Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farinciki ƙwarai inafatan kowa ma yakasance cikin happy.😁😁

.......LADINGO NA MODIBBO.................
Daga wajen nawwara kuwa tana kulle ƙofar takoma taxube jikin ƙofar ɗakin tafara kuka tamkar wacce aka aikowa dasakon mutuwar hajia,saidayatayi mai isarta tukunna ta xube awajen bacci yayi awangaba da ita
Gameda dr kuwa xuciyarsa kasa masa sukuni tayi domin tunaninsa wataƙilama bataci abinchiba donhaka hankalinsa yatashi dasauri yamiƙe yanaɗauko sapayan key ɗin ɗakin. Nata yaɗauko jallabiyyarsa ƴasaka yafito kaitsaye ƙofar ɗikin nata yanufa yasa key yabuɗe yatura ƙofar, ji yayi kamar wani abu yatokare ƙofar ahankali yatura yashiga kallonta yayi aƙudindine kamar maijin sanyi tawani haɗe wajeɗaya ta takure acikin mayafinta sai bacci take hankali kwance.yayi murmushi ahankali yasunkuya kanta yaɗauketa cancakat taɗan motsa amma batafarkaba tasakala hannunta awuyansa tana gƴara kwanciya ahannunsa, dr kuwa tamkar su dauwama ahaka tanajikinsa ayadda yakeji daga garesa,sbd karta tashi kawai yakaita bed yajablkd yarufeta tukunna yayi kissn ɗin hannunta yafice yana mayar daƙofar ƴakulle tamkar ba abuɗeba,
Yafice ɗakinsa cike da kewar amaryartasa game da muradin kasancewa tare da ita.
Musalin ƙarfe bakwai am ta tashi dasauri tana kallonta akan gado waya kawoni nan tafara tambayar kanta aa yasalam! Ko cikin dare natashi nadawo nan
Ta taɓe baki kawai ganin batada maibata amsa tunda tasan takulle ƙofa balle tai tsamman ko Dr ne, miƙewa tayi cikin yanayin gajia tana miƙe dukkan hannayenta kafin tadire ƙafafunta akasan kafet dake gefen gadon bayanta huta ta tashi kaitsaye tafaɗa bathroom tarufe
Xuwa takwas darabi tayi wankanta cikn tsadaddanless ɗinta kalar puppl,dark,ɗinkin rigada siket yakamata siket ɗin sosai riganma haka amma tayikyau sosai cikin kayan tamkar dominta akayisa, duba da yadda yaxauna ajikinta,
Tarasa yadda xata fita falo balleta gangara kitchin taɗauko ruwa tasha dominkishi takeji sosai bataso tahaɗu da Dr,
Mayafi taɗauko tasa tabuɗe ƙofar tafice kamar kuwa sunhaɗa baki kafin sufito yabuɗe kofar ɗakinsa yafito itama tafito sunahaɗa ido taiƙasa dakanta tana wasa da yatsun hannunta
Ahankali murya ƙasa ƙasa tace
Antashi lafiya?
Lafiya ƙalau amarya kintashi kema lfƴ?
Ya amsa tare da
Sakin ƙofar yaƙaraso inda take kamar xaitsaya saiya wuce kan kujera ɗaya dagacikin nafalon yaxauna tareda ƙuramata ido yadda tacoge taƙi gaba taƙi baya shi dariyama take bashi,
Ana haka sukaji ana kwankwasa ƙofar falon tashi yayi yabuɗe ƙofar amina ce tsaye hannunta riƙe da kulla babba da ƙarama sai plas natea dake ajiye kasa
Yaya gd mornng?
Mornng my sis
Yakarɓa kayan hannunta taɗauki plas ɗin tabi bayansa suka shiga falon amina sai murmushi take nawwara dasauri taƙarasa kusa da amina tana mata barkaɗa xuwa amina tagaisheta tukunna tadubi Dr
Yaya bari xankoma momy ce dama ta aikoni tace nakawo maku breakfast,
Sista sannunki daƙoƙari kicema momy inaxuwama anjima,
Tafice tana faɗin
Anty amarya sai anjima,
Ɗagamata hannu nawwara tayi tareda sakin murmushi
Tohm godiya nike
Kallonta yayi bayan fitar amina yace
Saiki xo kixauna bari naɗauko mana spn da kofna muyi break don nasan kinajin yinwa,
Takallesa domin kamar yasan abindake faruwa kenan kukacikinta yake nayunwa sosai domin rabunta da abinci tin sanda aka kamata saidai taɗansha tea ko lemo da cake ko cincin, jiyama bataci komaibatin ɗan lemon da sumayya tamatsa mata tasha,
Har yadawo tana tsaye a inda ƴabarta
Hannunta ƴariƙe tare da ɗagata yaɗora bisa cinyarsa yana xagayo da hanayensa yaɗora akan cikinta fuskarsa na gogar wuyanta,
Nawwara miyasa kike tawani ɗari ɗari dani nanfa gidan mijinkine, yakamata kisaki jikinki dani yanxu ke matatace baxanji daɗiba idankinmin wannan abun kinji
Tasinne kanta atafin hannayenta
Au bafa kunya nace kijiba kimin magana magana nifa banso kikemin haka
Tai shuru kamar ruwa yacinyeta. Saiƙoƙarin janye jikinta take harta samu takwaci kanta daga gareshi,ɗaya daga cikin kujerun wajen taja taxauna tare da ɗan hara rarsa "bama yunwa nike jiba.
Tafaɗa muryanta acikin sanyi tamkar maitsoron magana,yafiskanchi haka shiyasa yajanyo plas ɗaya yaxuba masu jalub intaliyane yajikifi saiƙamshine ke tashi dandanan nawwara taji abincin yamata yunwar dake damunta tadaɗa matsamata gabanta yamatsar da abinchin yasa spoon yafara ƙoƙarin kai abinchin bakinta
"karki min gaddama domin kwa yunwa kikeji gashinan duk fuskanki yasauya kinfaɗa dandanan,ta ɗan noƙe tana ƙasa da idanunta domin tana bala in jin kunƴar Dr,
Kabari toh naci da kaina
Yagirgixa kai tareda haɗe fuska
Yasamata abincin abaki dole ta amsa, ahaka yaytabata harta koshi yahaɗa tea shima dakansa yabata harsaidaya tabbatar takoshi sannan yatashi
Inakuma xaka kai bakaciba,tace masa
Yajuyo,wanka xanyi sainayi wanka nake cin abinchi.
Taiƙasa dakanta
Afito lafiya
Yaɗaga mata hannu ko xaki rakani?
Tagirgixa kai aa
Yayi dariya toh shikenan ngde tarufe fuskarta

......................ONE WEEKS.......................... LETER
Kukatake sosai tana riƙe dakanta wanda kemata ciwo tamkar yatsage dik sallamar da summayya ke ƴi vata jiyoba
Salati sumayya tayi tana ƙarasawa inda take suhanallahi nawwara mrnene yasameki?
Jikin sumayya tafaɗa tana kuka
Nashiga uku sumaƴya yaxanyi da rayuwata?
Kiyi shuru malama kifaɗamin menene yafaru ina Dr yusrab ɗin?
Ajiyar xuciya kawai take tana
Sharar kwallah
Ransa yaɓachi yafita inacutar dashi bana mashi adalchi,sumayya dai dai da farincikina naharamta masa ganinsa balle ninasashi, haƙuri yake dani kawai ƴau ne momynsa ta turo tace yakaini xamu gaisa,,,,,,,,,,,,,, muryarta ta fara rawa
Sumayya datinfarko tagane rashin gaskiyar nawwara ƙarara, tacika da haushinta tanajin tamkar tashaƙeta sbd haushi
Saime kuma?
Sumayya tabuƙata
Hannu nawwara tasa abakinta tana ƙara sautin kukanta tace
Bayan nashiga wanka nafito nashirya tsaf saina ɗauki turare nafesa naɗau mayafina natafi falo wurinsa inaxuwa yanafaɗuwa ƙasa tamkar yasuma dagudu nasamu ruwa nashafa masa afuska yasauke ajiƴar xuciya amma me sainaga yana min wani irin kallo maiɗauke da harara da tsana da haushi inamasa magana yawankeni da mari yafita yana faɗa,.
Takuma fashewa dakuka. Dr mutumin kirkine wlh sumayya amma natsamgwami rayuwarmu naƙi kulawa dashi ko kaɗan bayasamun farinciki daga gareni shiyasa yaxaɓi yarayu dani tamkar yadda xairayu da ƙanwarsa,harna fahimchi yadda yake sona bantausayamasa ba amma banajin iyawannan yasa yafasata sumayya yakoma kamar wani daban bashiba, taƙara fashewa dakuka,
Kinɓatamin rai nawwara kuma bakima dr adalchiba don kinga ƴanasonki shine zaki samu damar rinƙa wulaƙantashi kina masa yadda kikeso toh kisani wlh komai yasameshi kece sila da sa hanninki aciki,allah xai tambayeki
Sumayya ran aɓace tamiƙe
Baxan xauna wlh xanje nafaɗama hajia dik abindayake faruwa kawai tasani tinkafin ki haukatasu musu ɗah.
Kuƙa sosai nawwara keyi tana riƙe hannun sumayya ammata ƙwace ta tafi abinta.
Anan taxube tana kuka maicinrai, ahankali tafara tunano abubuwan dasuka faru abaya.har xuwa kan kullin da modibbo yabata amatsayin ajiyar da baffa yabasa yabata.
Dasauri ta tashi tafaɗa ɗakinta jakarta tajawo tafara xaxxage kayan cikin tana duba kullin harta ganta dasauri taɗauka tana ƙoƙarin kwancewa tana kwance kullin wata fata tafaɗo kasa saikuma wani ɗan abin hannu kamar awarwaro makyau da ƙƴalli takardar tafara ɗauka tana dubawa rubutune kamar haƙada ajami

"kiyi haƙuri ki ɗauki haƙuri da lamarin ita duniya domin komai dakikaga ansamu ko anrasa shi toh daga allahne kuma bai wuce kan kowaba, kiy haƙuri da abin daxan faɗamiki nauwara ni baffa da innarki bamune iyayen mahaifiyarkiba hasalima mu tsintar mahaifiyar ki mukaƴi adajin garinmu. Kuma munsameta bata magana agunmu muka mata magani taji sauƙi tafara ji da mayarda magana sannan aloƙacin da wani awarwaro ahannunta ninaciresa na ajiƴeshi sbd ƙyansa xa a iya sacesa, ni nama mahaifiyarki aure wurin hauhuwarki tarasu babanki yarasu bayan tafiyar mahaifiyarki hauwa u. Wannan awarwaron shine nasamu ahannun mamanki,........xakuma kiga wani hoto toh natane tindana tsinceta nasa akayimata shi na ajesa ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,


Wani kuka tasaki maitaɓa rai bataƙarasaba ta cikuikuye fatar awarwaron taɗauka tanabinsa dakallo ahankali tagano wani ƙyakkyawan rubutu ajiki maiƙyau da kyalli.
Tana kallo harta haɗa baƙi tahaɗa kalmar
HAUWA'U,
Kuka tatsinke dashi
Wacecene baffa nashiga uku wacece uwata kudawo kufaɗamin dangin uwata
Kukatake kawai tana bubbuga kasa da hannunta
Awarwaron taɗauka tasa ahannunta dayake mai gurin ɗagawa wane inkasa saiyahaɗe ɗanyen gwalne maikyau. Ta ƙurawa hoton ido macece maikyau baƙa ba dilinba tana da tsayin fuska da siririn hanchi idanuwanta masu girma ga gashintanan kwance abayanta fuskarta shuru dagani batada magana lafiyayyiyar macace, muna kama amma basosai ba fuskarce naɗaukota amma tafini ido da hanchi kuma ni inada haske sosai. Rumgume pic ɗin tai aƙirjinta tana fidda wani kuka maisauti
Inaxanganki ummana? Kintafi kinbarni umma, wayyo allahna


Yinin ranan ahaƙa tayishi sokoko tamkar mara wayo daga kuka sai kuka
Saiwajen karfe goma dr yusrab yadawo kota kanta baibi yawuce ɗakinsa batakumajin motsinsaba saida safe wajen ƙarfe takwas yafito cikin shirinsa nafita aiki nanma baikulataba yafice. Tayi kuka har idaninta sunƙanƙance
Kodaƴaushe tana tareda wannan awarwaron tana nishaɗi da kallonsa akullim domin dr yafita daha harkarta kwata kwata kamar ba mijintaba dik da dama hakaɗin suke xaune amma bakamar yanxuba dako ganinta bayasonyi
Yanaxaune a main falo tafito saiƙamshi take dasauri yatashi yana finciƙota saiji kake yibbb tafaɗi hannu takai gefen cikinta
Wayyo allahana
Wannan wanna irin iskanchi dazakifito kinawari kuma kina takuramin, abun ya ishene,wannan shine karo naƙarshe daxankuma jinwannan warin,nafaɗamiki karki sake fitomin cikin gida ina nan idan ba hakaba xanɗaumataki akanki wlh kingafa ni haƙuri kawai nake dake inaxaune dake amma ko araina natsaneki wlh.
Ƙamar anbugawa nawwara bulo aka tadafe kanta
Katsaneni Dr akanme?
Ta tambaya tana mai rushewa dakuka
Kallon wulaƙanci yake jifanta dashi
Sbd mugun halinki .natsaneki,don banasonki wlh idankwa kikaci gaba dashafo wannan abun maiwuri kinaficemin tanan xankaryaki inkwasa inkaima hajiar ke ahaka don banƙaunarki ,,,,,
Wani ƙara tasaki tana xubewa ƙasa
Wayyo allahna nashiga uku dr nice fa? Anya kana dubana dakyau, kaƴi hƙri da dik abindanayimaka wlh nadaina baxankumaba natuba nabika xanmaka biyayya nadaina bijeremaka wlh amma kadawo dasoyayyar dakakemin.
Yajallata da yatsa ranshi aɓace kamar xaidaketa
Tashi kibani gu kincikamin xuciya da tsanarki karna illataki avanxa,
Ganin yadda yake wani xare ido yana hayyayaƙomata yasa tafirgita tamiƙe da gudu tafaɗa ɗakinta tasa keƴ
Taxube ƙasa saidatayi kuka mai isarta sannan ta yanke wani shawara
Kayanta tafara haɗa a akwati tana kuka tamkar wacci xata haɗiyi xuciya.
Shikuwa daga garesa ƴanagama shirƴawa yaɗauki jakarsa yafice gidansu yanufa kaitsaye axiciyarsa yanajin tsantsar tsanar nawwara yanajin nadamar aurenta dajinkamar yasaketa, daga can ƙasan ransa kuma bayajin daɗin yadda yake mata yanajin taxamemasa alaƙaƙai ne tamkar rigar ƙaya dayakeso yafitar yahuta
Xaune ƴake gaban momy bayan sungaisa taga yayi shuru yahaɗa kaida gwiwa yatafi tunani gawata ramadayake kamar wanda yakwanta jinya yatashi, kallonsa taƙarayi
Yusrab!
Yaɗago yana kallonta
Momy na am
Tace yusrab menene yake damunkane kaxo kaxauna kayi shuru kana tunani ko akwai masalane?
Yagirgixa kai ƴana sosakansa
Momy kibari kawai bakomai
Tace kaga yusrab karka ɓoyemin komai kafaɗin dik abindayake damunka kasanfa cewa dole nagane kanada damuwa domin karame sosa haba yusrab kamar ba mai amarya aɗakiba,intsakanunku da itane masalar kafaɗamun sai anemi abinyi amma xama kana tunani bashine mafitaba.
Yaɗaga kai hakane momy wlh yanxu ni kwata kwata ba avin dayake min daɗi.kunchi kecimin rai daxaran naganta nake jin wani baƙin damuwa dahaushinta momy natsaneta yanxu banasonta burina shine kawai nasake ............
Kaiiiii,! Yusrab Karkataɓa soma wannan mummunan aikin, sokake al arshin ubangiji tagirgixa kayi kuskure babba inka aikata haka, ya isa amma donme xaka aurota kasan bakasonta au shiyasa danace kakawomin ita kwanakin baya baka xoda itaba duk da bantaɓa ganin yarinyarba naji inasonta kuma anfaɗamin tanada mutumchi donhaka karƙa sake ka aikata abindakakefurta min anan karma nasakejin wannan furicin abakinka
Yasunkuyar dakai
Momy wlh baxan iyacigabada xama da yarinyar canba dan allah kibarni insaketa kawai wlh ɓatamata loƙaci kawai xan
Tashi kaban gu
Momy tajefesa da harara sim sim yatashi yana jin tsanar nawwara na ƙaruwa acikin xuciyarsa,
Momy datin maganarsa tafarko tagane lallai yaronnata akwai damuwa atare dashi baƙalau yake ba, tallafe fuskarta tayi tana tausayawa nawwara
Amina ce tafito daga ɗakinta momy lfƴ naji saifaɗa kikema yaya.
Hum kedai bari dama sonake kifito na aikeki sauri kije gidansa kutaho keda matar tasa
Amina takalleta aa momy lfy kuma shiya yayan miyasa baxaikawotaba.
Tsareni da tambaya kema ko naji tsoro nafaɗamiki.
Murmushi amina tayi tana cewa
Ranki yadaɗe momyna angama bari naje saimu taho tare
Taɗau mayafi tafice
Dasauri taƙarasa ganin nawwara na kulle gidan hannunta janye da akwati,
Aa anty nawwara lafiya kuma inaxaki da akwati kina kuka?
Bata ɗaga kai takalli amina ba ta cigaba dajan akwatin tana sharar ƙwallah.
Amina taji tausayinta sosai domin batasan menene kedamunta ba amma tasan itada yayantaba.
Kiyi haƙuri komenene anty kixo muje momy nakiranki
Taɗago idanunta waɗanda suka ƴi jaxur sbd kuka
Takalli amina ɗaga mata kai aminan tayi sannan ta amshi akwatin tawuce gaba suka tafi.
Momy dake xamanjiransu ta amsa sallamar amina tana maikallon nawwara dake biya dabayan amina sosai taji gabanta yafaɗi,
Har ƙasa nawwara taxube tana gaida momƴ cike da kunya da girmamawa,
Shurune yabi bayan gaisuwar ba motsin dakikeji saiƙran esi da tv
Kafin momy tadubi amina.
Amina kije ciki xammagana da nawwara
Tashi tayi tashige ɗakinta
Nawwara nutsuwa taƙarayi tanamai ƙarajin kunyar momƴ
Nawwaratu
Ahankali taɗago kai ta amsa
Na am momy
Momy taƙara numfasawa. Menene yake faruwane dakuke ɓoyemun.naga abubuwa dayawa a'yan kwanakinku da aure abinda mamaki ace har matsaloli haka dayawa sinfito akwanaki goma da aure kifaɗamin dik abindake faruwa ni xansan abinyi,
Ƙasa nawwara taƴi dakai tana mai sharar ƙwallah
Momy bansan komaiba gameda abindayake faruwa ba, ,abindaxan iyadangantashi da hakan kuwa shine kwana uku da aurenmu watarana dasafe mukafara samun masala domin aloƙacinne yake faɗamun yatsaneni kuma yakuma maimaitamin yau, yanafaɗamin xai iyamun komi badamuwansa bane, shiyasa yau nahaɗa kayana xanfita nabar gidansa baxan xauna dashi ƴana nufanada mummunan furichiba, momy nayiwa Dr uxiri sbd yasoni abaya sosai kuma bansan dalilinsa natsanataba yanxu,shiyasa nayanke shawara akan dole nabar rayuwarsa kodan yahuta daganin ɓachin ransa,........ Tafashe dakuka maicinrai maisauraro
Momy ta girgixa kai
Ba haka xakiba domin baƙaramin abun kunya bane kwana goma da aure aga amarya takoma gidansu dakayanta wannan tashin hankaline babba nawwara kiyi haƙuri tabbas nafahimci wani abu acikin wannan maganar taki kuma xanɗaumataki babba akai yanxu xakicigabada xama anan gidan har xuwa loƙacin dakomai xai dai daita,kinji.
Taɗaga kai alamun tohm,
Momy tacigabada magana.
Kinga yanxu inkika koma gida hankalinta xaitashi sosai amma yanxu komai yawuce bawanda yasani kiyi haƙuri kekam kinji
Yawwa tashimuje ciki.
Aminace taƙira taɗau akwatinta sannan suka shiga da momy wani ɗaki tabata acan lungungidan inda bakowane xaisanda itaba sai inƴasan dama daitan,
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🐝🌱🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🌱🌱🍯🍯🍯🍯🌱🍯🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱🌼🌱🌱🌼
Umma narasata!
Narasa nawwwara,,,,,

umma nayi babban rashi !!!

wallahi narasa ladingo umma kingani ba abindakikaja jamun ko

Narasa nawwarana shikenan ni narasa nawa farincikin!!!
Abindayake faɗa kenan yana xagaye gidan wayar dake hannunsa yaɗaga yabuga daƙasa aikuwa saigata tayi watsawatsa aƙasa bako sim ɗin yayi filla filla,
Ummi da yusuf kuka suma kawai suke ganin yadda yayan nasu yakoma dandanan tamkar ba jarimin namijiba kanmace yakoma mahauchin ƙarfida yaji, yakoma mai rauni, ba abindake daminsa face soyayya, ƙamƙameshi sukai sina kuka umma kuwa takasa taɓuka komai saibinsa take da ido xuciyarsa bugawa kawai take da sauri sauri yanata fitar dawani irin numfashi kafin umma taƙarasa yafaɗi asume ba abindake motsi ajikinsa haka tafita agigice tana kuka daneman taimako mota ce tafaka saigata tafito tana kallon umma tace lfy umma menene yake faruwa kuka take sosai taja hannunta xuwa ciki
Modibbo take nunamata dake kwance yamutu suma yayi unhum
Mamakine yakama maimunt me yakawo modibbo gidan umma koshine ɗanta datake faɗamun, makwabcinsune malam saleem dayaji koke koke yayi yawa yashigo afirgice ƴana tambayarsu yasamu modibbo ayashe aƙasa komotsi bayayi shine yataimaka musu suka sashi amota akatafi asubiti,💜❤
💜❤...............................
Game da momy turai kuwa gida taje bayan kwana biyu tasanar da bahba (mahaifinta kenan)dik abindake faruwa shuru yayi nawani loƙaci kafin yaxare farin glass ɗin dake manne da idanunsa,yasauke ajiyar xuciya turai kinsakachi sosai akan yusrab shiyasa har wannan abun yafaru,kuma dama ai inafaɗamiki ko sai andage akansabayason shan magani,namiji kuwa aisaida shan maganin tsari domin lafiyarsa, amma bakomai xan magana da malam salisu yadda yace xaki jini saimuxo tareda shi gidan,
Kan momƴ aƙasa tace
Bahbah bansan hakaxai faruba me yusrab yatsaremusu dik da bansan kosuwayeba.
Bahbah yay murmushi
Hmm turai kenan kibar mutum,ki kalli mutum kawai domin kaidinsa saishi,kikuma nemi tsari da sharrin mutum, kinji
Tohm bahbah nagode xankoma naga yamma yayi.
Toh toh kigaida megidan inkinshiga ciki kifaɗama uwa tabaki wannan shaddar saiki kaima amina naga tamatace
Tai murmushi
Bahbah dakabar kayarka kaɗinka wlh
Aa turai ki amsa kikaiwa amina nace saitafi mata kyau kalar matace
Bahbah angode ai tana nanma xuwa ranan juma ah,
Masha allah toh allah yakawota lfy kugaida megidan naki.
Tohm bahbah xaiji
Taimasa sallama tatafi,
Kwanatayi ranan sallan dare tanakaima allah kukanta akan wannan masalar domin yanxu ko xancenta bayayi,
Gameda nawwara kuwa hankalinta yafara kwanciya ganin yadda mome kesonta take kuma lallaɓata kamar ƙwai ga amina tana girmamata komai yimata take, hajiace takira tace xataxo saigabanta yafaɗi domin kar hajia taxo gashi batanan, nantakewata dabara taxo mata tace suntafi dubai itada Dr, hajia taitamata nasiha da faɗa akan xaman aure sannan sukayi sallama ta aje wayar,
Baƴan kwana biyu saiga bahbah yaxo shida malm salisu, bayan sunhuta momy takira yusrab awaya cikin loƙaci kaɗan ya iso, tsoho mairan ƙarfe kaine haka agidanmu.
Dr yafaɗa yana saƙalo kafaɗar bahbah
Nine kai yakagani ainafika ƙwari kaine tsohon nikuma yaron.
Momy taidariya malm salisu ƴace
Aa wannan loƙacinsune
Dr yayi charab ya amshe
Faɗamasa dai malam
Dika sukai dariya kafin malam ya umarchi dr dayayo alwala,
Yayi yadawo wani rubutu yaɗauko aleda yabasa yace yashafa afuskarsa da ƙafa dahannu daƙansa. Dik yayi malam yaɗauko wani garin magani yace yashaƙa ahancinsa
Yana shaƙawa yafara fita hayyacinsa cikin ƙankanin loƙaci yafaɗi yana malelekuwa tareda jijjiga kansa malam yace
Waye kai
Yace
Nine
Malam yace sunanka mukeso muji da dalilinka na shiga jikin ɗanmu,
Wataƙara yayi xaitashi momy nakuka taikansa xatariƙesa malm salisu da bahbah suka daakatarda ita bahbah yarumgumosa jikinsa.
Malm yamatse masa hanchi sai yacigada magana
Sunana sunana sulaiman nini turoni akayi kuma,,,,,,, turoni jikinsa.
Kuka momy taƙara fashewa dashi tana kiran
Ina nillahi wa inna ilaihir raji un, meyamuku.
Malm yaɗagamata hannu
Kafaɗa mana tayaya kashiga jikinsa
Ƙara yakumayi
Ta hanchi sbd ta iska nabi nashiga jikinsa bayan yashaƙi turarenda akahaɗa dani aciki sainabi iskar nashiga jikinsa yaxama adik loƙacin daxai ji wannan ƙamshi toh ƙiyayya da tsana xata ƙaru axuciyarsa na matarsa har su rabu har abada
Ƙarya ƙake!
Malam yadakamasa tsawa kafita yanxu komu ƙoneka labarinka yashafe
Xanfita ai
Toh kafita,
Yayi shuru nawani loƙaci kafin aga dr yayiwani ƙwaƙƙwaran yunƙuri yabige bahbah baya yadawo ƙasa yibbb tamkar mara numfashi
Allahandulillahi malm yace yana dubansu
Tareda tabbatar musu futar aljani sulaiman, sannan yasanarma da momy sai bayan awa takwas xai dawo hayyacinsa, kuka momy take nawwara ma nayi bayan malam yabada rubutun daxa ashafa masa afuska dasafe dakuma wanidaren bahbah ya sallameshi yatafi nawwara tariƙe hannun bahbah tanamasa godiya abun mamaki saitaga yana kuka yana kallon awarwaron hannunta momy ma shitake kallo tana matsowa har ta xo daf da ita, taɗagota babah yarigata magana
Wacece ke nawwara?
Gabanta yafaɗi tadafe ƙirji
Nikuma bahbah
Yaɗaga kai alamin eh
Ƙasa taidakanta tana ƙara fashewa dakuka
Bakuka xakiyiba nawwara inada vavvan dalili natambayarki wacece ke domin akwai wani abin al ajabi dake taredake.
Bahbah yasake magana.
