Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka ji?" Ta girgiza kai, ya ce to in ba kin ji haushi ba, menene na cewa kin fasa? Kina nufin kada in amso mata magani? Ko don ba ke ba ce? Mamaki ya cika A'isha, ta shiga kallonshi a tsorace, muryarta tana rawa ta ce ba fa nufina kenan ba, ya katse ta, "Ke da Allah yi min shiru,ke in kina naki ciwon menene bana miki don kawai na amso mata magani za kiyi fushi? To ki fashe duk wadda na aje sonta nake don ki ji ki sani." Ya juya ya fita.

Kanta ya ɗaure matuƙa,lafiyan Uncle kuwa? Itama ta miƙe ta shiga zirga-zirga a tsakar ɗakinta, ba ta taɓa shiga cikin irin wannan halin ba, ba ta taɓa ganin Uncle ya faɗa irin haka koda ga wani ba bare ita. A ƙarshe ta ba wa kanta laifin cewa ƙila ya ji haushi ne ba ta bi umurnin shi ba,in ya dawo zata ba shi haƙuri. Ranar dai yini ta yi tana zubar da hawaye.

Shi ko yana fita ya shiga mota har zaya tada Jabir ya rugo da gudu ya ce, "Gani maigida, ya bashi makullin ya matsa gefen direba, maimakon baya da ya saba zama. Ya ƙwantar da naganshi a kujera ya yi ajiyar zuciya, ya lumshe idanu. Yana son tuno meke damunshi ne? Jabiru ma ya lura yau kam maigidan nashi ranshi ya na ɓace ne. Ko a Office bai ba wa sakatariyar sa damar ta shigo masa da kowa ba, duk da jiran da mutane suke mishi. Ya lumshe idanunshi yana karanta sunayan Allah,kusan minti talatin sannan ya soma ganawa da mutane. Kaɗan-kaɗan zuciyarshi ta soma sanyi, ƙarfe biyu yana zaune a ƙayataccen gidan cin abincin da nan ya kan ci abincin rana. Yana so ƙwarai ya sha zoɓon A'isha, ya ɗauki waya ya kira ta lokacin tana zaune kan sallaya har lokacin tana zubar da hawaye gaya ma Allah take yi da sauri ta miƙe ta ɗauki wayar, muryarta a dusashe ta ce, "Salamu alaikum." Ya amsa sai lokacin ya ke tunawa sun fa ɗan samu matsala da safe, take kuma ya ji a ranshi tamkar bai mata adalci ba, ya amsa da wa'alaikumus-salam , Beby zan samu zoɓon kuwa?" Ta ce, sai dai a dafa, ya ce to Uche za ya kawo min ko?" Ta ce eh, ta miƙe ranta ya yi ɗan sanyi ta shiga kujuba-kujubar dafa zoɓo.

Cikin mintina ƙalilan ta gama, musamman da ya ke tana da ƙanƙara ta kira Uche da wayarta. Tabawa ƴar rahoto tana kallon lokacin da Uche ya amshi ƙwando ya fita,ta shiga gurin Hadiza. "Antina wai menene ake fita dashi cikin ƙwando kullum?" Hadiza ta taɓa baki,zoɓo ne wahalalliya kullum sai ta dafa shi an kai ma maigidanmu." Tabawa ta ce, amma ya kamata a ɗauki mataki kan wannan zoɓon, Hadiza ta ce,ƙyale ta tayi,ni dai ba zan iya wahala ba. Tabawa ta gyara zama ta riƙe ƙugunta tare da miƙa kai ta ƙanƙance idanu, "Antyna an ce miki haka kawai Hajiya Lanti ta kawo ni aiki nan gidan? Ta cigaba to in baki sani ba bari na sanar da ke, sai da na ɗauki alƙawarin tarwatsa gidan nan tare da karɓar miki ƴanci gurin mijinki,ko kin san ni ce na kawo shawarar ace kina da ciki? Shin haka bai miki daɗi ba yanzun? Cikin mamaki Hadiza ta matso daf da Tabawa ta ce ,"Da gaske ki ke yi?" Tabawa ta ja tsaki "An ce miki a banza maza suke shakkar aurena? In da zaki ji tarihina tun ina ƴar ƙanƙanuwata sai kin sha mamaki, domin tun ina ƴar shekara uku na kashe auren wata da Ubana kan daddawa, sannan na hana duk matar da ya auro zama,to ki gaya min auran wa zan bari? Hadiza cikin jin daɗi take jinjina kai, sannan ta ce, "Tabawa nayi farin cikin samun ki, to yanzun me ki kace a batun zoɓo?" Tabawa ta ce, "Yauwa kin san takan zoɓon nan sai tafi ku ƙwarjini? Don haka ki bar batun zoɓon a hannuna kina nan za a gabza rigima takan tsinanne kuma a daina yin shege,in kun bar ni da yarinyar nan ba sai an kai ta gaban malami ba,tsabar kissa ma ta isheta, ita kuwa waccan tsohuwar guzumar biyu zamu haɗa mata." Hadiza cikin murna ta kai hannu suka tafa da Tabawa, tare da cewa. "Haka ni ke son ki ƴar gari."

