Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na ze aureni.
Wannan kalamin nata yasa na burkice na susuce kamar wadda aka sammace sam aka kasa gane kaina ko nono na daina bawa islam ko ance na bata sena saka kuka hakan tasa yake siyo madara ana bata domin nonon senaga dama.
Haka nai arba'in na koma gidansa cikin wannan matsalar da anty bata gayawa baba ba haka ta mayar da hankali tana min addu'a.
Banfi wata guda da komawa ba mukaje tofa dangin anty tunda muka dawo na tattare islam nake mikata wajan inna intai kuka akawota na bata nono kaɗan na bata madara.
Watana uku da komawa daman sun gama school akai posting ɗinsa katsina service da taimakon baban nuratu ya sami arewa.
Shikuma ya imran taraba.
Haka muka tarkata mukai can domin inna tace tunda gidane mutafi tare, a wajan tsoho kakansa da iyatu muka sauka ɗaki guda aka bamu wanda aka saka katifa da labule se ƴan kayan tarkace,sosai tsofin suke nunan gata muna waya da sakina inna sami network islam nada wata uku da kwana goma ya kara ribata ta da ƙyar ya sami kaina muka lula.
Wanda nan ma abu kamar wasa banfi wata guda ba na soma ciwo zazzabi ciwon kai kamar zan mutu haka muka ɗauki hanyar asibiti gwajin farko nan ma aka ce inada ciki na wata ɗaya zokuga tashin hankali wanda seda nai barazanar zubar mai da cikin haka naita zuba masa rashin kirki kala kala batare dayace min komi ba.
Koda su iyatu sukaji sosai sukai farin ciki haka jego ya zaman biyu gana shayarwar islam domin sunce baza,a yayetaba gana rainon ciki wanda daman banawa islam komi shiyake mata, bani da matsalar komi a yanzu seta ganin na zubar da cikin jikina da kuma kashe aurena na fita nazir ya auren wanda hakan yasa na ɗagawa kaina hankali na rame na fige shikuma baya da lokaci sosai sabida fita aikin daya ke da kuma rainon yarsa damma kakar tana kama mai wanda zuwa lokacin ƴar bata yarda dani sosai se ubanta.
Kwanci tashi babu wuya wajan ubangiji yanxu cikina ya tsufa sosai shima kuma ya kusa gama abinda ya kaishi haka yasa kullum tsoho zemin rubutu ya bani nasha wanda ikon Allah koda nakudar ma tazo ban jigata kamar ta farkoba.
Haka na haifi ɗana shima mai kama da babansa wanda ranar suna yaci suna Muhammadu, sunan baban ya umar kenan wanda ake cemai (aslam) babu wanda yazo daga kano sedai nuratu datazo daga cikin garin,katsina, wadda taita ɗaukar yaran tana musu hotuna, sosai tai musu sayayya ta bam mamaki ni daman ban shiga sabgarta ba, haka lamarin namu ya kasance raino ya zaman biyu konace ya zame mai domun shike wa islam komi shikuma aslam iyatu tai mai haka nan rainon su ya koma kanshi shida iyatu wadda ta dau son duniya ta ɗorawa aslam nikuwa daman basa gabana sema tsanar yaran data ubansu danakeji araina.
Shekararmu biyu a katsina domin seda ya kammala komi nasa harma muka ɗora watanni sannan muka dawo kano lokacin islam nada shekaru biyu ba watanni domin tana tafiya kuma tana magana wadda da daddy ta budi baki aslam yana tsaiwa sosai yaran suka shiga ran kowa domin tsabar kyansu da wayonsu hakan yasa wasu ma kece masu ƴan biyu.
Lokacin ya umar bayada sukunin zama sabida baban nuratu yana yawan kiransa a waya yana turashi wajan wani ɗan siyasa a nan cikin kano wanda ya kasance aminin sa akan ya sama masa aikin gwamnati domin takardunsa sunyi kyau baida matsala.
