Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ganni nafito daga dakinta a daidai
lokacin data mutu me kake tsammani? Kanajin yan sanda
zasu yarda da karyata cewa maganin ciwon ciki nazo
karba a dakinta na taradda ita a mace?
Na saba jakata a kafada sannan na dubeta nace da ita ina
dan makullin motarki ko kuwa kin baro shi a dakin?
A'a gashi nan tace dani ta miko min dan makullin na jefa
a aljihuna sannan nace tashi mu tafi ta dauki jakarta mai
taya ta biyo ni zuwa kofar dakin cikin mamaki da rashin
fahimtar al'amarun dake gudana duk da yake dai nasan
tasan babu lafiya amma bazan taba hakura na fada mata
ba sai mun fice daga cikin otel dinnan
.
Bani jakar taki saiki rike wannan na ce da ita ayayin dana
mika mata tawa jakar ni kuma na karbi tata akwatin ita
dai batayi min musu ba ko kuma tambaya kawai dai tana
bina kamar kumama mun kawo hawan benen na karshe
kenan sai naga dan motsatstsen tsohonnan yana kokarin
shigewa wani daki nayi sauri na matsa kusa dashi da
farko nayi niyyar na manta dashi amma sai nayi tunanin
me yiwa ya leka dakin yaga abindake ciki don hakane
yake kokarin bace min sa'adda ya hango ni babu mamaki
ma yanzu yan sanda suna kan hanyarsu zuwa otel din
Na rarumi kwalarsa na hada shi da bango kafafunsa da
kyar suke taba kasa sannan nace dashi cikin fushi
ka manta da duk abunda ya faru dazu ka gane ko? Na
buga matsa tsawa ko da anzo ana tambaya to amsar ka
itace banga kowa ba in ka sake ka kara cewa wani abu
daga nan ba na saina na fada maka ba na sake shi yafado
akan tsintsiyar dake hannunsa yaso yabani tausayi amma
dana tuna da masoyiyata badura da bala'in da take cki
saina dake zuciyata na sake buga masa harara ka jiko?
Nace dashi
Toh ya amsa cikin irin muryar da zakaji yayin da ka shake
zakara abinda nake nufi nace dashi
koda yan sanda zasu tambaye ka kokaga wanda ya shiga
daki mai lamba uku ko ya fita to amsarka itace
BAN GANI BA
toh yasake amsawa ban damu ba nasan ko ya leka ko kar
ya leka dole ne nan da awa daya a sami gawar zainab dan
tsurkun tsohonnan kuma dole ne yace ya ganni amma
yanzu nasan nayi maganin na dan lokaci
.
Badura na rabe ajikin bango jiki na rawa batace dani
komai ba na duba agogona dakyar naga karfe nawa ne
yanzu sainaga babu shi babu labarinsa na juya nakama
hannun badura dake tsaye kamar gunki muka nufi kasa
nasan na maka ban damu dana koma dakin badura ba
domin duba agogo na tabbata tataba anan na yada shi ko
yake nasan agogo ba wani abu ne ba dan yan sanda sun
sami agogo wannan wani abu ne da bai shafeni ba domin
kuwa ba ni kadai ne mai sa agogo ba tunanina ya katse
ayayinda naji wani abu kamar kukan jiniya na fizgi
hannun badura mukayi kasa da gudu muka fice ta kofar
baya
yi sauri ki kaimu inda motarki take nace da ita batayi min
gardama ba sai kawai ta wuce gaba da gudu nima na bita
a halin yanzu ta fara gane lamarin bata bata lokaci ba duk
da yake batasan meke faruwa ba amma nasan ta san
muna kokarin kaucewa yan sanda ne kafin na karaso inda
motar take tuni ta fada ta tashi motar tayi baya kadan
zuwa saitin da nake banyi wata wata ba sai kawai na bude
gidan gaba na fada na jawo na rufe duk wannan ya faru
ne acikin dakika talatin.