Misalin ƙarfe shida saura ya shigo, Tabawa ce kurum zaune a falo tana kallon T.V da sauri ta miƙe tana mishi sannu Alhaji sannu da zuwa,ya ce yauwa ya nufi ɗakin jummy. Ta yi karaf ta ce "Ta fita Alhaji bata nan." Ya dubi Tabawa,a ranshi baya son irin waɗannan mutanan, ya nufi ɗakin A'isha,tana zaune kan kujera fuskarta na kallon T.V amma zahiri ba tasan me ake yi cikin aƙwatin ba, har yanzun in ta tuna kalaman Uncle suna soya zuciyarta,sam bata ji murɗa ƙofar shi ba, kuma bata ji sallamar shi ba. Ya tsura mata idanu ya ce "Beby." Ba ta ji ba,ya sake cewa "Beby." Da ɗan ƙarfi ya yi maganar, firgigit ta ce "Na'am."



######
[12/18, 21:24] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 3*



Ta dubeshi ta zamo ƙasa tana mishi sannu da zuwa. A sanyaye ya amsa ta miƙe kamar yanda ta saba,ta ɗauko mishi ruwa ta cika kofi ta miƙa mishi cike da girmamawa,ya amsa yana kallonta, ya zauna yana sha,yasha kusan rabi kafin ya dube ta, Beby ba ki da lafiya ne? Ta dube shi hawayan da take ɓoyewa suka sulalo, cikin rawar murya irin ta masu kuka ta ce "Uncle don Allah ka yi haƙuri." Ya matso ya ɗagata ya rungume yana shafa kanta,ina tsokanarki ne fa Beby,ba wai faɗan gaske nake miki ba, daina kuka ya shiga share mata hawaye,kusan minti biyar yana lallashinta sai da yaga tabbas ta haƙura sannan ta yarda kan cewa yana mata wasa ne sannan ya fita.

Tabawa tana son sanin me yasa Alhaji ke daɗewa a ɗakin A'isha, duk in ya shiga ba ranar girkinta ba? Kuma me yasa sauran ɗakunan baya daɗewa? Ɗakin Hadiza ya nufa wadda tuni Tabawa ta sanar da ita dawowarshi, ta kuma bata shawarar cewa tunda ita ce dashi ta aje ciwo ta tashi ta yi shirin amsarshi, ta kuma ce wannan garin maganin da na baki ki tabbatar cewa kin yi tsarki dashi." Ta juya da sauri zata fita don kada ya isko ta ciki,ta juyo ta ca "Af,na manta ki tatsi kuɗi dai." Ta fice dai-dai lokacin da shi kuma ya fito daga gurin A'isha kamar ya wuce sai kuma ya tuna ya bar ta babu lafiya,don haka sai ya shiga. Tana cire kaya zata shiga wanka zaninta na ɗaure a ƙugu ta cire riga ta juya tana mishi sannu da zuwa,ya dubi ƙirjinta ya kauda kai, ya ce kin samu sauƙi kenan? Ta yi fari tare da cewa sosai ma,ya ce mun gode Allah, bari in shiga in ɗan watsa ruwa kafin a kira magriba.

