Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fito tana jiranshi

be fito ba se 7h30 bayan ta gaishe suka zauna sukayi break sanan suka fice tun bakin get( porte)d'in school
yace ke fita se mun had'u wurin directeur ( principal)

ta turo baki tace yo sanin wurin nayi ni..

kada Allah yasa ki sani d'in ya ficewar shi, memakon ta bishi dan shirme se ta tsaya anan can kuma seta kirayi sambaby ta ce mata ta zo ta rakata gurin principal

,a hanyar
tace idan na gwada miki wurin zan koma classe (aji)dan kar ya hanani shiga

,Kenan baza ki jirani ba.?.shikenan na gode,

,haba kawas ba haka bane ,,ke bakuwace baze hanaki shiga ba tunda principal ze baki takardar shedar sabuwar daliba nikuwa fa?

ahh to yanzu na fahimce ki..koda ta shiga ta iske shi a tsaye suna magana da principal d'in ya juya ya kalleta yace gatanan sannan ya juya ya fita..

aka mata yan tambayoyi sanan aka gaya mata classe din ta.koda ta fito ta tambaye wasu d'alibai ina ne anphi?
suka Nuna mata ,da taje se taga har an shiga

se tafara taper馃憦馃憦...yace entre (shigo)

d'ago idonda zatayi waza ta gani inba Doc Rid ba馃槼.ta iso tare da fad'in Bonjour monsieur (g.morning sir)

.yace bonjour ,tu ne sais pas que si je rentre aucun 茅tudiant ne rentrera apr猫s , (bakisan idan na shiga ba babu dalibin daze kara shigowa ba)

tace 'non je ne sais pas je suis une nouvelle 茅tudiante'(i don't no i am a new student ) seya yace. D...

Am sorry fans kuyi hakuri da wannan馃檹馃檹馃檹

Love you All馃槏馃槝


Fasma &A茂cha
1/28/18, 11:05 AM - Fassouma Zander: 馃挀馃挒馃應馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煈ㄢ€嶐煈р€嶐煈�

*Zuri'ar* *mu*
( *Notre* *Famille* )

馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈ю煈ㄢ€嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈ю煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煉曫煉�


