Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suke turawa idanunsu,sun kai 3mins a haka kafin Fadwa ta kauda idonta daga gareshi,ya taso ya koma inda yake facing dinta ya zauna sannan ya kira sunanta a hankali "Fadwa"ta dago batare da ta ansa ba tana kallonshi,yace "meyasa baki ansa ba da Baffa ya tambayeki kina sona?",Fadwa kanma dariya ya bata,ta kalleshi tace "bakaji ansan dana bashi bane?"Aliyu yace "wace ansa kuma?ba shiru kkayi ba๐Ÿ™"tace "karka damu shi yaji ansan dana bashi".."Yanxu muje kaci abinci saeka je kayi sallah dan naji kamar an fara kira"yace "barinje kwae inyi sallahn inyaso"tace "tou shikenan ga can toilet sae kayi alwalan masallaci kuma na qofar gida,idan ka fita ka tambayi me gadi zae nuna maka"yace "yes my princess"sannan ya tashi ya nufa toilet din,ita kuma cikin gida ta tashi ta shiga....



08102992472 for comments



ยฉ *Hama G Muh'd*๐ŸŒท
[8:37pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€ *KOMAI RINTSI 2*๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ



*Dedicated to Mom Sudaes๐Ÿ˜˜*



*_Written by โœ๐ŸฝHamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*


Page 6โƒฃ1โƒฃ & 6โƒฃ2โƒฃ
......Bayan ya fito daga toilet din sae ya fita waje,be tambaya kowa bama dan masallacin ba b'oyayye bane,bayan an idar da sallah yana shigowa ya kira wayanta,ta daga tareda yin sallama,ya ansa yace mata ya dawo tace tana zuwa sae yyi hanging.Be fi 2mins ba sae gata,tayi sallama ya ansa sannan ta shigo,"ina kema kinyi sallahn?"tace ae "eh,muje kaci abinci"miqewa yyi yana binta a baya har wajen dinng din,ta ja mai kujera ya zauna sannan tayi serving dinshi,bayan ta gama ajiye mishi komai a gabanshi saeta jaa wani kujeran ta zauna idonta na kan wayan hannun ta,kiran sunanta taji yyi "Fadwaa"ta dago kai "Naam"yace "keh baki cin abincine?"tace "ina ci mna,look kar ka damu ni naci nawa tun dazu",yace "tou nima na qoshi bazanci ba"ga mamakin ta sae taga ya miqe tsaye alamar wajen zae bari,tayi saurin tashi tace mishi "haba ya Aliyu meyasa ka tashi"yace "bazan ci bane indae kema bazaki ci ba",, "nace maka fa naci nawa tun dazu"inji ta,yace "tou meyasa baki bari munci tare ba?nifa bazanci ni kadae ba!"ta danyi murmushi sannan tace "tou zauna muci"ya nema gu ya zauna,ta dau wani plate a gun zata debi abincin ya hanata wae tare zasu ci,ta tsaya kallon ikon Allah kwae,deban abincin yayi ya kaimata baki taqi karba,yyi yyi amma firr taqi karfa,qarshe wani spoon ya dauka yasa ta gefenta tareda nuna mata "to ga spoon dinki"hakan ma da qyar ta yarda suke ci tare,kafin ta kai loma daya sae yyi aku a hakan shima yana saib'in cin abinci...
Bayan sun gama ta kwashe kwanukan abincin ta kai kitchen saeta dawo ta zauna a gefen shi,sun dan sha hira kafinnan yace tazo ya maidata gida sae ya wuce,cikin gidan ta shiga ta sanarwa Anty Rauda cewa zasu tafi,tayi musu sallama sannan suka tafi dan tym din Baffa baya nan ya fita....
Bayan baffa ya dawo daga sallahn azahar saeya shirya yace ma Anty Rauda zaeje gidansu Fadwa bayan ya kira Umma tace mai tana nan,yana isa yayi horn aka bude gate ya shiga,yyi parkng ya shiga ciki,a palour ya zauna yana jiran fitowarta,bata b'ata lokaci ba ta fito,bayan ta gaishe shi ya ansa sae yake sanarda ita abunda ke faruwa tace "Allah ya sanya alkhairi"yace "ameen,ko akwae abunda zakice? "Tace mishi "bbu"yace tou shi zae tafi..
Bayan su Fadwa sun fito gida straight ya maidata suna ta hiransu a motan,ji takeyi kaman bata tab'a rayuwan jin ddi ba irin na yau,sanda suka iso kaman kar su rabu suke ji (ayyrh soyayya ddi๐Ÿ˜ช).Daedae ta shiga gida sae taga Baffa yana fitowa,ta mai sallama sannan ta shiga ciki.A palour ta samu Umma ta cika tayi famm"munafurcin da kuka shirya kenan? Shiyasa aka kiraki can ko sanarda ni baayi ba kou,kuma kema kinsan dalilin kirannaki ae"Fadwa tace "kiyi hakuri umma wllhy ba haka bane", "yi mun shiru munafukan banza,na raeneki tun bakida hankalin har kika kai haka shine zaayi maganan aurenki ko sanarda ni baayi sae yanxu?tou *ayi dae mugani*",,hankalin Fadwa a tashe take bata hakuri "Umma dan Allah kiyi hakuri wllhy bbu wanda yakeda nufin munafuntar ki" "idan baki rufen baki ba zan tsinka miki mari "ae tuni Fadwa taja bakinta tayi shiru,ta tashi ta shiga daki dan umma batada niyyar magana,idan hankalinta yyi dubu tou a tashe yake,"Innalilla hi wainna ilaihir rajun,hasbu nallahu wa nimal wakeel"kwae take ta karantowa....



