Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da chagern wayan sai kudin da umma ta bata ta sa su cikin jakan sannan ta fesa turare ta fita, bata sha wuyan samun napep ba kuma, mintuna basufi 20 ba suka kaita gidan haj (gidan su momynta),sunyi murna da ganin juna sosae dan sun jima basu hadu tace "momy ina khalifa?"momy tace "ae baffan ku ya tafi da shi wancan zuwan da yyi" Fadwa tace "ayyrh, shine kou ya kira ya fada mun",tashi tayi ta nufi dakin haj.kakarta ta gaida ta sannan ta dawo palour gun momy sukayi ta hira..Fadwa tace "momy" in a cool nd sweet voice momy ta ansa "Yar momy" Fadwa taci gaba "dama ina sone ki dan bani kudi zan siya inner wears anjima a kasuwa,kuma ina son zuwa gidansu saeema dama nace mata zanzo kinsan ya Aliyu ya dawo, kuma ranan da suka je gidanmu bamu hadu ba an kira shi a gun aiki",momy tace "tou ba damuwa, nawa kke so?" Fadwa tace "koma nawane momy, inner wears kwae nake so ae" momy tace "tou shikenan in kin tashi tfya saeki mun magana kou" Fadwa ta gyada kai, "kije ki debi abinci kici"inji momy,Fadwa tace ta qoshi....
Bayan sallahn laasar fadwa ta ce ma momy zata,momy ta bata 5k na inner wears sae 1k wae kudin mashin dan tsakanin wajen da dan nisa,,Fadwa tayi godiya ta fita..Kai tsaye wani butique ta sauka, ta biya me napep kudinsa sannan ta nufa shagon, kaya neh masu yawa da kyau cikin sa, kai tsaye wajen inner wears ta nufa ta zabi wanda sukayi mata, tana gama jida ta je akayi mata total din kudin,a ranta tana ta addua Allah yasa ba sae tayi ciko ba, ga mamakinta ko sae sukace 4300 zata bada ta cire ta biya,taji mmaki da taga an bata change a 5k din dan kayan da ta deba na da yawa,bayan an samata a leda ta fita..Ta fito kenan ta ciro wayanta tana duba tym bata ankara ba suka ci karo da wani,shikuma tym din ya juya yana magana da wani, wayanta neh ya fadi a qasa,tsugunawa sukayi a tare tasa hannu shima yasa,kwae suka kalli juna,kallon kallo suka tsaya yi kaman masu tuna wani abun sun kai 2mins a haka kafin ta daga wayanta tayi saurin miqewa, shima miqewan yyi,bata rai tayi fuskan ta cike da masifa "sorry" yace mata dan ya lura da yanayin da take, jikinta yyi sanyi sae tayi saurin barin wajen,tana isa titi kuwa ta samu napep ta tsare ta shiga,ya kai 10mins a gurin yana tunanin fuskanta kaman ya taba ganinta, tou a ina? ...Itama ta wajenta hka neh,kaman ta sanshi somewhere,kuma meyasa suke kallon juna haka? (Ohonku daeπŸ˜‚)..Sun danyi tafiya me nisa kafin suka isa gidan su saeema, sunyi murnan haduwa sosae, ta shiga ta gaida maman saeeman tareda shaida mata su momy na gaida ta tace tana ansawa,,bayan sun koma dakin saeema ta kawo mata ruwa da wasu drinks din dan tace mata ita a qoshe take, koda ta tambayi saeema ina ya Aliyu sae saeema tace dazunnan ya fita wllhy..
Sun kai awa biyu kafinnan Fadwa tace zata tafi, koda saeema tace ta dan jira in ya Aliyu ya dawo sae ya maidata gida, tace aa gidan haj.kaka zata ba gida ba, bbu yadda saeema batayi da Fadwa ba akan ta dan qara zama amma Fadwa taqi,tayi sallama wa maman saeema sannan ta fito saeema na mata rakiya suna taba hira har suka rabu, Fadwa ta shiga napep saeema kuma ta koma cikin gida..Tana isa gidan hjy.kaka ana kiran magrib.......


