Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yi ganin ta buɗe ido sai ya yi murmushi, Beby dama idanunki biyu? Ta tashi zaune fuskarta babu yabo babu fallasa, ta gaishe shi. Ya amsa sannan ya isa gurin ɗan shi yasa hannu ya ɗauke shi yana kallon fuskarshi kafin daga bisani ya sumbaci gashin yaron tare da manna shi a ƙirjinsa yakan ji wani irin daɗi duk lokacin da ya rungumi ɗansa,yana addu'a ga duk wanda bai samu ɗa ba, Allah ya bashi A'isha tana kallonshi zuciyarta na yaba ƙyawun shigar shi, da ƙyan haibar shi banda ta san shi da in aka ce tayi mishi shekaru zata ce ashirin da biyar, ya dawo da dubanshi gare ta, sai ta ɗauke kanta yayin da suka haɗa idanu, ya matso daf da ita Beby wai me yasa naga kin kasa sakewa da ni ne? Ta ce ba komai, shi da kanshi ya sani abubuwan da ya yi mata can baya bai ƙyauta ba Sai dai shi ba zai ce ga dalilin da yasa yake yi mata hakan ba, ya ce Beby ɗazun na ce yaushe zaki dawo ba ki ce min komai ba, ta ce Uncle ka manta ne? Na ce sai dai ka tambayi su Hajiyarmu, ya ce kin dai san in dan ta su ne zaki yi ta zama ne ba zasu dawo min da ke ba, ta yi guntun murmushi a ranta ta ce kuji Uncle da wani zan ce mutumin da ke guduna. A fili kuwa sai ta ce, sun ga baka buƙaci hakan ba ne shi yasa ya ce Beby kenan cikin ruwan sanyi ki ke dafa mutum ni dai ki dawo gida kawai,ta tashi zaune Uncle jibi ne fa zan koma makaranta to menene ma zai sa in dawo tunda ba zama zan yi ba, ya yi shiru can ya ce ni fa don dai kawai su Hajiyarmu ne amma Allah da ba zaki koma yanzun ba sai yarona ya yi wayo bana son aje baa luran min dashi. Shiru ta yi mishi ya ce to in zaki shiga aji dawa zaki dinga barin shi? Ta dube shi da Uwani zamu tafi har ma da wata yarinya saboda aikin gida, ya ɗan taɓa baki da bana gari ma da sai dai in dawo in samu kin tafi abinki, ta ce Uncle naga kamar kafi buƙatar hakan ne shi yasa tunda tuni ka fitar da kanka daga cikin lamarina, ta sunkuyar da kai, wallahi a shekarar da ta wuce in wani ya ce min zan tsinci zuciyata cikin garari ba zan amince ba, domin na san uban goyona mai amana ne da halin dattako kuma zaya jure duk wasu laifuka da ƙuruciya zata aikata matsawar ba alfasha ba ce, sai gashi yana zarginta da alfasha wanda ke ɓata aure, ya ɗaga mata hannu, zuciyata bata zargeki ba Bebyna ko da baki ya furta zuciya ta ƙi amincewa, Beby an wuce gurin bana son ki dawo da hannun agogo baya, kuma kamar yanda nike fada koda yaushe ni baki yi min laifin komai ba....




######
[12/22, 12:13] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 11*



Amma da mamaki ace don jin daɗin kanka ka juya baya gareni,kafin ya ce wani abu sai kurum suka ji muryar Hajiyarmu tana cewa in nan zaka ƙwana mu kulle ƙofa ya dubi agogon hannunshi sha biyu saura,lallai lokaci ba wuya ko kuwa don yana tare da masoyanshi guda biyun ne?.

