Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

isa gurin Aminin nashi ya kuma samu sa'ar riƙe bulalar ya ce haba Friend wannan bai dace ba,ai Beby ta wuce duka.

Abban yana haki ya ce bata wuce ba, kuma daga yau bata babu boko na hana, ta zauna ta nemi aljannarta,bokon banza da iyakar shi duniya zata kashe aurenta saboda shi? Abu na gaba kuma ban yafe miki ba in har kika kuma shan wannan maganin sannan ki nemi wani uban ba ni ba,ke hanyar Jigawa ma kada ki yarda ki biyo ta, ya maida bulalar shi cikin aljihu ya nufi fita, Uncle ɗin ya bi shi don Allah ka tsaya ka jini, ya ce ba zan tsaya ba na kula kai ne ka shagwaɓa ta in ta ɓata maka tafi ƙarfin duka ne? Kasan sa mata tukunna ta san kai ba abokin wasanta ba ne da zata aikata laifin sannan ta raina ma mutane hankali wai ba ita ce ta kawo maganin ba, to ba sai ta faɗi uban da ya kawo ba? Uncle ɗin ya bishi suka fita ya yi yayi dashi ya bari sai gobe ya tafi ya ce shi sam bai shigo Katsina da nufin ƙwana ba, Kano zai ƙwana, dole ya kira wani direban domin Jabiru yana buƙatar hutu, ya shiga ya kaishi Kano.

Lokacin da ya shigo gidan har lokacin Aishan tana tsugunne a gurin tana kuka,sam bata ga laifin mahaifin nata ba domin ya yi mata haka ne domin gyara,in ma laifin ne tafi ganin na Uncle ɗinta wanda ya kasa yin haƙuri da ita koda kuwa ta aikata laifin da ake zargin ta dashi, ganin Uncle ɗin ya nufo gurinta sai ta miƙe da hanzari ta nufi ɗakinta tare da maida ƙofa ta rufe. Ya yi ƙwanƙwasawar duniya ta ƙi ta buɗe, ya yi lallashin haba Beby yi haƙuri ki buɗe mana,taƙi dole ya ƙyale ta,sai in ta huce ya san fushi ta yi domin kuwa bata da taurin kai tun zamanta da shi yau ce rana ta farko da yaga fushinta.

Wasa-wasa har washegari ba ta fito ba,ya zaci in ya tafi aiki zata buɗe, amma da ya dawo ya tambayi Tani ta tabbatar mashi bata fito ba, ita kuwa sallah kawai ke ɗagata daga gado, aikin kuka kawai take yi bai ɓata lokaci ba gurin nemo masu saka ƙofa suka cire mishi ita ya jingine ta gefe ya shiga tana ƙwance ruf da ciki ta kifa kanta kan filo ya ɗago ta Beby yi haƙuri tashi zaune,ji ya yi jikinta zafi rau, gashi fuskarta ta kumbura dam saboda kuka, ya yi lallashin duniya ta ƙi shiru,dole ya kira Nafisa cikin waya cewa ta zo da matsala. Tabawa tana kallon Nafisa ta fito cikin motarta ta shiga sheƙa dariya taje gurin uwargijiyarta tana cewa Antyna ga waccan uwar iya yin nan bata san wadda take son bata nan ba, suka yi ta dariya domin basu san cewa ta dawo ba, Tabawa ta ce na rasa zaman da yake yi a sasanta, Hadiza ta ce naci ne irin nashi, kuma zai haƙura da ita da kanshi.

