Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dadi taji sosai tace "ok wipe away d tears for me if u mean ur words" dasauri yace "yes, i meant it nana" yasa hanu yashare mata k'walla, wani shu'umin murmushi ta sakar masa shima murmushin yake mata yace "i miss u so much nana" tace "really?". Yace "yes nd ofcourse, u mean alot to me"
Nikam mamakine ta isheni nace oh ni sajna, shikenan sun asircewa jawahir mijinta, inaji ina gani sukai ta lobewa ba kunya, nana harda kiss tayiwa mus'ab πŸ™ˆ ooh allah nah ba yadda zanyi incigaba da zama gidansu nana, sbd i can't take it nima ina taya jawahir kishin mus'ab dinta dan haka gara naje gunta inga meke faruwa.



β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
"Maami...wayyo mamii nah ya zanyi in kika mutu kika barni mami......mami dan allah kitashi," kuka sosai jawahir takeyi tana rungume da maminta, wata nurse ne ta lallab'a ta suka fita aka shiga duba mami.
Sun dau lokaci sosai kafun afito da mami kan stretcher akayi wani room din da ita . numfashi nafita a hnkl amma bata farfado ba, likita ne ya buk'aci ganin yan uwanta, jawahir da sahib suka shifa doctor din yace jawahir taje waje sbd har ynz bata bar kuka ba, se da tafita sannan yayiwa sahib bayani cewar k'odan mami duka biyu sun samu matsala dole se anyi mata dashen k'oda,sannan jini ta yahau ga ciwon suga.
Hawaye ne ke bin fuskar sahib din , sosai yayi kuka sannan ya tambayi likita solution, likitan yace k'odan wani za'a cire asanya mata, sahib yace likta "kacire nawa kasawa maminmu rayuwarta yafi mana komai"
Doctor yadafa shi "cool down please, be a man ,mace tayi kuka kai kayi wats d difference btw u nd her? ka nitsu kajini inshaa allah ur mum will be ok. Sannan mu bamuda k'wararrun likitoci kan harkar dashen wani abu dan hk akwai asibtin da aka bude dis year amma is private hospital Ba na gomnati baneh. In har kukaje da yaddar allah zata samu lfy, doctor shahid ya k.'ware sosai, yanzu i advise u ku kaita can"
"Ok, doctor kavamu address din , ina dai za'a iya yimata ayau,?". Doctor yace "ba zayyi yuwu ayi mata today ba aikine dayake son nitsuwa da isasshen lokaci, kuma ganin doctor shahid dinma wani aiki ne sbd miskiline sosai, sannan kuma u have to pay first b4 d operation se kun biya kudin aikin wanda ze kai 85 thousand a hasashe na".

Kuka sukeyi dukansu both he nd jawahir .tunanin Su A a ina zasu samu kud'in aikin mami.
Jawahir ne ta daga wayarta ta kira mus'ab tafada masa, tsawa taji mus:ab din yamata sannan yace "ko da wasa kada ki k'ara nema na a kan tsiyatacciyar matar nan dan bani nasa mata cutar ba kuma banida lokacin ki" kuka ta fashe dashi sosae ta durk'usa har k'asa tafara pleading kamar yana ganinta "mus'ab ka taimake Ni duk abunda nai maka kabari in mami na tayi lfy se ka hukuntani"
Ranshi a b.'ace yace"kin ban ajiyan kud'i ne ko meye? Ko uwata ce ba lfy.? Toh in uba nane manajan cbn ma yau banida kudin dazan baki". Nana dake kusa dashi ta karbi wayar dadai lokacin da jawahir "ko sadakina kavani mus'ab zan nemi cikato, lfyr mami tafimin komai, am in need of ur help mus'ab, yanzune nake buk'atar taimakon ka da gaggawa mus'ab,dan allah kataimake ni......" tafashe da kuka me ban tausayi.
Muryar nana data jiyo cikin wayar ne yasa ta saurarawa tareda zaro idanu, nana tace" ke yar matsiyata jawahir kike ko waye? Ina gaggawan sanar da ke kifita hanyar mus'ab yafi miki alheri, on ba gaka ba se kinyi dana sanin zuwanki duniya, kiyi kuka da kyau kuma yanzu kika fara, sbd mus'ab nawane yanzu ba naki ba, in ba ki ba ki gane me mgnr ba toh ki saurara da kyau nana Khadija ce yar mum da dad, aminyarki ada" tana fadan hk ta katse wayar.
Jawahir tafashe da kuka tana fadin *"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un, allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minhaa"*
Oh poor jawahir,allah ze saka miki😭.




