Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata da larurar da zaa rasa gane kanta,wata tsawa boka yayi musu yace ni zaki rainawa hnkli yanxunnan sainasa aljanu su kakkaryamin ku,dan raini har zabi zaki bani,cikin tsoron da batasan tayi mgna ba tace A haukata min ita,dariyar mugunta boka yayi yace bukata ta gama biya hahahahahahahahaha,sai awannan lokacin taga shirmen da tai ,ya ma zatace a haukatata ai tabar doran duniya baki daya kawai,cikin rawar baki tace boka nafi san a kasheta,kanta rufe baki wata guguwa ta taso tayi sama da ita,ta dinga tamole da ita karshe ta yasar da ita a gbn currency ,tsoro ya cika currency har futssri ta saki na tsorata,idanunta sun furfuto waje,bata taba zaton hatsabibancin boka ya kai hka ba,cikin karaji yayi mgna yace ba'a canja mna mgna,ku tashi ku fuce min dagani bukata zata biya,in ta biya ki dawo ku biyani dubu hamsin ladan aiki,inkuwa kukaki to da sannu zan waiwayeku n dau fansa, currency cikin rawar baki tace Ala gafarta boka aini rakiya nayo,dariya ya saki yace yanda kika rakota nabiya mata bukata haka zaki rakota gaba ta kawomin hakkina,in ba hka ba ku ji tsoron gamonku dani,jikin asabe yyi mata tsami da kyar ta mike sannu a hnkli suka bar gun,ranta yayi masifar baci yanxu daya karyata da me zataje gida tace lallai wannan boka bashi da imani,currency rike da ita suka iso har cikin gari ,gidan currency suka isa tayi wanka ta canja kaya ,taci abinci ,ai kuwa ta sha alwashin tunda boka yyi mata haka ko bukata ta biya bazata koma biyansa kudin aikin sa ba tsinanne,azzalumi ,mara imani


*Daga taskar Ayusha da shamsiyya salis*
[29/08, 5:25 p.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU OF BAIWA WRITERS ASSOCIATION*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


~This page goes to u our yar uwa ,co writer ,Allah y bar zumunci,ya kara bsra,hazaka da kaifin tunani,RAHEENAT MAMOUDU marubuciyar MENENE HUJJARKI,kina wuta muna binki da Diesel~

9⃣6⃣-1⃣0⃣0⃣

Kwanci tashi ba wuya wajen Allah cikin khadja ya shiga watan haihuwa ko yau ko gobe, tinda cikinta ya shiga wata tara kullum take cikin damuwa ta rasa dalili, haka kawai take jin wani irin yanayi a jikin ta, bbu laifi ta dan samu saukin masifa wajen yusuf bbu wata rigima da take hada su, girki ne kawai bai dauke mata ba amma wanke wanke da shara kullum autar asabe ce keyi da safe da yamma kasancewar suna hutun makaranta, tin asabe na mita har ta hakura da ta tina alkawarin da boka yayi mata, khdja na haihuwa zata hauka ce, sosai baba karami ke kula da khadja yay ta faman nan nan da ita, sosai asabe ke jin haushin yadda baba karami ke yi ma khdja, ta rasa dalinlin da yasa yaran nan ke ta faman shishigewa Khadja musamman baba karami da Aliyu

Khdja ce kwance a tsakar gda, sai Aliyu da ke gefen ta suna hira kasan cewar la'asar ce, "aunty Allah yasa ki haifar mana baby gurl mai kama dake, sbda ba karamin kyau zata yi ba" dariya kawai khdja tayi ba tare da tace komai ba, "aunty magana fa nake kikai shiru ko kin fisan namiji" toh haidar me zan ce maka kasan bnda masaniya kuma bnda zabin abinda zan haifa, duk wanda Allah ya bani ina sanshi" kuma fa haka ne aunty Allah ya raba lpya" amin haidar yanzu kayi magana" ganin yadda khdja ke mgana da kyar yasa Aliyu kallnta "aunty ko dai baki da lpya ne" lpya ta kalau bbu komai " sallamar yusuf ce ta katse masu hirar, suka amsa mashi tare da yi mashi sannu da zuwa, ba tare da ya kallesu ba ya amsa ya wuce dakin asabe,


