Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

manyan bayin Masarautu daban daban na karawa wajen siyen shi ta dalilin uwar dakin shi Zubaina aka sawo shi mafarin zuwan shi kenan wannan Masarautar mai albarka"Abdussalam kenan wannan shi kadai ne asalin Umar."?
"Allah yataimake ka kamar yanda yazo a Bawan sa mu dauke shi a haka,tunda rabin bayin Masarautar nan suma a haka aka sawo su kuma bamu damu da sanin asalin su ba"kwarai kuwa kanina amma ai bana tunanin wannan yaron ainahin bawa ne shi." "nima haka yaya nayi wannan tunanin kamar yanda nace zamu amshe shi a cikakken bawan sa a yanda yazo mana kuma mai mamu hidima kamar kowa."Shikenan haka za'ayi."wani irin ajiyar zuciya Zubaina ta sauke sirrance tana kara godema Allah..."Allah yataimake ka ina neman izinin magana"injinka Ammar "kamar yanda muka sani Umar bawa ne amma bai dace da hidimar yau da kullun ba, saboda Allah ya bashi karfin hali da jajircewa shiyasa muke neman alfarma a wajen ka da abamu shi ya kasance a cikin jerin jaruman mu zamu bashi gwaji na musamman"Ammar kenan kasani ba Bawa ba jarumta, bawa bawane kubar shi a matsayin bawan shi saidai zaku iya tafiya dashi dan yai maku hidima"Ranka shidade kataimaka mana ka barshi a cikin Jaruman mu"Aryan karka kuskura inkara jin maganar Umar anan wajen...kamar yanda nace za'aje dashi Sirika amma a matsyin mai kula da Jarumai "ranka shidade kana ganin hakan ya dace."? "Kwarai kuwa Abdussalamu"shikenan."

"daga karshe ina son kowa ya shaida ban laminta Umar ya zauna da ya'ta Zubaina ba,amatsayin hadimin ta ba.....namiji bai dace da yiwa ya'ta hidima ba sai dai yan uwan ta mata kamar yanda al'adarta take akan Umar ba za'a fara ba,shima bawa ne kamar kowa"baki daya numfashin Zubaina neman daukewa yake kanta yafara sara mata....."Ranka shidade wanki kadai yake mani kuma shidin jajirtacce ne"ni Abdurrahman Abubakar daga yau na haramta maki shi bare har yayi maki wata hidima, zansa a shiga cikim sansanin bayi jakadiya taje ta debo maki bayi mata matasa masu jiki a jiki kiyi yanda kikeso dasu amma banda Umar bake ba shi.....kusani bawa namiji bai isa yazama hadimin ta Ya'ta ba"Abba dan Allah kabarman Umar yaimani hidima ina so....kallan da gimbiya Amina taimata yasata hadeye yawun bakin mai tsananin daci....."Mamana Kenan yaushe kikasan dadin aikin namiji da har zaki dinga hadani da Allah duk akan Umar?....lallai kam indai ni din mahaifin ki nedaga jinina kike ba Umar ba zama hadimin ki.....ku kuma Ammar na aminta Umar ya dinga kula da bukatun jaruman ku sannan dashi zamu tafi Sirika dafatan kun fahimta"eh ranka shidade Allah yakara girma mungode"ba laifi....mamana kinji me nace maki."? "Eh Abba naji"
"Da kyau haka nike so zaku iya tafiya"Allah yakara maka lafiya kuta shi cikin aminci "Amin."
Suma matan shi basu jima sukai masu sallama kowa yakama gaban shi suka bar shi shida ɗan uwan shi,suka ci gaba firar su.

Sadaukin Burhaan na kudi ne ki hanzarta kibiya domin jin dadin karatu yar uwa shafin karshe ya kare daga wannan siyen nagari maida kudi gida.

