Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wajansa batare danaji tsoro ko fargaba ba.
Kama hannunshi nai kokarin yi amman seya doke nawa hannun yana cigaba damin dariya.
"Wallahi kaine garin yaya kazama haka zomu tafi gida nasan su baba basu san yadda ka koma ba ina su islam ɗin?"
Nafaɗa da ɗan saurina alokacin gaba ɗaya hankalina ya gama fita daga jikina mijina uban ƴaƴana nagansa cikin wannan yanayi ai dole na shiga damuwa duk da bama tare amman dai ai darajar haihuwa ba wasa ba.
Gaba ɗaya duk wani tsoro ya fitarmin araina tunkarar sa nai ina kuka ina jan hannunshi shikuma yana doke nawa hannun yana min dariya.
Amman cikin ransa sosai yay mamakin yadda humaira tai masa ganin xata fara tara mai jama'a yasa ya soma kokarin fusgewa daga rikon datai masa domin ya nufi masaukinsa.
Nikuwa ganin hakan yasa na daddage na kurma ihun neman taimakon jama'a da mugun ƙarfina.
"Wayyo Allah jama'a na shiga uku kuzo ku taimaken baban ƴaƴana ne wallahi shine ze gudu kuma karna je yay wani wajan"
Nafaɗa ina mai daka uban tsalle na janyoshi jikina na rungume ƙugunsa tsamm ina kuka!.
Wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare kuma da lafewa ajikinta batare daya bari ta fuskanci hakaba tsohon tsumin mayatar tane yake bijiro masa haka xalika wata haɗaɗɗiyar ƙwallace mai yawa ta soma karakaini acikin kurmin idanunsa, tabbas ayanzu ta sami wani mahalli mai kyau acikin rayuwarsa wace macen ce xata ganka a haka ta tsaya dakai har ta haɗa jikinta da naka? ada yana mata kallon maƙiyarsa amman wannan kaɗai ta saka ta wanke dukkan wani tabo na cikin rayuwarsa, Ganin kukan nata na ƙaruwa jama'a sun soma isowa wajansu wanda bai shirya bayyana kansa a gareta a hakanba, yasa ya zameta da ƙarfi ya tureta daga jikin nasa sa'annan kuma ya arta aguje yabar wajan.
Cikin zafin nama nima na take mai baya ina kiran"Dan Allah jama'ar annabi ku taimakeni kada ya tseremin wallahi baban ƴaƴana ne wayyo na shiga uku ya Umar Ya umar" haka na shiga nana tawa.
Amman ina tuni ya tserewa ganina yama kulen na daina ganinsa ko kaɗan.
Wata irin faɗuwa nai a wajan ina birgima ina kuka! wanda nafi awa awajan ina yinsa kafin na mike jikina yay futu futu da ƙasa na nufi hanyar gida hankalina a tsananin tashe....


