Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana fallasa dukkan abinda ta yi anyi watanni kusan uku kafin Alhaji Saddiƙ ya gano kanshi, ya zaunar da Hadiza ya yi mata nasiha tare da nuna mata cewar ta dauki ishara daga abinda ya faru kan Jummai, ta nutsu ta dawo cikin hankalinta domin itama zai iya kasancewa da ita, Hadiza kam ta ɗan yi nazari game da batun maigidan nata lallai haka zancan yake. Amma Hajiyarta har yanzun tana nuna mata cewa aikin da suke yi ne nasara ta samu, sannan ta ƙara miƙe ƙafa gidan miji ya zama nata, haka nan kada ta damu da zancan A'isha ita ma data dawo za su saukar mata da nata aikin don haka sai hankalinta ya kasu gida biyu, amma wata safiyar asabar da Hadiza ta nufi gidansu don duba jikin mahaifinta,taga Jummai wasu ƙarti suna dambe zasu saka ta a mota don kai ta gidanta gefe kuma ga mijin nasu da alama shi ne ya bada umurni sai ta ƙara tsorata don haka ranar da kukanta ta dinga roƙon mijin nasu wai ya yafe mata insha Allahu ta daina kuma zata zauna da shi fisabilillah, to kun ji Allah yasa gaske ne.

Tun zuwan farko da ya yi gurin su A'isha bai sake samun sukunin zuwa ba sai wannan karon ita ko taso hakan saboda dama tana tsoron ciki, zuwan ba zata ya yi mata dawowarta kenan daga lecture ta samu Uwani tana tuƙa tuwon shinkafa, cikin jin daɗi ta ce Allah sarki Uwani,ke da kanki? Uwani ta ce ƴan nan na gaji da cin shinkafar nan tuwan semo ɗin nan naku baya ɗaukana shi yasa na ce bari dai ki gani, cikin dariya A'isha ta ce nima fa ƙuiya ce dani ina son cin tuwon wace miyar ki kayi mana? Ta ce a'a ga dai tumatur ɗin nan yana dahuwa. dama kiyi mana miyar ganyan nan me ƙara jini, ta ce ogun? Uwani ta ce shi kuwa, A'isha ta shiga haɗa miyar ji suka yi ana ƙwanƙwasa ƙofa,Tani ce ta buɗe su Hafsat Sulaiman ne, suna ganin tuwo suka ce sun zo a Sa'a. Uwani tana ta musu tsiya da cewa sai yau ƴaƴan nan ƙwana biyu kun mana yaji har dake uwata, ta ce ma Hauwa'u. Hauwa'u ta ce karatune ya yi zafi Uwani,sunan mahaiyarta ne Hauwa'u, A'isha kuwa sunan ƴarta ne ta fari ƴar ma ta rasu amma bata faɗa don kara,kai dai dai da laraba bata cewa saboda a ranar Laraba ne ta haifi ƴar sai dai ta ce ranar samu.

