Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin danaji sallamar anisa a ɗakin.
Amsa mata nayi tare dajan bakina na tsuke.
"Yaya humairah"
Ta kira sunana.
"Na'am Anisa".
Gyara zamanta tai a gabana tare da cewa.
"Ɗazufa naga yaya umar dasu aslam wallahi fafur sukaƙi yarda dani wai su akaisu wajan inno".
Ban ce mata komi ba naja jikina nai saman gado.
Babu yadda anty batai dani akan na fito nasha iska naci abinciba amman naƙi haka nai kwanan kuka
Washe gari kuwa kaina ya tashi da mugun ciwo,idanuna yay jajir sallar asubahi nai na koma baccina.
"Ke humairah yau bazaki aiki ba sekin makara"
Naji muryar anty akaina.
Ban motsaba nifa wallahi in akan ƴaƴana ne sena zubar da komai na makashi kotu domin bana jin a yanzu zan iya rayuwa babu su.
Fafur naki tashi bare na shirya nai makaranta haka naita juyi agado wajan karfe goman safiya naji kamshin turarensa tare da sallamarsa da sauri na mike na nufi gaban taga ina leƙen ƴaƴana.
Waige naga islam nayi tare da turjewa waje ɗaya taki shiga ɗakin anty.
"Daddy ina maman?"
Tafaɗa tana turo baki irin na shagwaɓaɓɓun yara.
Shafa tulun sumar dake kansa yay tun jiya islam ta hanashi sukuni ita yakaita wajan mamah mai kuka ta jiya har dukan ƴar yay akan nacin data kafa masa amman taƙi shuru ganin haka yasa ya tattarota sukayo nan( ɗada mahaifi se Allah).
"Tana ciki muje mana"
Yafaɗa murya ƙasa-ƙasa.
Amai makon ta shiga seta saka mai kuka wanda ya janyo hankalina nayo tsakar gidan,sabida daman ni ɗayace a ɓangaren namu su anty suna ɓangaren ummah.
Kaina babu ko ɗan kwali haka na zube a gabanta na ware hannuna ina kuka.
Da gudu ta shige jikina tana sakin ajiyar Zuciya.
Shafa kanta nai da hannuna ina jin wani irin nutsuwa a tare dani.
Kafin na soma kici-kicin ɗagata nai ɗakinmu da ita.
"Wait dakata! ina zakimin da yarinya kinga ajeta zamu wucene"
A dake na tsaya da ita a hannuna.
"Bazan bada ba ainima ina da hakki akanta dan jaraba ƴa nason wajan mamanta ka hanata zuwa"
Nafaɗa cikin rashin kunya.
A gabana ya tsaya yana zuban kallon banza.
"Bani ita Aisha bana son hauka"
Yana kokarin kwatar ta.
Seta saka kuka.
"Ni wallahi daddy bazani wajan mommy ba ita bata kuka akammu dukanmu take mommyn abuja".
Cak naga ya tsaya ya zuba mata ido yana kallonta kafin naga ya juya yabar tsakar gidan.
Yana gab da fita na ɗaga murya.
"Allah ya isana ga duk ƙatuwar data dokarmin ƴaƴana ubangiji yabimin hakkina"
Da gudu najata mukai ɗakinmu ina dariyar farin ciki.
Shima anasa ɓarin maganar islam ta kaɗashi batun yau take cemai mommy na dukansu ba amman yadda take nan nan dasu agabansa yasa ya kasa yadda da maganar islam ɗin sabida ance ba,a kama maganar yaro gefe ɗaya ga takaicin rinjayen da humaira tai mai na amsar islam wadda yaji kamar ya gaurawa islam mari sabida yadda take ƙulafucin uwarta.
Haka ya koma gidan inna aslam daman bayajin dadi yana bacci dan haka shima fita yay zuwa gidansu sakina wadda ya kasa gane kanta sam yanzu in sukazo kano bata yadda ta sauka gidan inna kamar da sedai shiya bita can gidan nasu.


A gado na ajeta na fita waje shayi na haɗo mana mai kauri nazo na zuba mata muka baje muna sha muna gamawa na tsefe mata kanta da kaina na wanke mata sannan na shiga ɗakin anty da ita se lokacin suka san an kawon ita nanfa anisa ta amsheta ta soma yarfa mata kitso mai kyau da yamma nai mata kunshi ja wanda ya haskata.
