Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanzun nasan duk yanda aka yi ina da laifin da nayi mishi mai girma,tsaki Nafisa ta ja sannan ta fita daga ɗakin,yarinyar ba zata gane cewa maza ba'a musu haka ba.

Daren ranar Alhaji Saddiƙ ya zo da daddare falo ya samu iyayan nashi cikin girmamawa ya zauna ya gaida su, Alhajinmu ya fi sakar mishi fuska,shima ɗin ba kamar yanda ya saba ba, ita ko Hajiyarmu da ƙyar ta amsa kalma ɗaya daga cikin jerin gaisuwar da ya jero mata,nan ya shiga kame-kamen cewa ya yi tafiya ne shine dalilin rashin zuwanshi, sannan in ya nemi Alhajinmu a waya bata shiga,sai Alhajinmu ya canza maganar da cewa ɗazun kaga baƙi a Office ɗinka? Ya ce ,eh sun zo mun kammala da su, zuwa satin sama zamu tura musu da kuɗi in mun ga kayan nasu. Alhajinmu ya ce, shikenan,ya yi ɗan jim sannan ya ce, A'isha na ciki? Hajiyarmu yi tayi tamkar bata ji shi ba,isowar Uwani kenan ta dire mishi ruwa ta ce eh tana ciki,ya miƙe ya shiga, daidai lokacin da A'ishan ke kan sallaya hannuwanta a sama idanunta suna zubda hawaye,tana cewa ya Allah kai ne mahaliccina da kai na dogara, kai ne kaɗai zaka sama min mafita cikin lamarin nan nawa da mijina. Ya Allah daidaitamu cikin gaggawa, Allah ka shafe wannan matsalar tamu,nan ta shiga kiran Ubangiji cikin sunayen shi keɓatattu,yana tsaye yana kallonta har ta shafa sam bata san da mutum ba, ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya shiga cikin ɗakin,ta bishi da kallo har ya zauna ta miƙe ta nufi ƙofa,ya danne wani abu da ke taso mishi ya ce ina zaki? Ta ce zan kawo maka ruwa ne, ya girgiza kai yanzun nasha a falon su Hajiyarmu, ta dawo ta zauna kan sallaya sannan ta ce ina yini? Ya amsa cikin cijewa domin lokacin wani irin haushinta zai ce ko tsana ma? Bai san ya ya zai kira abin ba, duk da ƙoƙarin dannewar da yake yi fuskarshi ta canza, ya daure ya ce ya ya jikin? Ta ce Alhamdulillah, ta sake duban fuskarshi gabanta ya faɗi saboda ganin irin yanda ya ɗaure, duk da haka ta daure ta ce, "Don Allah Uncle kayi haƙuri,bisa ga laifin da nayi maka,koda dai ban san laifin ba,ya miƙe tare da juya mata baya,ba abinda ya kawo ni yanzun ba kenan nazo ne na duba ki sannan ki min lissafin abinda ki ke buƙata ke da Bebyn."

Ta tsura ma bayanshi idanu bata gajiya da yaba mishi cikin kowace Irin shiga, muryarta a sarƙe ta ce sai dai ka tambayi su Anty Nafisa, ya juyo duk abinda suka zaɓa miki ya yi? Ta ce eh, sai dai batun komawata makaranta, ya kuma dubanta yaushe ki ka dawo? Ta ce, Uncle mu ba ayi mana hutu, ya juya baya domin in yana kallonta sai yaji ranshi ya fi ɓaci,ya ce makarantar ku sun tafi yajin aiki,ko dama ba a tafi ba bazan bari ki haihu can ba." Ya nufi waje ni na wuce hope ba wata matsala? Ta ce babu,ka sauka lafiya, har ya kai bakin ƙofa ta ce, "Na manta Uncle." Ya tsaya ba tare da ya juyo ba, ta ce wayata da kayana. To, kurum ya ce ya wuce, don ya ƙosa ya bar ɗakin, haka kurum yake jin tamkar ya make ta,yana barin ɗakin sai ya ji shi sakayau, ga mamakinshi da ya fito sai yaga mahaifan nashi sun canza mishi, da alama shigarshi gurin A'isha ya yi musu daɗi,nan ya nufi gidanshi.