Story&written by
馃嚦馃嚜 ~A茂cha~ and ~Fasma~ 馃嚦馃嚜

*Suwaiba da ke da Red munga sak'on ku mun gode Allah ya bar zumunci馃檹馃檹馃槝*


```Dedicated to Ramatou```



55--60


Sai yace va t'asseoir(jeki ki zauna) dor茅navant ne viens plus en retard (daga yau kada ki kara zuwa a laty)

tace d'accord dayake cikin amphin akwai wuri diyawa dan haka can baya kusa da sam ta zauna

shiko ya cigaba da cours din chi ta juya ta harare ta tace daman yaya Rid ke muku cours bansaniba kuma koki gaya min

ta watsa mata wani banzan kallo tace kada ki raina nani mana keda mijinki amman kice baki san har yana kowarwa ba,?

in nasani zan tambayeki ne ,?

hum dakamar wuya kuna gida daya daki daya amman kice baki saniba,

haba sai kace baki san halin yaya Rid ba suna cikin haka se sukaji an jefo musu craie(chalk) yace venez au tableau (come to the blackboard)

suka taso sam fad'i take mun shiga ukku yau dan wuya zai bamu,

ta zumburo baki toh mi mukayi mishi,

Tab ai mijin wannan naki akwai shi da tsanani baya so yana cours ana d'umi (to inba abunku ba waye zeso a dinga d'umi yana cours馃槒),koda suka iso craie kin ya bek'a musu yace:je vais vous poser une question 脿 chacune d'entre vous si vous trouvez vous allez regagner vos place et dans le cas contraire c'est la porte et vous n'allez plus revenir 脿 mon cours pendant 2jours (zan ma ko waccen ku tambaya idan kun samo seku koma ku zauna Inko ba haka ba baza ku kara shigo min lecture ba har na tsawon kwana biyu),ok yafara ma sambaby ta bada amsa dede bien(good) sannan yama Manane duk da yaune ta fara zawwa amman elle a trouv茅(ta samo)

,ba shiba hatta daliban abin yaba su mamaki itako a jikin ta dan an tab'a yi musu shigen cours d'in,

yace vous avez de la chance(kunci sa'a)allez y vous assoir(kuje ku zauna ) sukace merci monsieur (thank you sir),suka koma har zasu zauna yace separez vous(ku rabu) sam se tadawo tsaka2 ta zauna itako ta zauna a bayan......
Dayake awa biyu ne kawai ze musu dan haka iya gamawa yatafi clinik ..

su ko basu dawo gida ba duk da sunyi pause d'in 3heure(3hours) intervalle 12h-15h(wutu awa uku tsakanin sha biyu da karfe ukku) har sam tana tambayarta idan kin wuni nan wa zeba mijinki abincin rana

oho mishi yaci gidan Umma ko Mom duk da nasan Mom ta turo mishi tunda tasan bana gidan

,haba Manane. ...

Aa tsaya ta katseta da fad'in kinga yau acike nake da shi, .

Ta tun tsire da dariya tace.kadade kice min dan ya tura mu tableau kike fishi dashi,

aww kin sani ma ashe kike tambayya tafadi cike da masifa,

to meda wukaken tayi tsaki

se 17heure(karfe biyar na marece)suka tashi takirayi Mom dan ta turo mata direba tace aa'a bari ma ga mijinki nan zezo d'aukarki ok sai ya iso......
Koda ya iso itakade ya isko fuskar nan a murtuke tazagayo ta shiga ta zauna ,,yama motar key yayi ribose cike da masifa yace miya hanaki dawo wa gida da rana,,?wa kike tsanmanin ze miki girkin rana ne da kika ki dawowa?

tayi mishi shiru abin daya kara tunzurashi kenan ya dinga fad'a har suka iso gidan..,(馃榿Rid manya tunda aka d'and'anan girkin ta to fa babu lfy inbe ciba 馃檮abinda be kai ya kawo ba ma fad'a yake,,..,)

tofa tundaga haka kullum seya zo d'aukarta da rana KO kuma ya turo mata driver sannan kuma ta koma da marece

Hakanan dhiyayi ta kaita 茅cole kuma ya medo ta har satin ya cika tukon ta fara zuwa a motar ta

