Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gda mahaifinta baya nan sai matan babanta, gaidasu kawai tayi ta shige dakinta, tin da ta shiga daki bata kara fitowa ba sai da taji sallamar abban su bayan anyi sallar laasar, har kasa ta tsuggunna ta gaidashi, fuskarsa ba yabo ba fallasa ya amsa mata "me kuma ya dawo dake gda, ko halin naki na rashin mutunci kika karayi masa" abba bbu abinda na mishi haka kawai yace naje gda sai ya nemeni" nan ya fara sirfa mata masifa matansa na zugashi sannan yace ta tashi ta bashi waje jiki a sanyaye ta mike tayi dakinta tana kuka

Murna wajen asabe ba'a cewa komai ganin yusuf ya kora khdja gda burinta kawai ya aikawa da khdja takaddar saki, sbda su sakata su wala ita da yayanta

Sosai asabe da yarta maryam suke shirin tarbar saurayin maryam kasancewar yayi mata waya yana kan hanya nan da jibi, asabe da kanta ta biyawa maryam kudi taje aka mata lalle da kuma gyaran kai, sosai maryam tayi kyau kamar ka saceta

Tin safe suke ta girke girke sbda yaune khalid zai zo, gyara gdan sukayi tsaf, aka saka turaren wuta kala kala, kamshi ne ke tashi ta ko ina, karfe hudu maryam tayi wanka sannan ta shafa mai, bayan ta shafa mai ne asabe ta bata turaren da boka ya bata, aiko ta shafashi lungu da sako na jikinta sannan ta bata lkci wajen gyara fuskarta sosai kwaliyyar ta zauna a fuskarta bayan ta gama kwaliyar ne ta shirya cikin wata dakakiyar doguwar riga wadda ta bayyana surar jikinta, sosai rigar ta zauna a jikinta, bakin asabe yaki rufuwa sai faman murna takeyi ganin yarda yarta ta hadu, wayar maryam ce tai kara, ganin wanda ya kirata ne yasa tai saurin dagawa, "ranki ya dade na iso kofar gdan naku" murmushi tayi "sannun ka da isowa bari na zo" hafsat ce ta mashi iso zuwa dakin dake zaure, sosai dakin ya sha gyara ga kuma kamshi dake tashi, bayan ya zauna ne hafsat tayi mashi sallama ta fita har taje kofa Khalid yay mgana "kanwarmu baki fdan sunanki ba" dariya tayi "sunana hafsat" zaro ido yayi amin afuwa ashe autar muce zo na baki sako" sanda ta iso ya bata kudi ganin ya miko mata tace bazata karba ba, sai da yayi mata da gaske sannan ta karba,

A hankali ta daga labulan dakin tare da yin sallama, kamshin turaren ta da ya shaka ya sashi lumshe idonsa, a hankali ya bude idonsa tare da sauke su akanta, wani sabon sonta ya karaji yana shigarsa "barka da fitowa gimbiyata" yauwa barkanka da hutawa, amin afuwafa bnsamu na fito da wuri ba" ta fda tanayin fari da ido, bbu komai gimbiyata nan suka fara hira hafsat ce ta kawo mashi abubuwan da aka mashi nan yay mata godia, sosai ya zage yaci abincinsa, sanda zai tafi ya bata kudi mai yawa aiko asabe sai murna take yarta tayi sa'ar miji, tinda khalid ya koma gda ya takurawa iyayensa aje a nemo mashi auren maryam, ba musu suka amince akan karshen watan nan zasuje, sanda ya shaidawa maryam murna tayi sosai, lkcn da ta shaidawa ummanta ihu suka dingayi dan murna