Koda gimbiya Zubaina ta koma daki tana shiga ta fada saman gado sai uban kuka takeyi kamar ranta zai bar gangar jikin ta ga uban ciwon kai daya turniketa jitake baki daya Masarautar ta fita a ranta...."na bani ni Zubaina mike shirin faruwa da nine?miyasa Abba bai san abunda nike so a rayuwa? a haka yake nuna yafi sona yanzun ma hadimin nawa dana zaba dakaina shine zaice bai yarda ya zauna a tareda ni ba😭 meyasa na koyawa ma kaina sabo da Umar! nabani ni Zubaina ya zanyi da rayuwa ta!."
koda Fadila taga shigar uwar dakinta a gigice ta biyo bayan ta ko magana bata ji idonta ya gama rufewa kuka kawai takeyi duk ta fita hayyacin ta ko da akace za'a aura mata Yusoup Shehu bata shiga damuwa ba kamar wannan lokacin ba, dukawa tayi ta fara ba Zubaina hakuri sai a lokacin Zubaina taji sautin maganar ta...."ubanwa ya baki damar shigomin cikin daki na ni sa'ar kice."?baki daya jikin Fadila yahau bari."Allah ya huci zuciyar ki Fadila ce" "ki uwar Fadila ce! fitarmin daga daki karna sake ganin kowa a sashena kinaji na."? "Eh...kihuta lafiya."da sauri ta fita har yan hanjinta ke kadawa tana zuwa babban falo duk ta sallami bayi tace sai an neme su,suma daman duk sun tsorata da yanayin da suka ga Zubaina daman ko gaishe ta basuyi ba gudun kar su shiga cikin bala'i.....kowa ya kama gaban shi itakuma Fadila ta koma dakin ta duk a cikin sashen gimbiya Zubaina.....
Ranar Zubaina kuka take yi kamar ta mutu ko falo bata kara fitowa tana cikin daki sallah kadai take tashi tayi,wannan kenan.....

Anan nakawo karshen shafukan Kyautan wannan littafi na Sadaukin Burhaan yar uwa bazan ce komai ba saboda kinji nasa salon kamar yanda kikaji na Izzah ko Mulki ba'ayi komai ba domin yanzun wasan ya soma ya wannan katamurmurar zata wakana? Bazaki samu wannan ba sai kin mallaki naki akan farashi mai sauki da arha naira 300 ta Acct no 0777512438,Access Bank,Jamila Abubakar Bello shidar biyanki ta wannan number 08160508316.idan kika bari akayi babu ke ansha da rabon tafiya ta daban ce siyen nagari maida kudi gida.


JAMILA JAMEEY.
(Yar Mutan Kankia)



Share
Saboda Allah.

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA BIYU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shidar biyanki ta wannan number 08160508316.

*Assalamu alaikum yan uwa ina fatan kowa yana lafiya,jiya nayi posting last free page saida na duba nagani mistake nayi ba nan nayi niyar tsayawa ba ga cigaban free pages nan.*

_Ina kara jinjina ga masoya yanda kukayi payment na book din nan Allah yabar so da kauna ina maku albishir da_
_mungama free pages zamu cigaba da posting paid pages son so nike maku irin billions din nan._
A bangaren gimbiya Bilkisu,baki daya matan sa suka hadu sai al'ajabin lamarin mijin su sukeyi saidai sun rasa dalilin sa na yin hakan....saboda tunda suke dashi ba bawan da aka taba siyowa yace bai aminta dashi ba sai UMAR sun san dole akwai babban dalilin dayasa aikata hakan...."Umman Aryan ina mamakin lamarin Mai martaba abinda ya akaita yau ya firgitani sosai saboda ance za'a saka Umar cikin jarumai ya hana abin da yafi bani mamaki yaron nan akwai shi da Jarumta gashi yanada jajircewa lamarin yaron nan kamar ba bawa ba,saboda yana da nagarta."ajiyar zuciya gimbiya Aminatu ta aje tace."Bilkisu kenan,ni kaina lamarin mai martaba yana tsorata ni"gaskia ne ranki shidade....ni kaina Umar ya kwanta min arai ga sanin darajar manya idan yana wani abun kamar wani ɗan basarake"fatan mu dai Allah yasa haka yafi zama alkhairi."Amin."cewar gimbiya Rukayya....."abinda ya kara daure min kai yanda ya raba Umar da Zubaina yarinyar nan tana jin dadin yanda yake mata hidima."kada kice haka Rukayya ni hakan ma yai mani daman kyau ace taci gaba da zama da hadimai mata yan uwan ta hakan kamar zaifi "Gaskia ne shine kimarta ma."Allah yai mana jagoranci."Amin."da haka sukaci gaba da tattaunawa rabi duk akan lamarin mijin su ne.