08102992472 for comments and other issues



ยฉ *Hama G Muh'd๐ŸŒท*
[8:38pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINTSI 2* ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ



*Dedicated to Mom Sudaes๐Ÿ˜˜*




*_Written byโœ๐Ÿฝ Hamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*




Page 6โƒฃ3โƒฃ & 6โƒฃ4โƒฃ
Hankalin Fadwa be dad'a tashi ba saeda taji Umma na waya tana ta zage2*,ko dawa take? ohonta..Adduoi Fadwa ta cigaba da karantowa har ta dan samu nutsuwa a ranta,sae lokacin ta iya tashi ta shiga toilet tayi alwala sannan ta fito tayi sallahn laasar,tana idarwa bayan ta kammala azkar d'inta saeta dauko al'qurani tazo tayi ta karantawa har taji ta daena wani fargaba,hankalinta ya kwanta sosae..
Bayan sallahn isha ta gama dinner,dakinta ta koma bayan ta kai abincin,dan kadan ta iya ci dan bkinta ba apetite takeji.Wayanta ta dauka sakamakon ringing da taji yana yi,"Assalmu alaikm"ta fada bayan tayi answering,Ya Aliyu neh ya kira,ya ansa "Waalkis salm"tareda murmushi kaman tana kallon shi,"how s my Princess?",tace "I'm apsolutely fine dear"yace "harna ji ddi,gobe kuna da scul kou?"tace mai "eh, dazu munyi waya da Saeema ae tace wae in shirya mu tafi da safe,but lecturen zae kai 12 noon",yace "nima ita ta fada mun,wae akwae wasu abubuwan da zakuyi clearing kafin nan",Fadwa tace "eh"yace "tou Allah ya kaimu princess"tace "ameen ya Allah"..Sun kai 40mins suna hiran su me dad'i kafin sukayi sallama dan zaeje hosptal yau,ta bude data kenan tana kallon 1000's ov messages na shigowa tana jin mamakin irin wannan surutu da MIEMIE BEE GROUP members keh zubawa,ko danma ba su kadae bane harda 'precious writers' da 'Ice old students' (su Fatee AA an baza koli a kasuwan surutu๐Ÿ˜‚)...Tana cikin tunani kwae sae taji muryan Umma kaman a mafarki,a gigice ta fito ta sameta a palour ga masifa tsaf a idonta,"ma uwarki kika ajiye wancan foodflask din"tana nuna palournta da Fadwa ta kai mata abinci dazu,Fadwa tace"abincinki neh Umma"cikin qaramar murya wanda keh dauke da bitterness ov hrt,Umma ta watsa mata harara tace "aeni na baro kiyi abinci na karb'a naci,abubuwan da akayi ta samun ina ci a da ma ya isa,dan ni yanxu na baro rakiyarku munafukai๐Ÿ˜•"....Kuka kwae Fadwa keyi,umma tace "I bakiyi kuka ba tukun dan wllhi kuka na nan gaba,sannan for ur information ki hada kayanki na baki daga yau zuwa safiya ki bar mun gida tunda ba na uwarki bane,hakan ma nayi qoqari dana riqeki har kika kai yadda kke a yanxu"ta juya tayi upstairs ta shiga palournta,Fadwa ta kai 15mins a tsaye a gurin tana kuka daga bisani ta koma dakinta inda ta kira Momy ta sanarda ita abunda keh faruwa,Momy tace "ki hada kayanki yanxu ina zuwa zan daukeki ban isa tazo garin wani haukan ta illata mun keba,maza*2 gani nan zuwa kinji? Inyaso gobe in Allah ya kaimu zanyi magana da Baffanku yayi hakuri kwae na dau y'ata",Fadwa ta ansa da "tou"Momy tayi hanging tana me jimamin abun,a ranta taketa tunani _tou meye damuwanta yanzu kuma,sannan idan ba yanxun ba yaushe take son dama a fada mata?kuma mu din ma ina kwatakwata befi 2days da sani ba,kai Allah ya kyauta_....Maza maza ta tashi ta shirya ta dau keyn mota sannan ta shiga dakin hjya ta sanarda ita abunda keh faruwa,koda hjyan taji hukuncin da Momy ta yanke bata mata musu ba dan hakan ya dace sannan tasan yadda momy ke son Fadwa bazata hanata yin hakan ba..Momy ta fito ta dau mota,ta kira maman su saeema ta sanarda ita sannan tace zata zo ta daukesu itada Saeema dan Allah,maman saeema tace ba damuwa saeta zo tareda jajanta abun....


08102992472 for comments and other issues




ยฉ *Hama G Muhd*๐ŸŒท
[8:38pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINTSI 2* ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€



