Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kace me garin ƙaura yaɗaukada labarin anyiwa ladingo fyɗe jiya tsintota akai abakin hanya dahaka harmagana taje kunnen gidansu modibbo yusuf naba umma lbri moɗibbo dake shigowa karaf yaji labarin jikinsa har rawa yake yaƙarasa ya ɗauke yusuf dawani mahaukacin marin dasaida yaga ƙyallin wuta kafin yanunasa da yatsa
Uban wanene yabaka wannan labarin,
Jikin yusuf rawa yake kawai yariƙe kunchinsa dake tamasa xugi da raɗaɗi
Awaje naji anatafaɗa,
Rufemin baki banxa kawai karkasake naƙarajin ka danganta min ladingo da irin wannan mugun labari kuma tukunna abakinma wa kaji,.
Abokina iro
Ball yayi da ƙafarsa yajuya yafito kaitsaye gidan su ladingo ya nufo
,innace keta surfa masifa wa faffa akan yahanata fita taje gidan su ɗan tani tayagamasu rigan rashin mutumchi,domin labari yaxo musu akan yadda gari yaɗauka ladingo fyɗe akamata,kuma shine kaɗai xai iya wannan ƙaxafin sbd shiyakawota gida, daga dukan kawo wuƙar da lami da kawayenta sukamata.
Wlh saina kai wajen maigari maganar nan malam baxan ƙyale sukama yarinyar suyimata wannan mugun dukanba ace munƙyale munshiru
Faffa yakalleta
Abindanake ƙoƙarin yi kenan nima yanxu haka innafita can xan wuce don sai anfitar mana da haƙƙin jikarmu wlh bamaitakamin nawwara inbarsa, shikuma ɗantani nafaɗamiki ki ƙƴalesa harshi xanhaɗa nashigar saiyafaɗi waye yagani tareda nawwara,
Inna tashare ƙwallarta,
Allah ƴa isa tsakaninmu da ɗantani malam gari yaɗauka rauuu akan nawwara anyagamata mutumchi.
Subhanallahi donkansa ai allah baxaivarsaba kinga ki kulada ita bari ninaje nasamu maigarin,
Tohm shikenan saika dawo malam,
Yafice aƙofargida suka haɗu da modibbo yagaidashi sannan yashigo cikin gida, inna bayansungaisa tamaibayanin komai ganin yadda yashigo hankalinsa atashe kuka inna kawai take tana mai bayani akan abindayafaru.
Ladingo dake kwance goshinta akumbure tamotsa ta tashi jin maganar modibbo wani sabon kukan tadasa kuma
Ƙarya suke min ba abindayafaru bane, su lamine suka dakeni damanya bulali karka aminta da maganar mutane,
Yaxauna kusada ita
Baxantaba yardaba koda duk mutanen duniya xasu taru sufaɗamin wannan tatsuniyar,matuƙar baɗaga bakinki najiba ki kwantar da hankalinki wlh sainayi maganinsu acikin garin nan bamaicin mutuncinki yakwana ƙalau saina takashi kowanene kuwa .
Takalle tare da yaye hannayenta da nunamasa wuyanta
Kalla ka kalla nan yadda suka rinƙa dukana nabasu haƙuri amma lami tace sai sunga gatana miyasa xankasance inasonka,
Sunyi kuskure domin duk sai sunyi nadama wlh kinga barima inxo
Yafice tana kiransa amma kojuyowa baiba,daga gidansu ladingo ba indayanufa saugidansu lami yaci sa ah kuwa tana ƙofar gida tana tuyar wainan fula nayamma, saijin saukar mari tayi tako ina ta fuskarta saidaya tabbatar kanta yaɗauchajin dako kai baxata iyaɗagawa takallesaba sannan ya nunata da yatsa
Kaɗan kikagani matuƙar baki fita daga harkan ladingoba wlh banxa karya ajawo inbanmada abinki nikinga nayi kalada ƙaxamar mace irinkine?to ashir ɗinki wlh duk loƙacin dakika ƙara taɓa ladingona saina ƙarar miki da farinciki naɓatar dake gabaɗaya.
