Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*ZUMA A BAKI...!*🌹
    {  Painful love Story  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

_Bisimillahir Rahamanir Rahim dukkan yabo da godiya sun tabbata ga sarki buwayi gagara misali Allah mai saman bakwai Allah mai ƙasan bakwai Allah mai rufin asirin bayinshi, Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga shugaba jagaba annabi muhammad s.a.w Amin, Alhamdulillahi ya Allah daka kuma dawo dani acikin wannan sabon littafin bayan na kammala AUREN BARE lafiya Allah yadda na soma lafiya kasa na gama lafiya kai riƙo da hannayena Allahumma Amin_

_My fans yauma gani tafe da sabon littafi mai cike da sabon salo, ina roƙon ubangiji daya baku iko tare da ƙarfin biyoni acikin wannan labarin Amin summa Amin_

_Gargaɗi wannan littafi mai suna a sama labarin ƙirƙirarre ne daga gareni ban yarda a juyamin shi ta kowace sigaba wanda yaga yayi dai dai da tasa rayuwar yayi haƙuri akasi aka samu amman labarin tsararre ne daga wajena_

                        *001*

GARIN KANO
_Ɗorayi Unguwar Bello_

Cikin lokaci ƙalilan na kammala shirina cikin shuɗiyar atamfa mai ratsin ja' ajikinta senai amfani da jan mayafi mai adon stone mai yawa ajikinsa, jakata na ɗauka mai kalar ja itama senai amfani da jan takalmi kasancewar kalar fatar jikina baƙa ce shiyasa wannan jar kalar dana ratsa cikin shigata taimin masifar kyau.

Kallon agogon dake cikin ɗakinmu nayi da sauri na waro idanuna waje har ina ɗan jan numfashi tare da saurin ɗaukar lesson plan ɗina nai gaba har ina haɗawa da ɗan gudu-gudu kaɗan sabida ganin lokaci yana ja kada nai latting zuwa makarantar danake koyarwa.

Abakin ƙofa na tarar da anisa ƙanwata ta uku tana faman waya wadda daga gani da saurayinta takeyi, dan naga se faman kashe idanunta take tana faman ƙasa da murya, tana ganina ta miƙe da sauri har tana ƙoƙarin yarda wayar hannun nata, tana cewa, "YAYA HUMAIRAH' har kin fito kenan?"  ina tafe ina ɗaura agogo a hannuna na ce mata "eh! anisa sena dawo ina Anty take?"   "tana can cikin ɓangaren Baffa ƙarami wajan ganin lefen sadiya, "tom idan ta dawo kice mata na tafi school amma ta duba saman madubinta zan aje mata kuɗin cefane"   "tom anty ALLAH ya kiyaye hanya" aƙasan leɓena na amsa mata da amin sannan na saka kaina nai gaba abina.

Da ƙyar na sami abin hawa zuwa cikin unguwar ciranci domin anan makarantar danake koyarwar take kasancewar tsakanin mu da ɗan tazara kaɗan, gashi makarantar private school ce sam basa yarda da yin latti ko kaɗan dan yanzu kace zaka makara se anemi korarka shiyasa iya yina nike domin  ganin na kare mutuncin kaina wajan mai makarantar dan kada ta cimun mutunci kamar yadda naga tanai wa sauran staff ɗinsu danni kam bata taɓa min ba dan ba makararar nikeyiba.

Duk da haka ban samu shiga da wuriba se wajan ƙarfe taran safiya na ƙarasa, da sauri na zaro naira hamsin cikin jakata na baiwa mai ɗan sahun tare da nufar cikin gate ɗin cike da kuzarin jiki.

Abakin office ɗin da muke singh na tsaya tare da zaro biro daga cikin jakata na nufi cikin office ɗin, da sauri najawo singh book din dake kan teburin na fara yin singhning ɗin sunana, ina kammalawa na ɗago idanuna haɗa idanu mukai da malamar english cikin far,a tace  "a,a yau malama Humairah nake gani da ranar nan haka hala ko lafiya dai?" murmushi na ƙago akan fuskata tare da cewa "wallahi makara nai bara na ƙarasa aji" na faɗa yayin danake mayar da birona na nufi cikin makarantar ɓangaren ajin danake koyar dasu darasin social studies,

Cikin ladabi ɗalibaina ke gaisar dani har na aje jakata akan tebur nan nafara binsu ina duba aikin dana basu na ɗauki kamar minti goma ina faman yin abu guda kafin na kammala na koma wajan zamana tunda tsarin school ɗin na teacher par class ne, cikin haka naga masinger dake aiki a office ɗin shugabar makarantar yazo aguje cikin rawar jiki yake sallama cikin ajin danake.