Ajiyar zuciya yaja mai ƙarfi bayan ya tabbata daya mata nisan da bazata gansaba, Seda yaje ma ɓoyar kayansa ya ɗauka ya shirya kansa tsaff sannan ya kama hanyar masaukin nasa jikinsa gaba ɗaya a matukar mace.
Dakin daya kama ya yada xango bayan ya bude xama yay dabas a kasan carpet ya dafe saman kansa sautin kukanta yana amsa amo! acikin dodon kunnensa rintse idanunsa yay da karfi yana jin kansa na barazanar sarewa ya faɗi batare daya shirya ba.
Da sauri ya mike ya nufi bathroom ɗinsa a haka ya sakarma kansa ruwa batare daya tube kayan jikinsa ba.
Ya jiƙe jagab da ruwa haka ya tube kayan ya zubar cikin washing machine ya fito shirya kansa yay tare da ɗaukar wayarsa da system ɗinsa ya fita falo, zama yay ya mike kafafunsa a saman sopa ya ɗora system ɗin da agogon dake hannunsa wanda ya cire tun a lokacin daxe shiga wanka bayanan cigaban da aka samu ya soma turawa ya jima yana aikinsa kafin yakashe kayan nasa ya nufi toilet ya dauro alwala ya ɗauki abin sallah ya data sallar magariba.
*******
Kamar mahaukaciya na nufi bakin titi ina tafe ina haɗe hanya, har Allah ya haɗani da ɗan sahu, hawanta nai tare da kifa kaina ina cigaba da kukana.
"Hajiya ina muka nufa?"
Naji muryar mai ɗan sahun cikin kunnuwa na.
"Ɗorayi".
Nabasa amsa cikin kuka! har muka karasa unguwarmu ina kukana seda yacemin mun karaso sannan na ɗago kaina gabana ne ya faɗi tunawar danai ashe da maganin da jakar duka na watsar dasu garin gudun ɗazu.
Dabur cewa nai bayan na sauko ina faman kame kame ina raba idanuna na rashin makama.
"Kinga nasan abunda ke damunki, kije gida Allah ya kyauta kibar kudin kawai"
Ajiyar zuciya na saukar mai karfi tare da yimai godiya sannan na kama hanyar gidan inna kai tsaye.
Tundaga bakin kofar gidan nake faman ƙwalla mata kira.
Kafin na karasa a hargitse na kutsa kaina cikin gidan batare da nayi sallama ba.
"Innah! innah!! nafaɗa a furgice cike da ɗimuwa ta karaso gabana tana mai cewa.
"Humaira lafiyarki daga ina kike haka naga kayanki duk ƙasa?".
Ban bata amsa ba illah gaban frij ɗinta dake tsakar gidan dana nufa na bude ruwan faro na ɗauko babbar roba seda na bude sannan na kafa kaina a cikinsa na shanye shi tass sabida bushewar da maƙoshina yayi sannan na yarda jarkar duk tana tsaye tana kallona babu ko ƙiftawa.
Fashe mata da kuka nai ina mai ɗora kaina saman ƙafaɗunta.
"Wallahi inna shina gani kizo muje na nuna miki shi wallahi shine".
Nafaɗa ina kuma cigaba da kukana.
"Waye shikuma humaira?".
Tafaɗa itama agigice.
"Ya umar innah nagani kamar baya hayyacinsa da kayan datti amman wallahi shine innah duk da nagansa a tsananin hauka nai iya yina domin ganin na kamosa ya gujemin innah kixo muje wajansa kar a sabauta miki rayuwar ɗanki domin a yanzu dani dake da ƴaƴansa mukafi mahimmanci agaresa".
Naƙarasa ina mai fashe mata da kuka!
Ajiyar zuciya ta mayar tunawa da bayanin umar dayay mata akan ya shigo kano kan wani case amman baya son ma kowa yasan da zuwan nasa.
Cikin tsanaki ta jawoni jikinta sannan tai hanyar ɗakinta dani se lokacin na karewa ɗakin inna kallo ashe haka aka narka dukiya cikinsa.
Akan wata haɗaɗɗiyar royal chair ta zaunar dani sannan ta nufi ɗakin gadonta wayarta ta ɗauko tazo gabana ta zauna daga gefena.
Layinsa ta shiga kira amman harta katse ba'a ɗauka ba, sedaga baya wayar tata tashiga ringing! handsfree ta daɗo tare dayin sallama a nutse.
Ajiyar zuciya na sauke jin dakakkiyar muryarshi acikin wayar yana gaisar da inna sannan yana mai bata hakuri akan yana sallah ne yasa bai ɗauki kiran nataba.
"Humairah ce gata zaune tazomin da maganar ta ganka awani hali, dafatan dai kana cikin koshin lafiya ko?".
Ajiyar zuciya ya sauke wadda najita har ɓargona kafin naji yace mata.
"Lafiya kalau inna kinganni ma sallah na idar,amman wace humairan?"
Haɗe rai inna tai kafin ta soma masa faɗa.
"ta gidan ubanka ja'iri kawai dan ubanka yarinya taganka cikin wani hali tazomin agigice sannan kanemi ɓaɗa mata yaji cikin idanunta, to humaira matarka uwar ƴaƴanka in baka ganeta ba ai zaka shaida islam ko?"
Dariya ya saki yana mai cewa.
"Haba innata mayar da wuƙar seki cemin ƴarkice ta ganni, to kice mata bani bane ba tama daina wahalar da kanta".
Wata irin kunya ce ta kamani nan da nan naji na muzanta da wannan yarfin dayay min.
Amman kafin nai yunkurin furta wata kalma naji muryar inna nacewa
"Ai waƙa abakin mai ita tafi daɗi marar mutunci gata ai seka gaya mata da kanka ni sallah zanyi"
Tafaɗa mai tana mai mikon wayar saman cinyata.
Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji acikin dukkan ilahirin jikina lokacin danaji sautin............



