Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwa ta sa a jakarta ta nufi falo, hanun sadiq ta kama sannan suka fice, cikin sa'a suka samu adai daita sahu shi ta fara saukewa sannan itama ta nufi skul sanda taje mkranta bbu mutane da yawa sannan ta nemi shan layin baya kamar yadda ta saba zama ta zauna, haka aka zo aka gama karatu sannan suka nufi gda

Da yamma hajiya ta aike ta wani karamin super market, ta shirya cikin wata doguwar riga baka tayi roln da pink din gyale, da pink din takalmi, hoda kawai ta shafa a fuskarta ta fice, cikin nutsuwa take tafiya har taje tayima hajiya siyayya sannan ta dawo hanyar gda, a dai dai wani lungu da zai sadata da layin gdan su taji wani na saida ta, sai tayi kamar bata ji shi ba ta cigaba da tafiya, ganin ya cigaba da binta kuma gashi ta kusa karasawa gda yasa ta ja ta tsaya ta fara magana cikin muryarta mai dadin sauraro

"Malam ya akayi kake ta faman bina" murmushi yayi mata wanda ya karawa fuskarsa kyau,fararen hakoranshi suka baiyana "sunana al'amin sani ina aiki a asibitin Abdullahi wase hospital wato nasarawa, na zo gdan uncle dina ne anan baya shine na fito zaga unguwar ashe da rabon zamu hadu, wlh tin da na ganki naji kin kwanta min kuma da gaske aurenki zanyi ba da wasa ba" murmushi tayi "ngde sosai da nuna min so amma kayi hkri ni ba kowan kowa bace hasali ma aikatau nake yi a gdan can mai green din gate, ta fda tana nuna mashi gdan su" dariya yayi "ai so bbu ruwanshi da ko kai waye nidai fatana ki amince min" kayi hkri ta fda ta ficewa, duk yadda al'amin yaso siyam ta tsaya amma taki hasali ma shigewa cikin gda tayi, ganin bazai iya jure rashin ta ba yasa ya kwankwasa gdan Ado mai gadi ne ya leko ganin matashin saurayi kuma kyakyawa ga kudi da suka zauna mashi ya fara washe hakoransa, sannu baba suna na al'amin wata yarinya ce ta shigo yqnxu dan Allah kamin sallama da ita, "haba yaro kai kuwa me zakai da siyam duk matan duniyar nan, yarinya mai shegen *bakin jini* yar aiki ce fa a gdan, dariya al'amin kawai yayi "baba duk na sani plssss ka kira min ita" kaga yaro ni ina da abinyi wlh bazan kirata ba" duk yadda al'amin yaso ado mai gadi ya kira masa siyam amma yaki, dole ya hkra ya koma gda

Washe gari da sassafe al'amin ya fito da sauri sbda zai je asibiti, kqmar ance ya juya ya hango siyam rike da saddiq da sauri ya nufi inda suke, "amincin Allah ya tabbata a gareki ya ma'abociyar kyau da nutsuwa" ba tare da kalleshi ba tace "kai ma" sosai yaji dadin yadda ta mashi maganar ganin yadda al'amin ke mata naci yasa dole ta bashi numbern sa, ta tafi, duk yadda al'amin yaso ta hau mota ya sauketa taki, dole ya sarar musu adai daita sahu suka tafi

Tin daga ranar siyam da al'amin suka fara soyayya tin tana shasharewa al'amin har ta fara sakewa dashi, wulakanci sosai da habaici ado keyi musu, ga wulakancin hajiya sai tana zance zata kirata ta sata aiki kullum al'amin hkri yake bata

Kwanci tashi ba wuya wajen Allah, al'amin da siyam sunyi wata biyu suna soyayya, sai dai wani abu da ta kasa fahimta, shariyar da al'amin ke mata a yan kwanakin nan sai yay kwana uku bai kirata ba ,har sai ta kirashi yace mata yana aiki ne, zai kirata in ya kashe bazai kara kiranta ba

Kmar kullum tana zaune a daki tana tinanin me yasa al'amin y canja mata totally , tana cikin wannan tinanin ne message ya shigo wayarta ganin wanda ya turo mata sakon yasa tai saurin bude ganin abinda sakon ya kunsa yasa tai saurin mikewa cikin tashin hankali.........