Bayan sallar isha'i ya gama koman shi har yanzun zuciyarshi tana tana tausaya ma A'isha tana ƙara son Aisha tana muradin yarinyar sosai, ya kasa sukuni saboda ɓata mata ran da ya yi gani yake har yanzun tana can ranta ɓace, saboda bata iya fitina ba, ya ɗauki wayarshi ya kira ta ta ɗaga ya ce, "A'isha me ki ke yi ne yanzun?" Ta ce, "Ina kan sallaya ne ina Istigfari yau duk ban samu zama ba sai yanzun." Ya ce, "Allah sarki, Bebyn Uncle yau ya ɓata miki rai ko? Kiyi haƙuri..." Ta yi saurin katse shi da cewa,kar kace haka Uncle,kada ka bani haƙuri,ba ka min laifi ba,kai babba ne ba na zaton zaka yi abinda zaya sa har ka bani haƙuri,ta yi ƴar dariya,mun wuce gurin komai ya wuce, ya ce "shikenan Beby kiyi bacci tare da mafarki mai daɗi" ta ce kaima haka.

Sha ɗaya da ƙwata Hadiza ta shigo ɗakin maigidan, lokacin yana zaune gaban laptop jikinshi sanye da fararen kar ɗin kayan bacci, ya ji shigowar ta amma saboda bata yi mishi sallama ba sai yaƙi ɗago kanshi,ta zo ta zuba yatsunta a kafaɗarshi, lokaci guda kuma ta sumbaci kumatunshi, har lokacin share ta ya yi,ta manna ƙirjinta da bayanshi tsaf ya tsaya sannan ya ce wai Hadiza yaushe za ki koyi shiga wuri da sallama ne? Ta sa hannu ta matsar da laptop ɗin,ta ƙwanta a cinyarshi ni da ɗakin mijina sai nayi sallama? Ya ce ko ɗakinki zaki shiga ya dace kiyi sallama,tasoma yi mishi wasu salon nata da ta haddace su, na jan hankali,kafin wani lokaci ta zurma shi sai da suka yi nisa ya ɗanɗani maganin ta lura kuma ya soma zaucewa, sannan ta yakice shi ta ɓata rai, ya kasa ɗaurewa ya soma lallashinta ta ce ita shikenan kullum sai dai ya ƙwanta da ita ba ya bata komai,ta gaji, ranshi ya ɓaci amma ba zaya iya haƙura da abinda ya ɗanɗana ba, cikin zaƙuwa ya ce gaya min me ki ke so tunda ke ba zaman aure ki ke ba,babu yanda za'ayi in amshi haƙƙina gare ki sai na biya? Ta ce zaka sai min mota? Ya ce a'a ki je abinki, ta ce to in zaka bani dubu ɗari to in ba zaka ba ni ba shikenan. Ta kuma ƙwanta,don ta sani dole ne ya dawo mata tunda shima ba baya ba, ballantana ya dangwalo wannan laƙanin nasu wanda suka yi wa laƙabi da sa maigida hauka, yanda kuwa ta yi tunanin haka ne kasa jurewa ya yi sai da ya nemo ta tare da amincewa zaya bata dubu ɗari, amma abinda ya ba shi mamaki irin daɗewar da ya yi har kusan Asubahi ya kasa biyan buƙatar shi, sai da ƙyar, tun a nan ya soma zargin ta yi amfani da wani abu tunda yasan kan shi.

