatstsen lemon tsami yana gyangyadi bangama
mamakin abinda nagani ba sai naji wani na taba bayana
na juya cikin razana sannan mukayi ido hudu da Salman
yana murmushi daman nasan tanan zaka biyo yace dani
.Daman nasan tanan zaka biyo yace dani
.
Kada kayi mamaki da ganinmu anan Fadil.
Salman yace dani wannan alamace da take kara tabbatar
da maganar uwargidata kuma shugabata hajiya binta
inda take cewa duk inda kake ina biye dakai kuma
wannan gidan ma daka ganmu aciki ni na bada shawara
akama shi haya waya daya kenan yanzu tun lokacin da
hajiya binta ta dauko hayata.
Nayi shiru cike da mamaki lokaci guda kuma ina kallon
tagar dakin dasu hajiya binta suke
kar wannan ta dameka salman yace dani sun riga sun san
kana cikin gidan domin tunda ka shigo titin nan nake biye
dakai duk kuma zagaye zagayen da kakeyi ina kan soron
dakin nan ina kallonka don haka nake kara gargadinka da
cewa kayi kokari kaci nasa idan kuma harkay kuskura ka
fadi to ka lissafa kanka cikin matattu bita can ka tsallaka
da fatan zakaci nasara kafin na bude bakina salman ya
zagaya ya shige dakin koda na lura da inda salman ya
nufa sainaga wani dogon tsani jingine.
**
Abu na farko da ya fara yiwa idona maraba shine manya
manyan karnukan dake zagaya gidan suna gurnani kamar
saci babu kamar yadda badura ta sanar dani cikin
wasikarta kofofi goma sha biyu ne reras kowaccensu tana
fuskantar yar uwarta idan ka fita daga wannan sai ka
shiga waccan daga kan katangar da nake makale rib da
ciki ina iya hangen kowace kofa dauke da sojoji masu
gadinta guda huku kamar dai yadda badura ta sanar dani
ina iya kuma hangen karnuka uku uku akowace kofa
tsoro ya dada kamani nayi matukar tsorata da karnukan
nan hakan nema yasa na fara tunanin abinda yafi hadari
cikin abu uku
na farko dai soja na biyu bindiga na uku kuma karnukan
duk da yake nasan bindiga farat daya zata hallaka mutum
amma hakan baisa zuciyata ta amince da cewa bindiga
tafi kare hadari ba nasan dai bindiga bata harba kanta san
an harbata haka shima soja sai yaga abin harbawa zai
harba din to amma kare fa?
Na sunkuyo da kaina kasa na sake nazarin gidan nayi sa'a
saboda daidai inda nake saitin kofa ta karshe ne daga nan
babu wata kofa saidai kawai mutum ya tsinci kansa tsakar
gidan wacce a haskake take tsakar gidan nayi karo da
kare saidai kuma in har abinda badura ta fada gaskiyane
to da wahala naci karo da kare ko kuma maigadi tunanin
haka shi ya baiwa zuciyata damar raya min cewa nayi
kunar bakin wake na fada tsakar gidan amma duk da
haka saida na dan saurara akalla mintuna biyar ina
sauraro tare kuma da kallon tsakar gidan duk tsawon
lokacin nan banji komai ba bankuma ga wani abu da zai
sani shakkar shiga gidan ba.
A cikin dan lokacin danake jiran ko zanji motsin wani abu
daban ne sai tunanin Amina ya fado min wacce rabona
da ita tun safe data kawo min abinci takuma ce zata dawo
da daddare amma bata dawo ba wanda a karshe na
godewa Allah dayasa bata dawo ba saboda zuwan nata
yana iya kawo min bata lokaci wajen fitowa neman
sarkar sanin cewa yanzu fa tsakanina da Amina baifi taku
kadan ba shi ya jefo da tunanin ta zuciyata daman ance
rashin sani yafi dare duhu don na tabbata da Amina tasan
irin hadarin da nake ciki yanzu to da takawo min sarkar
har gida to amma bata sani ba nima kuma banason ta
sani din domin rashin sanin nata shi yafi alheri agareni.
Wani zakara yayi kuka na duba agogona karfe daya da
minti daya alamune da suke nuna cewa gari ya kama
hanyar wayewa nan da nan nayi tsalla na dira tsakar
gidan nayi sa'a ba'a kan dandamali na fado ba saboda
gindin katangar a zagaye yake da koriyar ciyawa tattausa
ina dirga sai mukayi arba da juna wani daki mai
kyakkyawar kofa ta gilas saidai kuma gilas din kamar
madubi yake idan na lekada niyya kaga abinda ke cikin
dakin saidai kaga fuskarka.