Yafice yana huci
Lami dake durkushe tana kwasar kuka taɗora hannu bibbiyu aka tana kuma ehu mahaifiyartace tafito tana tanbayarta menene yafaru tafaɗa mata abinda modibbo yaxo yayimata harda sharrin yadoketa abaki
Masifa innasalame tahauyi dagaƙarshe takama hannun lami suka tafi wajen maigari,
Tafiyar midibbo kuwa gidansu indo yasauka ya aika yaro akirata. Tanafitowa yaɗaɗɗauketa da mari tagegece tafara ehu yakwarfeta tafaɗi tafasa goshi yafice yabarta anan tana kurma uban ehu kafin mahaifiyarta taleƙo yafice itama sawota agaba tayi saiwajen maigari,
Mairoma kamar yadda yayiwa mutum biyun haka yayimata itama tashiga gida bakinta najini iyayenta suka sawota agaba akataho wajen maigari,
Gidan su ladingo yakoma yalabarta mata duk abindayafaru sannan kuma ya umarceta data tashi tashirya ita da inna suxo suje gidan maigari domin yasan kowacce iyayenta xasu kai ƙara wajen maigari ,
Baffa yasamu maigari sungaisa sannan yafaɗa masa abindayake faruwa kuma yakawo ƙara domin afitarmada ladingo haƙƙinta ranmaigari yaɓaci yadubi malam sallau yace aje ataho da indo da lami da mairo tareda iyayensu...........
Kukan daya nufo wajenne yadakatar damaigari daga maganar dayake.
Lamice da inna salame suka shigo bakinta ɗaukeda sallama
Dukka mutanen fdan suka amsa matsar ƙwalla tashigayi nankuma lami na gursheƙen kuka
Ranka yadaɗe kaduba fuskar 'yata duk sawukan hannun yaron nan modibbo yanxu yaje har gida yaɗaɗɗauketa da mari balaifi xaune bana tsaye maigari yadubi innasalame
Yanxu dama nake aikawa akan axomin da ita lamin daku ina mahaifinta?
Tohh axo kuma dalami ranka yadaɗe akanme kuma nidana kawo ƙara kuma anatahumarmu,
Kamar yadda kikaji 'ya yanku ne suka aikatawa yarinyar gidan malam faffa wannan mugun duka dayaxama raɗe raɗi acikin karkararnan akan fyɗe akayimata toh ƙaryane maganatafito allah kuma yakawoku,
Inda da mahaifinta da yayanta suka shigo suma suka kawo ƙara wa maigari ta modibbo suma yace susamu waje suxauna aje atahoda modibbo,
Kafin maikiranyatafi modibbo da inna dake riƙeda hannun nawwara sun ƙaraso yaƴan indone yayikansa tareda dannamasa ashar kafin yaƙarasa modibbo shima yakwaɓe riga suharɗe dafaɗa, daƙyar akarabasu kowa namaida numfashi. Mairo da babarta da babanta suma suka yi sallama baban mairo yakaiwa modibbo naushi yamiƙe xai shaƙesa maigari yatsawatar masa baffa yakalli baban mairo
Dakataɓa yaroncan wlh da anyi ɓatacciya awajennan
Bban mairo yayokan baffa
Toh bismillah mana shege kafasa wanda yafasa bayaƙaunar allah,
Baxan yardaba wlh sai anɗauma indo abinda yayimata koni faɗa da dangin moddibbo har abada wallahi mahaifin indo yake wannan maganar
Maigari yadakatardasu yadubi inna da faffa tare da kallon ladngo dake jikin inna tayi lamo yakira sunanta nawwara
Tamatsa tana matsar ƙwallah
Menene yahaɗaƙi da waɗannan yaran
Yanuna indo,mairo,lami. Tagyara xamanta taxayyana masa kaf avindatasani har gargaɗin da lami take mata akan tarabu da modibbo,
Sunkuyar dakai lami tayi yayinda innarta keta danƙwashinta kinban kunya wlh
Maigari yakallesu
Kuntabbata abindata faɗa gaskiyane?
Ƙansu aƙasa sika fara amsawa da eh
Ya dubu iyayensu tohm kunji dakanku yadda abun yake sunchi xalin ƴarinya kuma sun yunƙurin hallakata don allah yakarene yataƙaita wahala donhaka yanxu abindaxa ayi xankira birni akawo mota aɗebrsu akaisu can koto aimasu hukunchi domin sunyi yunƙurin kisa kuma sun amsa dabakinsu donhaka baxanƙyalesu ba.