Nafisa ta zuba wa Aisha idanu, me ya faru haka jikinta duk tabon bulala? Uncle ya ce Sister ki dai lallasheta,nasan zata gaya miki komai, ina zuwa,ya fita Nafisa ta ce A'isha rigima ku kayi da Brother ɗin?" Tana buɗe baki sai kuka ya ƙwace mata, muryarta ta ƙi fita, cikin kuka da dasashewar murya take sheda ma Nafisa yanda lamuran suka faru. Nafisa ta tausaya mata kuma ta amince cewa A'isha ba zata aikata hakan ba, ta ce maza kenan, amma shi Bros ya mance haƙurin da ki kayi dashi baya sannan babu binciken da ya yi,dan ya ganshi a sasanki ai gidan da mutane kuma yafi kowa sanin cewa Hadiza zata iya aikata abinda yafi ga wannan la'ananniyar mai aikin tata sai ka ce irin karuwan nan na maraba, ta dubi A'isha tashi ki shiga kiyi wanka tana fitowa zazzaɓi ya rufe ta,sai rawar sanyi take yi, Nafisa ta ce shirya muje asibiti, ya shigo ta ce dole zamu je muga Likita, jikinta sai rawa yake yi, ya ce to kuje ko in zo muje, ta ce bari kawai muje mu dawo..



#######
[12/24, 09:00] Ummi Tandama😇: *📔📔📔 Page 16*


Amsoshin da ta bawa Likitan sune suka sa shi ya ce ba zai bata magani ba har sai ya yi mata gwajin fitsari sannan ya yi mata wasu gwaje-gwaje ya fitar da sakamakon ciki wata biyu. Nafisa ta dube ta kin ga Ishara ko? To da yaja garin duka cikin ya zube da ya huta. A'isha kuwa shiru kawai ta yi fatanta Allah ya tona mata asirin wanda ya ƙulla mata sharri,ya bata magungunan da suka dace suka nufo gida.

Yana zaune yana kallon Aljazira suka shigo,su Hadiza basu ga fitar su A'isha ba sai dawowarsu suka gani, Tabawa ta ce"innalillahi, wannan tsinanniyar bata tafi daga garinnan ba ko ko dawo da ita aka yi?" Hadiza ta ce wannan fa kada tasa nima in yi kisan kai, wallahi na tsane ta, amma Tabawa dole ne ki samo wata dabarar."

Shi ko ya biyo su har cikin ɗaki, A'isha ta ƙwanta har yanzu in ta kalleshi ranta na zafi, ta lumshe idanu ya ce kun samu magani Sister? Ta ciro sakamakon daga cikin jakarta ta miƙa mishi ya amsa yana dubawa ya kalli Nafisa, wadda ke kiran layin Hajiyarmu, ya ce Sister yana nufin Beby tana da ciki? Kafin ta bashi amsa Hajiyarmu ta ɗaga wayar nan Nafisa ta shaida mata ciwon A'isha ta kuma shaida mata cewa ciki gare ta wata biyu, Hajiyarmu ta ce Allah ya bata lafiya, haka ta yi kiran sauran ƴan'uwa tana shaida musu, shi kuwa gaban A'isha ya zauna, Beby don Allah ki yafe ni lallai yanzun na amince ba laifinki ba ne ya miƙe ya nufi ɗakinshi ya ciro ƙwalayen maganin yaba Nafisa kin gan su nan har da alamun wanda aka sha a ranar sannan karanta ki gani da tasha da cikin ya fita tunda sun rubuta hakan, Nafisa ta gama dubawa ta ce kasa idanu sosai musamman kan wannan Tabawar, ya jinjina kai shi kanshi baya ƙaunarta, amma yanzun ba shi da hujja, sai dai zaya sa idanu.