Na matsa ahankali ina sanda zuciyata kuma tana bugawa
tsakanin hakarkarina kamar dai yadda badura ta fada
dakin daga bangaren hagu yake tsakanin dakin da kofar
gidanta goma sha biyun zaikai kimanin sawu na dogon
mutum ashirin daga nake tsaye ina iya jin gurnanin
mugayen karnukan dake gadin kofar
idan kuma har ba hancina bane ke fada min karya to ina
iya shakar warin tabar da masu gadin ke sha.
Good Morning Sir
wani soja yace da dan uwansa acan daga bangaren na
gidan abinda yabani mamaki don na lura da cewa shi
soja bashida dare bashida rana ko yaushe safiya ce na
matsa kusa da kofar dakin gabana ya fadi wannan ya
samo asaline saboda sanin cewa tsakanina da sarkar data
jefa ni cikin bala'i baifi taku uku ba saidai kuma ba anan
gizon ke sakar ba kofar ta gilas ce shafaffiya babu alamar
gurin budewa ajikinta.
Ina na taba ina tsoron kada na jangwalo wani sabon
bala'in to idan ma na taba din tayaya zan budeta? Nayi
kimanin mintuna biyu ina zagaya dakin daga karshe ne na
gano wata taga abayan dakin daga bangaren yamma
tagar yar karama ce itama kuma a rufe take da gilasai
saidai ita tana da wajen budewa ina jan wani karfe mai
ruwan azurfa sai tagar ta bada wata yar kara ta bude
sannan na leka cikin dakin kamar yadda badura ta sanar
dani a zaune a tsakiyar gilas din wanka ke kan wani katon
tebur mai ruwan gwal sarka ce tana kyalkyali kamar
walkiya hakan yanada nasaba ne da irin matsanancin..
.
Sarka ce tana kyalkyali kamar walkiya hakan yanada
nasaba da irin matsanancin hasken dake zagaye da sarkar
wanda kuma badura ta gargadeni da cewa kada na sake
na matsa kusa da gilas din saina kashe wutar dakin gaba
domin kamar yadda tace wai akwai na'urar kararrawa
mai aiki da inuwa kuma itace ke gargadin sojoji dakuma
karnukan gidan cewa gida babu lafiya
.
Na dada bude tagar sannan na zira kafata cikin dakin zan
dago kafata ta hagun kenan sai naji wani abu ya mari
fuskata ya kumayi sama da wani irin kuka da zaka tsaga
jikina alokacin ba zaka sami jini ba don tsoro nayi kikam
ko cikakken numfashi bana iya yi kafata daya aciki daya
awaje sai bayan dana dubi tsakar gidan ne sannan abin ya
ban haushi ya kuma bani dariya a zaune akan katangar
gidan wani kyakkyawan aku ne shida matarsa yana
kallona yana wani irin kuka ban ko kara komawa takansa
ba na fada cikin dakin ta tagar dumi ya bugi fuskata
saboda matsanancin zafin dake gauraye a dakin
sakamakon kwayeyen wutar lantarkin da suka zagaye
dakin a kalla goma sha uku na dubi gilas din da sarkar ke
ciki sannan na dubi hasken dake zagaye da dakin sannan
ne nafara gaskata maganar badura zaiyi wuya ko kuma
ince bazai yu ba ka gane cewa gilas din da sarkar ke ciki a
jone yake da na'ura mai kararrawa saidai ko an fada ma
ko banza dai badura ta taimaken tanan wajen duk da
yake kuwa har yanzu ban amince da ita ba ni aganina duk
zakin bakin datayi na yaudarane.
.
Shawara ta kasa yankuwa agareni na duba dakin sama da
kasa banga wajen kashe kwan ba sai bayan danayi minti
gudane ina dube dube sannan naga abin kunnawar
(swich on/swich off)
su na gani a rubuce ajiki cikin harshen turanci wajen
kunnawa da kashewa kenan sai dai kuma abin mamaki ko
kuma ince abin bakin ciki wai aka rasa inda za'a ajje abin
kunnawar sai akan teburin nan inda gilas din da sarkar ke
ciki da farko har na matsa da sauri domin na kashe cikin
dana fara nufar wajen sai kwakwalwata ta fara yi min
ihun gargadi
kai wawa baka ganin dabara ce aka hada don kama
marasa gaskiya irin ku baka ganin kana matsawa kan
teburin inuwarka zata fada akai bayan kuma an fada ma
na'urar ce keyiwa sojojin gidan nuni tana aiki kuma ne da
inuwar wanda yazo kusa da ita nayi turus na tsaya koda
na dubi inuwata sai naga tsakaninta da gilas din baifi
takun hannu ba nayi sauri naja da baya to a daidai
lokacin ne kuma kaddara tayi halinta.
.