..yau ma kamar kullum data gama gyara2ta tayi musu break tashiga wanka koda ta shirya ta fito.shi har ya kusan gama yin break d'in..ta zauna tare da gyasheshi ,ya amsa tare da d'ago kai ya kalle ta

tea kawai ta kurb'a ta tashi zata tafi
yace ke bade da wannan shigar zaki school ba?ta kalli kanta Riga ce har guiwa da wando na Pakistan tayi roll d'in kanta da mayafin kayan ..tace miye aibun kayan nan ?

yace inke bakiga aibunshi to ni na gani dan haka kije ki cire su

,,ta turo baki cike da shagwab'a tace latti fa zanyi ,

To kuwa sede kada kije 茅cole d'in yau.

Babu yadda ta iya dole taje ta canza kayan sannan ta tafi Allah ya sota bata yi retard diya wa ba ...


Bayan sun fito r茅cr茅ation (break) ta kalli sam tace yunwa nakeji mutafi cafet musha ice cream...bayan sun saye se suka zauna anan cikin cafet d'in ,,suna cikin sha Doc Rid yazo ya fice ta kusan su ,,daga nan bayan su suka ji wasu yan mata suna hira, daya daga cikin su tace walahi Doc Rid yana bala'in birgeni , ina sonshi tun lokacin daya fara sako kafarshi cikin school d'in nan ..KO kinsan saboda shi na zab'i zama head class (d茅l茅gu茅 adjointe) dan na samu opportunity samun number shi da sunan ya dinga bani information dan na sanar da sauran dallibe amman a banza tun ina b'oye mishi har,na gwada mishi mayta ta a fili amman kisan gayen nan miya ce mun ?,

wai shi be jima dayin aure ba kuma bashi da ra'ayin Karashi anan kusa ma kuma koda ze kara to ze zab'a ne acikin *Zuri'ar* su ,,abinnan ya b'ata min rai tun daga ranan nake neman hanyar da zan aureshi kota wani hali,,,ke..

Tofa ana wata ga wata...
Koya zata kaya ....?ku biyo mu danjin cigaba...

love you all


Fasma&A茂cha
1/28/18, 11:05 AM - Fassouma Zander: 馃挀馃挒馃應馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煈ㄢ€嶐煈р€嶐煈�

*Zuri'ar* *mu*
( *Notre* *Famille* )

馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈ю煈ㄢ€嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈ю煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煉曫煉�


Story&written by
馃嚦馃嚜 ~A茂cha~ and ~Fasma~ 馃嚦馃嚜

*Bamu manta dake ba Halima Warzagane Allah ya bar mu tare ya k'ara dank'on zumunci. Ameen馃檹*


_Dedicated_ _by_ _Ramatou_


60__65

Ke koda kuwa zanyi sanadiyar raba shi da *Zuri'ar* tashi ne...suka tuntsire da dariya suka tafa dayar tace haba Halima kada ki bani kunya duk iya kissar ki amman kice kin kasa shawo kan shi ,

,hum dan baki san halin shi bane ,

to Inde hakane hanya d'aya ce zaki bi ki sameshi

wata hanya kenan fa?matso kiji ..tama rad'a cikin kunne basu Manane dake gabansu ba h芒tta mu Bamu ji mitace mata ba,,..

ta d'ago tace anyan Hajjo zan iya kuwa?hum to zauna kallon ruwa kwad'o ya miki k'afa ''c'est ta seule chance '(it is your only luck)dan haka seki zab'a ko shawarar Dana baki ko kuma kina ji kina gani ya kara wani auren ,

,tabb to ai ko wannan imma bansan Yayi shi ba da bazan barshi ba bare har ya k'ara wani kuma bani ce matar ba..(kuji wani karfin hali) ke nifa komi nashi birgeni Yake bare ma yatsotsin kafar shi ,,ongles (farcuna )nan farare tas dasu bare in sun fara tofowa ji niki kamar name dasu nawa shiya sa nake zaman gaba2 dan nayi ta kallon su ....hakade suka ci gaba da hirar su ,inda Manane tacika tayi fam kamar zata fashe dan har zata ta tafi wurin yan matan tayi musu bala'i dan zuciyar ta har wani zafi take mata sambaby ta rik'e ta tace lfyr ki kuwa Manane kada de kishin Ya Rid kike ?haba wani kishi kawai de dan yana yayana ne haka ta dinga fad'a seda Sam tayi ta tausar ta har suka koma classe(aji) amman dama bata yi cours d'inba dan bata gane komi ba har aka tashi ,

