Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake jin kaina dasu suka bayyana gare shi.
Cikin wata razananniyar tsawa ya kira sunana na mike da sauri ina kare jikina.
Kallona yake da jajayen idanunshi wadanda suka cika da zallar fitina.
"A'isha kin dauka wani abun, zan maki? Aisha kin ɗauka jikinki nike so bake ba in dai da wannan abun dakike ɓoyewa nike sonki da daga yau bazan kuma kallonki ba sabida basa gabana kuma basu kai minzalin da zasu burgeni ba".
Yafaɗi hakan a wahalace kafin ya wurgomin hijabina tare da komawa saman katifar yay ruf da ciki yana fitar da wani irin zazzafan nishi.
Dawani irin sauri na ɗauki hijabina jikina yana rawa seda na saka ajikina sannan na dube sa.
"Allah ya isa ɗan iska mai kallon nonon mata kaje se Allah ya sakamin kuma bazan taɓa sonka ba har abada".
Nafaɗa ina fita a guje da maryam kanwarshi naci karo a ƙofar gida ban kulata ba duk uban kiran datake min haka naja kafata se gidanmu.
Allah ya taimaken anty bata tsakar gida da alamun tana ɓangaren ummah mayar da ajiyar zuciya nai lokacin dana faɗa saman gadon ƙarfenta.
Ina rintse idanuna, jikina yana cigaba da rawa wani abu naji kamar dutse ajikinshi aɗazun daya rungumeni, ina ayyana minene hakan, bani da masaniya ammanfa idanun yaya umar ya ɗagamin hankalina.
Muryar anty naji akaina tana min magana.
"Wato humairah aiken dana yi miki daman bakije ba a gida kika zauna abunki ko?".
Dirowa nai daga saman gadon.
"Wallahi anty naje wai ya umar ne baya da lafiya shine innah bata nan".
Ruɗewa naga anty tayi tana faman sakin salati tare da jimanta abin kafin naga tayi tsakar gida tana kiran ya imran.
Wani sanyi naji araina jin anty bazata min faɗan ƙin amso mata kubewar da banyi ba.
Nidai daga nan baccine ya kamani ban farkaba se wurin la'asar tsakar gida na fito idanuna sunyi jajur da alamun bacci.
Jin gidan shuru ya bani tabbacin ko an kawo nepa ne suna ɗakin umma suna kallo alwala nayi tare da komawa nai sallah, kana na fito tsakar gida kicin naje na ɗauko abincina na zauna ina ci.
Sallamar su nafisa kanwata yasa na dakata tare da amsa musu.
"Kufa daga ina kuke haka naga ƙafafun ku bututu?"
Zama nafisa tai anisa ma haka sadiya kuwa bakin randa taje ta ɗebo ruwa suka sha.
"Yaya humairah wai ke baki san tun ɗazu babu kowa agidan nan ba?"
Firfito da idanuna nai waje alamun mamaki.
"ina kuka je?"
Na tambaye su.
Sadiya wadda ita taimin wannan tambayar a ɗazu itace tace min.
"Muna gidan innah fa daga nan kuma asibiti mukaje da ƙafa asibitin murtala ankai ya umar ɗazu bakinshi yanata kumfa baya da lafiya inna se kuka! take harda ya imran dasu anty duka suna can muma shine muka bi bayansu".
Sadiya takai maganar tana share hawayenta.
Amai makon na damu sema masifar dana hau yi mata.
"Dalla malama matsa ki bani wuri, dan ubanki akan wancan ɗan iskan kike wannan hawayen ni ina ruwana yama mutu karewa suke da asara bani ba".
Tsit tsakar gidan namu ya ɗauka suka tsiramin idanu suna kallona.
Cikin nutsuwa nafisa mai bina ta dubeni.
"Yaya humaira ya kike abu kamar marar imani? ya umar kobai ce yana sonki ba ai ɗan uwanki ne musulmi wallahi yaya ina tausayin ranar da zaki wayi gari kiji kaf duniya baki da wanda kike so kamar shi ina tsoron ranar da zaki wayi gari kiga ya umar yayi miki nisan da bazaki tarar dashi ba".
Ƙwaɓe mata baki nai ina hucin masifa.
"To ina ruwana waya ga miki ni yana gabana?"
Murmushin takaicin halina tai.
"Amman mai yasa ada kike sonshi mai yasa ada kike kuka! in baki ganshi ba kada fa ki manta ya umar shike biya miki kudin makaranta shike ɗinka miki suttura duk wata seya baki kuɗin kashewa mai yasa kike amsa alhalin kinsan bakya sonshi?".
Tashi nai nabar masu wurin ina mamakin kaifin hankalin nafisa duk da lokacin tana da ƙarancin shekaru.
