Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

xaishafi damuwar ki hakaba kuma wlh ni bance maimuna tafiki awajenaba
Rufemin baki saminu! Tadaka masa tsawa
Kasan halin darayuwar ta xatashiga ko kawai rayuwar yaranku kawai itace agabanku ? Na tabvata dacewa nawwara mutumniyar kirkice abindakayi kuma kaƙyauta kaji, miƙewa yayi shima ransa duk babu daɗi bayan ya aikata abin kuma yanxu bayajindadi aransa maimunadake xauna kusadashi tayi ƙasa dakanta gudun karhajia tadawo kanta. Hajia kiyi hakuri dan allah komai ya wuce tunda abinyariga dayafaru insha allahu xa aguji gaba harara tabisa daita yayimata sallama yafice maimuna tabi bayansa wayarta taɗauko numban nawwara takira still akashe kamar yadda tai takira ɗaxu compny sukafaɗamata, sauke wayar tayi daha kunnenta ranta abace xuciyarta cike da tausayin nawwra,kamar kuma wacce tatino wani abukuma dasauri takuma ɗaukar wayar numban moddibo talalubo takira amma harta yanke ba aɗagaba tasake kira amma ba aɗagaba saidata kira yafi sau biyar amma ba aɗagaba kan kujera taxube tana furxar da iskar bakinta cike da damuwa.
Dai dai kan layin unguwar malam abdulsalam aka ajiyesu,sallamar mai keke napeep ɗin sukai, aƙafa suke takawa domin suƙarasa shigalayin daxai sadasu da gidan kowanne acikinsu abindayake saƙawa acikin xuciyarsa daban musamman modibbo dake tarera kukan da ba hawaye acikin xuciyarsa.tareda addu ar allah yaɗorasu akan umma tasauka daga kan ƙudirinta, dai dai loƙacin suka isa ƙofar gidan duk saikuma sukaja suka tsaya tare daxubawa juna ido kamar baƙin ganin juna, kafin tace muje
Tohm yace kawai suka shiga cikin gidan bakowa sai yusuf dake ƙoƙarin gyara kejin kaji yataso laaa anty nawwara tai murmushi yaxo yariƙe hannunta nadawo ɗaxu banganki inakikaje. Kallon sa tayi naje wani anguwanne nadawo. Modibbo dake gaba yadubi yusuf
"kai yusuf ina umma ?
Wanka tashiga
Ok yace kawai yanashigewa falon itama hannun yusuf ɗin taja suka shigaciki ƙasa taxauna tana tahira da yusuf shikuma wayarsa dake aljihungaban rigarsa yaɗauko yanaduba kiran da akayi masa yaga kiran abokinsa umar dana hajia goma donhaka kiran hajia yafara bi.tanaɗagawa yagaisheta cikin
ɓangare hajia tace na am nawwara yar kirki kuna ina
Tafara wasa da yatsun hannunta
Muna gidan inna
Nawwara karki kuka duk abindayafaru naji kuma banjidaɗi raina yaɓachi kinaji kikwantar da hankalinki allah yanatarwdake kumaxankula dake bamai rabamu dake sai aure xairabaki dagidan nan
Nagode hajia lallai kina ƙaunata ba abindaxancemaki saidai nace allah yajamana kwananki
Amin amin nawwara kin cancanci amiki komai yarinyata kuyi haƙri komai kuma yawuce karkice baxakidawoba
Tai murmushi xandawo hajia
Yawwa yar kirki kokefa toh bani yayan naki
Mika masa tayishima haƙuri tabasa yace bakomai shine dagodiya nansukayi sallama yakashe waya
Yusuf tashi kaje wasanka
Dasauri yatashi yafice takallesa miyasa ka ce yafita?
Yakaɗa kansa xuwa ƙofa sbd karyadameki da surutu naga yahanaki ki huta
Ta hararesa
Kajifa wata magana toh menene aciki.am kaji abinda hajia tace kuwa
Eh mana kuma najidaɗin yadda take nunakulawa akanki ummin yara sainaji nimata shiga raina tsohowar
Duka takaimasa ganin yadda yake maganar atsokana
Nikuma banaso nakoma nafiso naxauna atareda umma
Yaɗaga labulen xafita yatsaya
Tohm saiki sanar da hajia hakan amma dani gobe nake tunaninmaxaki koma tunda matar nasonki
Shikenan kabari muga mai umma xata nuna ra ayinta akai yaja numfashi
Shikenan bari nai alwala naga loƙacin sallar mangaruba yayi xanwuce masallachi.
Tohm shikenan saika dawo
Yaɗagamata hannu yawuce tashi tayi taɗauko tsintsiya tashare falon loƙacin umma tafito awanka tashige bedroom tana goge kanta data wanke agurin wanka, alwala itama taje tayo jin ankiran tada salla masallacin unguwar.tashinfiɗa pyramat domin binjam'i,
Bayan sun idar ta lalubo wayar data tararratse taharhaɗata tasa sim ɗinta cikin ikon allah kwa tana kunnawa takawo haske saida tayi murmushin farinciki. Tare da cewa allahamdulillah, bari nakira sumayya nasan tasake kira taji swichoff, ta kamo numban sumayya ta kirata dayake batada kati awayan nera ashirin yarage anaɗagawa bayan sallama tace
Kikirani banada kati awayana.
Daga bangaren sumayya bayanta kashe wayar tai dariya kai nawwara kenan badama , mamanta dake kusada ita tana jan charbi tace
ke yarinyar dake aiki agidan nanko niko tana ina yanxu kwana viyu banajin motsinta?.