*Dedicated to Mom Sudaes*๐Ÿ˜˜



*_Written byโœ๐Ÿฝ Hamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*



Page6โƒฃ5โƒฃ & 6โƒฃ6โƒฃ
......Maman Saeema ta nufa dakin Saeema kai tsaye ta sanarda ita abunda yake faruwa,har qwalla saeema saeda tayi dan tausayin halinda aminiyarta take ciki,tace "Allah zae mata sakayya,bari nayi fitsari na dauko himar sae in fito"Maman tace "to"sannan ta fita,Saeema ta tashi tayi fitsari ta fito ta dau himar dinta sannan ta kashe mobile data dinta tasa wayan a charge,chating din da basu qare ba kenan itada ya Suraj dinta ta fito...
Momy na isowa ta kira wayan maman saeema tace ta iso su fito,tace tou suna fitowa sae tayi hangin..Tym din ta fito daga side din Abba kenan taje fad'a mai zatayi rakiya wa Momy tareda sanarda shi abunda ke faruwa,beji dad'in abun ba gaskya,yace sae sun dawo.Suna fitowa ba b'ata lokaci suka tafi...
Fadwa ta gama firfito da kayanta daga walldrop saedae akwati daya neh da ita dan bama anfani dashi takeyi ba,ta zuba wasu kayan a ciki tana ta tunanin inda zata saka sauran sae taji ringing din wayanta,tayi picking Momy ceh tace tazo ta bud'e qofa,ta ajiye wayan ta fita da sauri taje ta bud'e tana ganin Momy ta rungumeta tana kuka,Saeema ma kukan ta soma taya ta,Momy ta dan goge qwallan idonta sannan ta shiga lallashin su,seda sukayi shiru sannan Momy tace su dauko akwatuna a boot na motan suje su shirya kayan a ciki sannan akwae wasu traveling bags a back seat su dauko suma zasuyi amfani,irin me set guda ukun nanneh,Momy da maman Saeema kuma suka shiga ciki har palourn Umman..
Saeema da Fadwa suka dauko akwatunan da bags din suka shiga dasu dakin,Kayan sawanta ta zuba acikin manyan akwatunan,sae daya akwatin tasa irinsu inner wears,gyaluka da su himarai,da qyar akwatunan suka rufu saboda cikar kayan,suka dauka suka fitar suka sa a boot sannan suka dawo suka dau daya daga cikin bags dinnan babban cikinsu suka zuba takalma a ciki,shima saeda ya cika, sae medium din suka zuba kayan kwalliya da sauransu,qaramin kuma wasu jakunkuna naga sunsa da purse sae ta dauko brush dinta a toilet tasa a wani zip.Ta dau igiyan charge dinta tasa sannan suka fitar duk sun shiga boot din kuwa,suka komo ciki tasa hijabinta ta dau waya suka fito suka rufo qofar,bbu komai nata a gidan dan har shirginta na scul ta da ta tara su a wani jaka ta dauko sun fitar da komai,suka shiga motar suna jiransu....