Ba abinda Sadauki keyi faman shara tare da bayi sai aiki sukeyi kowa da kalar abinda yakeyi daga wani bangaren kuma bayi ne aketa bugu dagani dai akwai abinda sukayi....wani bawa ne yazo kiran Sadauki suka tafi tare dashi har bangaren Yarima Aryan a can suka iske Yarima Ammar koda bawan nan yakai shi fita yayi ya bar su.
Izinin zama sukayi mashi ya zauna cike da ladabi sannan ya gaishe su cikin girmamawa."yauwa Umar barka...daga ina kake."? ɗan sadda kansa yayi kasa kadan yace."daga wajen aiki nike sai ga kiranku ya sameni"gyada kansa Ammar yayi yace."daman dalilin kiran da akai maka muna son mu sanar dakai cewa da ance za'a saka cikin Jaruman mu saidai duba da yanda mukeda yawan Jarumai shine Mai martaba yace zaka kasance mai ba jarumai kulawa tunda kanata jarumta da jajircewa." a hankali Sadauki ya dago kansa ya kalli Yarima Ammar yace."nagode Allah yakara girma duk abinda kukace haka za'ayi zabin ku shine nawa"bakomai Umar,sannan zaka shirya a watan gobe zamuje dakai wajen gasar da za'a gabatar a Kasar Sirika sai ka kara kulawa da al'amuran Jaruman mu sannan daga yanzun da kai zamu dinga zuwa wajen gwaji yana da kyau duk abinda zamu dinga aiwatar wa sai kadinga kulawa da kyau saboda bukatar hakan idan ta taso"in sha Allahu zan kula da kyau Umar godiya mai tarin yawa banda bakin da zan gode maku Allah ya saka da alkhairi."yima kai ne Umar....Mai martaba yace zaka daina yima Gimbiya Zubaina aiki zaka tsaya tareda Jarumai kana basu kulawa...komai kenan idan mun dawo zamu san abinda yakamata ka dinga yi."Shikenan Allah yakaimu lokaci lafiya."

_WASHE GARI_
Jarumai ne saman dawakai sai uban gudu sukeyi suna kaiwa wajen wata tuta sai bada gwaji akeyi abin gwanin ban shi'awa Umar ne zaune hannun shi ɗauke da kaya sai fiffita yake yima manyan Jarumai yana basu ruwa ranar yini sukayi suna rali anata tantance gwanayan da zasuyi wasan duk abinda sukeyi Umar na ganu kuma yana hardacewa cikin kan shi,saidai duk lokacin da zai ga suna gudu saman dawakai ji yake kanshi kamar zai rabe biyu tsabar yanda yakejin juwa na dibarsa baki daya yarasa abinda ke mike mashi dadi a rayuwar shi ta duniya.....
koda Ammar ya fahimci halin da Umar yake ciki da sauri ya karaso inda yake ya dafa kafadar shi yace."Umar mike damun ka."? "Kaina ke mani ciwo."sannu kaje gida ka huta."gyada kansa yayi sannan yai mashi godiya ya tafi ji yake kamar kanshi zai fadi ƙasa da kyal yasamu ya isa gida ya kwanta ba abinda yake gani idan ya rufe idanun shi sai sukuwar dawakai anata wasa saidai ya kasa gane su waye akan dowakan sai uban ihu da mutane sukeyi baisan sadda bacci ya dauke shi ba.....