Duk sun zube a falo suna ƙwasar tuwo, A'isha ko ta ce sai ta yi wanka wai warin zufa take, mai kurum ta murza ta zuro doguwar riga baƙa ta zauna tana shayar da Abulkhairi sai kuma suka kuma jin ƙwanƙwasa gida, A'isha ta ce maƙotana ne suma su shigo mu ƙara yawa yau gidana ya yi albarka, na gode da Uwani ta yi tuwon nan mai yawa,tuni Tani ta je ta buɗe ƙofa tun kafin ya iso falon ƙamshin sa ya shigo da sauri ta miƙe har ta tsorata ƙawayan nata tare da cewa Uncle da sauri ta fita, suka kalli juna fuskarshi tana ɗauke da murmushi ta ɗan sakar mishi irin hararar nan ta masoya cikin shagwaɓa ta ce Uncle ba notis? Ya ƙaraso ya cafki yaronshi cikin jin daɗi, sannan ya ce bana so in kira ki ce min karatu ya yi yawa gashi ina cike da kewarku,kin san saboda sauri ban zo da Jabiru ba, jirgi na biyo, ta ce sannu da zuwa Uncle shigo,yana shiga ya samu ɗakin da jama'a sai ya ce muna da baƙi kenan? Ta ce eh,ƙawayena ne ta gabatar mishi da su da kuma sunayensu, sannan su kuma ta ce musu ga Uncle ɗina dai yau kun ganshi suka ce lallai kam suka tashi wai za su tafi ya yi ciki tare da cewa suyi zamansu ganin yanda A'isha ta hana kanta sukuni yi wannan yi wancan Hafsatu ta ce kai Hauwa'u ina zaton Uncle ɗin nan nata shi ne mijinta baki ga kamar su da yaron ba? Ta ce na lura kuma fa haka ne don yanzun haka ma ta kan ce wa mazan su kai amma A'isha ta samu cikin ƙwali da harmun kama Hafsa ta ce sosai kuwa, amma fa tayi dace mutumin ya haɗu Allah da Uncle ɗin ta ne na gaske sai na ce don Allah ta haɗa mu, suna cikin hirar sai gata za ta je kicin Hauwa'u ta ce ji mana A'isha Musty ta zo tana dariya Hauwa'u ta ce Uncle ɗin ki ya yi kasuwa Hafsa ta ce ki shigar da ita, A'isha ta ce wuu ba zai ƙara ba, matan shi sun ishe shi, cikin dariya Hafsat ta ce ƴar wulaƙanci dama Uncle ɗin ne Abban Abulkhairi shi ne kike ta samu cikin ƙwali ko? A'isha ta juya tana dariya ganin sun harbo jirgin ta.

Ta yi murmushi ganin yanda yake cin tuwon hannu da baka hannu ƙwarya, ta ce Uncle da alama ka jima ba ka ci tuwo ba ko? Ya dubeta "Beby ba ma tuwo ba,na jima ban ci abinci ba, tun da matsalolin Jummai suka tsananta wata rana ma yini nake ban sha ko ruwa ba, lamarin ya girgiza ni sai tayi tamkar bata ji labarin ba ta ce jikinta ne ya yi tsanani? Ya dubeta kina nufin baki san me ke faruwa ba? Ta ce, "Uncle ina zan samu labarin Katsina, ina Sokoto?" Ya ce na zaci Nafisa ta tsegunta miki, ta ce muna waya amma ba ta ce min ga wata matsala ba, ya yi shiru can ya girgiza kai Beby na ƙara tsorata da lamarin mata, kuma na amince sharri tare da kaidin mata ya ɗarar ma na sheɗan, kazalika dole ne su fi yawa a wuta." A'isha ta ce "haba Uncle ya ya ka ke wannan zantuka ba duka aka taru aka zama ɗaya ba,wai ma duk me ya kawo wannan batun? Nan ya bata labarin komai, duk da cewa Nafisa ta bata labarin da take jin shi yanzun sai da ya girgiza ta, ta zuba tagumi cikin hawaye shi kam nasiha ya shiga yi mata da cewa A'isha na sani ke cikin mata daban ki ke,kin samu tarbiyya tare da yin gadon halayen mahaifanki, amma ina so ki ƙara zama cikin mata salihai,abin koyi kada ki amince ruɗin duniya ya ja ki ga halaka, duk duniyar guda nawa ce? Duk sonka da ita wata rana sai ka barta, tare da duk abinda ka tara daga kai sai halin ka zaka tafi, abinda Jummai ta kasa ganewa kenan, yanzun wa gari ya waya? Mai sammako inji ƴan magana, A'isha ta nisa ta ce to yanzun tana ina? Ya ce tana nan gidan sai dai ba a buɗe ta don ƙwanaki da ta ƙwace sati huɗu ana nemanta sai da ƙyar aka ganta hauka tuburan fa. A'isha ta ce, Allah ya bata lafiya, sannan don Allah ina roƙon mata arziƙin ka yafe mata ta ji da na sauran,ya tsura mata idanu sannan ya yi murmushi, A'isha ina son halayan ki to har zuciyata ta ci albarkacin ki na yafe mata nawa laifin, shi kenan? Ta ɗaga gira suka yi ƴar dariya.

