Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakinta har yau.
Gumi ta yarfe na wahala tana mai kallonshi a fakaice kafin ta karasa saman kujerar dayake zaune da sassarfa ta isa gareshi..........


#AUTAR MANYA
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *35 & 36*

Zaune yake dagashi se dogon farin wandon yadin kufta system ce a saman cinyarshi yana dannawa sabida wani aiki dayake gudanarwa acikinta.
Idanunshi manne da farin gilashi wanda ya zauna das a fuskar tashi abin sha'awa.
Cikin wani irin yauƙi da gwalli sakina ta ƙarasa gabanshi tare da saka hannu ta janye system ɗin dayake aiki da ita ta, kana ta mayar da jikinta ta zauna a saman cinyarshi hannunta ta ɗora a saman sajenshi taɗanja kaɗan tana wani irin ƙifta idanunta.
"Beby nai missing naka amman shine ka tawomin da yarana babu ko sallamar kirki ko?"
Tafaɗi maganar cike da salon jan hankali.
Murmushi ya sauke kaɗan domin a iya wannan lokacin yagama karantar cutar mai da yara da takeyi a bayan idanunshi, amman danya ɓatar mata da tunaninta yasa yace mata.
"Dafatan kin dawo lafiya?"
Ya kauda wannan maganar datake soko masa.
"Lafiya kalau na dawo se ɗunbin kewar ƴaƴana"
Tafaɗa da wata irin siga.
Shikam dariyama ta basa a wannan karon.
"Ƴaƴanki ko? kima daina damuwa dasu fa kin manta uwar data haifesu ma tana can tana rayuwarta babu su bare ke?"
Yafaɗi maganar da siga biyu.
Jikinta ne yay sanyi a wannan karon tai danasanin jefa mai tambayar ma gaba ɗaya.
"Nida ita akwai bam-banci domin ni ina sonka".
Tafaɗa a zuciye.
"Ita kuma ƙina take? look sakina idan kinsan cin zarafina zakiyi daga zuwanki zaki koma inda kika fito yanzu".
Yafaɗa cikin ɓacin rai matuƙa.
Wanda yasa hatta idanunshi seda ya soma fitar da jar kala.
Numfashi taja a galabaice dajin wannan baƙin furucin nashi.
"Umar mai kake nufi akan waccan marar mutunci kake gayamin waɗan nan maganganun? kalla fuskana akan naje gidansu gaisar da mahaifanta dan kawai mamanta tace ni matarka ce jiba yadda ta miƙe ta zubamin maruka har biyar jere"
Tafaɗa tana mai nuna mai fuskarta data kuma yin ja abinka da farar fata.
Zaro idanunshi yay waje cike da mamaki.
"Toke waya baki ikon zuwar musu gida da izinin waye?"
Rau rau tai da idanunta.
"Tsautsayine ya kaini ba wani abun ba".
"Yayi miki kyau amman bana tunanin Aisha zata mareki akan kawai dan kince ke matata ce gaskiya domin wannan kalmar bazata saka ta mareki ba? sakina sau tari kina yin abun da nake kallonki dasu kada fa ki manta ina aikine da shashin bincike ne na masu manyan laifuka wallahi! wanda ya fiki rashin gaskiya ma tashi ɗaya nake ganoshi bare ke! ke kina cin alfarmar aurena ne amman bada ban haka ba da tuni na watsaki waje, Sabida haka ki taka a hankali kisan da wa kike zaune ba sakarai bane sedai kawaici irin na fulanin usul".
Yakai maganar yana mai tashi yabar mata wajan ya nufi bedroom ɗinsa zama yayi a gefen gado gaba ɗaya abin duniya yay masa zafi.
Ya soma gajiya da halin sakina wanda kawai kallonta yake dasu bawai baya sane bane musamman akan yaransa wallahi kawai yana mata kawaici ne akansu.
Wayarsa dake yashe a bakin gadon ya ɗauka ya shiga contact ɗinsa lambar ogansa ya shiga kira bugu ɗaya ya ɗauka gaisawa suka shigayi, sannan suka ɗora akan bayanin binciken da aka sakashi ya gudanar akan wani mutum wanda ake zargi daya saci yara guda biyu yayi garkuwa dasu, sosai suka zanta akan maganar yanzu haka an samu nasarar gano inda mutumin yake zaune sabida haka dole ogan nasa yace mai zasu turashi kano sabida akwai waɗanda aka gano suna tare da mutumin sedai su suna zaune ne anan kano bayan sun gama maganar sallama sukai sannan ya kashe wayar yana mai dafe kansa dake barazanar tarwatse masa.