Ku kasance damu danjin mai sakon ya kunsa me kuma yasata tashin hankali


Ayusha iliasu nd shamsiyya
[18/09, 11:32 a.m.] Shmsy Sls: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

_Wnnan feji sadaukarwa ne gareku _*UMMY AYSHA, LITTLE PRINCESS,ACTION LADY,ANEESA DIDI,REAL AFREEN*Allah y kara basira,yasa kufi hka,dftan anyi bikin sallah lfy,Allah y maimaita mna ,Amin y rabbi_


1⃣2⃣0⃣-1⃣2⃣5⃣


A wannan haline da rayuwa ta fara tsanani,yan kasuwa n kuka d halin rashin siyan kayayyaki kosun kasa kaya bbu mai zuwa y saya saboda hauhawar farashin dala,shiyasa koda asabe takai siyam gun aiki yusuf bai taba cigiyarta b ko nuna damuwa,in karshen wata yyi tanadan san mai wani abu cikin kudaden aikatau din siyam din.


Asabe gwammacewa tayi gwanda zamn gbn asabe da zamn gidan aiki a yanxu,da farko matar gidan ta dauketa tamkar yar data haifa,amma siyam bazata taba mntawa ba wata sallah asabe ta kawo mata ziyara gidan aikin nata,ganin da taiwa siyama yasa hankalinta matsanancin tashi,tayi kiba,ta kara ja tamkar diyar turawa,gaba daya siyama ta rikide ta zama yar gayu tamkar diyar wani hamshaki,duk inda hajiya zata tare suke tafe tana takewa hjyan baya,kowa yaga siyam sai ya yaba yace barakallah ahsanil kaliqin,babu yanda mahaifiyar hajiya batai da diyar tata uwar dakin siyam din ta bar mata ita amma kememe taki,alokacinne siyama m take sanar da asaben hajiya tace bana zasu je umara kuma d ita zaa tafi,dan ta rike wa hajiya karamin dan da take raino,cikin tashin hnkli asabe tayi musu sallama,da ranta d lfyrta zata bar siyama taketa hazoin hartana numfashi hkn bazai taba tabbata ba, hajya tayi mata kyaututtuka masu yawa da suka hada d kayan sawa dana abinci harda jimillar dubu goma,badan komai b sai dan kaunar da takewa siyam,siyamar ta rako asaben har bakin gate,tinda asabe ta dau hnyar gida take sakawa da warwara,meye mafita meya kamata tayi,wata zyciyar tace mata to kiyi dabara kicewa hajyr mahaifin yarinya yace ta dawo zaa maidata gun dangin mahaifiyarta in yaso sai ki nema mata wani gidan aikin.tayi matukar farinciki da wannan shawarar da ta yanke ,dan arayuwarta batason taga siyam n walwala da jin dadi balle kwanciyar hankali.da tayi tunani zuzzurfa sai kuma tace gaskiya babu batun nace zan canja mata gidan aiki dan kuwa ana dadewa kan asamu ,kuma yan alkhairan da hjyr takemin ba lallai agaba n masu mai kamanta min ba,dan masu hannu da shuninnan ba kowa keson taimakawa talaka b,wasu iyakacinki dasu kudin aikinki byn hka sisi basu baki,ta yanke shawarar komawa gun boka y saisaita mata alamura yanda take so,dan shi ke share mata hawaye,hknce kuwa t kasance yyi mata alkawarin cikin kwanki uku,hjyr zata dinga jin kyama tare da dinga yiwa siyam din tsangwama mafi kololuwar tsangwama,jaki sai y fita daraja a xuciyar hjyar,cikin farinciki sukai sallama t isa gida,Abangaren asabe duniya ta mata dadi,azuciyarta take cewa nagodewa boka,badan komai ba a rayuwata ban taba nemn wata bukata ta gagara samuwa ko cika cikin kankanin lokaci,Allah y jada ran bokayen duniya su dinga biya mana bukatu,wal iyaxubillah,mutane basa tsoron mutuwa d gamonsu d Allah.