Kafin ya dawo sai da A'isha ta tabbatar da cewa babu sauran wata damuwa cikin zuciyarshi na shi ganin har wata ƴar ƙiba yayi, A'isha kuwa dariya ta ringa yi mishi lokacin da ya iso gida Hadiza ta tare shi da nata salon tarairayar.

Yau da gobe lokaci yana tafiya,ƙwanaki na shuɗewa haka satittika da kuma watanni har su A'isha sun sami ɗan hutu suna ƙarshen shekara, sun iso gida cike da ɗokin ganin ƴan'uwa.



#######
[12/22, 23:34] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 13*




Uwani garin su zata wuce don duba dangi haka ma Tani, Aisha kuwa gidan su da suka koma aka wuce da ita,tsarin gidan yafi nasu na da, haka nan kowace da gefenta babu abinda zai haɗa wata da wata, komai sabo ya zuba mata, Hadiza har da yin girki don taran A'isha. Tabawa kuwa ta turo baki ta ce in dai kishiya ce fa baza kiyi gwaninta ba, Hadiza ta ce don Allah Tabawa ki ƙyaleni,ni na gaji da halinku, Tabawa ta kuma taɓa baki,nan gaba za ki kuma neman mu,kin kama tashar daji in dai kishiya ce,ta fita waje.


Cikin ƙwanakin suna zaman lafiya da juna, Hadiza ko yaushe tana shigowa gurin A'isha musamman in ba ita ce da miji ba, sai dai ganin yanda A'isha ke kula da mijinta da yanda shi kanshi ke ji dasu ita da ɗan ta sai ta kasa daure ma zuciyarta,in ta koma gurinta sai ta yi ta ƙunci wannan damar Tabawa ta sake samu ta dinga zuga Hadiza tare da cewa in fa Aisha na gidannan ta bar Samun soyayyar mijinta har abada, sai dai ƙunci ya kashe ta, Hadiza ta ce bana son in koma gurin maƙaryatan Malaman nan ne,sun jima suna ce min A'isha zata fita ba zata haihu ba menene, menene,sai gashi duk babu abin da ya faru,a ƙarshe ma ita ce ta haihu. Tabawa ta ce tuni da kin yarda tun dawowarta da tuni mun soma shirya mata kissa, tunda ba ki son Malaman, Hadiza ta ce kada ki shirya min ramin da zan rufta, Tabawa ta ce kajiki da wani tunani, duk abubuwan da muka shirya can baya wanne ne ki ka rufta? Hadiza ta ce shikenan.

A'isha tana kallon su tana dariya, Uncle ne shi da ɗan shi suke rigima, ya rarrafa ya janyowa Uncle ɗin waya daga chaji ya jefar sannan ya hau kan kujera ya zauna kan laptop ya hana Uncle ɗin aiki, ya dubi A'isha Beby zo ki ɗauki yaron ki ya hanani aiki, A'isha ta ce tayaka fa zaya yi Uncle, ya dubi yaron Babana je ka gurin Mominka, A'isha tana tasowa yaron ya ƙanƙame uban ta koma tana musu dariya, ya ce kina dariya ne ma ko kin ƙi ɗauke shi in gama ko? Shima ya yi ƴar dariya tare da rungume yaron dama muna magana ne kan tafiyar ki aikin hajji, tunda ba zaki riƙe shi mu gama ba shi kenan. Asha wasa ko yaron Baba?" Da sauri A'isha ta tashi ta cafke yaron zo kada kasa in ga samu in ga rashi, ta zauna kusa da shi tare da dafashi gaske ne Uncle ɗina? Ya ce kalli ki gani lis ɗin sunayan waɗanda zasu tafi aikin hajji ne sunan waye farko? Ta kalli screen ɗin laptop ɗin, Beby ta gani farko cikin murna ta ƙwantar da kanta a kafaɗarshi tana cewa na ji daɗi bari na gani su waye sauran nayi musu albishir koda in samu tukuici, daga sunanta sai nashi ta dubeshi kai fa duk shekara sai ka je ya ɗora yatsanshi kan leɓanta ke zan raka ta ci gaba da dubawa, sai sunan mahaifanta biyu da yayanta Abdulrahman sai Nafisa da Uwani mai aikinta sauran kuwa bata san ko su waye ba,ƙila cikin danginsu ne. Ta dube shi ban san da wane baki zan maka godiya ba Uncle, ya ce kawo kunnanki ki ji dame za ki bani tukuici, ta miƙa kunne ya raɗa mata, dariya ta shiga yi sannan ta ce ka samu ban ga Hadiza ba, ya ce kin san dai ance Hajji kiran Allah ko? Ta ɗaga kai ya ce to Allah bai kira ta ba, A'isha ta ce to Allah yasa tana da rabo nan gaba, ya ce Amin.