Badura ta fizgi motar da gudu kamar walkiya muka nufi
kofar otel din dake baya don kuwa nasan yanzu yan
sanda sun cika daya kofar wata mata ta dauki kara
ayayinda motarmu tayi kan danta dake wasa a tsakiyar
titin otel din badura ta dauke kan motar tsakanin tayar
motar da kafan yaron baifi takun hannu daya ba duk da
haka bamu tashi ba kaga da laifi ya karu kenan muna isa
kofar otel din dake baya sai naga sai naga maigadin kofar
da wayar tarho a hannunsa nan da nan kwakwalwata ta
fada min cewa babu mamaki yan sanda ne sukayi masa
waya ya hana mu wucewa kafin na gargadi badura ita har
ta yanke hukunci ta nufi kofar da gudu kamar harsashi
maigadin ya tsaya cak yana kallon ikon Allah yana baiwa
kansa shawarar ya bude ko kar ya bude daga karshe dai
ya ga in yaki budewa su zasuyi asarar kofarsu domin
kuwa mu bamuda niyyar tsayawa ya bude kofar yayi
tsalle yakoma gefe guda mu kuwa muka wuce kamar
walkiya na jua baya na kalli otel din.
Sai naga duk mutane sun leko ta tagogi suna kallon mu
In ka dauke matar nan da muka kuskure danta da taku
daya ta dora hannunta akan danta wanda ke rungume a
kirjinta tana kukan murna badura ta kara take totur din
motar muka harba kan titi kamar kibiya dana duba
malekin motar sainaga ya nuna muna tafiyar kilo
mita.......
Dana Duba malejin motar sai naga ya nuna muna tafiyat
kilo mita dari da shirin a sa'a guda na jingina kaina
akujerar motar na rufe idona sannan nafara me kake jin
zai faru idan taya ta fashe awannan lokaci?
Lallai muna bukatar addu'a
.
******* ****** ******* ******* ********
.
Agogon dake jikin motar ya nuna karfe shida ta rabi na
safe a daidai lokacin da muka kawo mararrabar da zata
fitar damu wajen gari har yanzu bamu yanke inda zamu
nufa ba kokari na dai kawai shine mu fice daga kaduna in
yaso daga nan sai muyi shawarar inda zamu
a yanzu dai kilo mitar mu biyar da barin kaduna Badura
ta rage gudu sannan ta dauke kan motar muka shiga wata
yar siririyar hanya wacce ta shiga cikin daji muka wuce
ciki da gudu hakika badura tana kokari domin ki ni nake
tuka motar da kyar ne in zan iya irin gudun hadarin da
takeyi batareda gabana ya fadi ba saida mukayi gudun
kilo mita daya da rabi acikin dajin sannan muka isa wani
waje mai yawan bishiyoyi manya manya da kuma koren
gayayyaki ko ina tayi kwana ta motar ta shiga cikin
sarkakkiyar bishiyoyi da ganyayyakin har saida ya
zamanto bazaka iya ganin mu ba idan kanadaga waje
sannan ta taka burki ta tsaya ta kuma kashe motar
sannan duk muka fito daga motar.
Ta juyo muka kalli juna sai tayi min murmushinta mai
sanyaya zuciyar masoyi a karo na farko kenan tun lokacin
dana sami gawar zainab,
sai naji raina ya danyi sanyi.
.
Me ke faruwa? Tace dani daidai lokacin data hau bakin
motar ta zauna nikuma ina zaune akan wani reshen
bishiya dake kasa kasa
ya kamata ka bani labarin tun daga farko.
Tace dani sannan taci gaba da cewa ni duk ban gane
abinda ke faruwa ba
Na gyara zama sannan nace da ita zainab ta mutu tayi
min wani irin kallo kamar wadda take zaton kaina ya
tabu.