Sosai baba yay farin cikin ganin islam a gidan haka yayta sabga mata siyayya kala kala, a daren kuma har aka rufo kofar gida baizo ɗaukarta ba dan haka na cire mata kayanta muka kwanta tare washe gari ranar juma'a nafita aiki tare da ita.
Lokacin naga tashin hankali domin karfe goman safiya da rabi segashi a bakin gate ɗinmu koda naje cin mutunci yahau min akan me xan fito mai da yarinya.
Sunkuyar da kaina kasa nai ina mai wasa da yatsuna haka ya gama bala'insa yaja ƴarsa suka tafi ajiyar zuciya na mayar domin yanzu naɗanji dama sabida yadda islam ta ɗeban kewa a daran jiya.
Sedai maganar dukan da matar ubansu ke masu ita ta tsayan a raina na kasa mantawa.
Haka na yini a makarantar sannan na dawo gida bayan an tashi lokacin naji labarin sun wuce abuja.
Hmm ashe wucewa zasuyi can ɗin shiyasa yazo a burkice.
Watsar da sabgarsu nai a ranar na shiga sabgata washe gari na tashi da shirin tafiya gidan shugabar makarantarmu kamar yadda ta umarcen.
Shikuwa daman da yaran kaɗai ya tafi domin zasu koma school ne ita kuwa sakina taƙi binsa sabida fushin datake dashi tun jiya akan yace mata islam na wajan mamanta.
Wannan dalilin ne yasa ta dauki fushin dayasa har shima yay fushi ya tafi yabarta haka nan koda ta kira wayarsa bai dauka ba domin ta ɓata mai rai sabida yadda tace mai ai daman tasan munafurcin mazane amman yanasan matarsa har yau wannan maganar yasa yaji haushinta sosai.
Hankalintane ya tashi a washe garin asabar tai gidan inna domin tasakata ta basa hakuri akan laifin datai mai har yay tafiyarsa ya barta.
Shikuwa daman da biyu yay hakan na farko maganar islam na tana dukansu na biyu kuma furucinta gareshi wanda ba daban yakai zuciyarsa nesaba dase yay mata illah a daren.
Ita kanta inna, tai mamakin yadda sakina batazo gaisheta ba,amman dan rashin kunya tazo mata da wannan maganar agabanta inna ta kirasa ta hau yimai faɗa akanme ze tafi yabar matarsa.
Hakuri ya bata sannan yace gobe ta bata kudin mota ta tawo haka inna ta kirga kudi ta bata sukai sallama ba kunya ta kama hanyar fita.
Magana mukai akan sabon bazzawarin da shugabar makarantar mu ta sama min na taho inata tunani mai ƴaƴa takwas da mata ɗaya amman yana da kuɗi hawayene yake zubomin lallai rayuwa yau ni ake jonawa da wani duk irin soyayyar da umari ya nuna mini.
Cak na tsaya lokacin dana zo giftawa ta gidan inna ganin sakina tana fitowa daga gidan.........!
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

*29 & 30*


Cikin tsananin ɗauki na ƙarasa gareta fuskata a sake naja na tsaya a gabanta.
"A,a sakina daman ana ganinku a duniya? se yanzu kika tuna dani wallahi nayi faman nemanki amman rashin sanin gidanku yasa kikajini ɗiff gani ba waya akwai tarin damuwa a zuciyata".
Nafaɗa ina mai riƙo hannunta.
Zame hannunta tai daga cikin nawa tana mai jefamin ƙazamin kallo kafin ta kwashe da wata irin dariya.
"Hmm yaro!yarone yaro man kaza komi girman jikinka idan babba yafika tofa ya fika"
Ta numfasa tana mai cigaba dayin dariyarta.
"Humairah kenan ai bani da buƙatar ki bani wani labari akan mutuwar aurenki domin ina da labarin komi akanki ba kowa bace ba ke face bazzawara marar ƴanci mai baƙin jinin da tunda Umar ya rabu da ita batada mashin shini sabida tsabar baƙin halinki"
Jikina ne yahau tsananin rawa dajin kalamin da aminiyata take jefamin amman jin maganarta a karo na biyu ya kuma hargitsamin lissafina.
