Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bar su kawai ya fita ta bishi da kallo fuskarta ɗauke da murmushin cin nasara tasan in ya yi arba da ita wani sabon haushin nata zai ji kamar yanda Malam ya tsara mata.

Yana ta bugun ƙofa ba ta ji ba sai daga baya, da sauri ta sallame ta nufi ƙofar, ta buɗe lokacin ya cika tamkar zai fashe "waton wani sabon salon wulaƙancin ne haka,da kimarshi da komai a ce yana bugun ƙofa ƴan aikin gidanshi suna ji,ya dubeta a zafafe, watan kina jina ina ta faman bugun ƙofa ki ka min banza ko? Cikin sanyin murya ta ce kayi haƙuri Uncle wallahi ban ji ba, ina sallah ne ta kau ce ya shige ya kalli falon ko'ina ya taɓa baki sannan ya shiga bedroom ɗin zuciyarshi na zugi so kurum yake yaga abinda zai yi faɗa a kanshi ta buɗe fridge da nufin ta bashi ruwa amma sai taga wayam ta manta ɗazunnan ta gyara shi babu komai ciki, ta dube shi yi haƙuri Uncle,ba ni da ruwa cikin fridge, ya katse ta nace nazo shan ruwa ne? Ta girgiza kai, ya zauna kan kujerar madubi ita kam gabanta ne ke ta faɗuwa, ta cire hijabinta tana ninkewa, ya zuba mata idanu can ya ce "ke." da sauri ta dubeshi "mene ne a jikinki? Ta kallo cikinta kunya take ji ta ce mishi ciki ne don haka sai ta sunkuyar da kai tana ɗan murmushi da ƙarfi ya ce "dake fa nake magana?...



######
[12/20, 19:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 6*



Ta dube shi cikin in ina ta ce shi ne dama nake ta kiranka ina son nayi maka bayanin baka saurareni ba, ya ce bayanin me? Ya ci gaba da magana cikin ɗaga sauti kada ki ce min kina da ciki, ta zaro idanu gabanta na faɗuwa, ya ce ko shi ke gare ki? Ta ɗaga kai. Ya miƙe da sauri ina ki ka samo shi? Jin furucin shi yasa ƴan hanjinta juyawa me Uncle ke nufi? Bata ankara ba sai ta ji ya cakumi wuyan rigarta, abinda za ki min kenan ko A'isha ya ɗan tausasa murya,kin dai san zuwana gurinki na ƙarshe kina haila ko? Muryarta tana rawa ta ce eh, amma bai san sanda ya ɗauke ta da wani wawan mari ba,amma me? Ya hankaɗata kan gado kin cuceni don ina neman ƴaƴa ido rufe shi kenan sai a kawo min shege? A'isha kin yi kuskure yanzun so nake ki gayan uban da ya yi miki cikin? Kuka take yi sosai tamkar ranta zai fita, ina ma ta mutu ta huta da wannan baƙin cikin? Ya ce zaki gaya min ko sai ranki ya yi mugun ɓaci? Jin shi yake tamkar ya shaƙe ta ta mutu ya huta, ya dubeta a zafafe,kiji nan kafin da safe kiyi ƙoƙarin sanar da ni kowanene ya yi miki wannan cikin,ya juya fuu ya fita tare da bugo ƙofar.

Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un,wane irin mummunan zato ne wannan Uncle za ya yi min? Ta ci gaba da kuka,ya ma ƙi ya saurare na, yau shi ne har da marinta,to ko dai ya daina sonta ne? Shin dama haka ne maza ke yi? To in haka sukeyi me yasa Abbanta ba ya yi wa Ummanta haka? Ta tsorata da lamarin Uncle bata san me zai mata ba washegari cikin kishiyoyi,gara ta san nayi tun yanzun.

