Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soma matso hawaye shekaru nawa ba mu taɓa jin kukan ɗa ba cikin gidan nan sai bana, dole in yi zufa, Karima ta ce haba Jummai ai godiya zamu yi wa Allah ba kuka ba, Alhajin ya dafa kafaɗarta, Jummai na san dole ne kiyi murna, sannan ina miki albishir da zaran an tashi ya ye shi ke ce zaki ɗauke shi kiyi rainonsa har abada, ta dubeshi cikin muryar kuka tana cewa na gode Alhaji ni dama nasan ɗan ka ɗana ne Allah ya raya mana shi, suka ce amin ya ce bari in je in ɗauki wasu takardu ina da baƙi a Office suka ce to ya fita. Hajiya Jummai ta ɗora hannu a kai zata zunduma ihu Karima ta saka tafin hannunta ta rufe ma Jummai baki, sannan ta ci gaba da cewa kina hauka ne? Na kula garin taɓargazarki wata rana za ki tona kanki,ɗazun kin ƙwaci kanki yanzun in yaji ihunki ya dawo me za ki ce?

Cikin kuka Jummai ta ke faɗin na shiga uku ni Juma, yanzun shi kenan ni ko me nayi babu nasara cikinshi,na fi wata ina zirya gidan su Hajiyarmu na ringa daure zuciyata ina zama tare da tsinanniyar yarinyar nan ina kashe ma tsinanen cikinta kuɗi duk don in samu mahaifar nan amma haƙana bai cimma ruwa ba, Kari ta ce naji yi shiru ki shirya yanzun da ya fita muma sai mu nufi gurin Malam mu ji ta bakinshi.

Ya dubeta kin isa a yi miki jaje, domin in baki dage ba ƙila lokacin rushewar al'amuranki sun zo,yarinyar nan ita ce zata yi ta haihuwa dama kin yi nasara ne haƙiƙa da kin dace, cikin jimami ta dubeshi to ni yanzun yaya zanyi? Ya ce sai mun bincika ta ce yanzun in je in zura idanu kenan? Ya ce in kina da wata dabara sai ki je ki ƙwatanta, kafin mu mu binciko. Tamkar zata yi hauka ta baro gidan Malamin, Karima tana tausarta tare da lallashinta, tana nuna mata cewa ta yi a hankali kada mutane su gane halin da take ciki.

Gidan masu jego kuwa, al'umma sai tantsowa suke yi, wasu ma ba a san su ba,ƙwananta uku ƴan Jigawa suka iso, murna gurinta ba a magana har da su Jafar da Munnir aka zo,sai da Hajiya Lanti da Tabawa suka taushi Hadiza sannan ta zo barka, Hajiya Jummai ma ta cije ta sake zuwa ana gobe suna, yanda taga ana sauke kayan ciye-ciye da shaye-shaye ga gidan ya cika da jama'a sai hankalinta ya kuma dungunzuma ta bar gidan suna. Tafe a mota direba na janta tana surutai ita kaɗai.

Ranar suna yaro ya ci suna Usman,waton sunan Alhajinmu, labarta yanda sunan ya kasance ma ƙauyanci ne. Sun samu alkhairi mai yawa daga abokan Uncle har da masu ba shi motar zuwa makaranta. Hadiza dai babu wanda yasan tafiyarta. Jummai ma tunda ta yi arba da maijego tun daga ƙasa har sama take kallon A'isha kaya ƙarshen tsada ga gwala-gwalai tun daga yatsun ƙafa har zuwa na hannu,na wuya kam ai ba a magana, sai ta juya gida. Taro ya tashi lafiya danginta sun koma gida suna sambarka, haka suka ci da wankansu, A'isha tana matuƙar mamakin yanda dangin Uncle suke tsananin son yaron wanda Nafisa ta yi wa laƙabi da Abbul khairi, Hajiyarmu ce kurum ke karantawa bata ɗaukarshi, hakan ne ma yasa A'isha sam in Hajiyarmu tana ciki bata ɗaukar yaron ta bashi nono, sai ta dinga kara itama musamman tun bayan suna Alhajinmu ya ce su A'isha su dawo ɗakin Hajiyarmu. Matsalar A'isha ɗaya, Uncle wanda har yanzun bata cikin ƴan kayan shi duk da cewa wani lokacin abun yana damunshi, A'isha har ta soma ƙyau ta ci tasha duk abinda ranta ke so kuma Hajiyarmu ta ce kada ta damu da matsalar Uncle tana zaune za ya zo ya kawo kanshi.