Haka A'isha ta ci gaba da zama gidan surukanta gata na duniya tana ganin shi matsalarta ɗaya ce, Uncle ɗin ta wanda har yanzun yake nuna mata tsana da tsangwamma. Lura da ya yi cewa su Hajiyarmu ba su da matsala in dai suka ganshi ya zo da gurin A'isha shiyasa shi kuma kullum zai zo da safe in ya taso Office ma ya sake biyowa,duk kuwa da kasancewar dole yake ganinta,na ta gefen kuwa ta kan ji daɗin hakan duk da ba wata magana mai daɗi ko kulawa yake mata ba, sai dai ta lura yana matuƙar ƙaunar cikin in tayi la'akari da yanda ya narko ma Anty Nafisa kuɗi wai su je suyi siyayya, sai ga Anty Nafisa niƙi-niƙi,wai ta zo suje siyan kaya,da taƙi zuwa sai da Hajiyarmu ta ce ta kimtsa su tafi dama Likita ya ce ta ringa motsa jiki,ko a can idanu ta zuba Anty Nafisa ta ringa jidar kaya tamkar hauka, kuma bayan sun dawo washegari sai ga Nafisa da wasu shirgin kayan wai na Bebynta ne ta fara siya kafin ta yi ɓari, A'isha ta ce Anty Nafisa maimakon ki ajiye su tunda dai zaki samu wani, Nafisa ta ce don zan samu wani sai naƙi yiwa ɗan bros ɗina hidima? A'isha in baki sani ba yaron da Brother zaya haifa, shi ne gaba da duk wasu ƴaƴa da zamu haifa,koda gurin mahaifanmu, ballantana mu. A'isha ta yi ɗan murmushi ita kanta tasan hakan da Nafisa ta faɗa gaskiya ne.

Ga su Jummai kuwa gata nan zaune gaban Malam tana sanar da shi damuwarta, ta ce Malam da farko fa har ya ce cikin ba nashi ba ne, amma yanzun ya dawo ya amshi cikin, kuma sai faman zumuɗi yake yi kan cikin nifa na fi so inga an yi waje da cikin. Malam ya na jin ta kuma yana zuba aikinsa, ya dubeta kafin duk wannan aikin ina cikon kuɗina? Ta jawo jaka tana cewa, matsalarka kenan, kuɗi,ya ce kina zaton zan zauna ne in ta aikata saɓo a banza? Ba duniyar bayan dama na san a lahira sai dai in ana bada haya mu kama? Hajiya Jummai ta ce,ni dai gashi nan ya ya batun aikina yanzun? Ya ce sauƙi ne, amma in kin tafiyar dashi yanda na baki, cikin ɓarin jiki ta ce zan tafiyar malam,kai in ka faɗi abu matsawar an yishi babu mishkila aikin zaya tafi daidai, yanzun ka faɗa min duk dokar da ka ke so in kuma in cika aiki, ya dubeta ta na farko dai cikin nan sai an haife shi, sai dai in an haife shin asan yanda za'ayi da shi, sannan kamar yanda na taɓa gaya miki duk wadda ta soma haihuwa a gidan ita ce matar da zata zama uwar ƴaƴanshi, sai dai in za kiyi ƙoƙari in ta haihu ki kawo mana mahaifarta." Hajiya Jummai ta shiga share zufa, zuwa can ta ce tabɗijan aiki, Malam ya ce ba wani aiki ba haihuwar asibiti ba ne? Da zaran kin samu masu amsar haihuwar kin jona su da ɗan wani abun zasu ɗauko miki, ta ce to in kuma gida ta haihu fa? Ya ce ya ya kike yi kamar ba mace ba? Bana jin tunda sheɗan ya sara muku za'a samu wanda yafi ku iya makirci,ke cikin irin taki kissar ba zaki iya ɗauko mahaifar ba? Ta yi jim sannan ta ce zan ƙwatanta sai dai baka sanar da ni me za'ayi da mahaifar ba,don na fi zage dantse.