Hajiya Kari ta kalli Hajiya Jummai," ke matsalarki kenan, kullum in an ce miki ga wani malamin sai kina gida ba su iya aiki ba,kin fi son na daji ko na ƙauye, alhalin irin ɓarnar da na gidan keyi,zaki sha mamaki" Jummai ta ce to ai ni sai in zata na cikin gari imani ne dasu ba za suyi maka wani abin ba, Karima ta ƙwashe da dariya sannan ta ce, "Bari in sanar da ke wani abu,kin ga wannan malamin da na ce muje gurinsa? Bata jira amsa ba ta ci gaba "Tantirin malami ne,kin san mun ci karo da gwamnan garin nan a gurin shi ranar da na je da daddare? Jummai ta ce, ke haba? Kari ta ce, wallahi ban ma gane shi ba shi kaɗai ya zo a sace, malamin ke faɗa min." Jummai ta ce in ko haka ne muje domin duk wanda ki ka ga ƴan siyasa suna zuwa gurinshi kin san ya yi ne. Karima ta ce haka ne, yanzun dai abinda nike so da ke in mun je ya buga bai ga mutuwar kishiyoyinki ba, to sai ki ce mishi ya yi miki na wani abin abu ko ciwo ko hauka,ko ki dinga haɗa su husuma da maigidan,ke kuma ki koma kiyi ta lallashin mijinki."

Jummai ta ce "ai ni na tsani in gansu ne a gidan,Kari ta ce in lokacin mutuwarsu bai yi ba ya za kiyi? Jummai ta ce haka ne, tunda gashi nayi-nayi ɗin sun ƙi mutuwa, musamman wannan A'ishan duk nafi jin haushin matsiyaciya, wallahi da za a bani bindiga ace in kashe wanda na fi ƙi ko? Wallahi Kari A'isha zan kashe ita ce mutum ta farko da ta karya min ƙwarina, irin kuɗin da na narkar kan ta mutu yarinyar nan ko ciwon kai bata yi ba, sai ma ɗaukaka da kullum take samu gurin miji, nasara ɗaya na san na samu kanta shi ne cire cikin nan nata." Karima ta ce, "yanzun dai in mun je gaban Malam ki baje kolin matsalolin ki. Jummai ta ce shikenan.

Misalin ƙarfe huɗu suka isa gidan Malam, Kari ce ta zaɓar musu wannan lokacin a cewarta ba'a cika samun layi ba, mutum biyu suka samu. Ɗaya a ciki ɗaya na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ya jera a cikin zauran nashi,don zaman jiran shi. Suka dubi na zaunen suka ce da baƙi ne ko? Ta ce eh. Jummai ta kuma kallon matar lallai wannan mutumin da gani mai yi ne, tunda ta ga irin waɗannan mata.

Tunanin ta ya tsinke lokacin da taga waɗanda suka fito daga cikin ɗakin Malamin suka kalli juna ita da Karima kamar yanda suma waɗanda suka fito daga ɗakin Malamin suka kalli junansu, mai jira ta shige gurin Malamin daidai lokacin da Hajiya Kari ta ce (cikin kissa irin ta matan bariki) a'a Hajiya Lanti duniya ashe kema ki kan zo wurin Teacher? Lanti ta gyara zama cikin ƙarfin hali ta ce, a'a ai mu sai da su muke iya kama gashin kuma ko'ina sai mu cinye mu bada siɗi." Karima ta ce,ana ki tunanin kenan, tunda dai jin ta take tamkar ta dawo ta koma. Hadiza kuwa ita ma duk ta warware kallon kallo suke yi wa juna, Hajiya Lanti ta kama hannun Hadiza suka tafi. tana cewa wa kada ki damu ni dama ai na daɗe da sanin Jummai a wannan fagen sai dai ita da kanta ta sheda cewa ko gidan giya akwai babba,ta jima da sanin cewa ina samanta.

Ita ko Jummai ta kalli Kari ta ce, "Anya zamu shiga gurin Malamin nan? Kari ta ce, shiga kai,in kinji shiga ɗaya kenan." Ta ci gaba da cewa, "ke dai shawarata da ke ɗaya ita ce,ki saki kuɗi in har ki ka cire maƙo, to har sirrin su sai mun ji a gurin shi." Jummai ta ce kuma zai faɗa? Kari ta ce, sosai ma,in kin ji faɗi ɗaya kenan. Da zaki ji tawa ma tashin farko ki bashi kujerar Makka,kin san Allah da kin sha mamaki." Kafin ta ce komai har ta ciki ta fito,dan haka Kari ta yi saurin jan hannun Jummai suka shiga.