Fitar Uncle Tabawa ta miƙe cikin motoci domin tana laɓe tana sauraron duk hidimar da ake yi,jin Uncle zai fito ta ruga ta ɓoye,da gudu ta nufi Hadiza tana faɗin. "Antina zo ki ji." Ta shiga rattafo mata duk yanda ta ji, ta ce matar so har da mari ta sha,kin san ta dai dai wundon su na uwar ɗakin na maƙale, ciki tayo can a makaranta an zo a yaudareshi sai kuma Allah yasa ya gane. Hadiza ta ce kai Tabawa? Tabawa ta ce na taɓa kawo miki wani labari daga baya ki kaga ba haka ba ne? Hadiza ta dafa ta,ko sau ɗaya ba'a taɓa haka ba . Tabawa lallai ki ce lokacin fitar wannan matsiyaciyar matar ya yi,dama nafi jin haushinta sai inji da waccan guzumar ta bar gani yanzun tana jan zare na barta da ma in gama da wannan ne kai naji daɗin wannan labarin Tabawa zan baki goro da safe amma yanzun bari in je gurinta a zuwan na zo in yi mata sannu da zuwa ne, Tabawa ta ce kin yi daidai tama san an sani.

Lokacin da Hadiza ta shigo ta same ta tana kuka da sauri ta ƙaraso, lafiya A'isha? A'isha ba taji shigowar Hadiza ba sai dai ta ji magana akan ta, ta ce cikina ke ciwo. Hadiza ta ce assha to bari in kira Alhajin a waya. A'isha ta ce ai ya sani ya tafi ya zo min da Likita,harara Hadizan ta sakar mata shi ne zai je yazo da Likitan? A'isha ta ɗaga kai, Hadiza ta ce, Allah ya sawaƙe ta fita. Ta je gurin Tabawa tana cewa Tabawa gaske ne kuwa labarin da ki ka bani? Tabawa ta ce me ki ka gani ke? Hadiza ta bata labarin yanda suka yi, Tabawa ta ce to ke da kin zauna ne ta faɗa miki? Ko ance miki kowa ma irin ki ne? Hadiza ta ce ƴar iska ni zata yi wa bariki,ai muna cikin gidan ma ga yanda za a ƙwashe.

Shi kam fitarshi ke da wuya ya nufi sasan Jummai,tana zaune tana tunanin kada dai ta tura shi yaje kuma komai ya daidaita tsakaninsu? Kai ina ba zai yiwu ba, domin ta yarda da Malam ɗari bisa ɗari. Sai ko ga Alhaji ya shigo tamkar wani bijimin zaki, da sauri ta miƙe Alhajina lafiya? Ya zauna yana huci, ta ce kayi haƙuri ko mene ne ya ce wane haƙuri zan yi? Ya ci gaba, wallahi ba zan haƙura da cikin da ba nawa ba, Jummai ta zaro idanu tare da dafa ƙirji ban gane ciki ba? Ya ce A'isha mana yarinyar nan zuwana na ƙarshe gurinta fashin sallah na samu tana yi, yanzun sai gata ta zo min da uban ciki don ina neman haihuwa shi kenan sai a kawo min shege? Zufa ce ta shiga keto ma Jummai,domin tana tsoron kada a juya a sake juyawa cikin ya zama na shi,ai ko da ta shiga uku.

Ta juyo tamkar ta zuga shi, amma Malam ya ce mata babu wannan aikin ta ba zai tafi da zuga ba sai da kissa ta daure ta ce to Alhaji ko dai zuwan naka na ƙarshen ne ta samu cikin? Ya dubeta ta tana hailar ne za ta samu cikin? Jummai ta kuma jan dogon numfashi,ka dai a hankali, ya ce ke ni fa ba batun hankali cikin wannan lamarin, ta ce to ni bana sone ka ce zaka rabu da ita,ga mamakinta sai ta ji ya ce babu batun rabuwa amma sai na ji uban da ya yi mata wannan cikin,shiru Hajiya Jummai ta yi ilahirin jikinta kuwa rawa yake yi. Ta daure ta ce in ka samu wanda ya yi cikin tunda mu musulmai ne sai ka tuntuɓi malamai, ya dube ta ke ce kika fini sanin yanda zanyi? Ta ce a'a ya ce ki bar ni ya miƙe ya nufi gefenshi. Da kallo ta bi shi,takan rasa gane kanshi wasu lokutan itama ɗaki ta shiga ta kira Karima Aminiyarta, don jin wane mataki ya kamata ta ɗauka don cikin nan ba ƙaramin firgita ta ya yi ba.