Misalin ƙarfe huɗu saura ya fito daga sallar la'asar ya shiga gidan mahaifan nashi don yaga Abbul khairi. Yana shiga gefen Hajiyarmu sai ya soma jin kukan yaron, da sauri ya nufi ɗakin domin ji ya yi tamkar an watsa mishi ruwan zafi, kuma ƙila ɗakin babu kowa, amma ga mamakin shi yana shiga sai ya samu A'isha tana zaune tana cin abinci, Hajiyarmu kuwa tana sallah daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallon A'isha,ji ya yi tamkar ya shiga ya hau ta da duka, waton tana zaune ma tana cin abinci? Ta bar yaro,ya ɗauki yaron ya fita a falo ya tsaya yana jijjiga yaron, zuciyarshi na ce mishi A'isha bata son yaron kamar yanda Hajiyarmu bata so shi ba lokacin yana yaro kai har zuwa yanzun a fili ya ce tab in dai haka ne gara ya kai ɗan shi gidan raino. Hajiyarmu ba ta tsaya doguwar addu'a ba,ta dubi A'isha,amso shi ki bashi ya sha, ta dubi Hajiyarmu tamkar ta ce a'a amma bata iya jan musu da Hajiyarmu, ta miƙe ta fita yasa kai zai fita daga falon zuwa inda zuciyarshi ta raya mishi watan gidan rainon yara sai ya ji muryar A'isha, Uncle ya juyo wai ka kawo shi in ji Hajiyarmu, ya zuba mata harara,ai dama nasan ba son shi ki ke ba, in dai irin rainon da Hajiyarmu ta yi mun ne zaki mishi gara na kai shi gidan rainon jarirai. Ta zaro idanu, yi haƙuri Uncle don Allah, ya dube ta ba zan amince da nufinku ba, duk cikin al'adun Hausa Fulani wannan al'adar ce bata yi min ba,babu hadisi ko aya da ta nuna cewa iyaye su dinga jin kunyar ƴaƴansu, tun ina ƙarami babu irin wuyar da ban sha ba,dan kawai ina ɗan fari da kaina na dinga addu'a Allah yasa mahaifina ya sake aure,ƙila matar zata kula dani,gara na kaishi in da zan zuba kuɗina a luran min dashi.

Dukan su ba suji shigowar Hajiyarmu ba, sai kurum suka ji ta ce A'isha koma ciki barshi ya kai shi ta kama hannun A'isha tamkar ta ƙwace, amma ba zata iya bijirewa ba, ta bi ta suka shiga ciki, A'isha tana zama bakin gado yana shigowa ya miƙa mata shi. Ta kalli Hajiyarmu sai tayi mata alama da kai,don haka sai ta amshe shi shi ko ya fita. Hajiyarmu ta dubeta kada ki dinga barin shi yana kuka, mijinki za ya iya raba ki da ɗanki, domin nasan da zaran ya sanar da mahaifinshi wannan matsala za ya gaya masa,baya kan ƙudirinshi,kin ga ku, ƴan zamani ne ki kula da ɗanki kin ji ko? A'isha ta ce to haka suka ci gaba da wankan su.