*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_



*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼

*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*

_Nemi wannan numbern 08142105218 duk ɗaya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba ɗaya xaki biya naira 1000 ɗaya ne_
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *43 & 44*

Amon! muryarshi acikin dodon kunnena yana cewa.
"Tsananin soyayyar tawace ta saka nake miki gizo? to inma mafarki kike seki maza ki farka domin niɗin nan nai miki nisa yarinya".
Yaƙarasa faɗin maganar yana feson iskar bakinsa ta cikin wayar.
Wani malolon takaicine ya zomin wuyana nai matuƙar nadamar jin furucin nasa agareni.
"Hellow! nasan kina jina shuru kikai, to da kika cewa inna kinganni a wajan by pass ke uban mi yakai ki wajan? nasan dai nan ba arean mu bane ba, nidai dan ALLAH ki rufawa ƴaƴana asiri kada ki soma kule kule domin nasan halin jarabarki ba lallai ki iya riƙe kanki ba ko wancan lokacin keki ke ribata na".
Yafaɗa dawani irin salo na rainin hankali kafin ya katse wayar ƙitt! yabarni a dashe.
Tsanin tashin hankali zulumi fargaba da tarin nadama sune suka saka numfashina fitar wucin gadi.
Wani irin kukane mai karfi ya tawomin cikin azama na saka hannuna na toshe bakina kafin na kumajin wayar tai ringing.
Ban ɗauka ba kuma bani da niyyar ɗagawa illah kukan dana cigaba dayi na tarin nadamar mai ma ya kaini wajan shiga hurumin da yanzu nasan ba nawa bane.
Umar dariya ya kece da ita yasan tana can tana kuka domin Allah ya bata arhar hawaye, cikin mugunta ya kuma kiran wayar domin ya kuma hargitsa ta a karo na biyu.
Nikuwa hararar wayarma nake ina cigaba da kukana.
"Humaira ɗaga wayar nan lazumi nake".
Najiyo muryar innah daga cikin ɗakin gadonta.
Babu yadda zanyi, inyi mata musu dalilin hakan yasa na ɗauki wayar na kara a kunnena batare dana tanka masa ba.
"Nasan kina jina kuka kikeyi sabida nace nai miki nisa ko? Aisha mai matata tai miki kika mareta tsabar bakin ciki da hassada ne na ta aure miki tsohon mijinki yasa kika ɗaga samudawan baƙaƙen hannayenki masu kama dana mai walda kika zuba mata a fararen larabawan kumatunta, ko? to wallahi kinci bashi domin ki tara karonmu dake bazeyi daɗi ba.
Da sauri na miƙe tsam na fita waje takalmina na zira a ƙafata, nama fice agidan gaba ɗaya wayar tana kare a kunnena nayi hakanne domin kada innah taji raina a tsananin ɓace nace masa.
"Dakata ya umar! na buga masa tsawa.
"Dafarko maganar da kake akaina ta wai karnai kule kule sabida yaranka, shin ka manta magajiyar gidan karuwai ka aura ne karewar kule kule , sanin kankane yaya tarbiyar gidanmu take kasan hakan baya cikin tsarina".
Na numfasa sannan na ɗora...........
"maganar matarka kuma dakai da ita duka bakwa gabana bana ta taku domin witsiyar rakumi tai nisa da ƙasa har abada nai maka nisan da bazaka taɓa.kamoni ba, kuma bana fatan ma na kara wata rayuwa dakai, abu nagaba ko a ɗazu darajar ƴaƴana kaci dahar na nuna damuwata akanka nayi hakanne sabida makomar yarana amman ba dan kai ba kuma ka saka ka aje aranka ba'a sauyawa tuwo suna har abada ƙiyayyar nan danake maka bazan dainata ba haka zalika ni aurena ma ya kusa sabida haka se anjima".
Bai bari na katse wayar ba naji sautin masifarsa kamar ze faso wayar ya fito dan jaraba.
"Aisha dan ubanki ni sa'ankine? Aisha kijirani nazo nai miki rashin mutunci ni xaki duba ki faɗawa maganar banxa data wofi?".
Mamakine ya kamani to mai ya jawo abun xagi anan?
"A,a magana kaifa aka baka amsa nikam kadaina zagarmin ubana in kai baka ganin darajar sa naya haifa ya baka itama ta haifa ta barmaka toni nasan ciwonsa ya isheka haka malam ya isa kuma kaxoɗin in kacika kai ɗan........."
Baibarni nakaiba ya kuma katseni.
"Humairah zagina xakiyi nace zakigana xakiyi sabida kina taƙama da mai mata da ƴaƴa takwas yazo ya tayaki sabida fa tsabar bakin jininki tunda kike xawarci ba uban daya tayaki hakanan zaki hakuri naxo ki koma ɗakinki kiyi rainon ƴaƴanki dana kishiyarki domin bana hango alkairi ga wannan dattijon daya fito miki".
Takaici mamaki zulumi fargaba sune suka dirarmin a zuciyata.
"Ya umar waya gaya maka wanda zan aura?".
Nafaɗa cikin tuhuma.
"Hmm wayace miki komi naki ba,a tafin hannuna yake ba shima ɗin dayaya aka cusa miki shi? to albishirinki babama hango bakin jinin da zakiyi yay shiyasa ya laƙabamin ke a wancan lokacin".
Yafaɗa yana kunshe dariyarsa sabida jin sautin kukanta dayay a fili.
"Wallahi Allah Seya sakamin dik abinda kake aikatawa akaina kaida Allah, aikin banza  inba tsabar saka idanu da bakin ciki ba maye bama tare ma seka bi diddigina tokaje baza,a koma gidan nakanba kuma ƴaƴan ma bana so kaje ta rikesu wallahi ko a hanya na gansu bazan kula suba kuma kaima ko a hanya ka ganni kada ka nuna ma kasanni ko gidanmu kada ka kuma takowa tunda ba gidanku bane".
Awannan karon yakasa saita dariyarsa seda ya dara sosai lallai ƙuruci dangin hauka ƴaƴa biyu amman har yau bata sauyaba ashe da kwanto tai masa halin nan na nan.
"Hmm gidanku tun kafin kisan zakizo duniya nike rayuwa acikinsa haka zalika ko a yau nacewa baba zaki koma tofa ze kara bani sabida ba mai iyawa da cin abincinki ai seni ɗin,kuma ni ba bin diddiginki nike ba sedai ko kece kebin nawa marar kunya kawai, kuma nasan bazaki taba kallona a hanya kiƙi kulani ba tunda kika iya rungumar mahaukaci mai kama dani nasan ko iya nan aka tsaya da wasan wallahi nayi miki illah".
Kitt ya kuma katse kiransa yabarni da takaici.