Me kake nufi ta tambaya a rufe abinda nake nufi shine na
sami zainab a kwance akan gadonki matacciya sannan
naci gaba da cewa in duk wannan bai ishe ki ba to hadda
ramin harsashin bindiga a kirjinta
Badura ta dafe kirji ta lumshe idanu nayi saurin dirgo
daga kan reshen da nake zaune na nufi inda take da sauri
na tare ta a yayinda ta fara gangarowea daga gaban
motar sumammiya.
Na kwantar da ita akan koriyar ciyawar dake shimfide a
ko ina cikin dajin sannan na bude motar na dauko
kwalbar ruwan yankarin dana saya tun kafin mu bar cikin
kaduna nafara zuba mata a fuska ina dan jijjigata can
bayan kamar mintuna biyu ta farfado ta bude idanunta
kadan sannan ta sake rufe su.
Na sunkuya na ciccibeta nasata a bayan motar sannan na
gyara mata kwanciya hakika tana bukatar hutu ahalin
yanzu na bar kofar motar a bude domin ta sami
isashshiyar iska sannan na koma gaban motar na zauna
ina tunanin abinda ya kamata na farayi a halin yanzu
hakika muna cikin bala'in da bansan karshensa ba sannan
tambayar nan guda daya ce wai shin wacece take son
kashe BADURA?
Kuma akan me? Ya zama dole nayiwa badura wasu yan
tambayoyi kafin mu bar dajin nan domin ina bukatar
sanin labarnta dana iyayenta da kuma sunan unguwar
datake a kano
.
Agogon motar ya nuna karfe bakwai na safe wato munyi
kimannin rabin sa'a kenan a dajin dajin yayi tsit bakajin
komai sai kukan tsuntsaye dana kananan namun daji
akwai alamar hadari a garin har yanzu ga kuma sanyi
saboda ruwan da aka kwarara duk da yake dai ruwan da
akayi a dajin bai kai na cikin garin kaduna yawa ba.
Na kunna rediyon dake gaban motar kade kaden hausa
dana turawa sai tashi suke daya bayan daya mintuna uku
suka shude batareda naji abinda nake jira ba
JAMA'A GA WATA SANARWA......
A daidai lokacin duk wani kade kaden dake tashi a
rediyon ya tsaya cak.
Sannan sai naji mai sanarwar yaci gaba da cewa
JAMA'A KUYI HANKALI DA YA'YANKU SABODA AN SAMI
WANI SAURAYI WANDA BA'A TABBATAR DACEWA SHIN
MAHAUKACI NE KO MAI HANKALI BANE
Wannan saurayi ya harbe wata ma'aikaciyar daba otel
nan kaduna sa'o'i uku da suka wuce don haka yan sanda
suna rokon jama'a duk wanda ya hangi inda ya nufa to ya
sanar dasu
ganin karshe dai da akayi masa yana tare da wata yarinya
wacce a dakinta aka kashe ma'aikaciyar otel din ana
kuma tsammanin yarinyar ma da suke tare rayuwarta
tana cikin hadari domin kuwa yan sanda suna zaton
yarinyar ta ganshi a yayinda ya kashe ma'aikaciyar otel
din ya kuma kamata a matsayin garkuwa don Allah
Jama'a a taimaka fari ne dogo dan kimanin shekaru
ashirin da daya yarinyar kuma dake tare dashi itama fara
ce yar shekaru goma sha takwas dukkansu suna cikin
bakar mota 505 lambar motar shine KN 0912 NS kuyi
hankali dashi domib ana zaton bashida cikakken
hankali.......
.
Na kashe rediyon jikina na bari sansassayan iskar dake
shawagi a lokacin bata hanani gumi ba sai yanzu ne kara
fahimtar irin bala'in dana sami kaina aciki hakika duk
wanda ya biyewa mace saita batar dashi yana kuma tare
da mummunar rayuwa
Da ace na manta da badura na fitar da sonta daga
zuciyata na kuma ki karbar ta alokacin datazo dakina a
otel din daba da duk wannan bata faru gareni ba gashi
yanzu laifin ma ni kadai ya shafa
.