Ƙarasawa nai gabansa cikin mutuntaka muka gaisa dashi sannan na dubesa tare dace masa "masinja lafiya dai?"   "eh! lafiya daman ranki shi daɗe ce keson ganinki"   "ni kuma?" nafaɗa ina mai nuna kaina da yatsana guda tare da waro idanuna waje asual, "eh kefa malamar primary one koba malama Humairah Yusuf bace?" yafaɗa yana mai kallona, "eh nice jekace ina zuwa" da sauri ya juya nima komawa nai cikin ajin na dauki wayata batare dana dauki jakata ba na nufi cikin office ɗin mai makarantar.

Cikin ladabi muka gaisa da matar wadda waɗansu malaman ke mata kallon marar mutunci amman nikam bandani tunda bata taɓamin ba ko sau ɗaya,  da far,arta da komi ta karɓeni harda cemin ga waje na zauna bayan na zauna ne ta dubeni sannnan tace "malama Humairah ya akai yau kika makara keda bamu saba ganin hakan daga garekiba?"  cikin jin kunya na dubeta tare da cewa "dan ALLAH kiyi haƙuri insha ALLAH hakan baze kuma faruwa ba wallahi yau ɗinma akasi aka samu" murmushi ta ƙago kafin tace shikenan  babu komi tashi kije ALLAH yay maki albarka.

Sannan dan ALLAH idan babu damuwa kizo ranar juma,a ki karɓi addiress ɗin gidana ina son ganinki ranar asabar tunda babu school sabida da akwai maganar danike son yi dake.

"Babu damuwa nagode ALLAH ya nuna mana lokacin"   na faɗa ina mai tashi tsam na fita daga office ɗin.

Harna koma class ina tunanin wannan wani magana ce da shugabar makaranta bazata gayamin ba harse na je gidanta, nifa bana son irin wannan shige-shigen sam duk da kasancewarta matar ƙanin umma matar baffa ƙarami ƙanin mahaifina amman sam har yanzu ban ko taɓa zuwa gidan taba duk da irin faɗan da umma takemin na rashin ziyarar dangi.

Ƙarfe ɗayan rana na mike tare da nufar masallaci salla nai tare dayin addu,a akan lamarina ubangiji ya isar min yay min maganin matsalata wadda take addabar zuciyata.

Ina idarwa na koma class na dauki jakata ganin lokacin tashin yaran yayi sallama nai masu tare da nufar gate  batare dana sha wata wahalaba na samu mai ɗan sahu nai masa kwatancen anguwarmu tare da shiga cikin adai daitan na zauna gaba ɗaya wata mahaukaciyar yunwa nikeji acikina sabida ban ko karya ba na fita duk yadda anty da umma ke min faɗan yunwa amman sam bana ji shiyasa in ulcer ɗina ta motsa min sena dangana da asibiti.

Cikin mintuna goma mai napep ɗin ya kaini ɗorayi kasancewar layinmu da ɗan tazara da titi yasa na soma takawa da ƙafafuna duk jikina agajiye haka nan hannuna ya ƙage sabida nauyin jakar dake hannun nawa.

Tun daga farkon layinmu naga dan dazon matasan layin dama sauran da bana layin ba sunyi zaman jarabar kamar yadda na saka musu sabida yawancin su rashin aikin yine kan sakasu wannan zama domin inda suna da aikin yi da bazasu zauna zaman jarabar saka idanu ba, domin babu abinda ake a wannan majalissar face tsageranci da rashin daraja wasun suma kan ɗan taɓa shaye-shaye a wurin domin nakanji warin hayaƙi na tashi inna zo wucewa.

Sosai na haɗe raina tamau na kame jikina waje ɗaya kaina sunkuye haka nazo gab da su zan gifta araina nake ayyana da ranar Allah amman bazasu huta ba.