"A yanzu bani da buƙatar wata alaƙa dake humaira sabida daman buƙatar maje hajji sallah to alhamdulillahi ni naje hajji har umara ma naje ta dalilinki ƙawata"
Ta kwashe mini da wata shegiyar dariya.
"Da farko sunana sakina kuma ni haifaffiyar garin kano state ce mahaifina aiki ya kawosa garin kano, amman ɗan asalin garin nasarawa lafiya ne, har Allah yasa ya auri mahaifiyata umma, anan unguwar chiranchi suka zauna har Allah yasa umma ta haifi anty hadiza daga kan anty hadiza bata kuma samun haihuwa ba har seda ta shekara takwas sannan ta haifeni ni sakina, nayi primary da secondry a wata makaranta a gadon ƙaya daga nan babanmu ya rasu wannan tasa ban cigaba dayi ba bayan nai candy ita kuwa daman anty hadiza tuni tai auren ta anan kusa da gidanmu, babarmu mace ce mai hakuri hakama anty hadiza amman nikam inada zafi ina da kishi haka nan zuciyata mai riƙo ce da bin diddigin abinda take so shekaruna ashirin da huɗu da haihuwa amman bani da saurayi bare nai tunanin yin aure sabida akwai wanda na ƙwallafa raina akansa tun ina zuwa makaranta a gadon ƙaya nake haɗuwa dashi inze tafi BUK wannan tasa bana sauraran kowani ɗa namiji, sanin inada ƙaramin jiki yasa ummana bata damuwa da rashin aurena domin inna fita kamar yar shekaru sha bakwai zakaganni sedai ta idanu inada nuna shekaruna, Akwai watarana dana fito daga gidan anty hadixa kawai senaganshi hannunsa ɗauke da wata baƙar yarinya mai girman jiki tana ta mai sangarta ze tafi makaranta a ranar dana ganshi kasa bacci nai........
Washe gari nabi ta hanyar danaga yabi anan na sami makocin sa nake tambayarsa akan labarinsa atake anan ya gayan sunansa da kuma alaƙarsa da wannan yarinya wadda naji zata zaman Garkuwa a wajansa, Mataki na farko dana fara ɗauka shine na yaga takarduna gaba ɗaya na makarantar sakandire na sake neman sakandiren da wannan yarinyar take na koma daga farko ma'ana jss one.Cikin sa'a aka haɗamu aji guda da ita, da bin diddigi da shishshigi na samu na shiga jikinta ta zamen aminiya na fuskanci yarinyar batada wata magana seta masoyina wadda dukkan maganar da zatai akansa takan tafine da dukkan zuciyata.
NAZIR
Naje sabon gari nemo ankon bikin ƙawata xan gifa mukai clashing dashi adai dai wajan gidan gala, da sauri yazo gareni yana mai min magana akan yana sona sedai kallo guda nai masa na shaida cewar ƙwararran ɗan duniyane da wannan damar na amshi numbernsa wanda najewa wannan yarinyar dashi a matsayin yayana wanda na lasa mai wata ZUMA A BAKI wadda takaisa ga bani haɗin kai wajan cikar muradina, nayi amfani da ƙawancenmu ne na cika burina akan abinda nike so haka nan naje mata da wani irin salon yaudarar ƙawa wanda bata san dashiba......
Yaudarar kuwa itace.
Najenye jikina daga halaƙa da ƴan gidansu ma'ana koda wasa ban shiga jikinta a gida ba ta yadda har mahaifanta zasu lura dani su rabamu, nima kuma ban kaita gidanmu ba bare mahaifiyata da ƴar uwata su lura da shirina nabar ƙawance na da itane a iya school daga nan kuma se ranar dana taɓa satar jiki naje gidansu ranar da nazir yazo se kuma ranar daurin aure danabi zugar jama'ar biki na faɗa gidan nasu batare dana bar wani ya ankare ba, nayi amfani da tunanina sosai kafin wanzuwar hakan sannan koda wasa ban jata jikina ba amman ita ta jani ajikinta"
Seta juyo tana kallona.