Tsam, ta miƙe ko jakar ratayawa bata ɗauka ba domin tasan babu ko taro ciki, ta nufi barin gidan tun kafin gari ya waye ya yi mata tijara, gidan Anty Nafisa ta yi nufin zuwa saboda yanzun dare ne.

Da safe sai ta amshi kuɗin mota a hannunta ta nufi garinsu. Kafin ma ta iso babban titi ta samu mai mashin cikin mintuna suka isa gidan Nafisa sai da ya jira ta shiga ta amso mishi kuɗin. Mamakin ganin A'isha ya hana Nafisa zama har A'ishan ta dawo daga gurin mai mashin ɗin in da suka shiga ɗakin baccinta suka zauna bakin gado, Nafisa ta zuba ma A'isha idanu lafiya kuwa? A'isha ta nisa hawayen yana zuba daga idanunta,ta shiga rattafo ma Nafisa halin da take ciki da kuma wanda ta shiga yanzun nan,baki Nafisa ta saki tana kallon ta, lamarin kamar almara, ta ce shi da kansa Brother ya ce ba cikinsa ba ne? A'isha ta ce wallahi ya ma ƙi ya tsaya ya saurareni, balle ma yasan ga yanda Ubangiji ya juya lamarin cikin. Nafisa ta ce ni ko naji mamaki, amma yanzun yanda za'ayi bari in kira Anty Fatima ba zaki tafi gida ba,nan take ta shiga kiran layin Anty Fatima ko gaisawa ba su yi ba ta shiga sanar da ita abinda ya faru, cikin tsananin mamaki Anty Fatima ta ce,kada ki bar ta ta tafi zan zo da safe.

Ranar dai A'isha bata runtsa ba,ƙwana ta yi kan sallaya tana me zubar da hawaye, tare da sanar da Allahu matsalolinta. Ko kusa bata so ta tsani Uncle shi yasa take yawan ba shi uzuri, yanzu da haka zuciyarta na bata tabbacin in yaji yanda lamarin ya kasance za ya yarda da ita,ƙila ma ya bata haƙuri.

Shida daidai na sai ga Anty Fatima, ta tausayawa A'isha matuƙa yanda taga yarinyar ta ƙare ta fita daga hayyacinta. Nan Fatima ta shiga faɗa tana cewa, lallai Brother irin tsirfar da ya kama kenan Nafisa ta ce kin san ba haka yake ba,ni dai na ce ba haka aka barshi ba. Fatima ta ce shi dai ya sani yanzun dai ki tashi muje gidan Hajiyarmu ke Nafisa tunda mijinki ba ya nan ki zauna duk yanda aka yi zaki ji. Nafisa ta ce muje kurum babu wata matsala zan masa waya ai baya gari ne. Fatima ta ce shikenan mu je, cikin matar Anty Fatima suka tafi. Hajiyarmu ko tashi daga kan sallaya bata yi ba,ta ji sallama ta ɗago idanu ta dube su, suka zauna kan kafet suka jira har ta shafa, sannan ta dubesu ta ce lafiya? Nafisa ta ce da sauƙi, Hajiyarmu kallon A'isha kurum take yi. Anty Fatima ta ce wallahi Hajiyarmu Brother ne ya taso A'isha fa, gidan Nafisa ta ƙwana,jiya,-jiya daga dawowarta daga makaranta har an soma tsiya. Nan ta shiga rattafo ma Hajiyarmu Nafisa tana ƙara bayani, Hajiyarmu tayi shiru ɗakin ya yi tsit suna sauraron hukuncin da zata yanke. Ranta ɓace amma ba kasafai mutane suka cika gane ɓacin ran nata ba sai ƴaƴanta, ta dube su Nafisa ke da Fatima ku tashi ku koma gidajenku ita A'isha ku barta nan suka ce to, suka miƙe suka fito bayan sun yi musu sallama.