Kuka sosai iyayensu suka shigayi musamman innar lami da ita kaɗai taragemata aduniya harda tsugunnawa maigari tana kuka daƙyar dai akasamu dasa bakin baffa da inna ya haƙura akan basu ba ita kuma koda harara karta ƙarashiga tsakaninsu sukace sun amince
Shima modibbo akace bashi basu faɗansu da ladingo ba faɗanshi bane,nan yayimusu nasiha kuma ƴace suhaɗamasu kuɗin maganin da aka kai ladingo asubiti baffa yace aa abarshi yayafe,sunji dadi nan sukaita godiya yasallamesu ska tafi.

Tundaga loƙacin dawancan rigiman yafaru ba abundayaƙara shiga tsakanin ladingo da su lami,haka modibbo tskaninshi da lami ko kallonsa batayi tanaganinsa xata fitada gudu domin yanxu tsoron sa suke,
Soyayya kwa tsakanin modibbo da ladingo sai abindayaƙaru, sunshaƙu sosai ƙaunar juna suke abinhar mamaki yakebama jama an garin duk daxuwa ƴanxu sundaina mamaki domin abingaba yake iyayensu kuma akullum namasu fatan alkhairi, magana har manya sunshiga anyimasu baiko
Farinciki agurin masoyan ba acewa komai fuskokinsu haske kawai suke hankalinsu ƴaƙara kwanciya dasoyayyar tasu,🌱🍯🌱🌱🍯🌱🐝🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🌱🌱
🌱🍯🌱🌱🍯🌱🍯🌱
🌼🌱 MATAR YAYA ❤️ ceee🌱🌼

LADINGO NA MODIBBO,
darene sosai wajen karfe biyu da wani abu yayin da gari yayi tsit babu wani mutum dake yawo ba motsin komai, awannan lokacinne, garin TSADA yashiga firgici da tashin hankali yayinda'yan ta adda suka kawo musu hari cikin wannan dare gari yakaure da harbe harbe sukafara shiga gidaje suna harbi ko su cinna wuta bayansun watsa fetir , modibbo dake shagonsa nawaje,dama baidade dakwanciyaba sbd karatu dayaxauna yayisaiwajen daya nadare yakwanta ehun mutane daguje guje shine yatayardashi dagabaccindaya tafi dashi maidadi salati dauke avakinsa yatashi tareda kiran sunan allah yabude kofar shagon nasa ganin garin yayi hayaki ta ko ina ga wuta nacin wasu gidajen dake makwabtaka dasu, gida yafada yana kiran baba umma cikin gida ya riskesu baba rumgume da kannensa suna kuka umma hannunta hijjabine da charbi "baba kuxo mugudu batsayawa xamiba sai su riskemu nan ,
dasauri suka fito sunabin bayansa yanke kawai suke suna tsallake gawarwaki cike da tashin hankali gabda xasubar garin ya juyo , "modibbo kataho muje mekakejira katsayanan,
"baba nayi mantuwa
"kai modibbo komai kamanta nace kaxo muwuce mutsira da ranmu, koka manta wannanma barauniyar hanyace mukabiyo,
gumi yake yarcewa kawai yanunamasu hanya "xanje nataho da ladingo da baffa da innanta domin jikina yabani sunacikin garin nan, baba kuje bakin hanya xamu sameku,
yana gama maganar yakoma tawannan barauniyar hanyar yashiga garin,
umma kuka take sosai yayin dasuma kannensa yisuke dakyar baba yalallashe su suka cigaba da tafiya domin basu kadaibane,mutanen wadanda allah yatsiratan keta futowa sunayinbakin hanya gawasunan ma sai gudu ake takai takai,,
innace rumgume da ladingo tana sharar kwalla baffa dake xaune kafarsa akumbure ko tashi baya iyayi dama yana fama da wannan ciwon kafa wani iri maiwuyar sha ani domin anyi magani anyi magani sosai amma duk shekara saiyayi kafin wani lokacikuma saiyasami sauki shiyasa burin ladingo kenan tagirma tasamu kudi takaisa asubitin birni, ,,"kuje kulu dan allah kuje kar mutanen nan suxo susamemu duka sukashemu, kubarni nidama mutuwa xanyi,ai kobasu kasheniba,inna nasharrar kwalla "baxan iyaba malam xamu xauna kawai mu mutu tare anan,
ladingo ta fada jikn baffa "nima xanxauna ,mu mutu tare ,domin kaine muke kallo muke jindadi bafffa ,