Takoma gidan hajiar su maimuna da xama ai tin wancan loƙacin kuma wlh mama can yafi don harmakaranta take xuwa yanxu duka biyun batakuma aikin komai don allah kawai hajiyar ke riƙonta.mamata tajidaɗi
Kai amma abi yayikyau dama hajia aitanada mutumchi ubangiji yatayata riƙo
Amin mama kirana tayi tace nakirata sonake nayi sallar isha i saimi waya,
Yaykyau kigaida ita.

Game da moddibo saida akayi sallan isha i yashigo gidan.umma yasamu sunacin abinchi suna hira jefe jefe kamar bakomai haka umma tanunawa nawwara baƙaramin daɗi yajiba kusa da ummi da yusuf yaxauna tareda satar kallon nawwara yace
Umma barkada dare
Yawwa
Ta amsa tana cigaba da cun abincinta takalli ummi
Jeki kitchin kiɗauko ma yayanku abincinsa,
Naɗe kafansa ƴayi bayan yasa abincin agabansa shinkafa dawakece dafadika tasha kayan haɗi gwaninsha awa yasan umma da iya girki shiyasa har sauri yake yaga yasa abincin abakinsa.
Ummm umma kice kinan dai kamar dah😇😇
Suduka suka tintsire da dariya harda nawwara wacce tinda yaxauna bataƴarda sunhaɗa idoba tana kallonsa yadda yaketa lalubo idanunta ɗaxu tasharesa sbd tanajin kunyar umma sosai.
Yaya santi kake
Ummi tace umma ta kallesa tana ɗan murmushi kai modibbo kaifa baka rabuwa da abindariya inba hakaba yaukafara cin abincina
Yakai wanne yaɗebo acokulin sannan yariƙe kunnensa
Nadaɗe bamu haɗuba umma dole narinƙa jinkaina yana yawo asama gaskiya dai yakamata aragemin na anjima sbd xanƙara
Mixasuyi inba dariyaba umma tace
Kaga xaka ishi mutane da santi ni bani waje anan
Yay dariya yana ɗaukar ruwa yasha sannan yay hamdala tukunna yamiƙe
Inaso xankoma ni yanxu sbd akwai sauran abubuwan xanyi yanxu adaren nan
Umma takallesa
Yakamata ka samu kahuta
Xan huta umma amma saibayan kin haƙura kuma nasamu nakammalada abindana sa agabana
Tohm shikenan saida dafe kenan dai xakacemana
Eh tunda yanxu komawa xanyi can wajen shi abokina umar. Akan maganar aikin gidan mannan
Har yayi musu sallama yatafi yadawo