Wajan wata ɗaya yana faman cuku-cuku domin har abuja yaje yay sati kafin a kirasu domin duba suna cikin amincin Allah sunan *Umar muhammad sarkin gida ya fito a jerin sunayen da federal government ta ɗauka a ma'aikata na aikin ƴan sanda sedai shi yana ɓangaren sashin bincikene na fararen kaya( DSS POLICE ) wanda zasuna bincikar masu manyan laifuka ( criminal case )*
Sosai nai masa murna daya dawo yake gayan.
"Daman ya umar abinda ka karanta kenan shiyasa senai maka laifi kaimin shuru, kokuma innai abu nace ma banyi ba seka karyatani"
Dariya yay min.
"Aisha wannan aikin na jima da burin yinshi domin bawa ƙasata taimako sedai na ɓoye nemansa ne sabida aikine mai haɗari, naso mun sami aiki tare da imran to Allah baiba domin ba sashin karatunmu guda ba, kuma ni kinga baban nuratune ya sama min to abin alfarma kaima ka samu da ƙyar yasa ban zaƙe da yawa ba".
Awannan karon shuru nai mai sabida banson mu shirya.
Sosai su baba dasu inna sukai mai addu'a akan aikin nashi kafin ranar litinin ta farkon wata ya tafi training wanda seda yay sati biyu sannan suka dawo yazo yay sati biyu gida kana posting letter nasu ya fita inda ya sami aiki a garin Abuja.
Lokacin da muketa shirin tafiya abuja lokacin sakina tazomin da daddare mukai hirarmu daga nan tace min zata tafi.
Tashi nai na rakata amai makon naga ta tafi senaga tanata jana da hira akan tana missing ɗina zanyi nisa da ita, hasken motane ya haskemu a kofar gidan inna kafin naga nazir ya fito daga motar cikin sarsarfa ya karaso gareni yana kuka.
Kokarin riko hannuna yake na doke ina ja da baya.
"Nazir ni matar aure ce akull ɗinka"na faɗa da karfin gaske amman nazir yaki daina kokarin kamoni harseda ya rikoni yana kokarin rungumeni Ya umar ya doso gidan.
Cak numfashina ya dauke na waiga banga nazir ba kuma banga sakina ba se lafiyayyun marukan danaji a kuncina suna sauka.
Gabas yamma kudu arewa babu su se ya umar dake faman huci akaina idanunshi na zubar ƙwalla.
Jana yay mukai cikin gida ya watsani a ɗaki, ya rufo kofar.
"Daman abinda kike nufi kenan dani? shiyasa kika ƙi ƴaƴanki kika ƙini sabida wancan ɗan iskan da aurena akanki kike kula wani ƙato? yafaɗa yana shakoni, wallahi humaira nai nadamar haɗa zuri'a dake kuma kije na sakeki saki ɗaya!!! Hakkina dana yarana baze taɓa barinki zaman lafiyaba kije xaki fahimci wake sonki tsakani da Allah humaira kincu ceni!!"
Ya faɗa yana zubewa a wurin yana kuka
Bana fahimtar komi haka na ɗauki mayafi na nai gidanmu.
Gurfane nake gaban baba ina kuka anty tana zagina sosai mahaifana suka nuna bani da gaskiya washe gari koda baba ya kirashi ce mai yay baya nan domin ashe tunda asubahi ya hade kayansa dana yaransa sukai tasha yana kuka haka ya isa garin abuja.


*Tashin hankali muje zuwa*...........
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*25 & 26*


Koda ya sauka a garin na abuja bai da sani akan yana yin garin dan haka seda yasha wahala kafin ya sami dai dai tuwar komi, gidan da aka bashi a matsayin ya zauna a ƙarƙashin kulawar ma'aikatarsu ya nufa wanda ya kasance flate, mai ɗakuna guda uku se kicin da bayi tare da babban falo komi yana tsare tamkar da ɗan adam aciki kasancewar gidajan daman anyi sune domin ma'aikata gyara komi yay kamar mace sannan ya ɗora ruwa yaywa su islam wanka jikin aslam da zafin zazzaɓi ga kuka dayake mai haka ya haɗa mai madara a pida ya basa sabida sabon dayay da madarar yasa ba musu ya amsa yasha.