Nafisa tana gidan har dare sannan ta ƙara bawa A'isha haƙuri ta tafi shi kam har lokacin bai ga fuska gurin Aishan ba, gashi ranar gurin Hadiza yake,yana nan har sha biyu sannan ya nufi gurin Hadiza yana fitowa har ya gota ya nufi ɗakinshi sai yake jin magana ƙasa-ƙasa ɗakin Hadiza labulen window ya ɗaga,suna zaune kan gado Tabawa tana cewa ina zaton bata da lafiya ne fa dama tsinanniyar zata mutu da mun huta. Hadiza ta ce lallai wallahi da sai nayi party, yanzun wane kalar makircin za'a shirya mata tunda wannan na maganin sai mun ƙarasa shi, ta ce ai ba wahala zamu yi gurin shiga sasanta ba,kin san ita idan mijin na nan bata da lokacin kowa sai na shi, to bari zamu yi sai ranar da miji ke gurinta in ya kama week end sai mu samu wani ya haɗa mana layar ƙarya asa sunan ki da nashi ace an shiga tsakanin ku a zuwan ita ce tayi sai musa a inda zai gani kin san zai kai a buɗe mishi, to daga nan sai muyi yin wasu dabarun zai yarda tunda zai zarge ta yanzun ma dama cikin zargin take. Hadiza ta ce hakan ki naga zai yiwu? Ta ce to gidan da na soma aiki mata shidda muka kora da wannan dabarar, Hadiza ta ce shi kenan Allah yasa wannan karon mu dace ko da yake wancan karon ma mun dace tsabar naci ne da kuma ƙwadayi. Tabawa ta ce ina kallon lokacin da ya ɗaura mata mari da yaga maganin amma don rashin zuciya ta dawo ina zato har da saki ya yi mata, Hadiza ta ce ke in mungwada komai be yiwu ba Allah zan sa mata guba ne kawai. Tabawa ta ce kin Istigfari daga baya shi kenan kin huta,ya saki labulan ya zo ya turo ƙofar,dukkansu suka waigo ya ce to duk na jiku, Allah ba azzalumin sarki ba ne,yau gashi ya toni asirin ku ya juya ya fita ya barsu cikin zufa da tashin hankali shi kaɗai cikin ɗakinshi,ya zurfafa cikin tunani har hawaye sai da ya yi saboda tausayin Beby har amsa laifin nan don kawai tsabar bata son tashin hankali,ga dukan da ta ci bada laifinta ba,nan kuma gashi suna shirya mata sabon makirci ciki har da yunƙurin kashe ta lallai zama da Hadiza hatsari ni tunda har ta furta zata aikata gara ya ɗau matakin kada gidanshi ya zama sansanin ɗaukan rayukan jama'a.

Da safe kuwa ya miƙa mata takardarta,saki uku don ma kada ace ya yi haƙuri Allah yaga zuciyarshi. Da safe da ya fito bayan ya dawo daga masallaci ya gama duk shirye-shiryen shi zai fita zuwa Office zaune ya samu Hadiza da Tabawa tana bata shawara kan cewa taje ta bashi haƙuri, ya yi sallama sannan ya miƙa mata takardar, gashi kada in dawo in same ku cikin gidana, ya fita ya bar ta tana ihu tare da roƙonshi har gidan Aisha wato sasan A'isha ta bishi tana ba shi haƙuri kukan ne ya tashi A'isha daga bacci tun bayan da tayi sallar Asubahi,yana shiga ɗakin A'isha ta bishi ta tashi zaune a razane tana kallonta, ya ce na ce ki tafi me zan miki,saki uku ne ki je gaba kiyi kisan ba gidana ba na gaji, A'isha ta ce haba Uncle me zai saka yanke wannan hukuncin? Ya zauna kusa da ita wannan shi ne mafita,ya koro mata komai a gaban Hadiza haƙuri ta shiga bawa A'isha tare da cewa ta taimaka mata don Allah, A'isha ta ce Uncle me kaga za'ayi? Ya ce gidan su kawai zata sannan ya rusuna gaban A'isha, Beby don Allah ki min afuwa bisa abubuwan da na miki ba da laifinki ba, cikin sauri ta miƙe ta ce Uncle don Allah ta shi don Allah kada ka kuma min haka na sani kana da hujja sai dai na gode Allah da ka gane cewa ba laifina bane, sannan kayi saurin yiwa Hadiza saki uku,ka sani ko sanadin wannan ta shiryu? Ya ce sakin za ya fi sa ta shiryuwa in tayi wani auren gaba in zatayi irin wannan sai ta tuna da sakin sai ta fasa. A'isha ta dube ta kije gidan ƙila manya ba zasu rasa yanda za'ayi ba, Itama dai tasan ta faɗi haka ne saboda Hadiza ta tafi,ta kuwa miƙe ta nufi gidan nata ganin zai yiwu a maidata.