Yawwa ummah gobe da sassafe yusuf yasharemin shagonƙofar gida xandawo da duk kayana insha allahu gobe dama maigidan nawa yau yasallameni xankama nawa sana ahn daban kuma yabani ishashshen jari daxan amfani dashi wajen harkantawa, umma kiyi haƙuri dawaccan maganar dan allah ummanmu saida safe
Yafice yanagama maganar bataredaya dubi yanayin fuskartaba
Harxaifice titiyahau mashin yatafi yadawo ƙofar gidan yatsaya domin baxai iyatafiyaba bai ji muryantaba donhaka yakira wayanta loƙacin tatashi itada ummi xasuje sukwanta tana ganin kiran takarasa dagudu tana kashe ƙaran wayar
Hello yace
Tace na am
Kifito dan allah inƙofar gida inganki xantafi wlh harnatafi nadawo
Tasa hannunta abaki donkar ummi taji abindaxatace domin taga ummin matasanja mata fuska xata iyakwasa taje tafaɗawa umma hiransu intaji
Ƙasa tayi da muryanta sosai tukunna tafara magana
Kaje kawai xamu haɗu dasafe idan kashigo kawai kaga yanxu umma na falo bata shiga ɗakintaba.
Daga ɓangarensa.
Haba dan allah ni inxaki fito ki fito kawai umma aibatasan inaxaki ba
Wlh tasani domin vaka daɗe dafitabafa
Kinga tom nidai kifito ina nan inajiranki aƙofar gida
Ooooo wlh xakajajamin umma tana min kallon mara kunya inbahakaba yanxun da goben duk baɗayabane?
Cikin faɗa kuma yafara magana
Duk ɗayane amma yanxu nace nakeson ƙara kallonki waikinji kwa yadda xuciya take soyuwa akanki nawwara?
Jin yafaɗi haka yasa gudun karciwon kirjinsa yatashi yasa taisaurin tashi tsaye tana ƙoƙarin ɗaukar hijab tafasa domin kar umma tagane waje xata,tace
Tohm gani nan. Tayanke wayar
ummi dake bacci ƙarya tamiƙe xaune tanabin nawwara dakallo kafintace
Ina xaki anty?
Bakinta har rawa yake wajen bata ansa
Inaso xanshiga banɗakine
Wani kallo ummin tabita dashi
Tana fitowa taleƙa falon umma taganta xaune tana jin redio amma ba hanyar cikingida take kallowaba donhaka baxataga fitar taba
Dasauri tafice tana warware ɗankwalin kanta tarufe jikinta.
Kan dandamalin ƙofar gidan yake xaune sai wasa yakema hotonta awaya sai surutu yake ahankali ta salalaɓa taraɓe tabayansa dominjin abindaya kecewa
Xoomin ɗin hoton yayi yana ƙwarama fuskarta idotareda murmushi kafon yafara magana
"allah sarki abarƙaunata,farincikina, inasonki muradina irin soyayyar dabata rushe wa,ko talalace,kota gurɓace taxama ƙiyayya inamiki relly love mai wuyar samuwa aduniyarmu tayanxu,inasonki ummin yarana dama xan iyacikamiki alƙawarinki ke farincikina ce 💕

NIMA KAINE FARINCIKINA tafurta hakan muryanta narawa
Sam baisan da xuwantaba saida sassanyar muryarta tadaki kunnuwansa cikin yanayin soyayya taƙarasa taxauna kusa dashi
Nadaɗe dayimaka ƙyautar xuciyata dama akwai abindayafita danabaka aayau ɗin nan muradina amma ina so ka ƙara sani inasonka banida madadinka duk farincikina kaine
Murmushin dake fuskarsa yafaɗaɗa
Nagode sarauniyar iyaxance ƙwarai ni ma shedani dasoyayyar ki gareni karki wani damu niɗin nakine ke kaɗai.
Dan allah fa
Tace tana masa kallon tabbatarwa.
Ƙara fuskantarta yayi tamkar maishirin shigewa cikinta.
Ƙwarai makuwa ke kaɗai xam xamma mallaki
Ƙasa tayi dakanta tanasa sa hannu abakinta sbd kunya
Naji daɗi sosai kuma nagode dawannan

Bakomai nidake duk ɗayane kuma kincancanchi hakane ke mai alfarmace awajena akodayaushe ladingona
Ni gaskiya banason sunan nan
Tafara tirja kafafunta aƙasa tana kaimasa duka
Yafara gocewa yana karewa da hannunsa
Sunankine fa wanne naraɗamaki sabd ƙauna
Tahararesa
Dama haka xakace mana kuma ai yanxu bakamar dah bane.allah kaƙara saina daina maka magana.
Ah haba ah haba tauraruwas baxami hakaba kinga yanxu kihaƙuri amma duk bayan sati xanna rinƙa faɗa sauɗaya ko?
Taƙi kulasa yaleƙo fuskarta
Nace ko?
dunƙule hannu tai takaimasa dundu yariƙe hannun yamiƙe cixo takaiwa hannun nasa dasauri yacikata yana dariya yaɗaga mata hannu tare da huro mata kiss yatafi hannu taɗaga masa tare da kama kunne alamun xanrama,loƙacin datakoma ummi taibarchi kuma bata haɗu da umma ba don haka itama rage kayan jikinta tayi kawai takwanta tare dayin addu o in kwanciya baccci kafin tarufe jikinta dabargo. Asuba tagari