"Tunda na sanki humaira sau biyu na taɓa xuwa gidanku abotarmu a iya makaranta ta tsaya wadda yawanci iyaye basa sanin dawa ƴaƴansu suke mu'amala a makarantunsu kinga kuwa hakan ke sawa yawanci burin ƙawa ke cika akan ƙawarta musamman mai wayo irin nawa, Tun bayan da kika auri Umar na shiga halin damuwa kullum bani da buri face ganin na rabaku"
Ta kuma kallona.
"MATAKI NA BIYU Nasha matukar wuya kafin na gano maye halin umar! na fara karantar cewar bayan ke baya da wata macen dayake so aduniya inka cire mahaifiyarsa daga ke kuwa se ƴaƴan da kika haifa wanda bayan na gama amfani da uwarsu a matakin farko na cikar burina senai amfani da su wajan ƙarasa ƙudirina, wanda bayan mun haɗa baki nida nazir mun fahimci lokacin dawowar umar gida nazo akan zan miki sallamar tafiya abuja har yazo ya rike hannunki se kuma nazo nabi naxir abuja akan an saceni wanda duk nazir ne ya bincikon inda umar ke aiki da hanyar sa ta komawa gida da ƴaƴan cikin ki nai amfani har umar ya auren wanda hakan bakaramin kunci kesa ruhina ba domin bana kaunar abinda ze raɓeki bare naci albarkacin ki a wajan Umar, humaira a yanzu burina ya cika shiyasa ma na ɓata lokaci wajan warware miki zare da a bawa domin bana shakkar kisan nice matar umar mariƙiyar ƴaƴanki aminiyar ki ta bogi domin nayi amfani da daƙiƙiyar ƙwaƙwalwarki nai miki muguwar illah kuma ina miki albishir da cewa umar nawa ne for now an always dan haka sekibi wani sarkin badai nawa ba".
Tafaɗa tana mini dariya.
"Koda wasa umar bai san na sanki ba bare yay tunanin ni ƙawarki ce haka nan inna bata sanni ba haka zalika dattijawanki suma basu sanni ba bare ai tunanin naci amana sabida haka ina da fredom na shiga duk inda naso a dangin mijina batare da anyimin kallon mai cin amana ba bare naji kunya".
Tafaɗa tana ɗan rangwaɗa agabana kamar wata ƴar duniya.
Wani irin rawa jikina ya ɗauka kamar mazari kafin nai yunƙurin........................
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *31 & 32*

Ɗora tafikan hannuna biyar a saman fuskarta bata gama dawowa a hayyacinta ba na kuma wanketa da wani bahagon marin, kafin ta sosa na ƙara mata uku a jere masu ɗan karen zafi.
Da azabar ƙunar zuci na dubeta.
"Wallahi sakina sekinyi mamakin yaudara ta da kikai zan nuna miki ni ƴar kano ce cikakka ba zuwau ba kuma sena nuna miki wacece ni! cikin ilimi da nutsuwa irinta ƴaƴa masu tarbiya daga ƙarshe kuma ina mai tabbatar miki da cewa GANGAR JIKIN UMAR KIKA AURA ba zuciyarsa ba domin zuciyar umar ta AISHA HUMAIRA ce da ƴaƴanta har abada sakina bazaki mallaki umar ba matukar ina raye nai gabanki nai miki gudun wuce sa'a a fagen soyayyar umar domin ni sona yake daga zuci har baki haka zalika sone daga Allah ba boka ba malam ba kirsa bare bariki soyayyace ta asali ƴar gaske wadda turawa kewa laƙani da Pure love wadda ba algus cikinta kuma ko yanzu na mutu nagodewa Allah dayasa kika ci arzikin ƴaƴana har kika sami soyayyarsa koda haka seki bawa jakar ƙwaƙwalwarki amsar wacece aisha a zuciyar umar? bazan ji komi dan kinmin haka ba,domin sau tari daman makashinka yana tare dakai sedai kuma ta yaro kyau take bata ƙarko mu zuba"
Nafaɗa a dake.
Tare da saurin barin wajan zuciyata na suya na nufi gidanmu.