A'isha tana can maƙale gefe, Uwani ta shigo ɗauke da karin kumallon Hajiyarmu, ta dire a gaban Hajiyar, Hajiyarmu ta ce A'isha me ki ke son ci?

A'isha ta ce, sai anjima yanzun bana jin yunwa, to kurum Hajiyarmu ta ce bayan fitar Uwani, Hajiyan ta ce A'isha ki zama jaruma ba ki ga komai ba game da halin namiji,in zaki bincika duk matan duniya komai matsayin mace komai mulkin ta zata sanar da ke cewa ta yi kuka saboda namiji,wata ta yi shi a fili wata kuma ta yi shi a ɓoye, ta share hawayenta ta zauna a ɗakinta kema ina so ki saba na sani kina da haƙuri, to ki ƙara. Sannan ki dage da addu'a wata rana za ki ci ribar haƙurin ki, da addu'o'inki bana so ki sama ranki cewa an mishi asiri ne da sauransu,ki yarda a ranki cewa jarabta ce daga Allah, sannan ko a waya bana son mahaifanki su san ga halin da ki ke ciki,ki zama mai ɓoye sirrinki zaya kasance ki sanar da su hankalinsu ya tashi ke kuma nan ku zo ku shirya da shi kin ji duk abinda na faɗa? Kan A'isha yana ƙasa ta ce,eh insha Allah zan kiyaye. Hajiyarmu ta ce na gode yanzun ina son ki ci abinci kinga ba ke kaɗai ba ce, sannan ki yi wanka,matso nan ki zuba abinda ranki ke so, sannan ta miƙe in kin gama kiyi wanka bari in hau gurin Alhaji, A'isha ta ce to.

Cikin natsuwa ta yi wa Alhajinmu bayanin komai,shiru ya yi na tsawon lokaci, can ya nisa ya ce "Shikenan ki barta a nan kada a neme shi." Hajiyarmu ta ce, "Ni lamarin shi yanzun yana bani mamaki, haka kurum duk ya bi ya ruɗa kanshi, ya hana kan shi sukuni." Alhajinmu ya ce,ki bar ni dashi kawai wannan karon, zan taka mishi birki, Hajiyarmu ta ce bari in shirya maka abin kari, ya ce inda tuwon nan nafi son shi, ta ce da akwai bari inje in ɗumama maka,ta fita shi kuma ya ci gaba da nazarin matsalar ɗan nasu,ko harkokinshi yanzun ba kamar da yake tafi da su ba,lallai dole ne ya zauna da yaronnan in har yana da wata matsala ne mu sani.

Daren Alhaji Saddiƙ bai runtsa ba,ya yi duk iyaka nazarin da ya kamata ya yi amma zuciyarshi ta ƙi yarda cewa A'isha zata aikata wata alfasha,ya tambayi kanshi cewa to ko cikin ruwa tasha? Domin dai ya tabbata zuwanshi na ƙarshe tana Haila. Hajiya Jummai ta so ta lallasheshi amma ya dakatar da ita kan cewa ta barshi ba ya so a dame shi.