Washe gari khdja ta tashi da matsanancin ciwon mara wanda ta kwana yana danyi mata ciwo, juyi take ita kadai a tsakar daki, yusuf da asabe na zaune suna karyawa, kamar wanda aka mintsila ta mike zunbur, cikin mamaki asabe tace "lpya mai gda me ya faru" ko kallonta baiyi ba ya nufi dakin khdja, cike da tashin hankali ya isa inda take kwance tmkar ruwa, "khdja lpya me ya sameki" ya fda yana dagota, ita dai bbu abinda takeyi sai juyi da matagugu ta rike baya da ciki, cikin hanzari ya fito, dai dai lkcn da baba karami ke shigowa, yauwa je ka fitar da mota bari na dauko khdja mu kaita asibit..... Bai jira ya karasa ba yay waje da gudu dan fitar da motar ganin yadda yusuf ke rawar kafa dan duk wainar da ake asabe na kallonsu yasa ranta ya kara bacci, tabbas sai tayi da gaske dan taga asirin da tayima yusuf kamar ya fara barinsa, dole ta canza boka, daman akwai wani boka da kawarta jummala, ta kwatanta mata a grn katsina, cikin mintuna ashirin suka isa asibitin, kasan cewar asibitin na kudi ne ba a wani bata lkci ba aka wuce da ita dakin haihuwa, yusuf da baba karami kuma na ta faman zirga zirga a cikin asibitin, abu kamar wasa sai da khdja ta kwashe awa hudu bbu lbrin haihuwa, ganin yanayin da ta shiga yasa likitoci yanke hukuncin yi mata aiki, cikin minti goma aka gama cike komai, har za'a jata zuwa dakin aikin wata nurse taga alamun kai ya fara fitowa, aiko cikin gagawa ta shaida musu, nan da nan suka maida hankalinsu kanta, wani kwakkwaran nishi tayi wanda yasa yarinyar fadowa, lkci guda kuma khdja ta sume, nan da nan suka fara bata taimakon gagagwa, inda daya daga cikin nurse din ta bukaci yusuf ya kawo kaya za a gyara jaririyar, sai a lkcn ya tuna bai bata komai na haihuwa ba, nan yusuf ya shiga wani karamin shago na saida kyn bbies wato bby dream,yayo musu siyayya, sannan ya kawo, sanda aka shirya yar aka kawo wa yusuf, wani irin so da kaunar yar ne ya shiga zuciyar sa, yarinyar kyakyawa sak mahaifiyarta,nan baba karami ya karbi baby,sai faman washe baki yake yana yaba kyawunta

Sai da khdja tayi awa biyu sannan ta farka lkcn da ta farka likitocin suka miko mata yarinyar nan ta fara juya yarinyar, kamar ance ta kalli hannu yar taga wani tabo irin nata sak, sosai tayi mamaki nan ta shayar da yar tana kare mata kallo tana ji a jikin ta kamar bazata rayu da yar ba, kuka ne ya kufce mata, dai dai lkcn da yusuf da baba karami ke shigo wa nan suka shiga rarashinta amma kamar tiri, nan ta kalli baba karami, "ga amanar yata ka kular min da ita bisa amana ka dauketa tamkar marainiyar wadda bata da kowa sai Allah, gaba daya jikin su yayi sanyi yusuf ya bude baki zaiyi mgana sai yaji ta wani saka ihu tana kokarin sakin yarinyar yusuf yay saurin rukota, nan ta fara fizge fizge da sauri yusuf ya fita ya kira likita ,aguje likitan ya iso dakin ya taddata sai kokarin nemn hnyar futa takeyi,da taimkon likita da nurses aka daddanne ta,aka xurkuda mata allurar bacci



*daga alkalamin Ayusha iliasu nd shamsiyya salis*
[29/08, 6:32 p.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