In kin je me zaki roƙa? Ta ce Sa'a a karatuna sai kuma gamawa lafiya, tare da samun ƙyaƙƙyawan ƙarshe. Ya ce ni duk shekara haihuwa nake roƙo, ta dubi Abulkhairi da ke bacci a jikinsu, sannan ta ce Uncle ba gashi ka samu ba, ya ce ni da nike son dozin biyu Beby kina da sauran aiki fa, ta ce wai ba zan iya ba ana shan wuya fa sosai,ni dai wannan ya isheni, ya zuba mata ido, Beby ba ki yin tsarin iyalin nan ko? Ta ce me yasa ka ce haka? Na gane shiru, ta ce Allah tunda ka ce baka so an wuce gurin, ya ce shi kenan. Ta miƙe da yaron a kafaɗarta bari in shinfiɗar da shi ka ƙarasa ina zuwa yau zaka sha tukuici, murmushi ya yi tare da cewa Beby.

Tabawa wadda ke maƙe tana kallo tare da sauraron duk abinda ke faruwa tsakanin ma'auratan, ta riƙe baki sannan saɗaf-saɗaf ta bar gurin tana tafe tana tafa hannu gami da riƙe haɓa, irin na wanda ya ji ko ya ga abin mamaki, har Hadiza ta soma bacci Tabawa ta tashe ta,tashi-tashi Antyna wato ma bacci ki ke yi ke,ni ina can gurin neman zaman lafiyarki. Ta ce Tabawa na ƙi bacci tunda ke kin je kin yi zamanki? Ta dafa ta na taɓa ki da alheri kin san me na jiyo? Hadiza ta ce sai kin faɗa, Tabawa ta taɓa baki irin na wanda ya kawo gulma to ke me son bawa kishiya amana to gata can ita dake makaranta an biya mata Makka tare da iyayanta har fa da wata ke da ke nan kullum sai ya ɗaga ƙafarki ko oho,don kinibibi har tana cewa Hadiza fa? Cike da al'ajabi ta ce to shi me ya ce? Tabawa ta taɓa baki,ɓata rai ya yi tare da cewa,wai kiran Allah ne, wato ke bai kira ki ba, Hadiza ta ringa girgiza kai lallai gaskiyan su Tabawa ne ba aba wa kishiya amana.

Ranar kam ƙwana ta yi babu bacci,ko da ya shigo da safe lokacin da zai fita ta cije sun gaisa amma shi kanshi ya lura tana cikin damuwa, ta so mishi magana amma Tabawa ta ce in ta mishi magana ba zata ci ribar zance ba,tunda ranar zata amshi girkin ke ki kasan yanda za ki riɓa ce shi ki ji komai, amma ita ki bar ni da ita zan shirya mata gadar zare kuma zata faɗa, akwai batun da sukayi na ji.