Satin su shida suka soma fita asibiti suka soma zuwa sannan gidan Anty Sadiya sai gidan su Fatima da kuma su Nafisa. Ranar da suka je gidan Anty Nafisa cewa ta yi to A'isha an gama wanka lafiya yanzun kuma sai azo a soma shirin gyaran jiki, A'isha ta taɓa baki um wane gyaran jiki bayan har yanzun Uncle yana fushi da ni? Nafisa ta ce ni fa nawa ganin tsakanin ku aka shiga, A'isha ta ce Anty Nafisa wanene zaya shiga tsakaninmu? Ni dai nafi zaton cewa na mishi wani laifi ne. Anty Nafisa tunda kuna shiri don Allah ki same shi ki tambayan min shi mana? Nafisa ta ce kada ki damu, insha Allah komai zai daidaita, yanzun dai bari na yi wa Hajiya Aliya waya can kaduna don gyara ki zan miki sosai, A'isha ta ce kin yi sabuwar Aminiya kenan? Ta ce"a'a dama muna tare lokacin da zan yi aure don dai kina makaranta ne baki ganni ba gyaran sati ɗaya naje tayi min amma ni kaina nasan nayi ne." A'isha ta ce ni da nike saran cikin watannan za'a buɗe mana makaranta ko da nayi wani gyara sai inga kamar a banza ne. Nafisa ta ce A'isha ban san ki da jan zance ya yi tsawo ba, A'isha ta ce to nayi shiru,nan take ta yi waya da Hajiya Aliya mai Zahra Global,suka gaisa Nafisa ta ce ƙanwata ce zata koma gidan mijinta daga wankan gida ina son ayi mata gyara ne sosai,Aliya ta ce wannan ba matsala zan aiko muku da duk abin da ya dace tare da bayani a rubuce, sannan zan miki ƙarin bayani ta waya, suka yi sallama A'isha dai idanu ta tsura ma Nafisa ba zasu ga ne bane,sun san irin wulaƙancin da Uncle ke mata kuwa?

Yanzun dai lamura sun juyawa Jummai,ƙwana take zaune tana saƙe-saƙen zuci, yanzun ita ce dai Jummai ita ce duniya ta yi wa haka, ashe akwai ranar da zata zo da kuɗin ta amma ta kasa samun biyan buƙatarta,shin Malamai sun daina aiki ne? Rayukan da ta kashe a baya ba kuɗinta ba ne ya biya mata buƙata? Yanzun ma tana da kuɗin amma malamai da bokayan su kasa,an ya kuwa ba zata ɗauki hukunci a hannunta ba? Wannan tunanin da shi take ƙwana kuma da shi take ta shi rashin barcin nan shi ne mafarin birkita lissafin ta.

Hadiza kuwa na ta ganin yanzun zata soma tashenta na shiga bokaye, tunda A'isha ta haihu. Su kuwa su Hajiyarmu sun duƙa addu'a fatansu Allah ya juyo da hankalin ɗan nasu ga matarshi, domin gaban kowa ya nuna tsana A'isha, kuma koda wasa bai taɓa batun komawarta gidanshi ba,hakan nan suma ba su ce mishi zasu maida ta ba, maimakon haka ma yanzun sun fi yi mata shirye-shiryen komawa makaranta don an dawo daga yajin aiki.

Sun yi shawarar haɗa ta da Uwani don kula da yaron tare da nemo mata ƴar aiki ƙarama. A'isha ta so zuwa gida, amma Abbanta ya ce a'a ta koma makarantar ta in ta kuma samun wani hutun ta zo tunda shi ya zo Ummanta kuwa suna waya koda yaushe,gurin Alhajinmu Uncle ɗin ta yaji batun komawarta makaranta,nan take ya yi kicin-kicin ya haɗa rai amma bai ce ƙala ba, duk da mahaifin nashi ya lura da hakan bai nuna ya gane me ɗan na shi ke nufi ba tunda dama ya dai sanar da shi ne amma ba wani gana neman izinin shi ba ne. Koda yaje gida ranar bashi da walwala gefen Hadiza yake ya shiga bai same ta ba sai Tabawa,nan take ya ƙara ɗaure fuska, ina Hadizan? Ta ce Um ta tafi gaisuwar mutuwa ne. Ya ce,a ina? Ta ce unguwarsu nan maƙotansu,tsaki yaja kafin ya fita ya tsani halin da wannan matan suke yi na fita babu izini, Allah ya sani shi ba zai yafe ma dukkan wadda ta fita babu izini ba, gefen Jummai ya nufa so yake ya watsa ruwa yaje gidan Nafisa,saƙo zai bata zuwa gurin mahaifiyarsu, ya sani in ta amince Alhajinmu ba zaya yi wuyar fahimta ba.