*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_



*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼

*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*

_Nemi wannan numbern 08142105218 duk ɗaya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba ɗaya xaki biya naira 1000 ɗaya ne_
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *45 & 46*


Da ɗumbin takaicin baƙaƙen kalamansa gareni na koma gida idanuna jajir naci kuka nagodewa Allah domin ya umar yau ya cuceni kuma ya gama dani.
Da anty naci karo tana ɗiban ruwa a rijiya da kallo ta bini tana nazarina nikuwa sallama kawai nai na faɗa ɗaki tare da zama a saman gado ina cigaba da kukana ga wayar innah a hannuna.
Seda nai kusan mintuna biyar a zaune sannan anty ta shigo ɗakin namu.
"Humaira"!
Naji muryarta acikin dodon kunnena.
"Na'am Anti".
Nafaɗa cikin kukan takaicin danake yi.
"Ina kika tsaya tun la'asar daga asibitin ina kika nufa yanaga kina kuka sannan banga jakarki ba?".
Gabana ne yafaɗi sabida narasa amsar dazan bata,haka na cigaba da kukana yin duniya anty tai dani naƙi magana daga karshema masifa takamamin data gaji sannan ta ɗora da cewar bari baba ya dawo.
Tana fita na mike tsaye naje nayo alwala na dawo ɗakinmu sallah nai ina idarwa na kira anisa akan ta mikawa innah wayarta.
Ana sallar isha'i na haye saman gado na kwanta sabida ban shirya amsa tambayar baba gareni ba.
Seda na kwanta sannan ƙafata tace bata san zancen ba haka tasakani agaba da zafi ina kuka ina jamai Allah ya isa da kyar bacci yay awon gaba dani.
Koda asubahi ma dakyar nai sallar asubahi ina idarwa na koma gado sanin ranar week end ne yasa nasha malamin baccina raina fess.
Wajan karfe goman safiya na tashi raina a ɓace haka zalika idanuna sunyi ja tare da kumburi, yunƙurawa nai tare da fita tsakar gida seda na ɗora ruwan wanka sannan naje ɗakin anty muka gaisa.
Daga nan nai ɗakin umma cikin ɓangarenta, alokacin ne umma ta tareni da farin cikinta akan cewar wannan bawan Allahn yacewa shugabar makaranta dan Allah yau ze xo wajena sabida nan da next week zebar kasar.
Tsananin jin kunyar umma yasa na amince mata atake kuwa ta kira mai makaranta a waya wato matar kaninta ta sanar mata da, amincewata sannan mukai sallama na fito waje.
Gaban murhun dana ɗowa ruwan ɗumin naje domin na duba koyay zafi
Koda na duba ruwan yayi ɗumi saukewa nai na zuba a bokitin wanka na faɗa banɗaki se lokacin na lura ashe al'adata ce take zuwa a yau ɗin sabida yadda naji ɓacin rai mai tsanani atun tashina a baccin yau.
Sosai na gyara jikina sannan nai wanka na fito abina, kicin naje na haɗa ruwan shayi marar suga haka zalika ban saka madara ba, na nufi ɗakin anty ina kurba sabida yadda yake warwaremin hanjina.
"Humaira zauna nan daman jiranki nake bawai rabuwa nai dake ba".
Zama nai kaina aƙasa ina mai kurɓar shayin dake hannuna.
"Humaira jiya ina kika tsaya sannan kuma ina jakarki?".
Ƙasa nai da kaina bazan taɓa gaya mata abin kunyar danai ba.
"Anti suna gidan inna".
na faɗa kaina tsaye.