Indomie ya dafa musu shida islam sukaci seda yay sallah ya nitsu sannan ya kunna wayarshi saƙonni ne burjik ciki duka sharesu yay tare da kiran inna sosai ta rufeshi da faɗa akan dole seya dawo da humaira ɗakinta sabida butulci dan yasami aiki ze sakaeta sannan ya ɗebe mata yara dan zalunci harda mai shan mama, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba harta gama bai ce mata komi ba haka ya bata hakuri ya katse wayar batare daya amsa ze dawo da itan ba sannan kuma bai gayawa innar ai nihin abinda ya rabasu ba domin yana ganin taci darajar ƴaƴanta baya son wani abu marar daɗi ya gifta a tsakaninsu wanda ze ɓata sunanta yasa danginsa suna ganin baƙinta kodan darajar abinda ta haifa.
Tundaga lokacin ya daina doguwar magana da inna a waya sedai ya kirata su gaisa data ɗauko mai maganar humaira ze katse.
Daga ɓangaren aikinsa kuwa ya mayar da hankali sosai yake fita aikin wanda baya dawowa se wajan shidan yamma.
Abinda ze baka tausayi shine yadda Umar ya koma kamar macen gida shizewa yaran wanka ya wanke musu kashi ya saka musu kaya ya basu abinci seya tabbatar dasunci sun ƙoshi yake fita aiki, ya kullosu agida da karfe biyu ze ɗauki excuse yazo ya ga lafiyarsu ya kuma basu abinci sannan ya koma rayuwa yake marar daɗi bayada farin cikin daya wuce na ƴaƴansa domin yana ganin sune sanyin idanunsa yana da mahaifiya amman baya sha,awar bawa inna su sabida gudun kada humaira tazo ta ɗaukar maisu wannan dalilin yasa ya bawa yaran nasa dukkan wata kulawarsa da lokacinsa wanda yaran suka buɗi idanu dashi suka mayar shi uwa uba agaresu abinda ze baka mamaki yadda basa kuka inya fita daya dawo zasu tawo suna ɓangale mai dadashi suna dariya.
Haka yacigaba da kula da yaran nasa tsayin watanni ya saba da wannan rayuwa ga kuɗi sun fara zauna mai sedai yana kokarin turawa da imran wanda ze bawa su inna da baba domin hidimar gida shikam koda wasa baya tunanin komawa kano a yanzu duk da yasan yanzu ma tai idda babu maganar kome amman kanon ta fitar mai arai duk yadda inna take masa faɗa akan yazo yaƙi tun tana mai faɗa harta zo tana mashi nasiha amman yana ce mata akwai ayyuka agabansa nawani case ne shiyasa baze zo nan kusaba.
Lokacin daya cika watanni shida agarin na abuja,Inka dubi Umar da yaransa bazaka ce su bane sabida kwanciyar hankalin data bayyana a jikinsu sunyi kyau kamar larabawa sun murje haka nan yaran sunyi ƙiba sosai sun kara haske kamar su dashi sun kuma bayyana, shi kuwa ya kara cika ya ƙara xama babban mutum ya kara haske ga wani uban ƙasumba mai lafiya databi fuskarsa ta kwanta luf sabida sauyin yanayi da suttura da cima tare da kwanciyar hankali.
Sedai a yanzu ya koyi wani hali na rashin magana ya koyi zafin rai haka nan ya koyi wani irin miskilanci baka ganin dariyarsa inba gaban yaransa ba haka nan baka ganin maganarsa se yanawa islam wasa wadda yanzu tai wayo ta kara girma kamar ba ƴar shekaru biyu da watanni ba.
Koda wasa basu san sunada uwa ba haka nan basa da magana seta daddy ko inno dayake bata waya suna gaisawa.