Watsi nai da maganar ta tare da fito da uniform ɗina na makaranta domin na wanke su tunda yau alhamis, ban tarar dasu a tsakar gidan ba sabida haka ruwa na ɗiba na kaɗa omo ina yin wankina cikin farin ciki tare da rashin damuwa.
Sallamar sakina ƙawata dake ciranci ita ta tsayar dani daga wankin.
Tsame hannuna nai ina mai amsa mata sallamar tata.
Bakina a washe domin nasan sakina ba zuwan banza tai ba.
Sanin anty bata nan ba mai takurani yasa nai saurin kammala wankin tare da taimakon da sakina ta bani ta hanyar tayani shanya.
Zama mukai a tsakar gida saman tabar ma.
"Ƙawata tare fa da yaya muke amman shi yace baze shigo,layinku ba yana daga bakin titi a mota".
Dayake babansu sakina yana da hali yasa suke fantamawar su.
Murmushi nayi ina mai ce mata.
"Kai haba amman kun shammace ni, da yawa ga anty bata nan kada na fita waɗan nan munafu kan su faɗi in yaya ya dawo".
Shuru tai min alamun ranta ya ɓaci sannan ta dube ni.
"Humairah kodai kin soma son ƙato ne? naga bakya farin ciki da zuwan ɗan uwana bayan kinsan yadda ya kashe ayyukan dake shagon abban mu ya tawo wurinki".
Nisawa nai ban ce mata komi ba sabida sakina ƴar hayaniya ce shiyasa yawanci in muka ɗan sami saɓani bana tanka mata.
Seda tai shuru sannan nace mata.
"Yaya Umar ba lafiya shine su anty suka tafi wajansa".
Da sauri ta matsoni tare da dafa gwiwata.
"Haba da yaushe? meya samesa kuma?"
Tafaɗa da sauri
Ture hannunta nai ina mai jan tsaki.
"Dallah gafara can naga kin wani damu ni ina ma na sani amman dai yana can asibitin murtala su anty ma duka suna can".
Sosa kanta tai tana ƴar dariya kaɗan.
"Okey Allah ya basa lafiya".
Sekuma ta mike.
"Tunda dai yayana baya da ƙimar da zaki fito ni zan tafi".
Jikina yana rawa na mike nabi bayanta hijabi na ɗauka akan igiya muka fita zuwa wajan Nazir
***************
Shiko Umar lokacin daya rungume humairah kawai dauriya yay irin ta maza amman wata irin ɗaurewa mararshi ke mai, yana jin kamar numfashin sa ze bar gangar jikinshi.
Da sauri ya saketa sabida yana jin inya tsaya tare da ita komai na iya faruwa a tsakanin su.
Bayan ta fita kuwa dire ƙafafunshi yay a saman katifa yay rufda ciki sabida yadda yakejin kamar ransa ze bar jikinshi
Jikinshi babu abinda yake face rawa numfashin sa yana fisga da sauri da sauri kamar xe shiɗe.
Laɓɓansa na ƙasa ya kamo yana tsotsa kamar ze ciresu hannun shi yakai ƙasan marar shi yana shafowa tamkar zebar duniya yakejin kanshi tabbas a yanxu yagama karantar lamarin shi babu abin da yake bukata kamar mace atare dashi.
Sedai kuma rashin wadata da baya da ita daze aure sabida nauyin mahaifiyar shi dana kanwar shi gakuma karatun shi dayake kokarin shiga ajin karshe a jami'a, gakuma tsagoron ƙiyayyar da humaira ke masa wadda baya tunanin zata bashi haɗin kan daze riƙeta a matsayin matar rufin asiri.
Cikin haka bakin shi ya soma fitar da farin miyau mai yauƙi idanun shi sukai sama alolacin inna da maryam suka shigo ganin halin dayake ciki yasa suka fasa ihun daya janyo makota wanda da taimakon sune dana ya imran daya shigo gidan aka ɗaga shi aka sami napep akai asibitin murtala dashi da ƙyar aka sami gado a emergency ward, aka kwantar dashi nursers suka ɗaura mai ruwa da allura lokacin da su anty sukaji maganar ko abinci basu ciba suka bi inna asibitin bayan sun aika hafiza ta sanar da baba dake wajan kayan miyarshi wanda shima se nuhu ya bari a wajan ya tafi asibitin cikin ɗimuwa sosai su anty suke bawa inna baki da ƙyar tai shuru ita gani take ɗanta mutuwa ze shima kamar yadda mahaifin shi yatafi yabarta.
Zuwan likitan gabansu yasa inna ta tsagaita da kukan jin likitan yaywa baba magana akan ya same shi a office...............