Good Night nawwara 💤🌙
😊 Sweet Dream,
🌠🌠🌠🌠🌠🌠🌠
Assalamu alaikum warahamatullahi wabarakatuhu 'yan uwana al ummar musulmi inayimaku barkada wannan ranata sallah 2019.inakuma tayamu murna dafarincikin ganin wannan rana mai albarka allah yamaimaita mana yasa mawuce lafiya amin
Kuna tare dani shamsiyya Adam
🌠🌠🌠🌠🌠🌠🌠
Kafin umma ta tashi daga baccin datakoma bayan sallar asubah loƙacin nawwara tafara aiyukan gidan xuwa bakwai tagama kimtsa ko ina tashiga kitchin kasan cewar batasan abundasuke breakfast dashiba yasa tatsaya tana tunanin toh mexata ɗora tajuma tana tunani kafin tashiga duba kayan abincin kichin ɗin taga wanne xaifi sauƙi dankalin turawane dana hausa sai doya kwaya uku datarage sai kuma wani garin kunu da shinkafa wanne yafi rabi sai taliya kwali huɗu anbuɗe ɗaya bata gama duba sauran kayan abincinba tatsaya kan doya taɗauki ɗaya tagyarata taɗora tana ɗan dahuwa ba luguf ba tasauke tafasa ƙwai tasoya taɗora tea cikin ɗan ƙaramin loƙaci takammala tafasa shayin tajuye aflass sannan tagyara ɗakin girkin takashe mungal ɗin takoma ɗakin ummi ta ɗauro xani da hijab akai tashiga wanka loƙacin data fito ummi ta tashi tana wanke baki kayandata taho dasu kala ɗayata saka ta ninke waɗannan taxo dasu ajikinta tasa ajaka tashafa man ummi sannan ta nufo ɗakin umma.
Loƙacin umma tadawo daga kichin taga aikin datayi takuma tambayi ummi tace ba ita bace tajidaɗi sosai sallamatayi tashigo gefe tasamu taxauna tagaida umma
Amsawa tayi fuskarta da fara ah badai kamar dahba,
Yusuf da ummi ne suka shigo gaida umma sukafaraƴi sannan ska gaida nawwara,
Yusuf ne yace
Umma bari naje nashirya makaranta asamun abinchina ina karyawa xanɗauka natafi yau xamu fitaxiƴarada malamanmu ance muje dawuri.
Umma takallesa da kulawa
Shikenan ke ummi ɗauko kayan abincin akicin sannan kije kema kishirya
Tamike tana fita
Bayan sunkarya tare nawwara takwashe kayan takai waje tawanke ummi da yusuf sukatafi makaranta
Musalin tarada rabi modibbo ƴashigo anan yayi break suna hirada umma
Saidaya gama yadubi umma
Dama umma inaso muyi wani magana dake
Ta gyara xamanta tare da bashi hankalinta
Inajinka
Umma akan maganar nawwarane dah sonake tadawo nan gurinki tabarcan gidan damuke dah inaganin xatafi samun kulawa da kwanciyar hankali ananɗin lurada yadda taɗaukeki tamkar innarta tohn kuma gashi ita hajiar datake wajenta tace tanaso nawwara takoma wajenta taroƙi dai alfarma gashi ni namarasa mixancemata mundai ƙyale akan eh xatakoma yau.
Umma da tundayafara maganar taxuba masa ido tana daɗa karantar ɗan nata lallai baƙaramin so yakewa nawwaraba
Hummn naji tohm nidama ai afarkoma nanumaka bason xamanta nake taredaniba donhaka shawarar dakuka yanke tayi kuma karhakan yasa kaitunanin ƙin nawwara nake aa wlh inasonta ayau ta auri wani xanmata hidima dai dai ƙarfina.
Yakwantar da murya tamkar mai shirin kuka
Umma miyasa bakyasonta atare dani
Sbd kawai inajin wani al amari atareda ita wannan hujjar mai girmace baxantaɓa faɗamaka ita yanxuba duk dabanrantseba sbd dole wataran buƙatar kasani ɗin xata taso amma kasani baxaka auretaba nikam nagama wannan maganar
Ita ɗin rayuwatace baxan iyarayuwa babu nawwara ba
Tajallasa da yatsa
Xaka iya rayuwa batareda itaba donhaka kamaida hankali jikinka
Ƙafarta data ɗaga xatashiga falon tatsaya jikinta rawa kawai yake sbd baƙin labarin dataji daga bakin umma hawaye kwa batasan loƙacin dasuka fara sauka afuskartaba jikinta rawa kawai yake.dikkan hannayenta taɗora aka tafasa ƙara.da sauri modibbo da umma sukayo kanta kafin suka ƙaraso tafara jada baya tana shashsheƙar kuka tajuya tai ƙofar waje dagudu tana maicigabada kuka tamkar rantaxaibar jikinta tafice da gudu.rufa mata baya modibbo yayi umma ma hijabi taɗauko tabi bayansu
Gudu kawai take batamasan indaxata nufaba tsakiyar titin daya fito daga ƙofar ruwa dai dai fistbank tashiga tsakiyar titin idon ta arufe dayake ranace bama ababan hawa sosai atitin amma ɗaya hannun wucewa suke sosai ƙoƙari take tatsallakashi ta isa mai ababhawan taji andanƙe hannunta wani baƙincikine yaxo yatokare mata maƙoshi taji gwancin mutuwada abindaxata fuskanta gaba saiji yaytafaɗi dasauri yacicciɓeta yasata amotarsa dai dai loƙacin da modibbo ke ƙoƙarin tsallako titin amma wanne yasata amotar haryaja yacilla kan motar titi, gidan hajia ya nufa kai tsaye da ita yanyin horn getman yabuɗe yashiga dakan motar dasauri yafakata yafito ahannu yaɗaukota yashigo falon hajia