Sautin dariya naji daga bayana kafin naji fitar sautin ɗaya daga cikin samarin wajan.

"Waini kam B.smoll wannan ba tagidan su ƙwaro bace?"
Ina jin wanda aka kirawo da b.smool ɗin yace.
"Sosai ma ai yayar ƙwaro ce ƴar gidan yayan babansa ce shegiya mai baƙar fuska se uban girman kai kullum haka zaka ganta kamar ta faɗi, ita bata yarda ba ƴar boko, se tsabar baƙin jini duk ƙannenta sunata ɗagawa amman ita har yau babu wanda ya taya"
Banji abinda ɗayan ke cewa ba na ƙarasa gaban gidanmu.

Dab da zan shiga xauren mu naji hayaniyar su na tashi.
"Se OGA CIKA DAJI"
Haka naji majalissar tasu ta kaure da faɗi wanda sautin muryarsu tayi dai dai da sautin bugun zuciyata...............



SANNU SANNU..................✊

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }


NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*002*


Da gudu na ƙarasa shiga zauren gidan namu sabida yadda numfashina yake ƙoƙarin ɗaukewa.
Cikin sauri na faɗa tsakar gida kamar wadda aka jefa ina shiga nai ɗakinmu tare da banko ƙofar na zauna turus a bakin gado ina mayar da numfashina dake barazanar ɗaukewa hawayen da suka sami zarafin zubo min a yanzu sunake saka hannu ina gogewa.
Cikin dakakkiyar muryarshi mai cike da amo!
Yake doko sallama tsakar gidan namu kafin naji sautin takalman dake nuna min alamun bashi kaɗai yashigo gidan ba.
Cikin murna da farin ciki anty dake cikin ɗakinta take amsa mai sallamar kafin naji muryarta a tsakar gidan tana cewa.
"A,a lale maraba da mai gidana da kishiyata yau kace manyan baƙi gareni ku shigo mana UMAR"
Anty ta faɗa tana mai nufar ɗakinta da sauri domin shin fiɗa musu tabarma.
Jin kalamin anty yasani tashi kamar an mintsi nan na nufi gaban taga ina lekensu domin tsananin tsoro baze barni na leƙasu ba.
Gabana ne yay muguwar faɗuwa sakamakon idanu biyu da mukai da SANYIN IDANIYATA.
Hawaye ne ke ƙara zubomin a saman fuskata kafe islam nai da idanu ina kallonta yarinya mai shekaru biyu a duniya amman inka du beta seka ce ƴar shekaru uku, kafin na mayar su kan aslam ɗan uwanta wanda yake riƙe da hannun babansa dake sunkuye yana tube takalman shi ze shiga ɗakin anty.
Zuciyata ce tai rauni gaba ɗaya komi ya tsayamin cak hatta yunwar dana zo da ita ta gushe bakina ya bushe babu abinda nake muradi kamar in ganni gaban ƴaƴana da Allah ya bani amman kash hakan nasan baze yuwu ba domin na riga nabar kari tun ranar tubani.
Tabbas Nazir ya cuceni ya lasa mini ZUMA A BAKI wadda har abada bazan daina la'antar shiba, ya rabani da farin cikin rayuwata wanda har abada bana zaton zan sami farin ciki in bana tare dasu.
Tabbas na tafka babban kuskure acikin rayuwata UMAR ya lasan ZUMA A BAKI na soyayyarshi Nikuma na mayar masa da tawa ZUMA A BAKI'n ta yaudarar mu ta mata tabbas nasan har abada umar baze manta dani ba har abada umar baze taɓa dawo da soyayyata rayuwar shiba.
Na cuci kaina gashi har wasu mazan na min kallon mai baƙin jini sabida ƙaddarar data faɗawa Aurena.
Tsaye nayi a wurin kamar wadda aka dasa inajin yau koze daken bazan fasa tin kararshi akan ya bani ƴaƴana naji ɗumin suba.
Yafi mintuna goma a ɗakin anty kansa sunkuye a ƙasa yana kallon ledar dake tsakar ɗakin.