Tinda khadija ta koma gdansu take shan sangwama wajen matan babanta, harma da mahaifinta, duk wani aikin gdan itace ke yinsa basayin komai, ganin duk azabar da suke mata bata damuwa yasa suka yanke shawar shaidawa babanta akan ya koreta ta koma gdan mijinta, haka kwa akayi yana dawowa suka fara zugashi, nan da nan yadau zugarta su ya fara kwalla mata kira, a kasa ta tsugunna kanta a kasa, "ki shirya kayanki ki tafi gdan mijinki yanxun nan nagaji da ganinki a gdana" sosai khdja ta razana da furucin mahaifinta "abba fa haka yace sai ya nemeni, kuma ni ko ya zo, ni bnzan komaba kace ya sakeni" aiko nan ya fara masifa yana zaginta "toh ba a gdan nan ba, ki tattara kayanki inma duniya zaki shiga ki shiga ni na sallamaki, karki kuskura ki kirani a matsayin uba tashi kije ki kwashe kayanki, jiki a sanyaye ta nufi dakinta, kuka sosai khadja takeyi har ta gama hada kayanta ta fice daga gdan,tafe take da kunshin ledar kayanta guda uku,duniya tayi mata zafi tama rasa mafita,gashi ko sisi bata magani,dangin mahaifiyarta baa kusa suke ba balle ta tafi garesu,hwaye ta shiga xubarwa n kuncin rayuwa,wayyo na shiga uku ,kowa guduna yake,mijina y gujeni,bbana ya gujini,matan babana sun tsangwameni suna kullan zagon kasa,makota da abokan arxiki duk sun tsaneni ,sai kace *MAI BAKIN JINI*ya Allah ka yaye min wannan balai,kanta y kulle ta rasa mafita,ko bara zatayi danta samu kudin d zai danganata d dangin mahaifiyarta,danfarerean shagon dake gabanta ta kalla,ta hngo wata luntsumemiyar mota ta faka a gbn supermarket din,da rawar jini ta nufi matar da ta futo daga gidan bya ta zube akasa tace ranki ya dade kitaimaka min da koda dubu dayace zanyi kudinmotar zuwa gida,wani takaicine y kulle hajiya,lallai matar nan ta rainan hnkli danta ganni cikin mota zata wani xo ta xuben agba wai na taimaka mata,cikin fushi hajiya tace keee malama fice min daga gba,ance miki kudin a kasa ake kwasarsu ko kuwa basu da wuyar samu da zaki kayyademin abun da zan baki,to wallhi sisi bazan baki ba,tsaki hajiya tayi ta kara gba,tabar khdj zube akasa cikin takaici ga ciki jikinta ,koba komai ai ta tausayawa cikin dake jikinta,hka khdj ta yini bara da kyar tasamu dari uku,ganin yanma tayi ta yanke shawarar ta nemi taimakon masu mota ko zasu tausaya mata su raga mata.mai adaidaita ta tsayar da kyar ta iya karasawa kusa d inda yayi packing tace ...................


*ku kasance da mu danjin inda khdja zata dosa gdan mijinta ko kuma duniyar zata shiga, amsar ta na cikin shafin gaba*
[26/08, 8:07 p.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