A'isha ce a gaban Uncle ɗin ta da ke ɗauke da Abulkhairi yana cewa Beby tana duka fa? A'isha ta ce Ni ba zata min komai ba, ya ce ki dai leƙa ta window ne tunda kin dage sai kin gaishe ta. Yanda A'isha taga Jummai kuka sosai ta ringa yi,lallai wannan shine in kasan farkonka baka san tsakiya ba, ƙarshe dai dama mutuwa ce ta yi baƙi ta rame, jikinta babu sauran gashi,ga ciwuwwuka da ta jiwa kanta fuskarta tamkar ta ƙone ɗakin sai wari yake yi,da ta kalli ƙafafun ta kuwa ai sai ta kuma sa kuka dan ganin yanda wasu manyan tsutsotsi irin na toilet mara tsafta ɗin nan suna fita daga jiki, gashi sai surutai take yi in ka saurara zaka ji tana faɗin duk abinda ta aikata ne. Ta kalli A'isha ta window inda take kuka ta miƙe tsaye sai ta hango Alhajin,nan take sai ta soma dariya, Alhaji ka gansu ne? Zo ka zauna,in maka abinci? Hawaye ya kuma zubo ma A'isha, ta ce sannu Hajiya, Allah ya baki lafiya, ta maida kallonta ga A'isha ta tsura mata ido tamkar tana son tuno da ita,can sai ta ce ina yini? Sannunku tare ku ka zo? Tana ta gaida A'isha cikin kuka A'isha ta ce Uncle gurin babu tsafta ya kamata a gyara mata gurin. Ya ce Beby wa kika ga zaya iya shiga wannan gurin,duka fa take yi da cizo duk wanda ta kama sai ya yi jinya, abinci ma fa sai dai a ɗaura igiya, gidan mahaukata ma sun ƙi amsarta don ranar da muka kai ta mutum biyu ta sumar,zaman ta nan shi ne ƙwanciyar hankalin al'umma. Yaja hannunta zo mu tafi, ya lura in bai jata sun bar gurin ba sai ta ja ma kanta ciwo don kuka, ya ce ishara ce Beby Allah ya saukar mata, saboda masu hali irin nata,duk wanda bai yarda da ƙaddara ba ya zaɓi son zuciyarshi ina mai tabbatar miki da sannu zaya ga aya ta sauka a kanshi.

Cikin motar da ƙyar ya shawo kanta ta yi shiru. A'isha ta ƙara tsoron Ubangiji tare da tsinkewa da lamarin duniya,lallai kam duniya budurwar wawa ce, kuma duk wanda ya ɗau ɗamarar zamanta ya wahala, domin wanda ba a haifeshi bama jiranshi take yi,yazo ya ci yayin shi ya wuce, Allah kasa mu fi ƙarfin zukatan mu,Amin. A'isha ta ringa damun Uncle ɗin ta da son zuwa Jigawa, dole ya bar komai suka tafi. Mahaifanta sun yi murna da ganinta da ɗan jikansu. Haka nan sun sha mamaki lokacin da Alhaji Saddiƙ ya basu labarin Jummai sun jajanta mishi game da al'amarin haka nan sun yi godiya mai tarin yawa a lokacin da A'isha ta sanar da su batun aikin Hajjinsu,babu ma kamar Yaya Abdulrahman,tamkar anyi mishi albishir da gidan Aljanna,ga kuma tsaraba aka yi ta rabawa dangi na ko'ina da ina,da zasu tafi mahaifan nata suka yi mata nasiha tare da nuna mata cewa ta bi mijinta sau da ƙafa, kada ta biyewa ruɗin duniya da kayan cikinta, suka ɗauko hanya suka dawo gida.