Tunanina yakatse a daidai lokacin danaji kamar motsi a
bayan motar da farko na dauka tsuntsaye ne suke motsa
ganyeyyakin bishiya amma daga baya sai naji kuma
sawun mutum yana taka ganyayyakin nazaro kafata na
fito daga gaban motar da niyyar naga abinda ke faruwa
sannan na kalli madubin motar gashin jikina ta tashi.
Da farko na dauka iccen bishiya ne ya zunguri kuguna
amma daga baya sai tunanin bindiga ya fado min azuciya
kada ka motsa aka gargadeni daga baya.
Kamshin turaren danaji shekaranjiya a dakina shi ya bani
damar gane ko wanene ke bayana madubin motar ne ya
nuna min shi haryanzu yana sanye da farin wandonsa da
koriyar riga hancin bindigarsa a kuguna
.
Numfashina ya tsaya cak a daidai lokacin da bindigar
mutumin ke barazana yin ruwan harsashi a kuguna.
Kada ka sake ka motsa mutumin yace dani cikin wata
murya irin wadda zakaji a yayin da kayi magana acikin
hujajjiyar lasifika.
kayi kuma duk abinda na umarce ka
ya ci gaba da cewa idan kuma kayi kokarin yin wani abu
daban wannan shine zai zama motsi na karshe da zakayi a
duniya.
Abinda yafi bani tsoro shine badura bayan motar a
kwance sumammiya na tabbata in har yasan tana nan to
babu abinda zai hana ya karasa ta.
Nasan a halin yanzu kowa yake yiwa aiki na riga ya
yardamma kansa cewa an kashe saidai kuma abinda na
kaa fahimta anan shine shin me ya kawo wannan
mutumin nan?
Kuma yaya ma akayi yasan muna nan?
Duk wannan tunanin nayi shi ne cikin dakika ashirin
mutumin yasa hannunsa daya acikin aljihun wandona
dana rigata ya lalube ni ko ina a tsammaninsa ina dauke
da bindiga ko wani makami hannunsa dayan kuma yana
rike da katuwar bindigar dake kokarin yimin raunin da
bana tsammanin harsashinta zaiyi min.
Na tsaya nan yanata lalube ni kamar wani barawo bayan
dan lokaci kadan ya tsame hannayensa daga aljihuna na
gane hannayensa manya ne ta hanyar ganinsa danakeyi
ta jijkin madubin motar.
Ya tsaya nan yana kallona kamar wata sabuwar halitta
gabana yanata faduwa saboda tunanin abinda zai faru
har yasan Badura tana motar don na tabbata baisan tana
bayan motar ba yawun bakina ya kafe saboda abinda na
gani
BADURA na zaune a bayan motar tana kallon bayan
mutumin shi kuma duk hankalinsa ya tattaru a kaina nayi
kokari na yi mata alama da idanuna domin ta koma ta
kwanta amma hakan ya gagara ga dukkan alamu ita bata
ma san abinda ke faruwa ba.
.
Adaidai lokacibn ne ta juyo fuskar ta wajen madubin
muka hada ido da ita ta madubin babu alamar data nuna
cewa ta damu da bindigar dake barazana a kuguna nasan
taga mutumin ta kuma ga bindigar amma hakan bai ko
chanza kamannin fuskarta ba tana zaune kamar mutum
mutumi tana kallona sannan cikin abinda baifi dakika
biyu ba sai kyawawan labbanta suka fadada izuwa
murmushin da bai kai ido ba hantar cikina da hanjina
suka dankare a waje guda saboda tsabar kaduwa da
abinda na gani.