*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’βœ by Sajnaa*
*08140813180*
β£πŸ‘„
[3/12, 07:48] Hauwa Shuaib E: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
*WATA KAWAR TAFI*
*GUBA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

*TRUE LIFE STORY*

*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’βœ by Sajnaa*


*41β†—45*


Sunan allah kawai jahawahir take ambato har ta samu sassauci aranta, shawarar da yaya sahib yabata kenan bayan ta labarta masa abunda ya faru.
Tace "yaya sahib yanzu inaga zan kira nabila awaya in fad'a mata nasan mommah zata taimakemu tanada kirki".
"A'a jawahir base kin kirasu ba, tunda har kikaga mus'ab yamiki hk dere must be sum tin, kawai kibari allah zaisama mana mafita".
"Toh yaya what of mami? Tun safe take asume fah?" Yace "ni inaga mu karb'a adress d'in asibitin can mutafi kawai, mu nemi su taimaka mana suyi mata aikin daga baya ko gidanmu ne se mu sayar mu biyasu kudin". Tace "toh muje Yaya"



_*DR. SHAHID CLINIC*_

Da sauri aka shigar da mami emergency aka sanya mata drip dan yanzu har da k'arin ruwa take buk'ata.
Su jawahir kuma se tambayar likitoci da nurses suke a onah zauga dictor shahid? Sun tambayi mutane yakai biyar amma amsa daya ake basu, cewar yau doctor shahid bayada lokacin duba kowani patient, kuma yayi warning kada kowa yashiga ya dameshi.
Sosai jawahir taji haushinsa, mamin ta na Kwance a sume tun safe sannan yace yau bazai duba kowani mara lfy ba? Afili tace "allah wadarai da mutumin dake biyewa son zuciyarsa akan aikin allah"
Wata nurse ce ta toshewa jawahir baki tajata suka koma gefe kan wani benchi, tace "baiwar allah kirufawa kanki asiri dan allah? Wlhy doctor shahid zai iya yin sanadin kwananki a xell idan yaji wannan mgnr kuma he will send ur mum out of d hospital batareda ya mata aikin ba, doctor shahid yanada zafi sosai mire especially at dis tym dayake cikin matsala"
Jawahir tace "toh meye laifin mu acikin damuwarsa da zaice bazai duba marasa lfy ba". Nurse d'in tace "hmm yau vana tunanin akwae wanda ze iya sauk'o da fushin dr shahid sbd yadda ransa ke bace, dan hk kawai kiyi addu'a kawai allah yasa yasauko amma mgnrki bazai jawo komi ba face wani vacin ran."
Jawahir tace "toh meyene ke damunsa haka?". Nurse d'in tace " _doctor shahid dan uwana neh, ni yar goggonsa ne mahaifinsa kuma kawuna neh, yanzu hk ina zaune ne agidansu doctor shahid, su biyune agun mahaifansu shida addarsa nafisat yanzu hk tana aure a bauchi, yayi karatunsa ne a us. Dawowarsa daga can befi shekara guda ba yanzu, dad d'insa ya had'a sa aureda wata yar uwarmu zuhra, yanzu wata hud'u kenan da aurensa a lokacin aurensa ne aka bud'e masa sabon asibitun nan da dad d'insa ya gina masa_
_se de abun takaici zuhra batada halin k'warai duk da cewar yar uwarmu ce amma zan bada shedar gskia akanta cewar halinta bana kirki ba ne, tanada bin maza at dsame tym kuma ga shaye shaye, yanzu hk kwanakin baya ya saketa amma dad dinsa yasa aka dawo da ita, again ya dawo da ita ya fahimci tanada juna biyu, jiya yazo da ita asibitin nan ya gwadata, da muka koma gida ya kirani side dinsu yake tabbatar min cikin da ke jikin zuhra ba nasa baneh, wannan ne yasanya ya yanke hukuncin ze saketa kowa ya huta, Amma da ya sanarwa dad d'insa da mum dinsa se sukace basu yadda ba sbd in yayi hkn ze watsar musu da zumunci kuma yanunawa duniya basu isa dashi ba, wai yabari zasu k'ara yimata fad'a zata gyara, kinji damuwar dake damun yaya shahid_
Jawahir tace "toh allah ya yaye masa, ni yanzu yaya zanyi da mami na?"
Nurse din bata bata amsa ba se ga wata nurse da gudu gudunta tana cewa "sister sajida wannan patient da kika sawa ruwa ta farka amma numfashinta sama sama take , kizo dasauri please"
Da gudu suka shiga d'akin da mami take, sosai ta galabaita idanunta sunyi jawur se hawaye takeyi, numfashin kamar ze fita, kuka sosai jawahir takeyi, nurse sajida ne ta lallabeta sukayi waje da ita aka samu akayiwa mami allurar bacci.