Ba zato ba tsammani sai ga dan tsuntsun akun nan ya
fado dakin kamar daga sama ashe nine nayi kuskure ban
rufe taga dana shigo ba cikin kankanin lokaci
kwakwalwata ta fara min gargadi da irin aika aikar dake
shirin faruwa nan da nan na kaiwa akun nan cafka yin
haka shi ya tsorata akun shi kuma ya nufi kan gilas din
yana fuffuka da fika fikansa atake anan Al'amaru suka
watse inuwar akun tayiwa gilas din rumfa alokaci guda
kuma sai duk naji gidan ya dauki kukan jiniya mai
firgitarwa
TA FARU TA KARE
nace cikin zuciyata ina amfanin badi ba rai tunda abinda
nake gudu ya faru me kuma zanji tsoro atake anan na
nufi wajen gilas din da gudu haryanzu jiniyar bata daina
kuka ba saboda karin inuwa da aka samu akan gilas din
na ina zuwa saina bude gilas din na dauke sarkar na jefa a
aljihu sannan na kashe wutar dakin gaba daya na nufo
kofar dakin da gudu na manta da cewa ashe a rufe take
ina zuwa sainaci karo da kofar gilas din ya tarwaste ni
kuma na fado rub da ciki adaidai lokacin naji gudun
sojoji sun nufo kofar gidan ta goma sha biyu gidan ya
rufe da hayaniyar sojoji daga daukar sarkar zuwa ga
fitowata naji harbin gargadi da bindiga yakai dari.
.
Nayi sauri na mike sannan nayi cikin gidan da gudu da
nufin na sami gurin buya amma abin yaci tura filin gidan
har yanzu a haske yake da lantarki kuma babu wajen
buya dana lura da bangaren hagu sai naga wata yar
siririyar hanya wacce bangon gidan da wani ginin daki
suka kirkireta da gudu na shige kwanar da niyyar na sami
wajen buya ina zuwa sainaga ashe hanyar wani daki take
fuskanta abubuwa suka taru suka rikice min can kuma
sojoji sai harbe harben iska sukeyi adaidai lokacin ne
kuma naji ana bude kofa ta karshe wacce take fuskantar
gidan ina tsammanin da katuwar sarka suka daureta don
haka suka sami tangarda wajen budeta na duba sama da
kasa ko zanga wajen buya amma babu nasan kuma ko
wanne lokaci daga yanzu sojoji ne zasu shigo farfajiyar
gidan na kuma dubi katangar sai naga duk tsallen danayi
bazan kamo ta ba idan kuma nayi nasarar kamota ma to
na tabbata ba zan dira da yatsuna ba domin kaifafan
kwalabe ne da kusoshi akan katangar suna kuma maraba
da hannun duk wanda yayi kokarin tsallaka katangar wau
wauhn amsa kuwwar haushin karnukan ta dako dodon
kunnena haushin karnukan kamar duka da guduma ne a
kirjina idan akwai abinda nafi tsoro bai wuce karnukan
nan ba da ace karnukan nan sun kamani gara ace da
bindiga aka harbeni.
Kofar da sojojin ke kokarin budewa ta fara yi yowa gaba
gaba tsoro ya sake kamani saboda ganin irin yadda
karnukan ke dukan kofar da jikinsu tun kafin ma sojojin
su bude su har sun kosa su shigo.
.
Fadil... Wata siririyar murya tayi kirana kofar dakin dake
fuskantar siririyar hanyar dana biyo ta bude tana sanye
da doguwar riga ta barci kanta babu dankwali
AMINA CE shigo nan tace dani adaidai lokacin ne kuma ta
kama hannuna muka shige dakin sannan ta maida kofar
dakin ta rufe duk da yake ta rufe dakin hakan bai hanani
jin gurnanin karnuka a kofar dakin ba.
.
11
Haba Fadil Amina tace dani cikin sheshshekar kuka me
yasa zakayi min haka? Yanzu tsakanina dakai har akwai
wani abu da zai sameka ka boye min in daka fada min
kace sarkar kake so me zai hana na baka ita cikin ruwan
sanyi katuna fa irin son da nakeyi ma kafi karfin sarkar
awajena amma kuma......
Ta kasa fadar kalmar da take son furtawa saidai kuma na
gane abinda take kokarin fadi tana son tasan dalilin da
yasa na hauro gidan ne idan kuwa har bani da hujjar
hauro gidan to suna daya ya dace dani BARAWO.
Ba laifina bane Amina nace da ita wallahi tilasta min akayi
aka kuma fi karfina haryanzu amina bata daina kukan ba
amma jin cewa tilasta min akayi sai naga nan da nan ta
dago kai ta dubeni duba na nutsuwa sannan cikin
tattausar murya ta tambeyni
Wanene ya saka ka shigo gidan nan daukar sarkar?
Wadanda suka doramin laifin kisan kan da akayi a kaduna
na amsa mata kai tsaye
kana nufin kace duk akan sarkar ne aka dora ma sharrin?