**** ***** *****

Yana dawowa daga sallar Asubahi, gefanta ya nufa dole ne ta mishi bayanin inda ta roro wannan ciki? Ko tana nufin taje jami'a ne idanunta sun buɗe? Da wannan tambayar ya tura ƙofar ko ina ya duba bai ganta ba don haka sai ya za ci tana bayi,shirun da ya ji ya yi yawa ne yasa shi duba bayin,bata ba dalilinta, ya tsaya shiru sai kuma ya fita gurin Baba maigadi ya nufa,bai amsa gaisuwar da Baba maigadin ke masa ba, tambaya kurum yake masa,Baba ko kaga fitar Beby? Baba maigadi ya ce gaskiya ba wanda ya fita yau, sai dai kuma jiya da dare Hajiyar da ta dawo ta fita, amma bata dawo ba, ya ce ita nake faɗa,tun jiya kenan ta fita? Baba ya ce,ƙwarai kuwa ya juya cikin sasan Jummai zuciyarshi tana harbawa, to ina wannan yarinyar ta nufa? Me take nufi? Ya zauna bakin gadonshi ya lalubo wayarshi ba za ya iya tuna rana ta ƙarshe da ya kira wayarta ba,nan ya lalubo lambarta ya shiga kira, sai ta yi tayi har ta yanke ba'a ɗaga ba, shi bai ma san bata ɗauki wayar ba ya fito ya shiga mota sai da ya hau titi sannan ya soma tunanin ina ma zaya nufa ne yanzun? Ya kira Nafisa don yasan yanda suke,ya ce mata sister ko A'isha ta zo? Nafisa ta ce, a'a ta dawo ne? Ba tare da ya bata amsa ba ya katse wayar, gidansu Hajiyarmu ya nufa babu kowa cikin falon kai tsaye ya nufi ɗakin Hajiyarmu daidai lokacin da A'isha ke shan wani ɗan kunun gyaɗa da ta tarfa cikin kofi don dai kada Hajiyarmu ta ce bata ji maganar ta ba,yana ganin ta sai ya ji wani sabon ɓacin ran.

Ke me ya kawo ki nan gidan? Kina zaton za'a tursasa ni ne in amshi cikin da ban san daga ina yake ba? Ta zuba mishi idanu, muryarta na rawa ta ce, "Uncle da ace zaka saurareni da ka gano yanda Ubangiji ya zo da al'amarin. Ba zan saurari shirme ba, kuma ina so kiyi maza ki fita daga nan gidan, muryar Hajiyarmu ta katse shi gidan ai bana zaton naka ne ko? Ya juya da sauri, kada ku yarda da dukkan abin da yarinyar nan zata gaya muku."

Hajiyarmu ta ce, "to ubana." Jin haka yasa shi yin shiru tare da kauce mata daga hanya. Ta nuna ƙofa sai anjima ko? Zai yi magana ta haɗe fuska,sai ya fita domin babu shaƙuwa tsakanin su ko in ce suna jin nauyin juna.

Saman Alhajinmu ya wuce, Alhajin yana cin tuwanshi, Uncle ɗin ya shigo da sallama,kan kafet ya zube ya dubi Alhajinmu ga mamakin shi sai yaga fuskar Alhajinmu tamkar hadarin mangariba murtuk, iya tsawon rayuwarshi bai taɓa ganin Alhajin cikin wannan yanayin ba,nan take fargaba gami da tsoro suka shige shi cikin sanyin jiki ya zauna kan kafet ya soma da gaida Alhajin a dake kuma ba tare da ya dube shi ba ya amsa zai tashi Alhajin ya dakatar dashi da hannu.



######
[12/20, 23:02] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 7*


Ya koma ya zauna cike da tunanin me zai biyo baya,ya san Alhaji tamkar yunwar cikinsa, dattijo ne mai sauƙin kai mai zafi kuma ga wanda ya taɓa shi, sai da ya gama karyawar shi tsaf sannan ya dube shi jeka ɗauki matarka kuje gurin Doctor gani nan zuwa,za ya yi magana Alhajin ya katse shi da cewa, kada ka ce min komai bana son ji, Uncle ya miƙe ba tare da cewa ƙala ba, ya fito yana tunanin shin me yarinyar nan ta faɗa ma mahaifansa ne da zafi irin haka? Na shi ganin ai ita ce da laifi,laifin ma mai girma.

Ɗakin Hajiyarmu ya koma shima ranshi a ɗaure ya ce ke taso, Hajiyarmu ba ta ce ƙala ba, ganin haka sai A'isha ta miƙe ba tare da tasan inda za suje ba,ko cikin mota ƙala bai ce mata ba ita kuma ba tace mishi ba, sai dai taga sun tsaya asibiti. Tun kafin su iso Likitan yasan da zuwansu don sun yi waya da Alhajinmu, don haka suna zuwa Likitan ya shiga yiwa A'isha tambayoyi.

