Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane ko Jaruman wa ne masarauta ne.
Su Yarima Ammar sai shiri sukeyi daka gansu kaga ya'yan Sarakai kowa yasha ado iya ado kamar ba gobe....suna cikin karyawa Umar ya shigo hannun shi dauke da Jarumai sannan kayan jikinsa irin na bayi ne ya saka amman bakaramin kyau sukayi masa ba fuskar shi dauke da annuri,cikeda girmamawa ya gaishe da iyayen gidan sa suka amsa cikin girmamawa."zo muci abinci Umar."ba Umar ba hatta Ammar saida yayi mamaki har da mamakin sa ya bayyana a saman fuskar shi."taso mana."ya sake maganar yana sakar mashi murmushi."na gode ranka shidade nako shi."yace shima yana yi masa murmushin wanda yakara bayyana tsantsar kyawun sa."tubarakallah." Yusuf ya furta a cikin zuciya,saida ta fito a fili."bansan ka da musu ba Umar kazo muci."cewar Ammar,zama yayi a nutse suka fara cin abinci duk wani motsin da Umar zaiyi akan idon Yusuf yana nazarinsa musamman yanda yaga yana gayunar abincin kamar bai son ci babban abinda ta fahimta a tatare dashi ba komai yake ci ba,baiyi aune ba yaga Umar din harya koshi yana shan ruwa yace mike"haba Umar kardai har ka koshi.?"eh ranka shidade" haba daga fara cin abici zaka ce ka koshi kodai ka takura ne."? "Aaa nagode."shidai mamakinsa yake yi miyasa komai nasa na daban ne saidai kace ba bawa ba,ya tabbata bacin wani dalilin ba yanda za'ayi ace bawa yaga kabaki na abinci irin wannan yace ya koshi batareda nuna wata zalama ba....sake maida dubansa yayi akan sa yace."naga ba komai kaci ba? "Allah yakara maka nasara,ba komai nike ci ba"kaga Yusuf,bakasan waye Umar ba ina ga shifa haka rayuwar shi take,tun banjin dadin kawaicin sa har na saba,kuma tunda yace maka ya koshi to ya koshin."shikenan."mikewa sukayi duk suka daura rigar saƙi saman kayan su...Umar yakara gyarama uban gidan shi kayan jikin shi sannan suka fita suna gaba yana bin bayan su,ba inda suka wuce sai wajen yan uwansu Jarumai sukaita gaisuwa suna gabatr ma juna junan su,atare suka dunguma suka nufi filin wasa abin gwanin ban shia'awa......
tana gama shiryawa cikin doguwar riga kalar bila tayi kyau ga gashin ta yasha gyara sai kyalli yakeyi Fadila ta daura maya Jar alqabba saita kara haskata daka ganta sai ka kara kallan kyawun ta,kamar dan ita aka kaga kayan ita kanta saida ta kuma kallan madubi tayi murmushi ita kanta tasan ta gaji da haduwa.
baki daya hankalin ta na kan Umar shi kadai take tunawa tasan yana can suna shiri yau dai zaisha wahala wajen kula da Jarumai hakanan ta tsinci kanta da mugun jin tausayin shi a cikin ranta.....itama Fadila rigace ta saka ruwan goro itama tayo kyau, sauran bayinta ma kayansu na bayin Masarautar su suka saka.
Tana shigowa ta fara feshe uwar gijiyar ta da turaruka tana gama shiryawa suka fita suka nufi dakin gimbiya Rahama,duk inda zasu wuce sai bayi sun kawo gaisuwa baki daya labarin zuwan Zubaina ya karade illahirin Masarautar ta Sirika duk inda suka wuce kallan su kawai akeyi anata gaishe ta...saidai mai hali dai baya barin halin shi saidai ya rage,ko kallo basu isheta ba yanda take taku cikeda izzah ga wata irin kasaita da gadara amsawa takeyi wani kuma ko kallansu batayi har suka isa sashen gimbiya Rahama.