#######
[12/21, 08:48] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 8*


Ya ajiye allon dake hannunshi in har ki ka samu nasarar kawo min mahaifarta kin haye,don ina mai tabbatar miki ke kanki sai kin haihu, ita kuwa zamu ruɓar mata da gabanta yanda ma mijin ba zai je kusa da ita ba, sannan zamu maida ita juya har tsawon rayuwarta ba zata kuma haihuwa ba. Cike da farin ciki mai tsanani Hajiya Jummai ta ce ni ko ko tawane hali zan nemo mahaifarta zan dai haihu ka ce ko? Ya ce cire shakka, ta ce aikinka ba shakku a ciki, gafarta malam sai dai in ba a dire maka kuɗi ba, ya ce ashe kin gane kuɗin aikinki dubu ɗari da saba'in za ki bada in kin kawo mahaifa sannan zaki ba da kuɗin, ta ce aikin ma ya yi sauƙi na gode zan ƙoƙarta,kun ji matan da suka ɓata suka bar Allah da Manzo (S.A.W) Allah ka shirye mu.

Hadiza ma halin da ta ke ciki kenan, ya ya za'ayi taga bayan A'isha,ga ƙaryar ciki da ƙaryar ɓari,ga kuma amsar kuɗi hannun miji kafin ya yi auratayya da ita, duk sun haɗu sun firgita shi, shi da kanshi Alhaji Saddiƙ ɗin in ya zauna sai ya yi ta tunanin yanda aka yi yanzun baya gane kanshi, kuma yana da yawan addu'a ga ƙyautata ibada, haka nan mahaifanshi biyu suna tsaye kanshi da addu'a.

Wata tsurfa da Jummai ta ɗauka shi ne kullum zata zo gidan su Hajiyarmu dama-dama take da A'isha tare da nuna kulawarta ga A'ishan,tun A'isha tana ɗari-ɗari da ita har ta saki ranta. Su Nafisa ne dai ma suke cewa A'isha tayi hankali da Jummai,in Hajiyarmu ta ji sai tayi musu faɗa tare da cewa wato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne, A'isha kam ta ɗauki nasihar surukar tata kan cewa kada ta saka batun su Nafisa cikin ranta, ta zama mai zama da kowa cikin zuciya ɗaya. Wannan ne ma yasa har hira sukan yi da Jumman, tunda dama ba su taɓa faɗan sa'insa ba, ita dai in taga Jumman ne sai gabanta ya ringa faɗuwa,sai ga Jummai an je kasuwa an jido kayan beby na mahaukatan kuɗi an zo ana nuna ma maigidan, shi ko baki ya taɓa dan duk wanda za ya ƙyautatawa A'isha shi ka baya birge shi, duk da wasu lokutan yana ji cikin zuciyarshi cewa ba ya ƙyautata mata da ya so ya yi nazari kan abinda ya ke mata sai ya ji tamkar ana raɗa mishi a cikin kunnanshi ce wa ita taja duk abinda kai mata,in ya tambayi kanshi cewa da tayi ma ka me? Sai yaji zuciyarshi ta soma zafi ranshi ya shiga tafasa saboda kisisinar Jummai har faɗa suke yi da Alhajin kan A'isha, wata ranar juma'a ya shigo ganin su Hajiyarmu bayan sallar juma'a kamar dai yanda ya saba yi kowace ranar juma'a cikin ɗakin Hajiyarmu ya samu Jummai rashe-reshe tana shan farfesu,ya shiga yana cewa ƴar gidan Hajiya wai me take baki ne, kullum kina nan? Cikin murmushi ta ce ina zuwa taya A'isha rainon ɗanmu,ka dai san yanda na matsu mu ga Bebynmu.