*Littafin naira 300, Ne gamasu amfani da banki zasu tura ta nan 0078174806 starling bank sesu turo shaidar biyansu ta nan 08142105218, Marasa banki kuma zasu ɗauki hoton katin waya na MTN na naira 400, su turomin ta nan 08142105218*


*Masu son AUREN BARE*
Book 1
Book 2
Complt document.
Naira 500.
Ta nan.0078174806 starling bank shaidar biya,08142105218,
Masu son littattafaina dana gama gaba ɗaya na kuɗi har Auren bare sukuma naira 1000 ne.

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }


NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*007*

Buɗe kyawawan idanun shi yake sannu a hankali waɗanda suka cika da wani irin ruwa wanda ya baiwa ƙwayar idanun tashi damar haɗewa da wani irin ja kamar gaushin wuta.
Jajayen laɓɓan shi yake motsawa a hankali a hankali wanda baka sanin abin da yake faɗi kafin ya sami damar mikewa a hankali yana rintse idanunshi ledar drip ɗin da aka maƙala mai yake bi da kallo atake anan tunanin abin da ya kawoshi asibiti ya soma zuwar mashi daki daki acikin ƙwaƙwalwar shi.
"Sannu yanzu maike maka ciwo?"
Tambayar da nurse ɗin gabanshi tai mai kenan tana mai saka hannu tana cire mai ledar drip ɗin.
Rintse idanunshi yayi tare da buɗesu akanta yana mai zuba mata manyan idanunshi.
Batare daya tanka taba ya komar da kansa saman pillow ya kwantar yana mai cije ƙasan laɓɓanshi na ƙasa.
Tattare kayan aikin ta tai kana tabar bakin gadon nashi bayan ta tabbatar da komi normal ba wata matsala.
Maganar su inna ce ta kuma dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa na dangane da lamarin shi.
"Sannu yaro yanzu ina ke maka ciwo?"
Cewar inna tana mai dafa saman kanshi baki ɗaya hankalinta yana kanshi, kafin su anty suma suyi mashi sannun yana jinjina kai alamun da sauƙi.
Miƙawa baba hannu yay sukai musaba ba.
"Yanzu dai an mai allura tare da karin ruwa amman dai gaskiya in kuna son yaron ku ya rabu da wannan ciwon sekun mai aure".
Dr yafaɗa yana mai daukar biro da takarda ya soma rubutu ajikinta.
Kafin ya ɗago ya mikowa baba takardar.
Amsa baba yayi yana mai sakin murmushi.
"Babu komai likita indai dan wannan ne babu matsala akwai yarinyata da nai mai alkawari in yaso se a ɗaura auren kawai".
Murmushi dr yayi.
"Amman kwa dattijo daka kyauta sabida yana cikin bad condition akan lamarin kuma har ga Allah, in bakuyi kokarin yi mai aure ba komai na iya faruwa sabida yadda halittar shi keda ƙarfi irin hakan ne kan saka mutum yay zina da dai sauran su".
Murmushi baba yay irin na manya.
"karka damu likita nafa gamsu sekai kamar baka gayamin ba".
Dariya baba ya baiwa dr dan haka seda yaɗan dara kana sukai sallama baba ya fita imran ya baiwa takardar maganin shikuma yaje phamarcy ya siyo sannan suka karasa cikin ward ɗin.
Zaune yake yay matashi da pillow dagashi se, jallabiyar da inna ta zira mai lokacin da zasu tawo asibitin duk su inna sun zagaye shi suna masa sannu ganin baba yasa yaɗan muskuta kaɗan yana gaisar dashi.
Fuskar baba wasai babu alamun damuwa yake amsa mai gaisuwar tashi.
Domin yana tunanin inma wata matsala ce yanzu tazo karshe tunda yaji komi.
"Madallah Umari jikin da sauki kai imirana jeka samo mana shatar tasi mutafi gida yau dai ciwo ya ƙare".
Cewar baba.
Gaba ɗaya su anty basu fahimci mai yake nufi ba, haka imran ya fita yaje ya samo tasi.
Da taimakon imran Umar ya sami damar fita har zuwa bakin gate inda motar take shida imran a gaba su anty da inna da umma a baya baba kuma yahau adai daita yace ze tadda su agida.
Har lokacin da suka koma gida akwai matasa a kofar gidan inna suna jiran isowar CIKA DAJI sabida shiɗin na mutane musamman matasan anguwar da suke yinshi.
Faka motar yay dai dai da sanda matasan kofar gidan suka saka ihu suna murnar dawowar shi.
Fitowa yay daga motar yana ɗan yamutsa fuskar shi kasancewar shi bamai yawan magana ba amman akwai murmushi.
Se lokacin na sami damar karewa UMAR CIKA DAJI kallon tsaf.
Dogone mai jiki yana da suffar ƙarfafan maza farine mai sirki daja sumar kanshi irin ta fulanin usul ce haka nan yana da manyan lumsassun idanu masu kama dana maijin bacci.
Yana da doguwar fuska mai cike da tsantsar kyau wadda take zagaye da saje mai haɗe da gemu, fararen haƙoran shi masu kama da ƙanƙara yake buɗewa yana gaisawa da ƴan samarin anguwar da suka zo yimai ya jiki.
Har su anty suka isa gida yana faman gaishe gaishe da jama'a kafin ya samu ya zame da ƙyar gida ya shiga ya faɗa bayi yay wanka sannan ya fito yazo ɗakin inna ya zauna shayi ta haɗo mai mai lemun tsami.
Ta aje masa tana daɗa yi mai sannu da jikin?.
Ɗaukar kofin yayi yana kaiwa cikin bakinshi zafin shayin na ratsa shi yana jin sauki acikin jikinshi.
Seda akai kiran sallar magariba sannan ya kammala ya tashi ya nufi masallaci.