Tana isa sashen gimbiya Rahama baki daya bayin dake tsaron sashen suka zube kasa suka kwashi gaisuwa kai tsaye ciki ta wuce tana taka kasa kamar bata so irin takon nan na kasaitattun mata masu aji wa'anda suka amsa sunan su,tun kafi Zubaina takai ga dakin gimbiya Rahama taji ana sanar da shigowarta har ta iso duk hadiman da ke sashen sukaita kai gaisuwa wajen gimbiya Zubaina,cikin wani makimancin falo tasamu ta zauna ta daura kafa daya bisa daya ta harde inda bayinta sukaci gaba da yimata fita,shirun da gimbiya Rahama taji Zubaina bata karaso cikin uwar daka ba hakan yasa tashi cikin ta fito falo iske tayi zaune ta harde ita kanta saida gabanta ya fadi yanda ta isketa ita kanta tasan Zubaina ta wuce da ajinta duk yanda take takama da kyau saidai Zubaina ta wuce da ita.....
murmushi suka sakarwa junan su sai lokacin ta isa wajen Zubaina tana zuwa suka rungume juna sannan takama hannun ta suka shiga cikin dakin ta,saman wata kujera Zubaina ta zauna...Murjanatu ta duka ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa ba yabo ba fallasa amma saika saurara sannan zakaji abin da tace,gimbiya Rahama tasa a kawo mata kayan motsa baki har Murjanatu zata tafi ta daga mata hannu alamun ta gode"haba kawata taya zakice bazakici ba"da kyal ta iya bude bakin ta tace."nayi kalaci"gaskia ban amince ba ko madara ce sai kin sha ba yanda za'ayi ace ki,ki kicin komai."bata karacewa komai ba hakan yaba Murjanatu damar kawo mata dafaffar madara ta duka ta mika mata takai sakan biyar kafin ta miko hannun ta karba.
mamaki ya gama kashe gimbiya Rahama yau ta hadu da wadda tafita nuna isa da gadara."lallai kam Zubaina."ta furta a zuciyar taci gaba da shiryawa Murjanatu ma taya har ta ida shiryawa itama tayi masifar kyau, ita kuma makubar doguwar riga ta saka sai ta daura alqabba ruwan zuma...."masha Allah kawata kinyi kyau."cewar Zubaina."godiya mai tarin yawa gimbiyar Zairana."sai a lokacin Zubaina ta sha madarar yar kadan sannan ta aje kofin.a tare suka fito suma suka nufi sashen Mai martaba....da ka gansu sai sun shiga ranka yanda suka hadu sai kace yan biyu...Rahama nashiga ta rungume mahaifin ita kuma Zubaina ta gaishe shi a nutse ya amsa yanajin Zubaina har cikin ranshi bada jimawa ba sauran Sarakuna suka fito suma suka gaishe su,Sarki Abdurrahman ya rike hannun yar shi sannan suka dunguma suka wuce katan filin wasan Sirika suna isowa kowa ya mike ga jerin kujeru nan na royal sun sha ado ta tsakiyar itce ta Sarki Abdullatib ya zauna,sai ta hannun damar shi Sarki Abdurrahman ne ya zauna,a bangaren haggun sa kuma Sarki Abdulmuminu ya zauna wato Sarkin Kesar haka sauran Sarakunan duk suka zauna gwanin birgewa......inda su gimbiya Zubaina da Rahama aka aje masu kujeru guda biyu wajen sy ya gaji da kayatuwa a nutse suka tafi wajen kowa ya zauna cike da izzah baki daya idanun mutane ya dawo wajen su kadai ake kallo lokacin da Zubaina zata zauna saida aka dage mata rigarta kadan sannan ta zauna a hankali,Fadila da murjanatu kowace ta tsaya bayan uwar dakin ta suna masu fita a hankali....tunda Yusuf yaga Zubaina take yakamu da sonta bai kasa a guiwa ba ya nuna Ammar ita yace."nakamu da son ta wacece ita."?Murmushi yayi."gimbiya Zubaina kenan."Zubaina dai wadda nikeda labarin ta."kwarai kuwa....gimbiyar Zairana kenan."kallan shi kawai yayi da mamaki ashe kanwar shi ce daman yanada labarin ta yama san ba zata so shi ba ganin mijinta sai an shirya da haka yabar a ranshi.....