🌷Hama Gee Muh'd🌷



08102992472 for comments
[9:08pm, 12/5/2016] Hamagee🌷: [8:19pm, 12/5/2016] Hamagee🌷: πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ




*_Written by✍🏼 Hamerh gee Muh'd🌷_*



Page 3⃣4⃣ & 3⃣5⃣
Tana shigowa kai tsaye tayi dakin momynta dan lokacin ba kowa a palourn sae wata me aikinsu (Ummi) data fito daga kitchen riqeda basket na fruits data wanke ta ajiye kan dinng table, tana ganin Fadwa ta mata sannu da dawowa dukda ba wani girmanta Fadwan tayi ba sannan ta koma kitchen din..Fadwa na shiga dakin taga ba kowa momyn ta shiga toilet yin alwala.Dakin haj.kaka Fadwa ta shiga itama ta fito kenan daga toilet din, tace yauwa barin shiga fitsari ya matseni wllhy gashi momy ta shiga toilet din,kan haj.kaka tace wani abu Fadwa tayi sauri ta shige toilet din, sanda tayi alwala ta fito tayi sallah sannan ta koma dakin momy, ta sameta a zaune kan sallaya tana danna wayan ta.Tace "andawo?" Fadwa tace "eh, momy tace na gaisheki,yanzu zaki maidani gida neh?" Momy tace "yanxu kuma?,ki bari ayi isha kafinnan kinci abinci sae mu tafi" "tou"kwae tace sannan ta dauko ledan inner wears din ta nuna ma momy sannan tasa cikin jakanta da chagern wayanta...
Bayan sallahn isha around 8:40 haka,momy tazo zata maida fadwa gida,sanda Fadwa ta shiga dakin haj.kaka tayi mata sallama dan lokacin tana daki, har dakin ummi sanda ta shiga tayi mata sallama ummin ta rakota har mota,sanda suka bar haraban gidan kafinnan ummi ta shiga gida, a hanya sukayi ta hirarsu abun shaawa kaman qawaye.9:05 daedae suka iso,a gate momy ta ajiyeta ta juya bayan sunyi sallama, Fadwa na shiga baba me gadi ya bata keyn gidan dan har tym din umma bata dawo daga asibiti ba,ta qarba tace mishi "sannu baba" ya ansa da "yauwa Aisha,an dawo? "Tace "eh" yace "tou madalla",sannan ta nufi cikin gida, tana shiga tayi dakinta ta cire gyalenta sannan ta nufa kitchen,abinci su baba me gadi da driver ta dauka ta kai musu dan har tym din da zafinsa sosae dan warmern me riqe zafine, tana kaiwa ta dawo ta dau fruits ta wanke tayi fruit salad, ta zuba na umma tasa mata a fridge sannan ta dau nata ta koma daki bayan ta gyara kitchen din,ta dau wayanta da kunna mobile data sannan ta fara shan fruits salad din,messages neh keta shigowa daga groups kala kala daga ciki akwae wannan group dinda na taba ce muku naga ana turo kalolin abinci,tou na yau ma daban neh,abinci da drinks iri iri naga ana turawa (bansan sanda na dau numbern group admin din ba, nima nace tayi addng dinaπŸ‘€).Bayan wannan akwae groups kalakala irin su 'Home ov hausa novels', 'Novels world', 'Miemie bee novels group', 'Ksquare chambers' ,'Unique ladies' and lots more, novels neh ke ta shigowa kaman ruwa.Wani novel naga ta soma karantawa cikin nishadi me suna "IKRAM"novel din ya hadi iya haduwa daga ganin yanayinta...
Sae past 10 umma ta dawo, Fadwa taje bude mata qofa tana mata sannu da dawowa kamar kurma bata ansa ba ta wuce dakinta,Fadwa ta kulle gidan sannan ta shiga kitchen ta dau fruits salad din da tayi ta kaimata, bata sameta a palourn ba dan haka tayi saurin ajiye mata kan center table dan kar ta fito tace wani abun..Tana komawa dakin tayi shirin kwanciya sannan ta shiga tayi fitsari tazo ta kwanta...
Tunanin mutumin dazunnan neh kwae ya fado mata,meyasa bata mishi masifa ba? Ko dan ya bata haquri? Kuma meyasa yyi mata irin wannan kallon? Sannan ya taga kaman ta sanshi?,tambayoyi ta rinqa yima kanta wadanda ba ansoshinsu takeda ba, da taga ta kasa daina tuno shi sae kwae ta tashi ta shiga toilet tayo alwala tayi rakaa biyu tayi addua kan Allah ya zaban mata abunda yafi alkhairi a rayuwanta sannan ya cire mata tunanin bawan Allahn nan a ranta, ta tashi ta koma kan gado ta kwanta.Kar kuji mmki in nace muku batayi bacci ba sae 3😯 dan yadda take tuno siffofin mutumin nan....
Mutuminnan kuwa bayan tafiyan ta ya rasa meke damunsa, ya ma kasa siyen abunda yazo siya.Haka ya bar gurin, sae dare ya koma gida,har 12 beyi bacci ba yana tunaninta, tou ya tamun kama da wata? Meyasa take kallona haka? Oh God ya ban karba num ta ba,gaskya tana da kyau.......Washegari dasafe da kyar Fadwa ta iya tashi dan baccinda ke idonta, a haka tayi breakfast..
Mutuminnan kuwa komawa butique dinnan yyi ko zae ganta, "oh my goodness,gashi kou sunanta ban sani ba",...Ya jera kusan one week yana zuwa shagon ko ze ganta, amma shiru kke jiπŸ˜•...