Su Momy da shiga basu sameta a palour ba dan haka Momyn Saeema ta nema guri ta zauna a palourn,Momy kuma ta shiga,a kwance ta sameta sae tayi wuff ta tashi kaman taga malakul maut tace "Yaya dae"tana mata mugun kallo kuma Momyn tayi mata sallamah,Umma tace "jirani a palour daallah ina fitowa",Momy ta fito tazo ta zauna,sae bayan kaman 5mins haka saeta fito ko gaisuwa bbu "yaya neh?"momy tace "ba komai ya kawoni ba illah maganan Fadwa da kkace ta bar miki gida,ni a ganinah kuma koda laifi ta miki ba ma ita ya kamata ki fada ba saboda hali irinna dan yau saeta fada wani hannun,kamata yyi ki kirani ni kice inzo in dau y'ata kou kuma shi Baffan nasu dan kin gaji,amma gskya ban ji dadin abunda ya faruba",wani kallon tara saura kwata Umma take mata kafin tace "sannu iyayena,tou dake da baffan sun duk nafi qarfinku wllhy kuma baku kai in biku a hankali ba,yarinya kuma zama da itane ba zanyi ba sannan kuma kuje *zaku gani* tunda ni zaa munafunta",Momy tace "ni ba dogon magana ce ta kawo ni ba y'ata nazo dauka kuma na dauka sannan keh kuma na fadi abunda ke cikina dan ni ban iya riqoba"tace ma maman Saeema da kou A batace ba "haj Muje"sannan tasa kai ta fice abunta,suka fito suka samu Fadwa da Saeema a motan,Momy tace "kun ebo duka kayan ina? "Suka ansa da "eh".Momy suka shiga suka bar gidan,a hanya Saeema nata lallashin Fadwa kan tayi hakuri yanxu kan ai *KOMAI* ya wuce, Momy da maman Saeema kuwa sae fadi'n hali irin na Umma suke tareda bawa momyn haquri,momy tace "bbu komi,tunda bazamu tabbata anan ba",momyn saeema tace hakane..A haka har suka iso gidansu Saeema,suka saukesu saeema tace ita kan zata bisu,Momy tace ma mamanta tou ta barta suje mana tunda gobe zasu scul tare dan Fadwa ta fada ma momy dazu,Maman Saeema tace tou ba komai sukayi sallahma ta shiga gida,Saeema da Fadwa ma gidan suka shiga dauko kayan da Saeema zatayi amfani dasu goben Momy kuma na jiransu a waje..Basu dde ba Fadwa ta taya ta daukan kaya dasu brush da takalmin da zata sa,bayan sun gama sukaje Fadwa ta gaida Abban saeema sannan Saeema ta tambayeshi kan zata gidan su Fadwan yace bbu komai, daman tasan ba hanata zaeyi ba,nana da nan suka fito suka shiga mota suka tafi.....



