Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da sauran Masarauti da kuma kaunar zumuntar da muke so takara karfi a tsakanina da yan uwana Sarakuna wannan dalilin yasa na nemi alfarma aka maido babban gasar da aka kwashe shekaru masu yawa a hadata sai gashi ankawo ta cikin wannan Masarautar ta mu ta Sirika mai tarin albarka,lallai kam wannan ba karamin alfahari bane agaremu....saboda haka nike san inkara jan hankulan ku kukara zama masu mutunta jama'a da kimanta su kodan daukaka darjar Masarautar mu,sannan mukasance masu aminci da karamci ga bakin mu,ina kara nusatar daku akan misali dana jima ina baku kuma bazan fasa bada misali da mutanan Burhaan ba Masarauta ce babba mai dinbin tarihi a kasar hausa duk irin girma da tarin dukiyar da suke gadara da ita basu fasa taimako ga al'umma ba da jajircewa dan ganin sun gina al'umma ba, ina san ran zamu koyi dasu koma fiye dasu Sarkin su Sarki ne mai adalci,ina fatan zaku fuskanci sakona sannan ina san Sarkin yaki da sauran Jarumai da ku dage damtse wajen ganin kunyi kafada da kafada da jaruman Burhaan wanda muke ganin a duniyar mayaka da Jarumta ta gidan sarauta har yanzun basu da tsara...sannan ina kira da uban bayi da ka maida hankali ga bayin masautar nan wajen gani sun bada himma ga yin da'a ,mutuntawa da karrama bakin mu, su zam masu nuna kara,saboda kowa zai yaba akan kokarin ku koda sun koma gidajen su kuma a isarmin da sakona ga uwar bayi takara kulawa da bayi mata....Daga karshe ina kara jan kunne ga Jaruman mu su kasance masu kishin zuci sannan ku kasance masu nuna kara ga sauran abokan ku Jarumai tunda ku aka iske,ina fatan Allah yabamu nasara mai daurewa."Amin,Allah yataimakeka muna rokon Allah yabamu tsawan rai da lafiya mai anfani"Amin zaku iya tafiya daman wannan shine maka sudin hada wannan muhimmin zaman yakamata ku kara daukar shi da mahimmanci."
_____________
Sarki Abdulbaseet Abdulkareem zaune a saman karagar mulki anata fadanci amman baki daya hankalin shi na wajen Sadauki yana tunanin shirun da yaji tayi yawa danko a ranar ya tada dan aike da wasika zuwa Masarautar Burhaan ana cikin fa'da saiga dan aike daga masarautar Sirika an aiko mashi takarda,ana kawowa maga takarda ya amsa bayan izini da Sarki yai mashi....
"dan samari daga ina."?magatakarda ya tambaye shi sadda kansa yayi ya dan rankwafa cikeda girmamawa yace."Daga kasar Sirika nike sakone mai mahimmanci zuwa ga wannan Masarautar mai albarka."magatakarda gareka."cewar Sarki AbduAbdulbasit.
Budewa yayi yafara karanta ta kamar haka

_Assalamu alaikum_

```Amincin Allah yatabba a cikin wannan Masarautar ta Roowan mai dinbin tarihi daga masarautar Sirika ina fatan sakona ya isa zuwa ga uban kowa Sarki Abdulbasit Abdulkarim muna mika sakon gayyata agareka kai da jama'arka zuwa gasar da za'a gabatar a cikin masarauta taa ranar sha biyar ga watan jumada akhir,dafatan zaku amshi sakon gayyatarmu daga Sarki Abdullatib Muhammad Sirika, bissalam
```
Allah yataimakeka kaji abinda ke ciki"Gyaran murya ya danyi cikeda kamala yace."shikenan duk da kasancewar kunsan halin da nike ciki, a halin yanzun bana jin zan iya zuwa wata gayyata kamar yanda mukasani a ranar nake shirin zuwa kasar Burhaan domin jin halin da iyalina suke ciki duk da kasancewar na tura masu da dan aike kuma zamuyi tafiyar ne da Jarumai na,bacin haka da naturasu dan su wakilci wannan Masarautar tamu mai albarka, a matsayina na uban ga Sarakuna bai kamata ace ban samu damar zuwa ba."Allah yaja da kwanan ka ai sahun giwa ya doke na rakumi."hakane shamaki,amman nasan yanda za'ayi zuwa gobe insha Allahu."Allah ya nuna lokacin lafiya,Allah yataimaki Sarki mai adalci."Sarkin gida kaba bakon mu masauki mai kyau da tsari? "Allah yataimakeka anbashi harda wa'anda zasu bashi kulawa kafin zuwa ya wuce"aikinka na kyau sarkin gida"godiya nikeyi Allah yakara maka lafiya da nisan kwana."Amin Sarkin gida Sarki ya amsa."cewar Sarkin zagi......