koda yazo daukan ta da rana ,dayake motarta tasamu matsala tayi paci tun a mota take hararen shi duk da ya lura da hakan aman seya danganta shi da fad'an su na safe dan yasata tasauya kaya ,,

koda suka iso gidan fita kawai tayi tayi shigewar ta shiko tab'e baki yayi ya bi bayan ta koda ta ida abinci dayake jallof(sirundu)ne tayi yaji bushenshen kifi ,ta jera bisa dining ,yana palo taje ta fad'ama mishi ta gama amman yace se anjima ,,yana fad'ar haka ta shige d'aki can segata ta fito da 'coupe ongle'(abin yanke farce)dakuma reza ta zo ta zauna kusa dashi tace yaya kawo na yanke ma farcen kan mana naga sun fara tufowa (tofa kode Manane kishi kikeyine?),be kawo komi a ranshi ba ya gyara zama yana fad'i kamar kin san ko naso nacire su jiya kawai ban samu dama bane ita ko ta sauko ta fara yanke me a ranta kuwa fad'i take base kin k'ara ganin farcen ba bare har su birge ki(to ni Manane har farcen ma kishin kike ne halan,..?),,seda tagama yanke me tunkon suka ci abinci ,,,,a gaggauce suka shirya dan sun kusa yin latti dayake yana da cours shima dan haka tare suka tafi ....koda suka gamu da sambaby take sanar da ita ai na yanke me farcen shi yanzu bare har wata ta gani ta yaba ,,ita de sambaby kallonta kawai take dan ta harbo jirgin kawartata kawai rigimar ta ce baza ta bari ta gane cewa ta na son mijinta .......

Bayan kwana biyu dayin haka yau ma se ta sake saka kayan Pakistan dan zuwa ecole ta zata ya fita dan haka ko d'ar bata jiba ta fito zata fice ,

,daga bayan ta taji ance ke..!gabanta yabada damm ..ya iso kusa da ita yace wai ke miyasa bakya jin magana ne ?ranan nan bacewa nayi kada ki kara saka irin wannan kayan da zumar zuwa 茅cole ba?

Ta turo baki ,ya kama bakin ya murd'e ya ce to maza koma kici re su kuma walahi kika sake kikayi retard (latti)bazan barki kishiga mun aji ba ,,ta kalli 'montre'(agogo)taga bakwai harda minti arba'in da biyar(7h45)..tace dan Allah yaya kabar ni nata fi yau kad'e inba haka ba latti zanyi ,

,sede kuwa kiyi latti..

inko hakane to bazani ecole.din ba yau ,,,h

hh walahi inde baki jeba to 'devoir'(test)zan muku ,

,haba yaya ''vous etes si dure avec moi(you are so hard with me),,oho de dan kina b'ata ma kanki lokaci ,,babu yanda ta iya amman seta faki idondhi ta d'auke cl茅 (key)d'in motarshi ta shige d'aki ,,

hakayayi ta nema har sanda ta fito sanna ta mika mishi tana dariyar mugunta ,

,ya buga mata harara ya amshi key kin ya fita itama da sauri ta bi bayan tashige tata motar tabata huta dan seda ta rigaye shi zuwa.....,,
Bayan sun tashi da rana koda ta koma gida a palo ta iske shi ,,har zata d'aura tuwo yace aa tazo de su lek'a gidan Umma ,,bata kawo komi a ranta ba suka jera ,,

koda suka shigo gidan umma na palo suka zauna bayan sun gaida ta Rid yayi gyaran murya yace Umma dama akwai abunda nake so nafad'a miki gata de a gabata zan fad'a ba komi bane akan kayan da ta ke saka wane nayi mata magana taki ji ni umma idan hali harda safa da nikaf zata ringa sakawa inza ta fita.. tunda ya fara maganar umma ke hararar Manane har ya gama eee kuwa seta fara mata fa'da har seda kuma ya dawo yana bata ta hakuri tukon ta d'aura da nasiha daga baya.. amman har cikin ranta taji dadin nuna kulawar dayayi akan Manane... Umma na shiga cuisine (kitchen)Manane taja hijab d'knta ta fita sauri2 da sauri shima ya biyota koda ta fito gidan Mom ta shige haka shima ya shige gidan tana ganin Mom ta fashe da kuka(umm Manane sarkin b'aci kenan)ta kamo ta rungume tana bubuga bayanta kad'an2 ta kalleshi tace mikamata ?