faduwar modibbo gidan yasa suduka cikuikuye wuri guda domin sun sadakar mutuwa ce kawai,nishin dayake saukewa dasauri sauri yasa suka ƙara saddaƙarwa, saidayayi magana cikin tsoro da firgichi suka ganesa inna kuka take sosai tamika masa hannun ladingo "modibbo naroƙeka amana kaje da ita munbaka amanar nawwara nima inanan domin baxan iyatafiya domin tsira nabar malam ahalin nan dayake cikiba ba ,,
aa baxa ayi hakaba inna riketa kiga,
yasunkuya "baffa hau bayana muje,
mamaki yakama su duka amma sai sukaga yafara daga baffa yana taimaka masa yahau bayan mikewa yayi su inna na gaba sukafara tafiya ,ko ina hanyar wutace ke ci , su shiganan sufitanan su labe can dahaka harsuka fita xuwa bakin hanya nan suka samu wasu mutanen nashishshiga jeji da masu tare irin manyan motocin nan dasukeyo lodi daga wani garin xasu wuce, suna isa wani motar yaxo wuceba mutane suka tareta dakyar mutunen yatsaya yataimakesu, yasan masala irin wannan sai abinyafada kanshi aikuwa fal suka cika motar wasu atsatstsaye, ladingo na jikin inna modibbo narike da baffa ,tunanin iyayensa kawai yake domin baison indasukeba allah yasa sunsha allah ka karemun su don albarkan annabinka, jiyayi baffa nakama hannunsa ya kara rikesa yana sunkuyawa "baffa lafiya ? Hawaye baffa yake "yaro allah yayimaka albarka kaji,"kadaina kuka baffa
"yaxaman min dole kuka domin bansan ya rayuwan nawwara xaicigaba va , watakilama daganan shikenan munrabu ,
"aa baffa insha allahu muna kyautata xaton kuma muntsira daga nan,
"yaro ungo wannan kabawa nawwara dan allah
wani dan kyalleni dakulli aciki yadankawa modibbo amsa yayi yana damkewa sosai
kafin baffa yakuma magana saijikake tauuuuu sun harbe dirvern,kafin suce sunxagaye mutanen cikin motar kuwa ina kowa yayi takasan sunshiga jeji wasu kuma an harharbesu anan,kowa gudun kwatar rai yake, jikin wani bushiya yasamu yana xubewa banda haki ba abindayake hannunsa dafe dakirjinsa, baimasan inda inna tayiba balle baffa dabaya iyatashi yasan yanxukam anharbeshi wayyo ladingo na yafurta ahankali yana tashi dakarfinsa yafara cigabada tafiya yahadu da matane da dama wadanda yasani amma sam hankalinsa baya jikinsa domin baigantaba ta mutu kenan, ba baba ba umma ba kowa kenan, watakara yasaki yana faduwa akan gwiwoyinsa,
ladingo dake gigice ta makale jikin wani karaman bishiya jikinta bandarawa ba abindayake wannan kuuwar datajine yakara tsoratata saidaga baya tarinkajin kamar muryan modibbo kamar kukansa takeji kusa da ita, dasauri tamike tana bin indatake jin sautin ,harta isa inda yake durkushe amma dayake yanayin darene sosai bata ankara da mutumba tuntube tayi dashi, wata kara tafasa tana jadabaya "karka kasheni dan allah wayyo! W... Yatoshe mata baki da hannunsa sannan yayi mata magana duk da cikin kuka yake maganar taganesa dan haka gudu kawai suka cigaba da shekawa basu suka tsayaba saidayaga tatsaya tana tangadi " sannu kingaji ko ? Ta daga kai domin ba halin magana jitake tamkar 'yan cikinta zasu xaxxago sabata yayi kawai akafadarsa yacigaba datafiya, sai daya tabbar sunbar garin nesa makusaba sannan yasamu guri suka sauka , da hijab dinta yashiffida mata takwanta yasata agaba tare da tallafe fuska yana kallon ikon allah ahaka har gari yafara haske,dora tafiyar sukai bayan sun samu ruwa sun sallah wani mai amalanke sika cikaro dashi ahanya suka tambayeshi dan allah yanxu wanni garine kuma suka dosa yana kallonsu yace "ai akwai sauran tafiya sosaikafin ku isawani gari nan kusa saikuntafiyar kwana biyu yaro, tare suka kalli juna shida ita yayindata dabe kasan wajen shikuwa cikeda kwarin gwiwa yakallin tsohon bafilatanin yace "toh baba inaxaka
"xanje riganmu kiwo shanunu nafito dama ,