👽
👽👽
👽👽👽
👽👽👽👽
👽👽👽
👽👽
👽

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS*

8⃣1⃣-8⃣5⃣

```Wannan fejin sadaukarwa ne gareki Deejah small of herwwerh jidderh novel group,Allah y bar zumunci ```



Da kyar ta karasa gun mai adaidaitar tace yaro dan Allah ka kaini tasha ,yace to hjya nawa zaki bani tace naira ashirin gareni dariyama abun y bashi,yace hba hjya ku dinga tausaya mna bafa kyauta ake bmu hayar adaidaitar ba muma balance muke kaiwa kuma bada ruwa yake aiki ba,khdj ce tace yaro ka duba girmn Allah ka taimaka min ,gsky hjiya ni bazan iya ba saboda tafiyar naira dari bazan iya karbar ashirin ba,kwalla ce ta fara zuba daga idanunta,tace yaro ka tausaya min ,hade da kwalla idanunta,ganin babba na nemn kuka yasa ya amince,badan ranshi naso ba.


Adaidai kofar tasha y sauketa tana t mushi gdya ,bbu abinda take ambato sai sunan ubngji ta shiga cikin tashar,a ka ida dari uku ne kudin motar ,kuma iyakar kudin hannuta kenan ,d sannu sannu ta isa inda mota ke lodi ta shiga gidan bya ta zauna,tanata addua ,har mota ta cika akadau hnya,kwandasta y fara karbar kudin mota ,jikinta har rawa yake ta mika mai 250,yace hjya sauranki naira hmdin,tacevdan Allah yaro kayi hkuri iyakar kudin kenan,kwandasta yace kutumelesi tare da buga kofar mota ,yace direba faka a gefe mu sauke wannan yar rainin hnklin ko ance mata kyauta ake bmu man a filling station kokuwa anayi mna alfarma,gurgurgur direba y sauka daga kan kwalta ya faka a gefe,da hnzari kwandasta y wangale mota yace hajiya bisimillh sakko ga canjinki N200 dankin ci N50,khdj tace dan Allah direba kuyi hkuri walhi da inada shi dana baku,ganin batada alamar sauka yan mota suka fara mita,mu walhi gsky kar abata mna lokaci sauri muke,hka kawai akan hamsin zaa tsaya kace nace ,wanine yace ke hjya kinsan bki da cikakken kudi dan meyasa zaki shigo musu mota ,juyawa tayi dan yiwa mutumin byni,wata matashiyr budurwa take sanye da earpiece a kunne tana sauraran karatun kur ani tsyi saurin zareshi,tace malam me muke jirane ko motar takuce ta lanjare,byni aka shiga gya mata abinda ke wakana,hannu tasa cikin jaka ta zaro naira dari tace adau hmsin din abawa khdj canjin,budar bakin kwandasta kenan sai cewa yayi Allah y taimakeki walhi d sai kin sauka inkikaki n antayoki kasa,itadai khdj tayi shiru sbda hlin da take ciki shine a gbnta,tunanin irin tarbar da dangin mahaifiyarta zasuyi mata,sbda rabanta dasu tin bikinta,bata taba kawo musu xiyara ba,sai ynxu jikinta yayi sanyi ,lallai bata kyauta ba,Allah y gani bbu yanda batai y kawota b kullum sai yace ta bari so yake y samu lkci suxo tare,har takaiga kome y rincabe mata


Sun isa tasha,kowa y sauka,dan daidata khdj ta tsayar tasanar dashi y kaita unguwar gidan sarki ,ta tnbyeshi nawa kudinsa yace hamsinne,ta shiga suka dau hnya,tana xuwa unguwar sai kunya ta lullubeta dadi bai kawota garesu ba sai wuya ,gefen wani gida ta tsaya tanata saka d warwara ,ganin yamma ta yi tasa yanke shawarar shiga gidan.shigarta keda wuya tayi sallama autar su mmnta dake zamn gida ce tace me zan gani,hade d rike baki,badai deeje mama ta kano bace,jiki sanyaye tace nice maryama,lallai yau munada mnyan baki a gidannan,murmushin yake khdj tayi tace e walhi,tabarma tayi hnxarin dauko mata daga dakin gwaggo ta shinfida mata a tsakar gida,maryama