Sadauki na kudi akan naira 300 rak tafiyar ta musamman ce.

Halimatu ta ruga da gudun ta,ta ɗane saman mahaifin ta."sannu da zuwa Abba."yawwa autar Abba."tunda Halimatu tayi ihun murna yan gidan baki daya kowa ya fito da sauri su jamil da Kamal suka rungume shi sai murnar ganin mahaifin su sukeyi, suna cikin jin dadin su sai ga Hajia Mansura ta fito hannun ra dauke Ahmad tana mashi wasa tana ganin mijinta cikeda farin ciki ta rungume shi baki dayan su suka ta zauna sai murna sukeyi fira suka soma kowa na tambayar shi hanya."gimbiyata ina muka samu kyakkyawan yaro haka masha Allah."Murmushi ta sakar masa tace."Jikan ka ne."
mamaki kwance a saman fuskar shi yasa hannu ya amshi yana mashi sahihin kallo dke tuna mashi da wani abu ko mai son tantance wani abu."duk inda wannan yaron yafito jinin Muhammadu ne"Murmushi ta kuma sake mashi tace"kwarai kuwa dan shi."jini ba wasa kamar yaron da ubansa harta baci kice sun kawo mana ziyara?mine sunan shi."Allah sarki haka dama kama ta gaji haka ai sunan aminin nashi yasan ya."Ahmad ko Mukhtar."Ahmad."cewar Halimatu."Allah ya raya mana."Amin."ina Asma'un."? Ya kuma tambaya yana daura Ahmad saman jikin shi yana mashi wasa."tana fitowa"Allah sarki ya'ta baiwar Allah Asma'u badai hakuri ba"gaskia kam."fira yakeyi da iyalin shi gwanin birgewa....sallamar Shattimah suka tsinkaya baki dayan su suka maida kallan su gare shi yana ganin mahaifin shi cikeda farin ciki yazo ya rungume shi murnar sukeyi tsabar farin ciki dama sunjima basu hadu ba"inata kewarka Ahmad miyasa kayi mani nisa."?a hankali suka saki juna sannan Shattimah ya zauna gefen kafar mahaifin shi yace "nima nayi kewar ka Abbana kana raina kullin kawai dai abubuwa ne suka cakude mana sakdai yanzun komai ya daidai ta da iznin Allah"jibi yanda ka koma daganin ka kana cikin damuwa."bakomai Abba."badan ya yarda ba ya kyale dan nashi

Koda Asma'u ta fito kasa ta zauna ta gaida shi cikeda ladabi sannan tayi mashi barka da hanya"yawwa ya'ta sannu nayi farin cikin ganin ku naji dadin zuwan ku sosai,Allah yaimaki albarka."Amin Abba sannu da hanya"yauwa ya'ta."fira yaransa kowa ke mashi musamman abubuwan da suka faru da baya gida saboda mahaifin su fataki ne bai zama dan kasuwa ne sun jima suna fira cikin tsantsar shakuwa da junan su daga bisa ya mikama Jamil Ahmad, yata shi suka shiga daki shida matar shi dan ya samu shirya kafin ya fito suci abinci.
"Nikam ya lanarin Tafeedah."? Cewar Kamal."murmushi Shattimah yayi yace."kullun yana raina amma nasan zaizo nan saidai kafin nan inaso intura mashi da sako."Allah yakaimu nayi kewar Ya Mukhtar."hmm ina ruwan Tafidah."haka suka zauna kowa da abokin labarin shi kana ganin su kasan basu cikin damuwa bansa Asma'u data zurfafa cikin tunanin mijin ta ba karamin kewar shi tayi ba tana ayyanawa a ranta ko wane hali yake ciki? ji take kamar tayi kuka musamman idan ta tuna halin dasu Ammi ke ciki haka Mai martaba ko ya warke wani sashen na zuciyar na ayyana mata kodai ya rasu basu sani ba,hawayen da suka ziraro mata tayi saurin gogewa batareda ta bari kowa ya gani ba musamman Shattimah bai so yaga tana tunani.....