Hajiyarmu tana kan sallaya duk da ta idar da sallar tuntuni tana ta addu'o'i,ya gaishe ta cikin girmamawa, ya sani Jummai zata yi ta jan shi da hira ne shiko ba za ya sake ba gaban Hajiyarmu, don haka sai ya miƙe. Ya samu A'isha zaune kan sallaya duk ƙafafunta sun kumbura, cikin ya yi ƙato ita kuma ga ta duk ta sirance ta ƙare yana son ya tausaya mata, amma ya kasa maimakon haka ma sai haushin ta. Ya juya mata baya kamar ko yaushe wannan ɗabi'a tana mugun baƙanta ran A'isha,ya ya Uncle zaya dinga juya mata baya? Nata ganin tamkar rahamar Allah ta juya baya daga gare ta ne, muryarshi ta katse ta kina bin dokokin Likitan kuwa? Cikin rawar murya irin ta me kuka ta ce eh,ya ce wai ke baki da wani aiki sai na kuka? Salon wani ya ji ya ce ina cutar da ke ko? Ta share hawaye sannan ta ce Uncle ina kukan baƙin ciki ne tare da yin tir ga rayuwata,na aikata laifin da mijina ya kasa yafe min, duk da ban san laifin ba. Ya juyo,na ce kin min laifi? Ya sake kauda kai daga gare ni baki min komai ba. Ta miƙe ta zo bayanshi sannan ta durƙusa gwiwowinta ƙasa, Uncle don son da Ubangiji yake yiwa Manzonsa ka taimake ni ka sanar dani laifin da na yi maka, kada ka barni cikin duhu, nasan laifin mai girma ne domin idanunka ba sa son kallona,haka zalika kafi son juya bayanka daga gare ni, ta kama ƙafafunshi "Uncle don girman mahaliccinmu ka yafe min." Ji ya yi tamkar ta zuba mishi wuta a daidai inda ta riƙe, cikin wata matsananciyar tsawa ya ce "Sakar min ƙafa,kina hauka ne? Jummai ta shigo da sauri tana faɗin, "Lafiya,me ya faru?" Domin tsawar da ya daka ilahirin wanda ke kusa ya ji, itama A'isha cikin masifar tsoro ta sakar mishi ƙafar,don makirci Jummai sai ta ɗaure fuska tare da ɓata rai ta soma cewa, "haba Alhaji, gaskiya abinda ka ke yi ya wuce min sherin,me yarinyar nan ta yi maka da ka ke mata wannan tsawar? Duk lokacin da nazo gidannan cikin damuwa nake ganin yarinyar nan kuma na san kai ne zaka sakata cikin wannan halin. Ya dubi Jumman,ita kin san abinda ta yi min ne? Ta ce ban sani ba amma ai komai na duniya ɗan haƙuri ne ko? A'isha ta iso gurin Hajiya Jummai cikin matuƙar son ta san laifin da ta yi mishi,ta ce Hajiya don Allah ki tambaye shi me na mishi? Hajiya Jummai ta dubeshi, Alhaji ka sanar da yarinyar nan laifinta domin gaskiya kana cutar da ita." Ya dube su ya yi shiru kamar yana son tunowa, can ya ce to wai ni na ce ne ta min laifi? Ni batayi min komai ba, duk abin da suke yi Hajiyarmu tana kallonsu sai lokacinne ta yi magana cewa, kurum ta yi A'isha taho muje. A'isha kam ta bi Hajiyarmu zuwa ɗakinta, Hajiya Jummai ta ce to ka gani ga shi ma har Hajiyarmu tana fushi da kai, ranta ya ɓaci bata son yanda ka ke yiwa yarinyar, tsaki kawai yaja sannan ya fita.

Koda Jummai ta shigo ɗakin Hajiyarmu nata zaton za ta samu suna tattauna batun Alhajin, amma sai ta samu Hajiyarmu tana waya, A'isha kuwa tana duba littafin Hisnul Muslim, ta zauna tana ƴan mitoci gaskiya Alhaji baka ƙyautawa.

Hajiyarmu ta gama waya, Jummai ta ce Hajiyarmu ya kamata a yiwa Alhaji magana baya ganin ba ita kaɗai ba ce? A'isha bata da matsala ya ya zaya ringa matsa mata? Hajiyarmu ta ce ya yi dai mu gani, rayuwa ce amma cikin ran Jummai dam da murna sannan tafi kowa sanin dalilin da yake wannan abin ga A'isha ita dai burinta shi ne A'isha ta haihu gabanta ko daga ita sai ita,ta samu mahaifa ta ida tarwatsa rayuwar yarinyar.