tace ya kika bar mai gidannaki a waje ai da kinshigo dashi,bari naje nayo mishi iso,sai kace wani bako ai ya zama dan uwa,hnyar waje ta nufa,cikin karfin hali khdj tace ai da yake ni kadai ce,lokacin mryama harta kai bakin kofa sai dawowa tayi cikin mmki tace ai nai zaton tare kuke,gefe ta nema ta zauna suka kara gaisawa tare d tnbyr byan saduwa ta kawo mata ruwa,khdj ce ta tnbya goggon bata nan ne? Maryam ta amsa da eh walhi taje kasuwa amma nasan tana hnyar dawowa,suna cikin hira sukaji sallamar goggo a zaure,goggo macece dattijuwa ,kaka ce ga khdj,tana shigowa tsyi tozali da bkuwar abinka d mnya wasa ta shigayi mata irinna jika d kaka ,khdj yake kawai takeyi,wato saboda amarci ya kare shine zai kawomin ke yanxu? Daya bari kin haihu in yaso sai akawo min kishiya ko mai gida ,itadai khdj ta rasa bkin mgna,bayan mryama ta bar dakin ne,khdj ta fashewa goggo da kuka ,hnklin goggo ba karamin tashi yyi ba jin jikallenta n xub ta hawaye,dakatar da cin abincin da takeyi tayi ta matso kusa da ita,haba deeje me yayi zafi hka ? Kasa mgna tayi tabar goggo cikin daurewarkai n mmkin abinda zai sanya deeje a wannan hali baya ga babban rashi na uwa da tai,cikin daure kai tace isuhunne ba lfy kokuwa mutuwa yyi,duk bbu amsa,ko kuwa bbn nakine b lfy kikazo sanar damu sai a wannan lkcn tace a'a,cikin wata irin murya rarrauna tace goggo ni walhi bazan koma gdn yusuf ba,dana koma gwanda n kashe kaina,innalillahi wa inna ilaihi rajiun goggo ke ambata, ba shiri ta dau buta ta nufi bndaki cikinta y burga sai zawo take,Sai yanxu khdj ta fara danasanin xuwa ta tada wa yar tsohuwa hankli,kukanta ta shigayi a hka kannan mmnta suka iso gdn,turus sukai ganin ta tana kuka wiwi,nan aka shiga maida mgna,khdj ta kwashe komai kaf ta gaya musu tundaga irin azabar d yusuf ke mata da halin ko in kula d mahaifinta yake msta har xuwa irin hukuncin da ya ynke yanxu akanta.



Khdj ce ta cigba d cewa bani da sauran gata sai ku,ku taimakeni ku fiddani daga wannan bala'in in kuka takuramin na koma zan iya shiga duniya,wayyoni derjeh n shiga uku,a dakin bbu wanda bai zub da hawayen tausayi ba,mama safiya ce yayar mahaifiyarta tace tinda rashin mutuncin mahaifinnki d kiyayyar da yake miki ta kai haka to mu ya bar mna ke,tinda yace in baki koma ba bake ba shi mun amince kicigaba da zama damu ,zamu kuma tsaya tsayin daka dan karba miki takardarki daga gareshi dan baa aure dole,jin aika aikar da safiyar ke shirin yi goggo tace keee safiya ki futa a idona akul na k'ara jin wannan furuci daga bakinki keda zaki rarrasheta tayiwa mahaifinta biyayya amma ke zaki kangarata kar na sake jin kince uffan anan,abinda nakeso daku ke safiya tashi kije ki nemomin sallau,sallau din shine babban dan goggo,gwanda yazo ya tasata gaba ya mai da ita dakinta ,ya bawa isuhun da mahaifinnata hakuri,tinda duk wannan badakalar da kucincina maganar da ake batace yace ya saketa ba,kuma ba'a shedar dan yau watakila tayi musu wani laifine yasa suke mata haka,khdj ce ta mike ta dora hannu biyu aka wayyo na shiga uku,mutuwa kina ina kixo ki daukeni ki kaini gurin mamana




*Daga Alkalamin Ayusha iliasu da shamsiyya salis*✍
[26/08, 8:07 p.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

👽
👽👽
👽👽👽
👽👽👽👽
👽👽👽
👽👽
👽

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

8⃣6⃣-9⃣0⃣