Nikuwa fita mukai da sakina a wani layi muka tsaya nida ita da nazir, kana muka sami dan dakali muka zauna muka soma hira.
Nazir irin muta nan nan ne masu iyayin tsiya magana kaɗan seya sakomin turanci.
Sannan na fuskanci yana son ya taɓamin hannuna koya ɗan dukeni a cinyata amai makon naga sakina tai masa magana a,a sema kara gudun hirar mu naga tanayi.
Sosai nima na saki jiki muke hirar mu dashi.
Kafin naji yace.
"Ungo my bb"
Ya mikon kwalin waya daga hannun shi dayake Bb yake cemin ma'ana black beauty.
Jikina yana rawa nai kasa da hannuna naki amsa.
Amman seya kamo hannuna yana shafawa harya samu damar sakan wayan acikin shi.
Kafin ya kuma shafo gargasar hannuna cikin tafiyar tsutsa yana lashe baki.
"Ki amsa dan Allah sabida da ita xanna jin ɗumin ki".
Yafaɗa yana kokarin kamo hannuna ya ɗora a saman cinyar shi.
Lokacin idanuna yay tozali da yadda saman rigarshi ya tashi.
Da sauri na mike ganin sakina bata wurin tai gaba tana dariya tana cewa.
"Bara nabarku ku bawa shuka ruwa ina zuwa my yaya".
Cikin zafin nama shima ya mike tsayen yana kamoni.
Da sauri na fisge kamar zanyi kuka! nace mai.
"Yayan sakina maye haka wannan ba ɗabi a mai kyau bace, sannan kuma gaskiya bazan amshi wayarka ba sabida gudun matsala a shekaruna ban can canci rike wayaba".
Amai makon naga ya amshi wayar senaga ya ɗora hannu a saman kirjin shi yana tari.
"Wayyo Bb in baki amsa ba zan mutu wayyo zuciyata".
Da sauri naga yana tarin kamar ze sumar min.
Cikin azama na matse wayar ajikina ina ƙifta idanuna.
"Zan amsa kai hakuri"
Nafaɗa a sokon ce.
Amai makon naga ya ware senaga ya saki wata makirar dariya tare da manna min kiss a saman goshina.
"Wow thanks my bb ashe ana sona".
Yafaɗa yana dariya.
Nima dariyar na saki kafin kuma nai gum da bakina ina saka hannuna ina toshe bakina.
Kamar kuma an ce na waiga aikuwa idanuna ne sukai tozali da Ya Umar da Ya imran suna tun karo layin wanda daga gani kamar daga masallaci suke.
Kirjina ne ya bada sautin Dum! dum!! da sauri na matse wayar a kirjina kafata na rawa na..................


*Littafin naira 300# ta wannan acctn numbern 0078174806 starling bank shaidar biya ta nan 08142105218, in da AUREN BARE ne part 2 naira 500 ne*

*ZUMA A BAKI...!*🌹
{ Painful love Story }


NA
*AUTAR MANYA*