Bayan kwana biyu gimbiya Zubaina ce zaune cikin kayan buzaye sai uban kuka takeyi kwana biyun da tayi bata ga Umar ba jitake kamar ta shekara bata gan shi ba,banda aikin kuka ba abinda takeyi duk ta rame tayi duhu,ta maida kuka kamar ibada kwantawa tayi taci gaba da rera kukan ta marar sauti.
Fadila ta shigo wajen uwar gijiyar ta gabanta ta duka tace."Allah yataimake ki uwar ɗakina kasancewar ki cikin wannan yanayin yana daga min hankali damuwa bata kamata da ke ba Allah yataimaki gimbiyar Zairana."a hankali ta ɗago kanta ta dallama Fadila uwar hararar wadda tasa Fadila saurin mikewa jikinta na rawa ta fita kai tsaye wajen Yarima Ammar ta nufa,iso hadimar sa tayi mata tana zuwa ta zube kasa takai gaisuwa sannan tace."Allah yataimake ka halin da uwar ɗakina ke ciki ya daga mani hankali ainun taki ci taki sha bansan ko zata iya sanar maka damuwar ta ba."ita Zubainar? ke cikin hali?muje inji abinda ke damunka."toh ranka shidade."gaba yayi tabiyo sa baya suna isa ya shiga wajen Zubainar har yanzun tana aikin kukan ta duk sallamar da yayi bataji sa ba har ya isa inda take ya zauna gefen ta, ba tai aune ba taji ya dafa kafadar ta cikin sanyin murya sa son kwantarwa kanwar tasa da hankali yace"Mike damunki kike kuka."?da sauri rungume shi taci gaba da kukan da takeyi marar sauti rarrashin ta yaci gaba dayi har saida tayi."fadamin mike damun ki."bansan ya zanyi ba Yaya,yanzun Mai martaba ya rabani da Umar har abada."kalaman ta suka sauka cikin dodon kunnen sa zuwa zuciyar sa har saida ya rabata da jikin shi yana kare mata kallo yana so ya gasgata lamarin ra abinda take fada daga iya bakin tane kadai ko har cikin zuciyar ta ne ba kadan yayi mamakin jin abinda kanwar tashi ke fada ba."akan Umar zaki zauna kina kuka?haba kanwata yanzun kamar ke kina gimbiyar Zairana zaki dinga kuka akan namiji?haba kanwata kece fa gimbiya Zubaina wadda sunan ta ya karade ko ina har ake takara a kanki shine zaki dinga kuka dan an rabaki da Umar."?
"Ina san Umar yaci gaba da yimin hidima kamar yanda nasa aka siyoman shi kaima kasan inason mutun jajirtacce mai jajircewa shiyasa nike kaunar Umar."banda kallan mamaki ba abinsa yakema Gimbiya Zubaina baki daya ya kasa gane kurman zancen da takeyi masa."ban fahimce kiba Zubaina."ina son yaxi gaba da zama a kalkashin ikona."Haba kanwata,kidaina wannan maganar tunsa Mai martaba yace bai bukatar ganin Umar a matsayin hadimin ki kema ki hakura,idan hadimai kike so akwai kala kala sai kin zaba."Nasani Ya Ammar kaima kasani bantaba nuna ina son bawa yai mani hidima ba sai akan Umar."Naji minene dalilin ki na son Umar yai maki hidima."? "Saboda shidin Jarumi ne kuma gwarzo."ajiyar zuciya ya shida a hankali sannan ya riko hannayen ta yace."Tabbas Umar jarumi ne na gaske saidai ya dace ki hakura dashi kamar yanda Sarki ya bukata,sannan zamu aje shi dan kulawa da jarumai kinji."? Itama ajiyar zuciyar ta sauke tace."shikenan,idan kuka gama gasar zaku dawo min dashi."? gyada kansa yayi yace"zamu duba yuyuwar hakan keman kinsan Mai martana bai sauya magana ian har yayi ta ki daure ki sadaukar da Umar ga Masarautar kodan farin cikn Mai martaba."toh yaya na yanda kace haka za'ayi."ina alfahari da ke kin kyauta haka nike so."murmushi ta sakar masa ya jima yana kara kwantarwa kawar tasa da hankali kafin yai mata sallama ya tafi.....

_MASARAUTAR SIRIKA_

"Zaki iya zuwa ki sanar mashi bani da lokacin ganawa dashi,idan yaga dama ya dawo zuwa gobe sannan kadda ki kuskura ki bari kowa yakara shigowa sashe na har sai zuwa gobe kema idan kin kai sakon zaki iya tafiya sai gobe kidawo ki sanar da mai kula da ficen sashena kada yabar kowa ya shigo kodakuwa dan gida ne yazo neman ganawa dani kice mashi ni gimbiya Rahama bani da lokacin ganawa da kowa sai gobe in Allah yakaimu ina fatan kin fahimta? sake rankwafar da kanta tayi kasa tace"Allah yakara maki girma da daukaka na kiyaye komai umurnin ki shine abin tinkaho na yanda kikace haka za'ayi." "dolen ki kiyi biyayya Murjanatu."