Da mamaki saman fuskarta naji tace min.
"Mai ya kaiki gidan innah bayan nasan tunda kika rabu da umar baki sake kai mata ziyara ba?".
Gumi naji ya soma ketomin abinka da rashin sabo da karya, da ƙyar na ƙaƙalo wata akaro na biyu nace mata.
"Inna yadda yatsana kemin zafi wallahi na ɗauka mutuwa zanyi shiyasa dana dawo daga wajan likitan danaga can yafimin kusa na sauka wallahi nama jima agidan don harta kiramin su islam muka gaisa,To kukan da islam takeyi ne akaina yasa na manto jakar na tawo ina kuka"
Nafaɗa ina mai neman gafarar ubangijina abisa karyar danai a yanzun.
Murmushi anty tai sannan ta dubeni.
"Babu wani nan kedai kawai kice kin biya tacan domin kiji muryar yaranki, wato humaira wannan tunanin yaran ne yake hanaki cin abinci kwana biyu? mai yasa bazaki fawwalawa ALLAH komai ba?".
Ajiyar zuciya na mayar tajin daɗi sabida ada danaji tace ba waninan wallahi na ɗauka ƙaryatani zatai amman danaji tai wannan furucin senaji matukar dadi araina.
"Anty nifa ba dansu naje ba, wallahi anty da gaske nake".
Nafaɗa cikin shagwaɓa
Dariya anti tai tana tsokana akan naki daurewa da rashin ƴaƴana musamman a yanzu dana san kawata ke auren babansu.
Azuciyata nake cewa lallai anti bazaki gane yadda kishi yake ba tunda baba bai taɓa miki kishiya ba amman wallahi abin nan ya taɓani duk da bama tare daya umar amman bani ba masoyina ma nasan seya jimin takaicin wannan cin amana.
Amman a fili murmushi nai mata kana na soma rattaba mata bayanin zuwan wannan bawan Allah'n.
"To Allah ya zaɓa miki mafi alkairi amman inata addu'a akan Allah ya bayyana gaskiya ki koma ɗakinki sabida ina tausayin ki ashekarunki ace kinyi aure biyu kin soma raba ƴaƴa".
Ƙwallah ce ta tarar min a kurmin idanuna batare dana bari ta ganiba na goge na ƙaƙalo murmushin yake ina mai amsa mata da "amin".
Tashi nai na nufi ɗakinmu.
To wunin ranar nayisa ne cikin kasala da faɗuwar gaba, kuka kam nayisa kamar babu gobe sabida jikina yana bani kila in wannan mutumin yazo tofa aurena yazo sabida xan amince masane kawai ya auren domin na nisanta kaina da Umar.
Karfe biyar da rabin yamma yazo lokacin ina cin abincin rana, Umma ce ta aiko sadiya ɗiyarta akan shugabar makaranta tai mata waya cewar yana waje.
Hijabi na ɗauka dogo fari tass na ɗora akan doguwar rigar dake jikina naɗan fesa turare kaɗan sannan na fita seda naje wajan anty na gaya mata sannan na fita kofar gida gabana na faɗuwa.
Babban mutum mai kimanin shekaru arba'in da biyar nagani tsaye ajikin wata farar honda a kofar gidanmu.
Cikin nutsuwa na karasa gabansa sabida ya haifeni ba yaro bane har kasa na tsugunna na gaisar dashi.
Cikin farin ciki yacemin.
"Tashi tashi ƴammata barka da yamma my beby"
Gabana ne ya faɗi wata kunya ta kamani na mike naɗan raɓe daga gefenshi.
"Beby babu wajan zama ne?".
Yafaɗa yana washen bakinsa dayaci goro domin gaya nan jajir.
Batare danai masa magana ba na wuce gida sallaya na ɗauko mai na shinfiɗa masa a kofar gidanmu saman dakalinmu naje na gaya masa yazo muka zauna akai.