08102992472 for comment and other issues



ยฉ *Hama G Muhd*๐ŸŒท
[8:39pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINSTI 2*๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €Š


*Dedicated to Mom Sudaes๐Ÿ˜˜*



*_Written byโœ๐Ÿฝ Hamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*




Page 6โƒฃ7โƒฃ & 6โƒฃ8โƒฃ
......Suna isa me gadi ya bud'e gate din suka shiga,a car-park Momy tayi parking,dukansu suka fito suka fara kwashe kayan,Momy ceh tace ma me gadi ya d'an taya su shigoda masu nauyin,yace tou sannan ya fara kwasa yana shigarwa, a palourn Momy ya ajiye kayan sannan ya fita.Saeema ta taya Fadwa shirya kayanta a walldrop d'in d'akin Momy bayan sun gaida haj.kaka,lokacin Ummi me aiki har tayi bacci..
Bayan sun gama komai,dukansu sukayi wanka suka kwanta tareda Momy,tym din past 11 neh amma saeda Saeema tayi chattng,ta kai 12:15am kafin tayi bacci....
Umma kuwa kusan 2am kafin ta runtsa,sae saqe saqe takeyi wanda bashida dalili,kamar wata tab'ab'b'iya.A daren ta kira ya Faruq take ce mishi wae an ci mata mutunci har gida meye meye,ta kira Tasleem da Jaleel ma,Tasleem tace mata insha Allah zatazo gobe dake a garin take.Jaleel ko daman next week zae dawo daga Madeena dan ya gama karatunsa dama certificate yake jira...
Ya Aliyu tunda ya dawo gida yake ta neman layin Fadwa amma switch off,abun ya dameshi dan be saba kira yaji haka ba saedae ya kira baa daukaba,daga qarshe dae haqura yyi ya kwanta gashi yyi missing muryanta,ya jima kafin yyi bacci..
Washegari da safe ya fito karyawa kamar yadda suka saba tare suke cin abinci,ya gaida Abba da Momynsu,suka ansa suna tambarsa ya tashi lfya yace "lfya klou",har suka gama deban abincin bega Saeema ba kuma tunda yake tare suke cin abincinsu duka yan gidan,tou yau su uku neh kadae dama su hudu neh dan Haneef (wanda nace muku autansu neh)baya nan yana wajen Uncle dinsu dake zaune a Lagos (Baban ya Suraj kenan),yanxu shekaransa guda kenan acan,har sun shiga makaranta shida dan autan su ya Suraj din wato Saefullah.Haneef da Saefulla sunyi matuqar shakuwa da son junansu wanda hakanne yasa Uncle Ahmad ya dauke shi..
Ya Aliyu ya kasa haquri yace "Momy waeni ina Saeema ta shiga neh?",momy tace "Saeema na wajen Fadwa,jiya mun d'auko ta sae tace zata je su kwana yau zasu scul tare","kaman ya kun d'auko Fadwa?wani abuneh ya sameta komeh?"Aliyu ya fada confusely.Momy tayi mishi bayanin duk abubuwan da suka faru,kai kwae Aliyu ya kada tareda cewa "Allah ya kyauta"sukace "Ameen" sannan ya miqe,Momy tace "Ina kuma zaka?"Aliyu yace "na qoshi",bata qara mishi magana ba ya koma d'akinsa....
Momy na tashi da asuba ta tada su Fadwa,ta shiga tayi alwala ta fito ta basu guri suma sukayi, bayan sun idar suka gaida Momy sannan suka koma suka kwanta,sae tym din Fadwa ta tuno da wayanta a palourn Momy,charge yake yi,ta tashi ta dauko har yyi ๐Ÿ’ฏ ..Saeda gari yyi haske suka tashi sukayi wanka suka fito palourn gida,bayan sun gaeda haj.kaka da baban Momy sae suka zauna sukayi breakfast tare,bayan sun gama suka koma d'aki dan shirin scul...