Lokacin da ya kira Nafisar ya sheda mata cewa zai zo don yana son ganinta sai ta ce itama tana son ganin shi dama ɗakin Jummai ya soma shiga tana zaune ta zabga tagumi duk ta yamutse ta yi baki yace Jummai lafiya wai duk ƙwana kin nan kin yi wani iri, ta ce (cikin rawar murya) ni wallahi duk duniyar nan ta isheni, ina ga dai an sa min hannu ne komai nayi sai ya lalact, cikin rashin fahimtar zancan ta ya ce me ki kayi ya lalace? Nan kuma sai ta dawo hankalinta ta gane da wa take magana, sai ta ce ni dai Alhaji to kalleni fa, Allah asiri ne to komai na duniya baya min daɗi ya zauna gefenta,haba Jummai ina Tauhidinki ya je ne? Kullum kin fi son ki ji ki cikin jin daɗi da walwala? Ki sani Ubangiji yana jaraba imanin bayinsa ta kowace hanya,shin baƙya ganin kema imanin ki ake taɓawa? Sai ta miƙe tsaye imani? Ni fa babu wani imani asiri ne. Tsaki yaja ya miƙe ya fita fasa yin wankan ya yi ya nufi motarshi,yana tuƙi yana tunanin matsalar mata ita ce ajalinshi, ya fito ya shiga cikin gidan, ita ce ta fito ta buɗe mishi ƙofar falo, ya shiga ciki yana cewa Sister na gaji da halin da gidana yake ciki na gaji da halin matana,mata uku amma ba wadda zan tunkara in ji sanyi? Mata fitina ne bala'i ne shin ku ma dama haka ku ke yiwa mazajanku? Dole ne ace mata kun fi yawa a wuta. Nafisa ta iso kusa da shi ta nuna mishi kujera zauna Bros kada ka faɗi zauna mu tattauna insha Allah zaka samu sauƙi.



#######
[12/21, 22:31] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 10*



Ya zauna ta ɗaga waya ta kira mai yi mata hidima, ta sanar da ita cewa ta kawo abin sha mai san yi tana da bako,ta haɗo da zoɓo ta ce to sai da ya cika kofi da zoɓon ya shanye tas,ya dubi Nafisa da gidan Hajiyarmu nasha zoɓon nan da na ce Beby ta yi shi. Nafisa ta ce wannan ma ita ce ta yi shi shekaran jiya da tazo. Ya ɓata rai shi ne ki ka ba ni? Nafisa ta dubeshi,Bros ka ce kana son ganina dama nima Ina son mu tattauna wata matsala, ya ce ina jin ki, ta ce ko dai ina jin ka fara sanar da ni taka matsalar Bros.

Ya gyara zama Nafisa wallahi na gaji da abin da matan nan suke min musamman A'isha. ta gyara zama me A'isha ta ke maka haka da zafi? Ya yi shiru yana son lakubo laifin da take mishi, amma ya kasa. Ya lumshe idanu, Sister na kasa tuna laifin da take min amma nafi jin haushinta. Nafisa kinga dai ke ƙanwata ce kuma ƙarama daga cikin ƙannena, ina miki rantsuwa da Allah ba zan tuna ɗaya daga cikin laifukan da A'isha take min ba, amma ina tsakanin jin haushin ta." Nafisa ta ce "Brother nima dalilin da yasa ni ke son ganinka kenan, to wannan abin ba sihiri ba ne kuwa? Ya girgiza kai tare cewa, a'a Nafisa kada ki zama cikin marasa yarda da ƙaddara komai ace sihiri Nafisa ta ce amma kasan gaskiya ne sihiri ko? Ya ce na sani amma wannan mu bar shi a ƙaddara, yanzun a taki shawarar mece ce mafita? Nafisa ta ce Yauwa nawa ganin dama lamuranmu ga Allah suke,to mu sake miƙa wuya gareshi, sannan mu samu malamai na ƙwarai su taya mu da addu'a, Brother ka rage bacci ya ce haka ne,kin san ni ne? Ta girgiza kai, ya ce a ƙasan zuciyata ina jin zafin abinda nake yi wa yarinyar, amma tsananin haushinta ya sha ƙarfina, sannan ƙarin damuwata wai yanzun shirin komawa makaranta su Hajiyarmu suke mata ga yaro bai yi ƙwari ba,dama saƙon da zan miki ga Hajiyarmu ki ce mata ban amince ba, sai yarona ya yi ƙwari."