Tana gama waya da su Ummanta, ta kishingiɗa. Allah sarki! Su Abbanta sun zata har yanzu tana cikin ƙwanciyar hankali ne,sai dai tasha alwashin ba zata taɓa sanar da su ba, domin ko me zata ce Abbanta ba zai yarda ba,ƙila ma reshe ya juye da mujiya,wato laifin ya dawo kan ta. Cikin wannan tunanin ne taji tamkar an mintsine ta a baya,dama duk ƙwanakin a zaune take ƙwana in zata iya kuma ta yi ƴan nafilfili a haka ta yi sallar isha'i. Hajiyarmu ta shigo tana ce mata,kin ci abinci? A'isha ta ce,na ci zan ma ƙwanta ne. Hajiyarmu ta ce kina jin daɗin jikinki kuwa? A'isha ta ce eh babu damuwa Hajiya, fitar Hajiyan ke da wuya ciwo ya dawo sabo, ita kaɗai ta dinga kai kawo sam bata za ci haihuwa ba ce,ga nata zaton irin ciwon dai da ta saba ji ne yau da kullum,ya yi ya lafa,ya yi ya lafa cikin dare,biji-biji tayi zuwa lokacin ta gama yanke hukunci mutuwa zata yi,taso ace Uncle yana kusa ko zaya tausaya ya yafe mata laifin da ta mishi wani irin ciwo take ji wanda bata taɓa jin ko labarin shi ba,nishi yazo mata ta ji tana nishi mai tsanani tare da salati sai taji tamkar ana buɗe ta sai kurum wani ruwa tare da yaro jim kaɗan sai ga wani abu shima ya faɗo ashe mahaifa ce. Yaro ya shiga yanka ihu ita kuma ta koma gefe tana nishi.

Cikin bacci Hajiyarmu ta yi mafarkin wai ga A'isha an banƙare ta za'a yanka mata ciki, ta farka da salati dama duk dare tana zuwa duba A'isha kusan sau uku,ta kan ganta zaune ko kuma tana nafila,tana nufo ɗakin ta ji kukan baƙon duniya, da sauri ta shiga tana cewa ni ƴasu ke ƴan nan shi ne kina naƙuda ba zaki yi magana ba? Gashi ni yau sai Allah ya sauko min da bacci sannu kin ji? Ina kayan haihuwar? Ta nuna mata inda suke inda Nafisa ta ajiye su ko da yaushe tazo gidan tana shaidawa A'isha cewa tana jin burin ɗin ciwo to ga kayan da zata ɗauka nan,reza ta ciro ta yanke cibi sannan ta sa zani ta ɗauki jaririn lokacin da take karanto addu'ar da zata tofa ma yaron, idanu ta zuba mishi gabanta ne ya faɗi domin yaron tamkar mahaifinshi lokacin da ta haife shi,kamannin ya yi yawa sosai,nan kuma sai ta samu kanta da jin nauyin yaron,don haka sai ta matso ta ba A'isha shi a inda take cikin jin nauyi. A'isha ta amshe shi nan da nan Hajiyarmu ta tashi duk ƴan gidan suka shiga aiki, Uwani ita ce ta wanke yaro tas yayin da Baraka ta shiga gyara gurin Hajiyarmu kuwa gurin Alhajinmu ta nufa,kan sallaya ta same shi. Ya kalli agogo na jira ki sai naji shiru, shi ne na ce Hajiyar gidan nan yau batayi da ni, ya yi maganar cikin tsokana, ta ce Allah sarki,ba haka ba ne ɗan bacci ne ya sace ni ba farka ba sai da nayi wani ɗan mafarki haka ina tashi sai kukan jariri na ji,yarinyar nan ashe naƙuda take yi ba ta faɗa ba, ita kaɗai ta haihu, da sauri ya miƙe A'isha? Ta ce eh,nan ya shiga murna yana cewa alhamdulillah,ya so zuwa ɗakin Hajiyarmu ta ce ana gyara su ne.