Ranar daya fita wani case ya jima bai shigoba lokacin daya dawo gida ya tarar islam tana kuka aslam ma haka sabida sun daɗe basuga ya shigoba haka ya haɗesu yana mai zubda hawaye ya rungumesu yana basu hakuri a washe gari ya samo musu wata dattijuwa wadda ke zuwa da safe ta tafi da yamma haka rayuwar ta kasance ga Umar sam maganar mace bata gabansa bare yay tunanin aure nan kusa sabida gashin da humaira tai mai tabbas ta lasa mai ZUMA A BAKI na yaudara da halin wasu matan.
Ataƙaice Umar yau gashi ya share watanni harya tafi shekara guda a garin abuja inda cikin lokacin ya samawa su islam makaranta wadda inya kaisu 7:00am baze ɗauko suba se 6:00pm hakan yafiye mai sauki domin mai haɗe da tahfiz ce dan haka seya sallami nannyn tasu.
Yaran sun taso kamar tagwaye sabida sunyi saurin girman jiki irin na mahaifinsu haka nan bakinsu ya buɗe musamman islam shi aslam baida cikakkiyar lafiya sosai kamar yana da limonia ne ajikinsa shiyasa bini bini yake kaishi asibiti domin a duba mai lafiyarsa.
Haka rayuwar ta kasance mai cikin farin ciki da kuma bakin ciki,suna waya da nuratu wadda take matukar son yaran nasa kamar ta mayarsu cikinta sedai ko kaɗan kalmar so bata haɗasuba sedai tsantsar zumunci dayake wanzuwa a tsakaninsu.
Yau tunda ya tashi daga office ya biya ta banki yay wani uzuri sannan ya nufi hanyar gida, titin daya biyo babu kosa se ɗai ɗaikun motoci, horn yake dannawa wata budurwa dake tsaye ƙyam a saman ƙwalta sedai kamar yanayi da dutse agarin ya taka burki ne ya bugeta nan da nan ta faɗi wanwar a titin kamar gawa, cikin kiɗima ya fita ya daukota ya sakata a gidan baya dayake yana kusa da gidansa yasa ya wuce da ita nan, cikin rawar jikin son tai makon rai, ya fito da ita zuwa falonshi ya dauko ruwa a frij ya zuba mata ajikinta mayar da ajiyar zuciya tai tare da mikewa da sauri tana rintse idanunta.
Kafin ta dire akansa tana jan wawiyar ajiyar zuciya.
Zuba mata dara daran idanun shi yay masu rikita marar gaskiya fuskarshi babu sukuni, rabin hankalinsa kuma nakan yaransa dake school.
"Ina ke miki ciwo?"
Lumshe idanu tai cikin muradin soyayyarsa tace.
"Babu komi se zuciyata".
Lumshe idanunsa yay ya kauda kansa ga yanayin kallonta gareshi tare da tashi ya zube hannayensa a bocket ɗinsa yabar mata falon.
Sakina dira tai saman kujera tana mai cewa.
"My first target is successefully Alhamdulillahi"
Kana ta koma ta kwanta haka yazo ya wuceta ya nufi mota yaje ya zo da yaransa.
Da gudu ta miƙe tayi kan islam ta ɗagata tana "my dear your well come back ga new mommyn ki kina sona?" abin mamaki washe baki islam tai tana dariya haka ta kwashi yaran tai ɗaki dasu wanka tai musu ta fito ta basu abinci.
Tuni sukai sabo a wunin ranar domin yaran sunada son mutane.
Koda dare yay ita tai musu dinner dayace tazo ta wuce tunda ta warke kuka tasamai akan ita yar kano ce aka satota nan bata san kowa ba sosai kalaminta suka fusgi ranshi yace ze kaita tasha washe gari nan ma kuka tasamai akan bazata kai kanta gida ba sanin yadda garin namu yake yasa yace mata ta zauna na two weeks a gidan nasa inyaso kafin nan sesu wuce tare.
Godiya tai mai tare da kama yaran tai ɗaki dasu sedai ya ƙeƙashe ya hanata kwana dasu haka ya kwashe yaran ya nufi nasa ɗakin dasu ita kuma ya barta a extra room guda.