Yace,,nifa ba abinda na mata kawai dan se ya labarta mata yanda sukayi da Umma yaci gaba da fad'in dan Allah Mom ki mata magana ta dinga saka hijab har can kasa da safa kai in san samu ne har da nikaf ta dinga sawa inza ta fita...Mom tayi dariya irin nasu na manya tace shikenan zan mata magana a ranta kuwa cewa tayi yaro2 ne koda d'an giwa ne... ya tashi ya fice dan har an fara kiran sallah ,

,bayan ya fita Mom ta dinga mata nasiha tana gayamata cike da wayo ,

,ta d'ago kanta cike da shagwab'a tace Mom walahi shine ma ya dace ace yana sa safa da nikaf ,,bakiga yanda yan mata ke kallonshi ba suna cewa yana birge su wasu ko cewa suke suna sonshima ,,ni walahi Mom da inada iko dashi to da kulle shi zan ringa yi a cikin gidan ba wacce zata sake ganin shi inko ze fita to nikaf zan dinga sa mishi ..,,wai har sambaby na fad'in kode kishin shi nike ..ne. ..

To kika cemata mi ?

haba Mom kema kinsa ba kishin nake ba kawai de dan ya yayana nane.....mom tace shikenan tashi kiyi sallah ,,

haka ta tashi tashiga d'aki Allah yaso ta yau ba ecole d'in marece ..

Mom ko cewa tayi yaro man kaza kude kuka sani da gulmarku daga ke har mijin naki.




Ku biyo ni dan jin yanda zata kaya....shin Rid ze auri Halima ne? ko kuwa baze aure ta ba? Kuka sance tare damu ..
Mune de naku

Fasma&A茂cha
1/28/18, 11:05 AM - Fassouma Zander: 馃挀馃挒馃應馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煈ㄢ€嶐煈р€嶐煈�

*Zuri'ar* *mu*
( *Notre* *Famille* )

馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈ю煈ㄢ€嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈ю煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煉曫煉�


Story&written by
馃嚦馃嚜 ~A茂cha~ and ~Fasma~ 馃嚦馃嚜

_wanan nakune fans kin ZURI'AMU.haussa novel fans 馃槏馃槏馃槏

65-70


Rid ne kwance saman gadonci ba alamar baci a tare dashi se juyi yake yana tunani rayuwarsa,,,wata zuciya tace me mi zai hana ka kara aure 馃,,,dayar zuciyar tace mai a'a bai dace ba saboda wanan yarinya kanwar kace kuma amanace a gurinka, kuma ma kai da yarintarka zaka zab' zama da mace biyu ??? A haka har baci ya kwasheshi.

Anata bagaren Halima yaune zasu gurin ''boka me sunan gobe da nisa''.

suna zuwa kawatra ta labarta mishi abinda ke tafe dasu,,,

ya d'an duba ya buga kasa yana wasu surutai, sai yace dasu bukatar su zata biya anma fa da sharad'i.

Halima kuwa ji da tayi ance bukatarta na malaka Rid zata biya ranta yayi fari tace da bokan wane irin sharad'ine haka ? Ai ni a shirye ma nike da duk wani abunda zaka fadi.

Yace da ita zaki iya kuwa ?

Tace Eh da gudu ma
Seyace da ita sharadin shine "bazaki yarda ki aifu dashi ba ke kadama ki yarda ki dau ciki..inko har kin dauka to kiyi gaggawar zubar dashi ,

Ta danyi jim. kadan se tace inde wanan ne na yarda.

Yabata wasu kullulolin magani da zata sa masa a abinci sukai godiya ta baci 50mil(dubu ishirin) sukayi tafiyarsu, a hanyane kawartata ke cemata anya Halima zaki iya kuwa,