"Amman dai zaka bar mana su islam su ɗan kwana biyu kafin ka koma ko?"
Anty ta faɗa mai tana mai ɗora aslam saman cinyarta.
Rintse idanun shi yay yana mai fesar da hucin dake fasowa daga maƙoshin sa sam baya ƙaunar nesa da yaranshi haka nan baya son wata alaƙa da kuma shiga tsakanin shi da Aisha wannan dalilin yasa a kullum yake nesanta kanshi gareta.
Zuwanshi ma nayau ya samo asaline da yadda inna ta uzzira mai akan seya kawosu bada ban hakaba da baya tunanin ze kawo ƴaƴansa gidan anan kusa.
"Umar bakaji nane?"
Anty tai maganar tana kallon shi cike da tausayawa.
Ɗago da jar fuskar shi yay mai kama data turawa sabida yadda Allah yay mashi azabar kyau da jar fata kana ya zuba mata manyan idanunshi waɗanda atake anan launinsu yay mugun sauyawa cije ƙasan laɓɓansa yay tare da cewa.
"Ai suna makaranta amman in akai hutu zan kawo su".
Yafaɗawa anty hakane sabida jin daɗinta amman a ƙasan zuciyar shi bayajin hakan zata faru.
Tashi yayi tsaye tare da zaro damin kuɗi a cikin aljihun wandon jeans ɗinshi ya dire gaban anty.
"Gashi anty a saima yara wani abun ni zan koma agaida su baffa se watarana"
Sunkuyar da kai anty tai kasa tana mai kallon uban kudin dake gabanta.
"Haba Umar wannan kuɗi ai yayi yawa dan Allah ka dauke kana fama da nauyin iyali ai baka bada wannan kuɗi hakaba".
Shi dariyama kalamin nata ya bashi amman seya basar.
Tare da sunkuyawa ya ɗauki aslam daman islam batada yarda shiyasa bata ko nufi inda anty take ba
"Anty mun gudu a gaida sauran".
Yafaɗa yana mai saɓar ƴaƴanshi yabar ɗakin cikin sauri.
Kasa magana anty tai tana bin kudin da kallo lallai arziki nufin Allah humaira ta cuci kanta da tuni itake da wannan daular.
Ganin fitowar su yasani komawa da sauri na ɗauki gyale na rufa akaina nabi bayanshi.
Seda na haɗa da gudu sabida daman can ya umar yana da mugun sauri, koda na fita yama bar kofar gidanmu yana tsaye agaban dandazon matasan ɗazu yana raba musu kuɗi suna fama ihu suna masa godiya.
Ina laɓe yagama musu rabon kuɗin ya nufi kwanar gidansu.
Da sauri na gyara mayafina na nufi inda naga yayi baki ɗaya jikina rawa ike idanuna ko gani basayi.
Koda nazo zan gifta wannan majalissar ta ɗazu senaji wani daga cikinsu yana cewa.
"Kunga ƴar wahala kun san wata kebi haka?"
Ɗiff naji sunyi se sautin saurina dana muryar wannan matashin danaji yana kora musu bayani kamar haka.
"tsohuwar matar CIKA DAJI cefa ta rabu dashi yanzu kuma taga yayi kuɗi take faman binsa kamar zata tashi sama ai ƴar wahala kenan ta ɗorawa kanta girman kai shiyasa tunda ta fito babu mashin shini se faman zaryar koyarwa a ƴar ƙaramar private shiko oga ai yacigaba kuduba fa motar dayake hawa yanzu?"
Dariya suka kwashe da ita banji sauran ba nidai na nufi inda zuciyata take muradin zuwa.
Yana ƙorarin shiga gidan inna domin harya tura madai dai cin gate ɗin gidan nai saurin ɗora ƙafata kan dakalin gidan cikin rawar murya data zuciya na furta.
"Yaya dan Allah ka bani su nima suji ɗumina irin na mahaifiya ka tuna nima ina da haƙƙi akan ƴaƴana nifa na haife su kaiwa girman Allah kabani yarana"
Nafaɗa muryata tana rawa ina kokarin mika hannuna wajan islam domin a yanxu ita nafi mai tar so fiye da komai....