*SAKINA*
Azabure ta dafe fuskarta da dukkan tafukan hannayenta tsananin mamakin humaira ya hanata tafiya bare ta ɗago daga dogon suman wucin gadin azabar zafin marin data afka sosai humaira ta bata mamaki yaushe humaira ta zama jan wuya haka? yaushe humaira ta zama mai dakakkiyar zuciya haka wadda harta ɗaga hannu ta zuba mata maruka biyar lallai ɗan hakin daka raina shike tsone maka idanu, jikinta sanyi ƙalau ta nufi gidansu kai tsaye kicin ta nufa batare data amsa maganar da ummanta ke mata ba, harseda ta sami ruwan ɗumi ta wanke fuskarta dashi abinka da farar fata tuni fuskar ta haye tai suntum dole seda ta haɗiyi maganin zazzaɓi sannan ta wuce ɗaki ta kwanta da shirin tafiya gidan mijinta gobe dakuma tsananin tsanar humaihar mai zafi a zuciyarta.
*Humairah*
Kamar ƴar maye haka nake tangaɗi a hanya harna isa gida kai tsaye ɗakin anty na nufa ina zunduma ihu kamar ƙaramar yarinya, da sassarfa anty da baba wanda ya dawo daga wajan sana'arsa kenan suka fito rumfar suna tambayata a ruɗe.
Ajikin anty na zube ina cigaba da kukana wanda fitarsa ce kaɗai zata sakani jin sanyi acikin zuciyata.
"Ke humairah bani son sakarci, mi aka maki zakizo kina mana kuka kamar wata ƙaramar yarinya bana tunanin ko anisa zatayi wannan shirmen naki".
Naji muryar baba akaina yana faman faɗa.
Cikin hakan su umma da baffa suka shigo ɗakin a kiɗime sabida suma sunji kukan danike yi ashe.
Itako anti janyoni tai jikinta muka zauna a tsakar ɗakin hakan yasa suma su baba suka zauna suna sauraran kukana.
"Anty na shiga ukuna wayyo yaya zanyi?"
Nafaɗa cikin kuka, kusan a tare baba da baffa sukace.
"Wani abunne ya sami umar da ƴaƴan a hanya?"
Girgiza kaina nai tare da share hawayena kana na dubi anty na soma bata labarin abinda ke faruwa tundaga haɗuwa da sakina har kawo yau hatta abubuwan danikewa ya umar seda na faɗa ina kuka!
Daga ƙarshe na ɗora da cewa.
"Baba ku yafeni nasan ban kyauta muku ba domin ba irin tarbiyar da kuka bani kenan ba amman sakina tayi amfani da ƙaramin tunanina ta yaudaran harta auren mijina"
Nafaɗa ina kuka.
Gaba ɗaya tausayin tane ya kamasu tabbas wannan wata jarrabata ce tare kuma da ishara Allah ya nuna musu, gaba ɗayansu domin abin da ya sami ɗanka ai ya sameka.
"Karki damu humairah kanta taiwa amman kema kinyi sakaci waya gaya miki ana yarda da mutum yanzu ai mutum se Allah".
Cewar ummah wadda take share hawayenta.
Shikuwa baffa tsabar kiɗima ma kasa cewa komi yayi se uban share zufar dayake famanyi.
"Kinga wannan ma ya zama izina gareko? gaba in akace ki sake yin abu babu shawarar mahaifanki kya kumayi sakarar banza uban wama ya haɗaki da ita? wato ni ina nan ina miki tarbiya wata nacan tana rushemin, amman Allah ya sakawa da umar da alkairi yanzu a wannan zamanin wani namijine zeyi abinda umar yayi wani namijin zaki dinga sheƙawa wannan iskancin ya zauna dake? to wannan matsalar da kika shiga haƙƙi biyune ya jefaki cikinta domin kinsan yanzu tun a duniya ake nuna ishara, abu na farko hakkin mijinki da kuma hakkina ni mahaifiyarki danafi kowa kusanci dake amman kika je kika haɗa kai da wata take miki zagon ƙasa, to mu bazama mu nuna wannan maganar ta faruba ki zuba musu idanu Allah ze nuna ikonsa".
Anty ta faɗa tana zubar ƙwallah domin tsananin jin tausayin ɗiyar tata.