Bayan sun zauna bada dadewa ba alqalin wasa yafara shela akan kowa ya shirya za'a fara gabatar da wasa hakan yasa Zubaina ta maida duban ta wajen bayi saidai ba, sake dubawa tayi har ta fidda rai da ganinsa sai ta hango shi layin farko,sai murmushi yakeyi saita samu kanta da yin murmushin ita dai duniya Umar yai mata musamman idan tana ganin sa cikin walwala.... mai sanarwa yace."za'a fara wasan takobi za'a fars da Jaruman Yurii su da na Baizar take aka fara kiran sunan Jaruman da za'a fara karawa dasu, batare da bata lokaci ba suka fita kowa da takobi a hannunsa suka tafi wajen Sarakuna suka kai gaisuwa inda Sarki Abdullatib yai masu nuni da suje wajen gimbiya Rahama ita zata basu izinin fara wasan suna zuwa suka kai gaisuwa ta dauko bakin kyalle ta kalli Zubaina murmushi kawai tayi mata sannan gimbiya Rahama ta saki kyalen, baki dayan su suka koma saman layin da akaima zobe ana hura usir aka fara kaftawa kowa yanaji da Jarumtar shi...sharadin wasan ba'asan mutun ya fita daga cikin layin ko kum aka daka kasa shikenan an cika, akaita fafatawa da juna sunkai minti biyar ana abu daya daman minti goma aka bada,amman ankasa kai kowa kasa har saida aka hada jiki amman ba wanda aka kai kasa,har saida ya rage saura minti ukku lokacin su ya cika sannan Nura jarumin Baizar yakai jarumin yurii kasa....take wajen ya kaure da ihu musamman yarima Yusuf, Nura yasa hannu ya dago abokin karawar shi nan suka koma suka kara mika gaisuwa wajen gimbiyoyin su sannan suka koma wajen zaman su.....
Bayan sun zauna da minti goma aka kara kiran wasu Jaruman saidai wannan karan Ammar aka kira sai wani Ahmad daga cikin Jaruman Kesar batare da bata lokaci ba aka fito fili sukaje wajen gimbiya Rahama ta jefa masu wani jan kyalle,aka fara karyawa kowa sai gwada gwanintar shi yakeyi har suka cinye lokacin su, aka kara masu minti biyar haka suka cigaba da karawa ko minti ukku ba'a karaba Yarima Ammar ya fidda Ahmad cikin layin baki daya wajen ya kaure da ihun murna,danko Sadauki murna yakeyi kamar me, haka akaita kiran jarumai kala kala sai ci akeyi,sannan aka tafi hutun minti talatin kafin a cigaba dayin wasa, koda suka koma abinci kawai sukaci sannan Sadauki yasake hadama Ammar ruwan wanka,duk suka sake shiryawa, itama Zubaina tana gama shiryawa madara kawai ta iya sha gimbiya Rahama ta biyo mata sadda suka koma har anfara wasa,suka zauna wannan lokacin Aryan ne a cikin wasa shima haka akaita kaftawa,saura kadan akada Aryan Allah yasa ya tade abokin wasan shi yayi nasara....hatta Sarki Abdurrahman ba karamin dadi yaji ba,da harya fara fidda rai da nasarar dan nasa aka fara raba kayan sha dan jika makoshi sannan aka fara kiran jarumai ana kiran Jameelu Hassan Zairana akaji shiru, tunda aka koma hutu zazzabi ya turnike shi kamar zai mutu shiyasa Sarki Abdurrahman yabar bayi ukku dansu kula dashi, Yarima Aryan ne yaje ya bada sunan Sadauki duk waje yayi shiru ba alamun jamilu can sukaji mai shela na kiran."Umar Adam Zairana."Mai martaba yaita kallan Umar cikeda mamaki shi kanshi baiyi tunanin shi zasu bada ba,yayin da Umar ke waige waige duk mamaki ya kama shi sai yaji kamar ba shi ba saida Ammar yazo yai mashi magana sanann ya fito a sanyaye.
Zubaina keta kallan Umar cikeda mamaki da tarin al'ajabi yana fita ya wuce wajen Sarakuna shi da abokin karawar shi suka kai gaisuwa Sarki Abdurrahman sai kallan Umar yakeyi kallan dashi kdai yasan ma'anarsa sannan sukaje wajen su Zubaina wannan karon ita ta dauko farin kyalle tana murmushi ta saki kyallen suka koma filin daga....gimbiya Rahama keta kallan Umar takasa daina kallan shi har saida ta...