08102992472 for comments



ยฉ *Hama G Muh'd*๐ŸŒท
[8:39pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINTSI 2*๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž ผ๓ €ผ๓ž Š

*Dedicated to Mom Sudaes*๐Ÿ˜˜



*_Written by โœ๐ŸฝHamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*



Page 6โƒฃ9โƒฃ & 7โƒฃ0โƒฃ
....Suna komawa Fadwa ta ciro kayanta irinna Saeema har style din wanda maman saeema ceh ta musu,da gyalensa dan Saeema ma gyale zata saka,bayan sun shirya sunyi kwalliya wanda yasa sukai matuqa wajen kyau Saeema ta dau wayanta ta kira ya Aliyu,ringing d'aya ya d'auka "Hello d'an uwa"yace "hy,kin tashi lfya"tace "lfya klou wllh kaifa"yace "same here,ina Antynki"tayi murmushi sannan tace "gata nan"ta bama Fadwa wayan,"Aslkm"ta fad'a da siririn muryarta ya ansa da "walksm,kin tashi lfya"tace "lfya lou,nd u"yace "same my princess,kin san meh"tace "aa" tana me jin dad'in hira dashi,yace "I miss u more than words can say,I miss ur voice,ur sweet words,ur smile infact I miss every single ting about u"tunda yake maganan murmushi kwae takeyi tareda son ganinsa,tace "It's desame thing happnng here"yace mata "kun shirya neh? "Eh kwae tace saeyace "ohk ku jirani ganinan zuwa insha Allah"tace "ohk,Allah ya kawo ka lfya"yace "ameen my princess"sae yyi hanging...
Ta miqa ma Saeema wayanta wacce tunda suka fara hiransu take bin Fadwa ta kallo,tace "ikon Allah,nida wayana kumama nina kira baa bari nayi maganan dayasa na kira an karbi wayan sannan an gama baa jira nayi magana ba an kashe๐Ÿ™„"Fadwa tayi ta mata dariya sannan tace "wae mu jirashi yazo ya kaimu"Saeema tayi tsaraf tace "mu jirashi yazo kuyi hira dae๐Ÿ˜Ÿ",dariya Fadwa ta cigaba dayi kafin tace "wae meye damuwarki neh y'ar uwa?Ko dan baki ji muryan ya Suraj dinki ba",murmushin daba shiri ba kuma niyya Saeema ta soma yi sae tace "kin tab'o mun wani part na zuciyata wllh,kuma kin san meh?"Fadwa tace "saekin fad'a"tace "rabona da jin muryanshi tun jiya da safe,sae chttn",Fadwa tace "tou ba saeki kira shi ba yanxun",Saeema tace "barshi kwae,in ya tashi nasan zae nemen"Suna cikin hiransu wayan Fadwa yyi ringing ta d'aga tareda yin sallama tace "ohk gamu fitowa,amma bazaka shigo ka gaida Momy ba tukun"yace mata anjima in yazo saeya shigo tace "tou ba damuwa"sae tayi hanging,ta juyo ta kalli Saeema tareda d'aga mata gira daya "muje kou"Saeema ta miqe ta kai mata duka ta kauce tace "ke da ya Aliyu"kaman zatayi kuka,Saeema tace "au tanan kka b'ullo yau kuma"Fadwa tayi dariya sannan tasa kai ta fita Saeema na biye da ita,a palour suka sami Momy sukayi mata sallama ta basu 2 2k kowa,sannan sukayi godiya suka tafi Fadwa na Allah Allah taga ya Aliyunta...
Yana zaune mota ya qosa ya ganta,ya dau wayansa yana kallon picturen ta yana ta zoomng yana murmushi shi kadae,can ya hango su sun bud'e gate sun fito suna doso wajensa,kayansu iri d'aya abunsu kuma sun matuqar yin kyau,kafin su iso ya bud'e motan ya fito ya tsaya yana jiran isowarsu,suka iso tareda yin sallama ya ansa idonsa kyem akan Fadwa,ita kuma bata san meyasa idan sun hadu kunyarshi takeji dan magana ma kunyar yi takeji ba kaman a phone call,Saeema ceh tace "lurv birds huh!!idan kun gama sae mu tafi ae"ya Aliyu yace "bamu gama dinba in kin matsu kiyi flying ki tafi"Fadwa tana mata dariya tace "ni dinko ya Aliyu,kaga fa dariya take mun"kaman zatyi kuka,sae yace "sorry tou shiga muje"Fadwa dae dariya tayi ta musu tana mamakin irin shagwab'a irinna Saeema....