"dan allah kataimakemu baba kanwata nacikin wani hali,
yakalleta yana kallon saurayin "kutashi muje toh kunji,,
cikin amlanken suka shiga tsohon yacigabada kora shanun suka cigabada tafiya basudadeba suna tafiya suka isa rugan wasu kana nan yarane suka taho suna tarar wannan tsoho cikin harshen fillo suke maganr modibbo duk abindasuke fada yanajinsu har tambayar dawani dansa yayimasa suwaye wadannan fafa yace bakinmune,
atakaiche kwanan su modibbo biyu awannan rigan suna samun kulawa kwarai daga wajen fafa da maidakinsa kuma sunbashi maganin tsari sosai musamman dasukaji inda yanufi wato fitadaga wannan jajin, yau bayangari yawaye,sunkyakykyawan karin safe da madara mai dumi sai tuwo miyarkuka amma yasha manshanu,sannan suka dauko guxirinsu da fulanin nan sukabasu sannan sukafito domin tafiya yayinda fafa yataho nuna musu hanya harbakin wani katon hanya yakaisu kanan yadawo cike da kewarsu domin yaran sunshiga ransa adanxaman dasukayi yafahimchi wani abu atattare dasu,sunshiga ransa sosai amma baxasu iyaxamadasuba sbd yagwada tambayar saurayin amma yace suyi hakuri baxasu iyaxamaba sbd kanwarsa yakeso tayi kyakkyawan rayuwa ,
sunacikin tafiya bawanda yayiwa wani magana tana rike da gefen rigansa sbd tsoron hanyan shikuma jakane dake daukeda guxirinsu yarataya akafadarsa,ahakama dasuka tashi arugasaidayayi wanka ladingo kwa saida matar fafa tayi dakyar tatashi tayi "wai miyasa kike da tsoro hakane ba fa abindaxaikamaki kinga kicikamin riga
"dan allah kayi shuru wlh suna labe sunajin magananmu shikenan muma sunanmu gawarwaki daxaran sunganmu,
dariya yayi sbd yadda take maganar kamar rada,yanajin saukar numfashinta akafaɗarsa
Yaɗan guce jikinsa daganata domin yafahimchi batagane irin halin dayake shiga idanjikinsa danata sukahaɗu,itaƙam sai abinta take tanaƙarashigemasa,yayin dashi kuma yake ta axabtuwa dasonkasancewa da ita "aa basajinmu aiwannan hanyar bakamar waccan bace ki kwantar da hankalin kinji ,
tadaga kai ,har fuskarsu nagogar najuna "tohm amma wlh inkaga nasakeki munshiga cikin gari naganni cikin mutane
"sbd me ?
Taƙamƙame hannunsa aƙirjinta
"sbd kallonake kamar kaima rasaka xanyi ,
Yachije baki tareda ɗan wani murmushi
"tohm shikenan muje,
tausayin kansa yake tawani bangaren kuma yafi tausayinta domin yanxu batada kowa saishi,shima bayadakowa sai ita,lallai sudin ababan tausayine,sungaji likis bakamarma ladingo danhaka wani guri suka sauka, yatashi xainemo musu ruwa tariƙeshi, yace ruwaxainemo musu taxauna tajira tasa kuka yace suje tare haka bayan sunnemo ruwa sunsha dafuran dafulin nan suka basu sukadama suka sha wajen bacci saidayabari tayi bacci yaxare hannunsa daga nata yamiƙe yayi alwala yafara nafilfili,nanma kwana sukayi,amma kanan bacci domin basa runtsawa sosai sbd tsoro,tanafara bacci xatafarka afirgice saiyariƙeta yayimata addu ah, ranan ajikinsa tayi bacci shikuma yanagyangyaɗi. ahaka suke cigabada tafiya harsuka kuma kwana daya awani rugan dake kusada garin da fafa yakecewa kusada birnine, suna sallah suka karaso garin kaitsaye shigowa sukayi kauyene amma babbangarine kwarai yanada jama ah sosai sai shige dafice ake mutanen karkarar,yayinda modibbo yatsaida wata yarinya mai sayarda taliya yatambayeta inane gidan maigari tace aikusada gidansune subita ta nunamusu tanagaba sunabinta abaya ladingo dan dan sauri har tintibe take ba hali tarike rigar modibbo sbd mutane amma kallon da akemusu ya isa sbd sunhadu sunfutu futu bakidaya sunfita hayyacinsu ,
maigari yakallesu "maraba daku inayimuku marhabin 'dan saurayi daga ina ?