_HOME OF QAULITIES WRT ASS..._

*008*

Na soma takawa ina tafiya ina jin muryar nazir a bayana yana min magana.
"My bb wait! ina zakije kuma muna magana?"
Yafaɗa cikin sauri tare da kokarin tarar gabana, ganin hakan yasa na tattare zanin dake jikina na arta a guje!.
Ban dire ko ina ba se a kofar gida anan ɗinma karo mukaci da baba da baffa suna kokarin shiga gida.
Jada baya nayi ina ƙifta idanu alamun rashin gaskiya sun bayyanar min a idanuna karara.
"A,a wanake gani kamar humairah da wannan almurun?"
Cewar baba yana ƙoƙarin saka tourch light ɗin datake hannun shi domin ya haska min fuskata.
Rissunawa nayi ina mai cewa.
"Eh! baba nice".
Nafaɗa cikin fargaba da zulumin abin da ze faru dani.
"Daga ina kike a wannan lokacin?"
Cewar baffa wanda yake ƙoƙarin miƙomin ledar dake hannunshi.
Amsa nai jikina yana rawa sabida gabatowar su ya Umar wajan.
"Ai daman nagaya maka ita nagani".
Cewar yaya imran yana mai kallon ya umar wanda naga yana ƙiftawa imran idanu alamun yay shuru.
Se kuma naji muryarshi akaina yana cewa.
"Au wai gaba kikayo kenan,to ai duk saurin ki ga shinan seda muka tarar dake".
Dum! dum!!dum!!!
Gabana ya yanke ya faɗi wani sahihin gumine ke yanko min a dukkan ilahirin jikina ban gama dawowa dai dai ba naji yana cewa su baba.
"Baba taje duba ni ne semuka haɗu a hanya".
Yafaɗi maganar yana mai danne ɓacin ranshi domin yaga sanda wannan yaron na ɗazu yake binta a baya sannan kuma yaga sanda suke zancen.
Wata uwar harara imran ya jefa mai ta takaicin maganar dayay.
Washe baki baba yayi yana maijin daɗin hakan domin yana ganin in har Humairah na damuwa da umar kamar haka ai lamarin auren nasu baze musu wahalaba sannan kuma zasu haɗasu auren ne cikin farin ciki.
"To madallah ai canake ko wani wajan taje da wannan magaribar amman tunda dubiyar ɗan uwanta taje ai madallah".
Baba ya faɗa yana mai shiga gida haka nan baffa shima ya shige abinsa bayan yayma ya umar yaya jiki.
Cikin ƙufula ya imran ya shige gidan shima.
Wajan yay saura dagani se shi dani ke tsugunne.
Gaba ɗaya wata kunya ce ta gama kamani tabbas a wannan lokacin na shaida son da ya umar kemin ta yadda ya rufa min asiri bai faɗi cewar ya ganni ba wanda nike tabbata cewar yagan ni ɗin a ɗazu sabida yadda nazir ke uban kiran sunana.