Bayan fitarshi ne Hajiyarmu ta kalleta sanyinki ya yi yawa A'isha,me zai sa ki saurareshi shi da ya nuna baya ƙaunarki? Kanta a ƙasa ta ce Hajiyarmu in ma na ɗauki zafi dole in sauke domin daga gare shi zan samu aljanna, Hajiyarmu tana mamakin A'isha in da mata da yawa za su ɗauki halin A'isha haƙiƙa za su zauna lafiya da mazajansu kuma su ci ribar aure, ta ce haka ne amma mazan ku na yanzun sai kuna ɗan nuna musu kuskurensu,na ce baki sakir mishi fuska yanzun ba nan gaba zaya ji shakkar yi miki irin haka. Ta ce haka ne sai dai yana da ƙyau in bashi uzuri kasancewar bai taɓa aikata min ƙwatanƙwacin haka ba, sai wannan karon, sannan yana da ƙimar da ba zan iya rama abinda ya yi min ba, Hajiyarmu ta ji zuciyarta ta ƙara ƙaunar A'isha, ta ce to Allah ya daidaita ku,mu dai addu'armu kenan, sannan in ya yi ba daidai ba mu tsawata, sannan ki lura da ɗan ki kin ji ko. A'isha ta ce, to ta lura tana matuƙar son jikanta nata tana da kara ne.

Tafiya ta kama shi ranar da A'isha zata koma,bai so haka ba,ya so ƙwarai ya zama cikin masu rakiya in yaso ya ƙara wanke kanshi gurin Bebyn tashi, ya dai yi sallama da su kan cewa sai ya zo insha Allahu da zaran ya dawo daga Egypt. Nafisa ta zo da safe dan su yi sallama A'isha ke cewa ina son ki zo ki sha labari don ba za ya yiwu ta waya ba, Nafisa ta ce bani labari. A'isha ta labarta mata yanda suka yi da Uncle ɗin ta, nan Nafisa ta yi murna sai dai itama ta yi wa A'isha tsiyar cewa ta cika son miji daga sakar mata fuska shi kenan ta shiga wage mishi baki, A'isha ta ce to ni ya zan yi? Anty Nafisa kin san Uncle ya wuce wasa a gurina, domin sai fa ya ɗaga ƙafa sannan zan shiga aljanna,ya zan yi wasa da dama ta? Nafisa ta yi dariya kina burge ni A'isha Allah ya sani ma in gwada irin halinki. Itama A'isha dariya ta yi.

Yana ƙwance yana nazarin yarinyar ya sani sarai cikin ruwan sanyi A'isha magana ta gaya mishi, ita kowace irin mutum ce bata fushi? Gaskiya ba zaya gaji da godewa Allah ba,muryar Hadiza ce ta katse shi. Gaskiya ni na gaji, kullum sai ka tafi gurin A'isha ka raba dare ko ka je asibiti ni ce ban san haƙƙina ba don kaga ina haƙuri? In zata dawo ne A'ishan ba gwara ta dawo ba, amma sai a dinga shiga cikin haƙƙina ranar girkinta da ranar da ba tata ba.

Ya miƙe zaune to tunda kin gaji sanar dani yanzun me ki ke son in miki? Ta zunɓuro baki ta dawo a raba ƙwana mana, ya ce na ƙi ta dawo ɗin sai ya ya kuma kike so? Ta kalleshi,ai ni banida alfarmar da zan faɗi abinda ni ke so ayi wannan sai A'isha. Ya ce ƙwarai kuwa domin bata da san kai a rayuwa in kuma abinda ya kawo ki kenan to fita ba ni da lokacin ɓacin rai yanzun ya juya bayanshi, tunda ta wanke gaba ta baka a zoɓo kuma ta haihu ai gare ka babu kamarta, murmushi ya yi a fili kuwa ya ce mahaukaciya kawai, ta fita tana ƙunƙunai.