Bayan mun kuma gaisawa nan ya soma min bayanin kansa a taƙaice.
"Da farko sunana Alhaji sa'eed ni haiffffan garin kano ne kuma ni ɗan uwan hadiza ne, yarana takwas matata ɗaya dalilin ƙarin aurena shine matata bata kula dani".
Da sauri na ɗago sabida mamakin jin kalaminsa.
Ɗagen gira yay.
"Yes bata san tattalin miji ba haka zalika kome na kawo mata bata godemin se rainuwa wannan dalilin yasa a yanzu na sauwake wa kaina da wahalarta komi nawa nake direshi a ɗakina inci abinda raina keso,Haka zalika ga rashin kunya kala kala, hakan yasa nake kulleta a ɗaki nai mata ɗan banzan duka daga baya kuma ta bullomin da rashin bani hakkin kwanciyar aure shima sena daureta da igiya na haye kanta nai bidirina hankalina kwance wannan dalilin yasa nakeson na kara aure na huta".
Gumine naji yana ketomin kota ina.
Seda na yarfe sannan nace mai.
"Amman tayaya kuna zaman haka har ka kai war haka da ita batare daka mata illah ba?"
Murmushi yayi.
"Ada batamin kowani hali wallahi seda ta shiga wata makarantar matan aure tofa daga nan ta haɗu da ƙawaye na grp suka soma ɗorata a hanya, abinda ze baki mamaki yawancinsu matan manyan masu kudine wannan dalilin yasa suke gasa a junansu har hakan ta kawo tana min korafin ita kaza da kaxa yay mata kaɗan da sauransu atakaice dai yanzu komi nai mata bata gani sabida hangen na sama da ita,iya hakuri ina hakuri da ita bazan iya sakinta ba sabida darajar haihuwa amman aure zanyi domin na sami nutsuwa, kullum cikin tsurfar anko waya kaza da kaza ta fito na sai mata take".
Ajiyar zuciya nakai mai karfi kafin naji ya cigaba.
"Daga karshe ma inna kawo mata kayan abinci setaki yin girkin wai ita baxataci kalar abinci kaza ba se kaza ke danaga abin ze daman kawai sena kulle store ɗina, na soma dire mata ƴar awo inta ga dama tayi in bata ga dama ba ta barshi ai cikinta ne nikam ina zuwa da take away ɗina daga wje naci na koshi, sabida ita naga nasiha da bada baki baya mata se an haɗata da masifa".
Wani tsoron Allah ne ya kamani daman haka mazan suke? ahaka nake fatan nai wani auren? dama haka ya umar yay hakuri dani? tabbas ba namijin daze dauki abinda naiwa ya umar koda kuwa waye, duk da zugar da sakina kemin amman nima nasan kaina ban kyautawa ya umar ba ashe haka yayta hakuri dani har haihuwa biyu, da auren sakina da jarabawar dana shiga bayan rabuwa ta da umar wallahi kaf isharace gareni haka zalika darasi ALLLAH ya nuna mini.
"Beby bakya jina?".
Naji muryarsa a kunnena.
Firgigit! na juyo na sauke ajiyar zuciya sannan nace mai.
"Amman nikam inda zaka ɗauki shawarata auren dazaka daɗa wallahi baze kawo maka gyaraba face illah da haɗari sabida daga lokacin daka fara kokarin kara aure to wallahi kawayen matarka zasu soma zugata akan tabi malamai daga nan sekaga wata barnar ta afku amman addu'a da nasiha sune zasu kawo muku gyara a tsakaninku haka nan abincin da kakeci kai ɗaya a ɗaki ka hanasu wallahi rashin adalci........".
Dannowar hancin wata shegiyar mota layinmune ya hanani ƙarasa maganar tawa.