1⃣0⃣5⃣-1⃣1⃣0⃣

~This page goes to u Hafsat kabeer,Its Raheenert,Aysha Aminu Giwa,thank for your love,Hakika kuna cikin MSoyan wannan novel,Allah y kara zumunci ya biya muku bukatunku sis~


```Words are not enough to show ma happines to u ma co writers FATY AFREEN ,Allah y kara basira yasa kifi haka,Hakika Novel dinki yazo da salo n daban ``` *RIKICIN BABBAN GIDA* ```ina kira ga wanda bai fara karantawa ba yyi kokarin nema ,Daya ne tamkar da dubu ,cox akwai fadakarwa da ilmintarwa cikinsa,karku bari abaku labari da abaku gwara ku bayar```

Likitane ya bada umarnin kada ayi hayaniyar da zata sanyata farkawa,abarta har sai lokacin d zata farka dan kanta,yusuf ne zaune tare da ita yayi jugum abubuwa da yawa suka dunga gilmawa a zuciyanshi na halin ko inkula da yake nuna mata,a yanxu da batada lfy hanklinsa yayi dubu ya tashi,amma me yasa daya ganta zaiji tsanarta a zuciyarshi karara ,Addua ya shigayi Allah ya yafe mai zunuban da ya dauka,waya ya zaro ya danna lanbar mahaifinta,sun gaisa cikin girmamawa,nan ya sanar dasu hsihuwar khdj,mhfnta yaji dadi matuka tare da adduar Allah y raya ,suna nan tafe zuwa yanma insha Allah.atake ya sanar da iyalansa su shirya d yamma zaizo su tafi khdj ta haihu,gunaguni suka shigayi ,uwargidance tace,lallai an haifawa asabe mugun iri cikin ya yanta haihuwa da zuriyar uwar khdj ko asara,lallai kuwa asabe sai ta tashi tsaye in ba hka ba,wannan taliliyar ya da aka haifa ta shige gaban sauran ya yanta,hka suka yini sunata gunagunai,duk da irin tsananin kishin da matan mahaifin khdj ke xubawa ,indai mgna ce ta khdj yanzu zasu hada kai ,saboda tsananin kiyayya,ba komai ya janyo hakan ba irin kaunar da mahaifin khdj ya nunawa duniya yanaiwa marigayyiyar.

Lambar baba sallau ya kira,ganin kiran isuhu yasa ya dauka cikin hanzari sun gaisa ,y sanar musu d abin arziki,sunyi sallama da alkawarta cewa inshaAllah suna nan tafe,gwoggo tafi kowa farinciki da Allah ya sauki jikallanta lafiya,yaya safiyace da maryama suka fara shirin xuwa ganin msijego da abinda ta haifa.misalin karfe shida suka sauka a gidan khdj,karbar da asabe tayi musu bbu yabo babu fallasa itadai tunda yusuf ya sanar da ita haihuwar khdjn abun duniya ya taro yayi mata yawa,ruwama yaranta tasa suka kaimusu,cikin mmki sukace ina mai jegon,nan sujejin ashe tana asibiti baa bata sallama ba ,sallamar matan baban khdj sukaji,sun gaisa cikin girmamawa,duk da irin kiyayyar da suka dorawa khdj basa nunawa gaban dangin uwarta,dan madai sunsan khdjn ba makaryaciya bace da bazasu yarda da abubuwan da sukace suna mata ba.


Asabe ce tace barina shirya sai mu tafi asibitin baki daya,daki ta fada ta canja kaya,zuciyar nan tata a cunkushe fuskar bbu walwala,ta zura dogon hijabinta ,sannan tace su taso su tafi,taxi suka tsayar wadda zata kaisu har kofar asibitin,suna tafe a hnya suna hira samasama,ilahirin jikin mama safiya ysyi sanyi,mmkinta mutuniyar da akace ta hsihu tuni me ya hana asallameta,lallai bbu lfy,dan inharda lafiya a gida zasu isketa,kamar wadda akacewa asabe kalli tsallaken titi,khdj ta hanga tana tafe bbu mayafi,babu dankwali bare takalmi,ta ko ina jefa kafa takeyi tasa gabanta gabas,wani niimtaccen murmushi ta saki tare da cigaba da hira da mutanen cikin motar,isarsu asibitin yyi daidai da tada sallar magriba a masallacin asibitin hango yusuf tsyi yana kokarin shiga masallaci,da yake da rana tazo ta duba khdj dan hka tasan inda aka kwantar da ita,ita ta musu jagora har zuwa kofar dakin,tin daga nesa suka hsngo kofar dakin abude,isarsu suka shiga da sallama,abin mmki babu alamun mutum a dakin,can nesa mama safiya ta hangi zani akan wani karamin gado,tana kokarin karasawa sai baba sallau yace koba nan bne dakin asabe? Asabe tace da safe dai anan muka taradda ita bansaniba ko an canja mata daki,amma mu jira a idar da sallah sai na kira yusuf a waya,danna kikkira bai daga ba
[30/08, 9:42 a.m.] Ayush Iliasu: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU OF BAIWA WRITERS ASSOCIATION*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

1⃣1⃣1⃣-1⃣1⃣5⃣

~Wannan feji nakune yan uwanmu marubuta musammn My ASY KHALEEL,AUNTY ZARAH,YAR FICIKA da UMMY ABDOUL Allah y kara muku basira ,Da biunku na dabanne akwai ku da karamci da girmama dan Adam LYSM~