Shikuwa babanmu tunda ya sada kansa a ƙasa bai kuma ɗagowa ba har seda su baffa sukai sallama suka wuce nasu ɓarin sannan yaja hucin takaici.
"Yanzu Aisha wannan sakarcin kikai taiwa Umari ashe? ah dole yaron nan ya dauke mana ƙafa, ashe da walakin goro a miya! ikon Allah inda ranka zaka sha kallo wato ita wannan yarinyar ku rabu da ita kanta taima amman kuma wannan ma babban darasi ne wato inzaka shekara kana bawa ɗanka tarbiya daga can zaka sami wanda yake rusa masa, to dama munata shawarar zaki koma karatu nida imirana to matsalar nifa naji tsoro kada ki kuma haɗuwa da wata ƙawar ta kuma jefaki a illah amman da naso ki fara koda fce ce kafin Allah ya kawo miki wani mijin, Allah yay miki albarka aike ba abar jin haushi bace yanzu abar tausayice tabbas alokacin akwai kuruciya da kuma wauta Allah ya saka miki Aisha shikuma umari Allah ya fitar dashi daga sarƙar wannan hatsabiya amin".
Baba ya faɗa yana mai kokarin fita daga cikin ɗakin.
"Baba".
Nakira sunanshi.
Ya dakata yana kallona da tausaya wa.
Buɗe bakina nai kana nace mai........


#AUTAR MANYA

*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *33 & 34*


"Baba inada buƙatar makaranta nima dan Allah baba ka tausayamin ka mayar dani makaranta wannan kaɗai ze saka naji sassaucin zafin dake zuciyata".
Nakai maganar ina mai fashe mai da kuka!
Dakatawa baba yayi da fitar nashi kana ya dawo gabana ya gurfana hannuna ya kamo yana mai lallashina.
"Haba Aishatu na! maye na kukan aini yanzu na zubda makaman yaƙina akanki,Bara ɗan uwanki yazo inaganin zan sama miki gurbin karatu kima daina zubda hawayenki akan wannan".
Babana ya faɗa min hakan cikin tattausan lafazi.
Anty ce ta, tari numfashin, baba tana mai cewa.
"Amman babansu da kawai ta fitar da mijinta tayi aure inaganin hakan zefi mata ƙima, domin yanzu haka daga gidan Haladu ƙanin umma take kuma naji umma na maganar bazzawari hajiya zata haɗata dashi ai sekaji ta bakinta kafin maganar karatun ta miƙe ko?".
Anty takai maganar tana mai kallon babammu wanda yay tsam da ransa alamun ya ɗan shiga tunani ne na daban.
"To'to babu damuwa amman dai duk da haka ina son tacigaba da karatun nata yanzu ke Aisha yaya kukayi da hajiya hadizan?".
Baba ya jefamin tambayar yana kallona.
Hawayena na share domin ni tuni nama manta danaje gidan mai makarantarmu.
"Baba wai ɗan uwanta ne keson ƙarin aure matarsa ɗaya da yara takwas, amman ba gida guda ze haɗamu ba kowa da gidanshi, nan da sati ɗayama zezo mu gaisa".
Nakai maganar kaina a ƙasa.
Dafe haɓa anty tai tana mai sauraron abinda baba ze faɗi aikuwa baba se cewa yayi.
"To madallah Allah ya zartar da abinda yafi zame miki alkairi a wannan karon dama zamu baki domin ki fitar da mijin da kike so sabida haka duk wanda kika ɗauka kika kawo mana matukar muka bincika mukaga halinsa na garine zamu bakishi sabida nina fahimci a karon farko ma, Umar ba ƙinshi kikai ba tsabar zugace da hassadar waccan shaiɗaniyar ƙawar taki ya saka kikaita ƙulla masa tsiya salo-salo to yaya zamuyi da hukuncin Allah fatanmu Allah yay miki zaɓin alkairi amin".
Baba yafaɗa yana mai tashi tsaye ya kama hanyar fita anty tana mai masa adawo lafiya tare da amsa masa da amin.