Dawowarsu da ƙwana ɗaya suka soma zirga-zirgar gidan Nafisa, ta haifi ƴarta mace basu sami hutu ba sai da aka yi suna ta samu ƴarta Asma'u,sunan mahaifiyar Alhaji Bello,suna ce mata Husna, A'isha sun sake haɗuwa da Hajiya Aliya ta zo sunan ƴarta,Anty Nafisa nan ta buɗe bakin jaka ta ƙwashi kayan gyaran jiki, A'isha tana iyaka ƙoƙarinta don ganin ta ƙyautata wa mijinta, shima yana nuna sonta ko gaban wanene, wannan dalilin shi ne ya ƙara tunzura Hadiza sai ya kasance duk ranar girkinta ta dinga ƙorafi kenan ita baya sonta,ya fi son Aisha,kaza-kaza, shi kuma nuna mata yake cewa A'isha tana da biyayya tare da ladabi, itama in har ta bishi haƙiƙa zata iya kamo matsayin A'isha a cikin zuciyarshi duk ran girkinta ta dinga cika kenan tana kumburi ita a dole ba ayi mata adalci. Hutun A'isha ya ƙare ta tattara ta koma makarantarta tare da su Uwani,nan fa Hadiza ta soma tsiro mishi da kalolin tsirfa musamman in ya buƙace ta nan zata tirje ta ce dan yaga A'isha bata nan i, haka kawai ita da shan wahala A'isha ke morar shi, nan nema ta sako maganar batun Hajji da ya biya mata da iyayanta, shi ko ya ce ya biya kuma babu wanda ya isa yasa shi fasawa, kuma ta fitar mishi daga ɗaki taje ta riƙe kayanta,tun daga lokacin ya share lamarinta ko kanta ta kawo ɗakinshi baya sauraron ta daga baya dai ta bashi haƙuri tare da ɗaukar masa alƙawarin ba zata ƙara ba.

Ƙwanci tashi asarar mai rai, A'isha ta kuma zuwa hutu yaronta lokacin yana tafiya ya ƙara ƙyau tare da birgewa,kowa ƙaunar yaron yake yi. Hajiyarmu ta ce ba za a koma dashi ba yayeshi za'ayi. A'isha ta ce dama in zasu tafi aikin aikin Hajji nan zata barshi in ta dawo ma ba dashi zata koma ba, ta yi karatunta cikin nutsuwa, shi kuma Uncle ɗin cewa ya yi insha Allah kafin ki koma sai da wani cikin,shiru tayi mishi ya ce baki fata kenan? Ta ce ina fata mana amma sai na gama karatu bai ce komai ba cikin zuciyarshi kuwa sai ya ɗan zargi wani abu,an ya A'isha bata shan komai? Amma sai ya share wannan zargin, baya son ya zargi abu.

Dukkan ɗaukacin musulmi suna ta shirin tafiya aikin Hajji, haka ma su A'isha da mahaifanta, kasancewar wannan shine karo na farko da zata aikin hajji duk ta bi ta hana kanta sukuni burinta kawai shi ne ta ganta gaban ka'aba, Nafisa kuwa kasancewar taje ba sau ɗaya ba ba so biyu ba sai dariya take yiwa A'isha.