Haka lokaci ya yi ta tafiya A'isha tuni tana makaranta kuma ta dage ma karatunta, yayinda Uwani ke lura da Abulkhairi, kullum kuma tana ɗaga wayar Uncle ɗin nata a ƙalla sau huɗu a rana ko fi ma,don haka hankalinta ƙawance ta murmure gwanin sha'awa da ita, ranar suna waya da Nafisa take cewa Anty Nafisa Uncle yana son kawo min ziyara ina dakatar da shi da cewa karatunmu ya ɗau zafi in ya zo bazai samu kulawarmu sosai ba, sai nace ki bani kayan nan na gyaran jikin kafin ya zo, gefe kuma ina tsoron kada na kuma ɗaukar wani cikin ga Abulkhairi ga karatuna, Nafisa ta ce zan tura miki da kaya ta tasha gobe, akwai na sha sunanshi hurul'in da na matsi sannan turarukan shafawa da na tsuguno sai man gyaran jiki da sabulun shi sannan lalle na wanka da kuma haɗi na musamman irin wanda ta ke yi don Amare duk nasa ta haɗo min su, zaki gan su kawanne da sunanshi wanda baki gane ba ki kirani ko ki kira Hajiya Aliya zan turo miki lambarta, batun ciki kuwa a sakar ma ɗan uwana jiki ya huta haihuwa muke buƙata kema kin sani, A'isha ta ce haba Anty Nafisa baki tausayin Babanki? Abulkhairi bai yi ƙwari ba Nafisa ta ce za ya yi ne ma suka sa dariya sannan suka yi sallama.

Hajiya jummai kuwa yau in ciwo ya lafa gobe zai tashi domin ta kasa ƙwantar da hankalinta guri ɗaya, shi kanshi Likitan ya gaji da ita don haka yana ganin ta ɗan samu sauƙi sai kawai ya sallame ta ya ce zaya dinga zuwa gida yana duba ta,Indo ma tayi murna don tana so ta tafi, kuma halin ƴar uwarta ya isheta a gidan ma a daddafe ta yi sati ta haɗa yanata yana ta tayi tafiyarta sai ƴan aiki da kuma ƙawayanta da ke tururuwa suna cika gidan kullum kuma abin takaici har yau ba su daina ƙalla banza ƙwance wofi ba,burinsu wai su fitar da A'isha kuma wai A'ishan asiri ta yi mata wannan ciwon nata wai Hadiza ma tana jeho mata asirai kin ji fa.

A'isha suna hanyar su ta zuwa aji ita da wasu abokan karatunta, suna tafe suna hirar Abulkhairi ne, Hafsa Sulaiman tana cewa yaron ya fi ki ƙyau sam bai yi kama da ke ba. A'isha ta ce Abbanshi ya biyo sun yi kama sosai,Hauwa'u Hamza ta ce to kuwa Baban nashi yana da ƙyau kenan,don nima bana gajiya da yaron, kafin ta yi magana sai wayar Uncle ɗin ta ta shigo ringin ɗin shi na musamman ne don haka cikin sauri ta soma lalubo inda wayar take,cike da kissa ta ce Hello Uncle ɗina,ya gyara zama Bebyna, suka gaisa yana tambayar ina Babanshi ta ce suna gida tare da Uwani yanzunni ina hanyar zuwa aji ne ya jingina da kujera,na kasa komai Beby ina cike da kewarki ke kuma na kula baki son in zo inda ku ke, ta ce wacece ni Uncle da zan hanaka zuwa gurin mu ya ce in gaske ne in zo yau? Ta ce Uncle kaɗai shigo week end duk ƙwanakin nan bama samun lokacin kanmu, ya ce shi kenan zan dai samu tarba ta musamman ko? Don maƙogwarona ya bushe da yawa ina jin ƙishi, ta ce faɗi duk me ka ke so zan maka ya ce ke kurum kin wadatar dani, ta ce Uncle dama ni ai taka ce ko yaushe sai dai in kai ne ka ƙi hakan ya ce Bebyna kenan kin dai warware ni a hankali to kaina dai bisa wuya, sai na zo ta ce to shi kenan muna kallon hanya.