Nafisa ta yi ƴar dariya, "Bros ba zan iya yiwa Hajiyarmu batun A'isha ba,don zata ce bakinmu ɗaya da kai, kuma kaima a shawarce kada kayi mata magana, don kaima jiranka take yi ta warware ka, zuba musu idanu kafin lokacin da zamu samu warware matsalar ka." Ya ce shi kenan, bari in tafi ta ce dama kenan matsalar A'isha ce damuwarka?" Ya ce kusan haka ne, sauran ma da tasu matsalar amma bata shan kaina Kamar ta A'isha.

Ta fito da kasko yau ƙwana biyu bata kara hantar a rushi ba,kai anya ma maganin yana yi kuwa? To ta gane tunda A'ishan ta haihu sai ɓarin kuɗi kawai yake yi sannan in kana son gura ta yi tsawo to sai dai in labarin Abulkhairi zakayi mishi,bari taje ta aiki su Suby su ɗibo mata rushin wuta gurin matar maigadin maƙotansu,yau zata zafafa mishi zuciya, rufe ta samu ƙofar ta soma mitar cewa ƴan iskan yara yanzun haka sun bar gidan zan zo in san yanda zan yi da ku baza ku ƙara min hawan jini ba,bayan wanda nike da shi Allah ma ya sani. Tana tura ƙofar me zata gani? Suwaiba da Safiyya tare da wasu ƙawayansu guda biyu tsirara haihuwar uwarsu suna aikata masha'a da junansu, sannan tsakar ɗakin ga ƙwalabe nan na pakalin, totolyn da kuma wata ƙwaya wai roci. Jummai bata san lokacin da ta saki kaskon hannutaba tare da faɗin na shiga uku me zan gani? Wannan iftila'in da ya faɗa mata ta gani da idanunta shi ne sanadin fashewar kaskon ta gami da zubewar gantar ta har ta manta da batun kasko,da me ya fito da ita daga ɗaki ma,wata sabuwar damuwa ta shiga gami da tashin hankali mai tsanani,komai yana da sanadi wannan shi ne sanadin da Alhaji Saddiƙ yana zaune cikin Office ɗin shi yaji shi tamkar yana jin ƙishi, sai da ya shanye goran swan water babba guda ɗaya mai sanyi ya jingina yana mamakin kanshi, domin ya sani sai ya tashi daga Office bai shanye goran ba,jin zuciyarshi ya yi tamkar an wanke wani nishaɗi gami da annashuwa, ya rasa jin shi yake tamkar sabo yau akayi sht,nan take ya miƙe ya nufi fita daga Office ɗin cikin zuciyarshi yana son ya ji shin shi ne kuwa? Sai yake ganin tamkar wani zai kalleshi ya kira shi da wani suna ba nashi ba.

Gidan Nafisa ya nufa bai shiga ciki ba a harabar ya tsaya ya kirata da waya,ta kalli mijinta ta ce "Dear,Bros ne wai ba zai shigo ba sauri yake yi." Alhaji Bello ya ce to ki je mana zan fito mu gaisa nima,tana isa gurin shi da fara'arta me zai hana ka shigo Bros sai kurum taji ya ce kalleni Sister ni ne kuwa? Ta zaro idanu ban gane ba kamar ya ya kaine? Ya ce ji na nike tamkar ba ni ba, ta ce kuma? Gaskiya ka tsaya da addu'a tsayin daka ya ce ina yi daidai gwargwadon hali, Alhaji Bello ya iso gurin yana cewa Alhajin Allah haɗuwa ta yi wuya, Alhaji Saddiƙ ya ce a'a dama kana ciki ne? Ya ce dawowata kenan garin, Alhaji Saddiƙ ya bashi hannu suka gaisa, ya yi yayi su shiga ciki amma ya ce sauri yake yi.