tace ke tafi can banza kawai se kace bake kika dorani a kan hayaba, kuma ko kin manta cewa mu likitocine ? Wanan ba abu me wuya bane ga contaceptions iri iri (tsarin iyali) abun da sauki ma.yanzu so nike ki nema mana yanda za muyi musa masa maganinnan a abinci... Haka sukayi ta hirasu har suka karasa gida.

Yau lundi (litinin) Comme d'habitude Rid (kamar yada ya saba) yazo caf茅t茅ria dan shan tea, kan a hada abashi se wayar sa tayi ringing ya fita,,yana fadin ka bada a kawo min office d'ina

su kuwa su Halima ashe duk akan idonsu akayi se kawai taje tace Rid ya turo a bata zata kai masa office dinshi ba muso ya mika mata, ita ko ce murmushi take dan yau Rid zai shiga hanunta, a hanya ta zuba masa maganin, tana zuwa office d'in ta tarar Baya ciki se ta ajiye masa akan bureau ta fito. Shikuma daga zuwansa bai ma ka akaba kawai seya dauki tea din yasha ya fice dan kiran da aka masa daga clinik ne.

Tin a haya ya fara jin jikinshi ba dad'i (sha yanzu biya yanzu kenan)sosai yake jin kanshi na mishi ciwo Dakyar ya karasa clinik, yace wa Haidar zai koma gidz danbaya jin dadi.
Yana isa gida bai tsaya ko ina ba se dakinshi ya kwanta, nan fa irin tunanin jiya ya dawo maya anma nayau harda fuska Halima da kuma kalamanta yayi ta juyi har ya samu bacci

Washe gari daya fito ko break bai tsaya yiba, abin ya ba Manane mamaki anma seta share tace oho (Anti Fasma kinga sharin mata ko, Manane ina layfinta ???anan ni har Tana bani tausayi 馃様 ).
Y'a shiga gidan Umma dan gaidata fuskan nan tasa babu walwala, bayan ya gaisheta ta amsa

se kuma tace son lafiya kuwa ? Yace mata ba komi "shi kam yana jin kunyar ya gayawa Umma abinda ke damunsa saboda ko ba komi ita ta aifi Manane kuma ga irin kula da take dashi ",,, tadey kara tambayyarshi mi ke daminshi inba haka ba kar ya kara mata magana.

Yayi ji sanan yace Umma ba komi bane illa ina san in kara aure ne 馃様,,,,,,kamar daga sama taji maganar amman se ta dake tace masha Allah, saboda wan ne kake wani damun kanka ai abun murnane saboda shi namji mijin mace hudune, Allah ya sanya alheri ya nuna mana ranar.....yace amin jiki a sanyaye ya fita saboda betaba tsanmanin Umma zatakarb'i abin cikin sauri ba sa. Itama umma karfin haline kawai tayi.

Direct 茅cole ya fuce saboda yau seda marece yakeda patient, yana zuwa ya lalibo numba Halima yace tazo yana san ganinta,a office dinshi aranta taji dadi sosai dan tasan abun nata ya fara aiki.
Tana shiga yace ta zauna bayan ta gaisheshi, ke minene cikkenken sunanki ? Kuma inane gidan ku ?

Cike da yanza Ta amsa masa tambayoyin sa da fara'a, yace ta tashi tatafi,,,tana zuwa ta labartama kawarta yanda sukayi da Rid.

Bayan sallah isha '茂 Halima na daki na chat ummata tace mata tayi bako

Ko, data fito wa zata gani 馃槼,,Rid ne yasha wanka dan directly daga office gida yaje ya canza kaya,, bayan sun gaisa ta tafi dauko masa abin sha, a hanya seda ta kara barbada masa magani.(uhm su Halima ba馃槑....)


Sunsha fira tun 19h (7) se wajejen 21h (9) tukon ya tafiyarsa se walwala,yake hakama ita gimbiya kar kuso kuga murna.


Manane tayi mamaki yau yayan nata bai shigo da wuri ba saboda bai saba yin hakan ba, kuma ga abincin harya fuce.,

A palo ya isko ta tayi bacci ya kwasheta tana zaman jiranshi

dining table, ya nufa ya d'an taba abincin...ya dawo palon ya tadda ta yace ta tashi, taje ta kwanta ya fice yayi tafiyarsa,

itako zuciya tata cike take da tambayoyi anma batace komiba.