JAMEEY❣️


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan layukan 08160508316/07034464517.

Koda Umar suka koma cikin fili hannunsa rike yake da wani irin zareren takobi sai walikiya yakeyi basu wani bata lokaci na suka fara fafatawa shida abokin wasan shi....baki daya mutanen Zairana jinin su na kan hakaifa gani sukeyi kamar Umar zai iya kada su.
Wasa yayi zafi inda kowa ke gwada tsantsar iyawarsa da Jarumtar sa saida Jaruman suka kwashe sama da minti biyar suna abu daya...amma abu yaki karewa sai gabzawa sukeyi,yayin da ciwon kai ke dawainiya ds Umar ji yakeyi kamar zai fadi kasa daurewa kawai yakeyi haka sukaita fafatawa cikin ikon Allah Sadauki yasa kirjin shi ya bugi abokin karawar shi take ya fadi kasa wanwar har saida ya wuntsile ya bar cikin layin baki daya....take wajen ya kaure da ihun murna da gudu Jaruman Zairana sukazo suka daga Sadauki sama sai murna sukeyi hatta Sarki Abdurrahman saida yaji dadi aransa...Yarima Aryan kuwa yakasa motsin kirki tsabar mamaki,baki dayan su basuyi zaton haka ba domin duk wanda yaga Umar anayinsa baka taba cewa yasan wani abu Jarumta bare har yakai ga ya kware ga iya sarrafa takobi.
Tunda Umar yaci wasa gimbiya Zubaina ke jin dadi ba karamin murna takeyi ba batasan sadda ta riko hannun gimbiya Rahama ba tana tsananin jin dadi,mamakin Zubaina ya lullubeta gashi dai BAWA ne yaci wasan amma sai murna sukeyi akasa zuciyar ta tana yaba yanda Umar din yayi kokari....koda Jaruman suka sauke shi zuwa yayi wajen Sarakuna yakai gaisuwa sannan yaje wajen su gimbiya Rahama yakai gaisuwar girma,dan daga masa hannu tayi kallan sa kawai gimbiya Rahama keyi shiko murmushi kawai yaima gimbiya Zubaina.
yata fi zai koma cikin bayi yarima Aryan ya hana shi ya bashi kujera ya zauna cikin Jarumai....Sarki Abdullatib ya tambayi Sarki Abdurrahman."wanene wannan yaron?."shi kanshi saida yayi mamakin tambayar da yai mashi...amma sai ya bashi amsa a takaice"Sunan shi Umar kuma ɗan Sarkin bayin Masarauta ta ne"gaskia yaron nan ya shigar mani a cikin zuciya badan bawan amana bane lallai da ka siyarmin dashi."take Sarki Abdurrahman yaji kishin maganar da abokin shi yai mashi sai yaji bazai iya saida ma kowa Umar ba saboda ya wuce duk wani tunanin shi baki daya"kaga yaron nan akwai nagarta ga Jarumta gashi da kyau kuma dagani yasan darajar nagaba dashi."sake kallan Sarki Abdullatib yayi a karo na biyu sannan ya kara magana a takaice."gaskia ne Umar yana da nagarta saidai kasani tamkar ɗa yake a wajen mu,bacin haka da mun baka shi."shikenan."Basuyi aune ba sukaji ana shelar saka makon wasa da aka gabatar na yau inda Masarautar ZAIRANA tazo na farko,sai Masarautar SIRIKA tayi na biyu,inda Masarautar BAIZAR tayi na ukku,sai Masarautar KESAR ke mara mata baya sai Masarautar ROOWAN ke bi mata sai Masarautar YURII....haka akaita lissafo Masarautu har aka gama kowa ya tafi sai jin dadi sukeyi sai kuma gobe da karfe goman safe zasuci gaba da GASAR......