Sam bai shirya tunkarar kano a wannan lokacinba, sabida yaransa suna tsaka da karatune shikuma baya son abinda ze nesanta shi da yaranshi musamman a wannan lokacin da sakina take gallaza musu duk da bai nuna mata yasan komi ba, amman abin yana mugun taɓa masa ransa amman ta kusan tuƙeshi takaishi bango domin shi ɗabi'arshi ce kawaici zai taraka in kana masa abu amman da zarar ka kaishi bango tofa komi ma ze iya faruwa.
Tsaki yaja mai ƙarfi sannan ya miƙe tawul ya dauro a west ɗinshi kana ya faɗa toilet ya sakarma kanshi ruwa,ya jima yana cuɗe jikinshi da lallausan soson dake hannunshi,sannan ya kammala wankan nashi ya fito a centern ɗakin ya tsaya ya goge ruwan jikinshi gaban jerin kayansa ya tsaya ya ɗauki yadin kufta ruwan madara mai ɗinkin riga har ƙasa se wando sakawa yay kana ya feshe kansa da turare mai ƙamshi gyara sajen fuskarshi yayi sosai sannan ya ɗauki makullin motarshi ya fita makarantar su islam.
A hanya nuratu ta kirashi tsiya take mai akan rashin zumuncin sa wai ya manta da ita kwana biyu baya nimanta murmushi yayi yana mai bata hakuri akan yanayin aikinsa ne ya kawo hakan.
Koda ya ƙarasa makarantar seda ya jira su aka tashi sannan ya kamo hanya suka yo gida tun a mota daya ce musu mommy ta dawo yaga islam ta haɗe ranta saɓanin ada daya daukosu sunata murnar ganinshi, Amman tunda yace musu mommy ta dawo sukaja bakinsu suka tsuke harya ƙarasa gida basu tanka masa ba, abakin gate ɗinsa ya tsayar da motar tare da bude musu kofar kallon islam yayi gaba ɗaya yarinyar ta kom kamannin mahaifiyarta sak,inka cire farar fatarshi data ɗauko shiyasa tafi aslam kyau nesa ba kusaba sabida ita ta haɗe da kamannin humaira da kuma manyan idanun mahaifinta ne,
"My happiness zanje nai mana take away na dinner kuje gida maza ki kula da ƙaninki kafin na dawo".
Tura baki tai gaba tamkar yadda humaira ke masa inzatai rigima sannan tace mai.
"Mudai daddy kaje damu zamu bika can ɗin"
Tafaɗa tana mai kafesa da manyan idanunta.
murmushi ya sauke mata yana mai lakato kumatunta yana maijin soyayyar ta acikin ransa fiye da komi na rayuwarsa.
"Sorry my love jeki cire uniform ɗinki kicirewa ƙaninki ku zauna a ɗakinku kujirani ina zuwa"
Yafaɗi maganar cikin tausayin kansa dana yaran nasa.
Babu damar musu haka taja aslam tana ƙunci kamar zata kurma ihu! suka nufi gidan.
Ya jima yana kallonsu don seda suka ƙulewa ganinshi sannan yaja motar ya nufi inda ze amso musu abincin dare.
Yana tafe yana tunanin su aransa tare da fargabar abinda zeje ya dawo akan su.
Cikin sanɗa kamar munafukai sukai sallama a falon hannun islam rike dana aslam.
Tana zaune ta haɗe kai da gwiwa tana nanata cin zarafin da umar yay mata a ɗazun wanda shiya hanata tashi daga wajan bare ma ta kintsa kayan ta datazo dasu.
Cikin rawar jiki suka zube a gabanta.
"Mommy barka da yamma"
Islam ta faɗa sabida itace mai baki aslam kam bayada wani wayon kirki bare bakin magana sosai.
Wata uwar harara ta maka musu cike da tsanarsu.