β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

Mus'ab da nana sunsha love sosai kafun mus'ab yatafi se da suka gaisa da mum din nana kuma yamusu alk'awarin he will be coming to see her everyday.
Sosai nana sukaji dad'i da mum dinta, a waya aka k'ira hjy shabuki aka sanar da ita cewar aiki yayi kyau mus'ab yazo, shewa tayi tace gani zuwa yanzu.
Ranar bushasha sukayi kamar ba gobe, nana kuwa kamar ba itace marar lfy ba, tawani sakewa yau jin kanta take as d most luckiest lady on d earth.


β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
Mus'ab yana sgiga direct d'akin mommah yashige tana bacci ya sameta dan hk ya dawo falo yanata sak'e sak'e, wani tsanar jawahir ne ke ziyartar zuciyarsa, haushin kansa yakeji dayayi wata alak'ar soyayya ma da ita, nawa jawahir take? Kwata kwata lokaci guda ya mance halin kwarai nata, ya manta soyayyarsa dake tsakaninsu, ya manta yadda yake zuzucewa akanta, da yadda yake burin auranta, ya manta komai se tsantsar tsanar ta dake yawo aransa.
Wayarsa ne tayi k'ara yana dubawa yaga new number ne anyi masa message
_*My sweetberry! Ka isa gida lfy? Allah ya sa hk. Allah ya kara karemin kai*_
_*Ur beautiful darling NANA*_
Kamar ta k'ara haukata sa ya rasa yadda zeyi da ransa,wani k'aunar ta ke k'ara fizgarsa, wayar nabila yakira yace tazo falo ta same sa, da sauri ta fito falon itada sisTer hanifa da wata baby yar addarsu
Tanemi waje tazauna tace "yayanmu angon wani sati ya naganka hk somehow kamar ba lfy ba"? Yace "Lfy amma ba lau ba sister". Tazaro ido tace "me ya faru"?
Ya juyo ya fuskance ta yace _*"i hate jawahir, na tsaneta fiyeda komi just now, kuma na fasa aurenta sbd yanzu nana nakeso nana k.'awar jawahir ita zan aura next week"*_
"Me kake fad'a yaya? Anya lfyrka kuwa?"
"Lfy ta lau nabila, kuma i mean my words, yanzu zan kira dad dina in fad'a masa kuma idan papa yadawo ma muyi mgn daahi da mommah"
Tace "yaya i think bakada lfy, amma banaje nasamu mommah" hanifa kam.mamaki ne ya isheta tace "wlhy ba lfy ba kam,yaya dakaje gidansu nana din me suka baka?"
A fusace yace "i dont know. Wato ma u mean nana tabani mgn ne koh? Toh ki kama kanki akan nana sbd tafimin komai tafimun komai i repeat myself". Dukansu ido suka zaro masa hanifa uwar tsoro tayi gum da bakinta 🀐 tabishi da ido dan tasan ba normal ba! Nabila ne ta dage tace "yaya nana tafi ma komai?". Yace "yess, i mean my words"
Ya fice ya barsu da mamaki.


β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

Kwana mami tayi tana bacci sbd allurar da akayi mata, jawahir ne ta kwana agun mami itada sister sajida sbd itama a week din tana night duty ne, jawahir kuka tayi tayi sister sajida na lallab'inta takuma umurceta da yin sallah ta rok'awa mamin ta sauk'i ,jawahir taji dadi sosai tare Sallar sukayi addu.'o'i.
Da safe jawahir zata fita nemo abincin sayarwa ta sayo musu, se ga sister sajida a moto, jawahir bata ma lura da wayea moton ba, tana tafiyarta sannu sannu tana kuma kalle kallen kyawun asibitin amma a wayance ba yadda za'ai mata kallon k'auyanci ba..
Sister sajida ne tayi parking moton agaban ta ta leko tana cewa "baby jawahir ina zuwa?" Jawahir tajuyo tamata murmushi tace "sister sajida ina kwana"? Sister sajida ta amsa suka gaisa tace "se ina?" Jawahir tace "zanje sayo abun karyawa ne abakin hanya nan"
Sister sajidaTa jata tace "mutafi cikin office dinmu, d'azu ankawo mun brekfast dina. Ban bude bama yaya shahid ya kirani wai inzo gida in daukoshi he cant drive his car sbd bayajin dadi."
Haka suka wuce office dinsu nurse sajida, wani babban food flask ne shake da abinchi,su koyi ne da chips duk an tarasu in a different bowls. Har dakin da mami take sukaje basu jima da shiga ba ta tashi. da kyar suka lallabeta taci abincin, Jawahir se murna takeyi, sosai tayiwa sajida godiya, sister sajida tace ba komai an zamo daya.