Numfashina ne ya kusan ɗaukewa lokacin danaji sautin fitar numfashin sa a dai dai saman fuskata.
Gaba ɗaya ya tsugunna a gabana kamar yadda nake nima a tsugunnen ya zubamin kyawawan idanun shi yana kallona dasu fuskar shi ta ƙara ja ta murje tayi mugun kyau.
Ko kaɗan ban hangi ɓacin rai samanta ba sabida baiwar ɓoye damuwa da kawaici da rabbi ya kimsa mai.
"Aisha kin kyauta nagode! nima bani na ɗorama kaina sonki ba Allah ne ya ɗora min, ina rokon Allah daya hanaki kula kowani namiji a yayin da kika aure ni domin a lokacin bazan jure gani ko jiba".
Ɗago kaina nai a tsiwace na dubesa sama har ƙasa!
Sanye yake da baƙar t.shirt mai dogon hannu se dark blue jeans masu saukin kuɗi kayan sunyi matukar yi mai kyau a cikin farar fatar jikinshi se uban kamshin dake tashi ajikinshi na turaren element.
"Kai kana tunanin zan aure ka ni humairah".
Nafaɗa ina nuna kaina da yatsan hannuna.
"Inma mafarki kake ka farka ya umar niba kalar ka bace nifa bana sonka kona aure ka bazaka sami jin daɗin zama dani ba, ko kaɗan zaran ba kalar yadin bane dan Allah kaji dana cefanan gida ka kula da iya ƙarfin ka kada ka tattagowa kanka jidali".
Nafaɗa ina mai miƙewa tsaye.
Sedai kaifin marin daya ziyarci fuskata shiya hanani tashin sena koma zaune na baje ina kuka!.
Ya imran ne tsaye akanmu yana faman huci wanda kafin wani lokaci ya rufeni da duka gida nai aguje ina ihu wanda anan muka bar ya umar a adashe shiko ya imran bayana yabi yacigaba da buguna wanda ya jawo hankalin sauran mutan gidan suka fito suna tambayar abinda ke faruwa.
Bai saurari kowa ba seda ya tabbatar ya jigatani da mugun duka kafin ya ɗago yana share gumi.
Kallon baba yay.
"Yau baba nai nadamar abin da kunnena yaji gami da humairah wai yarinyar nan ce ta saka umar a gaba tana masa rashin kunya".
Salati su baba suka hau yi suna jimanta abin kana ya imran ya ɗora.
"Wallahi baba da idanuna naga yarinyar a lungun gidan sadi tana zance amman ko rufin asirin da umar yay mata agabanku bata duba ba shine harda kallonshi tace mai talaka".
Ai baba bai tsaya jin sauran ba ya rufeni da duka kamar ya sami jaka.
Seda baffa da umma sukai da gaske kafin su janyeni ranar naga lukutar masifa domin hatta yatsana kasa ɗagashi nai sabida azabar duka.
Wanda nike tunanin konai targaɗe nema a hannun, haka umma ta kaini ɗakinmu taimin nasiha kana tabar ɗakin.
Itako anty umma na fita ta shigo ɗakin xama tai ta dinga surfamin faɗa kamar babu gobe.
Kallona tai tana zabgan harara!
"Wallahi humairah in baki auri umar ba babu ni babu ke! talauci da arziki duka na Allah ne! to waima dame kika fi umar yaro santalele jinin fulani ɗan gata gaba da baya makaranci jarumi amman ki zauna kina shuka mai tsiya wallahi humaira ban miki baki ba amman ina guje miki ranar da zaki nadamar abin da kika ma umar ranar da umar ze zame miki ɗan hakkin daka raina sabida haka ki zauna ki nutsu duk tsiya wanda yake sonka a rayuwa yafi makiyin ka".
Anty ta faɗa tana tashi ta barmin ɗakin.
Ko kaɗan dukan su da faɗan su baimin tasiri ba sema wani zazzaɓin daya curemin wanda shiya haddasa min lulluba ina cigaba da kukan kiyayyar shi.
Da ƙyar ya mike yana rangaji ya kama hanyar gidansu kamar ɗan ƙwaya duka ya kaima iska yana mai cije labban sa.
Tabbas yau inda watace tai masa wannan cin zarafin baze barta ba amman aisha ta wuce komi wurin shi haka ya karasa gida tare da shiga ɗakinsa kayan shi ya cire yay saura dagashi se boxer kwanciya yayi a saman katifar shi ya kalli rufin kwanon ɗakin shi wanda bai yi aune ba hawaye ya soma bin kyakykyawan kuncin shi.