_Kou waye wannan mutumin? Yaya zasu kasance dan Fadwa ma ya kasa barin kwakwalwan ta, zasu sake haduwa? Ko zasu daena tuna juna? Ku biyo ni danjin amsoshin......08102992472 for comments


©🌷Hama G Muh'd🌷
[8:19pm, 12/5/2016] Hamagee🌷: πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ


*_Written by✍🏼Hama G Muh'd🌷_*


Page 3⃣6⃣ & 3⃣7⃣
Ba wani bane saurayinnan illa Aliyu wato brothern saeema,siyen kaya yaje randa suka hadu da Fadwa..Ranan da yamma around 4:15, ya Aliyu yyi sending cloud album ma abokin sa sae yaga new number a contact list dinsa,be damu ba sae ya kunna datan shi ya hau whatsapp yana ta chttng da frnds can sae ya shiga contact list na whatsapp din saeya sake ganin dsame num dazunnan kwae sae yyi saving da suna *UNKNOWN* sannan yyi magana "Hlw" saeya sauqa ya ajiye wayan ya tashi ya shiga toilet ya watsa ruwa, yana fitowa ya shirya ya fesa turare sae ya dubi kansa a mirror,mataji ya dauka ya gyara gashin kansa da ya cika da gashi,tsayawa yyi yana kallon kanshi a mirrorn shi kansa ya san yyi kyau,ya dau keyn mota ya fita.Yana fita palour saega saeema ta fito daga dakin mamannsu."Iyee, irin wannan wankan,sae ina kenan? "Ta tambaya cikin zolaya,yace"idon matambayi" sae tace "ni dae ba idona ba kam,da idona neh da bazakayi wanka hka ba",yace "ae idon matambyi nace ba idonki ba" tace "ni din kenan"dkansu sukayi dariya, sannan ya dau hanyan fita,Saeema tace "kou inzo inyi rakiya neh"ta fada tana dariya shima dariyar yyi amma be juyo ba ya fice, yaja mota sae shagon nan da ya hadu da Fadwa, ya kai 30mins a tsaye a gurin wae yana jira yaga kou Fadwa zata zo, amma ina ranan dinma dalili neh ya kaita, daya gaji ya shiga mota ya zuna ya dan qara wasu minutes kafinnan ya koma gida....
FADWA
Tun da safe bata jin ddi,cikinta yana mata ciwo, dama kowane period sae tayi ciwon ciki da baya na 3-4 days kafin ta fara, da qyar ta samu ta gama ayyukanta yau,bayan sallahn isha umma ta sata ta shirya zasu asibiti tare sae ta hada ta da wani doctor wae ita tanada abunyi, ita kadae ta tafi sae driver ya kai fadwa..Bayan dr ya mata wasu tambayoyi sae ya bata magunguna tareda prescribing mata, tayi godiya sannan ta tashi zata fita daga office din....
ALIYU
Yana komawa gida yyi wani aiki a system sannan yyi alwala ya tafi masallaci, yana dawowa ya cigaba da aikin saeda akayi sallahn isha sannan ya shirya ya tafi asibiti...
FADWA AND ALIYU
Yazo shiga ita kuma tazo fita sukaci karo,sorry yace be ma kula da waye ba ya shiga, itama kanta a qasa yake lokacin amma taji kaman ta san muryan.Bata juya ba kwae sae ta wuce abunta, gurin motan su taje sannan driver yaja suka tafi.Suna isa ta dau ledan maganinta ta bude motan ta fito,driver da baba me gadi suka mata Allah ya sauwaqa, tace ameen sannan ta karba keyn gidan ta wuce....