Tunda gimbiya Rahama takoma daki take mamakin Jarumtar Umar da karfin halinsa duk da gashi bawa,ita dai ranta na bata akwai abun dubawa a cikin lamarin Umar harta kwanta sai kuma ta tashi ta nufi dakin gimbiya Zubaina isketa tayi ta gama tasaka kaya zata kwanta kana ganin ta kasan tana cike da farin ciki marar misaltuwa saboda masarautar su sun lashe gasar farko,sallamar gimbiya Rahama tadawo da ita a tunanin ta."barka da zuwa gimbiyar Sirika."yawwa,yar uwa."bissimillah."ta zauna gefen ta sannan ta fara magana"Ranki shidade har yanzun ina cikin tarin al'ajabi."maida dubanta tayi kaco kam gareta tace."nami nene."? Ajiyar zuciya ta shide a sirrin ce tace."Ina mamakin wannan bawan da ya anshi wasan nan anya shidin ai nahin bawa ne? gaskia yai man kyau da kwarjini da yawa ina mamaki a kan shi har yanzun."wani irin masifaffan kishin Umar ya turnike Zubaina take taji ta tsani yaban da Rahama tai mashi,ita kanta saida tayi mamaki akan me zataji kishin Umar a zuciyar ta?amma saita wayance tace."haka Umar yake akwai shi kwarjini gashi jarumi ne na gaske"amma da gaske shifin BAWA ne."?"Kwarai kuwa shidin cikakken bawa ne."nayi zatan ko siyan shi kukayi."? "Aaa Sarkin bayin Zairana ya haife shi, bawa ne na amana."ɗan rausayar da kanshi tayi tace."gaskia yai mani kinga shi din ba bawan saidawa bane baccin haka dana siye shi"gaskia kam bawa ne na amana."(take takejin kanta a wani irin yanayi tana mamakin yanda idanun kowa ke kan Umar sai taji inama baizo gasar ba)a ranta take sake sake,tabata gimbiya Rahama ta dan yi ganin ta zurma a tunani."lafiya kikai shiru."bakomai."ta dan kakaro murmushi akan fuskar ta da haka sukaci gaba da fira kiran sallar isha ne yasa gimbiya Rahama yima Zubaina sallama sanann tace saida safe,itako Zubaina a lokacin take son ganin Umar kafin ta kwanta.Fadila tasa tai mata kiran Umar tanasan ganin shi......

_Ohh ni🤔 anya gimbiya Zubaina bata afka a tarkon son Umar ba gareku makaranta? Amma taya za'a ace gimbiyar Zairana ta buge da son BAWA???

A bangaren Sarki Abdurrahman ya aika akira mashi Umar koda dan aiken yaje a lokacin suna tareda Yarima Aryan a tare suka taho bayan sunyi sallama akai masu izinin shiga anan suka iske shi da sauran Sarakuna...Sarkin Yurii na gefen Sarki Abdullatib koda suka shigo dukawa sukayi suka kai gaisuwa sannan ya samu waje ya duka kan shi a kasa.
Sarki Kabir Usman ne yaketa kallan Sadauki yana so ya shaida shi amman yakasa gane ai nahin inda yasan shi."Umar."a hankali ya dago kanshi yace."Allah yakara maka yawan raibarka da dare"yawwa Umar,ya gajiyar gasa."Alhmdullh"dan gyaran murya Sarkik Abdurrahman yayi yaci gaba da cewa."Kamar yanda kaji kirana dama yan uwana suka ce aikiraka saboda kayi wasa mai nagarta kuma ka birge su ainun."gaskia ne Umar kayi wasa mai nagarta muna maka fatan alkhari Allah yakara hazaka."Amin,Umar nagodiya marar iyaka Allah yakara girma."dan shiru ya biyo baya Sarki Kabir yace."ina mamaki sosai akan yaron nan dagaske shifin bawa ne?"Abokina kenan,Umar amintaccen bawa na ne"ajiyar zuciya yaja yace."Hakane,saidai naso in shaida wannan fuskar"A ina."? Baki dayan suka hada baki wajen tambayar shi"na manta gaskia,ammayaso yai mani yanayi da Sadaukin Burhaan"baki dayan su saida maganar Sarki Kabir ta taba su kowa ya gaza cewa uffan sai kuri da sukaima Umar da ido suna al'ajabin maganar sa saidai sun san Sadauki ya tafi Kasar Mali kamar yanda mahaifin sa ya rubuto masu a wasika."Anya? shima Umar din Jarumin gaske ne,kuma Sadauki ai yayi tafiya."da haka kpwa ga gamsu." "Allah ya bamu nasara."Amin...Umar zaka iya tafiya."Nagode Allah yakara daukaka."da haka ya tafi.