Ba su wani jima ba aka idar da sallar magariban, hango yusuf din da sukai ne yasa duk suka mimmike daga zaman da sukayi, cike da mamakin dalilin kin shigar su dakin ya karaso inda suke, kafin mama safiyya tayi mgana yusuf yace "ya kuka tsaya a bakin kofar ku shigo mana har yanzu bata farka ba koh?" Ya fda yana kokarin shiga dakin, ganin bbu kowa akan gadon ya juyo ya kalle su fuskarsa cike da alamar tambaya, "yana ga bata cikin dakin" ai kai za mu tambaya dan mu tin da muka zo ba mu tadda kowa a ciki ba" maryam ta fda tana maida duban ta gare shi, cike da tashin hankali ya nufi wajen nurse din nan suka shaida mashi basuyi mata chanjin daki ba, sanda ya zo ya shaida musu ba kqramin tashin hankali suka shiga ba mama safiyya kan bnda inalilahi waina'ilaihir rajiun bbu abinda take fda, gaba dayan su sukayi hanyar fita dan nemanta raba hanya sukayi ko Allah zai sa a ganta, dan sanda suka fito gate an shaida musu anga fitar ta, asabe kuwa murna take sosai iya ranta, Allah ubangiji yasa kar a ganta, abu kamar wasa har karfe tara bbu khdja bbu lbrin ta cike da tashin hankali suka dawo gda, baba karami kuwa na makale da jaririyar bnda kuka bbu abinda yake yi, shike nan daman rabuwa zasuyi shiyasa take ta bashi wasiya, ranar dai yadda suka ga rana haka suka ga dare dan bbu wanda ya iya rintsawa a cikin su, washe gari tin da akayi sallar asuba suka kara ficewa ko Allah zai sa a ganta amma bbu ita bbu dalilinta har dare, sanda gwaggo ta kira a waya tace a hada ta da mai jego suka shaida mata tana bacci, sbda basu so su daga hankalin mahaifiyar tasu,

Abu kamar wasa yau kwana Uku bbu khdja bbu dalilinta hakan yasa yusuf yima jaririya huduba da sunan mahaifiyarta khdja amma za'a na ce mata *siyaam* ganin har an kwashe kwana bakwai yasa su mama safiyya suka hada kayan su dan komawa gda, a hada da rokon Allah,da daddare suka tambayi yusuf akan zasu tafi da *siyaam* amma baba karami ya dage akan bazai bada ita ba, nan yusuf ya shaida musu yadda sukayi da khdja kafin ta fara laruraar, ba dan sun so ba dole suka hkra suka tafi gda jiki a sanyaye

Sanda suka koma gda wa'azi sosai suka yima gwaggo akan yarda da kaddara daga karshe suka shaida mata batan khdja, sosai gwago tayi kuka, ta roki Allah ya bayyana musu marainiyar Allah,gidan malam musa ta nufa ,babban malamine mai dunbun almajiran da baa san yawansuba,ta shaida masa duk abinda ke faruwa da jikartata,tace malam ka taimakamin d addua ko jikata zata baiyana,marainiyace,bata da uwa,nice matsayin uwarta,hannu tasa aljihu ta zaro dari biyar ta mikawa malam,tausayi ne ya cika malm ganin yanda dattijuwa ke zub da hawaye,yace baba kibar kudinki insha Allah yau zan sa ayi saukar kur ani hade da sadakar wake da shinkafa,godiya goggo tayi ta masa ahka sukai sallama yasa aka rakota har gida.

Ganin yadda kowa ya damu da haukan khdja yasa asabe shiryawa dan taje wajen bokan dake zaune a grn khdja tin safe ta tambayi yusuf akan zata je gdan wani malami akan ayima khdja addu'a Allah ya bayyana ta cike da farin ciki yay mata umarnin zuwa tare da danka mata kudi ta bawa malamin sadaka, cike da farin ciki ta karba tayi hanyar fita

Tafiyar awa biyu tayi ta isa ga dajin lkcn da taje ta gama kwasar gaisuwa wajen boka sannan ta tsugunna tare da yi mashi kirari, dariya ya farayi sai da yayi mai isarsa yace "me ke tafe dake" ran boka ya dade kishiya ta ce ta haukace, to ina so kowa da kowa ya mnta da ita kamar ba'a taba yin tq ba a duniya ba, wata muguwar dariya ya saki, kije za'a miki komai, bamu bukatar ki wahalar da kanki, zaki kawo dubu hamsin kudin aiki, ba musu asabe ta dunkule mashi kudin ta tafi tana murna

Kwanci tashi ba wuya wajen Allah *siyam* ta cike kwana arba'in da haihuwa, sosai take samun kulawa wajen Aliyu da kuma baba karami, kwata kwata baza kace da madara ake shayar da ita ba, sbda yanda take kibanta kullum, ga kuma kyau da kullum take karayi, kamanin mamanta na kara bayyana a fuskarta, gashi kwata kwata bata da rigima,kjdja kan kwata kwata bbu wanda yake tinawa da ita ko lbrin ta babu wanda yake karayi

A bangaran khdja kuwa kullum yawo take a titi, yau ta kwana a can gobe ta kwana a can kamar kullum yau ma ta fito tana yawanta ta hawo titi, duk yadda mutumin nan ya so ya kaucewa khdja ya ci tura sai da ya bigeta, cike da tashin hankali, ya fito wasu mutane suka taimaka mashi ya shigar da ita mota, asibiti ya kaita cikin gagawa suka karbeta jinin da tke xubarwa sannan ya kira ya shaidawa matarsa, cike da tashin hqnkali ta taho, kwanan su biyu aka sallame su, direct asibitin mahaukata suka wuce da ita, ai kuwa nan da nan suka karbeta, haka Alhaji adamu da matarsa hajiya Asma'u suka juyo gda cike da tausayinta kuma da alkawarin duk karshen sati zasu na zuwa wajen har Allah ya bata lpya su mai da ta ga yan uwanta, dan kwana biyun da sukai da ita sosai ta shiga ran hajiya Asma'u


*ku cigaba da bin mu dan jin cigaban lbrin*


*MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU OF BAIWA WRITERS ASSOCIATION*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

1⃣1⃣6⃣-1⃣2⃣0⃣