Hafsat ta ce A'isha Musty dawa ki ke waya haka kina faman salo sai ka ce kina gabansa cikin dariya ta ce yanzun don Allah har wani salona yi? Da Uncle ɗina fa nake waya, Hauwa'u ta ce kai wannan salon ina jin dai da Abban Abulkhairi ki ke wayar, ta ce au baku yarda ba cewa da Uncle ɗina nike yi ba? Hafsat ta ce Uncle ɗin nan da kike kira yana ji dake kema haka, A'isha ta ce haka ne baki faɗi ƙarya ba Uncle yana ji dani tamkar rai, Hauwa'u ta ce yana da mata? A'isha ta ce matansa uku ɗan sa ɗaya. Hafsat ta ce aiko in bakin ci Sa'a ba matansa sai sun tsaneki, cikin dariya ganin ta shigar da su sun shiga ta ce suma ji dani suke yi, suka ce lallai,kin dace nan dai suka ƙarasa ajinsu don ɗaukar darasi, A'isha kenan tunda saƙon da Nafisa ta aiko mata dashi ya shigo hannunta ta soma amfani da su cikin ƙwana uku ta canza ta zama tamkar wata amarya abokanan karatunta kuwa kowacce sai ta dinga ce mata ana karatu ana rama ke kuma kina ƙara ƙyau dan Allah menene sirrin? Dariya kurum take musu tare da cewa suna dai zolayarta ne. Hatta Anty Maimuna ƙawar Anty Nafisa sai da ta dinga yiwa A'isha nacin son ta san man da take shafawa ta ce sunanshi Zahra Global in kina so zan yiwa Anty Nafisa magana.

Tunda ya yi waya cewa yana hanya duk ta rasa sukuni, ta ƙosa su fito daga lap,tana shiga gida kuwa yau ko ta kan Abulkhairi bata bi ba suka shiga aiki su da Tani mai aikinta,girka wannan sauke wancan har suka gama, ta haɗa mishi mutumin nashi wato zoɓo sannan ta shiga wanka.

Ƙwalliya sosai ta zauna gaban madubi ta yi tare da saka turarukan jiki masu ƙamshin daɗi. Atamfa ce ƴar Holand ja ɗinkin riga da siket sun zauna dam a jikinta tamkar a jikin nata aka ɗinka su. Hatta Uwani sai da ta ce kin yi ƙyau ƴannan wannan kaya sun karɓe ki, tana cikin shirya Abulkhairi ta ji ana ƙwanƙwasa gida. Kafin ta yi magana ta jiyo Uwani tana cewa Tani taje ta duba,don haka ta ci gaba da saka mishi kaya,ƙamshin shi ta ji ta amince shi ne ya iso cikin sauri ta ƙarasa tana cewa Abulkhairi kayi ƙyau babana" juyowannan da zata yi sai suka haɗa ido da Uncle ɗin nata yana tsaye yana kallonsu cike da sha'awarsu, A'isha ta ce la Uncle har ka shigo? Ya iso gabanta na iso Beby ya ɗauki Abulkhairi ya ɗaya shi sama yana mishi wasa ita kuwa tuni ta shiga gyara mishi gurin da zai zauna don cin abinci, ta amshi Abulkhairi, Uncle kawo shi kaci abinci bari in kai shi gurin Uwani ya ce a'a barshi nan abincinma nan za'a kawo min,nan take ta baza capet ta shiga jera mishi kuloli sai da ya zauna kafin ya fara cin abinci ta shiga gaishe shi tare da tambayar jikin Hajiya Jummai,su Hajiyarmu da sauran jama'a ya ce duk suna lafiya, Jummai dai jikin nata sai a hankali, da zoɓon ya soma sannan ya shiga cin abincin ya ma rasa me zai ci duk ranshi yana so rabon da ya yi ci irin wannan har ya manta, ya ce Beby kin ga kin sani yau har na wuce ƙa'ida,na ci na kasa tashi, ta yi murmushi Uncle kenan to ai ni nafi son haka.