Taxuve ƙasa tana sharar kuka
Nima bansan wacece niba domin,haka mahaifiyata itama take daga inda batasan wacece itaba, nasamu labari arubuce awasiƙar mutanen kirki waɗannan baxantaɓa mantawadasuba innatah da baffana,nasamu labarin cewa....... Nantabasu labarin mahifiyarta kaf dayadda suka tsinceta harsuka mata aure kuka sosai momy take tareda rumgume nawwara.bahbah ma yayi kuka sosai kuma yajiƙaunar nawwara fiye da tsamman ɗinsa aransa yanakallonta ayanxu tamkar hauwa'u dandanan farinciki yamamaye xuciyar nawwara jin momy ashe yayar mahaifiyartace,ita gida tafaɗo kenan,amina ma taji daɗin abun sosai bahbah da momy sunƙara gamsuwa da nawwara jininsuce dasuka ga hoton hauwa u awurinta kuka kuwa sunsha shi har alhaji yaƙub nera yadawo daga office,shima dayaji labarin nawwara abin yaɗauremasa kai amma yayi murna sosai allah ya amsa addu arsu yabayyana musu jinin hauwa u amatsayin ita dasuke ta nema💜❤❤
💜❤.............
Yana buɗe ido yagansa kwance agadon asibiti hannunsa anɗaura masaruwa, ummah nafitowa daga wani ƙofa, dataje wurin likita hangosa tayi yana ƙoƙarin tashi, ledar hannuntadake ɗauke damagunguna tA ajiye ta rugo garesa tare da ƙarasa tadashi tana jeramasa sannu
Ummah ina ladingona?
Tambayar dayafara jifanta da ita kenan cikin yanayin damuwa da ƙunchi
Umma tamkar maishirn kuka ta dubeshi
Kayi haƙuri modibbo ladingo ahalin yanxu matar wAnice.
Yarumtse idanunsa yanasa hannu yAdafe kansa tare da jijjigawa
Umma narasata kenan ?shikenan yanxu matar wani ce ladingona
Hawaye suka fara xuba aidanuwansa yacixge alluran hannun nasa yakife kansa aƙasa yafara rigan kuka tamkar bagobe
Sam baidamu dajini dake fita ahannunsa ba ummace takama hannu tasa audiga
Baxan iyaba
Ummaa wlh baxan iƴa rayuwa babu itaba
Tajanyo hannunsa tahaɗa danata
Kasaurareni modibbo ko ka manta wacece ni awajenka.
Yaɗago dasauri yana share hawayen fuskarsa wasu naxubowa.
Ke mahaifyatace umma kuma akullum da kuma kodayaushe baxangusheba inamiki biyayya sbd cancantarki, umma bamusu nike da maganarkiba aa ciwon danikejine yakasa gushemin inaji kamar huramin wuta ake acikin zuciyata da jikina kigafarceni dan allah ummA,
Tindayafara magana take kallonsa yadda hawaye kexuba wasu nakorar wasu amma ƙoƙarin dannewa yake don hankalinta yakwanta .tausayin ɗanta yaƙamata taji dama akwai wata dama yanxu data amince da aurensa da nawwara
Tabbas kai ɗane mai biyayya modibbo,amma kayi haƙuri allah shine yaƙaddara cewa dama nawwara ba matarka bace shiyasa haka yafaru,donhaka ka kwantarda hankalinka kaji,
Bai iya ɗago kansa yakalleta ba sai amsawa yayi
Tohm ummah
taimaka masa ummah tayi yashiga bathroom yayi brush yaxo tahaɗamasa tea da abinda maimuna takawo musu ɗaxu.daƙyar ya iyayin cokali biyar yaɗan sha tea ɗin yakoma yakwanta xuciyarsa cike datunanin ladingonsa da yanxu tanacan tareda wani bashi ba,saiyaji wani xafi da suka aƙirjinsa hannunsa yasa yadanne bangaren ɗake masa xafin tareda rumtse idonsa, maimunace da yusuf da ummy suka shigo hanyensa ɗauke da ledoji manya waɗanda maimuna tatsaya tayimusu shoping ajipatu,
Bayansun gaisa da umma takalli modibbo tare dayimasa yajiki,amsawa yayi ransa sama sama yana maidakansa yakife afilo,itakuwa aranta tsaki tayi tanacewa
Humm karma kaixaton inayin wani abu dominkane,ni banyinka yanxu muradina yakarkata kanwanda yafika,taja ƙaramin tsaki,
Batasaniba ashe tsakin yafito fili.
Umma tace
Aa lfy maimunatu kike tsaki
Dasauri tadawo hayyacinta
Amm bakomai ummah dama kafin nafitone yanxu kausar taɓatamin rai,danatuna yanxukuma sainayi tsaki
Kiriƙa haƙuri da ita dan allah kefa babvace maimunatu.
Umma tace tana murmushi.
Bayansallar magaruba maimunatu suka koma dayake tunda aka kwantar da modibbo ummake kwana dashi yusuf da umme kuma suna gidan su maimunatu,
Ƴau satin su biyu a hospital yaukuma akasallamesu suka tattaro suka dawo gida,
Umma sosai take kulada modibbo idonta nakansa tanakuma taimasa nasiha akwana atashi dakuɗin wajen alhj saraki yakafa kasuwanchi yaja jari.yafara safarar masurufi daga ƙasashen waje yakawonan yararrabawa 'yan kasuwa.masha allah kuma allah yadafamasa, 💜❤
💜❤................
Nawwara Tunda takwanta takasa bacci sbd tsabar tsagwaron farinciki data tsinci kanta aciki yau,, nasamun kanta acikin ahlinta tsumu tsumu kai dame wannan daɗi yaykama,ashema ɗan uwanane yusrab, masha Allah Allah nagode maku,har wajen ƙarfe biyun dare batayi bacci ba donhaka tajira uku nayi ta tashi tashige bathrm taɗauro alwala,tashimfiɗa prymt tafara jero nafilfili,bayan tasallame tafara miƙa godiyarta ga allah sannan taima mahaifiyarta addu ah sosai sannan takwanta saidatajuma akwancen kafin bacci yayi gabada ita,
Bayan gari yawaye Dr yadawo normal tamkar bashiba sai ramar daƴaƴi wacce shikansa yayi mamaki tambayar momy yashiga yi menene yasameshe yarame haka,daga baya dai akafaɗamasa dikkan abundayafaru,yayikuka sosai,jinyadda ya wulaƙanta nawwara,ashe datini yarasata taƙarfi daƴaji,sannan abindayaƙarasa shi cikin farinciki shine dayaji labarin 'ƴar ƙanwar momy cedatin dayataso yana ɗanƙarami yakejin labarin ɓatanta afamilyn ɗin nasu,yagodewa allah sosai dawannan makircin baitasiriba, momy yatambaya inda nawwara take nunamasa ɗaki tayi dake lungu aikuwa dasauri yamiƙe yanufi ɗakin.
Itakuwa nawwara dik abinda suke magana akunnenta taxo fitowa taji saita tsaya donhaka tanajin tahowarsa taɓoye abayan labule tana sharar hawayen dasuka xobomata
Waɗanda bana komai bane face nafarinciki da samun buyan buƙata, sannan da cutar da kausar tayimata domin tabbs turaren wajentane tafara shafawa kuma tindaganan bataƙaraganin farincikiba,
Shikuwa Dr yagasanda taleɓe donhaka lallaɓawa yaƴi yaɗauketa cancakat yana dariya
Kamotanan kamotanan,
Itama dariyace takwace mata tana ciccilla ƙafa tareda ƙoƙarin xamewa,safketa yayi ƙasa tareda juya da ita tana fuskantarsa
Allahamdulillah,gaskiya najidaɗin sake buɗe ido danayi naƙara kallonki amatsayinmatata nawwara,axahirin gaskiya bansan dame xangodewa allah ba akanwannan kyauta dayamin har yaƙaramin wata akanta,sai biyayya dabin dokokin daya sharaɗa yadda yakamata sannan indanƙe wannan kyauta hannu bibbiyu, da amana allah nagodema. Nawwara ke ƙyautace daga allah kuma gaki 'yar uwata nidaɗin yalilliɓeni harkaina,
Yabata dariyama yadda yake maganar cike da xumuɗi.
Tai dariya
Hakane allah shine abin godiya,kuma tabvas dimmin tsanani akwai sauki agabansa yah yusrab, nagodema allah daya haɗani da ahlina,
Yakalleta saitaƴi ƙasa dakai
Yayi murmushi ki mai maita mana
Tai murmushi
Hmm karkadamu ai xantafaɗa harsaiya isheka nangaba
Tafice dasauri tanamasa dariya da gwalo
Yabiyota da gudu, aikuwa itama tace ƙafa menaci banbakiba suka xuba.
Gaban momy taibirki tana boyewa da bayanta
Momy momy
Aa menene haka
Dai dai loƙacin dayaƙaraso yana haƙi ƴakaihannu xai danƙota
Momy taimasa daƙuwa
Ungo wannan yusrab metayimaka kake binta saikace tamasata
Yayiƙasa dakansa
Momƴ gwalo take min
Tai dariya wlh momƴ niban masa gwalo ba
Nawwara dataimaganar tana farfaramasa ido
Momy ta hararesa kaiba wlh kafita aidona yusrab
Yayi dariya itama nawwara tayi momy takallesu atare sannan tajinjina kai tanamiƙewa.
Tohm naganeku,sokuke kukoma gidanku,shine xaku faramin wasan yara ko toh kai yusrab gobe kaɗauki matRka ku koma gidanku, kajiko.
Yayiƙasa dakai yana dariya

Please Login or Register in order to submit comment