"Dan ubanki inda banyi yammar ba zaki ganni anan wato baku so na dawo gidan ubanku bako? shegiya mai fuska kamar anyi ɓarin kayan miya a injin markaɗe kutashi kubani waje ƴaƴan jaraba" ta saka ƙafa ta haure islam tai baya amman tsabar tsoronta bai bar islam tai kuka ba da sauri taja ƙaninta suka bar falon ɗakinsu suka nufa kuka! yarinyar ta saka a ƙasan tiles tana mai sosa wajan data duketan.
Cikin kuka aslam ya matso gabanta ya saka hannu ya share mata hawayen.
"Yaya ki bar kuka! dan gayawa daddy"
Yafaɗa da gwaranci sabida baya iya magana sosai.
Cikin son kanin nata ta janyoshi jikinta tana share mai hawayen dayake.
"Aslam ɗina kada ka gayawa dady kaga mommy tace in muka gaya masa zata yanka mu mudaina ganin daddy da inno da maman kano wadda na kwana a wajanta".
Tafaɗa tana mai tashi tsaye ta wanko fuskarta suka cire kayansu tsuru sukai a ɗakin suna jiran ubansu ya dawo domin tsoron fita suke waje.
*********
"Yaya humaira ki tashi ga abin karyawarki inji anty"
Naji muryar anisa kanwata akaina tana min magana.
Ɗago da jajayen idanuna nai na sauke akanta.
"Anisa kiramin anty ƙafata kamar zata cire wayyo yatsana...........



TOFA!
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *37 & 38*

Nafaɗa ina mai sakin kuka tamkar raina ze fita sabida wani irin azabar ciwo da yatsan nawa yakemin da sauri anisa ta fita tsakar gida mintuna kaɗan se gasu sun shigo tare da anty cikin ɗimuwa anty ta dubeni.
"Tashi humairah muga yatsan naki meke damunki?".
Da ƙyar na sami damar yunƙurawa na tashi daga kwanciyar danake ɗin, na saka matashi na gyara zamana, hannu ta saka ta ɗago yatsan nawa dayay jajir kamar ze fice sabida azaba
"Subuhanallahi yaya akai kikai wannan rauni haka kamar wadda bata kallon gabanta?"
Tafaɗa tana mai kallon yatsan nawa.
Rintse idanuna nai sabida zafin dana keji sosai ga zazzaɓin dayake damuna.
"Wallahi anty jiya naisa a bakin ƙofa bamma zaton ze zaman haka ba, wallahi bakiji yadda yakemin zafi ba kamar ze fitar min da yatsana".
Nafaɗa ina mai rintse idanuna kaɗan.
"To Allah ya sawwaƙe ya kuma kare gaba Allah ma yasa yau babu makarantar yaran da sedai ki fashi bara a kawo miki abincinki nan inyaso seki sha ko panadol ne insha ALLAHU zakiji afuwa".
Fita tai anisa ma tai mini sannu tabi bayanta.
Can kuma segata dauke da kwanukan abincin karyawa ta diren agabana, Godiya nai mata sannan na sauko ina ɗingisa kafar a hankali nake tafiya harna nufi gaban kayana na zaro zani na ɗaura sannan na matsi maclean na ɗauki brush na nufi tsakar gida.
Wanko bakina nayi tare da fuskata na koma ɗaki agaban a bincin, na zauna na saka hannuna na buɗe kwanukan tuwone ɗumame da miyar kuɓewa jan murfin nai na rufe sabida tsanar danaiwa tuwo ko kaɗan bana ƙaunarsa jan jikina nai na koma saman gado na ƙudunduna abina ban wani jimaba bacci mai nauyi ya kuma fusgata.
*********
A wani haɗaɗɗan gidan cin abinci yayi parking seda ya gyara dai dai ton motar tasa,Sannan ya kasheta ya fita waje yana mai shaƙar iskar dake kaɗowa daga sararin samaniya, taka ƙafafunshi yayi ya karasa shiga cikin wajan.
Direct wajan order ya nufa yaje yay order abinda yake buƙatar suci shida yaran nasa sannan ya nufi wajan biyan kuɗi akai amfani da Atm card ɗinsa wajan biyan kuɗin.
Hannunshi ɗauke da manyan ledoji masu tambarin wajan cin abincin guda biyu ya nufi gaban motar shi ya bude gidan baya ya zuba ledojin sannan ya zagaya wajan driver ya shiga yaja motar ya nufi hanyar gidansa.