Taƙwas da rabi daidai lokacin da ya dawo daga masallaci sallar Isha'i, ya ce Beby ba zan ƙwana a nan ba shi yasa muna isowa nasa Jabiru ya je ya kama min masauki ta ce don me? Ya ce ga su Uwani ko ba haka bama kin san ba ni son cikin makaranta, ta ce to ya za'ayi yanzun? Tashi zakiyi mu tafi, ta ce da Abulkhairi? Ya ce eh mana, ta ce can zan ƙwana kenan? Ya ce to ya ya kike nufi da? Ya ci gaba,kina nufin ni kaɗai zaki bari inje in ƙwana? Ta ɗan yi taƙwa-taƙwa da fuska haba Uncle gidannan fa dasu Uwani shi kenan sai nabi ka can da safe kuma idan na dawo da wane ido zan kallesi? Ya ɗaure fuska koda nan na ƙwana abin da kike gudun su kalle ki dashi in kin bini dashi dai zasu kalleki,kin gane? Beby duk mace mai miji in dai tana tare da shi an san me suke yi, balle ni da na ɗan ƙwana biyu ban abinnan ba, ya ƙarasa da ƴar tsokana ta ce Allah Uncle gaske nake faɗa zan ji kunya, ya ɗauki Abulkhairi muna jiranki cikin mota ki zo muku da duk abinda za ku buƙata, zuwa gobe.

Ta bisu da kallo ɗan murmushi ta yi sannan ta shiga haɗa musu kayan bacci da sauransu, ta kunna tiraran tsugunno ta yi tare da ƙara kimtsa jikinta, ta saɓa jaka tare da zura hijabi ta fito, Uwani suna kallon T.V su da Tani ta fito ta ce Uwani zamu in nan cikin gari kome sunan unguwar? Gidan dai wani ko abokinshi ne? Ku dai kulle gidan in mun dawo to sai mu buga. Uwani ta ce to ƴan nan a sanyin nan? Da kun bar Alhaji nan tunda shi bashi da rigima, ta ce yama riga ya fita da shi sai dai mun dawo. Tani ma ta ce sai sun dawo.

Cikin mota ta same su yana ta mishi wasa, ta shiga tare da tura baki Uncle ka sani zula ƙarya, ya ce kin so ne me ki kace? Ta sanar da shi yace in suka zauna jiranki fa? Ta ce shi ne ai ko in koma ince mun fasa sai ka shigo mu ƙwana ciki kawai, kafin ta rufe baki ya tada motar.

Cikin Reception suka ga Jabiru yana zaune yana kallon ƙwallo cikin T.V, ya tare su tare da amsar Abulkhairi, shi ne ya yi musu jagora zuwa ɗakin daga bakin ƙofa suka yi sallama tare da miƙa musu yaron.

A'isha tasha mamakin yanda Uncle ya ke ta rawar jiki tamkar yau ya soma sanin mace, ta dai sha wuya sosai shi ko sai kace bame mata biyu ba, haka ƙiri-ƙiri ya ƙi su tafi gida ranar tana ji tana gani dole ta kira wayar Uwani ta ce mata sun yi wata ƴar tafiya kada su ji shiru, cikin satin da lahadin wata rayuwa suka yi mai tsayawa cikin zukatansu, ranar Lahadin ma sai dare sannan ya kawo su gida shi kam Asubanci zasu yi don komawa KT,lokacin da zasu yi sallama ta kuma maimaita mishi batun da ta ringa mishi naci tun da suka je hotel ɗin bai ce mata ƙala ba.