Tunda Sarki Abdurrahman yaji an ambaci Umar sunyi yanayi da Sadauki ya kasa zaune ya kasa tsaye ba abinda ke damun shi a halin yanzun sanin ai nahin asalin Umar waye shi?daga ina yake?wane al'amari mutane ke gani akan shi?daga cikin su harda shi karan kanshi!tunda yake bi taba samun bawan da yagaza samun kwanciyar hankali akan shi ba sai akan Umar ganin farko da yai mashi saida ya kokonto akn asalin Bawan taka da akace shidin Bawane a hankali ya koma ya zauna samn kujera ya sauke nauyayyr ajiyar zuciya a zahiri yace."ance Sadauki yaje kasar Mali kai taimako mi zaisa a dinga dnganta Umar da Sadaukin Burhaan!?? Da haka ya watsar da zancen baki dayan shi duk da ya kudurci sai yasa anyi masa bin cike waye ne UMAR!....

Koda suka fita sallama yaim Yarima Aryan yakama hanyar masaukin shi,dan yasan Abba Ado yana neman shi,tafiy yakeyi a nutse kasancewar garin ya yafara duhu sboda wata ya tafara tsufa.
Hannayen sa ya goya a saman bayan yaci gaba da takon sa yaji ana kiran shi,a hankali ya waiga yaga Fadila,gaisawa suky sanann ta fada mashi sakon gimbiya Zubaina sai da yaji faduwar gaba ta dirar mashi karon farko da yaji sakon Zubaina ya sashi faduwar gaba badan komai ba saboda baisan me zatace mashi ba,gashi ya gaji da yawa yana bukatar hutawa.a haka ya daure ya bita suka tafi har masaukin ta,sallama sukayi ya tsaya waje,Fadila ta shiga ta fada mata zuwan Umar cewa."ki shigo dashi."angama ranki shidade."bayan fitar ta ta daelwo dashi dauke da sallama a bakin sa ya shigo,samun ta yayi zaune saman dardumar sallah tana tasbihi..tana jin shigowar shi ta bishi da ido harya duka gabn ta ya gaishe ta bata daina kallon saba ta amsawa cikin sakin fuska."ya gajiyar gasa."?sadda kanshi yayi kasa yace."Angodema Allah."murmushi ta sakar mashi du da kans na sadde a kasa tace"Ashe kai Jarumi ne Umar? har Jarumtar ka takai haka."?sai a lokacin ya dago kanshi ya kalle ta ya sake kauda kanshi gefe yace."Allah yakara maki daukaka,ni ba Jarumi bane karambani ne kawai irin na Umar."Umar."ta kira sunan sa a kausashe saida ya sakar mayar da hankalin sa kanta taci gaba da cewa." lallai kai Jarumi ne ,dole abaka lambar yabo."nagode."yace a takaice."Umar."na'am ranki shidade."zanso gobe in Allah yakaimu idan an kammala gasa ina san zan maka wasu 'yan tambayoyi"Allah yasa na sani" ya fada ynajin zuciyar sa na duka kadan kadan."Umar kasani,saboda suna da matukar muhimmanci a rayuwar ka"shikenan uwar dakina,Allah yakai mu lafiya."Amin,zaka iya tafiya."har ya juya zai fita ta kuma kiran sunan sa."Umar."a hankali ya juyo yana kallan ta baice komai ba."ina maka fatan alkhairi,Allah yaci gaba da baka nasara"murmushi ya sakaar mata yace."Amin, nagode saida safe."yajuya ya fita.