Bayan fitarta A'isha ta dubeshi baka ƙyauta ba Uncle,ai sai kayi mata ɗaya shi ne na gargaɗi in yaso sai ayi mata nasiha baka gudun Allah ya jarabce ka da sonta? Ya ce insha Allah na rabu da ƙaya ne, Hadiza ba zata taɓa hankali ba. A'isha ta ce gashi ka saba da mata uku, ya ya zakayi da ni ɗaya dole kenan sai ka sake aure? Ya kalle ta Beby ni kam kin isheni zaman duniya, ta ce yanzun shi kenan nayi missing ɗin makaranta ta kenan,ya ce in ji wa? Ta ce ka manta abin da Abbana ya ce? Ya yi ɗan murmushi ai dole ne muje mu wanke ki gurinshi ta ce yaushe? Ya ce da zaran kin soma jin sauƙi.

Mahaifin Hadiza da kanshi ya samu Alhajinmu da batun ya ce be sani ba, amma bari ya kira Abubakar ɗin, Alhaji Saddiƙ kuwa ya zayyano musu duk yanda al'amarin ya kasance, Alhajinmu ya ce laifinka a nan saki uku da kayi,Babansu Hadiza ya ce ai ana gyarawa inji wasu Malaman.

Alhajinmu ya ce a'a duk wani Malami da zai ce ana gyara saki uku wannan yana faɗin son zuciyarshi ne kawai, abinda wasu Malamai suka dogara da shi,shi ne lokacin da Manzon Allah ana saki uku a koma,to lokacin Umar Allah ya yarda da shi,sai ya hana saboda yanda maza suka maida saki uku kowa saki uku, shi ne wasu Malamai suke maidawa saboda Manzon Allah bai hana ba amma ya umarce mu da cewa muyi biyayya da Sahabban sa, domin su sun ɗora ne daga in da ya tsaya don haka muyi haƙuri Allah ya haɗa kowannansu da rabon shi na alkhairi in kuma da rabon zasu zauna can gaba sai su zauna. Baban Hadiza ya ce ka dai ɗaure mishi gindi ne. Alhajinmu ya ce to ni dai akan su koma saki uku gara na ɗauki laifin da ka ɗora min, ya tashi ya yi saman shi haka taron ya watse kowa ya kama gabanshi shi kuwa Uncle ya yi matuƙar farin cikin faruwar hakan.

Sun je Jigawa ƙwanansu ɗaya inda Uncle ɗin ya wanke Bebyn tasa gurin mahaifanta har sai da suka tausaya mata Uncle da kanshi ya sanar da Abban cewa zata koma karatunta, sai dai zata bar Sokoto zata dawo Kano ko Zariya.

To Zariya ta samu lokacin da zata tafi ta ce ba girmanshi ba ne zama babu mata, ya ce hakan ya fi mishi ƙwanciyar hankali, zai dinga zuwa mata week end haka rayuwarsu ta ci gaba cikin sha'awa, ta haifi ƴar ta mace wadda ta ci sunan Hajiyarmu, suna kiranta Ummulkhairi.