*ACIGABA DA BI WANNAN SALON NASA DABAN YAKE*

*ZUMA A BAKI...!*🌹
    {  Painful love Story  }
           

         NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

                        *003*

Daka tawa yayi da tura gate ɗin dayake ƙoƙarin yi tare da aje aslam a ƙasa sannan ya janyo islam ya turon ita gabana.
Ya kalleni yana sakin murmushin sa na rainin hankali kamar koda yaushe idan nai masa maganar yarana.
Kafin ya mayar da kallonshi gurin islam.
"My love je mama tana son ganinki"
yafaɗawa yarinyar haka dayake ire iren sunayen dayake gayawa yaran nasa kenan.
Wani irin daɗine ya kamani jikina har rawa yake a lokacin danaji furucin nasa gareta.
Amman kafin na ɗago idanuna na dire akanta naji sautin kukan ta! tare dana gudunta tai wurin mahaifinta ta riƙeshi katamau tana kuka!.
Cikin gwarancin su na yara naji tana cewa.
"Daddy! ban canci ba daddy kaini wurin inno".
Ta ƙare faɗin haka tana wani irin kuka wanda nima ya bawa nawa kukan damar fitowa fili.
Cikin rawar jiki na karasa gabanshi ƙwarjinin shi da kamshin turaren shi suka kuma kara gudun zuciyata hannuna na ɗora a bayanta ina kuka ina magana.
"Haba islam nifa na haifeki dan Allah kijuyo na kalleki islam ɗina"
Nafaɗa ina kokarin ƙwaceta daga hannunshi still ita kuma tana kuma ƙamƙame uban nata tana shigewa jikinshi.
Cikin sauri naga ya bude gate ɗin gidan inna ya tura su ciki kana ya rufo sannan ya juyo yana kallona fuskarshi babu sukuni.
"Yanzu maye amfanin sakamin yarinyata kuka da kikai ke hakan kina ganin kin kyauta min kenan?"
Yafaɗa a zuciye har wani mayar da numfashi yake.
Ganin kamar ze doken ne yasa naja baya daga wurin shi.
"Amman dai kaima kasan ina da hakki akan yarana ko? tunda kai baka da imanin da zaka kawon su nito inada ƙafar dazan biyoka koda zaka zaneni naga wata ƙatuwa ma ka bawa su take riƙonsu amman ni uwarsu bazaka bani ba".
Nima nakai maganar a tsananin zuciye.
Murmushi ya saki kamar koda yaushe domin mawuya cin abune kaga Ɓacin ransa a fili yana da danne ɓacin rai sedai tsananin soyawa mutum aya a hannu idan ka shiga gonarshi.
Ɗago ƙwayar idanunshi yayi tare da zubamin dukkan idanun shi yana kallona dasu lokaci ɗaya naga alamun ɓacin rai tattare dashi.
Takowa yake sannu a hankali har zuwa gabana yay min tsaye akaina kamar dogari.
Ya fini tsayi nesa ba kusa ba hakan yasa naɗan ja baya kaɗan ina haɗe jikina wuri ɗaya domin tsananin kusancina dashi yasa nakejin tsohon tsumin daya kwana biyu da lafamin na neman tasowa.
"Dan Allah ki kuma mai maita me kika faɗi? ke yanzu har kina da bakin faɗin abin da kika ce? ko kin manta abin da kikai a baya?"
Murmushi ya kuma yi.
"Gwara da kika gani da idanun ki wallahi Aisha! kona baki yaran nan bazasu barki kiyi bacci ba domin basu sanki ba, kina mahaifiyar tasu amman kika kasa basu hakki irin na uwa! ko kin manta yadda uwa keda hakki akan ɗa haka shima ɗan keda hakki akan uwa?"
Hanky ya fiddo daga aljihun jeans ɗinsa ya goge zufa sannan ya cigaba da cewa.
"Allah sarki babarsu in kinada ƙarfi kizo ki amshe su, kuma matar da kike cewa na bata su, ai ta fimin ke sau dubu ɗari tunda ita matata ce ta sunnah keko fa kokin manta kalamin ki gareni?"
Yafaɗa yana kallona.
"Umar na tsaneka bana ƙaunar ka ka sakeni nagaji da zama dakai ka kwashe gayyar tsiyarka ka tafi dasu bana bukata"
Ya mai maita maganar yana jefamin fitinannan kallo.