Bayan kwana biyu da asaben ta kawo musu xiyara ,komai y fara dagulewa siyama,hajya ke nuna mata kyama muraran,tare da hantara ,har sauran kawayen hjy suka fara mmki,sai hjyar tace wannan d kuke gani munafukace kunsan komai aka hada da matsiyaci sai y nuna halin gado,wai yarinyar nan duk kaunar da nake mata ban isa tayi min aikace aikace ba sai idanni nace tayi wani lokacin ko na sata sai ta ga dama takeyi,kowa dai mmki canjawar d hajiyar ke cewa siyamar tayi mata,dan ko mopping tasata in tazo sai taga gun duk jurwaye bai mopu ba.in wanke wanke tasata baya futa haka shara d wankin bn daki,ba komai yasa hjyr ke ganin hka b sai sharrin boka,dan kuwa ya futan fes.Allah sarki siyama haka take zagewa tayi ta dirzar toilet ko tile dan de kar hjyr tace bai futa b,amma bbu canji,lokuta d yawa sai dai ta zauna tayi ta kuka karshe ta fauwalawa Allah,inda sabo ta saba.mkrntar boko d islamiyya ce dai baa hnata zuwa ba,kmr ynda muka sanar daku d farko a mkrntar ma bata da kawa ko aboki malaman ma sun tsaneta saboda kokarinta ,komai aka koya musu ta haddace.


Gwamma cewa tsyi gwanda zamn gbn asabe,Dik rashin imanin asabe,in dai siyam din ta gama yan aikace aikace dole t barta t huta wani lokacin har bccn rana take samu tayi gdn mahaifinta sabanin nan data kwanta matar gdn zatace tashi kije kiyi wankin kayan bby ,wanda ada batayi,kina zaton zan daukeki aiki in dinga biyanki dubu goma kici mai kyau kisha mai kyau a banxa dole n fanshe kudina,dan hka banaso n dinga ganinki a zaune dole ki kasance cikin aiki ko yaushe


A yanxu siyam ta saba da ukubar rayuwa,Ado mai gadi dama haushin siyamar yakeji,dan kuwa yar kanwarsa yaso a dauka aiki a madadin siyamar,amma hajya tace tafison siyam din ,dan haka y tsaneta y kumadau alwashin sai y shafa mata bakin fentin da duniya zatai Allah wadarai da ita,a yanzu farinciki yake badan komai b ya fahinci irin zamn da suke da hajiya dan haka cikin sauki hakan sa zai cimma ruwa.............

*Ayush iliasu n Shamsiyya salis*❣
[18/09, 11:32 a.m.] Shmsy Sls: [07/09, 4:55 p.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS*

1⃣3⃣1⃣-1⃣3⃣2⃣

_Wannan page sadaukarwane ga kafatanin mambobin group din Ayusha Iliasu novel group,Allah y bar xumunci y kara mna lfy da zama lfy,ina alfahari daku da zamntakewar da muke_

Tashin hnkali da baa sa mai suna y dira a xuciyar siyam,bbu abinda take ambato sai sunan Allah tamkar wadda aka baiwa umarnin mikewa aikuwa jiri ne ya fara daukanta,taimakon Allah yasa kan katifa t xube sai awannan lokacin hawaye zafafs suka fara kwaranyowa daga idanunta,tace na shiga uku kaddai zancen da jamaa suke fadi y tabbata akaina,Allah k kawomin sauki da rangwame,hka tayi kukanta ta share,siyam yarinya ce mai zuciya duk da ta taso a wulakantacciyar rayuwa bata yarda takai kanta inda zaa wulakantata ba,dan hka cikin bacin rai ta dauki wayarta,contact ta shiga tayi deleting numbr Al amin tare da deleting duka txt msgs da suka dinga yiwa juna yayin dasuke cikin shaukin so.


Sai awannan lokacin tadanji sanyi a ranta,sunayen Allah ta shiga ambata,ahankali sai taji duk damuwar ta fuce aranta,siyam ta rarrashe xuciyarta ta kuma alkawarta har abada ba ita ba sake kula wani saurayi balle asake breaking heart dinta,musammn in tazo bacci abun sabo ya ke koma mata,cox y mata sabon jin husky voice nashi,suna waya ahka bacci zai dauketa sannan yyi murmushi y kashe wayar.