Yana zaune kan wani farin ƙaton buzu, gabanshi wani ƙaton carbi ne da wata ƙasa cikin faranti ko ina in ka kalla zaka ga kaya,ƙwalabe ne, litattafai ne da dai sauransu, suka zauna kan tabarma,ya ɗago ya zuba masu idanu zuwa can ya ce "Hajiya sannunku da zuwa,a tare suka amsa sannan suka gaidashi, Kari ta fara da cewa, " Na zata baka gane ni ba" ya yi ƴar dariya sannan ya ce me zai hana ni gane ki Hajjaju? Ina fatan dai aikin naki ya yi ƙyau, ta ce fiye ma da yanda na zata, shine dalilin da yasa na kawo Aminiyata domin tata matsalar ta doke tawa,Malam ya jinjina kai ya miƙa ma Jummai ƙaton carbi tare da cewa gashi ki ɗauki ɗaya, har sau uku tana zaɓa sannan ya bubbuga charbin a ƙasa ya riƙe shi jim ya ce Hajiya kina da abokan zama, kuma ba ƙya buƙatar zama da su ko? Ta gyara zama, hakane, ya ce ya ya sunannasu? Ya jawo tiren ƙasar gabanshi ta ce "Malam Hadiza da A'isha, amma nafi son komai ya fara takan A'isha,don tafi shige min gaba,na tsani yarinyar sosai. Ita ce ta soma karya min gwiwata, ta karya min shirina a cikin kishiyoyin da ake min ita ce ta fara kai labari har ma ta buɗe fagen da aka ƙara min wata kishiyar, cikin zafin rai ta ke maganar. Malam ya ɗaga mata hannu ya ce, bari mu bincike su mu gani, ya ɗan jima yana zane zananshi da ƙasa cikin farantin, ya yi ya share,yana girgiza kai har ya gama, ya ɗago kai ya dube su, dukkan su sun ƙagauta da son jin sakamakon. Ya yi gyaran murya ya zuba musu idanu tare da fara yi musu bayani kamar haka.

"Wato ita wannan A'ishan da ki ke faɗa ta banbanta da sauran mata da yawa, tauraronta yasha banban, wani tauraro gare ta mai ƙarfi wanda yana wahala in kin tara mata dubu da wuya ki samu ɗaya mai irin shi, duk wadda ta kasance tana da wannan tauraron yana wuya ayi mata sihiri ya kamata, sannan duk inda ta shiga zata kasance mutane na sonta don zata kasance mai ƙwarjini,kin ga ke nan dole ta fi ku samun shiga gurin maigidaku,da ma danginsa." Jummai ta soma share zufa, "to yanzun Malam ya ya za'ayi mata?" Ta ci gaba, "shi yasa nike ta tafka asarar kuɗina?" Malam ya ce, wannan shine gaskiyar magana, batun abinda zamuyi mata kuwa sai dai mu haɗa da maigidan naku in muka biyo mata ta bayan gida zai fi mana sauƙi, ita ko waccan yanzun zamu duba muku ita." Jummai ta yi karaf ta ce, "Malam ita ce muka ga sun fito daga nan ita da Hajiya Lanti." Ya zuba mata idanu, "kina nufin Hadizar Lanti ce ɗayar kishiyar taki?" Ta ce "Eh." Ya yi ɗan murmushi, "wannan nasan kowace ce bana buƙatar duba komai kanta."