Hakika badura ta chanza min kama cikin dan kankacin
lokaci ta taso ahankali ta fito daga motar banga alamar
mutumin dake bayan yayi koda motsi ba shi dai kawai
bindigarsa ya ajiye a kuguna yana shirin harbawa
kada ka sake ka motsa mutumin ya sake gargadina har
yanzu murmushin yana fatar bakina gushe ba.
Wani kamar juwa ya fara daukata kamar zan fadi kaduwa
da tsoro da kuma mamakin abin dake shirin faruwa
agareni suka cika min kwakwalwata kada kayi zaton
murmushi da takeyine kawai ya bani tsoro a hannunta na
hagu tana rike da damin igiya sannan hannunta na dama
tana rike da yar' karamar bindiga mai kama da ta wasan
yara ko kadan ban zolayi kaina ba na tabbata bindigar
bata wasan yara bace.
.
ME KAKE JIRA DASHI NE?
badura tace da mutumin naga giftawar gindin bindigarta
cikin madubi kamar walkiya nayi kokari na goce kaina
amma ina na maka gindin bindikar ya daki tsakiyar kaina
sannan rana ta bayyana a idanuna taurari masu haske
suka maye gurbin ranar sannan duhu ya maye gurbin su
gabaki daya abu na karshe danaji shine maganar badura
tana ceewa
'Daure shi sosai don kasan kakkafar ne sannan ta
kyalkyale da dariya.
**
Bansan iya tsawon lokacin dana dauka sumamme ba
nidai kawai na farka na sami kaina a daure kamar damin
gero acikin awani dan kankanin daki nake da baifi na
tattabaru ba yana dauke da taga daya da kuma wata
katuwar kofa wacce tafi dakin kwarjini gadon dasu
badura suka kwantar dani dan kankani ne na katako yana
dauke da wata latsatstsiyar katifa mai kamar silifa a duk
lokacin dana motsa sai naji gadon na kokarin rabewa na
fado kasa tsakar dakin na mamaye da wani rubabben
kilishi wanda ga dukkan alamu zai sami shekaru uku
rabonsa da yaga ruwa in ka dauke wasu dagargazazzun
takalma dake daf da kofar dakin dakuma karzan sigari
guda daya akan tagar dakin babu komai sai tsabagen
zafin dake kokarin dafani da raina
Tagar dakin a rufe take kada kayi tsammanin kuma za'a
bar kofar a bude wannan shine ya hanani gane shin
yanzu dare ne ko kuwa rana?
Duk motsin da zanyi sainaji kamar gabobin jikina zasu
ruguje saboda tsabar dauri na dan dago kaina sainaga
gaban rigata a rine da bushshan jini alokacin ne
kwakwalwata ta fara aiki SOSAI.......
.
Alokacin ne kwakwalwata tafara aiki sosai abubuwan da
suka faru sun bayyana a fili a zuciyata.
.
Ko kadan banyi mamakin abinda Badura tayi min ba
domin kuwa wannan kadan ne daga yaudarar mata tarko
ne dai na riga na fada za'a iya kiransa tarko mai kofa uku
biyu daga cikin kofofin a bayyane suke sai dai babu halin
fita kofar farko yan sanda sun tsareta kofa ta biyu kuma
su Badura sun tare ta. Kada ka yi tsammanin su Badura
sun kawo ni nan ne kawai don jin dadi hakika nasan zasu
bukace ni da wani abu shin toh menene toh dalilin
kamani?
.
Ya zama dole na samu kofar nan ta uku wacce na tabbata
itace zata fitar dani daga bala'in dana fada a halin yanzu.
Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji muryar Badura
a kofar dakin.
Har yanzu bai farka bane? Baduta tace
ina tsammanin tana magana ne da bakin mutumin nan
wanda har yanzu na kasa fahimtar sunansa.
Bai farka ba mutumin yace da ita
kaduba shi dazu ne? Badura ta tambaye shi
Sa'o'i biyu da suka wuce kenan yace da ita
daman ai na ce maka ka dake shi kadan kai kuma ka doke
shi da karfi, meyasa bakayin abinda aka sa ka sosai ne ?