Zuwa wayewar gari ko'ina labari ya je ban da gidan Uncle,domin daga Alhajin har Hajiyar babu wanda ya sanar dashi,su Nafisa kuwa an zo ana ta murna da ko tuno shi ba su yi ba, maijego tamkar ba ita ba,ta shirya tsaf asibiti za su je don Likita ya duba su . Ita da Nafisa suka nufi asibitin. Likitan ya duba su kuma ya tabbatar da lafiya suke. Aka yi wa yaron (Bcg) suka dawo,Likitanne ya kira shi lokacin yana shirin fita zuwa Office,suna gaisawa Likitan ya yi mishi barka,nan take Alhaji ya shiga tambayar Likitan ta haihu ne? Cikin mamaki Likitan ya ce ba ka sani ba kenan? Shi yasa banga ka biyo su ba? Ya ce Likita suna nan ne? Doctor ya ce a'a sun zo na duba sune gida ta haihu ko da ya gama shirinsa sai ya sake shiga bayinsa ya yo alwalla, nafila ce ya yi raka'a biyu yana yiwa Allah godiya, fuskarshi fal annuri ya fito ya dubi Hajiya Jummai Beby ta haihu,jin zancan ta yi tamkar saukar aradu, amma ta dake ta ce me ta haifa ne? Ya ce ban sani ba sai naje zan ji, ta shiga ɗakinta da gudu ta janyo gyalenta muje tare. A zuciyarta kuwa cewa take Allah ya bata Sa'a ta ɗauko mahaifa.

Sun samu ɗakin cike da jama'a ƴan barka, Uncle ya shiga mutane suna mishi barka, Hajiya Jummai cikin nuna zumuɗinta ta shiga ina ɗan nawa? Allah sarki,ko ƴa ce? Aka ce mata ɗa ne, Nafisa ta ce gashi nan mai kama da mahaifinshi,yaron na hannun Jummai Uncle ya tsura mishi idanu,wani farin ciki yake ji tamkar yau aka haife shi,ya miƙa hannu Jummai ta ɗora mishi yaron,nan take ya yi wa yaron huɗuba tare da addu'o'i,ko Nafisa ba ta furta ba lallai yaron hotonshi ne ji yayi tamkar kada ya bada yaron ya zauna yana ta kallonshi kawai, kaɗan-kaɗan mutane suka ringa fita har su Nafisa. Yana ɗago kai tuni sun watse sai matan nashi kurum, ya dubi A'isha a ranshi yana so ne ya yi mata sannu amma yana kallonta sai ya ji tamkar ya ɗauke ta da mari, Nan take fuskarshi ta canza ya kuma juya mata baya, zuciyar A'isha ta sosu amma sai ta danne, ta ce Uncle Ina ƙwana? Da ƙurar kuma can ƙasan maƙoshi ya amsa,ta ce ka faɗa ma su Abbana? Hajiya Jummai ta ce sai dai yanzu ya faɗa,mu ma ba yanzun muka ji haihuwar ba,wai tun yaushe ne haihuwar? Kan A'isha yana ƙasa ta ce da dare ne. Uncle ya ce to kin ji abu da dare amma an kasa sanar dani. Hajiya Jummai ta ce Alhaji sai ka amshi mahaifar mu je gida ka rufe ko? Ya ce haka ake yi? Ta ce eh mana,ai ba'a wasa da ita,ya dubi A'isha sannan ya kauda kai, ina mahaifar? Ta ce sai dai a tambayi Hajiyarmu, Jummai ba ta san sanda ta furta Allah yasa ba su rufe ba, sai kuma ta riƙe bakinta saboda katoɓarar da ta yi, ya dubeta in an rufe a nan laifi ne? Ni fa bana son canfi,ta ce a'a ina fa laifi wai mu ma muce an taɓa rufewa a gidanmu.