Tafiya yake cikin nutsuwa yana lissafa lamuran rayuwa waɗanda suke faruwa ga bawa.
Yau zakaga safiya tayi anjima zakaga azahar tayi daga nan se yamma se dare gaba ɗaya rayuwar gudu take wadda wasu daga cikin bayi basa gane yadda rayuwar take sema wata algaita da shaiɗan da muƙarraban sa ke buga musu.
Lumshe idanuwan sa yayi tare da furzar da sassayan iskar cikin bakinsa yana mai hasaso lamarin duniya yadda yake tafiya, Komi na rayuwa akwai geji tare kuma da iyaka wallahi a wannan aikin nashi yaga abubuwa da dama waɗanda suka basa tsoro ainun.
Babban abinda yake daɗa daure masa kansa shine yadda a yanzu wai mutum yazama abokin tsoron ɗan uwansa mutum a yanzu, In bakai taka tsan tsan da rayuwarkaba sekaji ance babu kai, yanzu wasa ake da rayuwar mutum kamar ba a bakin komi ba, babban abin da ya kuma ɗaure masa kansa shine.
Case ɗin wannan mutumin wanda ake xargi yana garkuwa da mutane, shi baban yaran da aka ɗauke abin da yake faɗa masa last week dayaje office ɗinsu shine.
Business yake na kayayyakin masarufi yana zaune a shagonsu na kasuwa kawai sega wannan mutumin yazo yace mai zeyi siyayya ta kimanin maƙudan kuɗaɗe, waɗanda suke da daraja.
Bayan sunyi cinikin ya amshi accnt numbern sa ya tura masa da waɗan nan kuɗaɗen.
Bayan sati ɗaya still ya kuma zuwa yay masa siyayya wadda tafi ta farko kuɗi sedai a wannan karon bai basa kuɗin duka ba seya bashi rabi seyace masa ze masa ciko Da zarar wasu kuɗi sun shigo masa.
Ranar da mutumin ya kirasa akan cewar ze kawo masa kuɗin se akai akasi yana gida baya shago amman seya ce mai ya tura mai ta accnt,A lokacinne mutumin yace wai accnt nasa ya sami matsala in ba damuwa yay masa kwatancen gidansa ya kawo masa mana.
Cikin yadda yay masa kwatancen gidan nasa da daddare yazo masa da kudin bayan sunyi waya ya shaida mai yana kofar gidan.
Fita yayi ya amso kudin kana sukai sallama.
Tafiyar mutumin da kwana ɗaya aka shiga gidansa aka ɗaukewa matarsa manyan sarƙoƙi na gwall sannan akai gaba da ƴarsa mace da kuma yaronsa namiji.
Ɗimuwa tashin hankali sun shiga, sedai abinda ze baka mamaki yadda aka kira wayar uban nasu akan cewar seya bada kuɗaɗe masu kauri sannan za,a sakar mai yaran nashi wannan dalilin yasa mahaifin yaran ya garzayo office ɗinsu ya bada report wanda nan da nan suka baza jami'ansu akan suyi bincike akan al'amarin wanda suka dauki wajan sati uku suna faman abu guda.
Wanda cikin hukuncin Allah suna ta samin nasara akai.
Wannan aikin ne ze kaishi kano nan da kwanaki guda, domin ya ƙara bincikar sauran waɗanda abin ya shafa kamar yadda jadawalin aikinshi ya basa dama.
Da wannan tunanin ya ƙarasa gida jikinsa a mugun mace.
Baya kaunar abinda xe saka ya tafi yabar yaran nan nasa a gida batare da wani ba.
Amman ya barwa Allah ikonshi domin shine mai tsare kowa.
Parking ya gyara a bakin gate ɗinshi sannan ya kashe motar,Ya shiga gidan kofar falon ya tura babu kowa a falon se Ƙarar tv.
Gaban tv'n yaje ya kashe sannan ya zube ledojin daya shigo dasu a falon ya nufi kofar dakinshi, alwala ya ɗauro a toilet sannan ya fito falon still baiga kowa ba.
Baiko dubi dakin sakina ba ya nufi ɗakin yaran nashi.
Hannu ya saka ya murɗa handle ɗin kofar tare dayin sallama.
Islam na zaune saman sopa tana duba littafin azkar a hannunta, wanda ya zauna ya koya mata, shikuwa aslam yana raɓe a gefenta yana kallon yadda take karatun nata.