08102992472 for comments and other issues.Wayanda sukayi mun magana kwana biyunnan ban ansa ba suyi hauri pls๐Ÿ‘๐Ÿฝ ina yawan samun matsala da chats history nawa neh,masu messages na good wishes tnks to y'll,Allah ya bar zumunci,masu magana kuma akan novel suna iya sake mun magana in duba musu,for my lurvers and suppoters _Hama G lurvs u too so very much,Allah ya barmu tare_๐Ÿ‘๐Ÿฝ



ยฉ *Hama G Muh'd*
[9:39pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: [9:33pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: [9:21pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: [8:40pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINTSI 2*๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€


*Dedicated to Mom Sudaes๐Ÿ˜˜*


*_Written byโœ๐Ÿฝ Hamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*



Page 7โƒฃ1โƒฃ & 7โƒฃ2โƒฃ
A mota sukayi ta zolayan Saeema har suka iso scul.Yace musu in sun fito daga lecturen sae su kira shi,sukace "tou"sae sukayi sallama ya tafi,a hanyarshi ta komawa gida yyi texting Fadwa,' _Hey,I really miss being wit u,mah eyes wants to c u. .mah mouth to tlk 2 u ..mah ears to listen to ur sweet and charming voice ..mah soul to b wit urs and forever we are_'...Sae dayan kuma yyi typing ' _I promise to luv u till d infinity,kin zamo soul dina Fadwa I can't live without u,I luv ur personality,infact everything abt u makes me fall for u more... kuma *KOMAI RINTSI*ina tare dake,Insha Allahu rabbi bazan tab'a cutarda ke ba coz innayi hka kaman nayi wa kaina neh..luvely noon dear๐Ÿ˜˜_'.....
Fadwa taji shigowan message,da kaman bazata kula ba sae kuma ta ciro wayan a jaka dake yana vibration neh shiyasa taji,ta bude ta karanta cike da nishadi da son kar ya qare..Bayan ta gama ta sake bi tana karantawa tana murmushi da farin ciki fal a ranta,Saeema kuwa har ta gaji ta d'ake ta da duka tace "wae yau ni meke damunki neh sekace wata sabuwar kamu",Fadwa ta d'ago ta kalleta daedae ta gama karantawa sae tace "Ae nafi sabuwar kamu,ke kuwa idan banyi smiling ma text nah apple dina ba me zanyi wa smiling?"ta qarisa tana kallon Saeema,saeema tace "oh ni saeematu๐Ÿ˜Ÿ dama wa text ake ta yiwa wannan murmushi?"Fadwa tayi dariya tace "ba zanyi ba? "Saeema tace "aa zakiyi,gashi nanma kinayi ae"sukayi dariya a tare sannan suka cigaba da hiransu Fadwa nayi wa Apple dinta reply kamar haka....' _I'm going 3ru desame thing dat happen to b wit u dear,I luv u too and can't do witout u just as I can't live witout mah hrt,luving u mean my world to me,I lurv u more dan words can say,and I also promise to b wit u till d end ov tym insha Allah,have a colourful day sweet๐Ÿ˜š_'โ€ฆTayi mai sending tareda maida wayan cikin jaka bayan ta tabbatar da message din ya shiga,12 daedae suka tashi suka shiga hall yin lecturen,qarfe 1pm daedae aka basu break nah 20mins saboda yin sallahn azahar,bayan sunyi alwala sunyi sallahn sae aka koma sae past 2 suka fitoo.....