modibbo yaxayyana ma maigari kaf abindaya faru game da kauyensu har kwanakin dasukayi kafin suxo nan ,
saida maigari yayi kuka sosai danhaka yakara kallonsa "yaro ni sunana alhji bello maigarin wannan kauyen dakuke ciki DANGUGUWA,dan haka dagayau ni nayimaka masauki agarina,
"godiya muke allah yasakada alkhairi ,
kanansa alhj bello yakalla yana cewa "yawwa kamees ga baki kadaukesu ka kaisu gidanka kafin akarasamin gyarana insha allahu,
wanda aka kira da kamis yace " babu komaima nima na amince suxauna agidana xanrikesu bakomai yaya,nidakai aiduk dayane,
daga akayi addu ah akashafa sannan malam kamis yayima modibbo da ladingo jagora xuwa gidansa,
matar sa naxaune aikin cikin gida take yayi sallama suka shigo "aa maigida bakine damu ?
yana murmushi yace "eh bakin maigarine amma anan xasu xauna ,
saikuma tadan hade rai "lafiya daiko "eh lafy kinga wannan kuxauna da ita anan cikin gida shikuma xanbude masa shagon kofar gidan yaxauna aciki,,
takalli ladingo "tohm shikenan maigida muje ,
takai ladingo wani daki sannan ta tambayeta sunanta "nawwara sunana amma anfi kirana ladingo
tayi dariya irin tarainin hankalin nan
"daga wanna kauye kuke dan da dukkan alama daga kauyen kayau kukafito wani kallo ladingo taimata amma ba halin rashin kunya domin nan ba kauyensu bane, dama kuma inna tasha fadamata akwai inda dole in akayimuki ki kyale kinji nawwara , saitace wlh baxan kyaleba ,
sai inna tayi dariya ,
tashare kwallar data silalo kan fuskarta lallai abinda inna take fadamin hakane yaugashi nagani agabana anacimin fuska amma ba halin ramawa sbd anfi karfinka,
takalli matar malam "xanyi wanka ,
tashi tayi tana cewa "kibiyoni in nunamiki bandaki,
daga wajen modibbo ma haka malam ya budemasa shagon gaban gidan sannan yakawo masa bokitin wanka da roban ajiye ruwa harda sabulu da soso, yaji dadi kwarai donhaka wanka yayi,shima ,
koda ladingo tayi wanka kayan matar malam tasaka wadanda tabata , amma sunyi mata yawa yawo kawai take acikin kayan musamman kafadar tana xamewa tana mayarwa haka ta dauki abincin modibbo da matar malam tace takaimasa tatafi kaimasa hijjabinta ta dawo tadauka tasaka duk da dukun dukun yake haka tasa, xaune tasameshi kan darduma yana laxima alama yanuna tundayayi sallar axahar yake xaune awajen,tayi sallama tana shiga shafa wa yayi yana juyowa yafuskanceta, "barkada yamma
tace tana tura masa abincin gabansa, "yawwa ladingo na kinci abinchin kema ko? tagirgiza kai "matar malam ce tace nafara kawo maka sainaje muchi,,
yayi murmushi "allahamdulillah allah yasakamusu da alkhairi toh kinga yadda rayuwa yake yau fari gobe baki , tadagakai takallesa "eh naga rayuwa domin natabvata dana rasa baffana da innata babu wani abudazaixo kuma haryafi wannan, modibbo,, "bami fidda raiba munasaran kuma haduwadasu inhar basu mutuba , tashare kwallar idanunta "himm hakane allah yasa hakane bari naje tana jirana
"tohm inkungama saikixo ko?