Kaga shekaranjiya ma haka kaso ka bata mana shirin da
mukayi wata shida munayi.
Ance kazo da wuri amma saida ka bata lokaci yanzu daya
sa mun fice daga dajin yaya za'ayi ka same mu? Kaga fa
wahalar da ka bani badon Allah yasa dabarar yin suman
karya ta fado min ba da yanzu shirin ya baci.
Kiyi hakuri mutumin yace da ita Badura kinsan dajin ne
wahalar ganewa ne dashi kuma ke kanki kinsan da wahala
a kai mutum cikin wannan dajin da daddare ya gane shi
da rana don haka daman na ce ki kaini da rana kika ki
to.....
Kada ka dame ni da surutu badura ta katse masa hanzari
in kasan bazaka iya aikin ba gara tun wuri ka fada mu
sami canji
kada kiji komai mutumin yace da ita daga yau bazan sake
yin kuskure ba bari na shiga naga ko ya tashi
Yi sauri toh badura tace dashi zaka same mu a babban
falo.
.
Jikina na rawa na koma da sauri na rufe idona kamar ina
barci a daidai lokacin da kofar dakin ta bude mutumin ya
shigo dakin yana tafiya kamar baya so haryanzu yana
sanye da kayansa na gado kora da fari ga dukkan alamu
mutumin yana tsananin kishin tutar Najeriya tafka tafkan
hannayensa masu kama da mahuci suka dafa kirjina
sannan ya kama kwalar rigata ya jijjigan na bude idanuna
na kalle shi ya kalle ni jajayen hakoran suka fara wani abu
dashi yake tunanin murmushi ne.
Barka da zuwa dan tsako yace dani daga yanzu sai abinda
aka sa ka shi zakayi haushi ya kamani na daga kai na tofa
masa yawu a bakar fuskarsa mai kama da ta biri nan da
nan idanunsa suka kada sukayi jajur kamar garwashin
wuta ya daga hannunsa ya sharara min mari wani abu
yabi ta kwakwalwata sannan ya gangaro ta babban dan
yatsan kafata da farko na dauka kunne na ya fita banajin
kome sai irin karar dazakaji ayayinda ka kara kunnen ka a
kan titin motoci hakika ba'a taba yimin mari irin wannan
ba.
Bayan nayi kokari na dawo da numfashina sai na sake
tofa masa yawu amma wannan karon sai na kasa jajayen
idanunsa suka tsoratani suka kumayi min kashedin cewa
yanzu fa in na sake kara marina toh kurumcewa zanyi sai
kawai na koma kan gadon na kwanta har yanzu akwai
murmushin mugunta a fuskarsa wuka ta fado hannunsa
daga bako ina ba don ko ni kaina bansan daga inda ya
zato ta ba nayi tsammanin fede ni zaiyi amma daga
karshe sai na ga ya kama igiyar dake jikina ya fara
yankewa.
.
In ka sake kokarin tofa min yawu ya gargade ni sainayi
maka marin da uwarka bazata gane ka ba.
Gara ma ni inada uwar nace dashi kai taka uwar ma ba a
san ta ba.