Haka zaman sakina ya wanxu a gidan umar itake komi sedai baya cin abincinta amman yana jin dadin yadda take kula da ƴaƴansa wanda nan da nan yaji yana ganin kimarta kamewarta yasa yaji ya gamsu da tarbiyarta domin ko kaɗan bata rabarsa da sunan iskanci.
Wannan kwanakin datai yasa su islam kece mata,Mommy daga sun dawo a school suke nufar wajanta ahaka sukai kwanakin suka gama ya loda musu siyayya sukai kano anan unguwar chiranchi gidansu yake, sallama yasa akai da mahaifiyarta domin mahaifinta ya rasu kuka babarta ta saka akan ita dai tundaga makaranta bataga sakina ba ashe saceta akai babu inda basu duba ba wannan yasa suketa addu'a har aka ganta godiya tai mai sukai sallama sedai me?
Fafur su islam sunƙi tafiya su se antafi da mommy sakina na kuka yaran na kuka haka ya tusasu sukai gidan inna akan ze kawosu su gaisa.
Sosai inna tai murna da zuwan ɗan nata kwanansa ɗaya da zuwa gidan yasa aka fashe shi aka ƙawata shi ya koma na zamani harda su fanti sabo, kayan abinci ya siyo aka raba gida biyu aka kai gidan baba sauran innah.
Kwanansa uku yay katsina koda wasa bai tunkari gidansu humaira ba seda ya xaga dangi sosai sannan ya dawo gida.
Lokacin inna ta kafa mai masifar seya kai musu yaran sun gani amman fafur yaki haka ya kaiwa sakina su daya tashi dawowa suka zo gidan inna tare inna bata san sakina kawar humaira bace haka nan shima maryam ma bata san sakina ba sosai inna ta yaba da hankalin sakina.
Dan haka sukaita hirarsu data tashi tafiya ya rakata hanya shi ko kaɗan baya sonta sedai ƙaunar yaransa data nuna yasa yaji ta shiga ransa ( mai ɗa wawa ) yana ganin uwar data haifesu ma ta yar dasu amman ita ta nuna tana so abinda yafi baƙanta ransa yadda yaga humaira koda wasa batazo domin ganin yaranta ba wannan abin ya ɓata ransa ya ƙara jin muguwar tsanarta.
Dan haka koda ya dawo inna tace mai to ya dace ya fidda mata ko a dangi ko anan sabida xaman waje ɗaya babu mata akwai illah.
Hangen wadda zata kula mai da yara yake nuratu ƴar boko ce haka nan bayajin ma ze iya auranta sabida yaga batada lokacin kanta sena aiki da karatu yaushe ma tai lokacinsa bare na yaransa tunaninsa ya tsaya akan sakina wadda taci darajar ƴaƴansa.
Shawara sukai da inna wanda babu bata lokaci manya suka shiga maganar bayan dogon binciken da akai babansu humaira da baffa ne suka kai kudin aure aka saka biki sati biyu sabida yace baya bukatar komi tare zasu wuce inze koma.
Zokuga farin ciki wajan sakina sosai take shirin bikin a wannan lokacin xata nuna true colour ɗinta domin batajin xatai mai bautar ƴaƴan maƙiyarta daman dasu ta kama ƙafa wajansa domin iya bincikenta ya nuna bazata samu aurensa ba harse ta kama ƙafa da ƴaƴansa wanda ba kowane yay mata wannan yaƙin ba face masoyinta saurayinta NAZIR wanda ta lasa mai ZUMA A BAKI na zata bashi kanta matukar ya farauto mata soyayyar UMAR ( hmmmmmm )
Wannan ƙwaɗayin yasa nazir ya shiga ya fita domin ganin ya mallaka mata umar sabida shibaya sonta da aure zumarta kaɗai yake da muradi wadda tai mai alkawarin bashi ita duk da kasancewar ta ba mazinaciya ba.