Daƙƴar hajia ta iya motsawa daga inda take bakinta narawatake furta
Inna nillahi wa inna ilai hirrajiun, me xangani yusrab kamar nawwara menene yasameta menene yafaru da nawwara?
Kan 3sta yashinfiɗar da ita yayiwa hajia baayani game da abindaya gani
Kan nawwara taje tana jijjigata
Kaga mukaita asubiti kawai ɗaukota muje yanaɗaukarta hajiana saɓa mayafi modibbo yafaɗo falon ahargitse hawayene kawai kexuba aida niyarsa
Karaf yahangi nawwara hannun yusrab. Wani baƙincikine yadunƙule masa arai yanufesa afasace tareda fincikota xuwa jikinsa yaɗaga hannu xai yarfa wa yusrab mari cikin xaman nma yusrab yacaɓe hannun modibbo .
Karka soma aikata kuskuren dakake ƙokarin aikatawa domin xakai nadama
yusrab yayimaganar yana watsi da hannun modibbo.
Axafafe modibbo yafara maganar tamkar xaishaƙe yusrab
Kayi kuskure kai kumada ka taɓamin mata domin sainai shira ah dakai wlh sai kafaɗi kai wanene daxaka kai hannunka jikin matar daxan aura,
Hajia tashiga tsakaninsu
Ya isa da allah duk kuxauna domin kunsamin kaina aduhu musamnam kai modibbo
Nawwara dake motsi tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta amma takasa jin maganar umma kawai take akunnuwanta
"baxaka auretaba domin hujja maigirma yashafi ahli inason kyakkyawan tsatso daga gareka mahmud"
Hannunta takai kunneta ta toshe sbd tadainajin maganar amma ina saima ƙari danhaka dawani kuka maicinre ta tsinke tana janye jikinta daga jikin datajita ajiki duk dabatayi ido biyu dakowa awajenba amma tasan tana guri mai aminci
Dukansu ido suka xuba mata hajiace ta taso taxo inda take tana kama hannunta
Nawwara kidaina kuka
Faɗawatai jikin hajia tana maicigaba da risgan kukanta,
Nashiga uku hajia rayuwana yanufi wani ɓangare daban nakasa gane komai.
Tashafa kanta
Menene yafaru ne
Taɗago takalli modibbo shima idanuwansa akanta suke ko ƙiftawa bayayi tanuna sa da yatsa
Shine xaibaki amsar tambayarki hajia abuɗaya nasani shine nayi asarar masoyi wanda yakemani soyayya domin allah soyayyar dabaxansamu mai mani irintaba hajia,nibakowa bace alamu yanuna amaganar data fito daga bakin dabaxaimin karyaba niban da tsatso maikyau waye toh xai yarda ɗansa ya auri 'yar tsatso gurbatacce, wannan shine dalilin hawayena,
ƙasa modibbo yayi dakansa yana sharar ƙwallah hajiama jikinta yayi sanyi anrasa mai kuma magana kukan ladingo ne kawai da shashsheƙa ketashi tana sharar majina
Yusrab tausayinta yamamaye xuciyarsa soyayyarta yajitaƙara ƙarfi aransa yanaji koda mahaifiyartace uwar karuwai shixai iya amincewa aurenta donhaka yamiƙe yaƙara inda suke
Idan don wannanne ki kwantar da hankalinki nine xansoki ahaka xan miki so wanne yafi wanda kikarasa xan iyasadaukar darayuwata wake inasonki baxantaɓa wulaƙantaki ba koki fuskanci masala yusrab nasonki nawwara kisharehawayenki kikuma amshi soyayyata,
Tana lamgwaɓar dakanta jikn hajia
Karya kake kai baka isa kasota irin yadda nake sontaba nawwara tawace
Modibbo kemagana yana tashi tsaye
Yusrab ya jefamasa wani mugun kallo
Yayima hajia sallama yafita modibbo xaibisa hajia tariko hannunsa
Kicikani baxanbarsa ba, babu wani ya isa ya rayuda kaunata bayanni, nine mijinta sai yasan yafurta so gareta wlh,
"Ya allah mahmud cooldown pls na ya ina magana kana ƙoƙarin kwacewa kabisa kaga xo nan kaxauna
Bin bayanta yayi ransa aɓace ƙasa yaxube tareda ƙuma kansa da kujera
Narasa yaya xanyi da rayuwata hajia komai yanaƙoƙarin yaxamemin maiɗachi, nakasa fahimtar mahaufiyata,wannan al amarin duk yanafaruwane sbd baba bayadarai da duk hakan vaifaruba,banaso narasata domin baxanbar wani ya auretaba wlh iyakarfina baxan yardaba,
Hajia tariƙesa tana karanto duk addu ar dataxo bakinta tana huramasa har yasamu yajingina da kujera tareda tallafe fuskarsa da dukkan hannayensa
Nawwara dake gefe tana sharar ƙwallah taxuba masa ido domin yanxu tafi tausayinsa kuma sama dakanta
Hajiace tashi ga yimasa nasiha da nunamasa ƙarfin ikon iyaye akan yaransu. Har saidataga jikinsa yayi sanyi yasauko sannanta umarcesa datashi yaje gurin mahaifiyarsa yayta lallaɓata har ta amince itaxata shiga maganar taje tasamu umman
Sannan daƙyar yalallaɓa yatafi amma nawwara ko motsawa daga inda take batayiba,

Rayuwane yasauya al amura suka kwaɓe yayin da modibbo rayuwa kemasa baraxanar rasa ladingo.domin umma ta take da ƙafar dama akan itasam batayarda da aurenta da yaronta va domin batada tsatso yayi yayi tagayamasa menene yasa tace haka amma tace ba yanxuba danhaka duk rayuwan badaɗinta yakejiba ko ina badaɗi idan yaje gidan hajia wajen ladingo kukane ke rabasu arasa mai rarrashin wani. Kasuwancin dayafara na gwangwan ba laifi yanasamu sosai domin umar aboƙinsa ne ke nunamasa kan harkan sana an, bayamasa hassada kokaɗan kuma shine yake kwantar masa da hankalinsa idan yakawomasa labarin abindake faruwa,
Gameda ladingo kuwa tarame sosai tayi wata fiyu da ita tamkar wacce ta tashi daga jinya dik inda hajia takai da matsamata akan tachi abinchi bataci saidai taci kaɗan ta tashi kotasamata kuka inta takuramata, dr yusrab kuwa yabuɗe wuta akan xuwa gidan hajia ba yakwana uku baizo yaga ladingo ba tunbata kulasa hartafara ɗankulasa suyi hira sama sama yatafi shima yanajindaɗin hakan domin yanasa ran xata amince dashi tasaba dashi watarana harta amsa soysyyarshi,