Idanunsa suka sake kaduwa amman wannan karon bai
kawo min mari ba sai yawai yaci gaba da tsinke igiyar
bayan jiran danayi kamar shekara awurina daga karshe
na sami kaina ya warware igiyar sannan ya kama wuyan
rigata ya tashe ni tsaye naji kamar kafata bazata iya
daukana ba kwana biyu a daure baci ba sha ba wasa bane
saura kadan na fadi amma sai kore da farin ya taro ni ya
kama hannayena yana jana kamar mai koyon tafiya
Muka fita daga dakin muka shiga wani da bai fi wanda
muka fito yanzu kyau ba daga gefen hannun dama akwai
kofofi guda biyu sai mutumin nan kore da fari yace dani
shiga kayi wanka ina nan ina jiranka ka kuma shiga
taitayinka ya gargade ni na lallaba na shiga bandakin ta
hanyar dafa bango naja kofar na rufe bandakin yafi dakin
da aka daure ni girma da kadan yana dauke da kwamin
wanka irin na turawa guda biyu kowannensu yana dauke
da famfo daya da kuma shaya daya akwai katon madubi
a manne a jikin bangon bandakin daga kudu na dubi
fuskata ajikin madubin sai naga duk ta fada lallai naji jiki
ciwon dake kaina yanzu ya daina zafi sosai na lallaba na
tube kayan dake jikina sannan na kunna shaya na shiga
karkashinta ruwan yana kwarara akaina ni kuma ina
wanke busashshen jinin dake kaina Lokaci yayi da
yakamata na nunawa baki mai kore da fari cewa nima fa
ba matsoraci bane nima fa ba karamin shaidani ne in dai
har mutum ya biyo dani da hanyar shaidancin to zan
nuna masa na fishi.
.
Bayan na wanke jikina tsaf na kuma shafa mai sai na sa
kayana sannan da daki kofar bandakin da kafata ta bude
na fito ina muzurai wai dan ya gane cewa to yanzu babu
wasa mutumin ya dago ya kalle ni a yatsine a hannunsa
na dama jakata ce wacce na dauko daga hotel din mu
shekaranjiya lokacin da muke shirin gudu,
Yi sauri kasa kayanka suna can falon suna jiranka yace
dani.
Sannan mutumin ya jefo jakar saitin fuskata da farko
nayi niyyar na kauce dan kada jakar ta sameni a fuska
amma dana tuna da halin danake ciki yanzu bana tsoro
bane sai kawai na tsaya waje daya ina jiran jakar ta
karaso nasa hannun hagu na cafe ta na girgiza ta a
gabansa sannan nace dashi.
Kaje kacewa uwarka badura ta jirani minti biyu fuskarsan
ta canja kala daga baki zuwa toka toka na kalle shi na
fashe da dariya
matsoracin mata nace dashi karka dauka ni ma tsoranta
nakeji kamar ka hannayensa suka dunkule ya fara
matsowa inda nake tsaye in yana tsammanin zan tsaya ya
dakeni to lallai yana bukatar sake sabon tunani naja da
baya ina duban ko ina cikin dakin ko zanga makami.
Can sai na hango wani manjagara a jingine a kofar
bandakin daga hannun hagu nayi sauri cikin dakika biyu
saiga manjagaran ya fado hannuna dakin yayi shiru
bakajin komai sai karar disar ruwa a bandakin dake
gefenmu.
.
Kada kayi fada shi SALMAN muryar badura ta ratsa
shirun dake dakin mutumin yaja da baya jiki na rawa
sannan ya daka min harara ya juya ya fuce daga dakin
yanata faman hadiyar zuciya.
.
A karo na farko tun ranar da aka danamin tarkon sai na
gane sunan mutumin nan mai koren wando da farar riga
SALMAN bantaba jin suna irin wannan ba mukayi ido
hudu da badura tana tsaye a kofar dakin wacce nake
tsammani zata kaini babban falon sannan sainaji gabana
ya fadi kofar dakin ta bude wata kuma Badurar ta fito
Al'amarin zai baka mamaki idan nace maka na kasa
banbancewa tsakanin yan matan biyu da suke kallona
kamar a majigi suna sanye da bakaken riguna dogaye
anyi musu adon fari a wuya muryarsu iri dayace kamar
su daya babu banbanci ko kadan tsawon su daya kalar
jikinsu kuma daya ce idan aka hada su su biyun zaka iya
kiransu BADURA waccan badura dana sani amma hakika
ayanzu bazan iya cewa wannan ce Badurar dana sani ba.