______________
Talatu keta waige waige cikin tsakiyar dare hannunta dauke da fitila saida ta tabbatar ba kowa a hanya sannan ta doshi sai sashen Sarki Hamza tana isa ta duka tayi katon rami sannan ta binne wasu manyan layu guda hudu tana gama binne su take kasar ta baje tamkar ba'a taba binne komai tana gamawa da sassarfa ta koma,ta gayama gimbiya Masau'da komai ya kammala."angaishe ki Talatu inajin dadin aiki da ke."ba karamin dadin sakon Talatu taji ba ji take kamar anbata kyautar hajji...
shiko Abba Ado koda Umar ya dawo rungume shi yayi sai murna yakeyi saboda shine ya lashe gasar da akasa saboda yafi kowa yin wasa mai kyau da daukar hankalin masu kallo zaunar dashi yayi gefen shi yakara mashi kwarin guiwa,akan yakara dagewa akan gasar da sukeyi sannan yasa shi yaci abinci yayi sallah ya kwanta yana kwanciya yafara bacci ya fara mafarke mafarke mararsa dalili sai kuka yakeyi a cikin mafarkin da sauri ya tashi zaune duk zufa ta keto mashi."lafiya Umar kana bacci kana kuka."ya gaza furta komai sai kallan sa da yakeyi Addu'a Abba Ado yai tayi mashi, shima sai ya samu kanshi da kama addu'ar da Abban shi keyi mashi yana kwanciya baccin ya sake dauke sa,kallan sa kawai Ado yakeyi yana ta'ajjabi yana jin sa ba banza akwai dai abinda basu sani a tattare da d'an sa a hankali ya bushe masu aci balbal dake gefensa tana ci sannan ya kwanta gefen Umar din yai masu addu'a yana ta nazari shima har baccin ya shamma ce shi.


JAMILA JAMEEY
(Yar Mutan Kankia)


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan layin 07034464517

Shafukan kyauta sun kare domin mallakar naki contact this number 07034464517

kamar yanda kowa ya sani da misalin karfe goma na safe daidai aka fara gabatar da gasar tseren dawakai yau ma kamar kullun an fara gabatar da gasar inda kowace Masarauta suka bada mutun ukku ukku,yayin da Masarautar Sirika ta bada zaratan Jaruman ta guda ukku itama Masarautar Zairana suka fidda gwanayen su hakama ta Kesar,Baizar,Roowan,Yurii da sauran manyan manyan Masarautu.
Tsaye suke jere saman dawakai ko wane Jarumi ya hau kan dokin shi.ka'idar wasan za'ayi zagaye huɗu akan doki duk wanda yakai tuta a zagaye na huɗu shine yaci wasan.
Batareda bata lokaci ba aka fara fafatawa kowane Jarumi ya dage damtse yana nuna iyakar bajintar shi,gudu sukeyi kamar zasu bar kasar baki dayan su tafiya ce sukeyi mai nisan gaske sukayi zagaye na farko Masarautar Sirika ce akan gaba,a zagaye na biyu Masarautar Kesar ke jan tuta,ana cikin yin zagaye na ukku Aliyu ya faɗo daga saman dokin shi duk yaji ciwuka da sauri masu kula da Jarumai suka rugo da gudu suka dauke shi zuwa wajen da zasu ba shi kulawa.
Sarki Abdurrahman ya bada umurni Umar ya fanshi Aliyu batare da bata lokaci ba Sadauki yahau saman doki a lokacin har an kusa kai zagaye na ukku,banda gudu ba abinda Sadauki keyi kasancewar shine karshe sai ba doki wuta yakeyi kamar ba gobe kishin Masarautar shi ya darsu a cikin zuciyar shi,gudun da yake zabgawa bana wasa bane ga wani irin kwarewa da salo da yakeji na fisgar sa cikin kankanin lokaci Sadauki ya zarce kaf Jaruman nan...Ammar kebin bayan shi cikin kaftawar ido Sadauki yakai zagaye na ukku,yana ciro tutar yakaima gimbiya Zubaina tuta,murna da tayi bata misaltuwa yana bata ya juya sadda zai koma zagaye na hudu suma sauran Jaruman har sun harzuka suna san sukai zagayen karshe dama Masarautu ukku sunkai zagayen farko yanzun so ake duk Masarautar data kawo zagayen karshe ita ta lashe gasa.kowa ya zagade basuji basu gani gudu suke bakin rai bakin fama yarima

Please Login or Register in order to submit comment