```wannan shafin tukuici ne gare Ku, sis Haima,sis basira, my muhievert, auta habiby, my habibty Aeeshat abba, A.y indabo, nd janna jay ana tare🀝Dafatan zamuyi bikin sallah lafiya```


*BACK TO THE STORY*

Kwanci tashi ba wuya wajen Allah siyam ta cike shekara 6 dan har an sata a makaranta, sosai take samun kulawa wajen yayen nata maza, kwata kwata basa so su ga ranta ya baci, hakan kuwa ba karamij batawa asabe rai ba, yusuf ma kulawa yake da yar tashi, yana nuna mata son da duk yayanta babu wanda ya samu so a wajen yusuf kamar siyam, baba karami ya samu aiki a nan cikin garin katsina yana samu bbu laifi, kasan cewar mutum ne mai rukon amana, autar asabe ma an shiga ss3 ita da Aliyu, suna ta fara shirin zana jarabawar waec, duk sanda bba krmi ya fita aiki ba karamin wuya siyam ke sha wajen asabe ba, hakan ne yasa kwata kwata bata kaunar yayan nata yayi nisa da ita

Kamar kullum yusuf da baba karami sun fice da wuri bayqn sun sauke siyam a makaranta, bayan ta dawo gda ta gaida asabe cikin girmamawa kamar yadda ta saba kullum, tsawa ta daka mata sannan ta fara mata masifa " shegiya mayya, ai uwarki ta bar mun mugun iri wlh, zaki bace ki bn waje ko sai na kakarya ki" asabe ta fda tana rankwashin siyam, jin zafin rankwashin ne yasa siyam fara kuka "iyeeee tin kan ma na dake ki kike kuka ai kuwa zanci ubanki a gdan nan sai kiyi kukan da dalili" asabe ta fda tana neman abin duka ganin da gaske dukanta zata yi yasata saurim shigewa daki tana bata hkr, kwafa kawai asabe tayi tare da shigewa dakinta