Bayan sati da faruwa haka, Manane se kara ganin canji take a gidan nata, dama 茅cole saboda yayan nata ya futa harakatra banda gaisuwa babu abinda ke hadasu, ko girkin ma tayi ba kulum yakeci bale ma na dare a tare da *ZURI'A* kuma 茅cole d'in ma ya fasa kaita a motarta take zuwa ko dreba ya kaita, abun mamaki shine har yansu Manane bata sanarwa kowa abinda ke faruwa. (mutumniya an fara girma kenan 馃槆),,,,Haider na zaune shida Rid a office suna tattanawa akan aiki,bayan sun gama ne Haider yace dan uwana wai yanaga kwana biyu ka canza ?

Rid yayi murmishi yace wly wata baby ce ke faman fasa mini kai,,,, what ! Dit moi que ce n'est pas vrai ? (kaka cemin dagaske kake ?)

Haba kaga alamar wasa a magananan ne ? Lalle dan uwana daga yin aure seka fara magana kara aure, kaji dadin ka mon fr猫re (brother)
Dade ka bari har se Manane ta haufu mana,

yaja tsaki yace ance maka tanada ciki ne ? Har yanzu yarinyace kuma ba irin dri nac茅 ba.
Yace anzu in kana so ka nuna mini kai dan uwanane na jini to ka goya mini baya a kan haraka nan, ina so ka shaida a *ZURI'A* cewa ina so nakara aure.
Haidar ya bushe da dariya 馃槀馃槀馃槀馃槀 yade ce masa D'accord,to ni yaushe za 'a kaini naga amariya ne 馃構'''yace seka shirya.

Haider na zuwa gida ya tarar da Salma bata gida, yakira bata dauka, seya kira Safara ko taje can ? Tace aa,,,,seya je gidan Momy, yana isa ya iske Kalifa a hanun momy yana shan madara,bayan ya gaisheta yace da ita ina Salma,tace masa yaje tana daki bata jin dad'in jikintane,,,,,,

koda ya shiga ya isketa a kwance ya mata ya jiki ta amsa masa da sauki,,,, Haider da tsokana ce cemata yayi kodey kalifa ya kusa samun kanene ? Batade ce tashi komiba dan ita kade tasan mitakeji (Allah baki lafiya Salma).


Shin ya Haider da dan uwansa zasu tinkari *ZURI'A* da zancan auren nan ? Anya zasu amince kuwa ? Kubiyo mu dan jin yanda zata kasance.



Muna neman afuarku na rashin yi tiping kwana biyu馃檹

A茂cha &Fasma
1/28/18, 11:05 AM - Fassouma Zander: 馃挀馃挒馃應馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煈ㄢ€嶐煈р€嶐煈�

*Zuri'ar* *mu*
( *Notre* *Famille* )

馃懆鈥嶐煈┾€嶐煈ю煈ㄢ€嶐煈┾€嶐煈р€嶐煈ю煈┾€嶐煈р€嶐煈︷煉曫煉�


Story&written by
馃嚦馃嚜 ~A茂cha~ and ~Fasma~ 馃嚦馃嚜

*Love you all Fans鉂も潳*

_Dedicated_ _to _Ramatou_

70__75

Ita de salma batace komi dan ita kad'e tasan abunda.take ji nan yayi mata gwajeje ,ya d'auki jininta dan zeyi test a lab(laboratoire)d'in clinik yamata 'bizou sur sa t锚te'( kiss on her head )sannan ya fice ,,haka de yau ta wuni gidan Mom ,......

Ita ko Manane duk abin duniya ya ishe ta dan inta yi girkin ma ba kullum yake ciba duk randa tayi beci ba wani abu yake zuwa ya tsaya mata a wuya kamar tayi kuka a ranta tace dama haka mata keji idan sun dafama mazan su yi wa mazan su girki sannan suk'i ci ?

bayan sun fito break yau se taki koma.wa gida sambaby tace hala yau bazaki koma gida ba?

aa shima yau baze koma ba shiya sa kika ganni nan ,haba kema kinsan daya ya na gida bame zaunar dani nan.
Hhhh masu mijine ...

ee naji de suka.isa cafet suka.saye abinci suka koma classe (su Manane an girma har an iya rike sirrin miji 馃榿)
Se 5 na marece ya dawo da resultat(sakamakon )test kin duk jikin shi yayi sanyi koda ya zo bayan ya gaida Mom yake sanar da ita Salma na ciwon hawon jini ,,

,Mom ta dafe kirji馃槼 hawon jini fa kace ?

Ee wly Mom ta sami ciwon ne tun lokaci da tanada cikin Khalifa to bayan ta haihu nayi mata traitement ta rabu dashi dan dama cikin

Please Login or Register in order to submit comment