β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’
Mus'ab motsi kadan nana motsi kadan nana abun ya damu mommah sosai yau two days kenan yak'i zuwa gun jawahir Kowa ya kasa gane masa, abun daya ishi mommah se ta bugawa hjyrsa waya.


*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’βœ by Sajnaa*
*08140813180*
β£πŸ‘„
[3/12, 07:48] Hauwa Shuaib E: . πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
*WATA K'AWAR TAFI*
*GUBA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

*TRUE LIFE STORY*

*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’βœby Sajnaa*


*46β†—50*


Hjyrsa ta kirasa a waya tayi masa fada sosai akan sabon salon daya fito dashi, amma mus'ab bud'an bakinsa yace " mummy, nasan kina sona, kinason abunda nakeso, kuma bazaki so abunda ze cutar dani ba, kuma a dalilina kikasan jawajir har kikesonta aranki, kina sonta ne sbd ina sonta, mummy ynz banason jawahir kema kidaina sonta please, kiso nana ita nakeso please mum"
Hjyrsa tace "wai wace tsiyace nanan kam kake k'ok'arin maidamu k'ananan mutane akanta, kuma me tafi jawahir din? Ni nasani vazata kai jawahir mutunci da tarbiyya ba sbd masu hali irin na jawahir basuda yawa cikin matan ynz, se an tona, kuma kada ka manta fa an riga anbuga katin nan, sannan ni bazan tunkari dad d'inka da wannan batu ba, u better know, gara kadau shawarar mu kawai , in ka k'i kuma u're d one to deal with him, not me!"
Yace "oh mummy, u too? Kema bakyason abunda nake kenan? Meyasa hk mummy? Mommah tace ba da itah ba, kema kince badake ba, toh dawaye zanyi? Waye zai yimawa su dad mgnr kenan?"
Mummyn mus'ab kam ta gama k'uluwa da wannan d'an iskan batu marar kan gado wai auren nana, kuma abun takaici ma nana din aminiyar jawahir ce, toh ita inta amince akayi bikin nan dawani ido zataga nana da iyayenta?"
Karaf ta katse wayar dan takaici, tasa hanu biyu tana buga tagumi, wayar tane keta ringing amma fir taki dauka sbd tasan mus'ab ne sbd ringing data sa masa daban ne, ko mijinta dad d'in mus'ab bata samasa special ringing ba, sannan kuma ga sunan data sanya masa *luvly one* da manyan baki se yawo yake kan screen d'in.

Missed call takai 12 ita kanta takasa jurewa, ta amsa wayar tace "my son? Ya zanyi ne da baby jawa? I love her so much, ita nakeso as my in law ba nana ba, kaga nasan halin jawahir nana kuma bansan ta ba totally, kayi hkr mus'ab, ni inaji ajikina jawahir is d best wife u will ever have"
Cikin sautin kuka yace "ok mum, tunda bakiso shikenan is okay, nabari"
Hankalinta yatashi sosai tace "a'a my son dont cry please, kasan wani abu?". Yace "no" tace "ok, i will come to gombe tommorow insha allah, zamu tattauna kaji?". Yace "ok mummy, se kinzo". Tace "yauwa fine boy, kada kayi kuka, kaji? Kafa gidan papa akwai k'annenka dayawa dey will laugh at u,". "Ok mummy se kinzo din, dasafe zakizo ko?". Tace "insha allah early in d morning zaku ganni". Sukai sallama dukansu suka aje wayar suka shiga duniyar tunani.


Shi mus'ab tunaninsa mummy'nsa tace batason nana, dole ya hkr kenan? nd again tace jawahir takeso a matsayin surukarta ba nana ba? Shikuma bayason jawahir, nana yake so, ya zayyi kenan? Kuma harga allah mummy'nsa means alot to him, he can't do without her, tanayi masa duk abunda yakeso why not shima just for once yabi zabinta? Kaaaiii, it can't be! Yadda yake jin son nana na fisgarsa bayajin ze iya jure rashinta.