Gabansu ya karasa ya zauna a gefen, su ya ɗaga aslam yana mai cewa.
"My boy bazaka kula daddyn naka ba?"
Dariya yaron nasa yayi yana mai kwantar da kansa a jikin mahaifin nasa.
Itako islam batai magana ba har ta kammala azkar ɗin nata ta shafa sannan ta mike.
"Daddy sannu da dawowa"
Abinda ta faɗa mai kenan taja jikinta tabar mai ɗakin.
Murmushi kurum yayi ya bi bayanta aslam a hannunshi.
Tana xaune a kasan carpet tai tagumi.
Cikin damuwa ya zauna a gabanta ya saka hannu ya cire mata tagumin nata.
"Bebyn daddy waya taɓamin kene?"
Ya faɗa yana tsareta da idanunshi.
Tura baki tai gaba tana kokarin yimai kuka!.
"Daddy bakai ne katafi kabarmu ba,inata kiranka kaimin banza".
Seta saka mai kuka! wanda hakan ya kumayi dai-dai da zuwan sakina falon wadda taci ado na burgewa.
Da sassarfa ta karaso gaban islam tawani kamota cike da kirsa.
"Ambebi na, waya taɓamin ke kike kuka tunda kika shigo nike maki magana kinmin shuru, ko daddy ne?"
Gaba ɗaya ido suka zuba mata daga islam ɗin har aslam ɗin suna kallonta wanda hakan ya bawa umar damar fahimtar wani ɓoyayyan al'amari a tare dasu ɗin.
Cikin rashin sabo da hakan, islam ta janye jikinta.
Kallo tabi mahaifinta dashi cikin kuka tace mai.
"Daddy dan Allah ka kaimu wajan maman kano, dan Allah daddy bama jin daɗin zama babu ita anan gidan...........
#AUTAR MANYA
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *39 & 40*

Tsira mata manyan idanunshi yayi yana mai kallonta dasu.
Kafin ya lumshesu ya ƙara zuba su akanta.
Sosai yayi mamkin furucin yarinyar tasa.
"Islam mekike faɗa ne banji ba?"
Yafaɗa rannan nasa a haɗe.
"Daddy wajan mamammu zaka kaimu".
Gabansa ne ya faɗi amman bai nuna ba.
"Islam wace mamanku kuma?"
Yajefa mata tambayar, wadda kusan a tare suka saki ajiyar zuciya shida sakina wanda shi na fargaba ne ita kuwa na ɗunbin mamakin yarinyar ne wanda take ganin in batai da gaske ba tofa ze zamane ka sare maciji amman baka kauda kansa ba.
"Wadda rannan ta gammu take kuka! wadda nace nima ka kaini wajanta,dady ranar daka kaini wajanta na kwana ko, Bakaga abinda tai mini ba ta goyani ta min wanka ta saimin alewa da safe, ta tafi dani school ɗinsu sannan kuma anty anisa taimin kitso ƙananu mai kyau dady ina sonta kamar yadd take sona".
Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfin gaske.
"Ita tace zata dawo?"
Dariya islam tayi sannan tace mai.
"Lah daddy tace bazata dawo gidanmu ba amman tana so adinga kaimu wajanta tace min itace mahaifiyata, kuma daddy ko a islamiyya ance kaso mahaifanka, shiyasa nake sonta".
Tsaki sakina taja tare da tashi fuww tabar wajan tanajin ranta idan yay dubu ya ɓaci tabbas duk yadda zatai ta salwantar da rayuwar yaran a yanzu take nema sabida ashe ita hauka tai abaya data raba humaira da umar domin waɗan nan yaran ma tana ganin har sunfi humaira soyuwa a zuciyar umar ɗin.
Zama tai a bakin gadonta tana mai nanata ƙiyayyar islam a ranta bata kaunar yarinyar domin tafi kowa tsaya mata aranta tabbas shiri nagaba zata san yadda tai ta salwantar da rayuwar yarinyar ne baki ɗaya.

"Islam kin bani mamaki tun a yanzu kin soma ban bantani nida mamanki wato kinfi sonta dani ko?"
Yafaɗa yana zaro mata idanunshi.
Rufe fuska tai da hannunta.