Ki hanzarta ki mallaki naki kada ayi babu ke Sadaukin Burhaan kenan.

Yauma kamar kullin Umar suna filin gwaji inda Jaruman su keta ansar gwaji na musamman sai faman sukuwa sukeyi da dawakai wasu na wasan takubba yayin da wsu ke tsere ba kadan suke bada gwaji ba,zuwa yanzun duk abinda sukeyi Umar yagama haddacewa kaf cikin kwakwalwar shi dan dai shi bai taba gwaji ba saidai ya kalla idan sunayi yana gani har suka gama komai suna gamawa ya kwashe kayan aikin yakai ma'ajiya sannan ya kama hanyarsa ta zuwa gida akan hanyar tafiya gida ne ya hadu da Laminu babban bawa ne da shi akaje aka siyo Umar ko da Sadauki ya ganshi saida ya shaida shi har kasa ya gaishe shi saboda Laminu na saman Sadauki.
Kamar jira ya hau Sadauki da zagi."naji ance dakai za'a tafi Sirika walahi sai nayi maganin ka harka isa aje dakai wannan gasar komu da da muka dade cikin Masarautar nan da kyal aka zaba damu sai kai."? Shiru Sadauki yai mashi sai aikin kallan sa yakeyi kara kulewa Laminu yayi yace." sannan kuma naji ance kai ne zaka jagoranci masu kula da jarumai ko."?gyada kansa Sadauki yayi batareda yace komai ba.."walahi sanaui maganin ka dan na fahimci kowa kai yake so harda yarima Ammar kai yake so ko."?wannan karon Umar ya daina mamakin Laminu kuma bai fasa kallan sa ba da ido kawai ya bishi baice uffan ba har yagama maganganin shi ya tafi cikeda tsanar Umar aran shi.
shidai Sadauki yana mamakin yanda wasu mutanan basu da hankali yanda yaga Laminu na tada jijiyoyin wuya duk akan aikin wahalar har wani abun bata rai ne da hassada abinda bai sani inda akwai yanda zaiyi daya yace bai zuwa shine yake bala'i dan karamin tsaki yaja ya tafi.

Sadaukin Burhaan na kudine kibiya ayi tafiyar nan dake ba algush a cikin wannan tafiyar nasan zakiji dadin sa siyen nagari maida kudi gida.


Jameey❣️

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA BIYAR

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shidar biyan ki ta wannan layin 08160508316.

"Allah yataimaki gimbiyar Zairana,zuciyata bazata taba samun nutsuwa ba idan ina ganin ki cikin damuwa bana samun sukuni a raina,kiyi hakuri uwar dakina banajin dadi kullun idan ina ganin bacin ranki"cewae Fadila ta karasa maganar tana sadda kanta kasa yayin da take ci gaba da dannawa uwar gijiyar ta kafafun ta a hankali."dole in shiga damuwa Fadila inajin daci raina duk abin da nikeso mahaifina bai mani shi,yanzun fa so nikeyi yabarni in tafi wajen Umma Rukayya ya hanani ga shi ya rabani da Umar ya zanyi da raina!"cikeda da tausayawa Fadila tayi kasa da muryarta cikim sanyi murya tace."Allah ya huci zuciyar ki,kidaina bata ranki akan wannan abun ina da yakini idan aka dawo daga gasa zai maido maki Umar l,nima kaina ina san in dinga ganki cikin farin ciki da walwala."ɗago jajayen idanuwan ta tayi da suka sauya launi tace."Fadila mi kika fahimta a tsakanina da Umar."? Bakaramin faduwar gaba ya riski Fadila ba har saida ta dan dafe kirji sannan ta sadda kanta kasa da sauri zuciyar ta na halbawa da sauri da sauri shiru tayi ta zurma cikin tunani( wannan amsar a bayyane take,uwar ɗakina ta afka tarkon son Umar!saidai bakina yayi kadan ya furta wannan kalamar kamar gimbiya Zubaina ta afka son BAWA saidai na fahinci har yanzun bata fahimci son sa take ba saboda tarin kuruciya irin tata sa wauta,natabbata idan wannan maganar ta fita daga bakina tabbas sai Sarki Abdurrahan yasa an sokeni lallai kam bazaki taba jin mutuwar Sarki a bakina ba dama.ance bakin wawa akejin zance)ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta dago idanunta ta aza akan Zubaina har yanzun ita take kallo alamun ansarta take bukata."Allah yakara maki lafiya da nisan kwana,ba wani abu ke tsakanin ki da Umar ba, sai tarin tausayin da kuma tarin kwarjinin shi da haibar shi su suka taru a cikin ranki zuciyar data shagala da yawan bege da dinbin tausayin Umar a koda yaushe."itama ajiyar zuciyar ta fesar tace."hakane Fadila ban da tausayi mi gimbiya Zubaina zatayi da BAWA? duk da wani lokacin raina na rayamani kamar zuciya tayi nisa a cikin kaunar Umar saidai kullun sai na karyata kaina,musamman ma yau da kika kara tabbatar man da taysayin shi nikeyi kuma na kara gasgata hakan"Allah yataimakeki uwar gijiya ta lallai dole ayima Umar san barka da Allah yasa shi a cikin ranki a matsayin shi bawanki wan da yafi kowa daraja a wajen ki"Fadila kenan, ke ke yima Umar kallan BAWa,zuwa yanzun ina kallan Umar kamar ɗan uwana yafi karfin bawa a wajena....lallai kam!narasa dalilin dayasa Umar yasamu masauki mai dinbin daraja a wajena,ace kamar ni gimbiyar Zairana na damu da Umar abin takaicin bawa ne shifa?wannan shine abinda ban taba yima wani ɗa namiji ba a rayuwata ta duniya"wannan haka yake ranki shidade amma karki damu in Allah ya yarda Umar zai dawo a karkashin ikon ki, a karo na biyu"Allah yasa Fadila."Amin."inasan ki shirya yau zan kaima Hajia ziyara sannan ina son zan kewaya lambu dan in mike kafafuna."angama ranki shidade,Allah yataimaki gimbiyarZairana."
________________
"Ku shiga ku fiddo mani shi!har ya isa in saka doka ya karyaman ita a matsayina na Sarkin Burhaan."baki daya dogarawan suka afka cikin sashen waziri Abdullahi da sauri gimbiya Sa'adatu ta shiga tsakanin su da ɗanta tana kuka tana basu hakuri amma saboda rashin imani irin na hamza sawa yayi akai wurgi da ita,Turaki yana ji yana gani mahaifiyar sa ta buge kai da bango jini na zuba,baki daga kattin Allah ta'ala sun kama shi kam....karar da gimbiya Sa'adatu ta saki ce yasa Abdullahi fitowa da gudu tun daga turakar sa yayi wajen iyalinsa daga shi sai doguwar jallabiya fara, tsaye yayi tsabar mamaki da al'ajabi yanama Hamza kallan mamaki,sai lokacin yayi kan matar shi ya dagata yakira baiwarta takaita cikin daki,dan ta bata kulawa.....
"kai kuna da hankali zaku kama mani ɗa?ku sakarmin da'na."baki dayan su sukayi shiru suna gudun kada su sake shi su fada cikin tarko da kalar zaluncin irin Hamza,koba komai sun san Abdullahi yafi shi saukin hali"Bakuji abinda nace maku ba ku sakarman da'na tun kafin dare yai maku."koda suka ga Hamza baiyi magana ba sai suka sake shi,yayin da ya watsa masu wata irin matsiyaciyar hararar da yasa suka sake kama Turaki,sannan yai masu nuni da ido suka fita da shi.
Abdullahi na kawo karfi zai riko Turaki,yasa Darwami ya rike shi zagaye Abdullahi yafara cikin kaskanci yace."Haba ɗan kanina mi kake kokarin yi haka?hmm na fahimci baka san wasa da wuta ba dadi ba! akan d'anka kake tada jijiyoyin wuya? ashe kasan dadin sa?hmm Garkuwan Burhaan kenan,ka saurareni da kunnen basira walahi tallahi koda Barde ne ya juyaman baya abun da zansa ayi masa kenan koma fiye da haka,amma shine kaje da kafafunka ka kwance shi ko?kaima ga ɗa,kai kasan baccin darajar muna ciki daya da kai kayi kadan Hamza yasa doka ka karya man?" a fusace yayi maganar."Damuwar ka ce Hamza baka isa ka kashemin da'na ba duk abinda zakayi nayi maka kawaici amma baka gani kalli yanda kamaida mani ɗa kamar marar galihu ba wani cikakken karfi a tare dashi duk yabi ya lalace,kai kasan ni bazan iya yima ya'yanka haka ba,kamanta duk tashi fadin da a kadinga yi akan Barde dani akeyi shi amma abanza yanzun ni zakaima haka?da'na tilo tal so kake in rasa shi kenan?duk wulakanta iyalina da zanyi ina son su!kuma dakasa akayi jifa da matata har kanta ya fashe kaji tsoron Allah Hamza,ina kaunar ta a haka walahi na gaya maki kayi gaggawar dawoman da da'na tunkan makiya suyi mamu dariya a cikin Masarautar nan."Hahhahh,Abdullahi kena lallai kam kayi kyan kai hmm kajini da kyau ni bazan iya wannan sakarcin ba ina magana kana yiba a gaban kaskantattun mutane,idan hakan ya dameka kasa meni sashe na."yasa kai ya fita shiko Abdullahi ya daukar ma ransa akan ɗansa saidai kowa ya rasa ransa,dan bazai iya jurar wulakan ta ɗansa da akeyi ba,shida man tuni ya sare da lamarin dan uwan shi yaaa azzalumi ne kansa kawai yasani......

koda ta shiga sashen shi bata iske kowa ba wani bakin magani ne ta ciro a zanin ta ta zuba cikin furar Hamza ta motse ta sannan tabi ta hanyar baya ta fita ba wanda ya ganta,bayan ta fita bada jimawa ba ya dawo duk ransa a bace,ace war shi dan uwan shi yaimashi rashin kunya akan ɗansa yana zama sabuwar Jakadiyar daya dauka ta shigo ta bashi furar shi bayan ta fita har zai sha sai ya aje ya sake fita a har zuke ya nufi sashen Umman shi, yafada mata abun da Abdullahi yai mashi har dare baidawo ba hakan yasa Jakadiya ta dauki kwaryar fura taba wasu bayi tace su shanye gudun kar tayi tsami,tunda gimbiya Masau'da ta koma sashen take murna dan dama bokanta yace da Hamza yasha furar take zai mutu amman har kusan mangariba shiru ba wani labari har akai sallar isha'i hakan yasa ta shirya da kanta ta tafi sashen gimbiya Saude dan tasan zata samu wani labarin ko yaya yake.....
★★★
suna gama gwajin karshe Ammar yakara yimasu fatan alkhairi sannan suka fidda mutun sha biyar wa'anda za'ayi gasar dasu suna suka zama zakarun gwajin dafi a Masarautar dasu za'a tafi Sirika sai sarkin bayi da Umar sai kuma Idris da kananun bayi guda goma,yau takama saura kwana biyu ayi tafiyar Yarima Ammar ya umurci kowa ya fara shiri kafin lokaci.....

Ki hanzar shiga cikin jerin da zasu kasance a cikin wannan tafiyar domin ta musamman Sadaukin Burhaan kenan cigaban izzah ko mulki.

"Umar ina so daga z gobe ka hado kayan tafiyar ka kadawo sashena kana cikin yan tawagata,kuma koda munje can ka kasance a cikin Jarumai Kamar yanda Mai martaba ya bukata."Allah yataimake ka ina godiya Allah yasaka da alkhairi"kafi karfin haka a wajena ina san in tambaye ka abubuwa masu matukar mahimmanci da amfani idan mundawo Sirika"Allah yakaimu ranka shidade."Amin."suna cikin magana sai ga dan aike daga Sarki Abdurrahman,bayan anyi mashi iso yafadama Yarima Ammar sakon Mai martaba...tare da Umar suka fito ya nufi bangaren Mai martaba
yana isa yayi sallama suka amsa mashi Yarima Aryan ne kadai sai Sarki Abdurrahman bayan ya zauna yakai gaisuwa wajen Mai martaba sannan ya samu waje ya zauna"dan shiru ne ya biyo baya na yan dakikai kafin Sarki Abdurrahman yace."nasa akira mani ku domin insan dami dami kuke bukata, dan gane da kayan da zaku tafi dasu,ku fadi duk abinda kukasan Jaruman ku zasu nema."? "Allah yataimakeka muna bukatar dawakai masu nagarta da aminci kamar guda talatin saboda muna da Jarumai guda sha biyar sai manyan bayi guda biyar sannan mun hada da bayi goma wa'anda zasu kara taimaka mana a cikin wannan tafiyar, kuma mun ware mutane biyar da za'ayi wasan takobi dasu daga ciki akwai Aryan sai ni,akwai Mansur da Yazid sai kuma Lukman,duk da kasancewa akwai Sarkin yaki a cikin tafiyar."Masha Allah,madallah da samum jajirtattun ya'ya kamar ku."godiya muke ranka shidade mun gama shirya komai lokaci kawai muke jira."Naji dadin aikin ku komai na tafiya yanda ya kamata kun birgeni,sannan ba abinda zaku bukata musamman kayan guzuri"Eh ranka shidade munsa sun hada kayan su cikin shiri,komai mun tanada kafin zuwan lokaci"da kyau Aryan"ina so a dubma ya'ta a cikin dawakan ta a zabi wanda yafi kowa ne lafiya da nagarta daga nan ku kara ware dawakai hudu wa'anda za'a hada Zubaina dasu a matsayin masu kulawa da al'amuran ta."angama ranka shidade."daga karshe zamu tafi da Shamaki sai kuma Waziri na akwai maji dadi sai kuma Garkuwan Zairana kunga duk dani muna bukatar dawakai biyar kenan daman kowa nada nashi kunga jimlar dawakan mu sun kama guds arba'in kenan.bayin mu sun kama guda sha biyar sai dawakan jarumai sun kama suma sha biyar sai tawaga ta data Zubaina munkama mu goma duka sun kama arba'in cif daga karshe ina san ku kara jajirce lwa kamar yanda kuka saba Allah yai maku albarka"Amin,Allah yakara girma da ɗaukaka."gobe idan Allah yakaimu zan zauna da Sarkin taska sai Majidadi da Sarkin yaki dan musan me zamu bukata har muje mu dawo batareda mun samu wata damuwa ba....duk da nasan Sarki Abdullatib zaiyi iyakar kokarin shi amman bana san nauyi yai mashi yawa."Allah yaja da ran Sarki hakan ya kamata muyi...Allah ya karramaka lafiya."Amin."
ranar yini sukayi suna fira da mahaifin su rabi da kwata duk akan yanda zasu tsara tafiyar su Sirika sukeyi.yana jin dadi aransa sannan yana alfahari da ya'yan sa......