tadaga kai "tohm,
kwanansu biyu agarin danguguwa,yayinda maigari yadinkama modibbo kayi kala shida ladingo kala shida itama atamfofine roba shikuma yadikane 'yan dari da hamsin hamsin irin na bonoxxan da ake baxawa agefen kasuwa, akwana atashi satinsu uku agarin yayin da modibbo yafara sabawa da samarin karkaran sbd har fitasuke sushiga dawanau boll sudawo duk daba ra ayinsabane boll amma yana dantabawa sbd xama yauda kullun jiki xaigaji, yauma sundawo daga boll sanye yake dakayan boll yakarasa gida ladingo dake wanke wanke taji bude shagonsa dasauri tamike tana futowa "modibbo yau kundade wlh,
yana kokarin sanyan jallabiya yace "eh muntsaya sabeer yataso daga kasuwarsu kinsan tare muke dawowa,
"tohm kayi wankan xanjiraka cikin gida ni, murmushi yayi yana kallonta "tohm shikenan xankiraki xakima rakani gidansu sabeer din don munyi maganadashi akan nima xanfara xuwa kasuwar tasu , murnace takamata "yawwa yayi dai dai hakan ,
tadagamasa hannu tana shigewa cikin gidan matar malam tasamu tsaye rike dakugu tana kallonta tsayawa tayi tana jin tsoron karasawa domin xata iya kaimata duka sbd matar malam,kwai masifa da rashin hakuri gashi tasamusu ido ko kaka suka motsa saita cewani abu shiyasa suke basarwa suna rayuwa kamar ya da kanwa, "kiyi hakuri matar malam yayanane yakirani,
harara tacillamata "yayan wa? ke tsayafa kiji duk munafuncinku naganeku wlh,donhaka karki sake nasake ganin kinshiga shagwansa inbahakaba wlh sainayimuku sharri agarin nan anmuku korar kare
jikin ladingo narawa ta tsugunna "kiyi hakuri dan allah wlh ba mudakowa baxankaraba daga yau, "tashi ki karasa wanke wanken da allah ,
dasauri takama tanayi tana hawaye wannan wacca irin rayuwace,haka akeso suyi , modibbo yashigo yanataje kansa yayikyau sosai cikin yadinsa ruwan toka amma maiduhu lokacin tagama wanke wanken shara take, wucewa yayi wajen matar malam dake kitchn suka gaisa sannan yadawo wajenta takarasa sharan tana dauraye wajen wanke wanken, "tunda kingama dauko hijabinki muje kirakani,
tsintsiyar ta aje gefe tanadauko hijabinta suka tafi ahanyarsu ta xuwagidan ne take cemasa "yanxu hakaxa mucigabada rayuwa babu wani farinciki modibbo ,
"aa bahaka xamucigabada xamaba nangabama kadan garin nan xamu bari duka
"wanne lokaci kenan ?
"lokacin danafara samun kudimana nasamu na iyawani sana an lokacinne xansanarwa maigari ya daura mana aure saimu tare acikin birni,,
murmushi tayi harda dan tsallenta "xanji dadi sosai sbd rayuwan birni na birgeni sosai ,
"kinga nikuma farincikinki kawai nake so nagani,akan ki farinciki xan iyakoma maye don in inganta rayuwarki ,sabon allah ne kawai baranba,ki kwantar da hankalinki modibbo nakine,
farinciki yacikata takallesa saikuma tana ganin sunhada ido taboye fuskarta "inasonka modibbo na ,
"nima inasonki ladingo ta ammafa abirni da nawwara xami amfani
tayi daria "eh mana kaga karsuna tsokanata ko
yayi dariya "hakane amma ni ai inmuka ware gefe xannakiranki dahaka ko ,
yarfa hannu tayi "ni aa gaskiya watarana sai sunji mutane ai,
"toh shikenan baxanfadaba
har suka karasa gidan su sabeer suna hiransu cikin farinciki, aikawa yayi akira sabeer din bayan sun xauna akan benchin dake kofar gida a ajiye,
"aa malam modibbo kace kaine har ka iso ,
musabaha sukayi dahannu "wlh ai bana xaunaba tunda munyidin xanxo,
xaunawa sabeer yayi kusadashi dayake benchin dogone "hakane kam kuma ka kyautaai,