"Daddy kaima muna sonka mana sosai ma daddy itama haka"
Baice komi ba haka ya tashi ya nufi kicin ya wanko tire yazo dashi wannan abincin daya siyo musu ya ɗora akai, seda sukai sallar magarib sannan ya zuba musu ya ajewa sakina nata yarasa mai yasa tama tashi daga wajan nasu.
Abincin su sukaci suka koshi sannan suka sha ruwa.
"Daddy naga mama tana kuka ranar dana kwana wajanta, bata san ina kallonta ba, setai ta share hawaye ita kaɗai".
Shafa kanta yayi.
"Islam iya magana ko idanunta ke ciwo ne?"
Murmushi tayi domin bata ma gane nufinsa ba abinka da yaro.
Sema kara nitsa masa wata hirar tata data kumayi a ranar haka islam ta hana ubanta sakat abu kaɗan mamanta kaza da kaza seda ya zare mata idanu ya fatattake ta sannan tai ɗaki tana dariya.
BAYAN KWANA BIYU.

Kwanansa biyu yana faman shirye shirye kafin ya nufi kano bayan yaje gidan wannan dattijuwar data taɓa masa aiki kwanakin baya ya daukota akan tana kwanar mai da yaransa domin yafi jin yarda da ita akan sakina.
Masifa ma sakinar tahauyi, akanme ze kawo mata wata tsohuwa gida cemai akai tsoron gidan takeji, baibi ta kanta ba haka ya saka kansa yabar gidan.
Tunda yasaka kafa kuwa ya taho kano sakina ta bude fai fan rashin mutunci wanda ta uzzirawa baba da yaran nasa kamar xata dafasu ɗanyu.
Rashin mutunci salo salo kaaar zata kashe mai yara haka take garasu.
KANO
Shikuwa tunda yazo kano baima sauka a ɗorayi ba hotel ya kama anan kusa da inda aka turashin bayan ya kintsa shirinsa na komi ya fara gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa.
Alhamdulillahi yau yake kwana biyu ciff a garin na kano kuma babu wanda yasan ya shigo garin idan ka cire inna,
Yauma kamar kullum seda ya fito daga hotel ɗin daya saukan bakin wani guri ya samu marar hayaniya kayan jikinsa ya sauya daga masu kyau zuwa wasu yagaggu masu datti sannan ya adana waɗan nan nasan baƙi ya samu ya shafa a fuskarsa nan da nan ya ɓadda kamarsa kamar ba Umar ba.
Tafiya yake ko takalmi babu a kafarsa bazaka taɓa kallonsa kace mai yana da hankaliba haka zalika duk shaidawarka dashi bazaka ganeshi ba.
Wajan dayake hasashen suna yawan wucewa yabi kan gwanar kwaltar layin yaje ya zauna yana faman sosa jikinsa kamar mahaukaci.
Unguwar babu wata hayaniyar jama'a idan ka cire motocin dake wucewa tsilla tsilla.
Wajan mintuna goma ya dauka anan a zaune kafin motocin sutaho ajere kamar yadda yake ganinsu idan zasu wuce.
Tashi yayi da gudu yana bin motar kamar wani mai hauka tuburan harya cimmasu kafin ya sami dutse ya buga a bayan motar.
Cikin sauri drivern yay revars kana ya kashe ya fito yana nufo wajan umar wanda ya sheke da dariya wadda ta nunawa drivern kamar umar mahaukacine sedai shi umar bayan dariyar haukan dayake harma data cin nasarar aikinsa, sabida wannan drivern daya fito shine ɗayan abokin aikin wannan ɗan garkuwan daya ma alhaji wada mai wake! Gaba da yaransa, wanda bincike ya nuna shi wannan mutumin na nan kano ɗin mai suna habu ɗan ƙwai, shine abokin aikinsa amman shi yafi zama anan kano inda shikuma wanda ake xargin ya kwashe ƴaƴan wada mai waken yana garin minna, inda aka tura wani jami'in can minna ɗin shikuma umar aka turoshi nan shida sauran abokan aikinsa mutum huɗu sedai kowa da ɓangaren da aka ɗorashi.
Cikin tsanaki mutumin yabi umar da kallo.
Sannan kuma yaɗan girgiza kai ganin alamun hauka a tare dashi ɗin kana ya koma motarshi yaja ya tafi.