(Allah sarki rayuwa.....gimbiya Rahama kenan,mai takama da gadara gamida tsantsar izza mulki wadda take takama da usuli 'ya daya tilo ga Sarkin Sirika ya dauki son duniya ya daura mata bai hadata da kowa ba yar da zai iya komai akan ta)
Tana gama fadar haka takoma ta kwanta saman gado tare da yin doguwar mika taja bargon ta mai tsananin laushi ta lullube jikinta ta rufe idanuwan ta kamar mai bacci.

Sarki Abdullatib ne tareda Shamaki suna tafiya a tsanake sai dogarawa dake take masa baya kai tsaye sashen yarsa ya nufa duk inda zai wuce hadimai da sauran bayi keta kawo gaisuwa har ya isa sashen gimbiya Rahama yana shiga ya tadda mai kula da ita da sauri ta zube kasa ta gaishe shi."Allah yataimakeka gimbiyar tayi bacci bari in mata magana."Aa rabu da ita ta huta da kyau kikara kulaman da ita."angama ranka sgidade."harya juya zai tafi ya waigo yace."idan ta tashi kice mata ina san ganinta sashena."angama ranka shidade."nan suka juya suka tafi tareda tawagar shi.
Duk abin da sukeyi gimbiya Rahama najin su kamar jira takeyi mahafinta ya fita ta kwallawa Murjanatu kira,jikin ta na rawa ta isa gabanta ta zube."ranki shidade gani."dauketa tayi da mari har saida ta rike kuncin ta tace."tuba nike,ranki shidade Allah yakara maki nasara kimin aikin gafara."Yimin shiru haka nace maki kifada? bana ce maki kice ban bukatar ganawa da kowa ba sai gobe."? "Allah ya huci zuciyar ki bakina yayi kadan ya furtawa Mai martaba kalmar nan ba"Maimartaban ubanki ne ko uba na."? "Allah yakara maki yawan rai mahaifin ki ne."Mtsw aikin banza aikin wofi dama danshi nake bada wannan sakon nasan zai isa kunnen sa,amma saboda ke dakikiya ce shine kika bata mani shiri"tuba nike bansan haka kike nufiba Allah ta huci zuciyar ki"aikin banza sama ba gane abubuwa kike ba,bacemin da gani, tunkan ranki yai mugun baci."kitashi cikin aminci." "mtsw dubeki baiwa dake yar wahala."
A sanyaye Murjanatu ta fita ta koma wajen aikin ta kamar yanda uwar dakin ta,ta bukata.
ba karamin bacin rai gimbiya Rahama ta shiga ba taso ace tafadama mahaifin ta sakon ta, tasan zai damu sannan zai kara daukar abinda take so da mahimmancin gaske,kuma tasan zai nema mata alfarma wajen Sarki Abduljalal,tasan zata dace da auren Yarima Sadauki, musamman yanda ta jima tana dakon son shi a rayuwar ta.....
_Tirkashi masoyan_ *daukar fansa* _kunji abinda gimbiya Rahama tace,tajima tana dakon son Sadauki 😂_