```Sadaukarwa ne gareki Zaynab marubuciyar Qaraurawar soyayya,Allah y bar zumunci y kara miki basira,Ameen```

Maryam ce ta mike tare da rikota, "gaskiya gwagwo baza ta koma ba, kamar wata wadda bata da yan uwa ko muke nemn kai da ita, kawai sai a maidata su bata wuya, yar uwar mu bazata taba yafe mna ba muddun muka bar tilon yarta a cikin wannan halin na toxarci, alhalin kuma muna da ikon taimaka mata" ta karasa maganar cikin kuka, jikin gwagwo ne yay sanyi, tabbas yarinyar na shan wuya amma gdan mijinta shine mutuncinta, ta barta ta huta inyaso a mai da ta daga baya, sai su tayata da addu'a dan itace gijiyar da zasu bita da ita,dan kuwa uwa da uba da dangi basa sa d'a ajin dadi face ubangiji,cikin sanyin murya gwagwo ta fara mgana "ya isa haka ki daina kukan ku tashi ku shiga ciki" farin ciki sosai khdja tayi maryam ta ja hannunta suka shiga daki, sanda kawu sallau yazo gwagwo ta bashi lbrn komi, sosai ransa ya bacci, ganin yadda yafi su saratu daukar maganar da zafi ya sata kin gaya mashi a maida khdja, duk ta bari sai sun huce tukunnah, yinin ranar khdja taga gata sai faman nan nan suke da ita kamar su mai da ta ciki ,abinci ma zabinta ake dafawa,cikin yini daya khadji ta yi kiba ta kara yin bulbul.

*Bayan wata biyu*

Shirin bikin maryam sosai yusuf da asabe suke dan har an sa ranar auren su nan da wata daya mai zuwa, sosai asabe ke shirya yarta, ango kuwa kullum jin san maryam yake kamar me, khdja kan na samun kulawa sosai wajen yan uwan mamanta, duk wani problem nata ta mnta shi,kwata kwata basa so su ganta cikin damuwa, kwata kwata basa so su ganta cikin damuwa, kullum burin su bai wuce su samarwa yar tasu gata ba, gwagwo sosai .A yau ne goggo tayi ma sallau bayani tare da tausar zuciyarsa hade da nasiha,yayi hkri amaida khdj dakinta,da kyar ya aminta kasancewar shi mutum mai zafi,in tashine baiki yaje y karbo mata takardarta ba,yayiwa goggo alkawarin zuwa katsina akan yaji abinda ke faruwa daga bangaran yusuf a k'arshen satin nan, ganin cikin kydj ya tasa ya fito ya cika,tayi cika orin ta masu ciki, watan cikin biyar yasa duk su safiyya suka sakko, kullum suna yima maryam nasiha akan tayi hkri ta koma gdan mijinta, sosai jikinta yayi sanyi,ala dole ta hkra badan tasoba sai dan gudun karsuma su ce sun zare hannunsu kanta.

Yau ta kama asabar ,yau ne kuma kawu sallau zaije katsina wajen yusuf, sanda yaje wajen mahaifin ta,ya nuna shi ba ruwansa da khdja tinda taki bin maganr sa, sosai ran sallau ya baci da yadda mahaifin khdja yayi mashi, kasan cewar yasan wajen aikin yusuf direct shan ya wuce, yusuf ya tarbeshi cikin girmamawa , sbda ya shaidashi nan kawu sallau ya tambayi yusuf dalilin da yasa yake ma khdja haka, ganin yusuf bashi da abinda zai fda ya dinga bashi hkr akan insha Allahu zai gyara kuma zai zo nan da sati guda, ya k'ara bawa gwagwo hkri, sosai kawu yaji dadin yadda yusuf ya karbeshi, sannan yayi mashi sallama ya tafi, sanda ya koma gda ya shaida musu yadda sukayi ,sunji dadi sosai .