Ƙwanci tashi babu wuya a gurin Allah,yau ga su A'isha ana rantsar da su matsayin likitoci ƙwararru, dukkansu suna sanye da kaya na musamman lokacin ƴaƴan A'isha huɗu ta ƙara Abubakar sunan Uncle suna kiranshi Khalifa, sai takwararta A'isha suna kiranta Humaira. Ta samu lambar yabo da ƙwarewa ta musamman, Uncle ɗin ta da ke zaune cikin ɗinbin jama'ar da suka halarci gurin. Alhaji Bello ya ce kai Alhaji Saddiƙ ban da na san A'isha zan ƙaryata ita ce me ƴaƴa huɗu, Alhaji Saddiƙ ya ce abinda zuciyata ke faɗa min kenan,taro ya tashi in da suka yi hotuna da danginsu da ƙawaye, su Abdulrahman da amaryarsa da su Jafar duk sun zo su Anty Nafisa kuwa sai rabon abubuwa da aka buga suke yi taro ya tashi suka shiga shirin zuwa gida.

Sati ɗaya da gamawarsu ya ɗauki A'isha tare da yaransu wai za su masa rakiya,sai gasu gaban wani katafaran gini mai hawa biyu, maigadi ya buɗe musu suka shiga, tun daga yanda aka tsara falon ƙasan ta gane cewa asibiti ne. Sun hau ko'ina da ina, duk abinda ake nema a cikin asibiti akwai shi a nan. Sai da suka fito falon ƙasa ya miƙa mata makullai tare da takardun asibiti ya ce Beby wannan ita ce gudunmawa ta gare ki. Ta zuba mishi idanu ta rasa me zata ce kawai sai ta rungume shi tare da sumbatar ko'ina a jikinshi sai kawai su Ummulkhairi suka soma tafi suna dariya suni ta murna da yaran.

Shi ne ya ɗauki nauyin nemo mata Likitoci waɗanda suka karanci fanni daban-daban sannan ta samu aiki a babban asibitin gwamnati na jihar ta Katsina domin taimakon talakawa musulmai. Domin ta sani ba kowane zai zo asibitin na taba mai suna (AishSadik Hospital)ita ce tasa mishi suna, haka nan A'isha ta ci gaba da aikinta tare da kula da Uncle ɗin ta da kuma ƙyawawan ƴaƴansu, Alhajinmu girma ya sa shi dole ya ajiye aikinshi duk Uncle ke kula da komai shi kuma ya huta rayuwarsu mai ban sha'awa.

Yasa hannu ya zare farin gilashin idanunsa ya bita da kallo, maimakon kallon (CNN) da yake yi,ta yi ƙyau cikin doguwar rigarta atamfa ƴar Holand,ƙirjinta cike tamkar ba ta taɓa shayarwa ba,yanzunne take cikin shekarunta ashirin da biyar in bai manta lissafi ba yanzunne komai nata ya ƙara zaunawa musamman ƙugunta,lallai shi kan ya gode mahaliccin shi da wannan baiwa ga kuma ƴan yaranshi, bai san ta iso gurin ba sai kawai ya ji ta hura mishi idanu, firgigit ya yi tare da jawo ta jikinshi, ta ƙwanta a cinyoyinshi tana kallon fuskarshi ya ce Beby kullum ƙara ƙyau ki ke yi da ƙuruciya bana gajiya da kallonki. nima ai bana gajiya da kallonka, ya ce in yaran nan sunyi hutu ya kamata mu ɗan fita ko na sati uku ne zuwa waje suyi mana rakiya ƙila ma su samu ƙani ko ƙanwa, ta ce ai sun kusa hutun nan da sati mai zuwa.

A birnin na Misira waton Egypt wata rayuwa suke yi tamkar sababbin aure,sam ya manta da Jummai da mummunan zaton da ta saka shi a baya, yanzun sai farin ciki tare da godiya ga Allah da baiwar da ya yi mishi na samun mace jaruma mai haƙuri da biyayya,haƙiƙa da duk mata zasu ɗauki halin haƙuri da sauƙin kai irin nata, da mace-macen aure ya ragu. Tabbas haka ne, Allah Ya bamu haƙuri domin Allah yana tare da masu haƙuri.



ALHAMDULILLAH!

Na gode ƙwarai
Taku ko yaushe, Halima Abdullahi K/Mashi.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment