Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah yasa da ta da rahamarshi duniya da lahira. Haka dai ta dangana ta rungumi karatun ta ka'in da na'in.

Jummai da Hadiza kuwa, duk sun miƙa lamarinsu ga boka, ko in ce ɗan tsibbu. Jummai kam yanzun ta yarda Malamin nan zai share mata hawaye da A'isha ta jima tana sa ta zubarwa,ta gane hakanne lokacin da ta tinkari Alhajin da maganar son ya yi mata ginin da ya jima yana son mata a cikin gidan, daga baya ya share zancan. Alhajin bai Musa ba, ya ce zai sa a auna gurin duk dai da cikin gidanne. Malamin ya ce ta haɗa da ladabi da biyayya, don haka yanzun wani sabon ladabi ta samo.

Hadiza kam tafi ga magungunan mata irin waɗanda ke saka maza fitina, gashi ta ƙware gurin iya jan hankalin namiji,takan zuba mishi cikin ruwa ko abinci in ya ci kuma ta zo da salon tana jan hankali. Ba za ya iya haƙura ba,don haka sai ta sara mishi kuɗi haka zaya bata sannan ta yarda suyi auratayya wa'iyazubillah. Hadiza ba wai ƙyaƙƙyawa ba ce, amma irin matannan ne waɗanda suka san kan shawo kan maza,ta hanyar fizgar hankalinsu ta iya ƙwarƙwasa sosai, shi kan shi ya so ace A'isha ce ke mishi irin salon jan hankalin da Hadizan ke mishi.

Tuni an soma ginin Hajiya Jummai, gini ne za'ayi shi me tsari, shi kan shi ba zai ce ga dalilin da yasa ya ƙuƙe kan cewa sai an yi ginin cikin ƙanƙanin lokaci ba. Hadiza ta dame shi da son sanin wanda zai shiga ginin sai ya ce mata me rabo.

Yau kimanin ƙwana sha huɗu kenan A'isha ta yi a makaranta, har yau bata saba da kowa ba, kasancewar ta mara saurin sabo,gata miskila bata cika sakin fuska ba,ran da ta cika ƙwana huɗu ranar ta nemi Maimuna ƙawa Anty Nafisa izuwa yanzun sun saba sosai,in bata da lakca can takan je ta yi hirarta, Maimuna wayayyiyar ce ta gaske,tana ganin A'isha ta ga cewa A'isha ta yi mata,tana koyar da ita salo-salon yanda zata da kanta da mijinta,kai har da yarda zata dinga yiwa mijinta magana, tafiya da dai sauransu. Wani kunun Aya,dabino da cukwi da take bata mara suga sai madara,ga wata gumba da take dama ta da madarar shanu, A'isha da kanta ta ji tana sha'awar mijinta. Yau kam da ta je ƙin sha tayi ta ce, Anty Maimuna Uncle ba ya kusa gashi kina ta bani waɗannan abubuwan sai su dame ni fa, Maimuna ta ce ke baki san yanda zaki jawo hankalinshi ya zo gareki ba ko? Nan ta shiga tsara mata yanda zata yi, sannan ta bata garin bagaruwa ta ce ta ringa tsarki dashi in taji ranar zuwan nashi kafin ya iso.

yanzun haka da take ƙwance kan gadonta kusan ƙarfe goma tasan yanzun yana gida gaban laptop domin lokacin ƙwanciyarshi bai yi ba. Ta shiga murza wayarta shi take nema,jim kaɗan layin ya shiga ta juya rigingine, muryarshi ce ya ce "Beby" ta ce na'am Uncle ya ya ka ke? Ya ce lafiya lau ke fa? Ta ɗan runtse idanu ta buɗe sannan ta ce ina cike da kewar ka,ya cire gilashin idonshi tare da matsar da laptop ɗin, A'isha nima haka,ta ce,kai ai kana da wasu matan, ya ce, Beby basa min rainon da ki ke min, ba tonon asiri ba ne ko yi dasu,ke daban ce wancan satin fa da kin ganni al'amura ne suka yi min yawa, da kuma tunanin kada ki ce wannan Uncle ɗin ya nace min. Ta yi ƴar dariya cikin kissa sannan ta ce "Uncle ɗina kenan,kana ganin in da zaka zo kullum zaka gundure ni ne?" Cikin mamakin ta ya ce, Beby sai ina ga tamkar ba ke ba, Beby da ba ki iya gaya min yanda ki ka damu da ni ba, da zaran abubuwa sun yi sauƙi za ki ganni." Ta ce, to sai da safe, ya ce zan zo miki cikin mafarki kinji, ta ce sai na ganka. Sai ta samu kanta da sumbatar wayar tare da saurin kashe wayar. Sautin kiss ɗin ya daki dodon kunnanshi ya ratsa dukkan jikinshi. Haƙiƙa ta saukar mishi da kasala,yana jin ba za ya iya ci gaba da aikin gabanshi ba, dole ya rufe komai ya tashi. Ita kuwa juyi ta yi tana jinjina ma ƙoƙarin da tayi tasan in a gabanshi ne duk da Anty Maimuna tana bata ƙarfin gwiwar ta ringa mishi hakan ba zata iya ba.

Washegari wuraren ƙarfe shida lokacin ta fito daga lakca don ranar uku da mintuna suka shiga, ta buɗe gidanta ta shiga dama ta riga ta yi abincinta, magriba kawai zata yi sannan ta ci. Zaman ta kenan sai ta ji ana ƙwanƙwasa mata gida ta je ta buɗe. Wasu ƴammata ta gani su uku, suka nuna mata wani gida kusa da nata,ga gidan mu nan munce ne bari mu shigo mu gaisa, cikin fara'a A'isha ta ce ku shigo ta matsa suka shiga.

Abinka da wayayyun ƴan boko,nan suka sake, ita dai taje tayo sallah ta basu abinci suka ci har suna santi, nan suka sanar da ita sunayensu. Saliha da Amina,Kiristar kuma Linda ƴar kaduna ce,su kuma biyun nan Sokoto suke,suma course ɗin da take yi shi suke yi. Tana zaune dai ta ma kasa cin abincin don bata sake da su sosai ba,su ne dai sukayi tamkar dama sun santa, sai ta ji ana bugun gida, ta kalli agogo cikin zuciyarta ta ce to ko wanene kuma, ƙarfe baƙwai da rabi,ta fita tun kafin ta buɗe ta ji ƙamshinsa, cikin hanzari ta buɗe tare da cewa, Uncle tafiyar dare? Jawo ta ya yi zuwa jikinshi ya rungume, tare da faɗin I miss You Beby, ta amshi Jakar hannunsa "zo mu je Uncle kai kaɗai ne? Ya ce ni da Jabiru ne, sai da na kai shi masauki sannan nayo nan. Anan nayi magriba da isha'i, suna shiga falon ya yi turus yana kallon ƴan matan da ke zaune, fuskarshi da alamun tambaya, ta ce maƙotana ne suka shigo don mu saba,ta dube su ga Uncle ɗina, nan suka shiga gaishe shi kafin suka miƙe suka ce sai da safe A'isha Mustapha, ta ce na gode. Ya zauna nan ta shiga rawar jikin kawo mishi wannan da wancan,shi kam duk in da tabi kallonta kawai yake yi yana sonta.

Yana cin abincin suna hira tana mishi mitar zuwan ba zatan da ya yi mata, gashi bata mishi wani abu na musamman ba, ya ce shi ai ita ce ta musamman ɗin shi, cikin ƙwanaki ukun da ya yi a Sokoto ya kuma yarda A'isha ce kurum ta dace da rayuwarsa. Haka ya taho da kewar ta itama tana kewarshi, haka abubuwa suka yi ta faruwa lokaci ya dinga zuwa yana wucewa, Uncle yana ziyartar A'isha duk bayan mako ɗaya ko biyu.

Ƙwatsam! Wannan zuwa ya sameta ta tana fashin sallah, kuma ranar ta fara, da ƙyar ta lallasheshi ya yi ƙwana biyu tare da gamsar dashi ta hanyar wasu ƴan dubarun nata.

Wani sabon al'amari tun daga lokacin sati na huɗu kenan rabonshi da Sokoto, sannan wayar ma yanzun ba kamar da ba, kullum uzurin yake bata wai abubuwa sun mishi yawa gashi ana gyaran gida, daga baya ma in ba ita ce ta kira shi ba shi kam baya da lokaci. Abin ya soma ba wa A'isha tsoro,nan gefe kuma ga wata matsala da ke damunta. Motsi cikinta ke yi,ta sa rai ya zo ta sheda mishi, amma shiru suna daf da fara jarabawa abin ya matsa mata don haka ta kira Nafisa ta sheda mata,Anty Nafisa ta ce baki gaya ma Uncle ɗin ki ba? A'isha bata son saurin tona cikinta nata ganin gaske ne uzuri ya yi wa Uncle yawa ne, shi yasa har yanzun bai zo ba,ba zata yi saurin kai ƙararshi ba, ta ce abubuwa sun yi ma Uncle yawa bana son na gaya mishi zaya tada hankalinshi, ya ce zai bar aikin gabanshi ya taho. Nafisa ta ja tsaki,wane abubuwa ne suka mishi yawa baya ga komai da ya tsaida, Ya shiga harkar yiwa Jummai gini. Gabanta ya faɗi ta ce gini kuma? Nafisa ta ce bai sanar da ke ba kenan? A'isha ta ce, yace min dai yana gyaran gida. Nafisa ta ce, to ai gyaran kenan, Jummai ya fafaramma gini irin kuɗin da yake narkarwa a ginin sai kin gani yanzun ya gama kayan da za'a zuba ma daga (Chaina) za'ayo Odar su, A'isha ta ce to Allah yasa alheri." Nafisa ta ce,au! Ke bakiji haushi ba? Ta ce, to in naji ma Anty Nafisa ya ya zan yi? Tsaki Nafisa ta kuma ja,ke tafi can ke dai son miji ya yi miki yawa,ba ki iya ganin laifin shi. A'isha ta yi ƴar dariyar takaici, sannan ta ce to in ma naga laifinshi me ganin laifin za ya maganta min? Nafisa ta ce shi kenan mu dai mun ga laifin shi gidaje nawa gareshi cikin Katsina da kewayenta? Ya maidata wani mana za'a tsaya ɓarnar dukiya,kin san Allah, Alhajinmu da Hajiyarmu sun ji haushi, harkokin shi ma fa yaƙi ya maida hankali sai ka ce yau ya soma gini. A'isha ta ce Allah ya ƙyauta kuyi haƙuri kada suyi fushi da shi,tamkar Nafisa ta shiga ta waya ta doddoke A'isha don haushi, ta kula A'isha ba zata taɓa ganin laifinshi ba, don haka sai ta canza zancan da cewa,ki je asibiti mana? A'isha ta ce nima tunani na kenan, sai kuma naga ni ba ciwo cikin ke min ba, kuma ba wani guri ne ke min ciwo ba a jikina, sai naje na cewa Likita ina jin motsi? Nafisa ta ce kin ji irin haukan naki ba? Ki je ki yiwa Likita bayani,in yaso ayi miki (Scanning) a ga me ke damunki,in bai ga komai ba a koma Islamic." A'isha ta ce, shi kenan zan je, ki gaida min su Hajiyarmu."

Lamo ta ƙwanta tana tunanin me ya shiga kan Uncle ne? Don kawai yana yiwa Jummai gini sai ya share ta? Zata ce kada ya yiwa Jummai gini ne? Ba tare da ta gansu ba? Haƙiƙa ranta fa ya ɓaci sai dai bata son ta nuna ma ƴar uwarshi ne. Ta kira wayarshi abin al'ajabi ya ƙi ɗauka, har sau uku, sai ta tura mishi da text cewa,in ta mishi laifi ne don Allah ya yafe mata, rashin sa ya saka ta cikin damuwa,don Allah yaushe zai zo? Saƙon na isa sai kiranshi har tana murna ga zatonta sulhu zaya nema, sai kurum ya ce "ke kin fa matsa min da yawa......




######
[12/19, 22:33] Ummi Tandama😇: *📔📔 Page 5*



Ban cika son mace mai jarabar tsiya ba, duka-duka yaushe ne ban zo ba na shekara ne? Kin dameni don Allah daina kirana in na matsu zan neme ki da kaina." Kan A'isha ya yi matuƙar ɗaurewa,bakinta yana rawa ta ce, "Yi haƙuri Uncle nima ba wai na ce kazo ba ne,na zaci na maka laifi ne shi yasa." Tsaki ya ja kafin ya kashe wayar, wannan lamarin ya firgita A'isha sosai, baiwar Allah ranar sai dai bacci ɓarawo, amma bata runtsa ba. Maƙotanta su kansu cikin ƙwanaki sun fuskanci tana da damuwa koda suka tambaye ta sai ta ce musu bata jin daɗi ne. Anty Maimuna ma ta matsa mata dason sanin damuwarta, amma A'isha sarkin zurfin ciki ta yi ƙememe ta ce zuwan jarabawa ne. Yanzun suna karatu ba dare ba rana,Anty Maimuna ta ce to Allah ya taimaka.

Cikin haka ne A'isha ta samu ziyartar asibiti inda ta samu ganin Likitan mata. Bayan ta gama mishi bayani ya tambaye ta ko tana da ciki ne? Ta shaida mishi ita kam bata da komai,don haka ya bukaci ta ƙwanta kan gadonsu na likitoci don yi mata (Scanning). Bayan ya gama bai ce mata komai ba, sai da ya fitar da sakamako ya dube ta, "kina da miji?" A'isha ta ce "Eh." Ya miƙa mata sakamakon, tana buɗewa idanunta na sauka kan (EDD) ta maimaita kalmar a fili (EDD) kuma? Ta dubi Likitan ta ce,kana nufin ciki ne da Ni? Ya ce wata baƙwai ta zaro idanu tare da ɗora hannunta kan mararta, sannan ta ce Likita ka kuwa duba sosai? Ya yi ɗan murmushi,a katin ki naga cewa ke ɗalibarmu ce amma kin kasa gane kina ɗauke da ciki,kina nufin ko kaɗan ba wata alama da ki ka gane kina ɗauke da ciki?" A'isha ta girgiza kai tare da cewa, "Ina al'ada duk wata sannan wata bakwai ɗin da ka ke magana nayi ɓari lokacin wata uku."

Ya zuba mata ido, "Ya ya abin ya faru wancan lokacin? Ta bashi labarin a taƙaice, ya ce to wankin cikin da baayi miki ba shi ne dalilin da ba a wanke ɗan ba, Allah ya sa zaya taka doron ƙasa, sai dai zaya iya kasancewa watannin cikin ya koma baya. Yanzun dai cikinki wata bakwai da sati ɗaya.

Jugum A'isha ta yi tana tunanin wannan lamarin na Ubangiji,lallai wannan shine mafi girman abinda ya fi bata mamaki,iyaka tsawon rayuwarta, sannan ta yi murna mara adadi kuma ta san wannan labarin in ta bawa Uncle shi zai kawo karshen rashin jituwarsu, ko ta ce fushin da yake yi da ita, wanda bata san silarshi ba. Ta jawo wayarta ta shiga neman shi da glo ɗin shi har sau biyu tana rurinta tana katsewa bai ɗaga ba hakan (MTN) ɗin shi jikin ta ya yi sanyi, amma duk da haka ta daure ta kira (Seltel) ɗin shi daf da zata katse ya ɗaga, gabanta na faɗuwa ta yi sallama,rai ɓace ya amsa sallamar, kafin ta yi magana ya ce wai lafiya ne? Ta ce a'a dama ina son muyi magana ne. Ya katse ta da cewa,bani da lokaci, sannan ya yi tsaki ya kuma kashe wayar. A'isha ta zabga uban tagumi nan take kanta ya shiga sarawa,kuka mai ƙarfi ne ya ƙwace mata,ta yi shi har ta gaji babu mai lallashi. A'isha ta zama tamkar wata zararriya wa zata tunkara da matsalarta? Zuciyarta ta ce mata Ubangijinki, ranar kuwa ƙwana ta yi kan sallaya tana kaiwa Allah kukanta, zuwa safe ta ji ɗan dama kuma ta yanke hukuncin har ma cikinta batun cikin jikinta dama Ubangiji shi ne ya ɓoye kayanshi, ko Nafisa ba zata faɗa mawa ba, haka ta ci gaba da rayuwarta cikin makaranta.

Jummai kuwa ta samu yanda take so,da tace kaza za ya yi mata, gini kuwa an gama an kuma danƙara kaya na iyayan kuɗi sannan ta shirya walimarta ta gani ta faɗa suka shige ita da Suby da Sofy Sai gefen maigidan. Hakan ya yi matuƙar tunzura Hadiza nan ta tada bala'in cewa ba zata yarda ba, rigimar ta kai su ga manya inda Alhajinmu ya ce tunda ya yi wa Jummai dole ne sauran matan ya yi musu, dole yasa aka bige gefen Hadiza da nashi da na Jummai na da aka hau yiwa Hadiza nata amma A'isha dama ko ƙasa da sama za su haɗe ba za ai mata wani gyara ba. Ya dai sa an ragi falon an bar mata ɗan ƙarami ya zuba mata tsofaffin kujerun falon. Rashin kunyar da Hadizan ta mishi lokacin ya isa sakinta, sai dai ɓarin da tayi ne yasa ya bar ta ko Allah zai sa ya kuma samun wani rabon daga gare ta, don shi ya yarda har ga Allah ciki ne kuma ya amince cewa ɓarin ta yi irin kuɗin da ya kashe lokacin da suka zo da batun ɓarin suna da yawa, sannan sun hana shi zuwa asibitin a cewar su ba sai ya je ba,daga ƙarshe ma da suka ga ya matsa kan cewa zai je sai suka dawo da ita gida, Likitan da suka naɗa na ƙarya ya ci gaba da zuwa duba ta.


**** **** **** ****

A'isha tana matuƙar tausayawa kanta don zurfin cikinta ya hana ta sanar da wani bare a tausaya mata,don haka ta shiga rama ta koma sirit sai nono sai ko cikinta wanda ya bayyana lokacin Anty Maimuna ta yi ta yi da A'isha ta sanar da ita matsalarta, amma ta ƙi cewa kurum take karatu ne don bata son tambaya ma ta rage zuwa gidan, cikin haka ne suka samu hutu na ƙwana goma jal, tamkar kada ta tafi Katsina, amma ya zamar mata dole tunda bata da kuɗi duk sun ƙare komai nata ya yi ƙarƙaf, ta yi ta kiran Uncle a waya don ta sanar da shi a zo a ɗauke ta, amma yaƙi ɗaga wayar. Abin ma ya daina bata mamaki ya shiga bata tsoro,bata son kowa ya san halin da take ciki, don haka ta ƙi kiran kowa ta nufi tasha.

Sun iso Katsina biyar saura,nan ma ta ɗauki shatar Taxi zuwa gida, har cikin harabar gidan ta ce ya shiga. Maigadi na ganinta ya buɗe Gate ɗin gidan,tana fitowa Uncle ta gani tsaye jikin mota yana waya, Jabiru yana riƙe da jakar Uncle ɗin ta Office da alama dawowarshi kenan daga Office ya bi motar da kallo don ganin wanene ya shigo masa cikin gida da Taxi? Ranshi ya yi mugun ɓaci lokacin da suka yi arba da A'isha, sai ya ji tamkar ya hau ta da duka,nan take ya ɗauke kanshi daga kallon gurin da take. Ganin haka bai bata mamaki ba, domin nata zaton na ma zaya kore ta ne, ta ciro kuɗi ta bawa ɗan Taxi ta saɓa jakarta tare da jan akwati, sai lokacin ta soma tambayar kanta wane gefe zata nufa, domin gaba ɗaya fasalin gidan ya canza, tana kallonshi ya nufi sabon ginin wanda take zaton shi ne na Hajiya Jumman.

Ƙofarsu ta da ta nufa duk da ta kula nan ma akwai ƴan gyare-gyaren da aka yi,taja ƙofar a kulle take gam don haka ta shiga ƙwanƙwasawa. Jim kaɗan ta ji muryar Tabawa tana tambayar wanene? A'isha ce ta ce,nice Tabawa buɗe. Ganin A'isha sai ta hau sheƙa dariya,dama ke ce haka? Ta taɓa baki,ai yanzun ƙofarki ta koma can, ta nuna gefen gareji, A'isha bata gane ba, amma yarda Tabawa ke tuntsire dariya shi ne ya sa ta saɓa kayanta ta nufi gefen gareji. Sule mai bawa fulawa ruwa ya nufo ta da sauri yana yi mata sannu ta amsa mishi, ya ɗauki akwatin tare da cewa ai Hajiya an samu ƴan gyare-gyare ne a gidan suna isa ƙofar tana kulle ya ce bari in amso miki makullin gurin maigida, da gudu ya nufi sasan Jummai.

Ya samu maigidan nashi yana shirin shiga wanka in da Jummai ke ta faman riritashi tamkar ƙwai, ya yi sallama Sofy ta zo menene? Ya ce maigida nake nema,taje ta sanar da shi. Jummai ta fito tace menene? Wanka zai yi, ya ce ranki ya daɗe zan amshi makulli ne na gefen gareji, ta yi guntun murmushi sannan ta juya. ya fito fuskarshi ɗaure hannunshi riƙe da makullan, gashi ka bata sakaryar yarinya kawai,Sale ya amsa ya fita daidai sanda Alhajin ya ci gaba da cewa don iskanci sai ta kama shigowa motar haya Taxi har cikin gidana? Jummai ta taɓa baki wannan tsageruwar yarinyar mara kunya mene ne ma ba zata yi ba,ya katse ta da ɗaga hannu saurara min tsagerancin me Beby ta yi miki? Nan ta tuna da sharadin boka da ya ce kada ta yarda ta kushe A'ishan a gabanshi, yin haka zaya ringa lalata aikin dole sai ta saka kissa cikin lamarin. Aikin da kissa zai tafi ba da hassada ba, don haka sai ta wayance da cewa ba Suwaiba ka ke nufi ba? Ya girgiza kai ni ban ce miki Suwaiba ba, kuma bana son in Ina ma wata faɗa a dinga sa min baki ta dafashi muje kayi wanka mijina,ni kaina ban za ci kana nufin Bebynka ba, ina zaton Suwaiba ce shi yasa,ni ko me A'isha zata min na tsageranci,yarinyar da magana ma bata dame ta ba,ai ita ce ta dawo? Lallai ina mata Sannu da zuwa,tsaki yaja sannan ya nufi gurin wanka.

A'isha ta buɗe ƙofa ta shiga, tsayawa ta yi tana kallon ɗan tsuku kun falon, kujerun suna da ne cikin falon sai ko T.V ta tura ƙofar ɗakinta ta shiga duk ko'ina ya yi ƙura,bata gaji ba ta tuɓe ta shiga gyaran ko'ina, da falo ta soma har ga Allah ita waɗannan dakunan sun ishe ta, ina laifi mutum mai zaman kabari ya samu ciki da falo a gidan duniya ai ya ishe shi rayuwa, ta goge komai sai abinda ke bata mamaki shi ne ba taga kitchen ba. Me hakan ke nufi? Ita dai tasha alwashin ba zata taɓa mishi zancan ba,zata fito da kayan girkin ta ko a ƙofar ɗaki ne ta saka risho, ta yo wanka bata shafa mai ba saboda zufa ta zumbula doguwar riga ta zo falo ta zauna, yanzun matsalarta yinwa ta miƙe ta fita harabar gidan, duk mazan ƴan aikin sun tafi gida sai Baba maigadi kurum. Ta isa gurin shi ta ce don Allah Baba duk su Sule sun tafi ne? Ya ce sun tafi Hajiya kina son wani abu ne? Ta ce biredi nake so, da kayan tea, ya ce to bari a karɓo miki dama ɗari biyar ɗin kenan ta miƙa mishi gashi duk yanda ya kama ka sai min,ta koma ciki. Can ta fito don tago ko ya dawo dai-dai lokacin da aka soma kiran magriba. Ya miƙo mata saƙon daidai lokacin da Uncle ɗinta ya fito,ya bi ledar da kallo ita dai ta amsa ta juya bayan ta ce ta gode.