Hajiya Kari ta ce," To amma hakan ba zaya hana ayi mana aiki ba dai ko?" Ya yi ɗan murmushi, "Sam illa dai wadda tafi ƙin jakarta aikinta ya tafi dai dai,in ko mutum ya so jakarshi nima in riƙe aikina." Jummai ta buɗe jakarta ta ciro ɗaurin ƴan dubu-dubu ɗai-ɗai ta dire gabanshi,sannan ta ce Malam me ya kawo Hadiza? Ina nufin da wace buƙata ta zo?" Duk da ba tace kuɗin na shi ba ne ya saka hannu ya ɗauki kuɗin ya juya su, sannan ya aje gefenshi ya ce,ta zo ne da buƙatar korarku,burinta shi ne ta mallake gidan da maigidan da dukkan abinda ya mallaka." Jummai ta yi murmushi, sannan ta ce, "Ni ko banƙi ace duk sun rasa rayukansu ba, amma yanzun Malam na baka zaɓi me ka ke ganin za'ayi musu? Sannan ina son duk aikinta kar a mata cikin da ta ce tana da shi a zubar, sannan in ta zo da wani bayani in sani, kullum a dinga yi min binciken kome suke ciki." Malam ya ciro kuɗin da ya ajiye a gefe ya ce duk a wannan kuɗin? Ta ciro irin su ta aje mishi sannan ta ce, "Me za ka bani in soma dashi yanzun?" Hajiya Kari ta ce, "Malam ka mata wanda zata san kai me yi ne ba irin waɗanda da an ce ga buƙatar da ake so sai su hau cewa Allah ya ce ba, yayi wata dariya sannan ya nuna Karima ya ce, "Ai ke kin sanni, wata roba ya ciro fara cikinta wata ƙatuwar tsoka ce gata nan kamar zuciya,ya miƙa mata kin san wannan? Ta girgiza kai,zuciyar mutum ce ta zaro idanu ya ce riƙe da ƙyau aikin wani da zan yi shi ne na fasa zan baki nasa a ciro min wata." Ta ce "a jikin mutanan ake cirowa? Ya ce to da ina za'a samu? Ta tsorata Malam da sassan jiki ka ke aiki? Kari ta katse ta tsoron me zaki ji bayan ke kanki rai nawa ki ka salwantar? Jummai ta ce amma ban taɓa amfani da sassan jikin mutum ba,Malam ya miƙa mata hannu bani in kina ganin ba zaki iya ba ne, ta ce, "zan iya Malam, yi haƙuri." Ya miƙo mata wata leda tare da cewa, "buɗe ki gani."

Wasu allurai ne cunkus cikin wani gari baƙi, ya ce " Guda ɗari ne da ɗaya, kullum ki dinga tsira ɗaya jikin wannan zuciyar,in zaki tsira ki ambaci sunan maigidanku sannan cikin zuciyarki ki ƙudurce cewa aikin yi ci, kada kiyi wasi-wasi da zaran kin yi wasi-wasi aikin ba zai ci ba, sannan aikin za ya yi tasiri ne kan maigidanku, duk wadda ki ka soma tsira alluran da nufinta cikin kishiyoyin to ita kaɗai ce zata samu matsala da mijin naku.

Sannan aikin mutum ɗaya ne,ɗayar za'a mata nata daban, ta ce to wannan na A'isha ne? Ya ce shikenan,in kun dawo zan baki na ɗayar, sannan kada ki ƙagara fa, don yanda kike soka allurar nan da ƙaɗan-kadan haka aikin zaya dinga ci da kaɗan-kaɗan,ta ce shi kenan, sannan kada ki ajiye inda za'a gani fa, ta ce to.

A'isha tana ƙwance sai zabga Game take yi, cikin wayarta sam bata ji shigowar Uncle ba,sai...



#######
[12/19, 15:33] Ummi Tandama😇: *📔📔 Page 4*



Sai da ta ji an ja mata yatsa da sauri ta tashi tana faɗin Hasbunallahu wani'imal wakil" Ganin Uncle yana mata dariya sai ta tashi tana dariya, ya ce,"Beby kin cika shegen tsoro." Ta miƙa mishi kofin ruwan cikin risinawa tare da ladabi ya amsa cikin farin ciki sannan ya zauna a hannun kujera yana sha,ta zuba mishi idanu, komai na Uncle birge ta yake yi, ya ɗago idanu ya kalleta ta yi murmushi shima yana murmushin ya ce kin san dame nazo miki? Ta girgiza kai, ya buɗe jakarshi ta Office ya fiddo takardu ya miƙa mata,sai ki zaɓi garin da ya yi miki, duk dai makarantun suna da ƙyau, cikin murna ta shiga dubawa ta dube shi cikin ɗoki Uncle zaɓa min Kano ko Sokoto,ko A.B.U za ni? Ya dinga yi mata dariya, kafin ya ce ke wacce ya fi ƙwanta miki cikin su? A'isha ta yi shiru alamun tunani,can ta ce Sokoto ko Maiduguri, ya ce gara ma Sokoto, amma Maiduguri ya yi nisa sosai, daga nan. To shikenan Uncle na gode, cewar A'isha kenan.