Da wannan damar suka haɗa plan dashi har takai ta sami yadda tai ta haɗu da humaira takuma haɗata da nazir a matsayin yayanta haka nan koda wasa sakina bata yarda takai humaira gidansu ba kullum tace mata zata zo setace ai gidan surukaine ashe ita da gadar zaren datake haɗa mata( wannan baya bukatar dogon shari domin abinda yake faruwa ne a wajan alumma cin amana yaudara da zamba cikin aminci, yakamata muna zaƙulosu cikin litattafanmu domin mufaɗakar da al'ummah ).
Haka nan naxir shiya kaita abuja har ya san yadda yay ya haɗata da titin da umar kebi don xuwa gidansa bayan yasha wuya kafin kammala binciken komi.
Haka lokacin bikin yazo ranar da akai ɗaurin aure da daddare ana gobe xasu bar kano nazir yazo kofar gidansu koda ya kirata a waya setace mai.
"Nazir idan abunsha ya ƙare shin mai za'ai da kwalba?
"Ban gane ba?"
Yace.
Tace
"Ina nufin naci biredi na yada leda daman na ɗaukane domin kaimin aiki to kagaman karkai tunanin zan iya bawa wani namiji jikina inba Ƙatona ba domin shine da alhakin cin gun! ina fatan ka fahimta dan haka seka kwashe ƙazaman ƙafafunka kabarmin kofar gidanmu domin daga kai har Humairah kidahuma nagama da babinku sabida na sami muradina dukkanku ZUMA A BAKI na lasa muku amman ai nihin ZAƘIN yana wajan Umar".
Ƙitt!!!
Ta katse wayar tama cire sim card ɗin baki ɗaya.
Dariya nazir yay irinta gogaggun ƴan barikin cikin sabon gari kana yace.
"ZUMA A BAKI"!
yay dariyar ƙeta.
Sannan ya shiga motar yabar ƙofar gidan nasu.
Haka sakina ta wanxu cikin nishaɗin cikar burinta washe gari suka wuce abuja da yayarta daman su biyune daga ita se hadiza yarta se babarsu, dan haka hadixan ita ta rakata abuja bayan ta kwana ɗaya ta juyo, shima umar a ranar da hadiza ta komo kano shikuma a ranar ya nufi abujan cikin ɗaukin so ta tare sosai ta nuna masa kulawa haka nan koda dare yay tai matukar nuna masa soyayya sedai bai kai first night ɗinsa da humaira ba sedai kuma ya sameta a cikakkar mace.
Zamansu suke son barka sabida daman shi ɗaya yazo abujan su islam suna kano wajan inna se an komo hutu ze ɗaukosu dan haka suka sake shida sakina basa aikin komi gida se romancing sabida yana matukar son romance.
Hankalinsa ya kwanta tuni yama mance da wata damuwar humaira acikin rayuwarsa.
********
Nikuwa daman gaba ɗaya na koma wata iri bani da wani tunani a yanzu sena ƴaƴana su anty duk sun fita daga sabgata nasara mema zanyi cikin haka na kammala idda ta dan haka umma ta roki matar kaninta akan ta saman aiki a makarantar datake a matsayin shugaba wadda ta kasance private da taimakon umma na soma fita ina koyar da ƴan aji ɗaya da kwalina na secondry inda ake biyana dubu bakwai.
Alokacin nutsuwa ta kuma shigata cikin wannan lokacin naji labarin ya umar yay aure kuma yama zo har ya tafi bai zo gidanmu ba ƴaƴana ma dana gansu ƙin yarda sukai dani haka naci kukana babu mai lallashina wayata na dauka na kira layin sakina sedai akashe na nazir ma haka jefa wayar nai a matsai na saka kuka ina mai cewa inama nasan gidansu sakina danaje ta bani shawara.
Tsayin kwanaki gashi na tafi shekara an saka bikin ya imran da maryam kanwar ya umar haka nan an saka bikin nafisa mai bina, a wannan lokacin na rame na fige su islam na gidan inna hutu amman kunyar inna ya hana naje na gansu domin ni a tunanina ya gaya mata yadda muka zauna.