*ZUMA A BAKI* _Is not for free book domin neman ƙarin bayani seki tuntubi wannan numbern 08142105218_



*Albishirin ku masu son karanta ƙayatattun labaran soyayya masu narkar da zuciya gami da ilimantarwa da faɗakarwa to gada ma ta samu ki nemi waɗannan zafafan littatan waɗanda aka baje soyayya mai tsayawa a zuƙatan makaranta cikinsu*👇🏼

*AUREN BARE*
*H A S K E*
*KOBA SO*
*DA IZZATA*
*ƊAN MAJALISSA*

_Nemi wannan numbern 08142105218 duk ɗaya akan farashin naira 300 ne amman idan siya zaki gaba ɗaya xaki biya naira 1000 ɗaya ne_

*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *47 & 48*

Dakatawa motar tai adai dai saitinmu domin tayar motar ma ta kusan takamin ƙafafuna da sauri najanye ƙafafun nawa na ɗagesu nai saman dakalin dasu ina mai kallon baƙar motar dataji uban baƙaƙen glass waɗanda ba,a ganin na cikinta, tsabar yadda motar ke sheƙi yasa ina kallon hoton fuskata ajikinta.
Tajima a tsaye batare dana cikinta ya fitoba haka nan ba,a kasheta ba, gaba ɗayanmu nida Alhaji daka tawa mukai tare da zubawa motar idanu muna kallon wanda ze fito daga cikinta musamman ni danakejin bada ban alhajiba da wallahi senaje na buga mai glass ɗin koda ɗan gidan ubanwaye domin rainin hankalin yakai ya komo ai.
Kamar daga sama naji anbude murfin motar da ƙarfi, gabana ne yay wata iriyar faɗuwa wanda yasa jinin dake zuwarmin na al'ada ya kuma zubomin aguje kamar an koroshi.
Sanye yake cikin wata ɗanyar gezner kalar sky blue anyi masa ɗinkin halp jamfa,babu hula a saman kansa se uban baƙin glass ɗin daya kafta a saman fuskarshi baƙin takalmi sau ciki ya saka aƙafafunsa, Ganin yana tunkaro inda mukene yasa nasha jinin jikina babu abinda ilahirin jikina yake face mazari yana kaɗawa da ƙarfi da

Please Login or Register in order to submit comment