Shikuwa baba hankalin shine yay mugun tashi da jin furucin imran na cewar yaga humairah tana hira da wani sabida haka a daran ya tara baffa da umma da anty da ya imran, batare da ɓata lokaci ba ya sanar dasu ƙudirin shi na cewar gobe insha Allah ze ɗaurawa ƴarsa Aisha humaira aure tare da ɗan aminin shi umar sabida haka kowa ya kwana da shiri.
Sosai su anty sukai farin ciki dajin hakan dan haka baba ya sallami kowa akan se goben da yardar Allah komi ze kammala!


*NAN NA KAWO ƘARSHEN FREE PAGE*
MAI SON CIGABAN LABARIN *ZUMA A BAKI*
Ze biya naira 300 ta wannan acctn numbern. 0078174806 starling bank, shedar biya ta nan 08142105218 marasa amfani da banki kuma zasu ɗauki hoton katin MTN na naira 400 su turomin ta lambar dake sama.

*YAYA ZATA KAYA A TSAKANIN ZAMAN TAKEWAR AUREN UMAR DA HUMAIRA* ?
WANDA BAN RIGA DANA BAYYANA SHIBA DOMIN SEMUN SHIGA DAGA PAID SABIDA ABIN MUHIMMI NE.
*SHIN TAYAYA HUMAIRA TAKE RABUWA DA UMAR*?
*DA ALAMU YANZU UMAR YA ZAMA MAI KUƊI HUMAIRA KUMA TA KAMU DA MUGUN SON SHI BAYAN SHI TUNI YAYI AUREN SHI*
*SHIN ZE MAYAR DA ITA ƊAKINTA? SHIN WA UMAR YA AURA? SHIN TSAKANIN HUMAIRAH UMAR NAZIR WAYA LASAWA WANI ZUMA A BAKI*?
*TAYAYA UMAR YAKE SAMUN KAN HUMAIRA HAR RABO YA SHIGA TSAKANIN SU*?
*TABBAS DAGA PAGE 1 to 8 LASA MUKU ZUMAR LABARIN NAI AMMAN RAGOWAR SEMUN SHIGA DAGA PAID GROUP DOMIN AKWAI TARIN ABUBUWAN DABAN RIGA NA BAYYANA SUBA WANNAN SALON NA DABANNE HAKA NAN TAFIYAR TA MUSAMMAN CE* 💃💃
*KUNSAN SALON LABARINA WANDA YA KARANTA LITTAFINA NA AUREN BARE! YA SANI WANDA BAI KARAN TABA KUMA YA DAURE YABI WANNAN SABON DOMIN KA TSUNDUMA CIKIN TAFKIN KOGIN DAƊIN LABARIN HUMAIRAN UMAR* 💃💃💃
MUJE ZUWA PAID GRP READERS DOMIN ABIN SEDA SHIGA LABULE💃💃💃💃💃

*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*9&10*


Zuwa asubahi jikina ya gama tsanan ta da mugun zazzaɓin daya rufeni

Please Login or Register in order to submit comment