Cikin abinda bai fi sati biyu ba, Uncle ya ɗauki A'isha, Jabir ne ke jan su sai Sokoto.

Masauki ya kama musu cikin wani shahararren Hotel. Suna sama Jabir kuma a ƙasa, ya kama mishi ƙwana biyu suka gama amma yanda Uncle ke samun kulawa gurin Bebyn tashi, sai ya kasance tamkar kada su dawo,don haka suka ƙara ƙwana uku ita kanta A'isha ta rubuta waɗannan ƙwanakin cikin zuciyarta.

Bayan sun dawo sai kuma aka shiga shirin tafiya makaranta, sannan ta ziyarci Jigawa ƙwananta biyu su Hajiyarmu da su Anty Fati duk tayi musu yini,nan ne ma Nafisa ta bata lambobin wasu ƙawayanta,kan cewa zata haɗa su ƴa Sokoto ne, kuma duk ba su da nisa daga makaranta. A'isha ta ji daɗi,dama bata san kowa ba, Nafisa ta sake tabbatar mata cewa zata ji daɗin zaman makaranta,don ita ma nan ta gama,ta ce mata waɗannan ƙawayan nawa wayayyu ne musamman harkar riƙe miji,ba ma kamar Maimuna ɗin nan , A'isha ta yi godiya tare da shan alwashin neman su, A'isha ka bata wasa da duk hanyar da ta ji an ce in tabi zata ƙara samun kusanta da mijinta matsawar ba hanyar saɓon Ubangiji ba ce.

Komai na ƴan gata Uncle ya haɗa mata, wani gatan ma sai da suka isa garin Sokoto,dama gida ya kama mata, cikin makaranta ƙwanansu biyu a hotel yasa ana ta gyaran gidan sai ka ce gidanshi,kaya yasa aka siyo aka shirya gidan tamkar sabuwar amarya ya zuba mata komai sabo ga kayan wuta har da laptop ɗin ta sabo, ya shirge mata abinci, shima sai da ya ƙwana a gidan sannan suka je ya buɗe mata account, tamkar kada su rabu lokacin da zai tafi, A'isha har da kuka.

Ya samu dai ya lallasheta, tare da yi mata nasihohi, sannan ya tafi. Ta koma ciki tana kallon falon, yanda ya tsaru ta shiga bedroom ɗin ta faɗa kan gado,duk kewar Uncle ta dame ta,ita dai a rayuwa ta gode ma Allah,don bata isa ta ce ga abinda Uncle ya yi mata ba a tsawon rayuwarta a gidanshi,ta sani Uncle rainonta yake burinshi kullum ya faranta ranta,ya ji da ita daɗi, ya fidda ta tsara cikin ƙawayanta, Uncle koda wasa bai taɓa yunƙurin ɓata mata rai ba,ko ta ko'ina abinda take so shi zata ci shi zata sha shi zata sa hannun iyayanta. Ta kula ko gurin auratayyane burinshi yaga ta shiga nishaɗi, shi yasa itama ko yaushe ba ta da burin da ya wuce mishi biyayya tare da neman hanyoyin ji da shi daɗi daga ni'imar da Allah ya yi mata. Kafin ya isa gida sun yi waya kusan sau goma, shi ya kira itama ta kira,shi kanshi bai san ya yi kewarta haka ba sai da ya yi ƙwana biyun shi na sauran matan da ace tana nan da yau ita ce da shi,a zuciyarshi A'isha daban ce yana sonta,tana kula da shi tana da baiwar da ba duk mata ba,in yana kusa da ita ya kan manta da duk wata ƴa mace a duniya. Addu'a kullum yake mata,

Please Login or Register in order to submit comment