Ya nuna murnarshi sosai a gaban mahaifan nashi da ƙannanshi, in da har yake tambayar ƙannan nashi me ake buƙata game da jariri da mamanshi? Nan take Nafisa ta shiga lissafi har da na tsiya, lokacin da Uncle ya sanar da mahaifanta sun yi murna sosai, Abbanta ya ce Friend na tayaka murna sosai, Allah ya raya mana ya ce Amin friend,na gode ina fatan za ku zo kada ka ce min don A'isha tana ƴarka ba za ka zo ba, dariya Abban ya yi kafin ya ce ban ɗaukar maka alƙawarin zuwa ba, sai dai ko bayan suna zan zo insha Allah. Dangin A'isha suma labari ya karaɗe ko'ina,ba labarin ciki sai na haihuwa, lokacin da labarin ya samu Hadiza tamkar zata suma don itama da yawa Malaman nasu sun sheda mata cewa duk wadda ta haihu cikin su shi kenan ita ce kurum zata yi ta haihuwa, kuma ta yi rantsuwa kan cewar in dai ba ita ce zata haihu ba, to sai dai kowa ya rasa cikin da yake cewa ba na shi ba ne shine zai amsa? In ko haka ne itama sai ta nemo shi wajen ai ba an fi su sanin kan bariki ba ne.





#########
[12/21, 18:37] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 9*



Hajiya Jummai ita dai damuwarta ta samu mahaifa, don haka lokacin da Alhaji zai fita bin shi ta yi gurin mota, faɗi take shin Alhaji ka amshi mahaifar? Ya dubeta,au Ina zuwa,ya koma ciki sai dai ya kasa tambayar mahaifiyarshi saboda nauyin da ke tsakaninsu,ya ce Nafisa zo mana,a gefe ya ke cewa ta tambaya mishi ina mahaifar don ya je ya rufe. Lokacin da ta yiwa Hajiyarmu batun sai ta bata amsa da cewa zasu yi ta ajiyar mahaifa ne ba za su rufe ba har zuwa yanzun? In kuma ya fi son ya rufe da kanshi to sai ya jira mahaifin nasu in ya shigo sai ya ce ya tono mishi yana son ya rufe da kanshi ne,yana jin lokacin da take faɗa wa Nafisa wannan batun,don haka sai ya juya kurum yasan har yanzun mahaifiyar tashi tana ciki da shi.

Jummai ta dube shi ka amso ne? Ya ce sun rufe tuni, ta zaro ido har ma ya tsaya yana kallonta, sun rufe? Ta ɗora hannu akai tare da cewa kash! Ta dubeshi ɗan jira ni in ɓari inzo muje gida, da sauri ta suri gyalenta ko sallama ba ta yi wa mutane ba ta wuce. Yana ƙoƙarin tada mota ta fito, sannan abinda ya dinga ba shi mamaki yanda duk surutun da yake yi bata san ma yana yi ba,ga uwar zufa da take zabgawa sai ka ce wadda ta haɗiye kunama. Suna isa gida tun kafin ya gama parking ta buɗe mota kaɗan ya rage ta faɗo, ta fita da sauri sauri gudu-gudu tana shiga falonta suna cin karo da Aminiyarta Hajiya Kari, ta ce Jummai tunda na samu labarin haihuwar matar mijinki na ce bari in zo kada kiyi sakaci, Jummai cikin wani huci mai tsanani ta ce na nawa kuma,ai an riga an gama sun rufe ta. Karima ta yi saurin cewa, sannu Alhaji dan ganin ya riga ya shigo kuma ga Jummai da shegen ɓarin baki, sannan ta yi mishi barka,cike da murna ya amsa tare da godiya, ya kalli Jummai ya ce, wani abu na damunki ne? Ta share zufa ta ce me ka gani? Ya ce duk kin canza irin kamar kina cikin mawuyacin hali? Ta kuma share wata zufar haba dai mu yau da muke cikin farin ciki? Ta yi ƴar dariyar yaƙe,ai mu yau dai babu bacci, ya tsura mata idanu Jummai wannan zufar fa? Ta ce tsabar farin ciki ne, sai ta

Please Login or Register in order to submit comment