Tun yaushe rabonki da al'ada? Uncle ya zuba mata idanu yayinda shi kuma Likitan yake ƴan rubuce-rubuce, ta ce yau ƙwana shida kenan, Likitan ya ajiye biron hannunshi ya ɗora hannuwanshi kan teburin shi tare da maida hankalinshi kacokan gurinta,kina nufin duk wata kina al'ada? Ta ce eh, cikin ya shiga ne bayan wanda ya fita anan watanni bakwai da suka wuce? Babu wanda ya ji takun sawun Alhajinmu sai kaɗai muryarshi suka ji ya ce ai cikinne bai zube ba, dukkan su suka juya suka dubeshi,ya ƙaraso yana ce ma Likitan shi yasa na ce ka ciro fayal ɗin ta ka duba sannan ka duba ta, Likitan ya bashi gurin zama sannan ya ci gaba da aikinshi, Uncle kuwa jinsu kurum yake yi yanzunne ya gano zancan da ta shirya wa tsofaffin nashi suka hau kai suka zauna, bayan tambayoyi da bincike gami da aune-aune sai kuma ya kira wani Likitan daban shi kuma (scan) ya yi mata sai da ya fitar da sakamakon sannan ya ba Doctor ya fita nan dai Doctor ya tattara bayanai ya tabbatar musu cikin nan shi ne dai bai faɗi ba, sannan yana cikin ƙoshin lafiya. Uncle ya yi zaraf ya ce, "Likita dama in mata suna da ciki suna fashin sallah ne?" Likitan ya zauna ya yi mishi dogon bayani tare da tabbatar mishi cewa akwai matan, kuma itama hakanne ya faru gareta, duk da yanda yake jin tsanarta cikin ranshi amma wani sashen na zuciyarshi na murna da wannan labari.

Ƙwarai ya so ya tafi da ita gida, amma sai Alhajinmu ya ce ya kai ta gidanshi can gurin Hajiyarmu, duk da ba taga canjin komai daga gare shi ba,ta ji daɗin yanda ya amince da cikin koda suka dawo har yanzun Hajiyarmu bata sakar mishi fuska ba, ya fito ya nufi gida.

Hajiya Jummai ta ƙosa ya shigo domin ta ji me yake faruwa, da kanta ta taka har gefen A'isha, amma bata nan lamari fa zaya jagule mata in bata yi Sa'a ba,ga Hadiza kuwa murna ce fal zuciyarta,tasan ƙarshen A'isha ne ya zo,wa ya sani ma ko tun jiyan ya danƙara mata saki? Inji Tabawa, Hadiza ta ce Allah yasa hakanne. Lokacin da maigidan ya dawo bai ce komai ba, Jummai kuwa ta yi ta maza ta daure bata ce mishi komai ba har sai da ya yi wanda ya zauna cin abinci, ita kuma tana kusa da shi tana zuba kissa da salo,can ta ce waini Alhaji daga masallaci ina ka nufa? Ya dubeta, gidan su Alhajinmu naje. Suna lafiya? Ya ce lafiyarsu lau, suna gaida ku." Ta yi shiru don tana son sanin ta ina zata fara batun A'isha? Can sai ta kira Uche wanda yanzun ta ɗauke shi zuwa sasanta, ta ce shirya breakfast ka kai wa A'isha ko? Uche ya ce to zaya tafi sai Alhaji Saddiƙ ya ce bata nan,da sauri ta sha mur sai ka ce gaske,bata nan ina ta je Alhaji kada dai ka ce min ka saki yarinyar nan? Ya dubeta dama na ce miki zan saketa ne? Cikin sanyin jiki ta girgiza kai alamar a'a, ya ce to ƙyamin wannan tambayar, kiyi harkar gabanki wannan ba matsalarki ba ce,ta karkata kai Allah ya baka haƙuri ni kaina bazan so ka rabu da ita ba,dama ganin yanda ranka ya ɓaci ne. Ya miƙe tsaye ya nufi ɗakinshi ba tare da ya ce mata ƙala ba.