_________________
"Umar katashi haka nan, baccin mi kakayi kaga lokacin sallah yayi,anya lafiyar ka ƙalau kuwa."? A hankali yayi mika sannan ya zauna yana addu'a yace "Eh Abba,banjima da dawowa daga masallaci ba, ina wajen gwaji kawai naji kaina naiyi mani ciwo shine nadawo na kwanta."ya kakejin kan naka yanzun."da sauki,walahi dana rufe idanuna sai in dinga ganin dawakai da mutane akai suna ihu saidai bangane ko suwaye ba, kuma bana iya tuna komai."hmmm yaro man kanza, baka ganin kullin kana hudda da dawakai sai inga kila dan kuna gwajin nan ne shiuasa kake ganin dawakan." Girgiza kansa yayi yace "Aaa Abba basuyi kama da kalan dawakan Masarautar nan ba....."kaga da'na karka damu kanka ba wata matsala, mafarki ne kawai kuma kasan ba gaskia bane"Shikenan Abba, yau yarima Ammar ke fada mani Mai martaba ya hani yima Zubaina aiki, sannan yace bazan kasance daga cikin Jarumai ba,saidai in zama mai basu kulawa kuma dani za'aje Sirika."karka damu da'na hakan ma bakaramar daukaka bane a wajen ka idan munje ka dage akan aikin ka"Abba kaima da kai za'aje? "Kwara dagske kaga ni ne shugaban bayi"kace nima ɗan Sarkin bayi ne."? "Kwarai kuwa da'na ni ne Adamu Sarkin bayin Zairana lallai kan kaf nahiyar mu ba wanda baisan niba, shiysa kaga bani aikin komai kuma har bayi nayi mani hidima sannan banda shamaki da fa'da damu ake fadanci, sannan ba bawan da ban sani ba kaf Masarautar nan "Kai tab kana kokari Abba amma suna dayawan gaske"nasani rabi da kwatar su dakaina na siyosu wasu kuma anan aka haifesu kaga ai baza suyiman alaye ba, saidai ko naman ta sunan bawa"hakane Abba na Allah yatayaka riko." "Amin da'na"Allah yaimaka albarka"Amin Abbana."
______________
Waziri Basheer daure cikin rana ga uban dukan shi anayi kamar wani bawa ba abinda yakeyi sai salati yana gayawa Allah halin da yake ciki,duk irin azabar da Hamza ke gana mashi Basheer bai da niyar fadar inda zoben nan yake,sawa yayi bayi suka dauko kattin duwatsu suka azama mashi bisa kirji baki daya numfashn sahi ya dauke ga uwar rana anayi amma ba ko digon tausayi cikin zuciyar Hamza, hakan ya tafi ya barshi ko ajikin shi......
zuwa yanzun Sarki Abduljalal ko gane mutane baiyi,ba wanda ya damu da shi daga yan uwansa har Masa'uda ba wanda ke duba shi sai Saminu,halin da yaga Mai martaba ya shiga,bakaramin tashin hankali ya shiga ba,yana cikin alhinin halin da Mai martaba ke ciki sai ga gimbiya Sa'adatu ta shigo itama sai a boye take kawoma Saminu magani tace ajika a bashi idan Allah yayarda zai samu sauki.....
"Saminu ya jikin na shi."da sauki ranki shidade saidai bai cin komai."Allah Sarki komai yana da lokaci ga magani kaba shi yasha gobe zan aiko hadimata ta kawo maka magani ka jika saika shafa mashi a jiki."toh ranki shidade."ta dan jima kafin ta koma sashenta tana mai tsananin jin tausayin mai martaba a ranta.