*Bayan kwana hudu*

Tin safe asabe ta nufi wajen boka bayan ta gama yi mashi kirari ta shaida mashi bukatarsa ta san a daurawa siyam bakin jinin da har ubanta zai tsaneta, sannan kuma a mallake mata mijin ta sai yadda tai dashi, kar ya tsallake maganarta ko guda daya, wata muguwar dariya boka yayi sannan ya ciro wani kullun magani, "ga wannan zaki na sa mashi a cikin abincinsa da ruwan wankansa na kwanta uku, daga lkcn koh kara kika ajiye kika ce kar ya tsallake toh bazai tsallake ba, sannan wannan kwalabar kuma kije ki ajiyeta a dakin ki kiyi mata boyon da bbu wanda zai ganta, mudum kika bari ta fashe duk wani sihiri da kikayi zai balle ciki kuwa harda bakin jinin da zaki sama siyam din, wani kullum magani ya kara mika mata wannan zaki bata taci abinci sau uku itama daga lkcin zata samu bakin jini har girmanta bbu saurayin da zai ganta yace yana sonta, ammafa in baki sakaki da kwalbar da na baki ba, godia sosai asabe tayima boka ta biyashi sannan ta tafi

Sai da asabe tayi kwana uku tana yin abinda boka ya sata sannan ta samu nutsuwa tin daga lkcn asabe take juya yusuf san ranta, tsana kuwa yana yima siyam fiye da yadda yayi ma mahaifiyarta,

Kwanci tashi ba wuya wajen Allah siyam ta kammala pri sch yayin da ake ta shirin auren autar asabe itama ta samu wani shahararen mai kudi, haidar kuwa na b.u.k yayin da malam kuwa ya dawo shima har ya fara aiki a taraba, asabe duniya sabuwa sbda duk yayanta sun kama kasa, siyam kuwa ta shiga matsin rayuwa duk aikin gdan nan ita ce keyinsa sai ta gama zata tafi makaranta, ana cikin wannan halin ne baba karami ya samu transfer ya koma adamawa da aiki, ranar asabe tayi farin ciki sosai daman shi kadai ne duk asirin da take baya kamashi, dan kullum shi ke kula da kanwar tashi,

Satin baba karami uku da tafiya asabe ta tatara siyam ta kawo ta kano aikatau wannan dalilin ne ya sata zaman kano, sanda yusuf ya dawo asabe ta shaida mashi ta kai siyam aikatau bai ce komai ba sai ma gode masa da tayi

Siyam ma kan inda take aikin ba wani samun sasauci takeyi ba dan karan tsana suka dora mata dan ma dai matar ta sata a makaranta inda ta dora daga jss1

Auren autar asabe ne ya dawo da baba karami gda, sanda ya tambayi asabe ina siyam ta shaida mashi itama bata san inda tayi ba wayar gr sukai bbu ita, sosai yayi kukan rashin ganinta tare da neman yafiyar Allah na kasa rikon amanar da aka bashi

Khdja kan ana gdan mahaukata kullum sai dai a canzata daga wannan asibitin xuwa wancan amma har yanxu jikin jiya iyau,

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin matsi, kullum siyam ke shan wuyan aiki a haka har ta kai yanxu da take ss2
[23/09, 7:12 p.m.] Mommah: [18/09, 11:32 a.m.] Shmsy Sls: *MAI BAKIN JINI*

πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½πŸ‘½
πŸ‘½

*WRITEN BY*

*AYUSHA ILIASU*
*AND*
*SHAMSIYYA SALIS OF ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*

1⃣2⃣6⃣-1⃣3⃣0⃣

_Wannan fejin sadaukarwane gareki Hawwa saleh,Mum sumy n Aneesa,Aysha humaira,Aunty jmla,Aunty faty Baba Danbala,mmn ihsan,mmn Aysha of Ayusha Iliasu novel grp,Allah y bar zumunci_



Kamar kullum tin da siyam ta tashi sallar asuba bata koma ba, gyaran dakuna ta farayi sannan ta dawo falo ta gyara, tana gamawa ta tafi kitchen ta dora musu girki, nan da nan ta gama kasan cewar ba wani mai wuya ta hada musu ba, saddiq ta zubawa abinci a lunch box din sa sannan ta shige daki ta yi wanka, sanda ta fito cikin shirinta na makaranta, lkcn hajiya da saddiq sun gama break fast, tattara kwanukan tayi taje ta wanke su sannan ta samu ta zuba abinci kadan a flask ta hada da

Please Login or Register in order to submit comment