08102992472 for comments



πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ



*_Written by✍🏼Hama gee Muh'd🌷*


Page 3⃣8⃣ 3⃣9⃣ &4⃣0⃣
......Tana shiga tayi dakinta ta cire himar ta fito ta dau ruwa a kitchen taje ta sha maganin kaman yadda dr ya fada mata, kwanciya tayi bayan wasu awowi tayi bacci....
ALIYU
Tun kafin ya dawo gida yake ta jin wani irin abu a jikin shi kaman yyi mantuwa a asibitin, sae ya gama iya tunanin sa amma be tuno wani abunda ya manta ba, kuma ji yake kaman wani abu me matuqar amfani ya manta..(nikam nace go sleep jare😏 ya manta mana fadwa kuma ya zauna yana babatu ananπŸ˜‚)..A haka yyi bacci ranan...
FADWA
Tana cikin bacci tayi mafarki wae sun hadu da wani, yace yana sonta itama ta yadda har sukayi aure, harda yaya uku😯.Tana tashi taga ashe mafarki neh kuma tayi staining kayan ta, tashi tayi ta gyara jikin ta ta sa wasu kayan,ta wanke wanda suka bacin ta shanya sae tayi fitsari tazo ta kwanta.....
Washegari sae wajen 7:30 ta tashi tayi breakfast ta kaima umma da su baba me gadi nasu sannan ta dafa lipton tasha dan bata iya cin abu me nauyi in tana period..Haka tayi na rana tayi na dare..
__________________________
Around 9:00pm ta kunna data zata duba group messages sae taga an mata 'Hlw' da wani num kwae sae tayi reply da "Hi"da kaman ma zata share sae kwae tayi sannan ta cigaba da chtng a groups.Bayan kaman 10mins taji shigowan messages sae ta duba taga ciki hadda wannan numbern,anyi reply da "yah kke"kafin tayi reply sae tayi saving numbern da UNKNOWN sae tayi reply "lou",sae yace "dat's gud, may i know u pls?"sae tace "know me as how? I don't tink so",ta burge shi da ya fahimci macece sai yace mata "alright den, ba wani abu but am sorry if i'm rude",jikin ta yyi sanyi tace "it's ohk"sannan ta sauqa dan ta fara jin bacci,gate taji an bude umma ta shigo, bata je bude mata ban dan jiya da yau umma na bude qifan da keyn ta neh...
ALIYU
Be wuce 20mins ba bayan ta sauqa shima ya sauqa..
2days after,su Fadwa suna ta shirin zuwa screening gobe,dan gobe zaa fara, monday kenan.Sun dan taba chttng da UNKNOWN da saeema kafi tayi bacci,dan gobe da wuri zasu je saboda layi..
WASHEGARI da safe saeema ta biyo ma fadwa tun 7:00am dan tasan kan su fita sae sun kai 8,yau da sassafe umma ta fita dan tun 6:00am bata kou karya ba, ta ba ma fadwa 1k sae su baba me gadi 500 na lunch sannan ta tafi..
Ai kuwa tym din da saeema tazo har fadwa ta shiya kwae sae suka tafi,Saeema take ceh ma Fadwa da ya Aliyu suka zo yace ta gaida ta dan yanxu haka yyi late wae tun 6:00 ya kamata yaje.Fadwa tace "ayyrh ni kullum bana cin saan ganinshi",saeema tace "zae zo daukana ae anjima, zaku gaesa😊"....


Kou Fadwa D Aliyu will b lucky today? Follow me.....