ladingo ne tagaidashi "lafy kalau itace nawwaran ko ? yatambayi modibbo "eh itace xanfito nagaba abindatake shine nadaukota mukafito daganan magarin xamu xaxxaga saimuje kuma mugaida maigari muwuce gida,
"yayi kyau kam hakan, toh gameda kasuwar danake lekawa ko toh ai malam modibbo shi wannan abun yana da wuyane saika daure kafin nan ka iya amma tunda kace kanaso kaga yadda ake shikenan ranan asabar saimu fita tare kagani,
"toh nagode sosai sabeer allah kuma yakaimu lafy xanxo muje,
nansukayi sallama sukataho , tagidan sallau sukabiyo yana nunamata gari tacan wajen makarantan boko suka billa gefensu kuma wani filin boll ne yara nata wasan kwallo, daganan yabida ita tacan wajen kasuwar garin sukabiyo gidan maigari suka wuce yanaxaune da mutane uku ataredashi,donhaka modibbo ne yashiga sukagaisa sannan ta leka tagaidashi suka dawo gida xuwa lokacin matar malam tacika taidam, ladingo nashigowa takaimata chafka amma tini ladingo ta goce tayo waje modibbo dake kokarin alwalan sallan magaruba yatashi bayansa takoma tana haki matar malam taleko "kaga karkasake kaimagana inkwa kasake kace wani abu laifin xaishafeka wlh, modibbo dabaisan abindake faruwaba yakalli ladingo amma saitai kasadakai yakalli matar mlam dake jijjiga jiki ita ala dole sai ladingo taxo tawuce ciki tadaketa, "wai mekike nufi malama yimin bayani kunsani aduhu,
ladingo na kallon inda matar malam take tace" dama tana marina kota haureni inadanyin kuskure yanxuma dukana xatayi nafito,
"tohh kinfadawa ubannaki xairamamiki kenan toh kaxo karama mata mana naga kacikabatse sai kumbura kake
modibbo wanda bakinciki yahanasa magana yakalli ladingo xauna anan bari malam yadawo,
wani sabon bala in matar malam tasaka domin tasan malam bayadaukar irin wannan yanajin wannan lbrin abindatake yima ladingo saiya sabamata domin shibai yarda da xalinchiba,, ganin modibbo baikulataba yasa takalli ladingo "taso kishige nafasa dukanki amma ki kiyaye abindabanaso , mikewa tayi modibbo yakalleta dasauri takoma taxauna domin nuni yayimata dataxauna, "kai wlh tallahi kafita daga idona inrufe,au dan kaji manasauka shine xakamin iskanchi toh kakiyayeni ke kuma xakitashi kosai naxo nan nasameki, dariyace taso kwacewa modibbo yakalli ladingo itama dariya take kasa kasa tashi tayi tabita gidan amma batayimata komaiba sai mita dai datake tayi,
saida yayi dariya bayan tafiyarsu vasu dade dashiga ba saiga malam yadawo nan suka gaisada modibbo sannan yashiga ciki,
ranan asabar kuwa karfe takwas modibbo yaisa gidansu sabeer shima fitowa yayi kawai sukatafi domin yashirya, takwas darabi suka isa kasuwar wacce akekira 'yar kasuwa,dayake motocin dake kawo kayatin dare suke kawowa,wasu kuma nashigowa yanxu wasu kuma nalodi sufita abindaisaikagani yadda kowa yake hada hadar gabansa,kofar wani shago suka tsallaka sabeer yadubi wani babban mutum "alhj antashi lafia "lafiya kalau har anfito kenan "eh alhaji anfito ainaga ankawo kayama
mutumin nafitowa "eh ankawo kuma yau akwai aiki kalli waccan motar ,
"eh naganta alhji
"toh toh kayanane kasamo abokan aikin naka kukawo munsu ciki,
sabeer yajidadi domin ganin yau daga fitowarsu har ansamu aiki watarana kwa insukaxo sai su yini basuyi aikin komaiba ,in akwai wannda kake yawan masa aiki inyaga har antashi ba aiki saiya dan yaga maka wani abu,, kallon modibbo yayi "aa wannan fa kamar bansanshiba akasuwar nan,
hannu modibbo yamika masa suka kara gaisawa "eh bakone yaunema yafara xuwa ,
"ok allah yataimaka

Please Login or Register in order to submit comment