Lamarin fa ya dagule wa Jummai lissafi,in maigidan ya yi kamar zaya juyu son rai sai kuma ya murɗe, tana fa so ta san shin ina aka ƙwana ne batun cikinnan? Dole ta je gurin Malam yau saboda ya yi mata bayani filla-filla, Lallai kam zata ga boni in har su Hajiyarmu suka ji batun ciki.

Ɗakin A'isha yana daf da na Hajiyarmu,tuni tasa aka gyare shi A'isha tana ciki a ƙwance tunanin rayuwa kawai take yi, ashe akwai wani lokaci da zai zo Uncle ɗin ta ya juya mata baya? Musamman irin wannan lokacin da ya kamata ace ya jata a jiki,ya so ta ya riritata, amma ba komai ta sani jarabta ce ta Ubangiji yana jaraba bayinsa ta kowace hanya, ta yarda itama yana jarabata ne don ya gwada imaninta, Uncle kuwa tana ta ƙara ba shi uzuri ba ta so ta tsane shi.

Yau ƙwananta uku a gidan tana cin gyaɗa dafaffiya da ta ce tana so Hajiyarmu tasa aka dafa mata, Nafisa ta shigo da sallama tare da ƴar tsokana tana cewa mai ciki Uhum ga ni nan tafe, A'isha ta yi murmushi ta ce Anty Nafisa ce yanzun? Ta zauna tare da ɗiban gyadar tana cewa tun ɗazun na zo ina gurin Hajiyarmu ne, A'isha ta ce ina yini? Suka gaisa ta ce Yaya Bebynmu? A'isha ta yi ɗan murmushi ta juya zancan da cewa yau fa sauran sati ɗaya mu koma makaranta, Nafisa ta ce har an gama yajin aikin? A'isha ta dubeta da sauri ba yajin aiki mukayi ba. Nafisa ta ce to tabbas ni naji da kunnena makarantarku suna barazanar tafiya yajin aiki,in har ba a biya musu buƙatunsu ba. A'isha ta ja tsaki, Allah yasa kada a tafi. Nafisa ta ce amin, Brother ya zo kuwa?

A'isha ta yi guntun murmushi, ina ganin abubuwa sun mishi yawa ne shi yasa, Nafisa ta kalleta cike da tausayawa,ke dai A'isha ba ƙya son laifinsa ne, amma in yana gari kullum sai ya zo gidan nan, yanzun dan kina nan ne shi yasa ya daina zuwa. A'isha ta ce to ni me zan ce? Nafisa ta ce, Allah duk da ke ma shiyasa yake miki wannan abin,ni duk son da nake maka wallahi in ka taka ni zan nuna maka kuskuran yin hakan. A'isha ta ce to Anty Nafisa kin san ko na mishi wani laifi ne? Ai da baya min haka, sai in ga tamkar nayi butulci in har na manta irin rainon da Uncle ya yi min a baya. Nafisa har da tagumi tana kallonta, kafin ta ce A'isha ke kam ban ma san irin ki ba,ko son shi ne ya yi miki yawa? Oho, A'isha ta yi guntun murmushi, sannan ta ce ke ba ki son Uncle Bello? Nafisa ta ce so kai amma fa bashi zai hana in ya min wulaƙanci in kasa ramawa ba.

A'isha ta tsura ma ƙasa idanu,son kawai take ta tuno ta ya ya zata iya yin sa'insa da Uncle ɗinta? Ko rama wulaƙancin da ya yi mata? Nata ganin yana mata hukunci ne sakamakon wani laifi da tayi mishi, damuwarta ɗaya shine ya sanar da ita wannan laifin ko zancan ciki ta mishi uzurin rashin sani ta kalli Nafisa tare da girgiza kai ni kam Uncle yana da wata irin ƙima a idona,ba zan iya ɓata mishi rai matsawar ina sane ba, kuma ko

Please Login or Register in order to submit comment