Tabawa ta kalli Hadiza kada ki nuna musu damuwarki bar su in sun tafi can zasu ƙwaɓe ƙila ma ya sako ta tun can ke dai kiyi ƙoƙarin zuba waɗannan ƙwayoyin cikin kayanta. Hadiza ta ce ƙwayoyin mene ne? Tabawa ta ce " Na hana ɗaukar ciki ne,in ma mace tana da cikin zubewa za ya yi." Tsaki Hadiza ta ja, Tabawa kin cika abin haushi, to kuma ce miki aka yi ita mahaukaciya ce tana ganin ƙwayoyin cikin kayanta sai ta hau sha ko? Tabawa ta dafats,saurara mana ke dai ba zaki ci ribar zance ba wallahi, ce miki aka yi zata sha? Mijinku kawai ake buƙatar ya gani,in ya gani kuwa kin san dai yanda yake son haihuwa, rigima ce zata ta shi, ballantana dama na gaya miki yana zargin tana shan wani abu, nasha jin yana ce mata ba dai ta yin tsarin iyali ko? Hadiza ta ce kai Tabawa, Allah ya biyaki sai dai ban san ya ya zanyi in sa mata ba. Tabawa ta sakar mata harara in nemo maganin in kawo miki sannan sai na koya miki yanda za ki sa? Hadiza ta ce taimakamin don Allah, Tabawa ta ce to kin dai san ita sakarya ce yanzun zata yarda da mutum, zuwa zakiyi har ɗakinta ki shiga da sakin jikinki da kuma sakin fuskarki ki ce kin zo ne kuyi sallama sannan don Allah ta yafe miki duk abinda ki kayi mata, to a nan zaki shammace ta ki saka mata. Na ce zan zo miki da lokacin da ya dace ki shiga sai na leƙo tukunna kin san za a sane in da zaya gani ba inda zata gani ta zubar ba, Hadiza ta ce to ina jiran ki sarkin ƴan leƙen asiri. Tabawa ta ce kuma ki sani in bom ɗin nan da muka ɗana ya tashi da A'isha za ki bani ƙyauta ta musamman, tare da yi mini ƙarin albashi, don na lura da ke in dai ba roƙon ki aka yi ba baki ƙyauta ba ki yin sadaka don tsabar rowar tsiya, Hadiza ta ce na ji zan miki uwar ƙwaɗayi,don ke ko komai zaki yi don ki samu kuɗi ko da halaka ne. Tabawa ta fita tana cewa,na ji dai ai halina ɗaya da uwarki, Hadiza ta ce iye? Lallai kinga gadon baccina, Tabawa ta yi wucewarta ta bar Hadiza tana surutai.

Washegari da misalin ƙarfe sha ɗaya lokacin maigidan ya fita zuwa Office. Tabawa ta shigo tana cewa ina Hadizan? Zo ki shiga yanzun wata jaka ta na nan cikin ta zaki sa, saboda ta haɗa suturarsu ciki,za yayi amfani da shi kinga zaya gani in ya zo ɗaukar kayanshi. Hadiza ta ce tana ciki kuma? Tabawa ta ce tana ciki mana kefa sokuwa ce yanzun sai ki ce sai na gaya miki yanda za ki yi ko? Hadiza ta ce ba wani sokonci,ban ga ji makirci ba, ba dole sai an nuna min sannan zan iya ba? Tabawa ta ce amma ai kin gaji asiri, makircin ma ƙila ta gurin uba ne ba'a gada ba, ta ci gaba da cewa yanzun in ki ka je kusa da jakar zaki zauna ki ba jakar baya kan gado kuma jakar take, tashi kiyi azama kada ta fito daga uwar ɗakan ta dawo falo.



######
[12/23, 11:57] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 14*



Aisha tana ta haɗa kayan Abdulkhairi,in Babanshi ya dawo za su kai shi gidan su Hajiyarmu, tare da yi musu sallama, domin tashin Asubahi za su yi, sai ta ji sallamar Hadiza cikin sakin fuska ta amsa tare da faɗin shigo, bakin gado ta zauna tare da ba jakar baya kamar yanda Tabawa ta yi mata ƙwatance. A'isha ta bar aikin da take yi don su gaisa, bayan sun gaisa Hadiza ta ce, ashe kuma tafiya ta zo? A'isha ta ce wallahi kuwa, yanzun nake cewa bari in gama in shigo muyi sallama." Hadiza ta ce, "Ina Abulkhairi?" A'isha ta dube ta yana bacci a falo, ba ki ganshi ba? Hadiza ta ce ban lura ba, to Allah yasa aje lafiya a dawo lafiya, kusa mu cikin addu'a. A'isha ta ce insha Allah ai naso ace dukkan mu ne zamu je, Hadiza ta ce to ai kin san an ce Hajji kiran Allah, kafin A'isha ta ce wani abu cikin Sa'a sai wayarta ta soma ruri,da sauri ta nufi falo domin ringing ɗin na musamman ne,don Uncle ɗin ta ne,hakan ya yi wa Hadiza daɗi, don haka tana fita ita kuma ta danna maganin ciki ta rufe ta koma ta zauna A'isha ta shigo tana waya, Hadiza ta bita da kallo tana cewa Uncle babu sauran nono fa,ya ce bana turo a kawo

Please Login or Register in order to submit comment