Mummy'nsa kuwa tunaninta shine meye ne yafaru tsakaninsa da jawahir haka? Ita yadda tasani mus'ab d'inta idan aka cireta aka cire daddy'nsa, toh ko y'an uwansa na gidan papa (su nabila kenan) basu kai masa jawahir ba, kuma wacce ta tab'a jawahir ranar ta tab'o jagwal, dan bata mantawa a gabanta ya make autan su nabila wai dan tace tafi jawahir fari.
Da wannan tunanin takira mommah tasanar mata cewar gobe tana zuwa, mommah tace "allah ya kaimu gobe d'in, gara dai kizo yafi, sbd nakasa gane kan yaron nan, bansan meyene nana tayi masa ba"
Mummy ta numfaa tace "wai nikam mommah who d hell is nana? Yar wayece itah? Kuma meye tayiwa mus'ab"?
Mommah tace "aminiyar jawahir ce, yadda ya fadamun wai 'yar gidan alhj ahmad ce ai, yaron daddy'nsa, inaga bazaki rasa sanin alhj ahmad din ba ai"
Mummy tace "what? 'Yar gidan alhj ahmad wanda nasani? Wanda alhj yaje gidansa kwanaki da mukazo gombe?"
"Yes, shi dai, au tare sukaje da mus'ab d'in"
Mummy tace "mommah bazan tab'a yarda mus'ab ya auri 'yar Rahana ba indai ina raye, baza ma afara ba ko da wasa insha allahu". Mommah tace "akwai matsala ne?" Mummy tace "ba kad'an ba ma kuwa, ke dai mommah se nazo gobe, zan fada maki komai akan Rahana". Mommah tace "toh allah ya kawoki lfy"


β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’

_*WASHE GARI*_

Misalin 11 na rana mummy'n mus'Ab zaune tareda mommah, isowarta kenan gidan, suka gaggaisa da kowa tace "hanifa kiramin yayanku mus'ab"
Hanifa tace "to" tawuce tasameshi rike da waya yanata danne danne, tashuga tazauna tace "yayanmu, ina kwana?". Ya amsa mata "lfy lau"
"Me kake yine da waya hk ko daga kai bakayi?" Yai murmushi "kun fiye gulma yarannan, mummy na turawa message sbd tacemun zatazo yau early in d morning kuma har yanzu shiru, yanzy kuma antynku nana nakewa msg"
Tace "toh mummy kam gatacan afalo itada mommah, yanzu ma itatace inzo in kiraka" ta mike tafita.

Dasauri dasauri Yashigo falon yana cewa "u're wellcome dear mumcy" Bata kulashi ba ya nemi guri yazauna, sannan suka gaisa, yace "mummy allah yayi kinzo, ya hanya?".
"Lfy lau,mus'ab inaso ka nitsu ka amsa mini tambayoyin da zanyi maka". Yace "toh mummy insha allah inajinki"
Tace "meye alakar nana da jawahir? Meye alak'ar ka da jawahir? Meye alak'ar ka da nana? Sannan meye dalilanka na yin danyen hukunci wa zuciyarka?"
Ya kalleta ya kalli mommah yace "mummy fa na aza zaki tambayeni ne gidansu nana kuje kuyi mgn amma.......". Be k'arisa ba mommah tace "kinji ko? Abunda yake fama dashi kenan mummy, in dai ba mgnr auren nana akayi masa ba yada wani interest din da zae saurareka"