Uncle ɗin nata ya bita da kallo tafiyarta irin ta masu ciki ya raya a ranshi ya isa gurin maigadi Baba ina ka je ne? Ya ce Hajiya na siyoma kayan shayi. Kayan shayi? Eh, inji Baba maigadi. Uncle ya kaɗa kai ya nufi masallaci. Ranshi ɓace,me yasa A'isha ke sha'awar wulaƙanta shi a idanun duniya ne? Ɗazun Taxi ta shigo mishi da ita har cikin gida yanzun kuma kayan tea ƙulli-ƙulli kamar gidanshi, motocin shi nawa? Sannan shaguna nawa ke gareshi cikin plaza, daban-daban? Ya yi ƙwafa.

Ita kam ta samu ta jona ruwa ya tafasa tasha tea ɗin ta ta ƙoshi, ta yi sallolinta, ta ƙwanta don ta huta. Sai dai maimakon bacci sai ta soma karanta matsalolinta. Tuni ta nemi bacci ta rasa, don haka sai ta miƙe ta soma da yin alwala, ta shiga kai kukanta ga Allah domin iyaka tunanin ta shi ne kurum zai yi mata maganin dukkan wannan halin da ta shiga.

Uncle ɗin ta kuwa don takaici ya kasa cin duk kayan alatun da Hajiya Jummai ta shirya mishi, zuciyarshi sai ƙara zafi take game da Beby. Jummai tasan komai,don tun lokacin da ta ji dawowar A'ishan sai ta zuba rushi cikin kasko ta kara hantar nan mai cake da allurai, shi yasa zuciyar maigidan ƙara zafafa,kamar yanda Malamin ya tsara mata, ta dube shi maigidana wai me ke damunka ne? Ya ce wallahi Jummai A'isha ce ta bani haushi. Ta ce haba Alhaji me A'isha zata yi maka ka ji haushi, irin haka bayan ka sani cewa yarinya ce? Ka dai same ta ne ka nuna mata baka son shiga motar haya tunda Allah ya hore maka, ya dubeta, to bayan ma wannan ina fita sai naga wai ta aiki Baba maigadi siyan biredi da madaran ƙulli dibi wannan cin zarafin? Hajiya Jummai ta ce,lallai bata ƙyauta ba, amma ka mata uzurin cewa daga tafiya ta dawo,kai itama da rashin dabara take maimakon ta zo nan ta amshi abinci in tana jin yunwa ne? Ya ce girman kan nata zai bar ta ne? Ya sake yin ƙwafa, zuciyar Jummai kar da murna, ta ce to kaje can gurinta don yau ita ce da kai tunda tafiya ta dawo. Ya ce bar ta ba zan je ba. Ta haɗa fuska wallahi sai kaje don bana son shiga haƙƙin wani, Allah ma ya sani. Ya ce kina korata ne? Ta ce a'a ni dai nafi son ko lahira mijina ya tashi daga cikin maza masu adalci, ya ce haka ne zata ci albarkacin ki ne zan je amma ba don ita ba, ta miƙe ta zo ta ƙwanta a bayan shi na gode mijina nasan kai nawa ne daga duniya har abada, tashi ka je bari na bika da abincin,ya ce

Please Login or Register in order to submit comment