*AFTER TWO MONTH*

Yau da dadi gobe babu ,siyam ce zaune adaki tana ninke kayanta data wanke,tajiyo muryar hajiya n kiranta,tsam ta mike dan amsa kiran hajiyar da rawar jiki ta karasa hade da durkusa,hajiya ta fara mgna kije ki hado kayanki kala biyar zaki je gidan kanwata ki zauna 2 weeks kafin a samo mata housemaid,ki tabbatar kin kular mata da gida yanda ya kamata karki sake ta kawomin kararki,cikin gyada kai tace insha Allah hajiya zanyi kamar yanda kikace.sai a lokacin siyam ta lura da wani matashi dake zaune a palon,tin shigowar siyam ya zuba mata idanu tamkar yaga sabon abu,cikin tsoro ta gaidashi ta mike dan hado kayannata kamar yanda hjya ta bukata,godiya ya shiga yiwa yayar matar tasa wato uwar dakin siyam.

Hijab dogo ta sanya harkasa,hannunta rike da ledar kayanta,ta karasa gaban hjya tace na shirya,ko kallonta hajiya batai ba tace Sudaiz zaku iya tafiya,gyaran murya yayi tare da sosa keya yace hajiya dama zaki bar mna ita inyaso in an samu wata sai ki rike,murmushi hajiya tace ai siyam da kake gani yar amana ce bazan iya rabuwa d itaba,sunyiwa hjya sallama suka futo harabar gidan,mmki ya cika mai gadi dan kuwa ya gama shirin sa tsaf na ketawa siyama rigar mutunci a wannan rana,abin takaici sai gashi y ga alamu bama a gidan zata kwana b balle hakkansa ya cimma ruwa

Kokarin shiga gidan baya takeyi yace ni driver dinki ne,sum sum s ta bude bangaren mai zaman bnza ta zauna,sanyin AC ne ya daketa ,ya fara sanyata jin zazzabi,sai awannan lokaci ya kara kai dubansa gareta azuciyarshi ya ambaci barakallah ahsanil khaliqin,cikin husky voice dinshi yace yadai ko sanyin ya miki yawa,idanu fiki fiki ta kalleshi tmkr kazar da kwai y fashewa tace A'a banajin dadine,ya ganota kawai sai y rage karfin AC din,A take awanman lokaci zuciyrshi ta fara saka mishi abubuwa game da siyam,duk lokacin da sukai ido hudu wasu sakonni yake ji suna isa ga xuciyanshi wanda ya kasa tantance me hakan yake nufi,sun isa mai gadi y bude musu gate hade da brka d zuwa,bynshi tabi har suka dangana da palon gidan,matashiya ce matar gidan wadda bazata wuce 22uears ba zaune a palo hannunta rike da jaririn da ko arbain basu karasaba,kasancewar sunsan juna d siyam,akasa ta zube tana gaidata ta amsa ba yabo ba fallasa ,ta nuna mata masaukinta da cewa gobe insha Allah zata fara gudanar d abunda y kawota,siyam taji dadin hka dan hka ta bi lafiyar katifa ta kwanta.

Tunda sudaiz y shiga daki bbu abunda idanunsa keyi masa sai gix n beauty face din siyam,daya rufe ido sauti sweet n charming voice dinta yakeji ,sunayen Allah y fara amnato,why why why oll dis,ya zuciyata zata kaini ga mtsala,matsala mana,dan kuwa in har da kara baici ace xucyata taimin hkaba,me wifey na zata daukeni,tindaga wannan rana y tsinci kansa cikin matsananciyar damuwa,kullum xuciyarshi ingizashi take ga kaunar siyam,yarinya ce mai tsafta,dan azuwanta kwanaki kalikan iskar gidan da annurinsa yafi baiyana
[07/09, 5:06 p.m.] Ayush Iliasu: A batun girki kuwa baa magana kyace food n nutrition ta karanta,cikin mako.guda siyam ta gama dasa kaunarta zazzafa a zuciyar sudaiz,Addua y shigayi in harda alkhairi tsakaninsu Allah y tabbatar ta kuma aminta dashi, in bbu Allah y yye mishi

Kullum abun xafafa yake azuciyarshi karshe ya ynke shawarar sanarda amininshi,atlast sunyi concluding tinda ba haramun bane yana iya nemn soyayyarta inta aminta ya aureta,yajidadin kwarin gwiwar da abokinshi y bashi,sadik ne ya kyalkyale da dariya,hba aboki kalleka duk ka rudu ka rikirkice akan yar aiki,ina batun son da kakewa samy dinka,hmmm bari friend ai wannan soyayyar ta dabance,ina tausayama yarinyar ya kmta ace itama tana gdn nata mijin tana aikin lada not aikatau,kafardarshi y dafa yace mutumina y kamata kada k bari samy ta sani sai komai y daidaita

Cikin farinciki y iso gida,tun a harabar gidan y fahinci samy batanan,da sallama y shiga y tadda siyam ta futo a guje dan xuwa kitchn kanta babu dankwali balle hijab din data saba kumshe jiki cikinsa ,bata lura d shigowar shi ba ta karasa kitchn,kuxo muga idanun sudaiz da yanda siyam ta tafi da hnklinshi more especially gashin kanta daya ganiya sha kitso,jikinta abun shaawa nan ta kara rikjta mai kwanya,jin shiru shiru bata futo daga kitchen dinba ya rufa mata baya azuwan ruwa ko drink zai dauka a kitchen din,motsin mutum taji a bynta bayan tasan ita kadaice a gidan tsakiyar kitchen din y karaso ya tadda ita ta hada gumi tana tuka tuhu,kyawunta y kara baiyana gareshi,karasowa yayi gbnta tare d cewa aminci y tabbata agareki my Queen,mganar tazo mata a bazata ,ta daga kai zata yi magana sukai ido biyu da samy dake tsaye a bayansa.



*Ayush iliasu n Shamsy salis❣*
[18/09, 11:32 a.m.] Shmsy Sls: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

1⃣3⃣3⃣-1⃣3⃣5⃣

_Wannan feji sadaukarwane gareku mambobin UNIQUE WRITERS ASSOCIATION ,Allah y dafa mana ya kara hadin kai yasa rubutun mu ya zamto hanyar samun lada da qaruwa ga Alummar annabi ,more especially RAHEENA MAHMODOU and LITTLE PRINCESS_


Gaban siyam ne ya shiga faduwa sai faman raba ido take tana jiran hukuncin da samy zata mata, shima sudaiz mutuwarzaune yayi yana jiran abinda samy zata ce,

"Habiby me kakeyi a kitchen?" Samy ta tambaya tana cire ear piece dn dake kunenta, ajiyar zuciya sukai a tare sbda fahimtar da sukai samy bata ji komai ba, murmushin karfin hali yayi tare da rungumota, "ruwa na shigo dauka kitchen coz naga na shigo ba kya nan" eh na dan leka makwabta ne, me kakeyi kusa da wannan kuma" ta fda tana maida dubanta ga siyam, bata ransa yayi "gwanda dakika tina min na shigo na ganta ba dankwali naje na mata gargadi ta daina zuwa mana kitchen ba dankwali kar gashi ya shigar mna abinci" toh in ka gama ina daki bari naje nai wanka dan a gajiye nake ta fda tana ficewa, ganin ya juyo zai mata mgana yasa tai saurin ficewa daga kitchen din, ganin ta fice ya sashi fita shima jiki a sanyaye,gdya ya shigayi na jindadin kwansa bai fashe ba.

Tana shiga dakinta ta turo kofar sannan ta zauna a bakin gado,dafe kanta tayi cikin matsanancin tashin hankali "me yake shirin faruwa dani, me yaya sudaiz yake nufi Allah yasa ba cewa zaiyi yana sona ba" haka dai tai ta sakawa da warwarewa, ganin hakan bashi ne mafita ba yasa ta fito waje dan karasa aikinta

Yau kwana uku da faruwar hakan tin daga lkcn siyam bata bari su hadu da sudaiz,wasan buya suka fara duk hanyar da zaibi su hadu ya rasa, suna zaune shi da samy a falo tace "honey kawo kudi na aika siyam kasuwa ta yo mana siyayya plssss" wani dadi ne ya kamashi jin ta fdi haka ko ba komai yau zai hadu da farin cikin sa, ki duba cikn inda nake ajiya ki dibi yadda zai isheki bari naje unguwa sai na dawo ya fda yana mikewa "a dawo lpya a taho min da ice- cream" to kawai yace mata ya fice, yana fita taje ta debo kudin taje ta bata bayan ta lissafa mata abinda zata siyo mata, ba tafi mintina gomaba ta shirya cikin wata doguwar riga ta atamfa, sosai dinki ya amshi jikin ta bakin mayafi dan karami tare da bakin takalmi ta saka sannan ta fice, sudaiz na fita ya tsaya nesa da layinsu yasan dole ta nan siyam zata wuce, tin daga nesa ya ganota ya fara washe hakoransa, tana karasowa yace "barka da fitowa gimbiyata" yauwa ta fda a takaice, ina so in bazaki damuba na kaiki inda zakije" a'a na gode aunty ce ta aikeni yanzu zan dawo" na sani ai dan Allah ki taimaka ki bari na kaiki, ganin yana bata mata lkci yasa ta yarda ya kaita da kansa ya bude mata kofar shima ya zagaya ya shiga sannan suka dau hanya