Mummy tace "mus'ab hk kadawo? Kaida nasanka da halin k'warai, nake alfahari dakai agaban duniya, na godewa allah daya bani da guda daya tamkar dubu, ina alfahari da halayen ka na kwarai, amma mus'ab lokaci daya akan wata mace har momnah ta kasa handling tunaninka? Ita da ta daukeka as her son, ache baku jituwa if she's against nana? me ka zama ne mus'ab? Who the hell is NANA?"
" Am sorry mum, please accept my apology both u nd mommah means alot to me, ba yadda za'ayi na bijire muku kawae dae mummy inason nana ne son da babu wani masoyin dake yiwa wacce yakeso".
Sosai mummy da mommah suka gwalalo idanu suna kallansa😳😳, mummy tace "mus'ab meye hadinka da nana? I mean alak'ar ka da ita?" Tayi mgnr ne cikin sanyin murya. Mus'ab yace "mummy as u know, nana k'awar jawahir ce ko ince aminiya, a dalilin jawahir nasan nana sbd randa nafara ganinsu ma tare nagansu, yanzu kuma bazan kira nana kawar wacce nakeso ba se dai ince itace wacce nakeson"
Mommah tace "mus'ab me kasha neh mun shiga uku? Kada dai yafara shaye shaye ne mummy, do something please in ba hk ba zamu ji kunya" tayi mgnr ne hnklnta atashe.
Mummy ta kwantar da murya tace "Luvly one fadamun mekasha please, let me know, nice mahaifiyarka ka fadamun yaushe kafara shaye shaye?". Hawaye ne suke sulalowa a idan mus'ab , he bend down on his knees, ya rik'e hannun mummy dana mommah yace "Dukanku iyayeba ne, kun sanni kunsan halina, kunsan abunda zan iya da wanda bazan iyaba, uwa uba kunsan tarbiyyar da kukai min.Baku dorani a karkatacciyar hanya ba, dan allah kubar tunanin nafara shaye shaye wlhy banashan komai, sanin kanku ne ko panadol bana sha without prescription of a doctor, kawai ni nasani kun fadi hakane sbd yaddda nake muku mgn with opened mind free, nima kuma bansan dalilin dayasa bana iya boye k'aunar da nakewa nana ba".
Momnah tace "ok stop crying , is okay tashi katafi dakinka, we will talk about d issue kaji?" Kai kawai ya gyada mata yatashi, ta juyo ta fuskanci mummy tace "mummy wayene Rahana? Kumameyene lbrn da kikace zaki fadamin?
Mummy ta numfasa tace "nasan Rahana wato mahaifiyar nana farin sani tun yarinta"


β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’


Yau ne ake shirin yiwa mamin jawahir dashen zuciya sbd doctor shahid yaukam yasaki jiki yana kula da marasa lafiyansa, jawahir se murna sukeyi, sbd sister sajida tace mata za'ayi musu aikin free, jawahir tace "ashe dai tun farko nice ban fahimci halin yayanki ba amma ynzn nagane yanada kirki kaman ke" sister sajida tace "ai yaya shahid zuhra ce kawai ke sanyashi misbehaving, amma in ba hk ba duk family'nmu mata da maza yafi mu sauk'in kai"
Dr shahid ne yafito ya katse musu hirar, idanu ya kurawa jawahir, itakuma gausheshi tayi a mutunce ya amsa sede har yanzu be cire idanunsa akanta ba, sister sajida tace "yaya shahid zaka yi aikin yanzu ne?" Ya juyo with a smiling face yace "yeah, ina bross din nakin?"ya juya yana tambayar jawahir.
Tace "yanzu zaizo yaje sayo katin waya ne" ba'a jima ba yaya sahib yadawo, babu b'ata lokaci aka shiga dashi dan duba kodarsa wacce za'a cire asawa maminsa, sedai anyi rashin sa'a kodarsa itama guda daya ta lalace, daya ce kawai me lfy, jawajir tana kuka tace acire nata asawa mami, yaya sahib yace "kema hkne jawahir tun kina k'arama koda daya gareki me lfy, babu wani me lfyayyan koda acikinmu, hk abbanmu ciwon daya kashe sa kenan in baki manta ba"
Cikin kuka tace "bazan taba mantawa da silar mutuwar abba ba, yanzu ya zamuyi ne yaya sahib , wayyo allah nahπŸ˜­πŸ™†πŸΌ"


*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’βœby Sajnaa*
*08140813180*
[3/12, 07:48] Hauwa Shuaib E: πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€
*WATA K'AWAR TAFI*
*GUBA*
πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€


*TRUE LIFE STORY*

*β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’β€’ ✍ by Sajnaa*

*51β†—55*



Sister sajida ne ta lallab'i jawahir har ta dena kukan nata.
Doctor shahid kuwa has already lost his control, lokaci daya hnkln sa ya tashi ganin yadda jawahir ke rufsa kuka, _*"OH POOR JAWAHIR, MAY GOD HEAL UR MUM"*_Abunda yafada kenan yayinda ya kifa kansa akan teburin sa, yarasa meke masa dadi totally, komai ya dagule masa, anata kawo masa files na marasa lfy amma ko guda daya yakasa bud'ewa.


Please Login or Register in order to submit comment