💚tofa kunji makaranta anyakuwa tunanin yusrab xai tabbata ladingo ta amshi soyayyarsa? Toh bari muga yadda xata kaya, takuce dai Shamsiyya Adam (Matar yaya) akodayaushe taredaku acikin littafin ladingo na modibbo💚

Maimuna ce kwance jikin wani saurayi wanne baxai wuce shekara 27 dandogo fari dakaɗan yafi ta shekaru ƴanashafa gashin kanta da dukkan hannayensa tareda kisss ɗin wuyanta tana danne dannen waya ta mari gefen hannunsa
Kaga kb nifa banason rashin haƙuri fa da allah. Sunkuyowa yayi dai dai fuskarta

Haba baby menene narashin haƙuri ke ma fa kinsan yadda kike da sugannan baxan iyahaƙuriba mutƙar kina kusadani
Taja tsaki kaɗan
Hmmn dama haka xakace mana kafin watama kafaɗamata don ku maxan nan bakuda tabbas wlh
Kafin yayi magana
nancy tashigo ɗakin tana xuƙan karan tabar dake hannunta xubewa tayi bisa kujeran dake fuskantar su
Kai kuna sha aninku baruwanku kb kanashanawa
Kb yaɗaga mata hannu tareda jinjina irin nawaɗanda suka jiƙu adniƴar holewa
Ƴayi babbar yarinya ɗanmiƙo min sigarin nan kara ɗaya.
Cillamasa tayi tana miƙamasa leter
Kaima xaka ɗan taɓa kenan
Maimuna takarkato da kanta tana kallon nancy. Tareda yatsine fuska domin batason hayaƙin taba
Ke wlh baƙaramar 'yar iskabace nancy tunjiya kikefama ɗurawa cikinki wannan hayaƙin don iskanci kuma saikinxo wajen danike xaki xauna kisha.
Harara nancy ta cilla mata tana janyo filo tatokare bayanta tace
Eh naji cikina dai nake ɗurawa ba iskanci nake ina yayarwa kaina xunubiba
Miƙewa maimuna tayi tana sa abayarta
Nikike faɗawa haka, toh ta allah shiyasa kullun nake ganinki agida akame
Nancy tai dariya
Kobanxaunaba dai nafi wata inaxamama xaki jawoni daina fito...............
Duka maimuna takaimata yasa tsayar da maganar tana hara rarta
Kb kwa dariya kawai yake
Nan suka gama tumbelensu suka tattara suka tafi shima yakama gabansa.

Wa iyaxubillah allah yakiyayemana xuri ah daga irin wannan mummunar rayuwa amin

Sumayyace xaune tasa ladingo agaba tambayar duniyar nan tayimata akan abin dayake damunta amma tace ba komai abin har yaba sumayya haushi tamiƙe taima hajia sallama tatafi ranta aɓace
Tanafita ladingo tasa kuka hajia tashareta sbd yanxu tasaba da wannan kukan kullun acikinsa take yanxu badare barana,
Bayan wata biyar da faruwan al amari inna tacije yayin da modibbo ke ƙoƙarin yanke ɗanyen hukunchi amma kafin haka ladingo ta ankare domin tayi alƙawarin baxata taɓa yarda yabijerewa mahaifiyarsa akantaba donhaka yau tana xauna agidan hajiama batanan
Dr yusrab yaxo
Yasha mamakin yadda taɗan saki raidashi
Yatambayeta hajia tace tafuta gidan gaisuwa
Yadubeta
nawwara har yanxu dai loƙacina tatafiya mahaifiyata nata matsamin kan maganar infitar da matar aure kekuma kinƙi ki amshi tayina wlh inbakeba saidai naitaxama har xuwa wani loƙaci ban aureba
Takaryan dakai
Dr kenan xanfaɗamaka wata magana amma karkamatsamin kansai kaji dalili.
Harsauri yake wajen sonjin maganar
Inajinki inajinki baxanmatsamikiba wlh
Kasan waceceni afarko domin duk abindayake faruwa kasani
Yaɗaga kai alamin eh
Tacigaba
Tohm ka amince xaka aureni ahaka?
Na amince mana xan iya aurenki ahaka akodayaushe mutƙar ke kin amince da aurena
Tashare guntuwar ƙwallar idanunta dake baraxanar xubowa dagacan ƙasan ranta kuma kukaxuciyarta take
Shikenan kaxo miƴi aure nanda kwana goma nakeso miyi auredakai yusrabb
Axabure yakalleta domin yanajin maganar tamkar amafarki kuma daga bakinta tafito yaƙura mata ido don tabbatar da gaskiyar maganar
Dagaske kike nawwara?
Tace
Eh kamar yadda kaji,
Allahamdulillahi allahamdulillahi allah nagode maka insha allahu xanyi kamar yadda kikace kwana goma bi ixnillahi ta ala xan aureki,
Tashi tayi tana dafe kanta
Wayyo kaina
Subhanallahi menene yasameki
Ganin yadda duk yatada hankalinsa yasa ta yatsine fuska
Um um ɗan ciwo yakemun kaɗan basosaiva xanɗanshiga ciki.
Sallamar hajia ne yadaƙatar da ita bayan tayimata sannu da dawowa tashige ɗaki,
Dr yusrab bayan sungaisa da hajia yake labarta mata duk abinda suka tattauna tsakaninsa da mutuniyar, hajia taji daɗi sosai domin itama tanaso nawwara ta haƙura da modibbo domin umma batada niyyar saukowa.duk da yana bala in bata tausayi yaron,haka suka rabu da yusrab akan xanturo asan yaxa ai lefe kwa yace tindaga ƴau xaije su siyo shida kanwarsa xuwa gobe sungama haɗawa, addu arsa dai ɗaya allah yasa momƴ ta amince akan kwanakin bikin,
Bayan koma warsa gida yasamu momynsa da maganar taji daɗi sosai kuma ta aminceda auren musamman dayafaɗamata kowacece yarinyar bai boyemata komaiba kanwarsa budurwa amina tayi murna yayanta xaiyi aure harta ƙagu taga wacece wannan domin batin yanxuba akefama dashi yayi aure amma yaki 'yammata da dama sun nuna soyayyarsu garesa amma yawatsar sbd bawacce tayi masa acikin kwana biyu labarin auren dr yusrab yabaxa cikin family saita ya momy murna ake daga kowanne ɓangare.na ahlin nasu kafin wani loƙaci maganar taiƙarfi anxo annema masa aure anbada kuɗin neman aure antsayar da ɗaurin aure laraba maixuwa farinciki awajen hajia ba acewa komai tabada kuɗi wa ɗaya dagacikin ma aikatan compnyn kawo kayan ɗaki naƙasar waje ya kawo mata kaya sannan tasamu watamace daxata kulada jikin nawwara har ranan laraba da xa aɗaura mata aure.