Ta ce don Allah Uncle kaga Abulkhairi be yi ƙwari ba, kuma ga karatuna. Nan take ya gumtse fuska Beby na fi son in kin faɗi abu nayi shiru ki ringa ƙyale ni, ke kina ganin ko'ina shaye-shaye zan yarda da wani tsarin iyali? Ki kalleni fa ki gani a shekaru na sai yanzun Allah ya bani ɗan fari, amma har in soma butulce ma Allah? Please bana son in kuma jin makamancin wannan zancan, kanta na ƙasa ta ce to, sallamar ma ba cikin daɗi sosai suka yi ta ba,in ba dan A'isha ba ce ma ƙila da wata ce tazo mishi da wannan batun sai ya mugun saɓa mata yanda ta kula da irin ɓacin ran da ya nuna cikin dare sai da ta kuma kiranshi ta bashi haƙuri kan cewa ya yi haƙuri ta ga ranshi ya ɓaci da batun da tazo masa dashi, ya ce ya wuce shi bai ƙima ace yanzun tana da wani cikin ba, dariya kurum ta yi amma cikin zuciyarta cewa take yi Allah ka tsare ni.




#######
[12/22, 20:35] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 12*



Tana ta gudu gyale a hannu takalmi a hannu tana zunduma ihu cikin ƙungurmin dajin mai tsananin duhu,yaran ta ke gani cikin wani muguwar kama mai ban tsoro, dukkan su suna furta mata kalmar fansa! Fansa!! Ko'ina cikin dajin amsawa yake yi, gudu take yi tun ƙarfinta duk ta gaji sai ta hangi wani rami nan take yi ta yanke shawarar tsundumawa cikin, tana faɗawa sai taji ta kan macizai da kunamu, ihu ta saki mai tsanani sai ta farka a tsorace ta tashi zata gudu Alhaji Saddiƙ ya riƙe ta da ƙarfi yana cewa Jummai lafiya? Masu aiki ma suka shigo da gudu saboda ihun da suka jiyo,faɗi take gasu nan,su murja ne da Hafsatu zasu kashe ni wai zasu ɗauki fansa su Jamila ne, da taimakon ƴan aiki ya samu ya dannata kan gado zuwa wani lokaci yana tofa mata addu'o'i sannan ta lafa sai kuma kuka tana faɗin na shiga uku ni Jummai. Ya ce me yake faruwa ne ki min magana mana ta ce su Jamila ne zasu kashe ni suna ta bina, ya ce wacece Jamila? Matanka mana da suka mutu, shiru ya yi ya zuba mata idanu, cikin zuciyarshi kuwa tunani yake yi me zasu ɗauki fansa yake nufi? Amma sai ya dubeta ya ce to kici gaba da addu'a ya miƙe ya fita cikin ɗaurewar kai,baya son zargi don haka sai kawai ya shafe batun daga zuciyarshi sannu a hankali mafarkin ya zamo wa Hajiya Jummai ƙa'ida in dai har zata rufe idanu da sunan ko gyangyaɗi ne ba ma bacci ba,tuni ƴan aikinta kunnuwansu sun soma sabawa da jin ihun Hajiya Jummai cikin dare da rana, ita kuwa tuni rashin bacci ya yi biji-biji da ita tamkar zautacciya ta dawo ko yaushe tana surutai waɗanda in ka saurare su asirin ta kawai take tonawa,ko yaushe tana faɗin kada ku kashe ni sun ce zasu rama na shiga uku na kuyi haƙuri wannan yasa Alhaji tsare Jummai da son jin me ke faruwa ne? Kuma me zasu rama? Cikin kuka ta ce ka taimake ni nice na kashe su dukkansu nan ta zayyane mishi duk yanda komai ya faru,kuka da hawaye Alhaji Saddiƙ ya yi sannan ya je yazo da Alhajinshi don jima kunnanshi shima, Alhajinmu kasa magana ya yi sai da yaje gida sannan ya iya furta ma Hajiyarmu labarin itama girgiza mahaifan Jummai sun yi baƙin cikin jin wannan zancan, Alhaji Saddiƙ ya samu mahaifan nashi don son sanin menene mafita shi dai ta gefen shi ya gama zama da ita, ashe duk ita ce silar da jama'a suke mishi mummunan zato kai Allah ya isa Jummai na tsane ki har abada, mahaifinshi dai ya ce in yaga bazaya iya zama da ita a haka ba to ya sauwaƙe mata domin kam dan cutarwa an cutar da shi Hajiyarmu kuwa shawartar shi ta yi da cewa in ya saketa to don Allah yabar ta a muhallinta wato gidan shi kenan, ya amince da hakan don haka yana shiga gidan ɗakinta ya nufa zaune ya sameta gefenta Hajiya Kari ce tana cewa, haba Jummai yaya zaki saki baki ki yi ta tona ma kanki asiri? Alhajin da basu san da shigowar shi ba ya ce ko bata fada ba dole ne wata rana asirin ya karye, domin ta ɗauki rayukansu ba tare da haƙƙinsu ba,shawarata gare ku ke da ita in kuna son samun sauƙi gobe kiyama ku kai kanku kotun musulunci domin a zartar muku da hukuncin da ya dace da laifukanku,in kuma kun fi son Allah ya yi muku nasa hukuncin da kansa to kuyi shiru ya ja numfashi sannan ya ci gaba da cewa Jummai am sorry to say na sake ki saki biyu in kina so za ki ci gaba da zama cikin gidan nan sai dai ni yazama dole in barshi.