Siyam nasan zakiyi mamakin da yasa nake miki haka, wlh tin ranar da na daukoki nakejin sanki, kuma so ba na wasa ba, kullum da sanki nake kwana nake tashi, dan Allah karki ce ba kya sona ya fda kamar zaiyi kuka, "yaya kayi hkri amma wannan ai cin amana zanyi, ina aiki a gdan ta sannan kuma na aure mata miji, sannan kuma bayan wannan ka duba matsayinka da nawa kasan bamu dace ba kwata kwata, dan Allah kayi hkri ka cire zancen so tsakanin mu" haka sudaiz yay ta faman tsarata, yana nuna mata ai ba haramun bane abinda yake shirin yi, a haka har sai da yay nasarar samun numbernta da amincewarta a haka suka gama siyayyar sannan ya biya ya siya musu ice-cream din a hanya ya sauketa sannan ya wuce gda


Tin daga ranar siyam da sudaiz suke soyayya tin siyam na dari dari dashi har ta sake kullum suna cikin waya in samy ta fita ya tayata aiki suna shan soyayyarsu a haka har ta cike kwanakin da zatayi a gdan hajiya ta kawo musu wata yar aikin duk yadda sudaiz yaso a bar musu siyam hajiya taki dole ya hkra barin ta gdan yasa shi shiga damuwa dan ya saba sosai da girkinta, a haka suka cigaba da waya wataran in zata fita ta mashi waya sai su hadu

*bayan sati biyu*

Siyam an fara jarabarwar zangon karshe a ss2 wanda daga ita zasu shiga ss3 sosai take maida hankalinta ga karatunta kwata kwata bata wasa, cikin hukuncin Allah suka gama jarabawar cikin nasara, kwanan su uku da gamawa tanemi alfarmar zuwa garin su amma hajiya tq hanata dole ta hkra ba dan ranta ya so ba

Yau watan sudaiz da siyam uku da fara soyayya, tana zaune bayan ta gama aikinta wayarta tai kara ganin wanda ke kiranta yasata saurin dagawa "siyam ki sameni a bayan layinku ina jiranki" bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa, yanayin da taji muryarsa yasa gabanta ya shiga faduwa, kasancewar hajya bata nan yasa tasa hijab dinta har kasa da nikaf ta nufi waje


Ku kasance damu danjin mai sudaiz ya zo fda mata

*Ayusha iliasu nd shamsiyya salis*
[18/09, 11:33 a.m.] Shmsy Sls: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*


*AYUSHA ILIASU OF UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*



1⃣3⃣5⃣-1⃣3⃣6⃣

_Yan uwa musulmi mu dukufa wajen yiwa yan uwanmu na burma musulmai addua game da iftila i da Allah y saukar musu,,ta inda ake musu kisa na wulakanci,mu sanyasu a adduoinmu Allah y takaita hka,y kuma yi mna sakayya ,ya kara daukaka musulmai d musulunci hade da karesu adik inda sukeAmin_


Inda yayi mata bayani ta isata hngoshi zaune cikin mota,bude kofar tayi ta shiga ta tadda fuskar nan tashi bbu yabo bbu fallasa,ta gaidashi ,cikin bacin rai y fara mgna,siyam na kirakine dan nayi miki gargadi d jan kunne ki futa harkata daga yau bbu ni babu ke,ki cigba da zama matsayin yar aikin dana daukeki,kicire wannan mafarkin da kike ada na zamtowa matata,koda inada raayin sake aure ba irinki zan aura ba,ya mai daraja zan aura,a aljihu yasa hannu ya zaro kudi bandir ya mika mata yace ga wannan kyayi hidimar gbnki,fuskarta cike d kwalla,mgna ma ta kasa saboda takaicin mgngnun da ya gaggasa mata,motar ta bude batare da tayi mai sallama ba

Please Login or Register in order to submit comment