💜💜ina bama masu karatu haƙuri gameda yadda xasuji wannan ƙarshen labarin,ba ina ƙirƙirabane aa labarin gaskiyane yafaru agaske sai kuma ɗan wani abu danaƙara domin labarin yatsaru yadda xaibada ma ana yakuma yi daɗi, inamaku fatan alkhairi💜💜
❤dagataskar MATAR YAYA❤

Adurƙushe yake agabanta kansa aƙasa kuka yake sosai yanaroƙonta
Umma rayuwata nacikin wani hali kitausayamin
Modibbo nafaɗamaka abindayake raina donhaka shawara tarage gamaishiga rijiya, damar kace kaje ka auri nawwara amma ba hannu na
Share ƙwallah yake wata nafitowa
Baxan iyaba nayi aure bakyaso baxan iyaba umma kuma nahaƙura da auren nawwara umma kuma insha allahu baxanƙaramiki maganar nan ba xanrabu da nawwara naƙƴaleta tayi rayuwarta.
Tashi yayi yafice yashagonsa yashiga yaɗauko wata tsohuwar jaka dayadaɗe daboyeta acikin kaya yakwanceta yaɗauko wani kullin abu yafito
Kamar kodaƴaushe hakayasameta kasan 'yar bishiyarnan tana aikin datasaba hawaye shi harmamaki yake yadda batagajiyada kuka. Saidayayi sallama yakaisau biyar sannan taji kusada ita yaxauna sannan yafuskanceta
Ki rage kukan nan nawwara karya cutar dake
Tasunkuyardakai
Hamm ba abunda kukan nan xaimin xubar hawayena shine sauƙin da xuciyata ke samu rashin xubarsa ba abindaxai ƙaran bayan ƙunar rai da raɗaɗin xuciƴa,ka ƙƴaleni xanrayune amatsayin da shine ƙaddarata
Tafashe da kuka
Nasan umma baxata taɓa amincewa ka aureniba,nikuma nafi so ka kasance mai biyayya agareta domin kasamu albarka da kyakkyawar rayuwa, koda badaniba ni nasan kainawane.baxandaina maka fatan alkhairi ba harƙarshen numfashina ina....s .o.....n. ka
Idanunsa suka kaɗa sukai jaxur bakiɗaya kansa yakulle xuciyar wani radaɗi take da tafasa. Daxaran yahaɗiyi yawun bakinsa saiyarinƙa jinwani ɗachi maitsanani,dole yanisanci nawwara domin mutƙar yanaganinta acikin wannan haln

Please Login or Register in order to submit comment