Cikin ƙwanakin Alhaji Saddiƙ yana jin canje-canje tare da shi, sai dai rashin lafiyar Hajiya Jummai ya hana shi nutsuwa sosai, zuwa aka yi aka sameta tana ƙwance cikin matsanancin hali a ƙofar ɗakin su Suwaiba, waɗanda su lokacin tuni sun bar gidan. Bayan gwaje-gwaje Likitan ya tabbatar wa maigidan nata da wata ƙanwarta cewa jininta ya yi matuƙar hawa fiye da da, sannan wasu alamomi sun sa mun yi mata gwajin suga, mun kuma gano tana dashi,ga kuma ciwon ta na tun farko waton zuciya,don haka tana cikin haɗari,in dai zata dinga sa damuwa cikin zuciyarta. Alhaji Saddiƙ ya tausaya mata tare da buɗe bakin aljihunshi don ganin ta samu lafiya, dangi suna ta zuwa dubara yawancin su sukan ce sai dai suje don mijinta amma ba wai don halinta ita kanta ba domin ba tsarin ta ba ne zuwa duba mara lafiya ko gaisuwa,ko barka, duk yanda ku ke in ba irin ƙawayansu ba.

A'isha tare da Hajiyarmu suka zo, sun same ta zaune ta jingina da filo fatan acca take ci watan tuni ta soma amfani da abincin masu shuga, cikin zuciyarta tamkar ta shaƙe A'ishan dan takaici,nan ta ture ƙwanon gabanta gefe tsani wannan tsinanniyar yarinyar,da ƙyar ta amsa gaisuwar su, maigidanne ya shigo yau ƙwana uku A'isha bata sa shi a idanunta ba,tun ranar da ya zo ya sake yi mata kashedi game da yaron shi kuma ya yi mata rantsuwa da Allah cewa in har ya samu labarin cewa ta tafi makaranta ta banzatar mishi da yaro zata sha mamakin hukuncin da zai yanke mata.

Bayan ya rage tsawo ya gaida gyatumarshi ta tambayi mai jiki ya ce da sauƙi, A'isha tamkar ko yaushe cikin girmamawa ta gaishe shi tasha mamakin yanda ya amsa cikin sakin fuska, idanunshi suna kallonta sannan ya iso kusa da ita yana cewa, kawo Alhajin nawa,wato Abulkhairi ta kunto shi daga bayanta ta miƙa mishi,yau idanunshi sun fi son kallon Beby fiye da yaron shi, itama ta lura da hakan ko in ce kusan duk ƴan ɗakin sun kula da hakan ne ma yasa Hajiyarmu miƙewa tare da cewa juma Allah ya ƙara sauƙi, sannan ko tana buƙatar wani abu ne ta faɗa a kawo mata? Jummai wadda ta zurfafa tunani gurin tuno kaskon ta wanda sai yanzun ta tuno da shi a'a kawai ta ce ma Hajiyarmu ba tare da taji me tace ba, Hajiyarmu ta nufi fita tana cewa A'isha goyo shi mu je.

Ta dubi Uncle ɗin nata zamu tafi ya yi ɗan murmushi, Beby ki zauna mana in kaiki,ta tsura mishi idanu,yaushe rabon da ta ji wannan sunan daga bakin shi? Yaushe rabon ta da ganin murmushin shi tare da muryarshi nan mai daɗin sauraro, ta sauke ajiyar zuciya, kayi haƙuri direba ya kawo mu ya ce to juyo in sa miki shi,ta juya mishi baya yana sa mata yaron ta goya shi da ƙyau ya ce kin yi ƙyau da goyon, murmushi kurum ta yi bata ce ƙala ba ta dubi Hajiya Jummai mun tafi Allah ya ƙara sauƙi,bata amsa ba sai hannu ta ɗaga mata. Shi kuma ya bi ta a baya sun fito daga ɗakin ya ce Beby ta ɗan tsaya amma bata juya ba, yaushe za ki koma makaranta? Ta dube shi sannan ta dubi ƙasa,jibi ya zuba mata idanu. Ta yaushe zaki koma ɗakinki? Ta ce sai dai ka tambayi Hajiyarmu, ta ci gaba da tafiya, daga nan ya tsaya yana kallonta, har ta ɓace ya yi ajiyar zuciya tare da juyawa.