Koda Masa'uda ta tashi da kanta ta aiki Talatu wajen bokanta zata anso mata sako a cikin gaggawa saida dare tafara sannan ta fita ta hanyar sirri ranar ko gezau Gimbiya Masa'uda ta kasa Allah Allah take Talatu taje ta dawo batare da ansamu matsala ba.....

A bangaren gimbiya Juwairiyyah ba abinda takeyi sai kuka tana kara yima mahaifin ta adduar samun lafiya,sannan a bangaren zuciyar cike take da begen dan uwanta fatan ta Allah ya maido shi gida lafiya sannan Allah ya dawo cikin hayyacin shi duk inda ya tsinci kanshi,baki daya hankalin ta nakan ahalin ta duk halin data tsinci kanta bai damunta tasan wuya bata kisa sai kwana sun kare.
`FA'Da`
Galadima hamza zaune saman karagar mulki sai busa iska yake yana nuna isa da tsantsar gadara yasa an kamo mashi Shamaki an gurfanar dashi cikin fa'da kamar wani katan barawo."Allah yataimakeka gashi mun kawo shi.
a dage yake kallan Shamaki kamar wani marar yanci,shiko yayi zugun kamar wani munafuki ranshi bakikkiri ganin irin cin fuskar da Hamza ke yi mashi tunawa yayi yaga su keda fa'da amma yau shine za'asa dogarawa su kamo shi a gaban bayin Burhaan lallai ko kadan hamza bai san kimaba"kai Ibrahim bada kai nike magana ba."? "Allah yataimake ka banji ba."minene dalilin dayasa ka daina zuwa fa'da."? "Ranka shidade banda cikakkiyar lafiya."Kataba ganin inda ake fa'da babu Shamaki."Allah yakara maka lafiya ba'a taba yiba kuma baza'a taba yiba"daga yau karka kuskura kara rashin zuwa fa'da koda zaka mutu sai kazo Fa'da kanajina"insha Allahu zan kiyaye."sannan ka maida hankali ka nemo duk kayan da kasan ana anfani dasu idan za'a nada Sarki,saboda sati mai zuwa nikeso ka tabbatar dani a matsayin Sarki Burhaan."ba Shamaki ba duk wanda ke fadar saida ya kalli Galadima Hamza cikeda mamaki."da yardar Allah zanyi iya kokarina kuma zan dauko komai ake bukata saidai dole saida zoben nan sannan zaka tabbata a Sarkin wannan Masarauta na dindin din."nafika sani kaidai kayi abinda na umurce ka"angama ranka shidade."daka kyauta ma kanka....zaka iya tafiya"nagode,Allah yakara girma da daukaka."
______________
"Barka da hutawa Abba"yauwa ya'ta,sannu da zuwa,taho wajen Abban ki mai kaunar ki."a hankali ta karaso kusa da mahaifin nata ta zauna"Abba na sakon ka ya same ni."hakane gimbiyar Sirika,dama ina san infada maki nan da sati biyu za'ayi wannan gasar shine nike san in fada maki ki shirya sosai yanda yaka mata ina son duk wanda yazo yasan cewa kece gimbiyar wannan Masarauta.sannan ina son kowa ya shaida ke cikakkiyar yar Sarkin Sirika ce wadda ta ansa sunan ta."shikenan ranka shidade zanyi iya yina kuma zaka yi farin ciki saidai ina fatan an gayyato yan Masarautar Burhaan nasan yarima Sadauki zai zo ko Abba."? "Ya'ta kenan an aika masu da takardar gayyata amman inasa ran zasu anshi gayyatar mu."Allah yasa Abbana."a hankali ya riko hannun ta yace."haba diyata mizai hana bazaki cire Sadauki a cikin zuciyar ki ba."da sauri ta mike tsaye tafara yan dire diren ta kamsr wata karamar yarinya tsabar shagwaba da sangarta"wayyo Abba nidai gaskia bazan iya hakuri da Sadauki ba kaima kasan shi nike son aure tun ba yau ba"ya isa naji,nasan bakisan cewa Sadauki yayi aure ba ko."? take numfashin gimbiya Rahama yafara sauyawa zuciyar ta tafara bugawa da sauri sa sauri batasan sadda ta fara kuka ba."haba Rahama ta,kukan me zakiyi hakan ba girman ki bane"ranka shidade kasan bazan iya zama da kishi ya ba."yanzun dai kitashi kije ki kwanta zuwa wani lokacin zan samo mana mafita kinji yar lelena"yanzun ranka shidade haka zaka zauna kana goyon bayan yarka akan abinda bazai yuyuwa ba kasan yarka ba aurenta yaron nan zaiyi ba saboda yagama samun wadda yake so yayi auren shi, daman fa bai san tanayi ba."
"Karki kuskura ki kara fadar wa'annan mugayen kalaman ga ya'ta"daga nafada maka gaskia Allah yabaka hakuri "bani bukatar gaskiar ki bacemin daga ni kada ranki yai mugun baci gimbiya Sadiya"Allah ya huci zuciyar ka"aikin banza aikin wofi."tana fita ya riko Rahama yace."kiyi hakuri kinji muddin Sadauki yazo wajen gasar nan dakaina zan gaya masa irin son da kike mashi"yauwa Abba na ina alfahari da kai."yimin dariya."dariyar tayi masa yaci gaba da kara mata kwarin gwiwa wannan kenan.....


_Yar Mutan Kankia ce❣️_



Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA UKKU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.Shaidar biyanki ta wannan namba 08160508316.

Dauke yake da kaya a hannun shi ya nufi sashen gimbiya Zubaina cikeda nutsuwa yake tafiya a kame kamar mai tausayin taka

Please Login or Register in order to submit comment