"Laifi ne danna kwashe ƴaƴana! yaran da basu cika wata uku ba kika yaye su yaran da madara ce tai musu madadi da nonon uwa mai ƙara lafiya ajiki, basu da kowa seni kamar yadda nima bani da kowa sesu nine uwar su nine ubansu ninaci kashi da fitsarin su keki faɗi ɗaya daga cikin abinda kikai musu na jin ƙai a matsayinki na uwa.......haihuwa kaɗai kika sani shima cikin da kikai barazanar zubarwa bada ban Allah ya duba wahalar danai wajan samar dashi ba da tabbas yajima da faɗuwa a rariya sabida wata banzar son zuciyarki shasha kawai mai baƙar zuciyata data fuska har abada hakkina dana yarana baze barki ki kwanta lafiya ba".
Ya ƙarasa maganar cikin ɓacin rai.
"Wallahi Aisha bada ban karamcin mahaifanki ba da har abada bazaki kuma ganin yaran nan ba wallahi! da sena nesan taki dasu nisa na har abada, sedai kash niɗin cikakken ɗan halak ne wanda baya mayar da alkairi zuwa sharri tabbas mahaifan ki sunmin halaccin daya zama dole nima na kamanta, amman fa ki sani Aisha na tsaneki tsana mafi muni har abada bazan taɓa sonki ba kuma kada ki saka ran zan kuma sauraranki kamar iwar haka sabida ayyukan dake gabana sun fimin ke mahimman ci acikin rayuwata"
Yafaɗa yana mai fir fitomin da manyan idanun shi waje kana yaja ƙafafunshi da ƙarfi yabar ni a wurin ban kumajin duriyar shiba se karar turo gate ɗinshi kurum.
"Innalillahi wa'innah ilaihirraju'
Kalmar danake ta faman mai maitawa kena da ƙarfi kuma a bayyane.
Ƙarfin ambaton kalmar ne ya bani damar jan ƙafafuna da sukai min nauyi nabar kofar gidan kamar mahaukaciya haka na faɗa cikin gidanmu da kallo Anty ta bini tana min magana amman ban kulata ba har seda na dangana da ɗakinmu na kife kaina a gefen gado ina risgar kuka kamar wadda aka cemin yau baba ko anty wani ya rasu.
Cikin haka naji alamun shigowarta zama tai a gefena tana mai kallona.
"Wato ke humairah haka rayuwarki zata ƙare a kuka? kullum na fuskanci in Umar yazo sekin shiga wannan hali, toki bude kunnen ki da kyau kijini inma banzan tunani kike akan umar to kidaina sabida ayanzu ya miki nisa yakamata ki kauda hankalin ki gareshi ki fuskanci abinda yake gabanki"
Anty mahaifiyata ta faɗi hakan fuskarta babu sukuni.
Wani ƙululun abu ne yazo ya tokaran kirjina hannuna na saka na dafe wurin ina mai kallonta.
"Anty ni a yanzu nafi bukatar ya bani ƴaƴana ba wai soyayyar shiba tayaya anty kina kallo gani amman yaje yay aure ya bata su"
Nafaɗa ina sakin marayan kuka!
Sakin baki anty tai tana kallona gaba ɗaya tagama cika da mamaki.
"A,a to shi dutse ne daze zauna haka? tunda keda kika haifa kin nuna bakya so se Allah ya kawo mai sonsu, maganar gaskiya inma kishin umar kedamun ki kima daina sabida ayanzu yay miki nisan da bazaki taɓa samun shiba"
Kuka na saka a wannan karon mai karfi wanda yasa anty tai saurin fita tabarmin ɗakin.
"Na shiga uku! ni humaira mai ke shirin faruwa dani? kodai na faɗa soyayyar tsohon mijina ne wanda nasan yaymin nisan da har abada bazan kamo shiba"
Koma wa nai saman gadon daɓar na kwanta ina risgar kuka!
Tsananin tunanin abinda ya shuɗe a baya ya fara dawomin daki-daki kamar haka.

*ASALIN LABARIN PAGE 4 INSHA ALLAH*
*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }


NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*004*

Asalin labarin.

Sunana Aisha amman a gidanmu ana cemin (Humairah) nice ƴata biyu a wurin mahaifina malam yusuf wanda muke kira da (baba) da kuma mahaifiyata khadija da muke kira (anty).
Yaya imran shine babban ɗa a wurin mahaifinmu da mahaifiyar mu kuma muna da tazarar shekaru sosai a tsakaninmu

Please Login or Register in order to submit comment