Seda ana ya gobe zasu tafi nasai omo da sabulai anisa ta rakani gidan a saka makon takuramin da anty tai akan naje na gansu a karo na biyu.
Tunda na doso layin jikina ke rawa sanye yake da bakar t.shirt se bakin wando yay wani haske ya karo kyau matasan layin zaune gefensa suna masa fadanci yana raba musu kudi gidan inna an gyareshi har wani gate aka saka domin rabona da gidan tun daya saken anisa ce ta gaishe sa nikuwa wucewa nai na shiga gidan inna maryam tana zaune tanawa islam wanka shiga nai muka gaisa da inna sannan na fito wajan islam sabida kukanta ya dauki hankalina kusan a tare muka isa gareta nidashi ajiyar zuciya na sauke ina mai kallon maryam.
"Maryam meke damun Aisha?"
Nafaɗa ina kallon yadda ƴar keta kuka!
"Wallahi anty humairah wanka ne bata so"
Kokarin kai hannuna nake jikinta yay saurin ɗauke ƴarsa ya makawa maryam harara tabar wajan.
A kokarina na kuma kamo islam saukar mari naji a kuncina.
"Kada ki kuma saka wannan jakin hannun naki ajikin ƴata banza marar zuciya uban me ya kawoki gidanmu wallahi nakuma ganin wannan ramammiyar fuskar taki sena la'antaki".
Yafaɗa yana mai tofan miyau a saman fuskata yaja yarsa suka bar wajan.
A tsakar wajan na zube nama kasa kuka dan takaicin tozarcin dayamin a wannan kadamin bana hango so se dunbin ƙi gareni.
Haka anisa tazo tajani mukai gida dan tsabar bala'i har zazzaɓi nai ranar tundaga wannan lokacin ban kuma saka ƴaƴana a idanuna ba haka zalika inyazo baya zuwa inda muke sedai aikensa haka zalika matarsa ma bamu taɓa ganinta ba kwanaki ma tai ɓari amman batazo nan ba kuma a gidan inna tai jinyar, haka lamarin nawa yay ta tafiya har zuwa wannan lokacin dayau ya kawosu gidanmu wanda shine zuwansa na biyu tin bayan rabuwarmu.
Wannan shine tarihinmu dafatan makaranta labarina zasu fahimta.
*DAWOWA LABARI*
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*27 & 28*


Nisawa nai bayan na gama tunanin tarihin abinda ya shuɗe a shekara ɗaya da rabin data gabata.
Share hawayena nai idanuna jajir na fito daga ɗakinmu, bakin rijiya naje na ɗauro alwala nazo na tayar da sallar magariba,bayan na idar na zauna nan ma tunanin bayan iddata na faɗa.
Wanda babu kalar ƙalubalan da ban ganiba, har wankau seda nai sabida baba yayi rantsuwa a lokacin akan baze ciyar dani ba tunda na kaso aurena haka nake xama nai wankau nai gogau na sami kuɗin abinci haka al'amura sukaita faruwa wanda har akai bikin nafisa mai bina tare da ya imran daya auri maryam duk ina cikin wannan ƙuncin rayuwa seda ayiya kakata tazo da kanta taiwa baba faɗa sannan ya janye ƙudirinsa lokacinne umma taiwa matar ƙaninta magana aka saman koyarwa nan wadda ake biyana dubu bakwai a duk wata.
Da kuɗin nake taimakon anty nake taimakon ƙannena,nima naɗan sai wani abun.
Haka al'amura suka cigaba da wanzuwa a tsakanina da mahaifana wanda seda aka kai ruwa rana kafin baba ya soma amsar gaisuwata.
Gaba ɗaya ni yanzu wannan rayuwar ta fita akaina bani da bazzawari bare na sami mai ɗeben kewa ga shi ban san gidansu sakina ba.
Na jefa wayata masai bare muyi waya da ita haka na nisa a tunanin

Please Login or Register in order to submit comment