Sosai anty ta zaunar dani tana min nasiha tare da bani manyan misalai akan yanayin rayuwa wanda nai matuƙar tsorata dasu tabbas nina shaida yarinya ce ni amman ƙaddarar auren wuri da haihuwa yasa na sami ƙarin girma ajikina da hankalina wanda ya zarta na shekaruna.
Bamu muka tashi daga rumfar anty ba seda akai kiran sallar magariba bakin rariya naje nayo alwala na shige ɗakinmu na shinfiɗa abun sallah na som gabatar da sallar magariba ina idarwa nai bangaren umma kallo.
Anan muka shantake har Anty tagama tuwon dare ta zubo mana namu mukaci daga nan mukai sallar isha'i kowa ya kama gabansa domin ya kwanta ya hutawa ransa.
Dare mahutar bawa amman a gareni hakan ya gagara domin gaba ɗaya nakasa rintsawa idanuna ya fushe sam nakasa yin bacci se faman nanata maganganun sakina nake acikin ƙwaƙwalwata.
Wannan rayuwa wato gaba ɗayanta abar darasice ga bawa yakamata tun da sauran damarmu mu dinga gyara halai yarmu kafin mutuwa tazo ta riskemu wannan itace ranar nadama ga bawa.
Wai yanzu ace zalinci cin amana zamba cikin aminci handama da baba kere sune suka yawaita ga al'umarmu? makashin ka yana tare dakai kana tare da mutum amman shi zagon ƙasa yake maka shin mai Umar yake dashine da har sakina zataimin wannan ƙullalliyar akanshi?
Lumshe ƙananun idanuna nayi ina hasko yadda umar yake a zahiri.
Umar dogon namijine mai suffar ƙarfafan maza farine tas mai dogon hanci da manyan idanu yana da mugun haƙuri tare da kawaici da rashin magana,Amma akwai zuciya idan ranshi ya ɓaci, Lumshe idanuna na kumayi ina Mai juyawa na rungume filon dake gabana tuno tsadaddiyar soyayyarshi wadda kansa naji kamar mu kaɗaine ke rayuwa a duniyar in yana gwadamin ita, yasan salon narkar da zuciyar mace haka nan yasan laƙanin mantar dake a duniyar da kike koke wacece wajan taurin kai matukar umar ya soma rikitaki da salonsa tofa bazaki kaucewa biye masa ba.
Wani azababban fitsarine ya kamani acikin wannan dare gani Mai mugun tsoro tashin anisa na soma amman taimin shuru,ganin ya soma zubomin a pant ɗina yasa na mike da sauri tare da fita ina tsaki.
Duk tunaninshi dana yaranshi dana matarshi ya hanani sukuni har yasa na raba dare idanuna bude.
Addu'a nai kana na shiga bayi na kama ruwan na fito nai alwala na nufi hanyar ɗaki adai dai dokin kofar ɗakinmu naɗan doki bakin kofar da ƙafata wadda naɗanji zafi kaɗan amman sena maze na shige ɗaki bayan na kaɗe shinfiɗata na kwanta abina.
Yatsana ne babba na ƙafa ya cigaba da zafi kamar an watsa barkono addu'a nai a wajan na shafa a wannan karon naji dama sannan bacci ya kwasheni wanda ban farkaba seda akai asubahi koda na tashi still yatsan nawa ya ɗan kumfura haka nayo alwala nazo nai sallah bayan nai azkar na koma bacci wanda rabi azabar yatsan ce fall a jikina wadda harta zuban zazzaɓi mai zafi.
***********
Da wajan karfe bakwai ta isa tasha wanda kusan bakwai da rabi motarsu ta tashi zuwa garin na abuja,Tunda tahau motar ta kifa kanta a saman jakarta tana tunanin matakin dazata dauka akan humaira haka har suka isa garin abuja bata wani yanke tartibin abinda zata mata ɗin ba.
Taxi ta tara ta shigar da kayanta sannan ta masa kwatancen inda zataje tafiyar mintuna kaɗan ta kaita unguwar tasu kuɗinshi ta bashi sannan ta saukar da kayanta tare da nufar cikin gidan ta kama kofar gate ta bude da ƙyar ta shigar da jakarta cikin falon tana uban nishin azabar gajiya data zafin ciwon kan marin jiya dayaki

Please Login or Register in order to submit comment