.
Muna son magana da kai idan kagama shiryawa sannan
daya badurar ta ce.
Badura da amira shine sunayenmu idan ka shirya muna
jiranka a falo sannan sukayi min murmushi iri daya suka
juya suka nufi dakin nayi kokarin gane banbancinsu
amma nakasa tafiyarsu iri daya sannan na tambayi kaina
tambayar da zata fitar dani daga tarkon dana fada shin
WACECE BADURAR ?
WACECE KUMA AMIRA ?
Na tabbata daya daga cikinsu itace ta harbe zainab. Amira
kenan?
Na tambayi kaina wacece to Amira daga cikinsu duk
abinda yafaru tun daga farko har zuwa yanzu sai ya zama
kamar mummunan mafarki agareni kiran da Salman ya
kwada min shi ya tabbatar ba mafarki nakeyi ba.
**
Ahaka na shiga dakin a rude na tsaya a bakin kofar farlon
kato ne mai dauke da kujeru goma sha shida kowanne
bango na dakin yana dauke da kujeru hudu kyawawan
kilishin mai taushin gaske ya mamaye dakin a kusuwar
dakin dake bangaren gabas akwai katuwar kanta mai
dauke da littattafai sama da dari bakwai kamar dakin
Al'huda huda bana tsammanin gidansu ne sai dai in na
wani ne suka ara koma na wanene zan iya cewa dakin ya
tsaru daidai misali
.
Shigo ka zauna mana badura tace nashiga cikin dakin a
hankali tattausan kilishin da ya mamaye dakin yana
barazanar shanye kafata iya idon sawu
na zabi kujera daga bangaren arewa na zauna ina
fuskantar su Badura ta Amira suna zaune a kujera guda
idan har kasan
sunansu shine Badura Da Amira to zaka iya kiransu
cikakkun yan biyu idan kuwa baka san sunayensu ba zaka
iya kiran Badura inuwar Amira kokuma Amiran inuwar
Badura.
Da gangan suke komai iri daya domin kawai su rikita min
kwakwalwa
Salman na zaune acan jikin bango a kusan kantar nan
mai dauke da tarin littattafai muka hada ido dashi akaro
na farko tun da muka hadu dashi sai yayimin murmushin
daya kai har idonsa.
FADIL daya daga cikin su tayi kiran sunana lokaci yayi
daya kamata kasan duk abinda ake ciki....
Me ya shafeni? Na katse mata hanzari
kwarai kuwa ya shafeka tace dani in zaka bani dan lokaci
yanzu kuwa zakaji abinda ya shafeka sannan taci gaba da
cewa kasan KANAL MUKHTAR ? Nayi shiru na dan lokaci
babu alamar razana a fuskata amma daga cikina har
zuwa kwakwalwata sun daina amfani alokacin.
.
Tun ranar dana farko kano sai yanzu ne na tuna da
AMINA Yarinyar datake matukar sona amma haryanzu
Allah baisa min sonta ba magana ma inayi mata ne don
kar tace na wulakantata duk da cewa bansan abinda
wannan yan biyun ke nufi ba murmushin dake yawan
bayyana a fuskarsu bana sonsa murmushine irin na
mugunta nakuma kasa gane abinda suke nufi idan baka
sani ba bari nafada maka ko wanene Kanal Mukhtar
.
Fari ne dan gajere kakkaura mai yawan tarin gashin baki
tsohon sojane wanda ahalin yanzu shekararsa goma
dayin ritaya daga aikin soja mutane da dama suna jita
jitar cewa shekarunsa saba'in a duniya wasu kuma...
.
Mutane da dama suna jita jitar cewa shekarunsa saba'in a
duniya wasu kuma sunce ya kusan tamanin Allah ne
kawai da mahaifiyar Kanal Mukhtar suka san yawan
shekarunsa a duniya

Please Login or Register in order to submit comment