08102992472 for comments and other issues.Luv u all😘



©Hama G muh'd🌷
[8:19pm, 12/5/2016] Hamagee🌷: πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ



*_Written by✍🏼Hama gee Muh'd🌷*



Page 4⃣1⃣ & 4⃣2⃣
Bank suka fara zuwa siyan scratch-card,aka ce 800 ake saedawa, saeema ta cire 1600 ta bayar aka basu guda biyu.Fadwa tayi mata godya, tace ma Fadwa ita bata son haka sannan suka nufi makaranta,nanma saeema ce ta biya musu ita dae Fadwa bata da ta cewa dan qememe saeema ta hanata kashe kou sisi.
Sun kai 2pm a wajen,daga qarshe dae sukace kwae su tafi gida sae gobe,hakan akayi Saeema ta kira ya Aliyu akan yazo ya daukesu sun gama unfortunately yace bazae samu zuwa ba wae suna aiki yanzu haka sallah yyi zae shiga wani ward neh zasuyi aiki,tace "tou ba damuwa",tana gamawa ta fada ma Fadwa yanda sukayi sae ta kira mamansu,"Asslmalkum" ta ansa "Walkslm, momy ki turo driver yyi picking dinmu a scul wae ya Aliyu yana aiki",momyn tace "ohk yana zuwa"saeema tace "tou saena dawo"sae tayi hanging call.Masallaci suka nufa daman akwae na mata akwae na maza daban, Saeema ce tayi sallahn dan fadwa bata yi, bayan ta idar suka tambayi inane cafeteria aka nuna musu sukayi godiya sannan suka nufi gurin ,ice-cream suka siya sae wasu chocolates suka zauna suna shan icecream din suna tadi, saeema tace "kin san meh?" Fadwa tace "saekin fada"saeema tace "ina wani brothern Abban mu uncle Ahmad, wanda yake zuwa daga Lagos?" Fadwa tace "hka na tuno shi" saeema tace "yauwa tou akwae wani danshi saan ya Aliyu neh tare ma suka gama karatu,sunanshi ya Suraj" Fadwa tace "ayyrh,me ya samu ya SurajπŸ˜‰"ta rufe ido daya alamun tambayan zolaya, saeema tace "bbu abunda ya sameshi sae alkhairi,in gaya miki yau one week kenan daya ce mun wae yana sona,nima kuma yanxu na fara sonshi tunda kou ba komai jini nah neh ae" Fadwa tace "haka ne wannan,ae kou ba dan uwanki bane tunda har yace yana so ae saeki bashi dama"ta qarisa tana mata dariya "tou meye abun dariyan😠 wllhy ya ishe ki" Fadawa ta qara dariyar sannan tace "haba yer uwa, meye abun fushi yanxu"saeema tace "tou meye na dariyan?"Fadwa tace "wllhy kwae kin ban dariya neh tym din da kkace kema kin fara sonshi kuma na tabbatar inda yanxu haka zae tambayeki bazaki ce kina sonshi ba saedae ma ki ta jaa mai aji"dariya dukansu sukayi saeema tace "kin iya iskanci Allah,da barin ajin nawa zanyi a banza kou kin manta ajina na yanzu neh level 100 fa nake"Sukayi ta dariya, can saega drivern yazo......