Kamar yadda yusuf ya fda haka ta kasance satin kawu daya da zuwa shima ya iso, sosai kawu da gwago sukayi mashi nasiha, sannan suka ce za'a rakota nan da sati guda, bai musu musu ba ya yayarda, sannan suka fice suka turo mashi khdja, tin da yaji muryarta sanda ta shigo, yaji shi cikin nishadi, tabbas yasan duk sanda ya ke tare da khdja yana jin wani yanayi wanda baya iya fassara shi, amma kuma ya rasa dalilin da yake jin tsanarta haka kawai, gaida shi din da tayi ne ya sashi ya dawo daga tinanin da ya tafi, sosai yay mamakin ganin cikin khdja ya girma, nan dai suka taba hira sama sama, har ya shaida mata bikin maryam nan da sati biyu masu zuwa, adduar fatan alkairi tayi musu sannan yay mata sallama ya tafi bacin ya ajiye mata kudade yace sayi kudin mota.

Mama saratu da aunty maryam ne suka raka khdja gdanta sanda suka rakota asabe bata gdan sun tafi kano karasa yin siyayyar kayan kitchen n diyarta maryam, sai ta kwana biyu zata dawo, ita da maryam suka tafi, baba karami kawai suka tadda a gda ya dawo ya gama makaranta, nan ya gaidasu cikin girmamawa kafin ya fice shima, basu wani bata lkci sosai ba suka kammala gyara dakin nata, suna gamawa yusuf ya shigo da kayan abinci yaje ya gaidasu, sannan suka dora girki, washe gari tin safe mama Saratu da aunty maryam suka tafi, bayan yusuf ya hada musu goma ta arziki, ranar khdja taga kulawa wajen yusuf ba laifi,tamkar daren farkonsu ,sun ba juna kulawa mai wuyar mntawa.

Lkcn da asabe ta dawo taga khdja tai mamakin ganin nataa amma bata nuna mata ba, Allah bai sa asabe ta lura da cikin da ke jikin khdja ba, nan suka cigaba da shaglin biki, ganin asabe bata sata a lissafi hakan yasa bata shishige mata gudun wulakanci da tozarci


Sosai gdan ya hargitse da mutane, asabe ana ta fama da jamaa kasan cewar yau aka fara biki, karfe hudu aka kama amarya sosai tayi kyau hakama asabe ansha kyau, baiwar Allah khdja kan a gda aka bartq jiran gda kasan cewar ba a gda zaa yi kamu ba, washe gari akayi dinner inda ango ya halatta, tsayawa fadar yadda amarya da ango sukai kyau bata lkci ne ba laifi an kashe kudi anci ansha kamar me, uwar amarya bakinta yaki rufuwa ganin yadda kowa ke yaba bikin nasu, nera ta koka,duk inda ka shiga lungu da sako labarin bikin maryam diyar yusuf da asabe ake,washe gari aka daura auren maryam da khalid akan sadaki dubu dari, wayyo zanso kuga yadda bakin asabe ya gagara rufuwa sbda tsabagen farin ciki, ba laifi khdja ta dan fito cikin hijab dinta, ko da hindatu da Aisha sukazo basu kulata ba, haka aka gama yinin bikin cikin farin ciki, washe gari aka kai amarya kowa ya watse.


Mijin mrym shahararren mai kudi ne,gidanda aka kaita ma abin ksllo ne,komai yaji,amarya da ango an gwangwaji amarci tamkar akansu aka fara aure,wata irin zafaffiyar soyayyar angon nata ke mata,kudi kawai yake an taya mata,alkawarin da tai wa boka in har auren ya tabbata zata bashi zunzurutun kudi dubu dari,cikin sati sun tatsi. Dubu dari biyu agun angon maryam,dan hka asabe ta tsara yusuf kan cewa zataje yiwa yan uwanta bangajiya,nan kuwa cika slkawarin boka zataje tare da muguwar aniyarta ,wannan karon ta dau alwashin ko boka ysyi mata aikin da khdj zata mutu ko ta haukace ko kuma asaukar mata da larurar da bata da magani,sun yi sallama da yusuf da sauran yaranta kan cewa ta tafi gida ,straight gidan currency ta zarce