Washe gari Umar keta fama hada yan kayayyakin shi cikin wata bakar jikka ta Abba Ado yana gama hadawa yayi sallama da Abban shi
"To Ummaru sai ka kara kula sannan ka kasance mai ɗa'a kaji."To Abba zan kiyaye da izinin Allah."da haka ya tafi wajen Yarima Ammar koda ya isa mai tsaron sashen ya tsayar da Umar yana shi shiga ya kai wajen awa biyu sannan yabar shi ya shiga ciki bawansa yai mashi sallama da Ammar bayan minti goma ya fito yace Umar ya shiga yana shiga karamin falon shi ya zauna kasa yana kallan tsaruwar da haduwar da falan yayi bai jima da zama ba Yarima Ammar ya shigo...Sadauki ya gaishe shi cikeda ladabi,fuska sake ya amsa cikin jin dadi,"Umar har kagama shiryawa"eh ranka shidade, gama kayana nan"toh Umar sannu da kokari ina so ka kara jajircewa kaji bani ba kowa na san Jarumtar ka da kuma jajircewar ka kada kaga na damu inyi tafiya da kai nasan zaka samu daukaka sannan zaka zama mutun mai kima da daraja a cikin Zairana, ldaga lokacin da Jarumtar ka da hazakar ka suka bayyana a bainar Jama'a."in sha Allahu zan kokarta."Umar mahaifin mu yana son Jarumai kuma duk wanda yasan labarinsa yasan shi din Jarumi ne,bai kasance daga cikin raggaye ba, shiyasa yake ba Jarumai muhimmanci a rayuwar shi,tunda yaga kokarin ka a ranar daka amsarma Aryan wasa,wannan ne yasa yace atafi dakai Sirika sannan ka kara kulawa da Jarumai saboda idan aka saka sauran yan uwanka bayi zasu ga kamar ba'ayi masu adalci ba shiyasa kaga munce maka ka kara kula da yanda muka gabatar da wasannin mu saboda tsaron lalura Allah yabamu sa'a." "Amin...da izinin Allah bazaka taba samun damuwa da niba duk abinda kukayi agabana Umar ya kiyaye shi"Allah yakara maka basira Umar." "Amin....Umar na godiya da nuna min karamci,Allah yakara maka girma.....
_____________
Ɗan aiken gimbiya Masau'da ya dawo,koda ya iso bakin Masarautar Srkin kofa ya tare shi dama Hamza ya bada doka karya kuskura yabari wani ya shigo cikin Masarautar koda kuwa dan Masarautar ne."Kai tsaremin shi yanzun zan dawo."angama." yasa wani bawa ya tsare shi,sai da yabari ya tashi dan kewa yawa ya fakaici idan bawan nan ya boye asirran da aka bashi kalkashin wani ganye mai duhu ba wanda ya gan shi Sarkin kofa ne yazo tareda Darwami yana zuwa ya tisa keyar shi yakai shi gaban Hamza cikin fa'da.
kallan da Hamza ya aikama wanann bawan saida yasa hantar shi ta kada tsabar tsorata."na tuba ranka shidade kaimin rai walahi bansan an hana shigowa ba, ka ga farceni."tun kan ya rufe bakinsa take Darwami ya ballawa bawan nan wani irin masifaffan mari mai rudarwa."kai harka isa kacema Mai Martaba ya hana shiga,daga ina kake bayan ba wanda yasan da fitarka,dama an rabu da ganin ka a cikin Masarautar nan"jikin Yautai ya hau mazari ya rasa abinda zai ce yasan dai kashin shi ya bushe musamman idan Hamza yaji gimbiya Masa'uda ce ta aike shi shiyasa aka rabu da ganinsa sake falla mashi mari Darwami yayi yace."ba dakai ake ba."tsoro da firgici suka rufe shi ya dago fuskar sa data suntume ya sake duban Hamza a karo na biyu ya sake sunkuyar da kanshi zuciyar na bugu da karfi ya.....


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA SHIDDA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.kituro shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316.

"Allah yataimaki Sarkin Burhaan ina nan ba inda naje walahi."Kai kafada mana gaskia idan Sarki ya gano kayi masa karya sai yasa an soke ka da mashi."Darwami yayi maganar a matukar tsawace har saida Yautai ya girgiza fuskokin su kadai ya kalla ya fahimci gaskiar abunda suke fada komai zasu iya yi mashi yace."Allah kuwa ba inda naje amma yau da safe na taje na ansoma gimbiya Masa'uda sako."Sakon mi."? Ranka shidade munyi rahin sa'a da rashin da cewa wanda zai bani sakon bai nan sai dai nadawo hannu biyu."dama nasan ba wanda ya aike ka daya wuce wannan makirar matar Masa'uda karya kakeyi ina ta aikeka."?sai.a lokacin Hamza ya tambaye shi."Iya kar gaskia ta kenan ranka shidade walahi ban anso sakon ba."Darwami." Allah yakara maka girma da daukaka."bai jira wata wata ba ya fara zanar bawan nan da bulala har saida yayi mashi

Please Login or Register in order to submit comment