08102992472 for comments


πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ


*_Written by✍🏼Hama gee Muh'd🌷_*



Page 4⃣3⃣ & 4⃣4⃣
Wayan saeema neh yyi ringing, tayi picking ta mishi kwatancen inda suke, be dde ya iso yyi parking,kiranta ya sake yi tace mishi gasunan zuwa,suna tafe suna tadinsu abun shaawa kai kace uwa daya ta haifesu.Suna isowa suka bude motan suka shiga baya dukansu,Fadwa ta gaida shi dukda ba babba bane ya dae dan fisu ya ansa da faraa yana musu sannu,nan da nan suka dau hanya,Fadwa suka ajiye sae suka wuce gida...
Tana shiga ta gaida baba me gadi ta karba key ta shiga cikin gidan,daki ta nufa ta cire kayan dan zafi take ji ta shiga tayi wanka ta fito tasa kaya marasa nauyi sae ta fesa turare, bata kou shafa mai ba saboda zafi saeta kwanta,bata jima ba bacci ya dauketa..
Saeema na isa gida ta nemi abinci taci bayan ta gaida momyn su dan ita ba irin fadwa bace tana cin abinci..Tana gamawa taje dakinta tayi wanka tayi alwala dan tym din laasar tayi, ta fito ta sa kaya tayi sallah,bayan ta idar tayi adduoi sae ta tashi ta cire hijabin ta hau gado,wayanta ta dauka ta kunna data, nan sukayi ta chrttng da ya suraj dinta.....
Sae bayan magrib Ya Aliyu ya dawo gida yau,saeema da momynsu na palour lokacin,suka mishi sannu ya shiga dakin sa yyi wanka tareda yin alwala yana fitowa ya ja jallabiya yasa ya fita masallaci, bayan an idar da sallahn ya dawo gida, sae tym din ya samu yaci abinci,around 9:30 bayan yyi kallo ya kunna data messages nata sintirin shiga...
FADWA
Ba ita ta tashi ba sae 6 na yamma dan bacci neh me nauyi ya dauketa, tana tashi tayi fitsari da brush saeta fito palour taga har tym din umma bata dawo ba.Kitchen ta nufa ta daura abincin dare, wajen 8:00pm ta gama komai ta kaima su baba me gadi nasu ta ajiye na umma,ta diba taci dan yanxu umma ta dena mata iyaka da abinci.Bude gate taji tareda shigowar motan umma,umma tana shigowa tayi dakinta dan yau ta mugun gajiya, ta ajiye jakanta ta cire hijabinta ta fito palournta ta dau ruwan sanyi tana sha,Fadwa ce ta shigo dauke da flask din abinci tazo ta ajiye tace ma umma "sannu da dawowa"umma tace "yauwa"sannan ta koma daki, fitowa Fadwa tayi ta shiga dakinta ta kwanta bayan ta kulle main qofan gidan, ta dau wayanta ta kunna data, sukayi ta chttng da su saeema a wani group na yar class dinsu......
ALIYU
Bayan ya danyi chttng saeya duba UNKNOWN yaga online,sae yyi magana "Aslm",(har Fadwa zata sauqa sae taga message ya shigo),ta ansa "waslm" yace "yah kke" tace "lfya klou and u"yace mata "same" tace "gud"..Dpn ta ya bude me zae gani? Pic din yarinyan da ya jima yana nema yace "my goodness,Allah yasa itace kou ta santa"yyi mata magana "hi,who's on ur profile pls"tace mishi itace, ya tambayeta "ta tuna randa wani ya bugeta taje siyen kaya? "Tace "ofcourse na tuno, ka san shine"yace mata "I'm d one" (ji tayi wani abu na mata yawo a kai)amma tace "ayyrh,zan kwanta saeda safe"yace mata "ohk, sweet dreamzz"..Batace komai ba ta sauqa 'sweet dreams kuma,me yake nufi?'sae kuma tace tou meye dan ya fadi hkan,da haka tayi bacci, shima saeda yyi ta tunani kafin yyi bacci.....



08102992472 for comments



©Hama G Muh'd🌷
[8:22pm, 12/5/2016] Hamagee🌷: πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI* πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ




*_Written by✍🏼Hama gee Muh'd🌷_*



Page 4⃣5⃣ & 4⃣6⃣
Washegari da sassafe saeema ta shirya,,,bata kou bi ta kan ya Aliyu ba dan tasan yadda ya gaji jiyannan be ko tashi a bacci ba, tana gama shiryawa tayi ma mamansu sallama sannan taje driver ya kaita.Suna isowa gidan yyi parking saeta shiga ciki,baba me gadi na waje lokacin saeda ta gaida shi kamar yadda taga Fadwa nayi sannan ta shiga ciki..Tym din Fadwa ta fito daga kitchen kenan zata kai breakfast din umma sae tayi wanka, kwae sae taji muryan saeema, "Aslkm" Fadwa ta asna sallaman "Walkslm",saeema ta tsaya kallon Fadwa irin har yanxu meh kke baki shirya ba..Fadwa tayi mata murmushi sannan tace "ya kka wani tsaya kaman sanda a wajen"Saeema tace "tou wa ya sani",dukansu sukayi dariya Fadwa tace mata ta shiga dakin tana zuwa, saeta juya ta kai abincin.A palour ta samu umma dan haka sae ta gaida ba laifi ta Ansa, Fadwa ta ajiye a fito dakinta ta nufa dan ta gama komai daman wanka neh ya rage mata batayi ba..
Ta samu saeema na toilet din, saeda ta jira ta fito sannan tace bari tayi wanka sae suje ta gaida umma,saeema ta ansa da "tou".Bayan yan mintunan da basu wuce 20 ba Fadwa ta fito daga wankan,tana daure da towel a jikinta,ta goge jikinta ta shafa mai da turare saeta sa kaya,daman kafin ta fito saeema ta ciro mata wata atamfa irin na jikinta, mamanta ce tayi musu,kayan sun matuqar mata kyau har saeeman,bata wani yi kwalliya ba ta dau gyalenta colourn kaya saeta rataya jakanta ta dau waya a hannu tasa takalmi tace "muje kou"saeema ta bita da murmushi sannan ta tashi tsaye tace "kinyi kyau abunki"Fadwa tace "keh kam baki gajiya da zolaya"suka fito saeema na biye da fadwa har zuwa dakin umma,lokacin da suka shiga tana palour tana karyawa sae saeema ta tsuguna har qasa ta gaida ta, ta ansa sannan saeeman ta fito,Fadwa tace "umma bari mu tafi"tace "ohk"sannan ta dau 1k ta bata,Fadwa tayi godiya ta fito tareda jin mamakin yadda umma ta bata 2k tsakanin jiya zuwa yau (nan ko uncle Khaleed neh ya tura mata harda na registration dinta)...
"Fadwaa" umma ta kwalla mata kira,ta ansa sannan ta shiga palourn,umma ta tashi ta shiga dakinta,da kudi a hannun ta ta fito ta miqa ma Fadwa "ga wannan akwae kudin da zaa tambaye ku a wajen saeki bada"ta ansa tace "tou na gode"saeta fice ta samu saeema a palour suka fita....
Yau ma sun taba wahalan amma basuyi zirga zirgan da sukayi jiya ba.Sae past one suka kammala komai da komai sae saeema ta kira musu driver ya kaisu.Be dde da kiran da tayi mishi ba ya iso, gidan su Fadwa ya kaisu sae Saeema tace yaje anjima bayan laasar ya dawo ya dauketa,yace mata tou sannan ya tafi,suna shiga ciki dakin Fadwa suka nufa Saeema ta kira mamansu ta fada mata sun gama amma yanxu tana gidansu Fadwa tace driver yazo daukanta bayan laasar, maman tace ba damuwa.....


08102992472 for comments




πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ *KOMAI RINTSI*πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊπŸ€πŸŒΊ



*_Written by✍🏼Hama gee Muh'd🌷_*



Page 4⃣7⃣ & 4⃣8⃣
.....Bayan sun gama wayan tym din Fadwa ta fito a toilet saetace mata "ki shiga kiyi alwala ni zan shiga kitchen dan bansan dawowan umma ba"saeema tace "tou our great cook"dukansu dariya sukayi sannan Fadwa tace "gara keh bakida damuwa"sannan ta fice fuskanta da alaman dariya.Saeema ta shiga toilet tayi alwala ta fito tayi sallah sannan ta fita zuwa kitchen din ta samu Fadwa nata fama,hanu tasa ta taya ta har suka gama suka gyara gurin, fadwa ta kaiwa su baba meh gadi nasu sannan tazo ta kai musu nasu palour,bayan sun gama ci suka kwashe plates din Fadwa ta wanke su ta kifa,daki suka koma sukayita hiransu me ban shaawa,suna cikin tadi wayan saeema yyi ringing ta daga, ya Aliyu neh ya tambayeta ta dawo gidane kou tana scul din, tace mishi ae ta bar scul tuntuni, tana gidansu fadwa amma ta kusa dawowa,yace daman inda tana scul dinne yana kusa da wajen da zaizo ya dauketa amma shikenan saeta dawo,ya tambayeta ko suna kusa da Fadwa su gaisa, tace eh sannan ta miqa mata

Please Login or Register in order to submit comment