08102992472

My whatsapp num๐Ÿ‘†๐Ÿฝ



ยฉ *Hama G Muh'd*๐ŸŒท
[8:40pm, 12/5/2016] Hamagee๐ŸŒท: ๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ *KOMAI RINTSI 2*๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ๐Ÿ€๐ŸŒบ



*Dedicated to Mom Sudaes*๐Ÿ˜˜



*_Written by โœ๐ŸฝHamerh gee Muh'd๐ŸŒท_*




Page 7โƒฃ3โƒฃ & 7โƒฃ4โƒฃ
.....Suna fitowa Fadwa ta kirashi ta fad'a mai yace yana zuwa..Wanka ya fito lokaci saiya shirya ya dau keyn motar da wayan shi ya fito...
MOMYN FADWA
Bayan tafiyarsu ta kira Baffa ta sanarda shi duk abunda ya faru sae yace mata tazo ta sameshi a gida in babu abunda zatayi yau dan gobe yake son komawa Abujan,tace "babu komai barin shirya inzo "sae tayi hanging,ta tashi ta shirya ta fad'a ma hjya yanda sukayi sannan ta fita zuwa gidan.Tana isa ta shiga tayi parking motar sannan ta fita ta nufi cikin gidan,tayi sallama sau d'aya ana biyu aka ansa,anty Rauda nagani ta fito daga kitchen,suka gaisa tareda kawo mata drinks sannan ta nufa d'akin Baffa dan fad'a mishi Momy tazo...
Aliyu..befi 45mins da kiransa ba ya iso ya d'auke su,wani snacks-shop ya tsaya yace musu yana zuwa,be kai 10mins ba ya fito da ledoji 3 a hannunshi,ya bamawa Fadwa d'aya,Saeema d'aya sannan ya ajiye d'ayan..Kowa favorite dinsa ya sayo masa,Fadwa kayan zaqi neh nata ciki akwae icecream,chokolates,cake da wasu abubuwan,na saeema ko tafi son salty abu saeya sayo mata su meatpie,shawarma,eggpie sae youghurt dan mayyar shiceh..nashi ledan kuwa wasu drinks neh kadae aciki ya dau bottle na swan water ya bud'e yana sha,bayan ya gama saiya ajiye ya juyo ya kalli Fadwa yace "baku jin yunwa neh kam?"Saeema tayi caraf tace "bana jin yunwa dae,ita kam kallonka da tayi ma ta qoshiโ˜บ"Aliyu yace "na sani amma inaso ta d'an cine kar inna tafi taji yunwa"saeya dawo da kallonshi kan Fadwa wacce tunda suke maganarsu beji tace komai ba kuma daga dukkan alamu bata tareda su,Saeema ta lura da hakan itama saeta d'an tab'a ta,Fadwa ta firgita kad'an sannan tace "Eh, me kkace?"Saeema tace "tunanin me kke haka Fadwa?Meyasa kke sa damuwa a ranki,kin san hakan zai shafemu muma kou"Fadwa dae bata ce komai ba sae wasan da takeyi da 'yan yatsunta kanta na qasa...
Aliyu yace "Dearrr"ta d'ago kai ta kalleshi tareda maida kanta qasa,be dameshi ba ya cigaba "fad'a mun,meyake damunki?na fahimci mood d'inki ya canza tun sanda muka shigo mota,ko waninmu neh ya b'ata miki rae?"tayi saurin d'ago kanta tana facing d'inshi tace

Please Login or Register in order to submit comment