*Daga alkalamin yan mutan dabo Ayusha nd shamsiyyah*
[8/30, 10:13 AM] A AYSHA: [27/08, 11:11 a.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

👽
👽👽
👽👽👽
👽👽👽👽
👽👽👽
👽👽
👽

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU OF BAIWA WRITERS ASSOCIATION*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSCTN*


9⃣0⃣-9⃣5⃣


~Wannan fejin sadaukarwa ne gareki mum sumy n aneesa of firstclass group n Ayusha iliasu novel grp,muna yinki,kina rainmu,Allah y raya iyali yyi musu albrka,Amin ILYSM~


Isarta ke da wuya basu tsaya bata lkci ba kasancewar aranar asabe tayima yusuf alkawarin dawowa shiyasa ma ta buga sammako,suka nufi tasha ,lodin farko suka samu sai da mota ta lula tsakiyar dawa inda bbu gida gaba bbu gida bya sannan currency taceda kwandasta akwai masu sauka ,cikin mmki jama'ar cikin motar suka bisu da kallo,mamaki fal zuciyarsu da tsoro,mezaisa wadannan matan sauka a wannan kungurmin dajin ,ai ko nmjine yayi hka ayi mmki balle mata harda mai goyo a bynta,ko tsoron mugun dawa da barayi basayi,kowa abinda yake sakawa aransa kenan,direba cikin tsoro ya faka mota ya saukesu,to namiji ma kenan balle mata,lallai xuciyar ta tsike babu burbushin imani

Wata siririyar hnya suka bi wadda zata sadasu da gidan boka,suna tafe suna hirararrakinsu har suka isa,sun tadda gidan jinkim da mata,kasancewar wasu tun kan sallqr asuba suke baro gidajensu dan asallamesu da wuri,sun tadda fin mutum talatin,nan currency ta fara mita ,walhi asabe duk ke kika jawo mana,sai dana ce kixo gidana ki kwana tin kan asuba mu taho amma shegen taurin kanki ya hana gashi zaki batan lokaci byn Alhajina yau zai kawo min xiyara mu shana,ni tsiyata dake duk abinda aka tsara dake saikin batawa mutane tsari,tsaki currency ta karayi,ganin zasu raba gari yasa asabe tace haba amini kiyi hkuri mna nasan duk laifina ne,bazan kuma ba,sannan currency ta jawo wayarta cikin jaka dan sanar da Alhajin sai dare zasu hadu ,bbu netwrk bbu alamunsa,tsaki ta karayi,tace in baki wasa ba zan tafi n barki kuwa, dan ba zaki sani loosing dubannin kudade ba,da kyar asabe ta shawo kanta ta amince zata jirata,badan ranta yaso ba.

Akan idansu anata sallamar jama'a har akazo kansu,sun shiga suka xube gaban boka,siffarshi kadai abar tsoro ce,gurgune mai ido daya da hannu daya,kansuyi mgna yayi wata irin kara mai tsoratarwar hade d miko hannunsa bani alkawarin da mukai,jiki n rawa ta sanya hnnu cikin aljihu ta zaro su kulle a leda,ta mikamai,wata irin girgiza ya shigayi yanaiwa kansa kirari tare da futo da harshe kyace lashesu zaiyi,sai daya nutsu yace cikin bukatun da kika xo dasu kowacce kika zaba zata biya,amma za'a samu jinkiri zuwa har lokacin da zata haihu sannan komai ma zai tabbata,yar cikinta alkawarin Allah ce sai tazo duniya,inmuka tsananta zaki. Iya rasa ranki amma inkika hakura da sannu bukatarki zata biya,badan taso ba tace Allah y kaimu,babban burina akashe ta ko tayi mutuwar wulknci a titi ko ta haukace ta shiga duniya ko a saukar

Please Login or Register in order to submit comment