Akanta ne aka kashe zainab na karashe mata.
Amina tayi shiru na dan lokaci sannan ta dago kai tace su
wanene Fadil? Ina bukatar jinsu yanzun nan bana bukatar
wani noke noke kuma.
Sunada yawa nace da ita amma shugabarsu itace kishiyar
mahaifiyarki hajiya binta yayarki kuma badura itace ke
taimaka mata ita da wani dan ta'adda salman sannan.....
Nayi shiru cikin kaduwa kallon da amina keyimin shi ya
sani rawar jiki kallone da zan iya fassarashi da kallon
tsana tunda nake da Amina ban taba ganin tayi min irin
kallon ba.
Ci gaba mana tace dani cikin kakkausar murya akwai
daya yar uwar taki Amina sai kuma wani dan tsoho da
bansan ko wanene shi ba nace da ita,
da wa kuma? Ta sake tambayata.
Sukenan na tabbatar mata.
Karya kake tace dani cikin kukan takaici sai wa kuma ka
rage guda daya idan bazaka fada ba bari na fada ma
dayan
Fadamin to nace da ita bakina na rawa
KAI NE tace dani wallahi daman tun farko saida nayi
zaton haka nasan Hajiya binta daman ba kaunar mu take
ba bayaga haka ma.....
Ta fashe da kuka ka cuceni Fadil wallahi ka cuceni an
hada baki dakai domin acuci mahaifiyata sannan tayi min
wani irin kallo sannan tace.
Fadil ta kira sunana muryarta a dusashe
Na'am na amsa muryata na rawa
Meyasa ka yaudareni ta tambaya
ba yaudararki nayi ba na amsa mata Haba fadil tace dani
na fa karanta takardar da badura ta aiko ma ta soyayya
wacce acikina ne har take fada ma sirrin gidan nan kaci
amanata ka kuma cuceni tunda kaso yar uwata sanan
kuma ka amsa min wai kana sona.
Ni bance ina sonta ba nace da ita
amina kin kasa fahimtata wallahi ba laifina bane kuma
takardar da kika karanta baki karantata har karshe bane
da kin fahimci gaskiya
kaima kasan bazan iya karanceta ba saboda irin kalaman
da badura keyin amfani dasu wai tana kaunarka wallahi
zuciyata bazata iya daurewa kuma......
Muryarta ta sake dusashewa ta fara kuka sannan ta dago
kai muka hada ido da ita.
Babu abinda zakacemin na yarda dakai Fadil tun lokacin
dana sami takardar da badura ta rubuto ma nake tunanin
irin bakin cikin da zan fada in har abin yazama gaskiya sai
gashi kuma ya zama din
wai fadil da kanka da kuma hankalinka aka hada baki
dakai don acuci mahaifiyata ko?
Wato wannan shine sakayyar irin soyayyar dana nuna
mak? Tun da nake dakai Fadil bantaba nuna ma rashin
kauna ba ban kuma taba cutar ka ba duk da yake ma
nasan daman can kai ba kaunata kake ba....
Kada ki fadi haka amina nace da ita ke kanki kinsan da
bana kau..... Karka bata bakinka tace dani alokaci guda
kuma ta miko min siraran kyawawan yan yatsunta na
hannu.
Bani sarkar da ka dauka tace dani nima ina sonta kamar
yadda hajiya binta take sonta da farko nayi niyyar kin
bata amma nasan hakan bai yiyuwa domin alokacin
daidai take data kwala ihu sojoji su cika dakin.
.
Mukayi shiru na dan lokaci muna kallon juna ko kiftawa
bamayi na dubi Amina babu alamun kauna a fuskarta sai
alamun tsana dakuma zargi da suka fito karara a
kyakkyawar fuskarta na danyi jim sannan na tura hannun
nawa a aljihu na zaro sarkar na mika mata amina ta karbi
sarkar ta buda rigar mamanta tajefa ta ciki sannan tace
dani.
Bace min da gani
saboda me Amina na tambayeta
saboda bana kaunar ganin mayaudari kuma makiyin
mahaifiyata ta amsa min
me yasa ki tunanin ni mayaudarine kuma makiyin
mahaifiyarki na sake tambayarta.
Saboda an hada baki dakai domin ganin an cuci
mahaifiyata kuma ka yaudareni ta hanyar hada soyayyata
data yar uwata badura naji na yarda tunda idan ma nayi
miki bayani bazaki gani ba nace da ita.
Saidai kuma kina ganin duk wannan yakai ace kin koreni
zuwa ga halakata? Na tambayeta maganar tayi tasiri
akanta saboda ganin irin yadda tayi kasake tana kallona
kuma tana wasi

Please Login or Register in order to submit comment