Sosa kai umar yayi yacigaba da bin mutumin har inda yaga yayi parking anan yaga ikon Allah domin sosai yaga mutumin yana gaisawa da makotansa cikin mutunci kafin a bude mai katon gate ɗinsa ya danna motarshi.
Juyowa yayi domin a yau ya shaida gidan mutumin sekuma aiki nagaba.
Dakatawa yay maganar ogansa na masa amsa kuwa acikin kunnensa.
"Umar sekayi a hankali ka iya takunka domin binciken mu ya nuna mana cewar habu ɗan ƙwai shararren ɗan garkuwa da mutane ne wanda yay ƙaurin suna a cikinsu sedai abinda ze baka tsoro da lamarinsa shine yadda yake ɓadda kama wajan nuna shiɗin nagartaccene kai hankali dashi umar domin mutumin hatsabibine yana da manyan yara ƴan daba dayake aikawa gari gari kaga acikinsu wannan wanda yay awon gaba da ƴaƴan wada mai wake yake, kuma kaga muna da tabbacin ma yaran suna nan gidan habu ɗan ƙwai ɗin a ajiye wannan dalilin ma yasa muka turoku kano, yanzu aiki nagaba akansa yake da kuma na naija ɗin sekuma maganar fitowa da wancan bawan Allahn ƴaƴansa, lallai lallai umar ka tabbata ka gano mana inda aka boye wannan yara, domin habu ɗan ƙwai ya wuce tunanin ka, yana da mugun wayo sekai a hankali".
Nisawa yayi tare da waigawa yaga babu kowa a wajan agogonsa na iphone wanda yake recording komi na aikinsa ya dauko ya gyara mai zama sannan ya nufi masaukinsa, akan ya xauna ya tsara shirin gobe.
Yana gab da shiga hotel ɗin nasa ya ɗaga idanunsa karaf.
Nima na ɗaga nawa idanuna ina kallon tsallaken titin danike na wajan arean by pass domin naje asibitine akan yatsana kuma sena sami napep wanda ya kawoni nan ya sauke yanzu ina neman wanda ze kaini gidane sabida yatsan ya tukuramin kullum da zazzabi nake kwana wannan dalilin ne yasa na yanke shawarar zuwa ganin likita wanda naje ya bani magunguna yanzu haka gasu a hannuna.
kamar ance na waiga na haɗa idanu da wani kamar ya...............
*GABA ƊAYA SADAUKAR WANE GA*

*HAJIYA ZULAIHAT* ( *MRS DR BASHIR*)
*Kainuwa dashan Allah, Rabbi ya ƙara lafiya da wadata mama*🌹

                          *41 & 42*

Umar da sauri na kuma murje idanuna still wanna mutumin mai kama da ya umar nagani yana kokarin juya bayansa, tsananin mamakine yasaka ƙafafuna sagewa da kuma sauri najasu na nufi tsallaka titin batare dana lura da manyan motocin dake shawagi a kan titin ba nidai fatana na isa gareshi,Cikin sauri na ɗage zanin jikina na ƙarasa da sauri lokacin yana kokarin barin wajan, seda na ɗaga ƙafata kafin na kamoshi yana gaf da nufar wata hanya mai dauke da yawan jama'a awajanta na ƙara ƙaimin saurin danake har ALLAH yasa na cimmasa ina hucin gajiya nasha gabansa.
Gabana ne yay mugun faɗuwa ganin wani riƙaƙƙen mahaukaci mai tsananin kama da ya umar, ya tsaya cak yana kallona, ƙasa nai da idanuna gabana yana cigaba da faɗuwa, haka xalika ina tsareshi da ido ina kallon sa tundaga sama har ƙasa, babu yadda za,ai kataɓa cewa ba baban islam bane sabida kamar ta ɓaci sedai wannan baƙine ƙirin haka na bisa da kallo a tsorace kamar kacemin katt na arce.
Shikuwa Umar ya tsaya ɗinne domin yaga wani irin condition zata shiga sabida haka ya dakata cakk yana binta da kallo haka zalika zuciyarsa na tsananin dokawa da sauri-da sauri wanda inda tana gabb dashi dazataji sautin bugun zuciyar nashi.
"Abban.......i....s....l...a...m"
Nafaɗa a rarrabe cike da zulumi a jikina.
Dariya naga ya sheƙe da ita alamun babu hankali agareshi.
Da sauri na matsa

Please Login or Register in order to submit comment