Kuka rurus ya samu Jummai tana yi, ya iso gurinta a tsorace lafiya kuwa Jummai? Ta soma tari cikin kukan faɗin "shi kenan ni yanzun ba ni da amfani tunda cututtuka sun min katutu shi ne kana ganin A'isha ka bita." Ƙanwarta taja tsaki, gaskiya Jummai in ba zaki ƙwantar da hankalinki ba zan tafi ba zai bita ba ba matarshi bace? Alhaji Saddiƙ ya ce haba Jummai,haba Jummai!! Wai shin ƙaramar yarinya zaki koma ne? Kin san fa halin da ki ke ciki, A'isha baƙuwa ce a gare ki? Don Allah kiyi ƙoƙari ki zama mai natsuwa don ki samu lafiya. Indo ƙanwarta ta ce ina zata ƙwantar da ranta ba saka damuwar ce tasa ta cikin wannan halin ba? Ita dai jin su take yi ba zasu gane halin da ta ke ciki ba ne. Alhajin fita ya yi cikin damuwa.

Yinin ranar A'isha ce a cikin zuciyarshi har zuwa dare. Ya fito wanka ƙananan kaya ya saka jeans blue da shirt fara turarenshi na ko yaushe ya saka, Hadiza ta shigo sanye da riga da sket na lallausan leshi mai ruwan madara. Ta dube shi Darling ka gan ka kuwa? Sai ka ce saurayi ɗan shekara ashirin? Ya dubeta kada ki maida ni baya mana. Ta ce Allah kuwa, ya ƙwashi wayoyinshi da makullin motarshi ta kalli agogo ina zaka yanzun tara ta kusa? Kuma ga abincin ka fa,ya ce zan ci gidan Hajiyarmu yau tuwo nake son ci kin san basa rasa tuwo,ko dan saboda Alhajinmu, ta ɓata rai shi kam bai kula ba ya fito abin shi ta biyo shi an kusan fara news fa, ya ce ai zan kalla a can ta tsaya tamkar hawaye ya zubo mata don takaici tasan gurin A'isha zai je ba wai don mahaifanshi ba, ta yi tsaki ta juya ciki.

Hajiyarmu tana kula da A'isha, tun da taga fara'ar maigidanta ta fara sukuni, yanzun ma su suna falo ne suna kallon labarai amma ita ta shiga ɗaki ta ƙwanta alhalin ba wanda ya kai ta son labarai. Ita kam A'isha so take ta keɓe kanta ta yi tunanin shin Uncle ya yafe mata ne? Ko ko don yaga Hajiyarmu ne? Kai a'a ba don haka ba ne tunda ko a cikin gidan ya kan yi mata wulaƙancin da ya so, tana ganin Allah ne ya amshi addu'arta ya juyo mata da tunaninshi gareta. A fili ta ce Allah yasa haka ne, lokacin da take wannan tunanin shi kuma ya iso falon har yasa Baraka ta kawo mishi tuwo, bayan sun gaisa da iyayan nashi ya kasa cin tuwon na kirki domin waɗanda ya zo domin su bai gansu ba, daga bisani ya miƙe yana kallon gefen da Alhajinmu yake yana cewa bari naga Abulkhairi ba su ce mishi ƙala ba ya nufi ciki,ƙamshin turaranshi shi ne yasa ta buɗe idanunta da ke lumshe fuskarta kurum yake kallo ga nashi zaton bacci

Please Login or Register in order to submit comment