Wani irin ihu ta saki mai ƙarfi tana cewa ka taimake ni kai ne kaɗai ka rage min saboda sonka ɗin ne fa na aikata duk waɗannan laifukan shi ne yanzun za kayi min haka? Ya ce ke kika zaɓo hakan, wacece ke da zaki ce ba za'ayi miki kishiya ba saboda kin ƙwashe kayan ki daga gaban Manzo,ya dubi Karima ku saurari ƙarshenku yana zuwa. Yasa kai ya fita abinshi, Jummai an shiga sabon ruɗu, hauka hauka ne ya sameta nan take. Lamari fa ya ta'azzara su Jummai yau gashi an kai ga rufe mata ƙofa domin zabura take zata gudu tana faɗin ga sunan baƙin wani kashi da ke jikin Jummai tuni ta yi mishi fizgar kaza,ya zama abinci sai dai a kulla ƙwano da igiya a tura mata Alhaji Saddiƙ tuni ya tattara su Hadiza da wasu daga cikin ƴan aikin gidan suka koma wani gidan shi da ke can cikin G.R.A. Hadiza a baɗini murna take amma a fili kuka rurus ta ringa yi wai ita dole nan me imani, shi ko Alhaji tuni ya dawo rakiyar su shi dai tsoron lamarin mata yake bashi domin bai taɓa zaton Jummai zata iya kashe koda ƙiya shi ba bare mutum. Shine dalilin da ya ji mata sun fita ranshi, hatta A'isha da bata san ma meke faruwa ba duk yasa su gefe shi ne dalilin da hankalin A'isha ya yi matuƙar tashi ga zatonta abinda ya faru ƙwana kin baya ne zai kuma faruwa cikin sauri ta kira Nafisa da kukanta tana cewa Uncle ya yi watsi da ita kota kirashi ba ya ɗaga wayarta,nan take Nafisa ta ce daina kuka mijinki yana cikin ruɗani ne sannan ta sanar da ita dukkan abinda ya faru. A'isha tasha mamaki lallai dole ne maigidan nasu ya shiga rudani.

Karima kuwa taje tazo da bokansu don ya yiwa Jummai magana,suna shiga inda take ta riƙe shi fatar jikinshi ta shiga yaga tana surutai Karima ta yi baya da gudu,tana fita mashin ya yi ciki da ita nan take wuyanta ya karye shi ko boka da ƙyar ya ƙwaci kanshi ya fito jina-jina ya fita da gudu, ganin ƙofa buɗe itama Jummai ta yi ficewarta ta shiga gari

Please Login or Register in order to submit comment